Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Allah yayi min.
Ana gama rufe min idanuna, na saka kwarin a cikin bakar, sannan na ja a hankali, ji nayi kamar anzo dai dai bayana, an kai hannun kan cikina, sannan aka d'aga hannuna da naja kwarin.
_Zuciyarki ta buga kamar yadda zaki dake kwarin, karki fadi domin idan kika fadi asara na ne, so nake Nasara ya aure ki_

Jan karin nayi da karfi, sannan na sake shi cikin wani irin nutsuwa da fitar numfashina, naji karan isar shi gurin domin yayi kara "fitttt"

     Kafin faruwan haka ina jin karan bushe bushe, amma ina sakewa naji shiru kamar an dauke ruwa.
"An gaida sarauniyar baka! Bude idanunki."

      A hankali na warware abin ina kallon gurin, wato da ya caki abun sai da ya huda shi har wajen idanun.

     "Ku dauko min ita!"
Inji Sultan, har inda yake na isa sakamakon sakani a gaba da dakarun suka yi. Ina zuwa na zube a gaban su.
"Yarinya meye sunanki?"

"Salwah!"
"Ina iyayenki?"
Murmushin gefen baki nayi sannan nace mishi.
"Ban san su ba"
"Kamar ya? Ki iya furucin ki, domin a gaban Sultan kike"
"Ni kaina ban san kai na ba, abu daya na sani an kashe min d'an uwana, kuma zanje daukar fansa, bayan nan hatta garin da na fito ban san shi ba. Iya sunana na rike"

       "Baki iya tuna kowa ne?" Sultan ya tambaye ni,
"Mmm!" Na fada tare da sunkuyar da kaina,
"Waye ya koya miki harbi?"
Damke hannuna nayi sannan nace mishi.
"Wallahi ban san shi ba! Kuma na manta dashi baki daya!"

       "Kinyi harbin da sak Almustapha ne yake iya harbin, dan haka zan saka ayi min binkice akanki."

"Nagode!"
Na fada. Sannan na mike, tare da komawa gurin. An nuna min yadda zamu yi wasa na biyu, duk sauran suna da masu horon su. Nice daya bani dashi. Takobin katako aka bamu, dan haka tunda ka hada ni da wani, na kayar dashi,.aka kuma hadani da wani na kayar dashi.

A take aka fara nuna rashin jin dadin yadda nake kokarin rushe tarihin samari ukun nan, ga baki daya duk abinda aka yi sai na nuna zarra, dan haka muna gama amfani da takobin aka ce zamu yi gwajin damtse.

Anan ne mutane da yawa, suka shiga murna dole na fadi, shi kuma al'amari irin wannan dabara ce ba karfi bane, dan haka Ni abokin karawa na, duka daya nayi mishi na biyu kuma sai da na kwantar da shi, sannan na koma gefen, abinda yafi basu mamaki zafin nama na.hakan muka gama sannan aka sallame mu.

     Duk yadda yaso ya dame ni, hana shi magana nayi, har dare ina zaune sai ji ina son fita, dan haka na shirya na fito, haduwa nayi da samari ka uku nan.
"Gwana!" Kallon su nayi sannan na dauke kai na, sake tare ni suka yi, naga zasu bani ciwon kai,

   Shine na sauki wani karamin itaccen da na a gefen hanya, na shiga hada musu zafin kai dashi, sai da suka gudu da kafar su..

     ~~~
SAMAIND

   Zaune yake yana bitar darasin shi, Fudail ya shigo yau kimanin wata guda har da sati biyu Baya faru, zama yayi a gaban shi, cikin murmushi suka kalli juna sannan yace mishi.
"Sultan da fatan na same ku lafiya!"
Murmushi yayi sannan ya kalle shi, iya murmushin yayi ne saboda Fudail, zama yayi. Ya shiga mishi bayani ne. Mika mishi wani kaya yayi sannan yace mishi.
"Kamar yadda ya faru dai tayi auren, har nazo da abokin shi. Sai dai a daren da muka fito niman su, aka kashe shi. Bari na kira shi"

    Ji yayi kamar ya cire zuciyar shi ya huta da wannan tashin hankalin, haka Fudail ya shigo da  Sarwat. Yana ganin Sultan ya zube tare da fashewa da kuka.

         "Wallahi iya bakin kokarina nayi amma ban ganta ba, banga dalilinta, lokacin da na dawo na sami Noman kwance cikin jini yace min.
Na dauke shi mu bar gurin, kuma nayi kamar yadda yace min, sannan yace min don Allah kar na sake ban nimo ta na kawo maka ita ba, Yasan ba kai ka tura a kashe shi ba, domin bayan faduwar mu, ruwa yaji daya daga cikin mutanen yana cewa.

Sun kashe dakarun Samaind, baki daya, saura Fudail ne kuma yasan suna hanyar zuwa, sai yake gaya min, don Allah na gaya maka kayi hakuri da ita, domin ba zata tab'a yarda ku zauna lafiya ba, karka biye mata domin ba lallai bane ta fahimce ka, don Allah kabita a Sannun, sannan yace min idan da hali na zauna a jikinta a matsayin me tsaron lafiyan ta."

     "Bayan kai waye yasan tayi aure?"   Fudail ya tambaye shi.
"Waɗancan dakarun sun san tayi aure.". Sarwat ya faɗa.
"Zaka iya boye maganar aurenta har abada a cikin masarautan nan?"

     Jinjina kai yayi, sannan yace.
"Eh Fudail!"
"Tashi ka tafi!"
Cikin sanyin jiki ya bar gurin, kallon Mehran Fudail yayi sannan yace mishi.
"Sultan!"
Dakatar da Fudail yayi tare da cewa.
"Kowa yana da damar zab'ar abinda yake bukata, ita rayuwar ta take bukata ya sabunta, Ni kuma na ajiye ta a guri daya. Shin kana ganin haka zai mana kyau? 

   Shi masoyinta ne, Ni kuma uban gidanta ne, shin nayiwa kai na adalci? Dan haka ka bar kowa yayi rayuwar da ya dace dashi, ya kuma zabi abinda yake bukata, karka tilasta wa wani yayi abinda bai da niyya sabida kai."

   Cikin damuwa da jin ba dad'i yace mishi.
"Sultan Mehran! Amma ai maganar gaskiya idan za ayi ta dole a cire son Rai, kana bukatar yarinyar a rayuwarka, kana Sonta."

   Wani irin juya hannun shi yayi tare da rike wuyar Fudail, kakari ya fara idanun shi sunyi jajjur, murmushi yayi sannan yace.
"Sultan MEHRAN! Kana son Baiwar ka"
Ture shi yayi sannan yace mishi.
"Karka kuma ambaton soyayya a nan, idan ba haka ba, zan hallaka ka."

     Cikin bakin ciki da takaicin halin Mehran yace mishi.
"Idan kaso karka barni a raye mana kai ka sani, amma kana son Ikram, soyayya me hade da kishi ma kuwa, kai kanka baka san wani irin so kake mata ba"

    Lumshe idanun shi.yaui ba tare da ya kuma kallon Fudail ba, haka yayi ta magana tare da masifa yadda yake boye shaukin shi.

         Bayan fitar Fudail, ya sake fuskantar shi kamar zai yi murmushi, sannan ya kuma daure fuskar, murmushin da bai shirya bane ya fado mishi, tare da tuna ranar da  zasu bar Madinatul Mah, murmushi ya sake sannan abinda ya faru a ranar ya dawo mishi kamar yanzun abun ya faru. Babu abinda ya fi d'aga mishi hankali, kamar ranar da suka kwana tare, haka kuma Noman ya ratsa tsakanin ta.

   Wani irin ajiyar zuciya yake saukewa kamar wanda ya sha kuka ya koshi, kuma zunzurutun kishi ne yake damun shi, dan haka ya lumshe idanun shi. Yana kuma hango cikin ƙwayar idanunta.  Juya kan shi gurin kunshin da Fudail Ya kawo mishi yayi a hankali ya janyo tare da fara warware shi.

    Turo kofar da aka yi ya sashi dakatarwa. Mahlika ce dauke da tire na azurfa, sai kofinan shi da yar butar ruwan zafi, tana zuwa ta ajiye a tabirin kusa da shi, ta fara zuba mishi.

            Da wutsiyar ido ya kalle ta, tana aikin jikinta yana rawa.
"Kin zuba min guba ne?"
Sake kofin tayi daga hannun ya ya fadi kasa, murmushi yayi sannan yace mata.
"Zoki min tausa!"
Jikinta yana rawa, ta mike tare da nufar bayan shi, ta kai hannunta a hankali tana mishi tausar wuyar shi.

    Ta jima a tsaye kafin ya sallame ta, sai da ta kwashe abinda ta zubda ta gyara wurin, sannan ya fita, Cigaba yayi tare da duba kayan, karamar fatar jimina da kayi rubutu a jikinta, nad'ewa yayi kafin idanun shi yakai kan Tambarin kasar marocco, sai wani tafar kura da aka yi rubutun shima da shi. Wanda yaga tambarin Askandariya, juyawa kayan yake tare da kallon su.

       Ko shi yasa take da tsananin zafin rai, toh amma ai wannan shaidar ba zai tabbatar da cewa ta fito daga babban zuri'a bane, kawai dai sun saka ne domin, mata bayani. Baya tunani me idanun nan kamar tsaka ta fito daga wata babban gida ne....
```BOOK one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```

#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: Monday-March-2021
*FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

11
      Cikin takaici ya kuma kallon kayan, yana mamakin halin irin nata, sam bai tab'a ganin me taurin kai kamar jaki irin, gashi garin shegen rashin kunyar ta, ya janyo an kashe ta a banza.

_Kana tsammanin zata mutu cikin sauki ne?_
Wani shashi na zuciyar shi yayi mishi tambayar, dafe goshinsa yayi, a sanyayye yace "amma kuma ance ta mutu?"
_Toh kai ka yarda ne?_
Yayi, tare da dunkule hannun shi,
_Idan har ka yarda ta mutu! Tabbas Zuciyar itace zata fara gamsuwa me yasa kullum_
Mikewa yayi dan ya fahimci, matsalar Ikram da shi, zata iya sakawa a fara kiran shi tab'abbe.

Koda ya fito falo ya sami Sultanah Fazilatul da Fudail, sai Sarwat da yake basu labarin yadda aka kashe Noman, kallon su yayi tare da isa jikin tagar falon me dauke da furanin, yana gyarawa da wata wukar gyara fure.
"Abinda suka fada ya sanyani jin tabbas Sultan Mehran bai mata adalci" shiru yayi tare da jan fasali, kafin ya cigaba da cewa.
"Don sanye suke da kayan dakarun Samaind, kuma suka tabbatar mana da cewa, Sultan Mehran ya turo su."

      "Ba shi bane!" Inji Sultanah Fazilatul nisa, ta faɗa a sanyayye tana kurb'an shayi, kallonta su kayi, sannan ta cigaba da cewa.
"Ba dakarun SAMAIND bane, sabida lokacin da kuka fita idan baka manta ba, kun hadu da wani mutum, a wani jirgin ruwa, kusan kunyi tafiyar tare ne!"

Shiru yayi yana nazarin abubuwan da ya faru, a hankali ya d'ago kanshi.
"Tabbas anyi haka!" Wani boyayyen ajiyar zuciya ya sauke daga can yana jin yadda Sultanah take wanke shi.
"Toh mutumin ya biku har inda aka daura auren nan, sai dai bayan ya bar gurin ya dawo, inda zai tafi yayi na shi uzurin,. Bayan ya koma inda Ikram take ya samu an tadda garin, dama na tura shi ya dauko min ita ne!

               Ko da yabi ku dajin yace ya samu ana ta saran Noman, dan haka ya dawo, a hanyar dawowa ne ya hadu da dakarun Samaind da aka kashe su tare da watsa musu wuta suna ci, sannan haka ya tabbatar mishi cewa wad'ancan ba dakarun SAMAIND bane, domin a cikin masarautan ai mutanen da Ikram ta hana su kwanciyar hankali, ta saka Mehran a Jikinta, ba tare da ita kanta ta sani ba. Zuwan ku ya kara musu kwarin gwiwa, amma dama can an shirya kashe ta a ranar da za a bawa Mehran damar zab'en yan matan da zasu zauna dashi."

     Cike da mamaki yake kallon ta, sannan ya cigaba da abinda yake idanun shi sun yi jajjur.
"Shigowar Ikram masarautan nan, a yarjejeniya sulhu ta shigo. Kuma da aka shigo da ita an tabbatar matukar ta haɗu da Mehran zai yi wuya tafiyar su bata zo daya ba, shi yasa aka barta a karamar baiwa har aka kawo ta shashina."

              Mikewa tayi sannan ta nufi inda Mehran yaƙe, ta amshi wukar hannun shi tace mishi.
"Koma can ka zauna!"
Ba musu ya iso gurin su Fudail ya zauna, tare da sunkuyar da kanshi.
"Nice na turo ta gare ka? Ina bukatar ta a tare da kai! Duk macen da zata zauna da kai dole ta zama me ilimin addini! Me iya hukunta duk wanda ya aikata laifi! Me iya fada maka gaskiya kamar yadda babu wanda zai gaya maka! Sai abu uku da take tare da shi. Bata da tsoro! Bata da gulma ko munafunci, sannan mafi girman abinda ya ja hankalina akanta bata karya duk abinda zata yi akan gaskiyar ta take yin shi! Bata sakewa da kowa sai da kanta, kuma babu abinda ya dame ta da kai dan kasan ta ko baka santa ba. Wannan shine ya saka Ni na turata gare ka. Ina da yar da naso ta zo gare ka, amma ba zata yarda ka bata wahala kamar  yadda ka bawa Ikram ba, ba zata iya jurewa ba, shi yasa naki tazo.

          A yanzun haka na tabbatar Ikram tana raye,. Abu na gaba da take yi ba mamaki tana faffutikar sai tazo daukar fansa abinda aka mata, tasan halin ka, ka san nata, ka fara shiri kafin tazo gare ka."

    "Amma kuma Sultanah na duba kasar ruwan baki daya ban same ta ba, nayi iya bincike na, bata cikin ruwan, sannan dakarun da suka aikata hakan sun dubata bata cikin ruwan." Inji Sarwat,

Wani irin murmushi tayi sannan ta dauke kanta, daga gare shi.
"Tana raye," ta faɗa bayan taja numfashin ta, kura mata ido suka yi, kafin suka jinjina al'amarin.
"Ikram ba gama garin mutane bane, tana da juriya da jarumta, zata dawo domin koda ta mutu dole za a kuma haihuwarta, dan haka ku saka a ranku zata dawo, kai ma baka tsira ba, domin duk ranar da ta shigo ta ganka sunanka makiyinta."

     "Toh don Allah meye nawa? Ikram da dama can haushina take ji wai Ni munafuki ne, ina sane nake barin Noman kula yan mata, balle kuma yanzun ta gannin a gurin Babban makiyinta ina ga cewa zata yi Ni ne na saka baki aka kashe NOMAN." Ya fashe da kuka. Me Fudail zai yi ban da dariya, shi kansa Mehran sai da yayi murmushi. Ganin haka Fudail yayi ta saka shi yana fadan halayyar Ikram,  sai ganin Sultan Mehran suka yi ya kishingida yana me sake murmushi.

       Musamman yadda take tafiya kiwo, tare da yadda take cin kaniyar yan matan dasuka ce zasu so NOMAN, sai gashi sam bai tab'a jin kishin noman ba, asalima jin dadin yadda ake fadan halayyar su yake, inda ya fahimci cewa. Noman yana da saukin hali, kasancewar ita kuma tana da zafi kome kashin abu zata iya dakatar wa.

       "Sai dai duk da wannan zafin na Ikram a cikin gidan su, kare yafisu daraja." Ya faɗa hawaye na zuba mishi.

    "Tun bayan mutuwar Mahaifiyar su, sai suka kasance kamar marayu, duk da kowa yasan mahaifin su, shi yake horar da duk wani matashin dake garin Gezira fada, Mahaifiyarta kuma tana horar da Mata yadda ake amfani da kibiya, ban tab'a ganin uwa me son yaranta ba, duk da basu son nunawa yaran muhimmancin rayuwa, kamar a baka damar kayi walwala cikin Arzikin da wadata.

    Sariya itace baiwar Mamar su, kuma tana matukar kula da yaran, dan haka da Mahaifiyar su zata rasu, ta bukaci mijinta ya dakatar da horan da yake bawa mutane, domin halin da ta tsinci kanta yana da nasaba da horon da suke bawa mutane ne, har wasu matasa daga wani yanki daga cikin garin suka farmake ta, bayan sun mata fyade da tsohon cikin."

Kofin da Mehran yake rike dashi na tankarar sai da ta tsage tare da soke mishi hannun shi, yana diga da jini.
"Suka wulakantatta, abinda ya saka bawan Allah nan kasa koda motsi, domin sunce zasu koma kan Babbar Yar shi da karamar, haka aka yi ta kokarin daukar mataki ya hana, sannan yace ya barsu da Allah, zai bi musu hakkin su.

   Bayan rasuwar ta da abin cikinta ne ya auri baiwarta, tun daga lokacin bai da kwanciyar hankali, ana haka wata rana ya fadi a gurin kiwo, "

Haka ya basu har labarin yadda aka dauko Ikram akan lafiyar kanwarta.
_Ce maka akayi sabida jin dadi nake nan! Rayuwata bata nan! Ina raye ne sabida kanwata da yau zan sami duniya da kome na cikinta tace tana bukata zan bar mata koda kuwa ace abinda nake so yana cikin shi! Ka kyale ni ba zan zauna ba!_

Kusan abinda yake yawo kenan aransu dukkansu uku. Wato Sultan Mehran da Sultanah, da Fudail.
"A ranar da ta bar garin Allah ya amshi rayuwar Airan, wanda zuwan mu ne Noman ya gaya mata, bayan nan ba zance ta san abinda ya faru da Mahaifiyar ta ba."

    "Zata sani! Kuma zata bi hakkin jininsu. Idan ta kyale su sun cutar da ita, dan haka dole ta rayu, dole tana bukatar rayuwa a duk inda take zata so taya nisan kwana"

        Kallon Fudail tayi tare da kallon Hannun Sultan Mehran, da sauri ya dauko kayan aiki ya fara duba mishi hannun shi. Kallon Sultanah yayi sannan yace mata.
"Ina bukatar zuwa gezira!"
Kallon shi tayi cikin murmushi sannan tace mishi.
"Ina zaka? Daukar fansa abinda aka mata? Indai har zaka iya haka toh ka fara bincikar waye ya kashe Mahaifin ka, idan har kayi haka zaka iya zuwa gezira."

Daga hakan ta mike tare da barin gurin.
   ~~~
Ji nayi an watsa min abu kamar raga, suka dauke ni sama aka nufi hanyar wani gida dani, watsa Ni suka yi a kasa.

     Fita nayi daga cikin ragar, tare da kallon su, nace musu.
"Ni bana son fada, don Allah ku kyale Ni!"
"So muke mu baki abinda wancan sakaran ya kasa baki."
Dariya na kwashe dashi sannan nace musu
"Idan har kuka iya cire koda rigar jikina, nayi alƙawarin da kaina zan kwanta kuyi ta hawa kai na kuna sauka, idan kuma nayi nasara kareraya ku."

Dariya suka kwashe da shi, sannan.
"Kai ku cire mata kayanta tsaf ku miko min ta"
Kai na a sunkuye, badakaren ya miko hannun shi, murɗe hannun shi nayi tare da juyawa nayi tare da karya hannun, sannan na naushi hakarkarin shi.

     Faduwa yayi tare da jijjiga kamar me farfadiya, mik'ewa nayi domin ina durkushe. Na tsaya ina shafa hannuna, sannan na musu alamun su tawo. Haka muka yi ta dasu..sannan na karya hannun Yazeed da Yasir, Samir kuwa targada mishi kafa nayi. Sannan na juya na bar gurin.

       Ina shiga gidan mu na bayi, sai ga dakarun.
"Ke!"
"Kayi kasa da muryan ka sabida mutane suna barci, muje!"

    A hankali na fita tare da binsu, har gidan da aka kai ni, ina zuwa na samu kujeru biyu babu masu shi, daya kuma Rahil ne jikin shi yana rawa.

          Ina zuwa na dafa kafad'ar shi, ina lura da yadda ya sauke ajiyar zuciya.
"Ke wacece?"
Kallon Amir Sulaiman nayi, sanan nace musu.
"Zan gaya muku wacece ni, amma shi wannan ku sallame shi. Idan ba haka ba. Zan iya samun kai cikin rashin nutsuwa."

              "Ke!" Amir Sulaiman ya saka min tsawa, takowa nayi har gaban shi, tare da  shafa fuskar Yasir, tare da kai fuskana kan ma shi.
"Kasan me? Da ace babu yarjejeniya, da na karya kashin wuyar wannan da yake cewa a kwab'e min kaya yayi yadda yake so dani, tarbiyyar da kai mishi kenan?" Wani tab'e baki nayi sannan nace mishi.
"Yadda kuke farautar Rahil ya sani fara shakku akan ku, dan haka ku zuba min ido ko ku rufe idanunku."

   Daga haka na riko hannun shi muka bar gurin, har mun isa baki kofar na d'ago yatsar hannuna nace musu.
"Kar a kuma tab'a min shi, domin zan iya samun damar kashe kowa"

    Sannan na fita dashi tare da kallon shi, kai hannun shi yayi tare da rungume ni, ina jin sautin bugun zuciyar shi.
"Nagode" ya faɗa hawaye na zuba daga idanun shi. Tausayi ya bani na rungume shi. A hankali na cire hannuna a jikinshi muka tafi gidan, har cikin gidan shi na raka shi. Zan fito. Yayi maza tare da riko hannun na.
"Ki zauna anan!"
Ya faɗa min cikin dakewa, tare da zuba min idanun shi. Haka kawai sai.naji yayi min kwarjini. Dan haka na zauna. Ya nufi ban daki bai fito ba, sai kawai yayi ta tsalla ihu.
Da gudu na shiga. Dariya ya saka min tare da cewa.
"Toh zoki taimaka min"
"Baka da hankali"
Na juya zan fito.
"Wayyo Allah!"
Da sauri na juya, "subhanallahi!" Na fada tare da juyawa da sauri nayi, ina jin takaicin wannan Iskanci tare da fita daga ban dakin. Koda ya fito ina tsaye, zama yayi tare da cewa.
"Zoki goge min kai na;"
Wato na lura da Rashin mutuncin shi wani yakewa, dan haka ina zuwa kusa dashi na zabga mishi naushi.
"Wayyo Allah na, kiyi hakuri!" Ya faɗa kamar zai yi kuka, hmm na ce tare da juyawa zan fita ya finciko ni,  na fado kanshi.
"Baka san ina d'aga maka kafa bane?" Juyar dani yayi. Kallona yake tare da lumshe idanun shi.
Kanshi ya kai wuyana nayi maza na kai hannuna wuyar shi.
"Kisan abinda nake ji akanki?"
"Don Allah!" Fada muryana na rawa, janye hannuna yayi tare da kallon cikin idanu, murmushi yayi tare da kallon yadda nake zare ido, hancin shi ya kai kan nawa yana gogan nawa.
"Don Allah kabari!"
"Har yanzun baki sona" gabana ne ya fadi,
"Kayi hakuri! So daya tak nayi kuma na binnewa me shi, zuciyata da ruhina yana gare shi, bana jin kome akanka shi daya nake jin tasirin kwayar idanun shi, shirun shi shine Yaren shi a gurina, na manta da shi amma zuciyarta yana rike da dabi'ar shi. Kishin shi akai na a bayyane yake, ban san fuskar shi ba, amma kaunar shi dawammamiya ce.....
```BOOK one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```

#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: Monday-March-2021
*FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

12
Ganin yadda kwalla ke cika a idanuna yasa shi girgiza min kai tare da cewa.
"Kiyi hakuri! Ba zan iya barin ki, ki subuce min ba, dole nayi abinda zaki zama nawa har abada."
Cikin wani irin sauri yake kokarin rabani da kayan jikina, riko fuskar shi nayi, sannan nace mishi.
"Me yasa kake ganin kamar zina itace saukakkakiyar hanyar da zaka same ni? Me yasa kake ganin kamar idan har ka kwanta dani ba zan guje ka ba, zan zauna domin rufawa kaina asiri? Karka manta ni zuwa nayi nan kasan dalilin zuwan nawa? Baka sani ba, daga ganin mutum a jikin ka har ka bashi zuciyarka, toh kashe nazo yi!" Na fada da karfi.
    
   Cikin wani irin tsoro da tashin hankali, ya kalle ni. Tare da sake ni. Yana kallona ilahirin jikin shi rawa yake, tare da nuna ni da yatsa.
"Meye nayi miki?"
"Sani aka yi! Dan haka karka yi tunanin soyayya tana cikin abinda ya sani nake zaune da kai, ganin ta kowani kusurwan gidan sarautar ku ana niman ranka ya sani bincike inda zan Fahimci meye matsalar su.

           Hakan ba zai sakani samun damar binciken ba sai na tsaya a bangaren ka, shine dake kai banza ne ka fada soyayya dani, ka kiyayye kanka domin Ni zan kashe ka ne" na fadi haka ina mik'ewa daga gadon, tare da gyara jikina na fita, ina jin yadda yake kuka ya bani tausayi dan haka na fita daga gidan.

      ---
Duk wanda na tambaya meke faruwa, basu bani amsar asalima tsoron tambayar suke, sannan abinda na fahimta, yaran Sultanah Balkisu Ikram sune kusan sadaukai a cikin masarautan, kuma basu nan a raye, dan haka na yanke hukuncin tun karar Sultanah Balkisu Ikram, sai da na bari dare ya raba, sannan na shiga hawarawa katangar gidan sarautar, ban tsaya ba. Har sai da na isa bakin kofar shashin ta, sannan na dake kafadar masu tsaron kofar. Sannan na shiga, a hankali har cikin dakunan sai a wani daki can na same ta, zaune akan abin sallah.

     Tana kuka, tsaye nayi cak ina kallonta, tare da jin kukanta har cikin kokon raina, a hankali na taka har gaban ta, ya cire mayafin dake kan fuskana na zauna a gabanta.
"Me yasa kike musu kuka?"
D'ago kai tayi tare da share kwalla tace min.
"Barka da zuwa! Amma me yasa kika zab'i shigar dare?"

"Ya akayi kika san zan zo?"na tambaye ta, murmushi tayi tana share kwalla, tun da aka ce Sulaiman ya kawo mace da Rahil ya bukata, naji

Please Login or Register in order to submit comment