Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kuka me kike yi? Kinawa Sultan Mehran kuke ne ko kinawa Noman Anwarulkharim kuka?"
Kasa magana nayi tare da d'ago kai na,.ina kallon shi.
"Idanun ki suna fadan min gaskiya me yasa ba zaki fahimci muradin ki ba? Me yasa kike son saka kowa kuka? Karki bawa kowa samar sakaki kuka domin wata rana da hakan za a sakaki kuka. Sannan kiyi hakuri tare da rungumar ƙaddararki saura kiris kici nasarar farko amma kuma kome zai lalace. Ki duba girman haka mana."

Kukan da nake ne ya kara yawaita, tare da kallon shi. A hankali ya mike tare da sauko ruwa a cikin wani akushin azurfa ya bani.  Na amsa a hankali tare da kafa kai na na sha ruwan me mugun sanyi ga dad'i, yace min.
"Ki duba girman dalilin da ya gaya miki  wasu kalaman ai abin a bayyane take, ki sallame NOMAN ya koma haka Allah ya nufa, kaddarar ki tana tare da Mehran."
"A'a baba wannan ba halacci bane, wannan son kai ne, taya zan rabu da mutumin da tun kuruciya make tare dashi"

     "Toh shi kenan, Allah ya tabbata da Alkhairi." Daga hakan bai kuma ce min kome ba, sai ma dauke ni da yayi na dawo inda nake, rike da akushin nan. Mik'ewa nayi tare da nufar cikin gidan sarautar, anan naga an bazama nima na. Yana tsaye hannun shi goye a bayan shi, ya zuba min ido, tsintar kai na nayi da kasa tafiya kafaffuna sun min nauyi, sakamakon irin kallon tuhumar da yake min, ina isa inda yake, ya juya min baya tare da cewa.
"Rakshan ku kai ta kebantaccen shashi."
      Babu musu suka wuce dani haramtacciyar fada, inda aka watsa ni a cikin gidan, tasowa tayi tare da d'ago ni.
"Sannun Ikram! Kinyi namijin kokarin da babu wanda zai iya, gashi nan dai saura kiris kuma kin fado daga tafiyar mu.".

        "Wai meye yasa kika sani wannan aikin ne?" Rike hannu na tayi. Sannan ta kalle ni.
"Da farko naso yaudarar ki ne, kamar yadda ya zama dabi'u ga duk wani ahalin gidan sarauta, dan haka na saka ki a cikin kaddarar Aamaan, daga baya sai na Fahimci kece kika iya razana min mutanen da ban razana su ba, Ranar da ya nime baki wakiliyar shi na Fahimci ya isa matakin da ya dace na dakatar dake haka kin gama min kome, amma sai na.
#Mai_Dambu
```Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Page 36

    Kidime na fara bin hanyar da naga ya bulla, da gudu gudu, sauri sauri. Har na kusan cimma shi tare da kiran sunan shi.
"NOMAN!!!!"
Na kwala mishi kira, fisgo ni aka yi da sauri na juya ina kallon shi, tare da juyawa nayi tare da kiran shi da cewa.
"NOMAN! Don Allah kazo." Kiran shi nake Mehran yana ja na, har yaga dai zan tara mishi jama'a, sakani barci yayi ta hanyar tab'a wuyana, sannan ya sabani a kafad'ar shi, muka shiga masarautan wanda babu nisa da kasuwan.
"Ka tabbatar ka nima shi, karka sake ya rayu!"

       Yana nufar kofar da zata kaika cikin farfajiyar dakaru ne a ko ina, suna ganin shi dauke da mace, suka shiga zuɓewa a gaban shi, har cikin gidan ya nufa da Ikram, ran shi na kara b'aci, tabbas lokaci yayi da zai dakatar da ita ga shiga harkan kowani namiji, tunda ya fahimci yanzun ta haɗu da wancan banzan.

         Haka ya ajiye ta, yayi ta yawo a turakar shi zuwa cikin falon shi, yana jiran Fudail. Kamar ya tafi yayi aikin da kanshi, amma babu halin haka yayi ta zuba mishi ido.
    --- Haka Fudail ya gama niman me kama da Noman bai samu ba, karshe dai ya dawo babu wani labari.

    ~~ Waiwaye.
Oman.
Zuba mishi ido Azizatul Nissah tayi tare da cewa.
"Kazo da al'amari me girma,  amma zan taimaka maka, domin  inda Ikram take ba sauki shiga gurin amma zan maka lamani daya, shine zan fita da kai ka gudu, ka tafi SAMAIND tana cikin fadar kasar, a matsayin baiwa. Amma maganar gaskiya Yayana da Nawwas cutarka zasu yi ba wai zasu bar maka ita bane.

   Yayana yana sonta, Ni kuma ina son Nawwas, shi kuma yana sonta, amma idan suka rasata zasu zauna lafiya sannan kai ma zaka same ta a cikin salama, idan kuma ka sake suka fahimci hakan tabbas zasu yi yunkurin kashe ka ne."

       Ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon Sarwat sannan yace mata.
"Na amince."
Haka kuwa suka shirya tare da fita bayan gari, karshe dai Noman da Sarwat suka gudu abin su..tafiyar da zasu yi a jirgin ruwa kwana biyu, sai gashi sunyi shi a cikin kwana ɗaya rak da wuni guda, ranar da suka shiga garin ranar Mehran ya dauki Ikram zuwa Madinatul Mah.

  Yaso ya bisu, amma babu halin haka. Domin Sarwat ya hana shi.
"Akan me zaka hanani bin bayanta?"
"Ikram tana tare da Sultan Aamaan! Idan ka sake ka bisu wallahi yagalgala namar ka zai yi, sannan kuma ya hanaka ita, d'azun naji wasu dakaru suna maganar cewa, ai dan ya bata Wakiliyar shi ce, Mahaifiyar shi ta azabtar da ita, dan haka baka san yadda aka yi har ya zame ta a matakin wakiliya ba, don Allah karka manta ni Maraya ne, daga kai sai ita nake dasu. Idan ka sake wani abu ya same ku, zan iya mutuwa."

    Kurawa Sarwat idanun yayi cikin tausayi, haka ya danne damuwar shi, har ya shiga fadar Sultan a matsayin me kula da dabobbin da ake ci, duk yana jin kome akan Mehran da Ikram,  yanayin da yaji labarin ne ya kashe mishi jiki, anya zata yarda ta dawo gare shi kuwa? Yadda kowa yake fadan albarkacin bakinsa.

       Lokacin da leken Mehran ya wuce a tunanin shi da ita suka wuce, sai daga baya ya lura babu kome a keken, shine ya juya tare da bin bayan inda keken ya fito, ya hango irin kallon da sukewa juna ita da Mehran, yaji zafin haka da kishinta, wato har ta manta dashi ta faɗa rayuwar wanin shi, yana nan yana dakin soyayyarta.

    Ko lokacin da ta hango shi kallon tsana da k'iyayyar yake mata, bawai kallon nazo gare ki mu koma bane.

            Shi yasa daga ta gan shi yayi maza ya b'acewa ganin ta, abin tausayi. Yana tafe hawaye na zuba daga idanun shi tare da danasanin akan zuwan shi da yabar ta kawai yasan Allah zai bashi wacce ta fita, amma haka ya dibo jiki ya tawo ba tare da sanin abin da take cikin shi ba.

     Muryanta da ihunta yana dankare a cikin ƙwaƙwalwar shi.
"Noman kayi hakuri mu koma daga inda muka fito."

Share kwalla yake tare da cewa,
"Bazan iya komawa ba, zan tsaya har sai itace tace min na koma zan koma, amma zan tsaya mata. Don Allah koda ina da rai ko bani da rai ka tsaya mata. Kalabi ce a tsakanin rawuna. Don Allah ka bata kariya."
  "Me yasa kake fadan haka? Me yasa kake niman kashe min zuciya ta, don Allah karka sare da wuri hakan"

         "KISHI a tsakanin zubda jini! Ba zan iya dauke kai na akan abinda Zuciyata ta rayu da son shi ba, koda zan iya rasa rayuwata sai na dauke ta mun bar yankin nan. Daga nan zuwa ranar da za'a fara zab'en matan sarki kasaka ido zan nimo ta"

      Ya faɗa tare da juyawa ya nausa cikin dajin.
  ~~~
"Noman! Noman karka tafi kabar ni, Ina sonka" na fada tare da ware idanuna akan Mehran da yake kallona, idanun shi tayi jajjajur,  huci yake kawai cikin shi ya kama da wuta, shi daya san halin da yake ciki. Kofin ruwa da aka ajiye mishi ya dauka ya shanye tass, sannan yayi wurgi da kofin. Ya taso yana hada hanya, tare da kallon ta.
"Ni zaki yagawa mutunci a cikin al'umma ta, Ni zaki ketawa haddi? Lallai kuwa zaki kan Karen da kike kira da Noman akan farantin karanunakan SAMAIND anyi gunduwa gunduwa da namar shi."

     "Lallai da kayi kuskuren da har karshen rayuwarka kana dana sani, Aamaan Kace zaka kashe min Masoyina? Kace zaka saka kan shi a saman tire karannuka suci naman shi? Ubangiji ya baka sa'a, kai Izza da mulggki haihuwar ka aka yi dashi, Ni kuma na rantse da Allah sai na nuna maka mafi girman izza da takama, ka tab'a min Masoyina!"

       Shiru nayi ina kallon shi, kafin na zube gwiwata biyu, na hada hannu na tare da cewa.
"Ka saka Ni duk abinda zaka saka Ni, ka min duk abinda zaka yi dan daraja Soyayyar da kakewa Iyayen ka, na zama fansa ga rayuwar Noman. Idan  akwai abinda kake bukata ka"  bakin shi rawa yake tare da kallo na, jikin shi babu inda baya rawa, zama yayi a gaban ta yana kallon yadda take kuka, tabbas yayi kuskuren ajiye ta, a matsayin sirrintacciyar shi.
  
Me yasa zuciyar shi bata mishi adalci ba, me yasa ba zata iya hakura da zama da ita ba, kuka take sabida wani? Ba dan shi ba. Kura mata ido yayi yaga da gaske dai sabida Noman take kuka sai yaji zuciyar shi kamar zata fado, magana yake son yi amma kamar an cika mishi iska a kirjin shi zuwa wuyar shi, kura mata ido yayi. Dakyar Allah ya bashi ikon furta mata.
"Sabida shi kike kuka?"
D'ago jajjayen Idanu ta tayi tare da saukewa, sannan na ce mishi.
"Taya bazan yi kuka ba, watanin goma sha ina wata duniya yana wata duniya, Aamaan me yasa ba zan mishi kuka ba! Don Allah."

Girgiza zai yayi tare da mik'ewa yana faɗin.
"Na haramtawa kowani namiji ke har abada."
"Wani irin son kai ne haka? Idan dan budurci na nake faffutikar ganin bayan shi, zoka amsa. Ka kyale mana rayuwar mu"
Na fada da karfi, sake kofin ruwan hannun shi yayi tare da juyawa yana kallona, ina tsaye tare da yaga rigar jikina, har kasa. Warware daurin kirjin na fara yana kallona, cike da al'ajabi, har na ware ya fadi kasa.  Cire komai nayi ina kallon shi.

    Tare da zuba gwiwata a kasa, ina warware gashin kai na, sannan na d'ago mishi maganar da yayi jiya.
"Duk da bani da daraja, na kuma zubda wani darajar, ka barni ka rayu da shi. Ko kuma sakamakon da zai biyo baya ba zai maka kyau ba."

       Tab'e baki yayi tare da barin d'akin ranshi a b'ace,  ya nufi shashin Mahaifiyarshi, tunda ya isa ta mika mishi wani tulu da ruwan giya, ya jima rabon shi da sha, amma yau da yake cikin damuwa, yana sha'awan sha ko zai yi barci, dan haka ya shiga tultula shi a cikin shi sai da ya shanye tass, sannan ya lumshe idanun shi, so yake yayi magana amma ya kasa, baya son tarwatsa mata damuwar shi tunda bata koya mishi yadda zai fadi na shi damuwar ba.

     Abinda ya sani ya ginu akan kaɗaici kuma yana da yakinin kadaicin ce ajalin shi haka yayi ta nazarin abinda ya faru, gefe daya surar ta yake mishi gizo, duk da ba wata shahara tayi ba, ko wani abu da zai nuna a cike take ba, amma kuma hakan yana da matukar muhimmanci ya bashi aji na musamman, dan haka ya lumshe idanun shi, kana ya kuma buɗe shi, kamar yanzun yake hango tsayayyen kirjinta tare da d'an karamin cibiyarta wanda yake dige a shafaffen maran ta zai ce ko ciki ne oho, idan bai kaucewa gani ba, bayan da cikin a hade suke, juya mishi ita akayi yana kallon tudun cinyoyin ta tare da hango bayanta wanda ya fidda wani fadi gashi kamar dasa mata akayi.

    Lumshe idanun shi yayi tare da sake murmushin jin dadi, yana kallon inda take mishi gizo, kuma dago kai yayi yana kallon yadda take juya mishi, tsintar kan shi yayi da wani irin yanayi, ya mike a hankali.
"Ina zaka Mehran?"

  Girgiza mata kai yayi sannan ya ficce daga cikin shashinta, ya nufi nashi. Tunda ya shiga ya same ta ta saka kayan, b'ata fuska yayi sannan ya koma saman kilishi ya zube daga nan dai barci.
Wanda yake cike da mafarkai, akan Noman ya gudu da ita, haka yayi ta walagigi da niman ta, har ya gaji, mafarki daya yake nanata kan shi, har giyar  ta sake shi ya farka, tana kwance.

          Tun daga lokacin ya saka idanu akan Ikram, wacce ta kuma lalacewa, bata cin kome idan zata yi sallah tayi ta faduwa kenan, sabida rashin abincin da bata ci, amma taurin kai irin nata, ya hanata hakura da burinta, ita kawai ta fita daga gidan.

         Bayan kwana biyu, aka bata wakiliyar shi, sosai bayi mata suka sami yanci a cikin su har da Inam, wacce take hannun Sultanah Hoyam. Tunda ta zama wakiliyar shi baya barinta sakat, duk wani abinda zai rubuta ko zai kafa doka itace ke rubutawa, wani lokacin idan aka turo sako ita ke karanta mishi, tunda ya fahimci haka kawai sai ya tsiro mata karatun dare, wato tsofin Littafin masarautan shi take karanta mishi yasa a kwaso. Gashi babu halin ta gaji zai tsiro da masifa da tsaki tare da mita, har dai ta dawo kusa dashi wai dan karta yi tunanin Noman ne, haka bai ishe shi ba, dai da ya tabbatar ya saka mata dokar bata fita wajen masarautan.

Lokacin da aka turo yaran Gwamnonin Yankunan SAMAIND, itace tayi mishi hira yana zaune tayi ta zance dashi, gaba daya ya dauke kan shi kamar shi ya rako ta, ba ita bace ta raka shi lambun ba, haka yayi ta juyata son ran shi kuma ba zaka tab'a jin ya rarrashi ta ba, asalima nuna mata yake duk abinda zata yi dolen tane. Kuma dokar shi ce.

    ~~~
Oman.
"Matukar Noman ya ci amanar mu, toh tabbas zamu kashe shi har lahira, Sannun kanwata kinyi aikin da muke bukata, idan da mune muka saka shi yaje can ba zai yarda ba, amma da kika kawo hikimar hakan kome ya tafi yadda ya dace....
Washi na gaji.
```Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Page 38

"Sai na Fahimci ashe bazan iya wannan b'arnan ba, domin Mehran ya d'aga muryan shi sabida ke? Ya kuma ragewa Hoyam matsayinta tare da rage na mahaifina. Ikram na Fahimci kin yin min abinda ban ma saka ki ba, Nagode sosai. Amma ki sani baki gama aikinki ba, domin akwai mutanen da sun shigo domin daukar fansa da laifin da nayi akan Mehran."

      Hawaye ne ya zubo min tare da rike hannunta, bakina ya gaza furta kome kallon ta nake a hankali ta cigaba da cewa.
"Sun dauke Jasrah na kawo ta ne domin tayi min aikin da kika yi sai na fahimci bata da bushewar zuciya irin naki.

      Bata da kome bata da kwarjini da kamala, bata da nutsuwar zuciya da ruhi, na san nayi laifi masu girma, tun daga ganin ki na fahimci kece zaki share min kuka na, amma ban tab'a sanin cewa kina da naki rayuwar ba, na zata idan kika zama makusanciya da shi zai sanya ki manta kome da kome ki fuskanci wata rayuwa, sai na Fahimci ba haka ba.

              Mehran yana rayuwa ne ba tare da yasan me yake yi ba, Mehran yana rayuwa ne ba tare da ya gane halin rayuwa ba, amma haduwar  shi dake ya sanya fahimtar darajar da Allah yayi mishi. Shairah, zo ka mata bayanin yadda zata fahimta."

"Ba zan fahimci sakon da zata shiga bayan wanda zuciyata take ciki, don Allah karki kara labta min azabar da nake ciki. Me yasa sai ni? Me yasa ba zaki zabi wata tayi miji aikin ba sai ni? Wato mareniya wacce bata da gata da galihu na shigo tsakanin ku kuna gwara kai na, meye nayi muka haka ne?

   Me yasa na fito karamar ahali, shin kuskure na ne ko Kuskuren kaddarata ce, me yasa kowa yake son cillani wata rayuwa na daban, meye laifin rayuwata?"

       Na fada da karfi ina kuka, tare da shasheka, na rasa Uwa na rasa Uba, na rasa kome nawa, sai yau kalaman Ummina yake dawo min da tace.
```Bilqusul Ikram! Duniya tana da fadi da yawa, ƙaddara mace ce da ba a san me zata haifar ba, ina ji a jikina bai zama dole na amfanar da gaba ba, amma tabbas rahamar Ubangiji yana bibiye da rayuwar wanda yayi imani dashi
   Karki manta! Halayyar da dabi'u suna tafiya ne kunnen doki, gashi ba zan kai ba balle nace zan so ki rayu kamar sarauniya! Zan so naga yadda zaki amshi karfin mulkin```

         Ajiyar zuciya na sauke tare da kallon kasa, hawaye na zuba min, abinci ta ajiye min da kanta tare da zama a gabana, wanke hannun tayi sannan ta fara diban abincin wanda aka dafa shi da nikekken nama, tana bani a baki hawaye na zuba min, itama haka. Tare da kallon yadda idanuna suke zubda kwalla.
"Ya kamata na cire wannan abun ki huta kema, ki rayu kamar sarauniya! Kinsan me ake kira da mulki? Ki zama sarauniya yana nufin ki adana darajar ki da budurcin ki ga sarki ne! Ina son ranar da ya amshi budurcin ki ya zama itace ranar da za a kiraki Sultanah Bilqisul Ikram Mustapha, ina son wacce ta iya fitowa daga yankin gabashin sahara ta mulke fararren fatan wannan yankin.

       Ina son izzar da nake hangowa da ikon nan ya tabbata akan ki, zama Magajiyar sarauta ba abu ne me sauki ba, idan har zai zo da sauki toh ina rokon Arzikin kar a tab'a kimar yaron can! Kar wani namijin ya kusanci nahiyar shi, ba dan Ni ba, ba dan na isa ba, ina rokon a kare budurcin shi domin cikar muradin mu, so nake ki wargaza."

    "Hmm!" Na fara dariya ina kallon ta, tare da cewa.
"Na wargaza rayuwar su, ki wargaza nawa. Bayan nasan kome akan ku ahalin Abbasiyyah, cin amana yafi yankan takobi kaifi a cikin zuciyar ku, cin amana yafi kome faruwa a cikin gidan nan..
     Wata goma sha daya nayi ina zaune daga nan zuwa nan har na isa shashin Sultan Mehran, yau kice zaki min farar dabara."

"Akul Ikram! Kamar yadda zuciyar ki take cikin kauna da bege haka itama nata zuciyar take kwana da begen shi, taya hakan zai kawo karshen rikicin masarautan nan? Sultanah Fazilatul nisa ce a gaban ki kike gaya mata maganar da tafito bakin ki?"

"Toh d'an daudu idan ban gaya mata ba, bari na tashi nayi rawa saboda ina murnan kun kashe min rayuwa? Jinka dan an haife ni a karamar ahali zai hana na kasa kwatar kai na ne? Tab kayi kad'an ka kasa," na faɗa.

A madadin naga fusace ko fushi sai murmushi nake gani me hada da zubar hawaye, tana me mika min abincin. Kallon ta nayi sannan nace mata.
"Kuka kike?"

"Hmm! Eh"
"Ni ne da kuka bake ce da kuka ba."
Murmushi tayi bata kuma ce min kome ba. Har ta gama bani abincin sannan tace min.
"Tun ranar da aka kawo ki na sami labarin irin halittar ki! Koda suka mika ki ga Hoyam nayi fatan ta dawo dake waje har akawo min ke? Idan har irin halittar jikinki Mehran zai samu. Cikin rayuwar shi tabbas sauran tarkacen da ake shirin zab'a mishi su. Sunyi asarar babba. Ni nan zan shawo kanki yadda zaki rike duniyar shi, ki zama kece a ranshi ko a ina ne!"

       Daga haka ta bar falon, tare da kallona.
"Ni budurci na da Ni kaina, na Noman ne"
Cak ta tsaya sannan ta juyo ta sake min murmushi, kafin ta wuce abinta.
  Ihu da bori nayi ta musu, tare da ture kome, babu wanda ya kuma bi ta kai na, wato ga mahaukaciya.
~~~
Duk wanda yake tare dashi sai ya fahimci, halin da yake ciki, duk wannan kuzarin da mulkin babu, sai dai ya koma musu wani irin masifaffen mutum, d'an kuskure idan aka aka mishi zai saka a kai mutum gidan horo,

     Mutumin da yabar giya, sai gashi ya dawo da shan giya sama da ruwan shan shi, a hankali Sultanah Hoyam ta shiga turo mishi yan mata, a duk lokacin da yake buge zata saka a kawo mishi mace, amma dake har cikin ranshi bayan son haka bai tab'a afka musu ba, haka zai gama shaye shayen shi, har ya  yayi barci babu abinda yake hada shi da mace. A duk lokacin da ya farka zai zauna yayi ta kallon kanshi a madubi, Sabida tashin hankalin da yake zuciyarshi.

Kasawa ne ace macen da take karkashin kulawar shi wani namijin ya zo ya dauke ta, Zubewar mutuncin shi ne da na daular shi, sannan kamar watsawa kanshi kasa yayi a ido, me zai cewa Mahaifiyar shi, idan ta mishi gorin wani namijin ya kwace mishi macen da take karkashin kulawar shi?

   Me zai cewa mutanen fada da kowa ya gama sanin ya kawo tane dan tayi goggaya dasu, me zai cewa Fudail da ya raba tsakanin su, lallai akwai tashin hankali a gaba kadan.
Tunda ya saka aka kai ta kebantaccen shashi, da kanshi ya shiga fita niman Noman.

Baya tashi fita sai dare, haka yake bin gidan baki, kullum sai ya fita, a irin haka, har ya isa wani gidan baki dake wajen gari.

   Suna cikin hira, ya shigo gidan. Kallon shi suka yi tare da cewa.
"Waye kai?"
"NOMAN nake nima?"

     Mik'ewa yayi sannan yace mishi.
"Gani nan"
"Ko za muje waje?"
"Toh!"
Fita suka yi Sarwat zai bisu Noman ya hana shi.
"Ka zauna babu wani abinda zai faru."
Yana fadar haka ya bi bayan Mehran, har waje..yana tsaye, a hankali ya nufa gaban shi..
"Gani nan!"
Shiru yayi yana kallon shi, meye noman ya fishi da har Ikram ta zabe shi akan shi? Tab'e baki yayi sannan ya cigaba da abinda yake, kan shi a kasa yana wasa da gashin kan shi, cire mayafin fuskar shi yayi tare da d'ago kan shi, yana kallon Noman.

     Maza irin gurjiya, ba gaba da gaba ba, ko ta bayan sai an shirya, ja da baya yayi, cikin nutsuwa da mamaki tare da sauke kan shi ƙasa.
"Kana bukatar gabatarwa ne?"
"A'a Sultan Aamaan Mehran! Bana bukatar gabatarwa, Abinda yake gurin ka nazo amsa."

   "Ko?" Ya faɗa a sanyayye, yana kallon Noman.
D'ago kai Noman yayi yana kallon shi, yana girmama al'amarin mulki, yana ji a bakin  mutane yana da Izza, yau gashi ya gani da idon shi, domin kuwa maganar ma ya kasa bashi lokacin shi yayi magana.

      "A bisa adalcin da zan maiay, shine zan saka gobe a kawo maka kyauta na musamman, daga dangin zinari, lu'ulu'u, da wasu abubuwan bukata, ka bar min ita! Kayi tafiyar ka duniyarka, idan ta nutsu zan kawo ta taganku. Ita din muradina ce."

"Gaskiya wannan adalci bane,  ba zan iya fansar da soyayyar mu akan kananun abun duniya ba. Kabani ita na koma da ita, kamar yadda tazo."  Inji NOMAN,
.ware idanun shi yayi tare da kurawa noman, a hankali ya dage takobin shi.

          Tare da zare ta daga kubenta, a hankali yace.
"Da alamu zan aika ka inda ba  zaka dawo ba."
.   "Idan har akan Ikram ce tabbas sai da na rasa rayuwata."

   Cikin fushi da fusata tare da d'aga takobin, aikuwa aka fara iska, me ƙarfi tare da alamar garin zai iya samun ruwan kankara ko kuma dusar ƙanƙara.
      Azzabbrn yaki ne ya sarkafe a tsakanin su, kamar zasu hallaka juna.
    ---
A firgice na farka sakamakon mafarkin da nayi Noman yana yaki da Mehran, ina tashi ban Nime izni ba, nayi ficewa ta tagar gidan.
Gudu nake sakamakon iskar da take kad'awa, shashin Mehran na nufa, da Fudail na hadu.
"Ina Mehran?"
"Ya fita niman Noman?"
Hannuna dukka biyu na saka a bakina, tare da kallon shi. Na kasa magana, da gudu na juya ya rufa min baya,  haka

Please Login or Register in order to submit comment