Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi sannan nace mishi.
"Kana jin me tace?"
Murmushi yayi sannan yace min.
Ai ba a wani waje bane a cikin gidan nan ne, Kinga wancan kofar gidan mu kenan, idan kema baki son zirga zirga zaki iya zama anan."

       Murmushi nayi sannan nace mishi.
"BABU matsala, haka ma yayi."
Koda muka taso kayan Izmah na dauko musu, sannan na bata hakuri Ni zan zauna a gurin mu.

    Alhamdulillahi, ki babu kome tana inda zata sami tsaro da kulawa, su kuma dakin mu, sabida ita nake d'aga musu kafa, domin ko jiya da ka rikice kuka ta fashe dashi tana ya da baya, alamar tana jin tsorona. Dan matuƙar raina ya b'aci Ni kaina har mamakin yadda nake juyewa nake.

          A hankali kwanaki suke tafiya, wani irin shakuwa ya shiga tsakanin mu da Amir Rahil, kuma kamar mayye, indai ban zo ba, zai damu kowa har sai an duba ni. Dan da gaske na Fahimci wawan sona yake, Ni kuma a duniya babu wanda na tsana irin shi.

    Dan haka muka yi ta shirya yadda zamu kashe shi, shakuwar da muka yi tasa shi matsawa lallai sai na kawo shi yawo.  Dan haka cikin kasada, na dauke shi bayan na mishi kwalliya da shigar wata baiwa, muka fita.

     Kamar zautacce haka ya rungume ni tare da sumbatar goshina.
"Ina son ki, domin ke daya kika bani farin cikin da nake bukata, don Allah ki taimake ni, kina dariya mana" (😬) ya wangale min baki.

  Tsuke fuska nayi, sannan na wuce abuna, yana bina a baya, har muka shiga kasuwar, nan yai ta sayan kayan ciye ciye, yana mika min, har muka gama, wani guri da babu mutane, ya nuna min muke zauna.
"Salsabila! Me yasa baki dariya."
"Hmm" nayi tare da murmushin gefen baki, sannan nace mishi.
"Ban san me yasa fuskata ta wadattu da fusata ba, a koda yaushe ina jin ciwon abinda aka min. Na kashe min mijina, bayan nan dama bani da farin ciki ko bakin ciki sai rasa shi da nayi, babban burina na nufi SAMAIND na kashe wanda ya turo min aka kashe min Noman ranar auren mu."

   Kura min ido yayi tare da sake abin da zai kai bakin shi. Idanun shi sunyi jajjur.
     Tashi yayi tare da nufar hanyar da zai kai shi wani gurin.
Bin shi nayi tare da fisgo shi.
"Meye nufinka? Zaka janyo min magana ne? Ka tsaya na maida kai inda na dauko ka."

    Kwace kan shi yayi tare da kallona yana zubda hawayen.
"Ki kyale ni, karki kuma tab'a ni"

  Karan sautin zuwan abu naji dan haka na kwashe shi ya zube ƙasa, kallona yayi ya ga ina raba idanuna, hango wasu mutane nayi cikin duhu, su uku.

Da sauri na fisgo shi muka bar gurin da gudu, tare da shiga cikin Jama'a, kallona yake.
"Kinga abinda kika ja min ko?"

Marin wuyar shi nayi tare da juyawa na goye shi, muka shiga barin gurin da gudu kamar zamu tashi sama, ina saka kafana a kofar gidan shi, na sauke shi. Suka harbo min.wani karfe kamar ƙaya ya suke Ni ta baya sai da ya fito ta gaba. Haka na samu na shiga tare da rufe gidan, masu tsaro suka tawo da sauri.

    "Ku shiga dashi cikin gidan" na fada ina layi, juyawa nayi tare da ɗaukar takobin ghaddafi, na fita, jini na zuba a kafadana, amma haka bai sani jin na hakura ba, komawa nayi inda aka fara abin.

Na zauna tare da ɗaukar abinda muka saya na fara ci a hankali, gani nayi sun kewaye Ni.

"Wato ke me taurin kai ko? Kin dawo"
"Waye ya harbe Ni da ƙwayar karfe?"
"Ba zamu gaya miki ba."
"Wannan shine mafi girman kuskuren da kuka aikata, daga kanku ya zama tarihi."
A fusace na juya muka fara yakan juna, a rayuwata na tsani kayan takaici, dan haka cikin fushi da bakin ciki, nayi ta kashe yan iska, aladu kawai. Ina gamawa na juya na koma gidan Amir Rahil.

     Na ajiye takobin na koma gidan mu, ina zuwa.
Ina isa na samu duk sun yi barci, dan haka na cire kayana, na dauki kayan kulawar gaggawa da yake dakin na wanke ciwona, ina fitowa na samu an sace kayan jinin.

       Ina kwance kawai sai ji nayi an watsa min ruwa, ina bude ido naga dakaru da manyan makamai, dan haka na mike a hankali. Haka suka tasa keya ta, zuwa gidan yari.

  Bude idanu nayi tare da kallon inda nake, ban damu ba amma kuma kasar raina ina jin tsoron halin da na kuma jefa kai na, amma kuma nasan wancan sakaran zai nime ne ni.

      Bayan an kawo ni sai ga wani mutum, yana nad'e da mayafi akan shi zuwa fuskar shi.
"Wacece ke? Meye na kawo ki masarautan mu da zaki kashe min mutane haka babu tausayi."

"Basu tausaya min bane, nima na shayar dasu nonan babar su." Na fada ina kallon shi.
"Hmm! Ku azabtar da ita yadda sai ta tuna ranar da ta gaya min magana ina Amir guda."

Bai bar gurin ba nace.
"Ko dai d'an Kwarkwarah ne! Amir Abdullahi ko kuma Amir Abdul Rahman!?"

Cikin fushi yazo ya shiga kwallo da Ni, ya na iya na zama kamar dole. Bayan yaga na suma ne ya kyale ni, Ni kuma ba suma bane. Kawai ina iya dauke numfashina na tsawon dakika dari uku da sittin, sabida kwanakin da nayi a cikin ruwa.

    Fita yayi abin shi, kai na a ya she, suka mai dani gurin da nake,
"Amma kuma yarinya karama ce fa?"
"Ba daga nan take ba, tana da horon yaki. Sannan ta iya kisa na fitan hankalin, kafin yau naji labarin ta a bakin bayi yan matan nan, wai an kawo mafadaciyar baiwa bata magana da kowa sai kawarta, idan kuma ka sake tayi maka magana sau daya toh na biyu zata karya maka wani guri ne."

     "Ni kuwa sai nake ganin kamar ba zata iya daukar kasadar haka ba, domin tun bayan shekaru ashirin da biyar, ba a kuma samun jarumi irin Amir Almustapha ba, domin ance shine yake iya kisa cikin abinda bai fi dakikai dari biyar ba."

Kirjina ne ya shiga bugawa, musamman idan naji sun ambaci sunan mutumin sak da na Abba na, lumshe idanuna nayi. Sannan na kurawa ciwona ido.

          Bayan awa goma, sai ga Amir Sulaiman. Yana zuwa ya shigo min, har cikin dakin.
"Ke wacce irin dakikiya ce?"
"Irin na wanda yake kanka."
Cikin jin haushi ya d'aga hannun shi, rikewa nayi sannan na kalle shi.
"Sam tunanin ka baya baka lissafi, ka tambaye su waye ya shigo bayan an kawo ni, sai ka dawo na gaya maka dakikancin da yake damun ka."

       
   Kura mata ido yayi, musamman yadda tayi maganar alamar babu wani tsoro ko fargaba a ranta, asalima ranta sake tayi maganar, bayan ya tambaya aka tabbatar mishi da wanda ya shigo gidan, kallon Juna suka yi sannan cikin karfin hali nace mishi.
"Kayi tafiyar ka, nan da jibi zan fita duk tsarina ne, sannan kayi taka tsantsan da kowa, sabida ba kai ɗaya bane kake niman ran D'an Aliyu ba, kuna dayawa. Amma abinda nake so da kai tukun mu fara rage abokan adawar ka, idan aka gama dasu zaka iya samun damar kashe Amir Rahil,  tunda shi daya ya rage maka."

       "Wai Ni kam wani irin horo kika samu ne?"ya tambaye ni,
Murmushi nayi sannan nace mishi kaje zan baka amsar wata rana.
        Na fadi haka,ba tare da na kalle shi ba, bayan tafiyar shine na kwanta a gurin, bana jin dadin jikina da rayuwata baki daya, ina jin kewar abubuwa dayawa, amma ban san meye su ba.. kawo mana hari jiya ya sani fara kokwanto akan meye dalilin da yasa ake kashe yaran Sultan Mu'allim, musamman y'ay'an Uwargidan shi Balkisu Ikram?

    Haka kawai ruwa bata tsami banza, haka kawai ana kashe yaran d'akinta yau ga kisar ya fado kan jikan ta. Shafa wuyana nayi.sannan na zubawa dakin ido, a sanyayye na sauke ajiyar zuciya.
#Mai_Dambu.
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: Monday-March-2021
*FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

09
..... Washi gari.
Ya farka yana kallon d'akin shi, murmushin takaici yayi tare da fashewa da kuka, yau shi ne wani ya dasawa Kaunar shi soyayya da ta kasa Mantawa dashi, dole yayi yaki da kaunar da takewa wancan mamacin.

   Bayan ya gama abinda yake yi, yayi ta zuba ido har rana babu Salsabila babu labarinta, fitowa yayi sannan ya kalle mutanen gidan, so yake ya tambaye su, ita amma kuma ya kasa, dan haka ya share batun, har zuwa yamma babu labarinta, anan suka ga ya birkice musu.

       "Amir kayi hakuri zuwa gobe zamu nimo maka ita "
"Dalla ka min shi, wani irin gobe kasan yadda ta tsare rayuwata da lafiya ta kuwa, kuje ku nimo min ita"
Haka yayi ta masifa, karshe dai suka fita babu wanda ya gaya musu abinda ya faru, har washi gari.
Rahil bai yi barci ba, kamar yadda yaga rana haka ya ga dare, can gurin asuba barci ya dauke shi, bayan ya farka yayi Sallah sannan ya tashi tare da ɗaukar alkalami ya tura ga kakan shi yana niman Izini a barshi ya fito.

Dakaru aka tura kusan guda dari biyu,suka saka shi a tsakiyar su, har fada, yana shiga cikin fadar ya gaida kowa sannan ya zuba gwiwar shi a kasa, yace.
"Allah ya taimaki Sultan!"
Hawaye ne ya shiga zuba daga idanun shi.

     Shiru fadar yayi sannan Amir Sulaiman yace.
"Shalelen Sultan meke damun ka?"
Cikin shasheka yace.
"Yarinyar da ka kawo min bata nan! Shekaranjiya na tistata muka fita."
Kallon Kakan shi yayi da ya kura mishi ido, yana hango yaranta Yaron dan shekara ashirin da biyar, amma gabaki daya ya sauya sabida rashin adalcin magauta.

      "Sultan! Yarinyar nan kare lafiya na tayi tayi har taga zan bata matsala ta dake ni anan! Kafin na fita hayacina, goyani tayi tana gudu kamar ba mace ba, Sultan don Allah idan baka son karasa ni a duba ko ina na cikin kasar nan, domin lokacin da zata mika Ni ga Ghaddafi ina jin yadda taja ajiyar zuciya, Sultan ba nauyi na bane, sai na shigar wani abu jikinta.

       Don Allah ku nima min ita. Na ganta, ko ita ce wacce Ummina take ce min zata zo wata rana."

      Duk da kowa yasan Mahaifiyarshi ta rasu da tsowon cikin kanin shi, sannan an kashe daya kanin shi. Shine kawai yake raye.
Cikin fusata Amir Sulaiman yace mishi.
"Akan Baiwa kake kuka? Yau duk inda ta shiga sai na nimo maka ita."

      Ya mike tare da dakaru aka fita zuwa gidan bayin anan suka samu labarin tana kurkuku, wani badakaren ne ya goye ta, har cikin fadar.

              Mikewa yayi miyafin da take bayan rigar shi tana ja, kamar wacce iska yake kad'ata, ya isa gabanta cikin tashin hankali.
"Salsabila!" Dakyar na bude idanuna.
*Amma Yarinayr nan makira ce! Irin wannan aka same su suka kai hudu a fada tabbas wuta ce zata kone kome*

   Tafiya nayi zan fadi ya tare ni, yana me rike hannu na.
"Don Allah. Bude idanun ki, gani nan a gabanki, ba zan kuma barin wani ya cutar dake ba kinji Salsabila"

       Murmushi Sultan Mu'allim yayi sannan yace.
"Dama Baiwarka mayakiya ce?"
Cikina ne ya bani wata kululu.

Amma dake na dauke numfashina, sai ake ganin kamar na suma.

Amir Sulaiman yace.
"Abba! Dole ta zama mayakiya domin kare rayuwar magajin masarauta gobe, kaga ai ba laifi bane dan ta kare shi ta hanyar yaki."

"Yawwa Baba na, ka fahimci abinda nake nufi." Inji Amir Rahil.
Ko ta kan kowa bai kuma bi ba, ya dauki Ikram yayi waje da ita, sabida gani yake kara zaman shi kara nisanta numfashin ta, dan haka ya nufi gidan shi da ita, da sauri aka nimo likita ya fara bata kulawa, har zuwa wani lokaci.

     ___
"Ya kamata a kuma saka ido akan mutanen da suke kawo mishi hari ta karkashin kasa"
Lumshe idanun shi Sultan yayi sannan yace.
"Wazir! Ina son ka bincika min Wannan yarinyar sam bana son na kamata da laifin da ban sani ba, domin ina jinta kamar Almustapha!"

       Dake su biyu ne a dakin sirrin, abokai ne na amana, kuma suna matukar kaunar juna, Mahaifiyar Amir Rahil yar waziri ce, me suna Abu Ayyub,

     Gyada kai yayi sannan yace mishi.
"Binciken zai iya daukar lokaci, amma zamu yi Insha Allah, sannan ita kanta yarinyar ina zargin turota aka yi, yanzun kuma toh."

           A hankali suka gama sannan suka fito. Abin su.

        --- rike take da Alqur'ani, tana karantawa. Zama yayi sannan yace mata.
"Sultanah idan an kai aya a daure kula ni,"
Rufe Alqur'anin tayi sannan tace mishi.
"Naji an kaiwa  Hibban hari shekaranjiya ko?"
"Eh wallahi"
Ya faɗa cikin sanyin murya.
"Haka suka kaiwa Almustapha na, suka kashe min shi ko gawar shi ban gani ba, suka kuma kashe min  Abubakar dina gwara shi naga gawan shi, Sannan suka kona min Aliyu Abu turab, don Allah Sultan ka tura mu, Minalik.

Na gaji da ganin zuban jinin yarana, Raziyana zata iya rike kanta amma shi bai."

"Insha Allah, yana tare da kariyar Ubangiji, Akwai wacce take kula da lafiyar shi."
"Taya zaka ce haka? Taya mace zata kula da lafiyar namiji irin shi, ki kamanta idan suka keb'ance."
"Yarinyar bata da wannan tunanin, naga fuskarta me dauke da kadaici don Allah karki raya wani abu a ranki."

    Had'iye kuka tayi tare da kwantar da kanta a kafad'ar shi,
~~~
Kifawa D'anta mari tayi sannan tace mishi.
"Alawadaran dakikin ƙwaƙwalwar ka, sannan ka zata mutane irin yarinyar gama garin mutane ne? Yarinyar da ta kashe mana mutanen da suke mana aiki? Abdullahi ashe girman banza gare ka, toh wallahi kaji bazan tab'a ganin wannan abun kunyar ba ka kashe yarinyar sai ka tawo na."

"Ammah, yarinyar nan fa ba zata kasu ta dadi ba, domin tana da horon fasahar yaki, sannan koda mun hada dakaru kimananin dubu ba zata kasu a hannunsu ba.

         Ammah naga yarinyar a cikin dakikai talatin zata iya kashe kartin maza sama da tamanin lokaci guda, kaifin basirarta ya wuce yadda kike tsammani. A cikin dakikai talatin da wani abu ta kashe mutane shida, me kike tunani zata aikata ga lusarin d'an baki da bai iya rike kan shi ba..idan har abinda na Fahimta akan yarinyar gaskiya ne toh tabbas bamu kadai muke bukatar ganin Bayan Rahil ba.

Akwai wasu a bayan mu, ko mu muna bayan wasu,.kiyi nazari mana."

        Shiru tayi sannan ta dauke kanta tare da kurawa Abdul Rahman idanu, tabbas yayi gaskiya.
    ~~~
Lokacin da aka ni inda Izmah take da gudu ta faɗa kai na, tana kuka. Rungume ta nayi tare da cewa.
"Karki damu,ina raye."
"Toh kawar mu, fita ki bamu guri a dubata ko"
Kallona tayi na rike hannun ta, tare da gyada mata kai.

Murmushi tayi sannan ta fita, da kanshi ya cire min rigar jikina, kallon na yake a sace fuskar shi a had'e, ya fara kokarin zare min. Mayafin da na rufe kirjina, da sauri na juyar da hannun shi. Tsalle yayi ya faɗa kai na.

   A hankali bakin shi ya shiga nawa, bude idanu akan shi, tare da lumshe idanun, jikin shi yana rawa, ya kasa cire bakin a saman nawa sai da na daki kirjin shi na wurga shi.

       Kamanin wani mutum nake gani, yana min gizo a idanuna tare da murmushi, ture Rahil nayi tare da kallon kofar da ake sallama.

    Kama gefen cikin shi nayi na murɗa sai da ya saka ihu.
"Oouch! Ke wacce irin mutuwa ce?"
"Likita yana kallon mu!"
"Don Allah Karki gayawa kowa nace ina sonki, Sabida Zubewar darajar gidan mune"

       Mikewa yayi a kaina yana gyada min kai,

     Haka ya tashi daga kai na, likitan ya shiga duba ni, yana gamawa. Rahil ya shigo tare da zama ya zuba min ido, can ya b'ata rai.

   Sannan ya mike tare da cewa.
"Na manta ma ina jin haushinki."

Ya saka kai yayi ya fita.

     ----
Alhamdulillahi kwana na biyar na warware, takamaimai bani da abin yi, domin naje har gidan yana hanawa na shiga cikin gidan, wai yana fushi. Ni da na fishi daru, sai na koma shashin bayi abina.

"Baba kasan me? Salwah tana d'agawa Rahil kafa, amma bai Fahimci haka ba, wai ya hana a barta ta shiga gurin shi."

"Yarinta ke damun shi, kuma har yanzun bai san ciwon kanshi ba."

       Haka suka yi ta hira, tare da fadan halin Rahil, yadda bai da damuwa.
        Yau sati na uku, tare da bin gidan mutumin da ya dake ni, Aikuwa na sami gidan, ranar da na warke sumul. Ai ku ranar da misalin karfe biyu na dare na dira mishi. Yana tsaka da barci shi da wata baiwa, tab'a shi nayi ina cin wani tufan da na gani a d'akin.

       Yana farkawa ya bude baki zai min ihu na zabga mishi naushi. Sannan saka shi a gaba na mishi shegen duka, sannan na bar gidan, washi gari bai tafi fada ba.

             Yau dan renin hankalin can ya nime na shiga gidan, nima na murza mulkina, naki shiga aikuwa ko awa ba ayi ba, sai gashi, kallona yake kamar ya dauke ni.
"Salsabila! Laifin meye nayi miki da zafi?"
" Na gaji da zama da sakarai irinka" idanun shi ne, suka cika da kwalla, alamar yaji haushina, tab'e baki nayi sannan na juya, mishi keya.
Takowa yayi sannan yace min.
"Nan da sati Uku, za ayi wasan shekara, kuma ban iya kome ba, wannan karon na sami labarin Amir Yasir da Yazeed zasu halarci taron, sannan Amir Samir zai yi.

     Taron duk shekara ake yi, kasancewar Abba Almustapha ya kware a abubuwa guda uku. Fada da takobi, fada da hannun, sai mafi soyuwa a zuciyar shi sarrafa kwari da baka.. Abba Abubakar, ya kware a iya amfani da mashi sai fada da hannun sai amfani da watsa reza, Abba na kuwa masanin fadar da takobi ne, kawai bayan nan sai gashi an kashe su. Ban iya kome ba, ke kuma kin iya fada kuma zaki iya kare."
"Waye ya gaya maka nazo ne domin na kare lafiyar ka? Ni nazo ne takanas sabida kai. Dan haka ka tafi ka nimo me tayaka ka aikinka, Ni ban iya ba."

           Kamar zai fasa kuka, haka yake kallona, tare da sauke kan shi kasa, ya jima a tsaye sannan ya fita, daga gidan, dariyar da naji yasani fitowa daga cikin gidan, wasu matasa uku na gani, sun saka shi a gaba suna mishi dariya, sunkuyar da kai yake hawaye yana shirin zuba min.

   "A duk inda aka tara taron jakuna, dole sai sun nuna halin su, ku saka kai ku bar gidan nan ko kuma ku tashi da kafar daya hannun daya"

            "Ai kace ƙaruwar da Abbana ya kawo maka kenan, me idanun mage." Ya faɗa yana kallona.
Isa nayi gaban wani bishiya tare da karyan reshen, murmushi yayi yana share kwalla, a hankali na isa gaban su.
"Kuyi tafiyarku?"
"Babu inda zamu sai mun tambaye shi bana ba zai kare kimar mahaifin shi bane, gwara Abubakar yana da Almirah zata kare kan mahaifin shi. Almustapha kuwa dama bai bar baya ba, dan haka babu me kare kimar shi. Kai kuma lusari."

"Zan kare Mahaifin shi, zan kare Almustapha, zan kare shi. Na karb'a kuma sai ku a kara gaba."
"Ke Yar uban waye?"
Lumshe idanuna nayi, cikin wani irin zafin nama na daki bakin shi,
"Ba a zaga min Uba a kwana lafiya"
Na yarfe hannuna, tare da kura mishi ido.
"Kika dake ni?"
"Ubanka ma yayi min ma dukar shi zanyi"

      "Keee!"
"Kai kare! Zan dake ka na daki mazauninka!" Na fada mishi.
"Lallai kinyi na kudin ki, kuma zaki biya."
"Karka damu, ai na rigada na biya kuma haka zan iya tayawa."

     Ganin da gaske zan iya karya sune suka fita, tare da kallona suka yi tare da murmushin mugunta, tsayawa nayi a gaban shi. Ina kallon su.
Ina jin yadda yake sauke ajiyar zuciya....
```BOOK one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```

#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: Monday-March-2021
*FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

10
Akai akai, tausayi ya bani, ina tsaye har suka fita. Suna fita daga gidan, juyawa nayi hannuna a kirjina.
"Nagode!"
Na fada min a sanyayye, tausayi ya bani. A hankali na daure fuskana nace mishi.
"Ba wai ka fadi haka bane, dan sami damar zama a lusarance, dole ka."

Wani irin juya ni yayi lokaci guda yayi kamar zai kai ni kasa, hannuna dukka biyu suka wuyar shi, ina zare ido.
"Jarumta idan har gadon shi ake dole na gada, Allah bai halicce ni akan ki kuwa hmm!"

      Ya faɗa tare da d'agani, kasa magana nayi, ko daya bana jin shi a raina, domin sai kana yin abu kake shin shi toh shi koda wasa bana jin shi.

             Haka na shige cikin gidan abuna, tun daga ranar na hana shi, barci muka fara horon yaki. Amma bana samun lokacin shi, baya nutsuwa. shi da zai nutsu muyi abin sai ya kama kai hannun shi yana wasa da gashina, ko kuma ya kai hannun shi k'uguna, sai uku ina fasa mishi baki.
"Don Allah ki daina saurin hannun mana"
"Baba wallahi bana son dukar shi, baya nutsuwa ne sam."

              A hankali lokacin yayi ta tafiya,  kwanaki suna kara zuwa. turowa aka yi wai naje fada za a yi mana gwaji, lokacin da muka shirya yana gaba ina baya. Har muka isa fadan.

    A wani babban filin aka ware domin gwaji, tunda na shiga suka ganin da shigar mata, suka yi ta min dariya. Sultan Mu'allim yana gani na, ya kura min ido. Haka kawai yake mata kallon kurilla. Tare da jin wani irin abu akan yarinyar, har aka nuna mana kwari da bakan, Yayan Sultan Mu'allim, waɗanda da suka rasu, kallon kari da bakar nayi tare da shafawa, wato na Amir Almustapha. Cireta nayi tare da kaɗe ta.

       "Ki ajiye za a baki wani."
"Don Allah ka barni nayi gwajin dashi." Kallon Sarkin kira yayi ya gaya mishi. Shi kuma ya gayawa Amir Sulaiman ya kalli Amir Rahil ya gaya mishi, cikin rawan jiki yace.
"A bata ko Baba na"
Kallon Abdullahi da Abdul Rahman yayi, harara suka zabga mishi, tare da su Ahmad.

         Maida kallon shi yayi ga Sultan, cikin sanyin murya ya gaya mishi bukatar shi, murmushi yayi mishi sannan yayi alamu a barta ta dauka. Su Amir Yazeed da Yasir, da samir sunji haushi. Domin shi Yasir dan gurin Raziyana ce.

     Kallon mutumin yayi sannan yace min.
"An amince kiyi amfani da shi, amma don Allah karki karya alkadarin kwari da bakan, domin ta zama na tarihi, me shi ba rago bane, sannan tarihi yake kafawa da ita ba rushe tarihinta ba."

Ya faɗa min a sanyayye, amsa nayi tare da kallon shi. Haka kawai nake jin wani bayani yana zuwa min.

_Wata rana wannan yanayin zai amfane ta Fudail! Zai amfane ta Rakshan, ku rufe mata idanunta ta harba kwarin jikin wancan bango!_

   Kallon gurin nayi tare da jin kalaman kamar yanzun ake gaya min, ban san waye shi ba, amma tabbas zan so Allah ya kuma hadani dashi. A hankali na nake taryo maganar da wasu ma.
_Dole kiyi aiki da ƙwaƙwalwar ki sama da zuciyar ki, ki auna nisan inda kike da inda zaki harba kwarin ki, haka zai taimaka miki wurin_

   "Magana ake dake!"

     Juyawa nayi tare da kallon shi, sannan nace mishi.
"Kace me?"
"Sunyi harbin ko zaki yi!"
Kallon su nayi tare da ganin duk sun sami abun da ake bukata saura ni ce.

      "Akwai kyale ka rufe min idanuna?" Na bukaci haka, juyawa yayi ya dauka domin akwai a jikin inda kwarin yaƙe, dariya suka saka ganin ana rufe min fuskana, Amir Sulaiman kan yasan zan ci, domin yana mamakin baiwar

Please Login or Register in order to submit comment