Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san abin yi!"
Daga haka  mata sallama ya fice daga d'akin,
           Tunda ya fita take zullumi, cike da damuwa, tare da hana kowa shigowa dakin ta. Abincin dare na bata ci.
     :
        
           Taje mata gashinta Narmin take, tare da kallon yadda take gyara fuskarta, murmushi tayi tare da cewa.
"Kuma idan naje me sanyi wa Sultan?"
"Idan kika je zaki gani."
Cikin danyen yarinta tace mata.
"Amma zan kwana ne a can?"
"Idan kika je zaki gani."
Tura baki tayi, sannan ta kalli Narmin daga cikin madubi tace.
"Amma Sultan yana Kwarkwarori da yawa, kuma naga suna tsoron Sultanah."

    "Ke baki tsoron ta ne?" Ware idanu tayi sannan tace mata,
"Tab wallahi mugun tsoronta nake ji!"
"Yayi kyau haka nake bukatar ji daga gare ki."
Tana gama shirya ta, ta rike hannun ta, suka nufi shashin Sultan, ta tsaya daga bakin kofar shiga shashin sa, tare da yiwa fadawan da suke jikin kofar magana.
"Bakuwar Sultan ce!"
Bude mata kofa akayi wanda yayi dai dai da isowar Sultanah, kallon juna suka yi ta kalli yadda Hoyam ta diriri ce.
"Sultanah Fazilatul nisa tana niman Iso Sultan!"
"Sannan Baiwarka Hoyam tana nan itama!"

                       Dake ciki akwai wani Bafaden me suna Rizwan..
"Ka sallame Sultanah, Hoyam nake son ganawa da ita"
.  "An gama ranka shi dad'e!" Ya fadi haka tare da ficewa daga dakin karatun Sultan.

              ."ranki shi dad'e, yace ba yau zai gana sake ba, Hoyam yake son ganawa da ita!" Cikin mugun fusata ta yi yunkurin zata shiga.
"Ranki shi dad'e, Sultan baya son ganawa dake, da Hoyam yake son ganawa!"
Ya fadi haka ne sakamakon yadda take kokarin lallai sai ta shiga cikin shashin Sultan, shi kuma yasan halin Sultan sama da shekaru talatin idan ya tsaya akan abu toh babu makawa ba zai canza ra'ayin shi ba, idan kuma aka sami akasin haka, zai iya sanyawa a sare kan mutum. Dan haka ya nunawa Hoyam hanyar shiga. Ai kuwa Sultanah Fazilatul nisa taja rigarta sai da tayi baya zata fadi.
"Sultanah! Zata rena ki fa!"
Sake rigar tayi, sanan ta juya tare da barin gurin, ranta na kara b'aci, wato itace ba zai gana da ita ba, tana shiga shashinta ta fashe da kuka tare da cewa.
"Shairah maza ku nima min iso ga Abbu na!"

          Da sauri suka fita shi da Narjis, kallon juna suka yi.
"Me kika fahimta?"
"Me kuwa ban fahimta ba"
"Wai nan alƙawarin Allah za a dakatar?"
"Zai dakarun kuwa! Tunda sun shiryawa haka ba iya ita ba, jimawar da Sultan yayi akan mulki bana wasa bane, sannan kuma sauran barorin shi ba Haihuwa suke ba, balle ace zasu zama magadan sarauta.

    Idan ka duba a cikin masarautar mutane da yawa suna jiran kujeran can, da ake fada akan shi waye zai sake ya rasa shi? Waye zai yarda ya rasa shi."

"Kedai inda ranka kasha kallo. Muje zuwa."
Shairah ya faɗa tare da kallon hanyar gidan su, Amir Hood.

     Bayan sun shiga suka sami mahaifinta, yana ganin su ta fahimci al'amarin ya girmama, dan haka ya taso da kanshi.

      ... Tunda suka iso ya same ta yashe a kasa tana kuka, zama yayi a kusa da ita, yana shafa kanta, tare da sake murmushin takaici.
"Albasa bata yi halin ruwa ba! Ina nan ina yaki domin ke, ashe Ni kike kunyatawa a cikin masarautan? Ina ƙoƙarin ganin mun sami karfin jama'a ashe kina nan kina b'ata min aikin da nake, bani nace kiyi hakuri ba! Bana ce ki dauke Kanki akan shi ba? Toh indai Ni ne Sarkin yakin Samanid kar na kuma jin kinyi tari Barsu muga iya gudun ruwan su."

     Gyada kai tayi tare da share kwallar ta.
Mik'ewa yayi sannan yabar shashin, yana jin wani duhun bakin ciki a ranshi, dole ya dakatar da kome kafin lokaci ya kure mishi. Idan lokacin ya kure sai dai a zab'i wata hanya na daban.

  -
Zaune suke dukkan su,.suna kallon juna.
"Koda ace mun dakatar da Sultan bamu da hurimin hana shi abinda yake so! Dan haka kawai mu yi abinda muke ganin shine dai dai, amma kusan Abdus Samad bai da dad'i idan muka takura shi."

    "Toh Fujai Matsalar...
Littafin kuɗi ne....
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *_ᎠᎪႮᏞᎪᎻ BIYU_*

   _The Historical_
~BOOK ONE~

Bismillah Rahamani Raheem

Page 3...

       "Karka ce zaka yi wani yunkurin! Masarautan nan cike yake da baƙar siyasa, idan ka sake wani shirme ya fito daga gare ka, zai zamewa kabilar mu abin kunya!"  Inji Amir Anas,

          Murmushi yayi sannan ya gyara zama, kafin yace.
"Kasan har yanzun bai gama gano meye silar mutuwar Sultanah Afeefah ba, dan haka kayi ƙoƙarin gano inda."

        "Amir Hood yana shigowa!" Inji Bafaden da yake bakin kofar shiga zauren tattaunawa, nasu na yarimomi masu jiran gado.

       Babban tashin hankalin su, kawo Baiwa da Sultan yayi cikin masarautar shine damuwar su,.idan so samu ne a fitar da ita daga jikin shi, domin suna da yakinin duk macen da ta fito ta jikin sarki karshe bala'i take zamewa masarautan, sannan kuma tana iya baza mulkinta na son ranta, dan haka suka fara nazarin yadda zasu tunkaro Sultan.

          ***
Kallon fuskarta yaƙe, yadda kwalla suka bushe a a saman fuskarta, shafa fuskarta yayi cikin nutsuwa, yana murmushi musamman yadda take ajiyar zuciya. Shi kanshi yasan cewa yayi mata bazata, domin ya saka mata karfi ainun.

    "Hoyam!" Gyara kwanciyar ta tayi sannan ta kuma lumshe idanun ta, sabida barcin da yake cike a idanunta. A hankali ya mike tare da barin gadon, ban daki ya shiga ya shirya kanshi.
Sannan ya fito, jin Rizwan yana buga mishi kofar shi ne ya sashi cewa.
"Hmm!"
Shigowa yayi sannan ya gaida Sultan.
"Manyan dattawan Fada suna son magana da kai. A zauren tattaunawa."
Bude wata takarda yayi ya dauki alkalami ya fara rubutu, yana gamawa. Ya mikawa Rizwan.
"Akwai wani mahayi zai tafi kasar Carboda ka bashi."

          Mik'ewa yayi tare da saka alkyaba, sannan ya saka kai zai fita, ya sami Narmin tana bakin kofar shashinsa, tare da wasu manyan masu tsaron lafiyar shi.
"Narmin ki kula da lafiyar ta."
Dukar da kai tayi sannan tace mishi.
"An gama Sultan."

      Suna barin shashin, ta shiga cikin da sauri, ta hango Hoyam, tana barci. Tashinta tayi ta fashe da kuka.
   
      Fita Narmin tayi tare da samun Shairah ta gaya mishi, zaro idanu yayi waje. Sannan ya kuma juya tare da niman Narjis ya gaya mata, take aka nimo masu kula da lafiyar matan masarautan, suka nufi har dakin Sultan, anan suka taimakawa Hoyam aka gyara ta sosai, sannan aka kuma dauketa zuwa Chamber na musamman, sakamakon ita din Zab'in Sultan ce.

               Sannan aka Narjis da Shairah suka nufi Shashin Sultanah suka gaya mata, murmushi tayi hawaye na zuba mata, tace.
"Ki bata bayi yan mata da zasu zauna da ita, kuma ku saka ido akanta, karku yarda ku.."

   "Na'am Sultanah!" Sannan suka fita, suna komawa aka duba bayi da kunyangi aka saka Narmin ta zab'esu sannan aka kai su Chamber din Hoyam, wacce take barcin gajiya domin babu abinda ba ayi mata na kulawa ba. Abinci ne kuma ana kawowa tace ta koshi a barta barci take ji.

**
Murmushi yayi tare da dauke kanshi, kafin ya kalle su kasancewar fuskar shi babu burbushin fara'a.
"Idan na fahimce ku, na zare ta daga cikin rayuwata, bayan kusan haka ba sauki ne a gare Ni ba, sannan kun dauko min labarin karni masu yawa, wato babban karni, na rabu da Hoyam sabida karta haifi namiji ta kwace masarautan ko ba haka ba?"

   Maida kanshi yayi sannan ya kalli Ubaidullahi. Aminin shi na kut da kutt, ya kuma lumshe idanun shi, sannan ya ce mishi.
"Ubaidullahi! Me zaka ce?"
Shiru suka yi sannan yace.
"Ai duk abinda ka zab'e naka ne, kuma muradinka ce, dan haka umarni zaka bani."

     "Rizwan me kace?"
"Rayuwata da kome na, mallakin Sultan ne! Umarnin ka ya wadattar dani."
"Fujai, Kaisan, Hood, Anas, Abu Yusr, Abdul Muxxalib, ina jin ku me kuka ce akan zab'ina"
Had'iye yawu suka yi, sannan suka dukar da kansu,.tare da mubayi a, wannan itace dokar shi..
Idan kuka ja, ya kuma ja. Toh abinda zai faru gaba wasan takobi da jini ne.

Mik'ewa yayi sannan ta bar su a gurin, cikin jimamin abinda zai iya faruwa gobe.
**
Tunda aka sanarwa Sultanah, Cewa Sultan yana gayyatar ta, turakan shi, take kwalliya. Tare da gyara wasu abubuwan ta, sannan ta shirya ta fita, ana take mata baya, isowa babban falon cin abincin kuyangi, ware idanunta tayi tana niman inda Hoyam take tayi, bata ganta ba.
"Shairah ina Hoyam?"
"Tana shashinta, bata cin abincin da sauran matan"
Ya faɗa kan shi sunkuya,
"Akan me?"
"Ai tafi su daraja!"
Gyada kai tayi sannan ta wuce zuwa shshain sultan.
"Sultanah ta iso!"
Aka gaya mishi, kallon Rizwan da Ubaidullahi yayi sannan yasa su, suka nad'e aikin da suke, sannan suka fita. Kafin ta shigo cikin falon shi me dauke da kayan tarihi na sarakunan larabawa.

    Zama tayi a falon, ganin yadda yake ta shirya abubuwan shi. Ita nan zata ja mishi aji ne, sai ta lura shi karshen aji ne, dan tunda tayi sallama, Sultan bai d'ago ya kalle ta ba, amma kuma ya amsa mata.
         Tashi tayi tare da zare alkyabar jikinta, sannan ya rage daga ita wata rigar barci ruwan hanta, wanda ya tsaya iya cinyarta. Takowa tayi zuwa bayan shi, tare da mishi matsar kafadar shi. A hankali tana sauke ajiyar zuciya, tausayi ta bashi. Ya jingina kan shi a kan cikinta, sannan ya juya yana kallonta. Zaunar da ita yayi akan cinyar shi yana shafa fuskarta a hankali.

       Daukarta yayi, zuwa turakar shi, daga nan ya kwarkwance mata, tare da kiran sunan Hoyam, cak farin cikin da take ji tare da jin dadin da yaƙe yawo a ranta da gangan jikinta, suka tsaya, kokarin datakar dashi ta fara, amma fir yaki sai da ya biya bukatar shi, sannan ya kyale ta, wani irin kuka take babu shiri ta maida kayanta, tare da barin d'akin shi. Sam ya kasa fahimtar me ya faru, kawai dai yaga tana kuka ne, dan haka ya share batun ta.
......Kwanaki ƙalilan ya kuma niman Hoyam, a lokacin aka gaya mishi tana cikin fashin sallah.

Dan haka aka nimo mishi wata yar kasar Masar me suna Alima, kyakyawa ce yarinya ce kamar Hoyam, amma kuma sai dai ita tun kafin a kawo ta cikin masarautan, ta samu matsalar fyade.

  Dan haka lokacin da Sultan ya haɗa shimfid'a da ita, sai yaji ya rena mata, musamman yadda ya tuna Hoyam, matar shi ma ya rena mata balle kuma Alima. Dan haka koda ya gama da ita, a daren ya sallame ta, amma kuma sai dai kash.
Yarinyar ta faɗa kaunar Sultan, dan haka take ji koda Bala'i sai ta haɗa alaƙa da Sultan.

          Bayan haka, ba zata iya zama a matsayin baiwa ba, shi yasa lokacin da Shairah ya gaya mata zai kaita dakin Sultan tayi ta murna, koda ta kasance dashi abinda ya kuma d'aga mata hankali Hoyam.
Itace kalmar da take fita a bakin Sultan. Dan haka taji ba zata iya barin shi ba, dole itama yayi mata wannan son da yake ma, Hoyam tana son ya mallaka mata zuciyar shi.
               
                Dama Chamber din Hoyam babu ruwa, kuma tayiwa Narmin magana har tasaka bayin su kawo mata ruwa, ashe basu kawo ba. Dan haka tana ganin babu ruwa ta shirya sannan ta nufi hanyar ban dakin kuyangi, bata da matsala, amma yadda aka tsaneta abin har tsoro yake bata.  Dan haka tana isa ban dakin ta saka bayinta suka mata kome cude mata baya suka fara. Alima da ka gaya mata ai Hoyam tana ban Dakin.

    Tana zuwa tasa ka mikar mata da bayin ta shiga dukar su, abinda yabawa kowa tsoro har da Hoyam cikin dariya tace musu.
"Uwar dakin ku bazata iya taimakon ku ba, to bari kufa yadda zan mata."

   Haka ta kunce tawul din wankar da yake daure a kirjin Hoyam, suka shiga mata dariya suna dukarta, kafin kace me sun mata taron dangi, sun mata dukar Bala'i.

    "Ranki shi dad'e, uwar bayi.  Alima ta daki Hoyam fa" da sauri suka kalli Juna da Shairah, tare da Narmin da take gurin a tsaye, bata jira abinda za ace ba, ta wuce da sauri zuwa ban ɗakin, ta sami Hoyam akwance ta suma, Alima tana murmushi, tare da kai mata duka, a cikinta tana faɗin.
"Jaka! Ke har kin isa ki mallaki zuciyarshi, toh na aiki lahira kafin na sami Sultan kowa ma na mai dashi bawa na."

        Ture ta Narmin tayi lokacin da Narjis ta shigo, ta kuma kifa mata mari.
"Lallai kina cikin azabar da tafi ta wuta Bala'i. Maza ki saka kayanki kafin Sultan Abdus Samad ya nime ki."

                  Da sauri aka shirya Hoyam, aka fitar da ita zuwa shashinta sannan aka kira masu kula da lafiyar matan shashin, kafin kace me, maganar ya yadu har Chamber Sultanah. Tayi farin ciki, amma kuma ta danyi shakkar abinda Alima tayi, dan haka tasa aka kama Alima, tun kafin Sultan yaji labarin. Sai dai abinda basu sani ba, kawai sai ganin Sultan aka yi yazo Chamber din Hoyam. Ganin halin da take ciki. Ya fusata shi ainun.

   Dan haka ya saka aka kawo mishi Alima, kallonta yayi sannan yace mata.
"Meye kika aikata?"

        Zubewa tayi a gaban shi tana kuka, tare da kallon Narmin.
"Sultan na cancanci mutuwa, amma kafin nan ina son na fadi wacce ta sani aikata wannan ta'asar," ta kuma rushewa da kuka.sannan ta fito da sisin gwal, a cikin wani san karamin jaka, ta zuba.
"Sai da nace miki Narmin ba zan iya ba, kika sani na dake ta, toh gashi kin sani zan sadaukar da Rayuwa ta. Sultan Narmin ce ta sani."
Cikin tsananin tsoro Narmin ta zaro idanu waje, sannan tace.
"Kiji tsoron, Wallahi ban aikata kome ba"

Kafin kace me, Narmin ta faɗa cikin maganar, kallonta Sultan yayi sannan  ya nuna ta hanyar fita, tare da saka masu tsaro su tafi da ita, ita kuma Alima a mata bulala talatin ladar aikata abinda aka sata, ita kuma Narmin kar a mata kome sai an gama bincike,

    Hoyam kuma kulawarta ya koma hannun Narjis, tare da Shairah. Dan haka duk abinda zata yi kar a takura mata. Bayan an gama shara'ar, Sultan ya tafi da ita shsshin sa taci abinci sannan yace daga lokacin da ta ji yunwa a shashinsa zata ci abinci, kuma ta amince.

      ---
"Amma, Shairah baka tunanin akwai wani abu a kasa, taya Alima zatayiwa matar da muma mun same ta da aikinta haka?"
Inji Narjis.
"Yau naga abinda ya fi zare tsayi, Yo ku mata kaidin ai sai a hankali, kawai tayi haka ne sabida dalilin kanta, tayu kuma sakata akayi, tayi kuma ita tasaka kanta."

         Kus-kus suke maganar, har na wani lokaci, sannan suka isa shashin Sultanah, kallonta suka yi ranta a b'ace.
"Waye a cikin ku ya saka Alima aiki?"
"Sultanah tuba muke, amma babu wanda zai saka Sultanah aiki akan wani dalili mara hujja,"
Inji Shairah,
"Kuma kawai anyi haka ne dan a rushe Yardan mu ne a ranki."

"Toh waye? Waye ya sakata aikata haka?" Ta faɗa da karfi.
Shiru suka yi, tare da sunkuyar da kansu, suna jiran hukuncin da ya dace da.
    
**
Istanbul.
Daular Umayyad
Salmanu Abul Hassan Bin Abrad.
Shine Sarkin wannan daular, kuma ana mulki bisa ka'ida da adalci, sannan su masarautan basu da fitina da tashin hankali, bayan haka kuma basu da magadar mulkin, sabida basu tsarin Magajiyar sarauta, wato (Empress Mother of King) kenan.

   Tattaunawa suke akan Taron da suke halatta duk shekara, a babban hakwatar musulinci da take garin baghdad. Sannan Sarki Abul Hassan tana son isar korafin shi ne akan yadda Daular  Abbasid, suke kwashe bayi karfi da yaji, sannan kuma suna kai hare haren wulakancin ga talakawan da suke iyakar su, daukar Umayyad basu da tashin hankali. Domin suna yin kome tsarin addinin Musulunci ne, shi yasa talakawan da suke wajen iyaka suke ta dawowa cikin daular.

       **
Daular Abbasid.
Kukan da take mishi ya tsaya mishi a ranshi, rike hannun shi tayi tare da cewa.
"Sultan Narmin ba zata tab'a sawa a cutar dani ba, don Allah ka sake ta ni na yafe matar ina bukatar ta!"
"Toh bar kuka haka, zaa saketa, sannan ki kula"
Gyada kai tayi, tare da mikawa ta shiga ban daki tayi wanka, zata fito shima ya shigo."

Dan haka suka kuma komawa cikin ruwan wankan wanda aka janyo mishi kamar wata korama, a cikin ban dakin shi...
Tana fita, ta nufi shashinta, sannan ta koma gurin Sultan, ta sha ruwa. A hanyan da zata gidan tsaro, suka bangaji juna da Alima, ai kuwa ya ta yanki jiki ta fad'i. Tana shure shure.

          *Shin wacece ta fadi Hoyam ko Alima*
BANI DA SALO! Amma ina da chakwakiyyoyi🤫🤨
#Paidbook
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: https://www.wattpad.com/1030677648?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=UAFVn6IqJPyhet8kdMafauzI6wppA5jaY51yBCvSwl%2FcN4uLk7Q7lAmpMHMD0fir5Z6QacntpbxI11YFe%2Fi%2BDwUpDABGp7ATfdvnLZHFieJDX6S1r%2FtPBG4sMaCfMkGe
*_ᎠᎪႮᏞᎪᎻ BIYU_*

   _The Historical_
~BOOK ONE~

Bismillah Rahamani Raheem

Page 4...

A razane Hoyam take kallon Alimah da ta yanki jiki ta fad'i. *Me take nufi?*
Kafin ta bawa kanta Amsa, Alimah ta danna wani irin ihu da yaja hankalin masu kula da shsshin su, shigowa da gudu.
Jini ne ya b'ata inda take da jikinta, kuka take tare da nuna Hoyam.
Wani irin tsoro ne ya kamata, dan dole ta zuba mata ido, haka Narjis da Shairah suka saka Bayi mata suka dauke ta.

Ita kuma Hoyam aka tasata keyarta, zuwa gidan Yarin, domin ta aikata laifin zubda cikin jikin Alimah. Kafin kace me har sun ririta alamarin zuwa babban al'amarin da har ya kai kunnen Sultanah.

   Take tasaka aka kamo Hoyam, aka kai ta Fadar Sultan, aka fadi abinda tayi aka kuma kambama al'amarin da yana cikin tsinuwar da aka yiwa masarautar akan Sarki ya b'oye.

    Dole aka tura Hoyam horo me tsannanin na tsawon sati biyu. Tare da hukuncin ba zata kuma zama babban shashin ba, sai kebantaccen shashin dake wajen masarautan, a can zata yi wa'adin da aka diba mata.

  Wannan abun da suka yi yayi mugun fusata ta, dan haka tana kallon Sultanah irin kallon sai na miki kwatankwacin abinda kika min, sai na rama sama da abinda kika min.

   
         Bayan tafiyar Hoyam, Sultanah Fazilatul nisa tasaka aka kama Alimah, tare da dauketa cikin masarautan baki daya, tare b'atar da ita baki daya.

  Bayan sun mata wulakancin na fitar hankali, aka mata barazanar kada ta kuma dawowa cikin masarautar idan ba haka ba, zasu kashe ta.
     *
Bayan an rufe Hoyam, bai hana Sultan Abdus Samad zagawa gurin Hoyam yana rage daren shi a gurinta har ta gama kwanakin da aka diba mata.

         A hankali kome yake tafiya har bayan wata biyar, aka sami labarin Hoyam tana da ciki, wannan shine dalilin da yasa aka dawo da ita cikin masarautan sannan aka bata shashi me girma irin na Sultanah Fazilatul nisa.

 
                Tunda Hoyam ta sami cikin ta shiga bada wani irin umarni wanda shi kanshi Sultan. Ya kasa magana akan haka, emirate councilors sun so dakatar da ita, sai ya  kasance Sultan ya bata kariya,

     A hankali cikinta na girma matsalolin masarautan na kara girma, har cikin ya isa haihuwa.

    Wata daren ƙaramar sallah ta haifi Yaronta namiji kyakyawa dashi, tun da aka d'ago mata yaron ta ganshi, aka kuma fitar dashi gurin Sultan, ya mikawa babban Limamin masarautan, yayi mishi huduba. Bayan Sultan ya gaya mishi sunan shi.

       **
Tunda aka fara shagalin suna sai da akayi sati Daya ana abu daya, sannan aka tsagaita.

    Matsalar da aka fara samu, shine Sultanah Fazilatul nisa, tana masifar kawo tarnaki akan Aamaan, wanda har ya kaita tayi tuntuben harshen cewa.

"Tunda ka zaɓe ta sama dani, sai naga bayanka har ita ɗin." Akan wannan furucin, sai da aka dakatar da mahaifinta, wanda haka ya fi mishi sama da ace baiwa ce ta kori yar shi daga cikin gidan da yake saka ran shine zai mulke ta nan gaba.

            Haka Hoyam ta cigaba da baza mulkinta har ta kai, ta sauke wasu gwamnoni na cikin yankunan kasar, ta dauko yan ƙabilar ta, ta daura. Kasancewar itace mahaifiyar Crown prince yasa babu wanda ya dakatar da ita sai Sultan.

      "Hoyame! Bana son kina shiga sha'anin mulkin na, nasan d'anki shine zai zama sarki anan masarautan, dan haka ki bar shiga harkokin cikin masarautan!"

    Cikin kirsa da kisisina, tace mishi.
"Toh shugabana, duk abinda ka bukata haka zanyi, tuba nake ya shugabana!" Yadda take maganar tana matse kwalla yana cikin abinda yake masifar sosa mishi rai, dan haka ya rungume ta, yana gaya mata sabida akwai masu Niman bayan su ne, idan aka ce yau tana shiga harkan mulkin shi tabbas zasu ga gazawar shi.

   Shi kuma baya fatan samun haka, kafin kace kwabo Sultan da Hoyame, sun lula wata duniya na daban.
          ***
"Amir Ansas! Baiwar Sultan tana min kama da wani anan masarautan." Inji Amir Fujai,

       "Bani daya na fahimci haka ba, ba kowa bane sai Ghanim, wannan Mutumin.."

        Da sauri yayi shiru, tare da juyawa yana kallon Inuwar mutum ya juya da sauri, take yasa aka bi bayan mutumin babu shi babu dalilin shi.

      *"Hmm! Ina sane da abinda yake faruwa, amma kuma taya kuke ganin zamu kawo karshen Abdus Samad, sannan taya zamu iya samun damar mulkin kasar nan bayan shi kanshi yana da magaji, sanan itama Hoyam din ba kyaleta zai yi ba"

Kallon Abdul Mannan suka yi sanan suka ci-gaba da cewa.
"Dole zamu bada damar canja wurin da kome, amma Sultan kan dole mu idda aikin mu akan shi, koda taimako ko babu taimako, sannan.yadda aka wulakanta mana mahaifi dole mu tsaya domin kare mutuncin shi."

         Haka suka bar wannan batun tare da tsayawa ka'in da na'in, kowani kusurwa na masarautar kowa burin shi ya zama shine magajin Izzah, dan anyi Mamakin yadda Sultan Abdus Samad yakai wannan lokacin. Ba tare da an sami matsala ba.

   Sanan kuma wani abun da ya d'aga hankalin mutanen da suke harin karagar, ba kome bane. Sai wayen gari da akayi Sultan Abdus Samad yana maida duk wani kundin tsarin mulkin ƙasar tare da da saka sunan Aamaan shine sarki na gaba.

   Tare da maida wasu abubuwan da ya kasance nashi izuwa na Hoyam da Aaman. Babu wanda ya saka baki ko ya nemi dakatar da Sultan, sai dai daga kulawar da ake bawa, Hoyam da Aaman. Sultan ya gayyace Yan uwan shi a wani liyafa.

Wanda ya bayyana Hoyam a matsayin Matar shi da zai aura, wannan shine mafi kololuwar tashin hankalin.

      "Na gabatar muku da ita ne domin kuwa gobe Insha Allah zan aureta, kuma itace Sultanah Hoyam."
Kallon shi suke cikin fusata, amma babu wanda ya isa bayyana fushin sa, tare da gabatar da b'acin ranshi bisa ra'ayin shi. Amir Kaisan yace.
" Ya kai d'an dan uwana, kasan kuskuren da kake cilla rayuwarka ciki kuwa?

Wannan shawarar bata dace da wannan tunanin ba, kayi min afuwa amma tabbas akwai abinda Hoyam take nufi da ta shigo rayuwarka! Ita din Y'ace ga Ghanim, mutumin da ya ciyar da Sultan Aamaan dan uwana, tare da matar shi Sultanah Sajiyah guba, ga ta nan tambaye ta.?"

     Juyawa yayi yana kallon Hoyam,. wacce kwalla ya shiga zuba mata. Dakyar ta bude baki tace.
Sultan! Baka yarda dani bane? Kai ka sayo ni, kuma ka..."

" Ya isa tashi kije zan zo yanzun."
Tana tashi ta rungume D'anta tana kallon su baki daya, sannan ta lashe bakinta, hawaye na zuba mata. Tabar gurin.

Tunda ta tashi aka fara cacar baki tsakanin Sultan wanda shi kan shiru yayi musu, duk abinda suke fada ana jin su, karshe haka suka mishi barazanar zasu kashe shi, idan bai dakatar da auran Hoyam ba. Fita yayi daga cikin su ya dawo shashin Hoyam, a daren ranar ya rubuta takardan dakatar da duk wanda ya gayyata aka ci abinci dashi.

Haka ya kwana zuciyar shi babu dad'i.
Sannan wani abun

Please Login or Register in order to submit comment