Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata takwas zasu yi suyi suna nazartan tsarin mulkin ƙasar da yanayin cikin gidan.

           Dan haka aka shiga kwaskwarimar masarautan baki daya, tare da dawo dashi asalin tsohon shsshin Mahaifin shi.

         ----
Yau naji a raina ina son bisa sarewan Uwaisul Qarni, dan haka na tafi d'akina bayan na gama abinda zan yi na fara busawa, a hankali duk da bawai ina fahimtar abinda nake busawa ba, amma kuma ina jin wani irin kewa da son kasancewa da yar uwana, ina busawa hawaye na zuba daga idanuna.  A hankali dakin ya fara wani irin sanyi da kad'a iska me dad'i,hade da sanyin kamar nadamina.

               Lumshe idanuna nayi ina kara bisa sarewar,  ina kuma yi tare da hango Airan tana dariya tare da gudu da wani dan karamin rago suna gudu a tare.

     "Barka dai magajiyar sarauta" da sauri na bude idanuna, tare da zuba mishi. Murmushi yayi sannan ya kuma cigaba da tasbihin da yaƙe yi,. Kallon gurin nayi tabbas ina dajin nan ne.

    "Baba yaushe nazo nan?" Na tambaye shi bayan na koma kusa dashi, dariya yayi min sannan yace min.
"Ai kin bisa sarewa kuma Insha Allah zata kawo ki har nan da yardan Ubangiji. Nasan kina cikin kaɗaici bayan kaɗaici, gashi kin fara aikin da ya dace amma kuma kina zubda ladar ki"

   Kallon shi nayi tare da sake baki sannan nace mishi.
"Wani irin aiki na fara kuma na ke zubda la.."
"Kin fara ai! Kuma kin gama gina kome a cikin aikin ki, saura ki jira lokacin da Cigaban shi zai zo miki, don Allah ki taimaka ki saka shi ya san waye shi ? Ki taimaka ya san halin da al'ummar kasar shi suke ciki, baki san wani abu ba.

           Aamaan na biyu sunan yana mulki ne amma ba shi yake mulkin ba wasu ne suke mulkin, Jikata ki taimaka ya san inda yake ya kuma san waye yakewa Hidima. Don Allah ki taimaka. Koda zaki na fuskarta wahala a tare dashi ki tabbatar yasan abinda yake yi, akwai mutumin da ya kama kafin ya kwanta ka jinya, amma an kubutar dashi bayan an fitar dashi sun nemi kashe shi dan kar ya tona musu asiri sai dai Allah bai basu Sa'a ba, guguwar ƙaddara tana zuwa gare ki, don Allah ki tsaya ki bashi kariya."

    "Baba ka sani a duhu wallahi, duk na rude na kasa fahimtar kome."

"Da Sannun zaki fahimci abinda nake nufi, yanzun dai ki taimaka ya fahimci alkibla." Kura mishi ido nayi tare da cewa.
"Me yasa sai Ni?"

"A duk lokacin da tafiyar dare ta kama fatake, abu uku yake zuwa mishi! Na farko namun daji! Na biyu yan fashi! Uku ina zai saka kafar shi babu hasken farin wata babu fitilar da zata taimaka mishi. Toh dole ya hakura da tafiyar ko ya tsaya ya kwana a gurin ko kuma yayi taradda aradu da fadin kai! Bilqisul Ikram dole ki zame mishi fitilar makafi!"

Wallahi duk sai na rud'e tare da zuba mishi ido, ga baki daya na rasa abinda yake nufi, kamar zanyi kuka nace mishi.
"Baba don Allah me kake nufi? Don Allah ka min bayani"

Dariya yayi sannan yace min.
"Ko na miki filla filla ba zaki tab'a yarda ba, sabida rashin adalcin da zuciyarki take miki."

---
"Sultanah, har yanzun babu wani abu daga Ikram!" Inji Shairah.
Murmushi tayi sannan tace mishi.
"Babu wani abu, aikin da na saka ta take min, kuma nasan zata dawo min da Alkhairi nima kuma zan mata kyautar alkhairi."

"Mama, don Allah a kashe ta, bana kaunar ta. Bana son ganin ta, wallahi gani nake kamar ba zata." Wani irin kallo Sultanah Fazilatul nisa tayiwa Jasrah, cikin b'acin rai nuna mata hanyar dakin ta, babu musu ta nufi hanyar d'akinta.

Babu wanda ya kuma magana, sai ma shiga hankalin su da suka yi, domin har yanzun babu wani sako daga Ikram sai suke ganin kamar zata ci amanar su.

---
Jikina wani irin rawa ya dauka tare da jin sanyin ya lullube ni,

"Don Allah karka bani abinda ba zan iya dauka ba, wallahi bani da yancin."
"Zaki iya tafiya! Domin na gama abinda zan iya miki, taimako gkg yi tare da jahadi."

Girgiza mishi kai nayi, zan yi magana na tsinci kai a dakina. Wani irin gumi ne yake karyo min, a hankali na koma na kwanta da baya, ina sauke ajiyar zuciya. Wannan wacce irin ƙaddara ce ta shigo min babu sani na.

Bayan yan kwanaki, Mehran zunzurutun rashin yarda ya mai dani Jelar shi, eh toh dai yanzun haka dai tun jiya aka kawo min kaya daga kasar roma, kallon kayan nake wata irin doguwar riga ce, sai kallon kayan nake ina kuma kallon shi, a hankali.

Buga min kofar dakina aka yi na mike tare da buɗewa, Rakshan na gani.
"Kina b'ata lokaci fa"

Gyada mishi kai nayi tare da cewa.
"Toh."
Sake kofar yayi tare da jirana.
....
Ajiyar zuciya ya sauke tare da kurawa wani gurin ido, meke damun shi? Shi kansa bai san lokacin da ya yanke hukuncin bata wakiliyar shi ba. Ya san dai ba zai iya rabuwa da ita ba, shi yasa ya yanke shawarar bata wakiliyar shi, ko mahaifiyar shi bata san cewa zai bawa Ikram wannan muka min ba.

Haka kawai yake ji Tabbas akwai matsala a tare da wannan hukuncin da ya zartas, dan haka ya mike a hankali tare da nufar hanyar fita bayan ya shirya tsaf sannan ya bude kofar shi. Hangota yayi tana ta gyara zaman mayafin kayan, tana son zata rufe jikinta, bai ce kome ba ya nufi kofar Darakshan ya bude mishi, yana fita mu ma muka bi bayan shi.

Yadda yake tafiya a hankali haka muma muke tafiya a hankali, har muka isa fadar. Na koma bayan kujeran shi na tsaya. Darakshan ya mikawa Magatakardan masarautan wasikar da Sultan din yasa shi ya rubuta juya da dare.

_Budaddiyar wasika! Zuwa gare ku. Abisa ka'idar daular nan Sultan yana da ikon sakawa kuma yana da ikon cirewa Dan haka Sultan Aamaan Mehran ya nad'a Bilqisul Ikram Mustapha a matsayin Wakiliyar shi daga yanzu zata fara aikin ta, sannan tana da ikon ta shiga cikin hurumin fada!"

Cikin kafuwa suke kallona, tabbas duk yadda aka yi an tab'a kimar masarautan,mik'ewa Amir Hood yayi sannan yace mishi.
"Sultan Mehran shin ka tuntubi mahaifiyar ka akan haka?"
Kallon shi yayi sannan ya dukar da kan shi.

" Toh gaskiya dole ta san wannan al'amarin idan ta kama ayi binciken"

"Ita me muqami na biyu a cikin wannan Daular, sai bana nan zata zartas da hukunci idan ina nan bana bukatar kowa yayi min katsalandan akan abinda na saka raina da zuciyata zanyi."

Tabbas gaskiya ya faɗa amma kuma tun shudadden zamani aka daina wannan al'adar ta wakiliya, sannan kuma a tsarin daular mahaifiyar shi ita keda ikon zab'a mishi wakiliya, idan kuwa har shi ya zab'o toh ba makawa sai an dakatar da wacce ya zab'a.

Dan haka sai basu damu ba dan sun san babu yadda za ayi Ikram ta zauna a cikin su, kiri kiri suka suka ki rantsar da ita akan lallai sai Sultanah Hoyam.

D'an aike aka tura ya kira Sultanah Hoyam, koda ta iso ta zauna a kujeran kusa da shi, nan magatakarda yayi mata bayani, kamar farko, juyawa tayi tana kallon shi, sam Mehran baya jin maganar ta, tuntuni taso ya rabu da Ikram amma yaki. Tana zaman lafiyarta zai janyo mata masifa.

Ganin yadda ya b'ata rai ne ya saka ta dauke kai sannan tace mishi.
"Ita wacce aka bawa muqamin wakiliya, ba jinin sarauta bane dan wakiliya Ni ke da ikon nuna maka ita, dan haka Akwai wacce tafi cancanta a bata muka min ba baiwar ka ba, Jasrah Abdul Mannan Hood, itace ta cancanci zama wakiliyar ka, yau kwana biyar kenan da Amir Hood ya kawo min batunta.

Sannan ita kuma Ikram zata iya zama nakusa da wakiliyar ka, hakan na yanke."

Kurawa kasa ido yayi, duk sai ya bani tausayi. Taya yana sarki za a ce sai yadda aka yi da shi, wato idan na fahimta mahaifiyar shi itace dai a mulkin. Bai ce kome ba, ya mike zai fita daga fadar, suka dakatar da shi.
"Sultan!" Cak ya tsaya tare da lankwasa hannun shi, kallona yayi tare da nuna min hanyar da zata fitar dani, duk sai jikina ya mutu.

Kallon Fudail yayi tare da mishi alama da ido, ya rufe kofar, sanan ya tsaya a gaban su.
"Sultan Aamaan! Akan me zaka kawo mana bakar fata cikin tsarin mulkin mu? Taya zaka nemi lalata mana tubalin daular mu. Sannan kaskantacciyar baiwa a bata muqami dai dai da na yan majalisan mu?" Inji Mahaifiyar shi, Mir Rahil da yasan halin Mehran shiru yayi, yana jin sauran manyan fadan suna bin bayan Sultanah Hoyam.

Shi dai baice ta tafasa ba balle ta kone, dan haka ya cigaba da sunkuyar da kanshi kasa, yana jiran zantuntukar su. Bai tab'a nad'a kowa ba, amma yau da yayi kowa yana jin haushin sa,asalima kamar dama suna cike dashi, gashi lokaci guda Mahaifiyarshi har da ita a cikin masu mishi wannan rashin darajar.

Ya shafe awa daya yana sauraron su, idanun shi rufe, kuma yana tsaye akan kafar shi. Dan haka suna ganawa bai ce musu cikanku ba, ya juya tare da barin su nan suna luguden lebbe.

Ina tsaye a gaban Madubi, ya shigo min dakina, har na manta rabon shi da ya shigo dan tun bayan azumi da yaji sauki ya koma dakin shi. Yana shigowa ya zauna sharaf tare da zuba min ido, muna kallon juna ta madubi.

Janye idanu na nayi sakamakon yadda idanun shi suka fara min siddabarun shi nan dai, kasa Cigaba nayi da kallon shi ina me dauke kai na, a hankali. Tare da yin kasa da kaina.

Shi kanshi sauke kan shi yayi tare da ajiyar zuciya, yana cikin damuwa sosai, ban matsa ba a gurin sai wani dabara ce tazo min na fice a hankali na dibo mishi ruwa, na kawo mishi. Kamar jira yake na mika mishi ruwan ya amsa ya kafa kai sai da ya shanye, sannan ya kuma shanyewa. Wurgi yayi sa kofin yana kallona idanun shi yayi jajjur yace min.
"Waye Allah?"
Littafin nan na kuɗi ne....
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
     
Page 30
Da sauri na mike ina kallon shi, sabida tambayar  shi yazo min bazata, yadda yake min abu kamar wanda ya sha giya ya sani yin baya, biyo Ni yake fuskar shi tayi jajjur, dan bakin shi ruwan pink sai wani rawa yake, a hankali ya kai ni bango tare da dafe hannun shi daya da bangon, yana kallon fuskana wanda ya ke cike da mamaki.

   "Ki gaya min waye Allah?" Cikin rawan murya yake maganar. Jan hancin shi yayi tare da cewa.
"Ba zaki gaya min bane?"
Ya kuma tambaya na, kasa nayi da kaina, tare da cewa.
"Allah shine wanda ya halicci samman da kassai, babu abin bautawa da gaskiya sai shi. Shine wanda ya halicci Annabi Adam ya samar da Nana Hauwa'u daga jikin shi. Ubangiji shi ya halarci kome a cikin kwana bakwai, wata rawaya suka ce a cikin kwana shida. Kuma shi yafi cancanta mu bauta mishi."

        Kai hannun shi yayi saman kai rigar jikina, yaja igiyar gaban rigar, rike hannun shi nayi.
"Ubangiji ya halicci Annabawa, kusa dari da goma sha uku, sannan ya zare manzan guda ashirin da biyar, sannan ya basu addinin suyi da'awa shi."

Sake fauce hannun shi yayi sannnan ya zare rigar zai fadi kasa na rike hannun shi.
"Ubangiji ya aiko Manzon Allah, Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama,cikin kabilar larabawa sabida yawan damuwar da suke me yasa ba a aiko wani daga cikin su ba, domin Yahudawa sun fi yawa a cikin annabawan. Sai gashi ya aiko musu dan uwan su, bakuraishe! Bahshimi, Dattijon kwarai,  kuma aminttacen ya zo mana da addinin musulunci.  Kafin nan dole idan zaka yi imani da Allah sai ka isa sharudan musulinci. Ubangiji yayi mana gata da ni'ima."

   Zare igiyar yayi, cikin tashin hankali, na shiga mishi bayani tare da gaya mishi girman musulinci da abinda ya haramta, idanun shi sunyi jajjur, jijjiyar goshin sa sun mik'e. Uwa uba na jikin shi. Wani irin zazzaɓi ne ya rufe shi, kifi kanshi yayi bayan ya sunkuya goshina.

             Har ina jin zafin jikin shi, ga baki daya ya narke min, gashi ba kadan ba, duk sai na damu da kai na. Kasa mishi kome nayi. Shi a tunanin shi yana rayuwa ne cikin takura ashe akwai babban kalubale da yake ciki.

           Me yasa Mahaifiyar shi ta kashe mishi rayuwa? Me yasa ta hana shi fahimtar Meye rayuwa? Musamman da yake kuma jin tasirin addinin Musulunci.

          Kasa fadin kome yayi har na kai shi bakin gadon ya zauna, kasa rabuwa yayi dani, yana rike da hannuna.kanshi a jingine da cikin, wani irin ajiyar zuciya yake saukewa daga lokaci zuwa lokaci, ban san ya ban tausayi ba, sai da na shiga shafa kan shi ina yatsina gashin kanshi sannan na fahimci tausayin shi da yake raina.

. A hankali na kawo mishi sharudan musulinci, tare da dokokin su, d'ago kai yayi tare da kallona sannan ya kuma mai da kan shi, ya rungume ni, nasan yana cikin damuwa ne, amma haka kawai Mehran ba zai tab'a rungume ni ba, fahimtar lokacin sallah yayi ne ya sani, janyewa daga jikin shi. Kallon na yayi  tare da dauke kan shi, a hankali ya mike yana dafa bango, tab'e baki nayi a raina nace.
"Miskilin banza kawai, ya wani kwaso jiki kamar wani abun Arziki akan azumi ranar kamar zai dake ni, yau kuma kaje sun kulla maka tsiya zaka sauke min. Mitseww!"

Naja yi tsaki abuna, ban kuma jin zuriyar shi ba, domin iya abincin da na girka na rana yana nan na daren ma bai ci ba, ashe yana can kwance babu lafiya, shirun da nayi yayi yawa ne na tashi dake ban tab'a shiga dakin shi na wannan shashin ba, sai yau.

       Da sallama na shiga a hankali, kamshin turaren sandal ne ya daki hancina, wannan shashin Narmin ce take shigo da wasu bayi mata guda uku har da Mahlika suke gyara mishi, tunda na shiga na hango shi can tsakiyar gadon, ya dunkule cikin bargo, a hankali na isa ta gefen shi na haura gadon tare da jan bargon na dafa goshin sa. Tab'e baki nayi a raina nace.
*Mazaje ana jin jiki*
    Taba goshin sa nayi tare da gyara mishi kwanciyar shi, a hankali na fita daga dakin na je na sirka ruwan zafi, nazo na taimaka mishi ya rage kayan jikin shi sannan na shiga goge mishi jikin shi tare da dafa goshin sa.

      Ina gamawa na gyara mishi kwanciyar shi, sannan na fita dama alkama nayi da madara, sau zuma da na saka kaɗan. Yayi kauri kamar me, bai tab'a sha ba, haka na shiga na taimaka mishi ya tashi, na fara bashi yana sha, tare da kallona, har ya kusan shanyewa sai ji muka yi an bankad'e kofar ko alamar sanarwar ana shigowa gurin shi ba yi ba, da sauri na mike zan bar d'akin,  ya dawo dani na zauna tare da zuba mata ido ina bashi yana sha.
"Ke zoki fita."
Rike hannuna yayi tare da dauke kan shi daga gare ta, ina bashi yana kallona a fisge, ganin nima ina son na fitan don haka ya sake ni a sanyayye. Satar kallon shi nayi hankalin shi yana kan hannun shi, amma nuna a zahirin gaskiya Ni yake kallo. Kamar zai zun duma ihu yake bin bayana da ido.
"Mehran! Meye alakarka da ita?"
Shiru yayi tare da dauke kanshi yana Cigaba da abinda yake yi.

    "Kana Sonta ne?" Ta tambaye shi a tsawa ce. Nan ma bata samu amsar ba, jikinta a matukar macce ta zauna a kusa dashi tare da rike hannun shi, kwalla na zuba mata.
"Mehran me ye tsakanin ku da har ka zabi ka bata matsayi dai dai da ahalin ka " murmushi yayi sannan ya gyara kwanciyar shi tare dauke kan shi daga gareta ta yana me juya mata baya.

           "Toh tunda babu yau zan watsar da ita wajen masarautan." Tashi yayi zaune yana kallon ta cike da al'ajabi yana hango son kai murarran a tare da ita suke fuska yayi tare da dauke kan shi, sannan yace mata.
"Na rantse da Allah dan baki koya min bauta mishi ba, sai na zubda jinin wanda bai ji ba bai gani ba, karki sake wani abu ya same ta domin zan iya daukar kowani kasada amma ban da na tab'a Ikram, Bana sonta ban tab'a jin sonta ba, kawai dai ina mutuntta ne sabida yadda itama take sadaukar da nata rayuwar domin ni."

Cike da mamaki tare da tsoron da ya bayyana akan fusakarta ƙarara mikewa tayi tare da gyada kanta, tana kallon shi girgiza kai tayi. Tare da hango iyakar gaskiyar shi a kwaryar idanun shi, tare da kaunar yarinyar da yace baya sonta.

Mikewa tayi cikin iko tace mishi.
"Toh zaka ajiye mana mulkin ƙasar nan kuwa?"

Murmushi yayi cikin nutsuwa yana shafa kanshi sannan ya kwantar kanshi akan matashin sa, a fusace ta ficce daga d'akin.

...... Tana fita bata tsaya wata wata ba, tasaka aka kawo Ikram aka fita da ita, tare toshe mata baki. Tunda aka wuce da ita darul Azab, akayi ta manna mata wuta a jikinta.

Duk karfin zuciya da taurin kai sai da nayi ihu tare da kiran shi ina niman dauki shi, sabida hannuna da kafaffuna duk sai da aka kona min su, sannan aka dauke ni zuwa dakin da yake dauke da wasu irin beraye, takowa tayi har cikin ɗakin. Ta saka takalmin ta tana taka min ciwon jikina.

"Shekaru ashirin da bakwai ina shirya kome, yar iska a cikin wata bakwai kin lalata min kome! Kice zan zuba miki ido. Shima Mehran lallabashi nake sabida kar ya fahimci manufar da take raina, anan zaki tabbatar har karshen rayuwar ki, kuyi ta barbada mata gishiri kuna azabtar da ita har sai ta mutu. Sanan ku barta da berayen suci namar jikinta har sai ta kare."

Haka matar nan tayi tafiyar ta tare da barina a cikin mugun yanayi, wanda ko fahimtar kai na bana yi.

Ban san iya adadin lokacin da na dauka ina kwance ba, sai da naji kamar ana caccakar ciwon jikina yasa Ni motsawa, beraye ne suka cika kai na, suna gurguran jikina, ihun da nake yasa su guduwa, tare da niman mafaka, haka nayi ta ihu ina niman dauki.

~~~
Tun kusan rana yake jiran abincin shi babu Ikram babu labarin ta, haka ya sashi fitowa a hankali yana kallon yadda aka cika mishi babban falon shi da yan mata suna ta jiran shi. Ko kallon su bai yi ba ya wuce abin shi d'akinta, yana zuwa ya bude kofar, yaga kome a watse kuskuren da Sultanah tayi kenan, dan tabar mishi alamar cewa daukar Ikram tayi da karfi, da ace ta saka an gyara ko ina babu abinda zai bayyana mishi cewa daukarta aka yi.

Juyawa yayi a fusace tare da shiga dakin shi ya shirya cikin kayan yaki, yasan tabbas zata iya sakawa a hana shi fita dan haka ya dauka har da makaman shi. Yana fitowa matan da suke falon suka razana, bai bi ta kansu ba ya fita abun shi.

A kofar fita ne ya ga dakaru kusan hamsin.

Saka kai yayi zai fita suka hada hanyar kallon su yayi tare da musu alama su bashi hanya suka dauke kansu, dan haka ya zare takobin shi. Babu tausayi a ranshi ko digon imani ya shiga musu wani irin kisar gilla, ko nace kisar kiyashi. Sai da ya karar dasu a cikin dakika dari uku da talatin, sannan ya share jinin da ta b'ata fuskar shi ya saka kai ya fita tare da isa bakin kofar shashin, kallon shi dakarun duka yi yadda jini yake diga daga jikin shi babu musu suka bashi damar wucewa.

Nufar hanyar shsshin Sultanah, anan ya same wasu dakarun da ta saka. Murmushin mugunta yayi domin yana ganin kamar ta manta da waye shi. Yasa ta zuba mishi kananun dakaru, gyara tsayuwar shi yayi sannan yace musu.

"Kuna da iyalan ku! Dan haka bana son ku rasa rayukan ku a banza" ya fadi haka tare da kallon su. Bashi hanya suka yi dan ya gaya musu gaskiya, yana saka kan shi falon ta ya samu suna ta shagali da mutanen fadar shi. Gyara tsayuwar shi yayi tare da rikon takobin shi ya nufe ta.

Tana ganin shi ta mike tana kallon shi, gabanta ya isa tare da wurga mata takobin shi. Yana kallonta. Huci yake kawai amma a ranshi kadai yasan abinda yake ji.

" Da na gaya miki cewa karki tab'a ta kin zata ba zan sani bane? Kin zata bazan Fahimci abinda kika aikata bane.

Yarinyar da take kokarin akai na kike saka Ni magana akanta, ko? Yarinyar da tunda nake ban tab'a ganin tayi fashin sallah ba.

Yarinyar da take kare kanta da addinin ta, kike so ki hallakata. Na rantse da Ubangijin da kika hanani bauta mishi, sai na sare kan duk wanda ya azabtar min da ita."

Gaba daya ya haukace musu. Ya gigice musu fada yake tare da musu alƙawarin sai ya sare kawunan mutane, Allah yasa yaga ba daidai ba, kawai ya juya ya bar musu falon.

" Dama yarinyar tana ibada har haka ne? Me yasa kuka kai mishi ita?"
"Tambaya na kake Amir Hood? Toh Yarka zaka tambaya Fazilatul nissa, itace ta saka aka kawo ta shsshinsa."

...... Yana fita ya nimo Fudail suka nufi darul Azab, suka shiga har karkashin kasa, inda ake azabtar da mutane, ihunta yaji tana niman taimako, ji yaƙe kamar zuciyar shi zata fado haka ya isa bakin kofar, ya saka Gatari ya fasa kofar sannan ta shiga d'akin da yake dauke da mugun duhu.

A hankali ya shiga jin yayi tuntube da ita, dan da taji an bude kofar bata kuma ihu ba, bata iya hango na waje haka kuma na waje bai iya hango ka.

"Wayyo Allah na!" Na fada lokacin da ya taka

Please Login or Register in order to submit comment