Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita yayi cikin tausayin MEHRAN, domin baki daya yayi laushi. Tausayin yadda soyayya ta maida shi yake.

   Ya jima yana nazarin abinda yake damun shi wanda yayi itifakin Babu shakka Ikram itace rayuwar shi, sannan bayi da wani kuzari sai idan tana tare da shi. Ya san a wannan lokacin tana tare da Rahil. Suna soyayyar su. Haka kawai idanun shi ya shiga hango su, suna hira a lambun suna soyayya.

Watsi yayi da kayan gaban shi,yana haki. Kwalla ne ya cika mishi ido, a hankali ya kai hannun shi kirjin shi yana jin kamar zuciyar shi zata buga.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ubangiji ka yayye min, ka kuma kara min hakurin rashin ta. Ya Allah ka jarabce ni ta inda ba zan iya cinyewa ba. Ya Allah na tuba ka yafe min."

Ya faɗa tare da jin kwalla nason zuba daga idanun shi mai dasu yayi, tabbas yana cikin wani hali, Ikram ta shiga rayuwar shi. Ya jima sosai a gurin kafin ya daidaita nutsuwar shi yayi sannan ya fita daga dakin.

--- tunda ya isa shashin Sultanah, bai ce kome ba sai dai duk tambayar da tayi mishi baya ko motsi balle ta saka ran zata sami amsar tambayoyinta.
"Aamaan" ta kira sunan shi kamar ,zata fashe da kuka tana cewa.
"Meye gaskiyar abinda."
"Anneh bana son kina shiga cikin al'amarin gidana." Daga haka ya mike zai bar d'akin tace mishi.
"Amma me yasa ba zaka gaya min abinda yake damun ka ba?"

Juyawa yayi tare da sake murmushin takaici, sannan ya bar dakin yana ji kamar ya had'iye zuciyar shi ya huta, ranshi ya kai kololuwar ɓaci, baya ganin gabansa. Yana shiga cikin d'akinta ya tokari kofar shi, kallon shi tayi a razane. Amma ta dake, juyawa tayi tare da kallon bayin d'akinta. Da sauri suka fita,

Da sassarfa ya isa gabanta, zai kamo wuyar ta, tayi baya tana girgiza mishi kai. "Duk abinda aka gaya maka karya ne, tunda suka ji labarin samuwar cikin jikina suke kokarin ganin bayan shi, sabida."

"Na tambaye ki ne? Nace kiyi min magana ne? Meye ya kai ki shashin Mahaifiyata." Ya tambaya ta a tsawace. Diriri cewa tayi kafin ta saka mishi kuka, tana faɗin.
"Ita Fazilatul nisa ce Mahaifiyar ka?" "Tauuu!" Ya kifa mata mari, wanda yasa ta ganin taurari, a hargitse ta d'ago kanta, wani shegen tsoro ne ya kamata bata san lokacin da ta sunkuyar da kanta ba, gwiwarta zube a gaban shi.
"Na kuma jin labarin haukarki ta kwashe ki har kofar shashin ta, sai na karya ki na maida ke yankin ku, kije can kuyi ta haukar ku sakarya."

Yana gama fadar haka ya juya tare da barin d'akin, tunda ya fita yake jin kamar ya tattara ya bar SAMAIND ko zai sami sauƙin damuwar da yake ciki, amma ina.

----
Dan haka ya tattara ya koma can gidan shi da ya tab'a zama, dan anan yake jin zai iya samun nutsuwar da ya rasa. Tare da Fudail suka koma sai masu kula da abinda zai ci, sam baya son magana ko da kuwa a cikin mutane ne, yafi son ya keb'e kanshi yayi shiru.

----
Merocco.

Da wani zai gaya min yadda rayuwata zata koma ba zan yarda ba, dawowar Nimrah bai kara min kome ba, sai damuwa domin tunda tazo bata da wani aiki sai kukan halin da ta sami Mahaifiyarta, ga kuma soyayyar Fudail da ya kamata, kwanciya tayi a jikina. Tana zubda kwalla, tare da gaya min halin da take ciki.

Shafa kanta nayi domin ita kukan dad'i take, kuma nasan zata sami abinda take so ni kuma fa? Waye zai bani abinda nake so? Sam mulki da nasabarta bata dace da rayuwata ba, ni rayuwar Yanci nake so.

Bana bukatar kome bayan Yanci, shi yasa da zan mallaki Mehran tabbas zamu bar SAMAIND har karshen rayuwar mu, mu shiga inda ba za a kuma ganin mu ba, muyi rayu daga mu sai Yaran mu. Wannan shine tsarin da nake shirya mana,.kamar Yadda iyayena suka bar gidajensu, haka mu ma zamu bar cikin daular mu. Muje mu kafa kanmu tare da boye asalin mu.

"Assalamun Alaikum!" Sallamar Rahil ya katse min nazarin da nake. Lumshe idanuna nayi kamar ina barci, shigowa yayi tare da zama yana kallon yadda na sunkuyar da kaina, murmushi yayi tare da cewa.
"Toh meye laifin sallamar da ba za a amsa min ba?" Ya tambaye ne ni, tare da tsare Ni da ido.

Mikewa Nimrah tayi tare da kallon shi tace mishi.
"Barka da shigowa Amir Rahil," d'aga mata hannun yayi yana murmushi, a hankali ta bar d'akin. Dawowa gabana yayi tare da zama ya zuba hannun shi akan cinyata.

"Me yasa kika fi son shi akan Ni? Meye bani dashi? Dame ya fini da kike zubda hawayen ki sabida shi?"

D'ago kai nayi ina kallon shi sannan nace mishi.
"Kai zab'in kakannin mu ne, shi kuma wani shashi ne na rayuwa ta, zan amshi aurenka ne...[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

25
Ina zai kai tilin abin kunyar da ya faɗa? Ya zai fahimtar dasu ba laifin shi bane na zuciyar shi ce da bata da adalci? Ina gwara ya had'iye kome koda haka na nufin ciwon da ke zuciyar shi itace ajalin shi.

  Da kunya ya bude bakin shi yace soyayya ce ta maka shi da kasa, da wani ido zai kalli jama'ar fadan shi, da wani bakin zai gaya musu ba yin shi bane zuciyar shi ce da bata san Yakana ba, kai tir da wannan kalama me sunan *SO*, bata mishi adalci ba.

   "Allah ya baka lafiya, ga magani nan za a baka naka sha, don Allah ka rage damuwa da tunani." Ya fada mishi, juyawa yayi tare da hada kayan shi, ya fita daga gidan. Jungu jungu suka yi tare da kallon shi. Lumshe idanun shi yayi yaki magana, dan gani yake kamar zasu kasance tsaf abinda yake damun shi. Shi yasa ya juya musu baya, dan baya son su karato abinda yake damun shi.

      ~~~
Da gaske Mehran ya targada min hannun, asalima irin targad'en nan na kan wuyar hannun ne, dan haka naji bakin cikin ainun.
"Ikram me ya sami hannunki?"
Murmushi nayi sannan na maida hannun na rufe.
"Faduwa nayi?" Na fada a gakile,
"Amma sai wannan bai kama da faduwa ba, sai dai ko an murɗe hannun aka yi, don Allah waye ya miki haka?"
Tashi nayi zan koma cikin dakin. Suka sha gaba na.
"Ikram! Kin fita daren jiya gidan Sultan Aamaan!"
"Babu inda naje!"
"Matsala baki iya karya bane dubi yadda fuskar ki yake nuna alamun karya kika yi? Idanun ki juyawa fa suke? Kalli yadda kike kyafta su, wallahi baki iya karya ba, kin yafi jiya ganin Sultan Aamaan ko?"

Suka sani a gaba da tsokana, tare da cewa.
"A haduwar farko aka targad'en hannun haduwar gaba, ba zata muku kyau ba wallahi!" Suka fada suna dariya, tsaki nayi tare da barin su a gurin ina jin haushinsu.

            Zama suka yi ina jin su, suna gulma ta, share su nayi ina kula da hannuna, domin bana son damuwa da zata kuma kara min ciwo na.

  Da dare ma, sun ta zuba ido ko na fita, suka ga ban nuna alaman zan fita ba suka hakura, dole suka kyale ni.
~~~
"Sannun Sultan Mehran! Ashe baka ji dadi, d'azun Darakshan yake sanarwar a fada." Murmushi yayi sannan ya kalle su. Fuskar shi a sake kamar babu abinda yake damun shi, nan kuwa kasar zuciyar shi, Ikram ce take yawo har da ingiza shi akan a duba garin ko anyi baƙi daga wani gurin.

            Ya bude baki yayi magana yana ganin kamar wani katon aiki ne, shi yasa yake bin su sa ido, shigowar Sultanah ya sashi mik'ewa zaune.
"Anne!"
Wani irin dad'i taji a ranta,. Musamman yadda yake kiranta da Uwa, zama tayi a bakin gadon.

    "Mehran! Ga maganinka, sannan don Allah meke damunki? Aamaan ka gaya min don Allah meye matsalar ka?" Murmushi yayi sannan ya juya yana kallon Mahlika da take dauke da tiren maganin, a yanzun yana bukatar mace a kusa dashi, dan haka ya dauke kanshi dan baya jin kome akan ta, duk da yana bukatar mace, baya jin Mahlika takai matsayin Ikram.

    "Miko min na bashi yasha." Ta mika mata, hannun. Cikin girmamawa ta bawa Sultanah.
"Anne barta ta bani!" Ya fadi hakan cikin wani irin yanayi, da ta fahimci yana bukatar nutsuwa,  dan haka na shafa kanshi tare da cewa.
"Ko Mehran zai barni na kintsa mishi ita?" Kasa d'ago kanshi yayi domin yana matukar jin kunyar ta, ganin bai mata magana ba, yasa ta ajiye maganin sannan suka fita.

    Bayan wasu mintinan, sai gata ta dawo d'akin. Murmushi yayi sannan yace mata.
"Zo nan!"
Durkusawa tayi a gaban shi, murmushi yayi sannan yace nuna mata tiren maganin, bayan ta bashi ya sha, sannan ya ce mata.
"Zaki min wani aiki ne!"
Nutsuwa yayi tare da kallonta, saka hannun shi yayi a haɓɓar ta, tare da d'ago ta.
"Zaki shiga cikin gari"
Kura mata ido yayi sannan ya kuma kai kanshi fuskarta, a  hankali yake yawon da hannun shi cikin jikinta,  tare da kai kunnen ta, tare da faɗin.
"Kina da kyau!" Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, domin kuwa ta shiga cikin wani irin yanayi, tare da rike shi. Wato Mehran wani irin mutum ne da ya san kan tafiyar da mace, domin cikin siyasa da hikima yake birkita mata lissafi,kafin ya bata aikin da zata mishi bayan ya kai goshinsa kan gefen fusakarta. Yana goga hancin shi har zuwa wuyarta,  rike rigar shi tayi tare da sauke wata irin ajiyar zuciya.

           "Sultan!" Ta kira sunan shi, tare da shigewa jikin shi.
"Kinji abinda nace miki"
"Eh Sultan naji kuma Insha Allah zan yi yadda kake so."

   Shafa fuskarta yayi tare da cewa.
"Maza yarinyar kirki, jeki maza."

  Jikinta na rawa ta mik'e, kamar zata fadi,  fisgo ta yayi tare da cewa.
"Zo nan!"
Kafaffunta ne taji kamar ba zata iya daukarta ba, shimfid'a ta yayi tare da gyara mata kwanciya, a jikinshi. Wani irin yanayi yake ji, tabbas idan yayi haka kamar yaci amanar zuciyar shi ce, dan haka ya mata masauki a jikin shi, tare da shafa bayanta, har ta fara sauke ajiyar zuciya, kafin ya d'ago kanta. Ganin yadda idanunta tana juyawa, shafa fuskarta yayi tare, da shafa bakinta tare da kallon yadda take kuma tsima, da mugun sha'awar shi.

      "Ikrammmmmm!" Ya ja sunan kasar makoshinsa, kafin ya d'agota yace mata.
"Maza ki tafi inda na Turai"
A hankali ta sauka daga gadon, tabbas tana bukatar shi, amma anya jin koda wasa ba zai bata wannan damar ba.

        Domin wallahi mace daya zai iya bata kanshi da ruhin shi, gangan jikin shi ta da ruhin shi mallakin Ikram ce, dan haka yake jin ba zai iya sake ya bawa wata mace ba. Ita daya ce nata ne kuma baya jin zai bata kuma.

      ---
Gyara zaman igiyar da na zarga hannun a cikin shi nayi ina rintsa idanuna, ga wani uban zufar da nake kamar na had'iye gaushi. Kallon hannun nayi tare da kallon yadda hannun yayi fushi, tabbas sai na mishi illa. Domin bazan tab'a daukar wannan kasadar ba.

            Kallon juna muka yi da Izmah, murmushi tayi sannan tace min.
"Gaskiya Sultan Mehran ya iya mu'amala, kan Uba yadda ya daki hannun nan bana jin zai kuma moruwa."

Kwalla ne ya cika min idanu, na miki ina huci.
"Kinga Mehran bafa banza Allah ya bashi duniya ba, wallahi baki isa ba, ba irin sakarkarrun da kike musu kisar gilla bane, dan haka karki kuma barin kuyi gamo na biyu, dan na rantse zaki sha mamaki!"

    Zuɓewa nayi kasar d'akin, kwalla naso zuba min nace.
"Billahi azim! Idan na kuma zuwa gare shi sai na karshi!"

"Me yasa baki karshi ba? Hmm! Ki daina zafaffawa fa"
"Fitar min a daki bana son ganin ku!" Me fada da karfi ina me juyar da kaina, kwalla na zuba min. Domin ban tab'a faduwa irin na yau ba, Mehran ya hanani samun galaba akan shi, goge kwallar nayi dan nan da kwana uku zan koma mishi.

    ..... A hankali muka sami kwana uku babu wani abinda zan kira na jin zafin Mehran, sai ma tsanar shi da yake kuma samun zama a raina.

A ɓangaren Mahlika kuwa wani irin haukacewa tayi da kaunar Mehran, domin idan ta zauna ji take kamar zata gigice.  Kamshin turaren shi ya rike kayanta, har yau tana jin hancin shi da yake gogawa a wuyarta, wani irin shauki take ji, bata san lokacin da kuka ya kwace mata ba, domin yau kwana uku tana zaga cikin gari domin nima mishi labarin bakin da suka shigo babu labarin dan kullum SAMAIND bai rabuwa da baki, dan haka ta koma yau zata gaya mishi babu bakin da suka shigo garin.

         Sai dai ko zata mutu zai ta haɗa shimfid'a da matar da zai kira tashi, kamar yadda zai yi da Kwarkwarorin shi haka itama zata bashi damar yayi da ita, ba zata iya barin ya subuce mata ba, dan haka ta kulla iniyar haka a ranta, tare da zuba idanunta akan shi da kuma matan da zasu zo gare shi.

Wannan shine alkawarin Mahlika, kamar yadda mahaifiyar ta, taso yi da Sultan Abdus Samad, yau itama tana kuma alkawarin zata gwada sa'ar ta akan Mehran.
(Inda ba kasa nan ake gardaman kokuwa 🤔)

        ~~~
Ba haka yaso ji daga gare ta ba, kauda kanshi yayi daga kallonta, sannan ya mike tare da cewa.
"Jeki!" A hankali ta juya tare da barin d'akin da sauri, tana jin kamar tayi kuka, amma kuma bata da halin haka, domin ita bata ki yace tazo ta kwana dashi ba.

    A falon kasa ya sami Sultana,
"Akwai abinda ya shiga tsakanin ku ne?" Cikin girmamawa, ta sunkuyar da kanta sannan tace mata.
"A'a!" Sai dai kuma ba haka taso cewa a'a ba, domin taso ace tace eh domin kuwa bata ki, tayi karya akan wani abu ya haɗa su ba, toh amma sanin cewa ba yarima bane sarki ne guda wanda haka zai iya janyo mata rasa rayuwarta yasa ta amsawa da babu. Domin wallahi ba a Samaind zaka yi wasa da rayuwarka ba, ai ko kura yasan gidan me babban sanda.

Safa da marwa yake yana jinjina qarfin halin wanda ya kawo mishi hadi matukar ba ikram bane, toh tabbas babu aikawa yayi biyar cutar shi. Wato yayi niyyar mishi kisar gilla ne fa, domin yayi imani da wukar da za a caka mishi, daukar yayi yana murmushi, sannan ya ajiye wukar tare da kura mishi ido, yayi tare da cewa.
"Koma waye zai kuma dawowa!"

   Dan haka ya dage kirjin shi da yake mishi zafi kadan, sabida damuwar da ya saka na kwana biyu, sakamakon binciken da ya tura Mahlika.

     Wasa wasa sai da hannun yakai sati daya sannan na iya juya takobi, dan haka wannan karon ina jin sauki na sake murmushin mugunta, sannan na nufi inda kayana suke na ware su. Sai da na bari dare yayi tare da rabawa sannan na nufi SAMAIND.

     Tafiyar minti arba'in ya kai ni cikin Alharami, ban tsaya bin wancan salon ba, na bi ta bayan gidan, sannan na hango shi tsaye a jikin tagar dakin shi, dan haka na shiga ta babbar kofar da yake sama, sannan na ciro gatarin da nazo dashi. Jin karar cire karfe kawai yayi bai juya ba.

        A yadda na kai farmaki ya bani mamaki domin kuwa kai min duka yayi tare da dukar kafana ma zube, sake kai min duka yayi a cikina, na hantsila can bakin kofar, kafin na sami Arzikin fita yayi nasarar dukar bayana, na zube a gurin,. Dakyar na mike dan ya tsaya tare da raba kafar shi a kaina,.kwashe shi ya fadi a kaina. Kokarin kwace kaina nake shi kuma yana ƙoƙarin gano fuskana, ganin haka yasani kaiwa abin shi duka, ya tintsira can, yana nishi.

Sake mik'ewa nayi ya finciko ni, aikuwa na sake kawai maranshi duka, sai da ya sake wata irin gurnani, wanda ya sani razana. Kamar zan tsaya sai kuma na fita cikin farin ciki, finciko Ni yayi tare da matse ni da kasa, ina ƙoƙarin mik'ewa.

   "Waye kai?" Ya faɗa tare fisgar numfashin, sake kai mishi duka nayi a cikin shi, wani irin gurnani ya kuma sake min, tare da da cewa.
"Meye nayi miki?" Da sauri na kwace kaina.

    "Ikram!" Tsigar jikina ne ya mike sakamakon jin yadda ya ambaci sunan, da sauri na kwace kaina baki daya bayan na kai mishi duka, a gefen cikin shi. Na fita na barshi dan nasan tabbas sai dai gawan shi ba dai wani ba, na gama da babin Mehran,  tunda na samu na bar gidan, haka kawai naji zuciyata ta rabu cikin wasi-wasi, lumshe idanu nayi lokacin da naga tuno abinda yayi min, na tarkato na dawo gida.

     Duk lokacin da na tuna halin da na barshi sai naji kamar baka kyautattawa kai na ba, taya ya fahimci nice? Taya na san nice? Me yasa ya gane Ni? Babu wani dalilin da na bari da zai fahimtar da nice, domin ko turaren na daina shafawa, gudun kar ja fada cikin matsala, sai gashi ya gane ni.

*200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

26

Tunda na shiga cikin gidan, na zauna dab'as a kasa tare da cire bakin mayafin fuskana, ban tab'a jin nayi kuka ba, bayan daukar fansa sai yau, zuciyata tayi rauni ainun, naji a karan kai na ban kyauta ba,. amma kuma yadda nake jin zan amshi kuskurena ne bana jin zan amsa cikin sauki domin nasan nayi laifi babba.

   Amma kuma ya cancanci haka ne, ya cancanci haka daga gare ni, haka da nayi mishi shine hukuncin da ya karb'a amma kuma na kashe shi. Na kashe Mehran.

     Wani irin bugun zuciya ta take yi, tare da jin kamar zata fadi kasa, kuka nake wanda ya farka dasu daga barci suka tawo kai na, zuba min suka yi bayan sun ga jini a bakina.
"A ina kika ji ciwo haka?"
"Izmah! Nimrah na kashe shi!"

Bakin su a haɗe suka tambaye ni.
"Waye kika kashe?"
Cikin mugun kuka nace musu,
"Mehran!"
"Au shine kike mana kuka? Toh an kin kyautawa kanki" kamar hadin baki suka barni zaune ina kuka. Dan tausayi sun ji amma bakin cikin taurin kaina ya saka suka juya min baya.

  Nayi kukan da tun bayan rasuwar Iyayena ban yi shi ba, kai ko mutuwar Airan banyi kukan ba kamar yadda nake kuka akan na kashe Mehran, ina zaune a gurin har kusan tsakiyar dare, ga garin yayi wani irin sanyi.
  Kwanciya nayi, ina sauke ajiyar zuciya kuma idanuna basu fasa zubda kwalla ba. Ina tuno lokacin da muke tare kafin mu zama abokan gaba.

   Duk da bana jin dadin shi, amma kuma yaki barin koda wani abu ya cutar dani, yana tsare lafiyata da rayuwata, Yau shi na kashe sarki guda, wanda ba a tab'a yin matashin sarki irin shi na, shine yazo a karnin na baya baya, me cike da ban mamaki. Matashin da ya haɗa kome ma rayuwa na kashe shi, me yasa nake da bakar zuciya ne?

  Me yasa ban Nime mutanen da suka kashe Airan ba? Amma nazo..
_Kashe miki miji yayi a daren ranar auren ku! Shin zaki yafe mishi? Idan da ace kun zama abu daya a wannan daren da yanzun kina dauke da Yaron ko yarinyar Noman, shin ke kina ganin ya cancanci a yafe mishi._

  Wani irin kuka ne ya kuma dawowa min, dakyar na tashi nayi sallah asuba. Sannan na koma na kwanta, ina jin zuciyata bata min dad'i. Ba laifi bane dan na ɗauki fansa amma kuskure na aikata na kashe babban mutum irin Mehran.

     ...
Bayan tafiyar ikram, Fudail yaga lokacin da aka sauka a katangar gidan, amma bai kawo kome a ranshi ba, dan haka yacewa dakarun.
"Ku shirya an kawowa Sultan Mehran hari! Bari na shiga cikin gidan."

Da gudu ya shiga cikin gidan, koda yazo ma, ya sami Mehran kwance cikin tashin hankali da gurnani, Kiran Sultana yayi suka kashi dakin shi aka shiga bashi taimakon gaggawa. Fita Fudail yayi tare da dauko likitan masarautan, aka zo dashi. Ya kusan kwana akan Sultan Mehran. Dan ana kiran sallah farko yana fitowa daga d'akin shi.
"Ya jikin shi?" Inji Sultanah ta tambaye shi, ajiyar zuciya yayi sannan yace mata.
"Alhamdulillahi! Da sauki sosai, sai dai ya sami barci? Taya aka yi Sultan MEHRAN ya fuskanci irin wannan harin? Anso kashe shi ne fa, domin dukar da aka mishi kan halittar shi na d'a namiji aka dake shi zuwa marar shi, sai dukar da aka mishi a kirjin shi don Allah ku kula"

     Shiru kowa yayi, ran Sultanah ya b'aci domin gani take a garin shegen bin mazan shine ya hadu da shu'umin da yayi mishi wannan dukar.

Bayan tafiyar likitan kacokan ta dauki laifin ta daurawa Fudail, Domin gani take shi yake taimakawa Mehran yake sheke ayarshi idan ba haka ba, taya zai iya dauko namiji har zuwa sama, dan haka tayi tafiyarta dakin ta bata kuma zuwa gurin shi ba, sai da gari ya waye tangaran, sannan  ta shigo dakin shi, yana ganinta ya sunkuyar da kan shi.
"Meye amfanin dakarun da aka zuba su a kofar shigowa? Meye amfanin zamanka jarumi? Meye amfanin bibiyar maza yan uwan ka? Ka ga kenan babu, ba zan hana ka abinda ake so ba, amma matukar ina da iko akanka na kuma ganinka da namiji.

       Gawata zaka dauka, shine karshen biyan laifin da nayi maka tunda narasa da yadda zan biyaka." Daga haka ta fita daga dakin, lumshe idanun shi yayi tare da kallon Fudail da yake mika mishi abinci. A hankali ya karb'a yana ci bai koma d'ago kanshi ba yacewa Fudail.
"Tana raye"ya faɗa tare da d'ago kai, yana kallon bakin kofar shigowa dakin, da sauri Fudail ya rufe kofar, sannan ya dawo gare shi ya d'an sunkuya yana fadin "wacece take raye?"

"Yarinyar da tabi SAURAYINTA!" Cikin wani irin azama ya d'ago kanshi, yana me jin ina zai kyaleta ta rayu, juyawa yayi zai fita yace mishi.
"Ina zaka?"
"Zanje na sare kanta!"
"Zata dawo, sai dai bana son Anne ta ji labarin, domin zata iya tsaneta domin idan ta tsane ta, ba zanji dadin ganinta a tare dani ba, kuma itama Anne ba zata ji dadin ganin mu a tare ba.

         Tunanin ta ya bata cewa ni nasaka a kashe shi, ita kuma tazo daukar fansa, domin irin yadda take niman hanyar da zata kashe ni ba na kananun makasa bane, nasan na koya mata kare kanta, amma ban zata a kaina zata kare ba, na zata zata iya tsayawa kanta ne.

     Alhamdulillahi tunda yana cikin koshin lafiya, babu abinda ya same ta,. mahaukaciya ta kara girma da taurin kai" ya faɗa yana dafe kanshi sakamakon yawan maganar da yayi, sannan ya lumshe idanun shi, yana jin wani irin abu a ranshi, murmushi yayi sannan kalli Fudail da yake kallon shi cike da mamaki.
"Na zare ko?"
Girgiza mishi kai yayi sannan ya maida kanshi yana cewa.
"Anya itace kuwa!"
Murmushi yayi sannan yaja bakin shi kamar ba zai magana na,sanan ya d'ago kai yana kallon shi..yace mishi.
"Na tab'a maka karya ne? Na tab'a maka musu ne? Toh ka saka ido nan da kwanaki zata dawo, kuma zaka sha mamaki." Kasa magana yayi yana kallon Mehran, dan gani yake kamar na gaskiya bane, shi yasa ya dauke maganar a matsayin mara muhimmanci.

     Shi kuwa Mehran, murmushi yake lokaci zuwa lokaci, yana me kallon kofar yadda suka tukwaikuye kan su, sai ya sake murmushi. Yana jin babu wani ciwo da

Please Login or Register in order to submit comment