Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

me kike bukata?" Inji Sultanah Fazilatul nisa. Tana kallonta,
Dariya tayi sannan tace mata,
"Bana son a kuma barin Mehran yayi mu'amala da wata mace! Sannan bana son ana shiga shirgin shi. Idan da hali a fita hanyar shi. Domin nice Magajiyar sarauta nan gaba, Uwar Yaron shi da yake kwance mahaifana!"

Ta mike tare da zaga dakin tana murmushin mugunta, tana faɗin .
"Mugun hukunci zai tabbata a kan wanda ya Kuskura ya shiga lamarin Mehran. Zan gyara mishi tunanin shi da nazarin shi, kar na kuskura naji mugun labarin akan haka, a sanar da matan da suke dakon ya kwana dasu."

Tana gama fadar haka ta bar dakin cikin jin dadi tare da jin ta isa domin ta kaftawa Sultanah Fazilatul nisa kashedi kuma hakan zai taimaka mata, domin idan ba haka ba tana ji tana gani sauran matan da suke hareem zasu iya daukar cikin Mehran.

       Koda ta fita, kallon matan da suke hutawa tayi, sannan ta zauna tana gyara gashin kanta, tana murmushi. Baiwarta Rubina ta kalle matan gurin ta shiga musu bayanin cikin Azizatul Nissah, take Jasrah ta mike tana faɗin.
"Karya ne, baki isa ki"

"Kawo min ita nan" inji Azizatul Nissah, babu musu aka kawo ta, jefata aka yi a gabanta, mik'ewa tayi a hankali, tare da kallon ta. Murmushi tayi sannan tace mata.
"Kika ce me?"
"Kar..." Kifa mata marin da tayi yasa ta had'iye maganar da zata yi.
"Rubina, ki zane min ita." Inji Azizatul Nissah wai a zane Jasrah.

  Duk sauran matan hatta Sakeenatu binti Abu Waqqas, sai da jikinta yayi sanyi, domin tunda take rayuwa bata tab'a tsintar kanta cikin mugun yanayi ba, sai da ta shigo cikin Samaind. Akan idanun su, aka zabe Amirah Jasrah irin mugun dukar nan da babu wanda ya isa yayi maka ita sai mugu.

   Shafa Jelar gashin kanta tayi tana faɗin.
"Ya isa haka, ba ita ba hatta ku idan kuka kuskura kuka d'aga min murya zan ba kowa kyautar hukuncina, ku dauke ta ku kaita shashinta."

        Cikin wani irin tsoro da fargaba tabbas Azizatul Nissah ta shirya fuskarta kowa kuma a cikin wannan yanayin, ta gaya musu ciki ne da ita, dan haka kar kowa ya taka shashin Sultan Mehran sai da izinin ta. Gyada mata kai suka yi. Domin babu wata hanya da zasu mata bori.

       ----
"Meye ya hadaki da ita har ta sako Ikram a maganar ta." Fudail ya tambayi Mahlika.
"Kawai sharri take son yi mata, kuma tasan a halin da Mehran yake ciki na kewar Ikram zai iya tsanar." Rike bakinta tayi tana kallon shi.

     Murmushi yayi sannan yace mata.
"Karki damu. Yanzun me kike ganin zaki yi?"

Shiru tayi sannan ta sunkuyar da kanta kasa, tana me jin kamar tace mishi zata koma Madinatul Mah, sai kuma ta d'ago kai tana faɗin.
"Babu abinda zanyi."
"Ni kuma zan sakaki aiki" ya faɗa mata yana leka hanyar, a hankali ya matsa tare da gaya mata abinda yake son tayi mishi, zaro idanu tayi sannan tace mishi.
"Zanyi amma da sharadin. Zaka hada ni da sultan Aamaan!
 
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Ba zan iya hadaki dashi ba, mutum ne me ra'ayin kanshi, idan kika sami damar ya gayyace ki toh idan kuma baki samu wannan damar ba, ina me tuna miki aikina da na baki. Sultan MEHRAN yana cikin kewar Ikram ne ko yayya aka tunzura shi zai iya aikata wani abu bayan haka."

             Yana gama gaya mata haka ya juya abin shi ya barta a gurin. Shiru tayi na wani lokaci kafin ta bar gurin tana jin itama zata tsayawa kan.
......
A can cikin gidan kuwa, kallon Juna ake tsakanin Sultanah Fazilatul nisa dasu Shairah. Kura musu ido tayi kamar tana son gano gaskiyar abinda Azizatul Nissah ta faɗa, sai kallon su take kamar tana hango abinda.

"Ina Mehran? Maza ku nimo min shi." Ta faɗa da karfi. Kallonta suka yi kafin suka ce mata.
"Yanzun lokacin hutawar shi ce, idan muka."

"Nace ku nimo min shi ko?"
Babu musu suka fita, shashinta suka nufa, inda Shairah yayi karo da Sultanah Hoyam, itama tana kokarin shiga shashin Sultan Mehran.
"Dama kana raye?"
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Ina nan daram."  Ya bata amsa.
"Toh haka ma yayi, sai dai har yanzun baka gaji da bautawa matar da bata san ƙaruwar ku bane."

Murmushi yayi sannan yace mata.
"Gaskiya labarin da nake ji bai kai adadin abinda zaki bani ba, koda yake ai girman jiki gare ki bana shekaru ba, idan kika sake mummunar alaƙar da kike da Darakshan ya fito tabbas."
A firgice take kallon shi.
"Karka min Sharri!" Sassauta muryan shi yayi sannan yace mata.
"Karki damu, babu wanda ya fahimci haka sai ni, kuma babu wanda zai fahimci abinda kike aikatawa sai har kin tonawa kanki asiri." Daga haka ya wuce ta bai kuma mata magana ba, karshe bata shiga gurin Mehran ba, ta koma da baya.

    ....
Yana shiga ya same shi zaune ya faɗa cikin mugun tunani me shegen zurfi, dan ya jima akan shi kafin ya mishi magana ya farka. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kalli Shairah.
"Sultanah tana son ganin ka!" Kurawa Shairah idanu  kamar wanda yayi mantuwa, a hankali ya janye daga kallon shi tare da gyada mishi kai, fita yayi cikin tausayin MEHRAN, domin baki daya yayi laushi. Tausayin yadda soyayya ta maida shi yake.

   Ya jima yana nazarin abinda yake damun shi wanda yayi itifakin Babu shakka Ikram itace rayuwar shi, sannan bayi da wani kuzari sai idan tana tare da shi. Ya san a wannan lokacin tana tare da Rahil. Suna soyayyar su. Haka kawai idanun shi ya shiga hango su, suna hira a lambun suna soyayya.

Watsi yayi da kayan gaban shi,yana haki. Kwalla ne ya cika mishi ido, a hankali ya kai hannun shi kirjin shi yana jin kamar zuciyar shi zata buga.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ubangiji ka yayye min, ka kuma kara min hakurin rashin ta. Ya Allah ka jarabce ni ta inda ba zan iya cinyewa ba. Ya Allah na tuba ka yafe min."

Ya faɗa tare da jin kwalla nason zuba daga idanun shi mai dasu yayi, tabbas yana cikin wani hali, Ikram ta shiga rayuwar shi. Ya jima sosai a gurin kafin ya daidaita nutsuwar shi yayi sannan ya fita daga dakin.

--- tunda ya isa shashin Sultanah, bai ce kome ba sai dai duk tambayar da tayi mishi baya ko motsi balle ta saka ran zata sami amsar tambayoyinta.
"Aamaan" ta kira sunan shi kamar ,zata fashe da kuka tana cewa.
"Meye gaskiyar abinda."
"Anneh bana son kina shiga cikin al'amarin gidana." Daga haka ya mike zai bar d'akin tace mishi.
"Amma me yasa ba zaka gaya min abinda yake damun ka ba?"

Juyawa yayi tare da sake murmushin takaici, sannan ya bar dakin yana ji kamar ya had'iye zuciyar shi ya huta, ranshi ya kai kololuwar ɓaci, baya ganin gabansa. Yana shiga cikin d'akinta ya tokari kofar shi, kallon shi tayi a razane. Amma ta dake, juyawa tayi tare da kallon bayin d'akinta. Da sauri suka fita,

Da sassarfa ya isa gabanta, zai kamo wuyar ta, tayi baya tana girgiza mishi kai. "Duk abinda aka gaya maka karya ne, tunda suka ji labarin samuwar cikin jikina suke kokarin ganin bayan shi, sabida."

"Na tambaye ki ne? Nace kiyi min magana ne? Meye ya kai ki shashin Mahaifiyata." Ya tambaya ta a tsawace. Diriri cewa tayi kafin ta saka mishi kuka, tana faɗin.
"Ita Fazilatul nisa ce Mahaifiyar ka?" "Tauuu!" Ya kifa mata mari, wanda yasa ta ganin taurari, a hargitse ta d'ago kanta, wani shegen tsoro ne ya kamata bata san lokacin da ta sunkuyar da kanta ba, gwiwarta zube a gaban shi.
"Na kuma jin labarin haukarki ta kwashe ki har kofar shashin ta, sai na karya ki na maida ke yankin ku, kije can kuyi ta haukar ku sakarya."

Yana gama fadar haka ya juya tare da barin d'akin, tunda ya fita yake jin kamar ya tattara ya bar SAMAIND ko zai sami sauƙin damuwar da yake ciki, amma ina.

----
Dan haka ya tattara ya koma can gidan shi da ya tab'a zama, dan anan yake jin zai iya samun nutsuwar da ya rasa. Tare da Fudail suka koma sai masu kula da abinda zai ci, sam baya son magana ko da kuwa a cikin mutane ne, yafi son ya keb'e kanshi yayi shiru.

----
Merocco.

Da wani zai gaya min yadda rayuwata zata koma ba zan yarda ba, dawowar Nimrah bai kara min kome ba, sai damuwa domin tunda tazo bata da wani aiki sai kukan halin da ta sami Mahaifiyarta, ga kuma soyayyar Fudail da ya kamata, kwanciya tayi a jikina. Tana zubda kwalla, tare da gaya min halin da take ciki.

Shafa kanta nayi domin ita kukan dad'i take, kuma nasan zata sami abinda take so ni kuma fa? Waye zai bani abinda nake so? Sam mulki da nasabarta bata dace da rayuwata ba, ni rayuwar Yanci nake so.

Bana bukatar kome bayan Yanci, shi yasa da zan mallaki Mehran tabbas zamu bar SAMAIND har karshen rayuwar mu, mu shiga inda ba za a kuma ganin mu ba, muyi rayu daga mu sai Yaran mu. Wannan shine tsarin da nake shirya mana,.kamar Yadda iyayena suka bar gidajensu, haka mu ma zamu bar cikin daular mu. Muje mu kafa kanmu tare da boye asalin mu.

"Assalamun Alaikum!" Sallamar Rahil ya katse min nazarin da nake. Lumshe idanuna nayi kamar ina barci, shigowa yayi tare da zama yana kallon yadda na sunkuyar da kaina, murmushi yayi tare da cewa.
"Toh meye laifin sallamar da ba za a amsa min ba?" Ya tambaye ne ni, tare da tsare Ni da ido.

Mikewa Nimrah tayi tare da kallon shi tace mishi.
"Barka da shigowa Amir Rahil," d'aga mata hannun yayi yana murmushi, a hankali ta bar d'akin. Dawowa gabana yayi tare da zama ya zuba hannun shi akan cinyata.

"Me yasa kika fi son shi akan Ni? Meye bani dashi? Dame ya fini da kike zubda hawayen ki sabida shi?"

D'ago kai nayi ina kallon shi sannan nace mishi.
"Kai zab'in kakannin mu ne, shi kuma wani shashi ne na rayuwa ta, zan amshi aurenka ne...
[5/22, 7:48 PM] Mehkram1256: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat
Book3
_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
6..

Cike da mamaki yake kallon yadda nake kokarin gaya mishi gaskiyar da ya kasa Fahimta, so nake lallai ya gane babu dole a soyayya. Kura min ido yayi tare da sake murmushi yace min.
"Koda zaki na yankan namar jikina kina ɗona min gishiri zan zauna da ke haka kuma zan kare rayuwata dake!"

      Murmushi nayi mishi tare da shafa kanshi nace mishi.
"So bai maka adalci ba, kamar yadda ya ratsa tsakanin zukatar mutanen da basu shiryawa zanen ƙaddarar su ba, ba zan hana ka ba."
Rike hannuna yayi cikin na shi sannan ya matse a hankali, yana murza yatsuna hannun.
"Ikram ni na dace dake, karki manta zan zauna dake a duk yadda kike, Ikram ina tsananin kaunar ki"

Rike hannun shi nayi cikin nawa tare da kura mishi ido, ina hango iyakar gaskiyar shi. Dauke kai nayi tare da cewa.
" Nasan kana sona, amma ya aka ji idan ka taso daga sahara me matsanancin zafin rana, sannan kuma kana murnan zaka tsallake kana hango koramar ruwa, kana isa ka sami ruwan an hanaka sha. Ya zaka ji? Toh haka ka shiga tsakanin mu."

      Mikewa nayi zan shiga ban daki yace min.
"Zan iya hakuri dake har zuwa lokacin da zaki soni amma Tabbas zan aure ki. Kuma zan zauna dake."

     Cak na tsaya sannan na juya ina kallon shi, kafin nace mishi.
"Zaka zauna da ni Tabbas zaka ƙunshi bakin ciki, domin zan zame maka kamar ramin maciji ne, kowani motsi kayi da dafina zaka motsa, bana son mu kai ga haka shi yasa nake gaya maka illar haka." Na shige abuna.

   Shiru yayi tare da jin babu dadi a ran shi, amma kuma babu yadda ya iya, dole haka ya saka kai ya fice daga d'akin. Tunda na shiga ban daki na fashe da kuka, tare da zama a gurin ina kuka, Tabbas na san yana sona, amma haka bayana nufin zan iya rayuwa da shi bane, Mehran shine zab'i na, Rahil dan uwana ne shi. Ban shirya zama dashi a matsayin abokin rayuwata ba.
 
   A hankali na fito daga ban dakin ina sauke ajiyar zuciya, tare da zuɓewa a jikin gadon dakin ina jin kwalla na zuba min.

       Mehran shine zab'i na, shi din farin cikina ne..idan ana iya musayar so ba zan tab'a musayar Soyayyar shi ba, ina mugun son shi, a lokacin da ba zai min amfani ba. Lokacin ya gama kure mana, dan haka na had'iye kukan tare da kifa kai na a jikin gadon, ina jin wani irin kewar shi.

      ***
Takowa yayi har gaban gawar da masunta suka dauko shi daga ruwa. Babu abinda ya sami gawar, kamar bai jima da mutuwa ba, sai hasken fatar da yayi irin fari fauu din nan.  Kallon gawan Nawwas Fudail yayi sannan yaja mayafi ya rufe kafin yace.
"Wannan gawar shugaban dakarun daular Umayyad ne, dan haka ba zamu binne shi ba, sai mun san ta yadda aka yi gawar ta wanzu a cikin yankin mu."

  "Toh shugaba!" Suka amsa mishi.
"Kwanakin Baya mun ga lokacin da ya shiga wata jirgi, tare da a yarin  daga nan ne na shiga jirgi na, na haura saman Teku, daga nesa na hango lokacin da ake jefa wani a cikin ruwan amma ban sani ba ko shine ba."

               Gyada kai Fudail yayi lokacin jin da yaji bayanin wani mutum da yaga lokacin da Abrad yasa a wurga gawan Nawwas a ruwa. Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Toh babu kome zamu bincika." Gaba yayi sannan dakarun suka ɗauki gawar a makara, suka  nufi cikin garin SAMAIND da shi.

       .....
Kallon Mehran Azizatul Nissah tayi tare da toshe bakin ta, tana me fashewa da kuka, da gudu ta nufi hanyar da zai sadata waje,

      Bin bayanta yayi sabida karta tab'a lafiyar cikin jikinta, zuɓewa tayi a gaban gawar tana kuka da ihu, sabida yadda ta ga gawar shi bata kawo hakan ba a ranta, dakyar Mehran ya d'aga ta, ya koma da ita, sai da aka gama bai bincike sosai, kafin aka nad'e gawar aka mishi jana'iza.

"Zan tafi gida, ina ganin babu wanda yasan da labarin mutuwar shi don Allah karka hanani." Shafa kanta yayi tare da maida gashin ta baya, yana me jin tausayinta a ranta, sannan yace mata.
"Ba yanzun ba sai kin haihu." Wani irin kuka ne ya kwace mata, bata san lokacin da ta kuma sake kukan ba, ta rike hannun shi tana faɗin.
"Toh taya zasu sami labarin mutuwar shi."

            "Zan aika da sako a gaya musu. Insha Allah" sake rungume ta yayi, ta kuma narke Mishi kamar wacce take cikin tashin hankali na gaske. Haka yayi ta rarrashinta, domin kuwa baki daya ta birkice mishi. Kwana biyu tsakani idan ka ganta zaka Dauka jinya tayi nan kuwa dauke hankalin shi tayi da makirci kamar mutuwar ya dake ta. Duk da kuwa ta kadu da mutuwar amma ba wani jijjiga ta ba, sabida cikin jikinta kar yace dai kwace abin shi, ko wani dalili da zai fito ya fadi gaskiyan cikin nashi ne, Tabbas akwai matsala domin haka zai iya janyo yakin da za a rasa rayukan al'umma, sannan itama bata tsira ba, kisar wulakancin za a mata a gaban jama'a. Dan haka mutuwar Nawwas yazo mata a gaɓɓar da ya dace, dan haka bata ga abinda zai wargaza mata lissafin ta ba. Shima Mehran duk ya damu, domin a tunanin shi da gaske take, dan haka duk ya shiga damuwa duk da yana cikin damuwa, amma sai ya tsinci kanshi da tausaya mata sosai, har yakan zauna yana b'ata lokacin shi akan ta, ita kuma haka sai ta narke tayi ta nuna alamar bata ita fa tana kewar gida, dan haka ya taimaka ya kaita ko da yayya ne yan uwanta sun san yadda take ji gashi babu wanda ya san da mutuwar sa ita.

Dan kar ya samu damar da zai nufi gurin Sultanah Fazilatul, yasa ta baki daya ta kawo mishi yanayin da take ciki, yana fita sallah zata ware, ko kuma tayi ta kuka, asalima ta hana shi ko zuwa fada, domin yana fita zata saka rigima haka zai dawo matan da suke dakon shi kuwa haka suke jin babu dadi ga zafin kishinta da suke ji.

     Wata idan ka nutsu zaka Fahimci burin Azizatul Nissah, bukata take ta dauke hankalin Mehran baki daya, haka da sauran suka gani yasa su hade kan su, suka tsayar da shawara. Akan su shiga jikin Sultanah Fazilatul nisa, sai aka yi rashin Sa'a an sami munafukai a cikin su. Wato Sakeenatu binti Abu Waqqas, ta rubuta wasika ta bawa baiwarta mesuna Munirah ta kaiwa  Azizatul Nissah.

     Ita kuma da ta tashi hada rigima sai ta sauya tsarin labarin tare da kwafe wani ta saka wani abu na daban. Sannan ta bawa Baiwarta me Suna Unaizah takai Fada. Inda Sultan Mehran yaƙe, tare da shaidawa duniya cewa tana dauke da juna biyun shi.

    Shiru Fadar yayi sannan magatakardan ya cigaba da karanta wasikar kamar haƙa.
_Sultan Mehran a halin da nake ciki ina dab da rasa rayuwata, ba dan kome ba sai yadda Fazilatul nisa! Tasa Matan da suke Hareem su dake ni! Sultan MEHRAN ka kawo min a gaji domin zasu kashe ni da goyan bayan Matar da kake mata kallon Mahaifiyarka, tare da amintacciyar baiwar Ikram_

    Wani irin lumshe idanun shi yayi tabbas, yana bukatar ya dakatar da Sultanah Fazilatul nisa, amma yana jin wani irin girma da darajar ta a ran shi, shi yasa yake kasa murza mata kome, dan haka ya mike ba tare da yayi musu magana ba, ya nufi cikin gidan.

       Kallon juna suka yi manyan Fadar.
"Kanwar Abrad ce ta samu damar daukar cikin shi? Lallai akwai abinda yake shirin Faruwa, idan har muka dake wata daga wata daular ta haihu da Mehran har abada mulki ya fita hannun Daular Abbasiyyah! A barar da cikin"

Dariya Sultanah Hoyam tayi sannan tace musu.
"Cikin ba zai tab'a zuba ba! Sabida shi kanshi cikin zan bukaci na tsaya kan shi kamar yadda na tsaya akan uban dab haka babu batun zubda jinin Mehran"

"Amma!"
"Na yanke kuma ya yanku, babu wanda ya isa ya sauya min ra'ayina, ko kuma dole kubi abinda nace." Ta fadi haka tana mik'ewa daga kujeran ta.

  Bin bayanta suka yi da ido, Tabbas sun dibo ruwan dafa kansu dan haka su san abinyi domin kuwa har da hannun yaransu a cikin abinda aka turo, wani irin hukunci Mehran zai dauka akan Yaran su?

Kuma me yasa ya ajiye FAZILATUL a gidan sarautar? Duk basu da amsar tambayoyinsu dole shi ne zai basu.
"Toh ya zamu yi idan da hannun Yaran mu a ciki!" Inji Mir Umdatuddawla,
"Sai mu maida laifin kan Fazilatul nisa, ai tafi su hankali, kuma sunanta ya fara fitowa kan nasu, dan haka karka damu sune zasu kwaci kan su."

Daga haka suka watse daga fadan.
----
Lokacin da Mehran ya shiga cikin gidan, Ya samu Sultanah Fazilatul nisa tana kokarin shiga tsakanin su Jasrah da Azizatul Nissah, sakamakon fadar da suke yi, wanda dama can tana cike da ita akan zaneta da ta saka aka yi, dan haka ta same ta da bugu, a bangaren Azizatul Nissah itama abinda take bukata kenan Mehran yazo ya same su a wannan yanayin, sabida ta sami damar sharrin da ta kulla musu.


Tana ganin shi ta yanki jiki ta fadi tare da rike cikin jikinta.
"Wayyo Allah na, wayyo cikina, wayyo Mehran"
Ga baki daya ta birkice mishi tare da murkusussu, kallon Sultanah Fazilatul nisa yayi, cikin matsanancin b'acin rai.
"Anneh! Sad'akata ce kika sa Jasrah ta sake ta da cikina?"

Zaro idanu tayi waje tana faɗin.
"A'a Aamaan akan me zan saka su dake ta? Me tayi min da zafi haka da zan tab'a lafiyar ta."

"Ya isa! Ki tattara ki bar cikin fadar nan ko kuma."
"Sultan MEHRAN!" Fudail ya kira sunan shi da karfi.
"Karka hana shi, bar shi ya kore ni barshi ya tura ni waje saboda Azizatul Nissah."

Sanyayye ta juya zata bar falon, amma ba haka Azizatul Nissah taso ba, taso idan ya kore ta yasa a kaita gidan horo, b'ata fuska tayi sannan tace.
"A haka zaka kyaleta, ba ka hukunta ta ba, bayan so take a kashe ni itama Jasrah hukuncin. Da ya dace da ita kenan, sannan a nuna musu matsayina."

Kallonta yayi tare da kai hannun shi kan cikinta yace.
"Fudail ka kama Anneh,. A kaita tsohon gida ta zauna a can kar a hada da masu kula da ita, a barta ita daya, Jasrah kuma a kaita gidan horo."

Daga haka ya mike tare da Ɗaukar Azizatul Nissah, kura musu ido Fudail yayi, a ranshi yana cewa.
*Ikram itace kawai zata iya dakatar da wannan wulakancin* sannan ya raka Sultanah Fazilatul nisa yana bata hakuri, murmushi tayi sannan tace mishi.
"Karka damu, tunda Ikram ta bar gidan nan na fahimci babu me iya tankwara Mehran bayan ita, Azizatul Nissah kuma tayi amfani da cikin jikinta ta juya mishi tunani, amma nayi mishi Uzuri."

"Yanzun babu abinda za ayi Ikram ta dawo?" Ya tambayi Sultanah Fazilatul,
"Itama danginta suna kaunar ta, babu wanda zai so ta shigo wannan rayuwar." Ta faɗa tana share kwalla.

Haka ya takata har gidan, sannan ya dawo ya tasa keyar Jasrah. Bayan Mehran ya kai Azizatul Nissah d'akinta, lallab'a ta ya shiga yi har tayi kamar ta fara barci, kallonta yayi sannan ya mike zai bar dakin ta rike hannun shi.
"Sultan MEHRAN! Shin kana kaunata?" Kura mata ido yayi sannan ya zare hannun shi cikin nata, sannan yace.
"Ina Sonki mana, koda abin cikin jikinki."
"Me yasa ba zaka kaunace ba?"
Murmushi yayi sannan ya shafa kanta, bayan ya mike zai fita.
"Ko har yanzun wancan Yarinyar da maza suka gama hawa da sauka akan ta kake kauna? Amma kuma taya zaka gayawa Al'ummar ka Ikram ta tab'a aure har ta kwanta da wani namijin? Koda yake ai baka san yadda akayi kome ba, domin Yayana ya sha kwanciya da ita ni ganau ce ba juyau ba....
[5/22, 7:48 PM] Mehkram1256: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat
Book3
_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

7...
"Ya isa haka!!!" Ya daka mata tsawar da sai da dan cikinta ya juya zunzurutun fusata, jikin shi yana kerma ya nufe ta kamar zai rufeta da duka.
"Kika sake raina ya b'aci dake, ba zai miki kyau, wallahi sai na baki mamaki. Sai na wulakanta ki a cikin Masarautan nan, sakarya me kike son nayi miki? Ita nake kauna. Ita na fara sani, ban damu ba ko mazan duniyar nan zasu kwanta akanta abinda na sani kaunarta dani gaskiya ce, babu karya a cikin shi. Idan na kuma jin Kinyi irin wannan haukar zan baki mamaki."

Daga haka ya fita ya barta, ita a tunaninta Mehran irin mazan nan ne da zaka. Sarrafa su cikin tsarin da ka gindayawa musu sai ya nuna mata shi baya cikin mutanen da zaka tanada domin bukatar kanka.

Mehran da Ikram ba tasha ta da a tare da shi ba, duk da kuwa suna kaunar juna Kamar ya, murmushi da farin ciki ne suka rufe ta, kamar zata tashi sama. Ta jefe tsuntsun biyu da Dutse daya, ta sanya shi ya kori Mahaifiyar shi da Jasrah ta kuma cusa mishi jin haushin Ikram, kenan babu amfanin da ba zai mata ba,. Dan haka daga yau tayi ta sanya shi cikin wani yanayi kenan. Kiran Rubina da Unaiza tayi tare da basu silallar zinari akan suje su watsa a ko'ina na farkon da bayi

Please Login or Register in order to submit comment