Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya rayuwa babu ruwa ba, kamar yadda zai iya rayuwa babu abinci matukar akwai ruwa zai iya samar da abinci.

      Ba zaka gane baiwar da Ni'imar da Allah yayiwa Ruwa ba sai ka shiga sahara babu ruwa dai abinci nan zaka ga mutane da yawa suna mutuwa, amma idan da akwai ruwa zaka samu zasu kai labari duk lokacin da zaka ci abinci dole ka bukaci ruwa, dukda dashi ake sarrafa abincin, wannan shine dalilina na amfani da ruwa a cikin tsarina."

      Shiru kowa yayi musamman yan matan da suke ganin kamar sun lashe zab'en, sai juyawa suke suna kallona, wato nayi abinda basu iya ba, bayan an gama wannan sai aka bukaci mu dafa shayi. A tare muka tashi. Da haka iya ganyen shayin ne sai zuma.

   Tashi nayi tare da nufar Lambun da yake gurin na tsinko ganyayyekin masu kyau da kamshi, sannan na fara dakawa a hankali ina maida hankalina akan abinda nake, a cikin ganye akwai janye minnan nas, akwai ciyawar lemo,.akwai ganyen citta, da ganyen kanumfari, sai ganyen na'ana dan haka duk na dake su, sai ganyen ciyawar lemo ne ban saka ba, na barshi sai da shayin na dauko dafuwa na saka, a hankali kamshin ya cika gurin su kansu yan matan kallona suke kamar zasu yi ihu.

           Dan haka ina gamawa na zuzzuba a cikin kofunan sannan kuma na d'iga musu zuman,a hankali aka yi ya kai na sauran kafin aka zo kaina, suna zuwa Fudail yace.
"Sannun da ƙoƙari." Murmushi nayi mishi sannan suka wuce da shayin, kai na a sunkuye na zauna,.ina jiran sakamakon. Kamar yadda aka raba na kowa haka aka kai nawa ya dauka a hankali yana kallon yadda na sunkuyar da kaina.

                    A hankali ya kurb'a, dadda'ar d'and'ano da kamshi me gamsar da zuciya Yasaka shi d'ago kai yana kallona, kurb'an shayin yayi sanan ya kuma kallon yadda kowa yake shan shayin cikin gamsuwa, musamman Abrad da yake jifar Ikram da kallon duk da bata san yana yi ba.

              A hankali suka tashi suka fara bayanin su,.duk kusan abu daya suka yi dan haka ina mik'ewa nace musu.
"Gabaki daya ganyayyekin da nayi amfani dashi yana magani. Domin dukkan su, ana mana abinci da shi. Sannan ita kanta wannan shayin idan mura ta dame ka, aka hada maka kana sha da Yardan Ubangiji zaka ji sauki sosai, shi yasa na hada shi sabida nasan dayawa ana fama da ciwon mura. Kasancewar muna yankin da take da yawan dusar ƙanƙara. Ita kanta maganin sanyi ce."

           Zama nayi domin sun yarda da abinda na faɗa, can aka kuma zuwa da wani bayani. Inda Darakshan ya kawo bayanin kamar haka.

    "Kasancewar kina matsayin Sultanah sai sarki ya tafi yaki, kuma bai talakawa babu abinci a tare dasu, kayan abincin su ya kare, gashi Sultan bai bada Umarnin a raba ba, sabida haka ke a baki tunanin me zaki iyawa talakawa?

Sai manomin da yayi noma tare da saka tsammanin abincin shi zai kai labari, sai aka wayi gari d'an shi bai baida lafiya kuma yana da saniyar shi na hud'a, dan haka sai ya saka.saniyar shi da abincin shi a gaba wane zai sayar?

Sai na uku, mutane uku  sunyi laifi kuma ba a san waye mai laifin ba, dan haka sarki ya basu wasika akan su tafi can wajen gari su bawa dakarun. Sai kafin su isa sai aka fara ruwan sama, dan haka sai fada ta kama su. Har takai sun sake wasikar su a sunyi musayan wasikar, daya kuma yana rike da wasikar shi. Dan haka da suka isa gurin dakarun sai suka maida abinda ya kawo su, sannan aka amshi wasikar dayan su, aka duba..su kuma aka yanke musu hukuncin kisa? Bayan kuma daya ne mai lafiyan shin taya zaku gano me laifin?"

        A hankali Sakeenatu binti Abu Waqqas ta mike sannan tace.
"Idan Sultan bayan ba zan tab'a dukiyar masarauta ba, sabida babu hurumina a cikin wannan yanayin.
Na biyu kuma manomi zai sayar da saniyar shine domin  lafiyar d'an shi.
Na uku kuma a kashe su dukkan su biyu, domin koda za a tsananta binciken ba za a gane ne gaskiya ba. Wannan shine hujjata."

Azizatul Nissah ta mike sannan tace.
"Bazan yi katsalandan ga shiga harkan tallafawa talakawa ba, ai daman tun kafin a fara yaki dole zasu bukaci su tanadar da kayan abincin su.

   Na biyu manomi zai iya sayar da saniyar shi domin idan ya sayar da abinci bai da abinda zai ci,saniyar kuma ba zata isha shi ba.
Na uku, wanda za a kashe shine wanda yazo da wasikar."dafe kai Abrad yayi. Sabida sam amsar ba haka ban.

       A hankali akayi ta tafiya har aka zo kaina.
"Idan muka duba dalilin da yasan manomi zai fidda kayan abincin shi da saniyar shi ba ƙaramin lalura bane, domin abincin nan idan yayi tattalin shi zata kai shi har kafin faduwar damina me zuwa, dan haka babu hujjar sayar da saniya, abincin zai raba gida biyu ya sayar da rabi tunda yayi noman a wadacce, saniyar kuma da ita yake aikin nomar idan ya sayar da ita bai da wanda zai miki kwaftu, saboda dan shi bai kai wanda zai iya noma ba, shi kuma karfin shi ya kare.
Kuyi min hakuri na fara da amsar manomi ne..

A matsayina na Sultanah, aka wayi gari Sultan Mehran ya tafi yaki kuma bai ce min kome ba dangane da al'ummar shi, gashi akwai kayan abinci a cikin Baitul Malin masarautan! Zan duba soyayyar su da kaunar su ga Sultan Mehran,.zan saka ayi ta diban abinci cikin dare ana kai musu kofar gidajen su, domin ya rage musu zaman dar-dar da suke yi. Bayan nan idan suka gani washi gari addu'o'in su itace kashin bayan dukkanin mulkin shi da nasarar shi.

Sai batun masu laifi, akwai wani dabi'a na mai laifi ban sani ba ko wasu sun fahimci haka, amma idan mutum ya aikata laifi yana iya fin kowa firgice, sannan da zaka saka kanka a kirjin shi bugun zuciyar shi yafi na kowa, sannan abinda na Fahimta shine Mai laifin da ya fahimci shi za'a kashe shine ya dauke wasikar wancan,  badan kome ba yasa ni fadar haka sai dan hujjar da nake da ita. Duk yadda akayi mutane biyu da suke jajjayan nan sun bude wasikar su..shi na ukun su bai san meke faruwa ba, dan haka su biyu sun san meye a cikin wasikar su.daya ne za a kashe ba dukkansu ba."

"Shin ko Ikram zata gaya mana taya zata iya gane mara gaskiya, duk da, sun kafe akan cewa wasikar su ne?" Amir Hood ya min tambayar.
Dan mik'ewa nayi tare da gaishe shi, sannan nace mishi.
" Bayyana nayi bayanin domin mara gaskiya duk inda yake zaka iya d'ago shi, idanun shi yana yawan budewa, sannan shi kansa baya iya tsayawa guri guda ba,  jikin shi kuwa rawa yake yi, tsoro takan zame mishi shimfid'a akan fuskar shi. Bayan haka yafi kowa zakewa da rantsuwa."

       Na fada sannan na zauna sai lokacin na kalli Mehran da ya haɗa ya dunkule hannun shi, yana kallona, fuskar shi ta bayyana farin cikin shi. Dayawan dattawan gurin magana daya suke, yarinyar yayi kokari tana da basira.

Murmushi nayi ina me jin dadin nasarar da na samu, a hankali.suka yi ta bayyana mana sakamakon mu, karshe dai aka bankad'o tafiya na da nayi shi ya saka ban samun damar tsayawa a.matan shi sai suka barni a shugaban Kwarkwarorin shi. Mikewa Fazilatul nisa tayi sannan tace musu.
"Wannan sakamakon bai yi ba, dan haka Ikram itace matar Mehran, ko kuma allura ta tono garma..,
*Toh fa wata sabuwa....*
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

35
Cikin fusata Sultanah Hoyam ta mike tare da kallon ta, cikin fushi mara iyakata tace mata.
"Wacece ke da zaki saka mana ,doka Mu kuma mu bi?"

Murmushi tayi tare da gyara zama sannan ta kalli Ikram tace mata.
"Kin cika duk wata sharudan da ake bukata, dan haka kece yau zaki gana da Mehran! A matsayina na mahaifiyar shi, na baki shi gudan shi ba b'ari ba."

   Kallonta gabaki daya Emiraters councilors din, suka yi domin abinda suke gudu kenan shigar Fazilatul nisa cikin harkokin Masarautab,. Tunda da suka ji labarin bata mutu ba suka san cewa tabbas tana raye ne domin fansar ta, dan haka suka mike tare da kallon ta, kafin suka ce.
"Mun amince Yaran mu zasu zama Kwarkwarorin shi, sanan muna rokon Sultanah arzikin karta bawa Ikram karfin da zata juya a kalar masarautan."

        "Karya ne,  Mehran d'ana ne dan."
"Bani da lokacin ki, Ita wancan Yarinyar nake da Muradin a bata matsayinta! Ko kuma hmm!" Fazilatul ta sake murmushin mugunta.
Cike da mamaki nake kallon ta, domin dai nasan tana da nata Muradin idan ba haka ba, me zai saka ta kafe akai na.
"Toh an bar mata matsayinta a bisa sharadi guda uku! Sharadi na farko dole ta kasance budurwan! Sharadi na biyu dole ta kasance yar da tafito daga Masarautan? Sharadi na uku karmu kama ta da wani kuskure ko muji labarin wani mugun abu yafito idan ba haka ba. Hmm!" Yayi wani irin murmushi hade da kumshe bakin shi, yana kallon ta.

    Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Insha Allah! Na yarda da Allah kuma na yarda da ita, kuma Allah zai bamu sa'a."

Ta faɗa tana murmushi.
"Shin wai ince wannan kika tsayawa? Wannan kika tsayawa? Lallai kina bukatar nazari. Amma lokaci zai nuna mana."

   Takowa tayi daga sama, inda take zaune ta tawo har inda yaƙe,  sannan tace mishi.
"Mir Umdatuddawla ko kana da matsala da ita ne? Dan naga Yarka Yasmin kake taya kishi! Duk wanda yayi magana tabbas yayi magana ina da yakinin Yar shi yake tsayawa kishi, dan haka kowa ya zuba ido."

         Shiru duk suka yi tare da sunkuyar da kai, sannan ta juya kai ta kalle ni.
"Daga ranar da kika amshi matsayinki na Sultanah ina son ki shiga binciken sanadin mutuwar Abdus Samad, idan kika amshi ragamar Sultanah ina son ki bincika mike faruwa a cikin masarautan nan! Idan kika yi haka zaki taimakawa mijinki gurin bincike! Kina da damar tuhumar me yasa aka dakatar da mijinki akan muqamin sa? Bayan nan kuma ina rokon adalci daga gare ki na bi min hakkina akan kazafin da aka min. Ina tayaki murna."

      Daga haka ta juya daga gurin taron, tana me jin dadin ta wanke abinda yake ranta, tabbas tasan ba zasu iya dakatar da matsayin Ikram ba, kodan tsira da mutuncin su. Sannan ba zasu so asirin da suke aikatawa ya fito fili ba, dan haka ta barsu da tashin hankali. Domin kuwa matukar suka barta tayi magana. Zata iya fadar abinda zai daure su har karshen rayuwar su, dan haka suka yi farin ciki barin ta gurin dan tana magana da yawa, duk yan matan an kira su tare da karrama su.. sannan aka kirani daga karfe aka bani kyautar da yafi nasu, bayan na amsa ni dasu Izmah da Nimra muka bar gurin.

         Takawa Abrad yayi har gurin Mehran, ya kura mishi ido sannan ya mika mishi hannun, cikin girmamawa yace mishi.
"Kana ta farin ciki zaka auri budurwa ko? Koda yake naji an cire gwajin budurci. Domin wasu yan matan zawarawa ne, idan kuma dattawan masarautan ka suka ji labarin Sarki Abrad ya tab'a kwanciya da ita fa? Hhhh koda yake shima wancan ai sauran Abrad ya samu.

    Ka tambaye ta, tun bata kai haka ba, na saka mata girmana jikinta kuma ta dauke ni cif. Dan haka kasan dole sai ta cika sharadin budurci ko kuma hukuncin kisa ya haura kanta. Itama zata so na rufa mata asiri dan haka ka ajiye a ranka zaka fara jin kararrawan tashin hankali. Matukar ina raye Ikram tawa ce ni daya."

             Kura mishi ido Mehran yayi tare da sunkuyar da kan shi kasa, yana jin kamar ya dauki takobin shi ya dauke mishi kai cikin tashin hankali yake murza hannun shi, kafin ya d'ago kanshi yana murmushi yace mishi.
"Zan iya cewa haushin ka rasata yasa ake gaya min magana haka ba. Dan haka babu damuwa koda a gidan ƙaruwai na samo ta, tabbas zan zauna da ita."

      Cikin fusata ya kalli Mehran sannan yace mishi.
"Tabbas zaka yi kuskuren da ba zaka manta ba, domin zan kashe duk wanda yake tare da ikram, domin ita mallaka ta ce"
"Ina ga baka tab'a kowa Askandariya ka tambayi ina Yar uwan matanka take ba ko? Zanga yadda zaka iya hada kazamtar da kake shirin aikatawa."

Daga haka ya juya tare da barin gurin, domin jin kirjin shi yake kamar zata fashe, yana shiga ya hango ikram daga nesa, wani irin tausayin kan shine ya kama shi. Meye laifin shi da kaddarar ta yake walagigi dashi? Me yasa ba za'a barshi ya huta da ita ba, sai tashin hankali da damuwa. Kura mata ido yayi yaga yadda take dariya da farin ciki. Ji yayi wani kamar zai fashe da kuka domin kuwa yana hango yadda Abrad ya kwanta da ita, tare da hango Yadda Numan yayi ta juya ta a shimfid'ar shi.

  Wato maza biyu sun keta mishi alfarman shi, sunci mutuncin shi sama da yadda ake cin mutuncin wani a duniya, da takalmi suka dauka suka dake shi da shi ba zai mishi ciwo irin wannan da Abrad yayi mishi ba, ji yayi duk wata alfarmar da yake dashi ya tsinke gani yake kamar duk wata mutuncin shi sun tsinka mishi. Duk da yasan tayi aure baya jin haka yayi mishi ciwo kamar yadda Abrad ya nuna mishi ya kwanta da ita..mafi kololuwar ɓaci rai da ya tab'a ji a ranshi kenan.

    Dan haka ya bar abin a ranshi kafin yasan mafita.

  ***
Had'iye yawun Abrad yayi tare da juyawa yana kallon taron jama'a da suke watsewa. Ba dai Ikram Yar Joindah bace?

  . tabbas idan yarta ce ta haramta mishi, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun me yasa haka ya faru dashi. Lallai dole ya dakatar da kome ya tsaya Domin rusa Mehran da ya ikram, idan ba haka ba tabbas zai yi biyu babu, ya kwadaitu da jikin Ikram, dan haka koda zai mutu ya dawo wallahi sai ya shiga ya mata faca faca da ruwan jikin shi.

    Wannan shine tunanin da ya tsaya a ranshi, dan haka yayi wucewar shi zuciyar shi daya..yana haduwa da Nawwas ya gaya mishi abinda ya faru. Ba karamin kaduwa Nawwas yayi na, tare da cewa.
"Wallahi baka da kirki!  Me kake shirin aikatawa? Yarinyar da babu aure a tsakanin ku shine zaka shirya mata mugun makirci haka..toh wallahi zan gaya mata gaskiyar abinda kake shirin aikata mata domin ta farga daga abinda kake shirin aikata mata ai wannan rashin imani ne idan kanwarka aka yiwa haka ba zaka ji dadi ba, dan haka wallahi dai na gaya mata idan ban sami ganinta ba zan gayawa Mehran dan yaji abinda kake shirya musu.. son kan ka yayi yawa toh wallahi ba zan tab'a barin ka, ka lalata musu rayuwa ba, tunda kai kana da naka rayuwar!"

    "Nawwas ni kake gayawa Magana? Toh naga wanda ya isa ya dakatar da ni." Ya faɗa da karfi, nan fada yaso kaurewa a tsakanin su, dakyar wasu daga cikin dakarun suka raba su.

Cikin fushi Nawwas yace mishi.
"Wallahi ina sane da kome da ka aikata, kyale ka nayi kawai amma wannan karon zaka sha mamakin abinda zai faru."

           Cikin mugu mugun fargaba ya kalli Nawwas, sannan ta danne abinda yake ranshi.

"Na gina ka da hannuna, sannan Ni zaka kashe. Tabbas kai butulu amma zan baka lokaci ka nime yafiyana kafin na fusata akan ka." Inji Abrad.

       Dariya Nawwas yayi cikin takaici da haushi yace.
"Wato kai har dama ake bani na nemi yafiyarka? Toh karka yafe min, ka zauna a gurin na kyale ka ne, amma tabbas idan akwai wanda ya dace da Ikram ni ne ba kai ba, domin ni na fara sonta lokacin da na sayo ta." Hannun shi ya saka a cikin aljuhun shi sanan ya ciro jakar kudin da Abrad ya bashi lokacin da ya tura ya sayo mishi ikram.
"Wannan Shi ne, jakar kudin da ka bani, ita kuma da kudina na sayo ta, dan haka karka kuma alakanta kanka da ita, domin ni na barwa Mehran ita."

  .ihu Abrad yayi tare da kaiwa kasa duka, yana fadin.
"Wallahi baka isa ba, Ikram tawa ce wallahi sai na kashe ku dukkan ku, akan Ikram sai kashe kowa domin ita tawa ce. Kai ma ka fara gudu domin na kyale ka zanyi ba."

Wannan rigimar bata yi musu dad'i ba, domin karfi da yaji suka zama abokan gaba, kuma Abrad yayi alƙawarin sai ya kashe Nawwas shima kuma yayi alƙawarin sai ya fadi gaskiya kafin ya kashe Abrad. Da kyar aka fidda Nawwas daga cikin gidan, domin fadar sun tayi ƙamari Sosai.

     ~~~
Yana zaune yayi shiru tun da ya idaar da sallah, yake kallon waje yana son ganinta amma idan ya tuna zantuntukarka Abrad sai yaji kirjin shi yayi zafi, shigowar Fudail a karo na biyu ya sashi d'ago kanshi yana kallon shi.
"Sultan MEHRAN! Ikram tana son ganawa da kai."

            "Kace mata ba yanzun ba."
Ya faɗa fuskar shi a daure,
"Toh sai yaushe Mehran?" Na tambaye shi lokacin da na shigo d'akin, juyar da kai yayi tare da cewa.
"Ka fitar min da ita bana son ganinta." Ya faɗa tare da juya min baya.

"Akan me baka son gani na? Meye nayi maka da zafi da kak'i kallona, ko baka so na zama abinda kake bukata bane?" Na tambaye shi muryana yana rawa,
Mikewa yayi tare da nufo ni, bai yi wata wata ba, ya riko damtsen hannuna ya turo ni waje, sannan ta kalli Fudail shima ya fita dan baya son magana.

   Kasakai nayi ina kallon kofar Mehran, na rasa gane abinda Mehran yake nufi dani, kallon Fudail nayi domin shi daya ne kawai zai fidda Ni cikin duhun da nake ciki.
"Karki ga laifin shi. Sultan Abrad yayi mishi wasu maganarki wanda ban san me ya gaya mishi ba."

   Bakina yana rawa na kura mishi ido, sannan na juya tare da barin shashin sa, na nufi inda nake da zama, a hanyar wucewa ta naji Kwarkwarah shi wato Sakeenatu binti Abu Waqqas tana faɗin.
"Idan mace ta isa bata bin namiji shi yake binta" halin da nake ciki bana jin zai barni nayi magana kawai na kad'a kai nayi gaba abuna, sabida ba zan iya daukar tashin hankali biyu ba, ga nashi ga na wad'anda ban san kansu ba.

....
Tunda na zauna nake kallon madubi, abisa ka'idar zan kai mishi abinda da kuma zama dashi dan hira, sai dai shigowar Sultanah ta zuba min ido.
"Me yasa Mehran ya bukaci Jasrah bake ba."

    Murmushi nayi sannan nace mata.
"Eh naje d'azun nan kuma gaskiya ni bana son na amshi ragamar shi sai ranar da aka daura min igiyar shi a kaina, su kuma suna da damar shiga gare shi. Tunda matar da zai aura ce ni kamata yayi nabi tsarin addini da na Ubangijin."

Takowa tayi gabana, sannan ta zauna kamar yadda na zauna..kafin tace min.
"Addinin ki da Ibadar ki yasani mishi kwadayin ki, idan ba wani abu me karfi ba,.nayi imani da Allah ba zaki juya mishi baya ba, domin kuwa babu kwaɗayin duniya a ranki don Allah ga Mehran nan ki tsaya mishi Insha Allah zaki yi nasara."

   Murmushi nayi domin kuwa ban san me zance mata ba, amma kuma ina tunanin zan mata yadda ta bukace ni.
*Ana dara ga dare yayi....*
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

36
Kasa gane kan MEHRAN nayi kowa yana jin dadin mu'amala dashi ban dani, tun Fudail yana ƙoƙarin gano yadda zai magance matsalar mu ya kuma sassanta mu, abin yaci tura. A cikin kwana uku kacal Mehran ya nunawa kowa baya tare dani, domin kuwa Zanyi kokarin tinkarar shi domin magana yana gani na zai mike ya nemi hanyar barin gurin. Ko kuma yana gani na zai tsira fushi da b'ata rai.

      Bana jin dadin haka ko babu kome bai dace sabida Abrad ya gaya mishi magana ya nemi juya min baya, ranar da ya nime jasrah.  Dan sai da tayi kwana uku a cikin turakar shi, kafin  hudun ta fito, nan ne tana fitowa aka bata matsayin (Lady royal) tafi kwarkwarah ta kuma fi karfin a kirata da kuyanga, matsayi ne wanda yafi na kwarkwarah. Shi yasa tana fitowa ta fara gudanar da aikinta yadda ya dace. Abinda ta fara shine ta turo da wasikar lallai sai dai ina fitowa cikin su ina cin abincin.

    Sannan ta zab'a min bayi mata guda biyu, sannan ta turo min su.
      Ajiye takardan nayi sannan na kalle su, a tsanake kafin nace musu.
"Nagode! Sannan ku gaya mata bana bukatar kowa, ina da yan uwana na jikina bana bukatar masu taimakona. Batun cin abinci kuwa kice mata shima na gode ni mace ce kamar zinariya baka cin abinci a gaban kowa sai wanda ya ajiye ni da kuma yan uwana."

          Haka suka fita abinsu, ban san me ya faru ba, sai gata tare da Mahlika. Suna zuwa basu yi wata wata ba, tasa aka rufe Izmah da Nimra da duka.
_Dole zasu biyo ki! Musamman yadda suka fahimci kina da matsala da Mehran, kiyi kokarin dauke Kanki kansu_ inji Fudail.

Dauke kai nayi haka suka musu lillis, kafin suka juyo kai. Tare da takowa har gabana, sauran matan suna bayan ta.
"Na saka doka kuma dole kibi yadda nake son domin nice budurwan masarautan. Idan zaki ga Mehran dole sai kin biyo ta hannuna."

    Ban kalli inda suke ba, dan haka suka juya suka fita. Da sauri na isa gurin su Izmah zanyi magana tace min.
"Karki damu, ai Sultanah ta gaya mana. Dole zaki fuskanci wannan yanayin, ta bamu hakurin mu tayaki jurewa, Babban matsalar ki kama Mehran a hannunki, idan kika kama shi har abada ba zaki kuma fuskarta matsala ba."

            Hawaye ne ya zubo min tare cewa.
"Dole na nimo Abrad, naji meye ya gayawa Mehran haka?" Kallona suka yi sannan suka ce.
"Babu Matsala a fitar ki? Don Allah Karki kuma yin abinda zai jefa ki cikin matsala."

   "Babu kome zanje ba zan jima ba. Kayanki zaki bani Nimrah." Had'iye yawun tayi sannan ta mike ta cire, sakawa nayi sannan na fita a saɗaɗɗe. Ina samun na bar harami na sauke ajiyar zuciya. Ban tsaya ba, sai masaukin su. Ina zuwa na sami Nawwas yana tare da wasu dakarun. Ka rasawa nayi gurin shi. Sannan nayi mishi magana.
"Ikram!" Ya ambaci sunana da mamaki.
"Ina Abrad?"
"Yana cikin gidan!"  Nufar hanyar cikin gidan nayi, ban tsaya ba sai da na dangana da cikin dakin da yake. Tun a bakin kofar shiga, na dauki takobin shi. Ina shiga na same shi da mace shi banyi wata wata ba, na saka mishi tsinin takobin a kirjin shi.
"Meye ka gaya mishi?"
"Dama nasan zaki zo aiki, abinda na gaya mishi kike son sani?"
"Maganar banza nake son ji?"
"Wannan kuma duk ke ta shafa, dan haka ina tayaki murna domin tarko na d'ana miki kuma yanzun haka Mehran yana bayanki! Zai zo ya same ki a cikin gidan nan."

Cikin fushi na yanke shi da kaifin takobin, cike da mamaki yake kallona idanun shi waje.
"Ko zaki kashe ni ba zan fasa gaya mishi magana ba, kuma zaki gani da idanun ki idan ya karaso!" Cikin mugun b'acin rai na kuma dukar shi da kasar takobin, abinda ya bashi damar riko hannuna,

Please Login or Register in order to submit comment