Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah mata basu burge ka?"  Ta tambaye shi cikin kaduwa tare da mugun tsoro,
Cuna bakin shi yayi kamar wani yaro karami,, sannan ya wani kwaɓe fuskar shi, ya wani jijjiga kanshi. Zaro idanu tayi kamar zasu fado kasa.

           Tare da saka hannunta dukka biyu akan fuskarta, tana jijjiga kanta.
"Don Allah! Karka min haka"
"Kiyi hakuri Anne, nafi" toshe mishi baki tayi tare da tambayar shi.
"Tun yaushe kafara?"
"Hmm!"
Ya faɗa mata, ba tare da ya kuma kallonta ba, fita yayi tare da nufar inda dakarun suke horon.
da yayi sannan ya zuba musu ido, ganin yadda suke horon, shiru yayi yana tuna Ikram, murmushi yayi lokacin da suke bawa kansu wahala. Tawowa Mahlika tayi da tiren shayi.

       Tana zuwa ta ajiye mishi sannan ta koma gefe, tana satar kallon shi, yadda yake jingine da wani matashi, murmushi tayi tana me jin yau zata sami kusanshi da shi Insha Allah, kallonta yayi alamar ta zuba mishi shayin. Cikin sauri ta fara kokarin zuba mishi.

"Sultan MEHRAN! Ga Amirah Jasrah nan shigowa!" Aka fada daga bakin kofar shiga gurin da suke. Bayi mata da maza suna bin bayanta, jikin Mahlika ne ya dauki rawa, har ta rasa yadda zata yi da butar shayin. Murmushi yayi daidai shigowar Jasrah, a hankali ya daura hannun shi, a saman na Mahlika, da sauri ta d'ago kanta tana kallon fuskarshi. Cikin Wata irin bazata, dauke idanun shi yayi akanta tare da juye mata shayin a hannunta, cikin sauri ta yarfe hannunta.
"Idan kina gaba karki kuma razana, gaba zan kona miki hannun sama da haka!" Gyada kai tayi da sauri,  kallon takaici Amirah Jasrah tayi sannan ta harde hannunta a kirjinta, sai da ta bari Mahlika ta mike kafin ta kalli gabanta ta saka mata kamar kamar yadda Ikram ta tab'a mata .

       Yana halkance dasu, amma ba zaka Fahimci haka, domin hankalin shi yana kan masu rehazal, faduwar kayan shayin sa ita kanta yasaka duk suka dawo da hankalin su kansu. Take mata hannun Jasrah tayi sannan ta durkusa.
"Wannan shine haduwar mu ta farko! Kar na kuma ganinki kusa da Inuwar Mehran! Balle kiyi kokarin shayar dashi shayi, idan ba haka ba ni nonar Mahaifiyarki zan shayar dake." Ta fadi haka tana karamin murmushi.

A hankali ta cire kafarta daga kan hannun Mahlika, sannan ta sake wata yalwataccen murmushi, tana kallon Mehran.

    "Ko zan iya zama kusa da Sultan?" Lumshe idanun shi yayi tare da jingina hannun shi akan matashin sannan ya daura kan shi akan hannun shi, yana wata da d'aya hannun shi.

          Ganin yaki mata magana yasata, kasadar zama a kusa da kafarshi. Aikuwa sai ganinta suka yi can tana dungure, domin shureta yayi da kafarshi. Da sauri dakarunta suka d'aga ta. Suna kallon Sultan.
Muryan Fudail ne ya katse musu, shurin da suka yi.ta hanyar cewa.
"Zaku iya tafiya da aita, laifi biyu tayi bayan ta ture baiwar shi, sannan kuma ta take mata hannun ta, kana kuma ta nemi zama kusa  dashi, bayan bai bata Umarnin  haka ba. Shi yasa ta sami damar tashi a raye."

         A fusace ta juya tana kallon Mehran.
"Ni ka tozarta sabida wata kaskantacciyar baiwa? Sai na shayar da kai mamaki kuwa mu zuba mu gani" ta faɗa a masifance. Sannan ta bar gurin tana ji ina ma da zata sami dama sai ta hallaka Mahlika.  A fusace ta bar gidan.

              Tashi yayi tare da kallon Fudail, yace.
"Ka turo min ita!" Ya shige abin shi. Koda ya shiga dakin shi zama yayi akan wani kujeran hutawa, kan shi a kasa. Yana fadi a ranshi.
_Nasan da kece! Babu wacce ta isa ta takaki ta kwana lafiya! Ina kewarki idan kin mutu kuma Allah ya gafarta miki! Idan kina raye kuma Ubangiji ya dawo min dake cikin koshin lafiya!_ ya faɗa yana me kumshe idanun shi.

     Karar bude kofar tare da sallama ya saka shi kumshe idanun shi bayan ya kishingida.
"Sultan!" Ta faɗa a sanyayye, wanda hakan ya nuna mishi cewa tayi kuka,
"Haka zaki cigaba da kuka?" Ya tambaye ta idanun shi kumshe, a hankali ta zube a gaban shi, tana me rike hannunta me ciwon.

           "Ba dake nake ba ne?" Ya daka mata tsawa, zuɓewa tayi cikin kuka da tsoron shi.  Dukda muryan shi bata bayyana b'acin rai, murmushi yayi sannan ya ce mata.
"Tashi ki bar nan" da sauri ta mike, har ta fita bai san lokacin da ya sake tsaki ba, a duniya ba zai kuma ganin mace me zunzurutun juriya da hakuri irin Ikram ba, dan haka ya juyar da kanshi yana me jin karin b'acin rai.

   Wanda ya kashe kiran bai mishi adalci ba kwata kwata, yaso kanshi da yawa, taya yarinyar da babu ruwanta zata fuskanci wannan kisar gillan, gaskiya ba a mishi adalci ba, kuma ba zai tab'a yafe jinin Ikram ba.

       "Sultan!" Fudail ya kira shi.
"Hmm!" Yace mishi.
Shigowa yayi tare da mishi magana a kunnen shi, sannan ya kura mishi ido, sabida shima Mehran shi yake kallo.

      Mikewa yayi sannan yace mishi.
"Yau ka bugi cikinta mana!"
"Sultan!"
"Uhm!" Yace mishi, tare da juya dara darar idanun shi akan Fudail.
"Toh zan gwada haka" ya faɗa tare da barin d'akin.
"Amma Sultan! Ya batun dayan binciken?"
Yadda ya tsuke bakin shi ya saka Fudail shiru, yana mamakin irin wannan kishin Mehran.
"Afwa!" Ya faɗa a sanyayye, gyara zaman rigar shi yayi sannan ya juya ya fita abinshi, yana ji kamar ya rufe Fudail da duka, akan me zai tsananta binciken shin Noman ya kwanta da Ikram ko bai kwanta da ita ba, shi sakarai ne za zai yi wannan kuskuren. Da zai aikata wanda ba zai tab'a yafewa kanshi ba.

   Kuma shima Fudail din bayayi mishi tunin da wata manufa bane, kawai sabida matsalar fada ne..
....
Kallon Jasrah Amir Hood yayi sannan ya sake murmushi.
"Akan me zaki tab'a wata baiwa a gaban shi? Ina ruwanki da tab'a wata mace akan idanun shi?" Karki kuma kar na kuma kama ki da laifin haka" ya fada tare da kallonta. Had'iye yawunta tayi sannan ta ce mishi.
"Naji Amir!" Ta faɗa a sanyayye, tana share kwalla da yake kokarin zubo mata.

    ~~~
SAHARA.
Dukar kafarta suka yi ta zube a gaban shi.
"Takaddirirancin ki yayi yawa, kullum da sabon labarinki nake kwana nake tashi, wacece ke?"

Banza nayi dashi ina kallon gefen da Izmah take zaune.
"Wacece ke?" Ya kuma daka min tsawa, dauke kai nayi, ya kuma hasala tare da mik'ewa tsaye.
"Wacece ke?" Juyawa nayi ina niman da wacce yake magana.
"Ina magana kin maidani sakarai?"
"Dama dani kake?" Na tambaye shi ina juya kaina gefe, murmushi yayi sannan yace min.

"Wacece ke?" Ya kuma tambaya na, murmushi nayi sannan nace mishi.
"Ba zan gaya maka kome a kaina ba, sai ka biyani."
"Niman kudi kika fito yi ne?" Ya tambaye ni,
"Farauta na fito, kuma duk wanda ya dakatar dani, kashe shi zanyi koma waye!" Na fada ina dariya.
"Me kike bukata?"
"Zaka iya dauka ta a matsayin yar kisar haya, zan kashe maka tun daga kan karamin makiyi har babban makiyi."

"Meye hujjar ki?" Ya tambaye ni, yana kallona.
"Ka bani umarni na nuna maka irin baiwata"
"Na baki! Ki kashe min Irffan bin Aslman!"

"Me kake bukata na kawo maka shaida?" Murmushi yayi yana me dauke kanshi ganin irin ba dan iya ba.
"Ki kawo min gawarshi!"

Juyawa nayi tare da mikawa Izmah hannun, muka fita.
"Wannan mahaukaciyar ina ce?"
"Wallahi kashe mutum bai da wahala a hannunta, har gwara kiyashi yana da nisan kwana da daraja."

Had'iye yawu, yayi tare da zubawa Sarautar Allah ido,
....
"Ikram meke damunki? Me yasa ba zaki zubawa Zuciyarki ruwan sanyi ba, bana son wannan yanayin, tsoro nake ji bana jin dadin yadda kike kashe mutane? Wacce irin kaddara ce haka?

    Ya kin fito daga cikin manyan gidajen duniya kike irin wannan abun? Ikram iyayenki bazasu ji dadin abinda kike aikatawa ba, ba laifi bane fansa, amma kashe wani dan biyan buƙatar rai kuskure ne"

Tsayawa nayi na kalle ta, sannan na durkusa muna kallon juna, nace mata.
"Ba zaki gane ciwon da nake ji ba, sabida basu kashe miki muradinki ba, idan ina tare sai na cire kan Mehran, nayi ado dashi a mashigar Masarautan SAMAIND!"

   Murmushi tayi sannan tace min.
"Kina kuskre! Kuma baki son gaskiya, zan so na rayu dan na ga yadda zaki Fahimci abinda kike aikata."

Banza nayi da ita, dan na gaji da maganarta, haka kawai za zata saka min tausayin kowa a raina ba, dan haka ya share batun ta.

    Koda muka isa gidan Irffan, ban tab'a su ba, kai tsaye cikin gidan shi na nufa, kamar yadda na sami labarin ya dauke Nimrah, haka na same shi ya wulakantatta tare da ajiye ta a wulakance,  jan iska nayi a hankali. Sannan nace mishi.
"Kuskure daya kayi bayan shi maza irin ka masu yunkurin aikatawa ba zasu kuma ba, me yasa ka tab'a yarinyar da bata san kome ba?

      Meye laifinta? Meye taci maka? Me yasa mata basu da daraja a gurin ka? Lallai zaka biya kudin aikin da kayi domin a tsarina bana hakuri. Izmah Kinga dalilin da yasani kai gawan shi can" itama kuka take sosai, sannan na kalle ta tare da cewa.
"Rufe min gidan!"

Daukar wani mayafi nayi tare da lullube ta, sannan na zaro wasu kananun wuka, na wurga misho har sai da suka shige kirjin shi.

"Ban maka kisar da zaka mutu ba, zan kai ka ne can ka mutu a gaban Aabis!" Na fada mishi. Kakari yake sannan na juya abu na, tare da ɗaukar jakar da na ajiye tare da cire wata buhun algarara ma cusa shi, sai da na gama sannan na fito, tare da kiran mutanen shi suka saka min shi akan keken dokin shi. Tunda muka fito, yaran shine zasu min gardama, na rufe idanu nayi ta girbe yan banza, sannan na dauki wacce na biyo bayanta, muka nufi keken sannan muka bar gidan, tunda na kalle ta sau daya ban kuma kallonta ba, har muka isa fadan Aabis, na wurga mishi.

    Kallona suka yi sannan suka bude buhun, aka ciro shi. Ana fidda shi yana mutuwa, murmushi Aabis yayi sannan yace min.
"Daga yau mun zama abokan ciniki!"
"Ina fatan babu cin amana?"
"Me yasa kike tsoron cin amana!"
"Sabida san iya azabar da duk wanda yayi min haka ne?"
"Ni kuma tsarinki ne yayi min!"
Murmushi nayi sannan nace mishi.
"Bana hada harkalla da kai na, da ƙwaƙwalwata nake aiki."
"Wai! Toh zan so mu cancare!"
"Mmh!" Nayi murmushi me sauti, sannan na juya zan fita, yace min.
"Ke makashiya shin zaki fita anan cikin sauki ne? Ko ance miki zan kyale ki ne?"

"Aabis bin Ansar, dan gudun hijira daga SAMAIND! Koda yake banga laifin ka ba, zaka iya haka dukda Ni nafi kaunar kashe mutane sama da kashe dabobbin, Sultan Aamaan Abdus Samad Mehran na biyu, ko ba zaka tafi domin daukar fansan mahaifinka bane? Idan ka shirya zamu iya kafa sabuwar harkalla, domin farautar da zanyi na gaba SAMAIND zan dirka a saman wuyar Zakin su. Nayi wasan kura da shi."

    Murmushi yayi sannan yace.
"Ku kama su. Ayita azabtar dasu har sai sun fadi wanda ya turo su."

"Zan dawo an jima tayaka hira!" Na gaya mishi haka domin tabbas zan fita daga inda aka ajiye mu.

Tunda suka tafi da mu, suke azabtar damu, wallahi na sha wahalar da tunda nake a duniya ban sha ba, sun taramin gajiya iya gajiya amma ban yi musu magana na, har sai da suka gaji da kan su, duka kyale ni, kwanciya nayi ina sauke ajiyar zuciya, domin na gaji da wahala. Zuwa na SAMAIND ba shine matsala ba, yadda zan shiga masarautar shine matsalar, dan haka na koma gefen Nimrah ina shafa kanta, tare da cewa.
"Kiyi hakuri! Laifin Mahaifiyarki ce ya shafe ki, gashi baki ji ba baki gani ba kin sami tawayan Sa'a, kiyi hakuri zan maida ke amma ba yanzun ba, dan nima sai na fita daga gidan nan tukun."

"Me zanyi nayi a can? Bayan na san mahaifiyata bata aikata daidai ba, laifi laifi ne. Hukuncin da na samu ba wani me yawa bane, gashi nan kin kare rayuwata da lafiyarki ba, ki dauke ni a Matsayin baiwarki ....

*200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

21
Wani irin tausayi ta bani, domin a girme ta girme ni, amma lokaci guda ta bada rayuwarta domin laifin mahaifiyarta, dauke kai nayi ina share kwalla da ta zubo min. Girgiza kai nayi ina kallon ta, sannan na dauke kai na, ina me kallon Izmah nace mata.
"Ba zan iya wannan b'arnan ba, ba zan amshi bukatar ki ba.

    Ni ba kowa ba ce face, me niman fansa, idan na kammala kuma zan dawo gurin ahalina idan kuma na rasa rayuwata ku zaku iya tafiya inda yayi muku, amma ba zan iya daukar ku a matsayin bayi ba."! Na fadi haka ina me juya musu baya.
"Ikram ina tare dake, kuma bana jin zan iya rabuwa dake, dan haka zan biki duk inda zaki shiga a duniya nan"

    Inji Izmah, matsowa kusa da mu, Nimrah tayi tare da daura kanta a kafadana tana faɗin.
"Gashi baki da shekaru masu yawa, amma Allah yayi miki baiwar jarumta, anya kuwa ba kashi daya bane a jikinki? Irinta Sarkin yakin Askandariya?" Murmushi nayi sannan na dauke kai na, sabida aman da nake ji, matsawa nayi, tare da kwara amai sosai.sannan na koma ina me kwanciya a kasa sabida cikina da ya kulle.

       "Sannun Ikram!" Suka zagaye ni, tare da goge min zofar da ya karyo min, "Ikram! Ko zaki iya zama ne na."
"Karki damu wancan d'an iskan zai yi magana!"

     A hankali barci ya kuma dauka na, bayan na farka na same su a takure, ruwa na nima nayi alola dukda bata wadacce ni ba amma kuma  nayi yadda ya sawwaka, sannan na gabatar da sallah da suke kai na. Anan aka turo mana abincin da ake kawo mana kullum, nan muka tab'a sannan suka kalle ni,zasu yi magana na saka musu hannu a baki dole suka yi shiru. Bayan dakarun sun wuce nace musu.
"Ku daina yawan magana!"
Gyada min kai sukayi .

   A hankali kwanaki suka yi ta tafi, ina son na fita amma kuma bana son nayi garaje, dan haka nayi kokarin koyawa kaina hakuri domin biyan bukata na, shine kadai mutumin da nasan bai da yar tsama da SAMAIND bawai dan bai da ra'ayi bane, asalima akwai fansa a ranshi dan haka nake son nayi amfani da fushinsa.

      Da kuma wasu abubuwan da dole sai nayi hakuri zan same su. Ba zai yiwu na same su da karfi ba, dan haka nayi kokarin dauke kai na daga abubuwan da suke min.

    Duk da yanzun kusan watan mu takwas kenan, a gidan yarin. Kuma bai tuna damu ba. Tun su Izmah basu saba ba, har suka saba.

  Da na hada jimilar rabuwa na da SAMAIND shekara daya har da watanin, murmushi nayi ina Kuma hango tazarar da take tsakanin mu da SAMAIND, tabbas nisan tayi yawa, kwanakin na kuma tafiya.

     ~~~
SAMAIND.

Duk kwace kwacen shi, wannan karon kan an sami nasarar gabatar da zab'en dan kusan shekara daya kenan da barin Ikram garin kuma a yau za a gabatar da kome, amma idan ka ganshi zaka rantse fuskar shi bai tab'a murmushi ba. Sanye yake da kayan irin na sarakunan larabawa, fuskarshi me yalwacce da kwarjini tayi lub lub, fuskar shi da tafad'a ta taimaka wajen fidda hanci shi har baka.

          Gefe guda ga wata yar kasumbar da ya tara, yayi wani irin kyau, yana zaune cikin isa da mulki, yan mata hudu ne da Jasrah ta biyar su, lokaci zuwa lokaci yana yawan kallon kofar shigowa harabar, mace d'aya tal yake dako! Shin zata zone? Ko ba zata zo ba? Wannan ita ce tambayar da yakewa kanshi tun da aka saka lokacin da za ayi abun.

Yake fatan Allah ya kawo ta, ya kuma kawo sanadin da zata zo, dan haka yana zaune a gurin har aka fara gudanar da abinda aka tarasu suyi. Mikewa Fudail yayi sannan yace musu.
"A bisa wannan zab'en da za ayi muna maraba da yan matan da suka zo kama daga wasu yankunan kasar zuwa na nan cikin gidan.

    Sannan akwai Amirah Azizah tana nan tafe itama, akwai kuma wata wacce Sultan bai bayyana mana sunan ta ba, tana nan tafe. Dan haka wannan zaben ba wani zab'e bane kece zaki zabawa kanki damar zama da Sultan MEHRAN.

   Kasancewar shi mutum me son cin abinci daga makusantan shi, yasa ya baku daman dafa mishi abinci me sauƙin yi, tare da sarrafa alkama da wasu dangin sa, sannan kowa yasan yadda ake dafa shayi a sha. Toh Sultan Mehran yana cikin mutane masu sun shan shayi, sai kuma wasu abincin da kika san anayi a cikin masarautan ku, zaku iya sarrafa shi indai zaki iya ci kuma Sultan yaci, bismillah..

    Sanan a cikin gwajin mu akwai tambaya akan sarauta, dan haka zaku iya farawa kuna da lokaci daga nan har azhar."

  Tsuru tsuru suka yi tare da kallon Fudail, domin dukkan su Amirorin basu aikin kome a gidajen su.

  Bayan Amira Jasrah, sai Yasmin Bint Mir Umdatuddawla, sai Ramziya yar Mir Jazib, sai Sawda yar Mir Rabib, shigowar Azizatul Nissah, Kanwar Sultan Abrad. Ya saka Mehran d'ago kanshi da sauri yana kallonta.   Dauke kanshi yayi tare da maida shi kan abinda yake gaban shi.  Yana jin babu dadi a ranshi. Tabbas ya rasata ya kuma tabbatar da haka ne ta hanyar ganin yadda yan matan suke kokuwar sarrafa girki.

     Ga kanshi ya cika ko ina, amma a gurin Sultan Mehran ba haka bane, fuskarshi bata da walwala, ya wani sunkyar da kanshi, sake maimaita bayanin da Fudail yayi, sannan ya shiga  kallon Azizatul Nissah da tayi tsuru tsuru,kafin ya fara aikin da ke gabanta.

           Haka suka yi ta aiki tare da gabatar da kome har kusan lokacin salla yayi, sannan aka turo dakaru suka tsaya a gurin dan suma sun idar da sallah.

Bayan kamar minti talatin suka kuma dawowa,  nan aka shiga kwashe abincin tare da jera su, a gaban Mehran kowacce idan ta ajiye zata rubuta sunta da inda tafito. Murmushi Fudail yayi domin dai kamshi ya ishe shi.

     A hankali aka shiga dibawa Sultan din tare da zuba mishi a wani tire, a hankali ya dauki data kofi me kyau ya wanke hannun shi,sannan ya dauki abincin yayi loma daya, cak yayi tare da kallon Yan matan da iyayen su da suka zo suma ganin abinda yake faruwa.

      Kallon Fudail yayi tare da mishi alama ya bashi abinda zai juye abincin bakin shi. Yana juyewa ya kalli, shi sannan ya tura mishi, shima yayi loma daya , zubda yayi tare da ajiyeta a gaban Mir Umdatuddawla, wato abincin Yasmin.

   Mika mishi abincin Jasrah akayi ya kalli Amir Hood, sannan ya dauki abincin ya kai lomar bakin shi. Kallonta yayi sannan ya dauke kan shi, tare da zubda abincin a cikin abin zubda. Ruwa ya sha, idanun shi sunyi jajjur,dauran kofin ruwa yayi tare da sha sosai, sannan ya mikawa Fudail yana zuba loma ya furza yana niman ruwa.

     Dauka abincin Azizatul Nissah yayi, ya kura mata ido, sannan ya kai loma daya,.sake kallonta yayi sannan ya maida kan shi dakyar ya had'iye sannan ya mikawa Fudail, shi kuma yaci ya mikawa Nawwas, sai Ramziya. Itama haka aka ajiye nata, kafin aka ɗauki Na Sawda.aka tab'a ajiye mata yayi tare da mik'ewa ya wanke hannun shi. Shayin aka fara jera mishi, dukkan dai ba a cewa Kome, kallon iyayen su yayi sannan yace musu.

"Ana tilastawa boya koyan yadda zata iya kyautatta iyayen gidanta me yasa Yaran ku baku koya musu yadda zasu rike mazajen su ba. A cire batun mulki ni mutum ne mai mugun son naci abinci daga cikin muhalina, yau gashi abin kunya yaranku da kike kaunar su, sun gaza bani abinda zancl. A haka kuma idan naji ace min mijina. Toh gaskiya ina son abinci."

Ya faɗa tare da dafe goshin sa, sabida ya gaji daga surutun da yake yi..kallon su yayi.
"Fudail ka ji dasu." Sannan ya mike tare da barin gurin.

"Abisa wannan namijin kokarin da kuka yi, toh mun kara muku shekara daya zuwa biyu,ku koyi yadda ake sarrafa girki, domin  koyi girki da zuciya daya karku yi tunanin zaki dawo ki hada mana zafin kai dan ba kyalle ku zamu yi ba.

    Sannan ku mai da hankalin ku, Allah ya bada nasara, karku manta an sami kusakurai dayawa, a cikin abincin ku. Dan haka wata shekara idan muka hadu ku tabbatar kunyi abinda ya dace.

     Sannan akwai kyautar da Sultan Aamaan Mehran ya bada a baku kowaccen ku!" Jinjina kai suka yi, sannan ya bawa dakaru umarni a mikawa kowa kyautar da Mehran ya basu, yan kunne ne na duwatsun lu'lu'u da sarkan su.  Amsa suka yi tare da godiya.

     Tunda suka juya suka fita shi kuma Fudail ya shigawa Manyan fada magana yadda zasu fahimta.
"Kuma kun ji yadda abincin yake ba? Toh zaku iya taimaka musu, ta hanyar amfani da zaman da zasu na koyan girkin, don Allah su maida hankalin su sosai, idan ba haka ba wata shekara haka zasu yi ta fama da shi. Mutum ne me son cin abincin."

        Kallon shi suke, cike da takaici dan zunzurutun wulakancin a rasa abinda za a saka yaran su, shine girki. Jinjina qarfin halin Mehran suka yi sannan suka mike tare da barin gurin. Har zasu wuce. Amir Hood yace mishi.
"Fudail ka tambaye shi baya tsoron guba ne?"

"Ai shi ba matsroraci bane? Mutum ne me wankakken zuciya, da yana tsoron guba da tuni yayi bankwana da duniya, su koyi yadda zasu saka mishi gubar yaƙe bukata." Inji Fudail,

      Juyawa suka yi suna kallon shi, kafin suka fita, daga gidan. Tabbas sunyi sake barin Sultan Mehran ya sami damar abokin kirki a tare dashi dan haka ba zasu kuma barin yaran su, zama mishi mutanen kirki ba. Domin yin haka zai iya dakushe Muradin su.

     ~~~
"Toh ya kuka yi dasu?" Sultanah Fazilatul nisa ta tambaye shi.
Hannun shi dukka biyu idan kirjin shi, ya juya yana kallon ta, sannan ya sauke ajiyar zuciya, yana kallon waje.
      Ita kam ta fara gajiya da wannan shegen miskilancin Mehran, ayi mutum magana ma sai kayi mishi jan aji kafin ka amsa, shegen yanga tayi mishi yawa. Had'iye yawun bakinta tayi tare da sake jefa mishi tambayar,

Niman gurin zama yayi sannan ya kalle ta, kafin ya sauke idanun shi yace mata.
" Basu iya ba!"

"Kamar Ya?"
Sake dauke kanshi yayi sannan ya cigaba da abinda yake yi, kwana biyu nan ya tsani magana, dan haka yadda yake tambayar shi kamar watsa mishi ruwan zafi take, dan haka yaja bakin shi ya tsuke,duk yadda taso yayi magana fiir yaki tanka mata, kuma yaki d'ago kai yayi magana.

Juyawa tayi zata bar gurin, muryan shi ya dakatar da ita, cikin sanyayye yanayi yace mata.
"Afwa Anne! Bana son magana ne!"
Goge kwallar da yake sauka mata tayi sannan ta girgiza mishi kai tana faɗin.
"Babu kome, Allah yasa mu dace!"

     "Amin!" Ya faɗa a sanyayye, domin ya fahimci tana cikin damuwa, duk da har yau zargin shi take yana bin maza, shigowar Fudail ya katse shiru su. Shi kuma ya koro musu bayanin yadda suka yi da amir Hood.

       
        "Hmm!" Yace tare da sunkuyar da kanshi kasa, yana wasa da yan yatsun hannun shi.
"Me yasa kai baka son ka fadi abinda yake ranka? Me yasa kake yunkurin rena min hankali? Idan anyi magana sai kace Hmm! Wato ga mahaukaciya kai baka san halin mutumin nan bane da zaka ce hmm! Kasan yadda nake jin damuwar shirunka? Da zance maza ne yanzun zaka dauki maganar da muhimmanci,"

     Kasa danne dariya Fudail yayi yana,toshe baki yayi. Fuskar Mehran a sake, duk da babu fara'a amma zaka fahimci, kalmar mazan da takira ya

Please Login or Register in order to submit comment