Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan yace mishi. "Maza ka koma ka dauko keken dokin" da gudu ya fita, tare da kallon su Izmah da suke kuka. Kamar me,  gani yake kamar Fudail baya dawowa, kamar yayi kuka haka yake ganin ta, dan ma ya tab'a wuyarta yaji tana raye, amma zubar jinin yana d'aga mishi hankali. Dan haka ya kalli Izmah da itace zata iya bashi amsa Nimrah kan tsoro ya cinye ta baki daya. "Basu kira sunan wani ba?" Shiru tayi tana nazarin abinda suka fada tare da kallon shi, girgiza kai tai tare da cewa. "A'a" shiru yayi tare da sake wata tsaki sabida ganin har yanzun  Fudail bai iso ba ji yaƙe kamar ya kurma ihu, dan haka ya dauke ta cak zai fita da ita sai ga Fudail nan.
"Afwa Sultan Mehran, dakyar suka barni na fito!" Ya kalli Izmah sannan yace musu.
"Ku fito!" Ya juya tare da bin bayan Mehran, yana fita aka bude kofar keken ya sakata a kujeran sannan ya juya tare da riko hannun Izmah ta shiga sannan ya kalli Fudail da yake rike da Hannun Nimrah da take kuka.
"Ina da abin yi!" Ya gaya musu a gaggaucce, da sauri sauri itama ta shiga cikin keken, hawa dokin shi yayi, Fudail ya hau gaban dokin.

      Basu B'ata lokaci ba suka nufi masarautar, inda dakarun suka nemi hana Keken shi kasancewar Sultan Mehran yana baya, ganin shi ya dawo gaba duk suka zube akan gwiwar su. Tare da niman afwa. Nufar gidan Mehran yayi da ita, shi kuma Mehran ya nufi gidan likitan masarautar yana shiga yayi karo da Amir Hood.

   "Zo muje ka duba min mara lafiya!"  Ya faɗa a sanyayye, ko kallon Amir Hood bai yi ba,shima likitan haka, bai kalli inda Amir Hood yake ba, zasu fita yace.
"Aamaan ba dai akan karuwar na bace kake damuwa?"
Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Bani da lokacin ka!" Suka fita a fusace, Amir shima ya fita daga gidan yana jin lallai dole ya kashe Ikram, wannan itace bakar kaddarar da aka ce zata shigo masarautan. Kuma ya fahimci haka ne tun daga ranar da Sultan Aamaan ya saka aka hukunta Zuhair, sannan bayan an konata Aamaan ya dauke ta suka yi balagoron har Madinatul Mah, wannan yasa shi kara fahimtar haka akanta. Amma baya fatan abubuwan da ya aikata su biyayya har yarinyar ta sani.

   ~~~
Tunda likitan ya isa gidan yake famar bata kulawa har ya dinke ciwon jikinta, Mehran yana tsaye akanta tare da sintiri, idan kana gidan sai ka fahimci yadda Mehran ya dawo, bayan wani lokaci likitan ya fito yana faɗin.
"Insha ALLAH zata samu sauki, sannan a kula da bayanta da kuma cikin ta."
"Zata ji sauki nan da sati biyu?" Mehran ya tambaya a dame,
"Eh Toh ya danganta da yanayin jikinta ne" rike bakin shi yayi sannan ya kalle shi, yace.
"Babu wani matsala bayan Ciwon jikinta?'
"Babu gaskiya"
"Mun gode!" Inji Sultanah,
Yana fita ta shiga dakin tare da kallon ikram, zucuyarta a raunane yake akan Yarinyar, amma tsoron goben D'anta take, tana gudun abinda zai je ya dawo mishi. Ikram itace ta dace da Mehran, amma idan ta duba yadda rayuwar su take, zai yi wuya kome bai faru ba, tana jin ciwon yadda kome ya cab'e mishi .
      
Shigowar shi da yayi ne ya sata dauke kanta daga Ikram.
"Naji kama tambayar zata sami lafiya nan da sati biyu. Meye kike nufi?"
"So nake ta shiga cikin zab'en matan da za ayi."
"Akan me?" Zuba mata ido yayi sannan ya sake murmushi.
"Sabida ta zauna a matsayin shugaban Kwarkwarorin na!"
"Yarinyar da take da sa'ar ce zata zauna a kwarkwarah? Hmm!.....
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

32

Ta tambaye shi tare da kallon shi,bakin shi ya gaza furta kome, sai zare ido yake.
"Mehran ba zan hanaka abinda kake so ba, amma ya girman hatsarin shi a rayuwarka, iya yanzun ma an fara samun matsala ina kuma ta shiga harkokin cikin masarautan? Ka duba abinda nake nufi akan Ikram kayi hakuri ka rabu da ita, bata da Sa'a a rayuwarka. Idan so ne a duniyar nan babu wanda ya kai ni sonka da kuma kaunarka da Ikram, amma dole ce Kanwar naki zata sani na iya dauke kai na daga Ikram, don Allah ka rabu da ita"

      Girgiza mata kai yayi, sannan ya juya tare da barin d'akin,  numfashi ta sauke sannan ta kalli yadda ikram take barci cikin wahala, kafin ta juya ta fita. A gaskiya bata kin Ikram amma halin da zata jefa rayuwar shi ce take jin tsoron Allah akan haka, kuma tasan zai yi wuya ya rabu da ita, shi yasa take jin kamar ta kori ikram idan taji sauki ko kuma ta saka a a lalata mata jarabawar da zasu yi.

               Amma kuma idan ta tuna yadda yarinyar ta b'ata lokaci tana zaune da Mehran sai taji jikinta yayi mugu mugun sanyi, taji bata da wani hanyar da zata iya cutar da ikram, sai dai kuma ba zata iya daukar kasadar barin shi ya zauna da ikram ba, Allah ya gani ba zata yarda da wannan tunanin ba, gwara duk abinda zai faru ya faru, amma tabbas zata raba su Insha Allah. Dan haka ita zata zauna da ikram har ta warke ta kuma maida ita garin su ta gaji yanzun son D'anta take bata jin zata bar shi ga kowa.

     ***
Kura musu ido yayi tare da cewa.
"Akan me zaku ce min Sultanah ta hana a cire al'adar duba al'urar mace? Gaskiya ba zai yiwu ba a cire shi ko kuma."

"Indai akan ikram ce kake wannan zakewar ba dai kai ka ba, domin haka da zaka aikata shi zai sanya kowa ya zargi wani abu daga gare ta, dan haka ka ɗauke kanka akan Ikram ko kuma na sanya a fidda ita daga Masarautan nan baki daya." Inji Sultanah, shafa kanshi yayi tare da kallon kasa, tabbas yana tinzira ta, domin bata tab'a juyawa muradin shi baya ba, sai wannan karon.

"Shi kenan, amma ba zan lamunci kasawa ba, dan wallahi idan aka min kuskure za a ga mugun tashin hankali.".ya fadi haka a zuciye, sannan ya bar gurin su....

   ..~~~ a cikin wannan yanayin aka fara shirya abubuwan da za ayi, duk da kuwa an fara tarb'an baki daga yankunan kasar. Musamman y'ay'an gwamnonin shi, Sakeenatu binti Abu Waqqas da Azizatul Nissah, sune kawai suka rage basu iso ba. Gefe guda kuwa zamu iya cewa Alhamdulillahi domin jikin Ikram ya d'an samu sauki, sai dai bata iya jure tsayuwa ko kuma wani abun da zai sanya ta zauna na wani lokaci. Sannan wani karin tashin hankali yadda take wasu abubuwan kamar tab'abb'iya, domin zata iya daukar wasu lokuta bata yi magana ba, idan kuma ka bata abinci zata na kallon shi kamar taga dodo, dan haka wannan yanayin ya sanya shi shiga tashin hankalin da ya kasa fahimtar kome. Itace dai yake sakawa a gaba da tunanin halin da zata kasance.

      Ganin haka yasa Sultanah ta kuma niman Uwaisul Qarni, sunyi magana sosai har ya gaya mata cewa.
"Ku godewa Allah da iya haka ne ya same ta, domin ban da Allah ya taimaka na bata  addu'o'in kwanaki ba da wallahi sai abin yafi haka, dan haka ku kai mata wannan, sannan karki zata abinda kike bukata zaki samu, karki kuma yunkurin rabasu, hakan kuskuren ne babba, karki nunawa Ubangiji wayonki, shi da ya had'a su shi yasan yadda zai yi da kowannen su. Dan haka kar na kuma jin kin ce zaki raba su, domin wani tunanin dake ranki."

     Da wannan yayi mata sallama, tare da barin gurinta,  haka ta kai wannan ruwan addu'o'in dakin Ikram ta bata, sai da ta shanye sannan ta fita. "Anne meke damun tane?" Ya tambaye ta ranshi a jagule, ajiyar zuciya ta sauke sannan tace mishi. "Jini yake bibiyarta, amma Insha Allah idan tayi barci ta farka zata ji sauki wasu abubuwan."  Kasa jure bayanin da Sultanah tayi mishi, dan haka ya juya ya bar gidan. Bai tsaya ba sai shashin da Su Izmah suke ya shiga ya same su a tsaye Mahlika tana cin kaniyar su.
"Waye ya baki damar hukunta wasu?"
"Afuwa Sultan ba zan kuma ba!" Dauke kanshi yayi sannan yace musu.
"Muje" haka suka bishi, cikin jin dadi ya kawo musu dauki. Bayan sun bar gidan ya kai su lambun da yake cikin gidan, suka nufa. Tun da suka zauna yayi shiru kafin ya tambaye su.
"Izmah meye faru da Ikram domin na Fahimci kun jima tare," gyada mishi kai tayi sannan ta fara bashi labarin abinda ya faru, lumshe idanun shi yayi sannan yace musu.
"Lallai biri yayi kama da mutum, sai yanzun na fahimci dalilin da yasa take saurin fushi, dalilai na rayuwa sun sauya ta, Ikram din da na sani ba ita bace wannan,wancan Yarinyar bace da nasani,  halin wannan ya banbanta na wancan."

       A hankali yake gaya musu abinda ya faru, da yadda aka kashe Noman ba tare da sanin shi ba. Amma yasan koda yayi mata bayani ba kula shi zata yi ba, dan ranta yana kan fansa, dan haka ya kyale ta tayi yadda take so.

    ~~~
Sintiri take hannun shi goye a bayan shi, tun sati biyu ya sami labarin Ikram tana cikin Samaind bai yarda ba, sai da ya tura amintattun bayin shi mutane biyu, suka je har can suka binciko mishi ita, dan haka ba zai iya kyale ta ba, dan wallahi sai ya kuma dawowa da ita rayuwar shi. Shigowar Nawwas ne ya katse mishi shirun shi.
"Sultan Abrad!"
"Hmm!" Ya faɗa kamar zai zunduma ihu, kafin yace mishi..
"Ikram tana raye!". Cike da mamaki ya d'ago kanshi tare da kallon shi sannan yace mishi.."waye ya gaya maka?"
"Na tura har mutane biyu sun duba min ita, amma tana cikin masarautar bata da lafiya, ka tabbatar sunyi aure da Noman?"

Ya tambayi Nawwas yana me kallon shi. "Eh na tabbatar sunyi aure aka kashe shi." Murmushi Abrad yayi sannan yace mishi.
"Kace min a daren amarcin su ko?"ya tambaya tare da kallon Nawwas, had'iye yawun yayi sannan yace mishi."eh Sultan Abrad" wani irin murmushin mugunta yayi tare da kallon Nawwas sannan yace mishi. "Dole Mehran ya bar min ita, domin an ce min zai gabatar da ita a zab'en da zai yi, ya ka gani idan na fasa cewa ta tab'a aure?"

"Amma wannan kuskure ne babba, karka yi amfani da abinda kake ji akanta ka cutar da ita mana! Kayi mata adalci idan."
"Kayi min shiru! Ikram tawa ce!" Ya faɗa da karfi, kafin ya shiga wasu zautattun bayanai kamar tab'abbe, yana gaya mishi abinda yake ji akanta,  tare da yadda yake ji duk wanda ya shiga tsakanin su, sai uwar shi ta haifi wani amma tabbas sai ya kashe shi.  "Sultan MEHRAN kuma sai na tsaya da karfin tsiya na raba su, ko kuma na raba mishi hankalin shi akan mulkin shi."

"Gaskiya kana sonka ka da yawa, da yarinyar nan tana da ra'ayinka dangane da zama da kai da Nan zata dawo, amma dake bata da ra'ayin ka,  gurin shi ta nufa, don Allah karka shiga abinda zai dame ka har karshen rayuwar ka" ya  fadi haka a sanyayye. "Shawara kake bani ko gargadi na kake?" Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Abrad bani da ikon baka umarni sai dai shawara idan zaka dauka idan na zaka dauka ba kabarshi Allah ya kyauta, an jima zamu bar garin!"
"Ka kira Samim! Zamu bar mishi garin zan biku!" D'ago kai yayi yana kallon Abrad cikin mamaki me tattare da damuwa. "Shi kenan!" Ya faɗa mishi, sannan ya bar d'akin. Wani irin murmushi yake irin na samun nasara akan abokin gaban ka. Yau zai je ya sami Ikram.
~~~>
Yau saura kwana uku,

A hankali na kalli Sultanah Fazilatul nisa, sannan na maida kai ma ga maganin gaba na, ina sha.
"Yau ma gani a gabanki kamar can baya, nazo domin Mehran yana bukatar ki shiga cikin zab'en."
"Tab" na fada tare da tab'e baki,
"Me yasa kike son ganin sai na sami  kusanci da shi? Wato dan d'anki ne ko? Toh gaskiya ni ba zan shiga dan shi ba, zan shiga ne dan biyan buƙatar kai na, dan haka ki kyale ni ba zan shiga dan shi ba sai dan rad'in kaina."

Kallonta Sultanah tayi tare da jin babu dadi.
"Amma me yasa baki jin Magana? Me yasa kike wahalar da mutanen da suka damu dake? Shi kenan, kiyi yadda kike so, amma ki sani, Allah ba zai tab'a barin hakkin shi ba, wallahi matukar kika jagoranci wulakanta shi, Allah sai ya saka mishi."

Kasa nayi da kaina sannan nace mata.
"Lokacin da ya kashe min mijina baki tausaya min ba, baki san yadda naji a lokacin b.."

Bamu san shigowar shi ba sai ji nayi ya shake wuyata ranshi a jagule. Huci yake kawai dan bai iya magana ba, sai ɓari jikin shi yake ya bani tsoro sosai.
"Sake ta nace" ta daka mishi tsawa, cikin fushi ya fita daga dakin bayan ya sake ta.  Itama fita tayi daga d'akin, Izmah da Nimra da suke bakin kofa suka shiga d'akin.
"Amma baki mutunci ko daya? Wallahi ba haka Mahaifiyar ki take ba, duk da sanin yarinta nayi mata Wallahi bata da rashin da'a, ke wacce irin shaidaniyar yarinya ce? Me kike bukata a rayuwarki? Kin san halin da Sultan Aamaan yake ciki? Ko damuwa da mutanen da suka kashe miki Mahaifiyarki baki yi ba, kin zo kin Buwayi rayuwar shi? Sabida ke yake rayuwa a nan,.sabida ke ya zabi ya xauka babu mulki wallahi Allah sai ya saka mishi, mutumin da bai ji ba bai gani ba kika tsana akan mutumin da bai kai iyayenki daraja ba,.na zata zaki tafi daukar fansan kanwarki ashe ke gurin bawan Allah zaki tsaya, jahilar banza jaka dabba,  idan kin so karki shiga dan Mehran ki shiga dan ki kashe shi wawuya doluwa wacce jahilci da rashin kunya ya cika mata kai,Mahaifiyarki koda ta kasance Sarkin yaki bata yi aiki da hauka irin taki ba, idan kin so karki bar Mehran a raye. Ban da shima da damuwa meye zai tsaya samun damun kanshi da yarinyar da babu mamora a jikinta. Dube ki har zaki kira kanki da mace, banziya kawai." Sake baki nayi ina kallon yadda ake tijara, domin tsakani da Allah suka zage ni tass, sannan kuma suka rabu dani.

  Ban kuma ganin su ba, sai ma suka daina shigo min, har ana gobe za ayi abun lokacin Sultanah Fazilatul nisa, ya ajiye ranar zata bayyana kanta. Sai dai bata da kwarin gwiwar haka,.ina zaune Fudail ya zagayo bayan gidan da nake zaune, zama yayi sannan yace min.
"Gobe Insha Allah za a gabatar da abubuwa da yawa,. Sannan Mehran zai so ki lashe zaben baki daya, Ikram Mehran yana raye cikin makiya ne, duk yadda nake son ki fahimta ba zaki gane ba, dan haka iya yau kike dashi tare da saka ido idan an gama zaben abinda sakamakon ya bada kina da karfin iko kashi talatin da biyar cikin dari, dan haka wannan damar da kike dashi ya isa ya tabbatar da cewa zamu sami sabon sauyi a Samaind, sannan don Allah karki saka idanu akan sauran matan, ki zuba musu ido idan suka tab'a ki ne zaki tab'a su karki yarda su miki tambarin da zai kai ki har fada domin matukar kika shiga makiyan Mehran da wasu zasu bayyana a rayuwarki.....
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

33
"Sannan karki yarda wani yasan batun kinyi aure, idan ya fito daga cikin masarautan nan zamu dakatar idan ya fito daga wajen masarautan nan zamu kashe koma waye, Ikram Mehran ya shirya tsaf domin baki rayuwar shi, don Allah karki bari wannan damar ta subuce miki domin na rantse da Allah, mutane dayawa suna niman kusancin su da Mehran amma Allah bai nufa ba, ke da kika samu kina mishi rikon sakainar kashi, Mehran yana da kirki kuma yana da hakuri, rayuwa da kika ga yayi tsara mishi aka yi wanda Allah ya tsara mishi kuma aka ruguje shi don Allah karki juya mishi baya lokacin da yake bukatar ki, don Allah ki taimaka mishi wallahi yana cikin damuwa ainun."

"Yana ina ne?" Na tambaye shi..
"Yana dakin shi da yake sama" ya faɗa tare da barin gurin, a hankali na mike tare da nufar cikin gidan, dakin shi na wuce. Samun shi nayi a dakin shi. A hankali  na bude kofar d'akin shi.  Karatu yake dan naji muryan shi yana tashi,  da sallama na shiga d'akin. Ajiye Alqur'anin yayi tare da amsa mata, daga haka ya cigaba da abinda yake, tun da na shiga tare da niman guri na zauna. Ganin ya cigaba da karatun shi ya sani kallon dakin da yadda yake cikin. Kome a shirye yake sai kamshin turaren shi yake, ga wani sanyin dad'i da dakin yayi. Ya bada wani irin yanayi, me wiyar fassaruwa. Lumshe idanu nayi tare da ware su akan wani loka, haka kawai naji ina son ganin abinda yake cikin shi. Dan haka na kai hannuna zan bude naji yace min.
"Kinyi min ajiye ne?" Juyawa nayi tare da barin bude kofar, kallon shi nayi yadda ya tara kasumba, idanu shi sunyi zuru, faffarar kirjin shi me cike da gargasa, ya kara cikowa sakamakon tarin kwanjin da suka cika kirjin. Sunkuyar da kaina tare da cewa.
"Kayi hakuri da abinda na aikata" juya bayan shi yayi tare da Cigaba da abinda yake, domin idan ya cigaba da kallonta, ran shin ba zai so yadda take nuna nadamarta ba, dan haka ya juya abin shi zai bar dakin. Shan gaban shi nayi tare da cewa.
"Ya ina magana ka share ni?" Na tambaye shi,

  "Me kika ce?" Ya tambaye ni cikin gajiya da gani na, eh mana ya gaji da gani na, idan na gajiya ba meye zai wani ce bai ji me nace ba.
"Kenan baki ji me nace ba?" Na kuma kuma tambayar shi a karo na biyu. Tab'e baki yayi sannan ya girgiza min kai, da naga da gaske shiga ban daki zai yi nayi maza na tare kofar, zuba min ido yayi sannan ya bude baki zai min magana na riga shi.
"Kayi hakuri mana"
"Toh bani hanya na shiga wanka," matsawa nayi daga jikin kofar, da yazo shiga cikin banɗakin. Tsayawa yayi tare da bude kofar zai shiga. Riko hannuna yayi muka shiga tare, tunda muka shiga na fara hada mishi ruwan wanka, bayan na gama, na kalle shi.
"Zoki goge min baya!"
Ya faɗa min haka yana shiga ruwan wankan, zama nayi a saman gurin wankan na shiga wanke mishi kanshi tare da taimaka mishi har na gama na fito shima ya karasa, ina gamawa na fito daga dakin shi. Sannan na sami tawada da alkalami na rubuta musu karamar wasika, sannan na bar gidan tare da su Izmah basu so haka ba, amma babu yadda suka iya dani.

         Lokacin da ya fito yaga Anne da sakon ta karanta, murmushi tayi sannan tace mishi.
"Yarinyar nan tana da kaifin basira, zata shiga amma bada ikon ka ba, zata shiga da ikon Aabis Bin Ansar,  Sarkin sahara. Kenan idan ya shigo da tambarin wata masarautan."

"Amma lallai Ikram mahaukaciya ce, kinsan daga Masarautun da tafito? Daga Askandariya da kuma Merocco ne fa, taya ba zata shiga da ahalin ba? Me yasa ba zata iya tsayawa danginta ba,.idan tayi kyau sahara za a kira idan ta ɓaci kuma wa za'a kira?" Ya faɗa a zafaffe, yau da Ikram tana gaban shi babu abinda  zai hana shi ya mare ta, domin ya tsani renin hankali.

         "Ba zata so tab'awa daularta suna ba, sannan idan ta tsayawa danginta ta fadi abin kunya ce a gare ta,.idan kuma tayi nasara Cigaban su ce, dan haka ka kyale ta,.muga tsarinta tunda gobe za'ayi abin."

Ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon Sultanah, "Ni yanzun ban," "gidan Mahaifiyar Fudail ne zasu zauna domin ina ganin yau sahara zasu tawo da wakilar su."

            Haka suka shiga tattaunawa da yadda abin zai tafi yadda ya dace.
---
Tunda na shiga dakin mahaifiyar Fudail,nake murmushi sabida dattijuwar tana da kirki da addini, tana yawan ganin yadda Nimrah ta takure guri guda, ni da Izmah kuwa hiran mu tayi da ita. shigowar Fudail ya kura mata ido, sunkuyar da kai tayi tana murmushi, murmushi mahaifiyar shi tayi tare da cewa.
"Fudail itace Nimrah ko?"  Kunyar Maman shi ce a kama shi yace min.
"Ikram Sultan Mehran yana farfajiya."

      Fuskar damuwa nayi sannan na mike tare da yafa alkyabar ta, ina fita ha hango shi hannun shi cikin aljuhun wando shi, ya jingina da bishiya, tare da juya min baya. Tausayi ya bani a karo na farko bayan na dawo da niyyar sai na kashe shi. A hankali na taki bayan shi, na tsaya.
"Amincin Allah ya tabbata a gare ka"
"Kema haka ya tabbatar a gare mu baki daya, sarauniyar yan taurin kai, wallahi Ikram ina tausaya miki ranar da zaki shiga hannuna, Kinga kwana biyu ban saka ki kuka ba ko? Shine kike min yadda kika so? Sama kin bani hakuri zaki bar cikin Harami ne? Me yasa kike son nunawa duniya baki da daraja ne?"

   D'ago kai nayi sannan nace mishi.
"Na sani mana, taya zan kai kaina cikin dangina nace musu nima daya ce daga cikin su? A'a kawai dai na zab'i muradun zuci ne nayi nisan da zasu nime ni ban sha'awa ace na kai kaina suyi tsammanin nazo yaudarar su ce!"

Ta fadi haka a matukar sanyayye, rike hannun ta yayi cikin nashi yana kallon yadda take sunkuya da kai kasa,
"Kina da hankali amma ba me yawwa ba, domin haukarki tafi yawa" murmushi nayi, bance mishi kome ba. Kuma ai bani da abinda zan ce, kawai dai na cigaba da zama kafada da kafada da shi, duk da hiran ta kurame ce amma kuma yana matukar muhimmanci.
"Ashe kin iya fada haka ranar da nazo ma zata zan samu an yi gunduwa gunduwa da yar kwailata sai naga ashe kwaila jaruma ce har ta iya salon Mehran?"
Kallon mamaki nayi mishi domin mutum ne da baida yawan magana, amma yadda yake surutun sai abin yazo min  wani sabon a gurina.
"Ki daina irin wannan dabi'ar mazan, ke mace ce bana son ki gaji mahaifanki. Sultanah nake so ki zama ba wata bardiya ba."

       "Kana sona ne?" Na tsinci bakina da tambayar shi, kallon juna muke tare da kasa furta kome, "kiyi hakuri! Ban tab'a sonki ba, kawai ina bukatar kine a rayuwata, kuma nasan kema kina bukata na a rayuwar ki!"

          Sunkuyar da kai nayi ban kuma cewa kome ba, kawai dai nasan nayi kuskuren tambayar shi, amma kuma me yasa kowa yake ganin kamar yana sona ne! Bayan shi ba sona yake ba, kawai ra'ayina yake.
"Ki daina abubuwa dayawa ki zama mace sosai, na bawa Fudail sako yabawa Umman shi zata miki bayani," juya fuskana yayi tare da hura min iskar bakin shi yana me kallon kwayar idanu na, d'ago kai nayi tare son zan mishi magana, ya zira min harshen shi cikin bakina, zaro idanu nayi cikin wani irin tsoro da shaƙar shi. Iska ta hancina hannun shi yakai keya na, ban san lokacin da na cusa hannuna cikin rigar shi ba, tare da shigewa jikin shi.  Ban tab'a jin yanayin da nake ji ba, mun jima a haka kafin na janye jikina daga cikin nashi, riko hannuna yayi tare da cewa.
"Don Allah ki tuna da wannan gobe karki bani kunya,!" A hankali ya mike tare da mikar dani, hannun shi ya kai k'uguna.

     "Ina bukatar ki daina wannan dabi'ar mazan ki koma mace, duk cikin su kin fisu yarinta, so nake ki zama yarinya kamar yadda nake so."

     Kallon shi nayi tare da jin tausayin shi,

Please Login or Register in order to submit comment