Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dama kuma an mishi wannan shedan.

Cikin kankanin lokaci aka fara mishi bore da Zanga Zanga, wanda ya saka asalin dakarun masarautan tarwatsa Yan zanga zangan.

.....
"Toh ina Mehran yake? Yasan ba zai iya zama haka ba, sai ya saka ana kwaso musu ɗiyoyin talakawan shi yana lalata dasu "

Shiru duk suka yi suna sauraron Amir Hood, wanda ya zakalkale yana masifa, zaka rantse da Allah ya kama Sultan Mehran da aikata laifukan da ake zargin shi da su. Dalilin da yasa mahaifiyar shi da makusanta shi suka zo niman shi kenan, suka ji muryan shi da Ikram suna cikin wannan yanayin.

.... Zirga zirga take a cikin babban falonta, abu biyu ya tsaya mata a rai, na farko abinda yake faruwa a gari na biyu, samun shi da suka yi yana masha'a da Baiwar shi. Abinda ya girgiza ta, kenan duk gudun da take na tsawon shekaru ya rushe?, duk wannan hakilon da take na tsawon shekaru ya tashi a banza? Wabi irin zufa yake karyo mata tare da tsinewa Ikram yafi kwando dubu. Da alƙawarin idan ta same ta, tabbas sai ta saka an mata mafi girman uƙubar da har ta koma ga mahaliccin ta ba zata manta dashi ba. Gyada kai take kawai gashi ta hana kowa shiga gurinta, saboda kar bakinta ya fadi abinda bata shirya gyara shi ba.

---
Gyaran murya Fudail yayi lokacin da ya shigo babban falon ya tsince Ni kwance, munyi kaca-kaca da gurin, alamar babu sauki, kirjin shine yayi mishi nauyi sam bai so wannan alaƙar ta shiga tsakanin Mehran da Ikram ba, dan Allah ya gani yana jinta a ranshi. Amma ya zai yi da ƙaddara ta riga fata, daukarta yayi zuwa dakinta. Gyara mata kwanciya yayi tare da shiga ban dakin ya dauko tsumma da ruwan zafi, yayi ta saka mata a goshinta har ta farka, sannan ya mike tare da kallon ta.
"Nagode!"
Na fada a hankali, girgiza min kai yayi tare da daure fuskar shi yace.
"Allah ya gani bana son alaƙar ki da Mehran!"

Da sauri na kalle shi na wasu dakikai, sannan na lumshe idanuna, tare da yada kai ina jin bayana yana ciwo. A hankali ya tako tare da sunkuyar da kanshi, yana kallon fuskana.
"Ki taya masoyinki kanki kare kanki!" Lumshe idanuna nayi a karo na biyu, tare da maida kai na saman matashina ina sauke wani irin ajiyar zuciya.

Kewar Noman da kaunar shi yana kara samun matsuguni a raina,
Juyawa yayi ya fita, bai jira me zance ba, sai dai kuma yana cike da ɓacin rai, koda ya isa bakin kofar da zata sada shi da dakin Mehran.

Wani irin abu yaji ya takore mishi kirjin shi, dan dole ya juya tare da barin shashin, dan yana shan alwashin duk abinda Mehran zai yi sai dai yayi dan sai ya raba shi da Ikram. Da wannan alwashin ta fita daga gidan.

Sallah azhar ya d'agani na nufi ban daki nayi wanka tare da alwala, sannan na fito nayi sallah. Tare da saka kaya na fito, ina tafiya a hankali, sannan na nufi madafin, abinci nayi har da na bude bakina, ina gamawa na fito na ajiye mishi na shi, sannan na gabatar da sallah a falon. Ina cikin sallah naji motsin shi, ban fasa ba har ya shigo.

Kura mata ido yayi cikin nutsuwa, yadda take da kokarin yin sallah da Ibadar ta yayi masifar tab'a zuciyar shi, bai san akwai ranar da zai ganta bata sallah ba. Har mamaki yake idan yaji muryanta tana karatu ko waka ne oho, duk da shi Balarabe ne baya fahimtar karatun da take, sai dai abinda yake yawan ganewa shine idan tana karantawa tana mugun jin dadi dan har akan fuskarta yake ganin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Zama yayi tare da kallon yadda take addu'a, dukda yana jin haushinta na wani lokaci, amma yawan ibadarta yakan sashi jin dadin zama kusa da ita. Bai san ya jima a tsaye ba, har sai da Rakshan ya shigo falon yayi mishi magana tare da gaya mishi halin da gari yake ciki. Ko takan abincin bai duba ba, ya fita daga gidan, kayan jikin shi daga farar jallabiya babu kome.

Ganin dattawan fadan sun fusata kamar zasu cinye shi, yana kallon shi, tare da jin su dan baya fahimtar abinda suke fada sai da can. Ya gaji da hayaniyar su ya daka musu wani uban tsawa wanda Yasaka suka shiga cikin nutsuwar su, zama yayi yana kallon su, sannan ya kura musu ido, ya kalli Fudail da magatakardan masarautan, yana sauraron shi.
Yadda yake bayani cikin nutsuwa da zargin shi da ake, ya sashi gyara zaman shi cikin nutsuwa, ya daura daya akan daya yana wani girgiza kafar shi, tare da kallon su daya bayan daya.

Murmushi yayi sannan yace musu.
"Idan kuma ba Ni bane fa?"
Shiru suka yi tare da kallon shi, mik'ewa yayi sannan ya kalli wata agogon karfe wanda wani mutumin rum ya kerawa masarautan, da zallar karfen azurfa sai dutsun jauhari, wanda aka yi adon madubin agogon dashi.
"Karfe nawa?"
Sunkuyar da kansu suka yi,
"Karfe uku Sultan!"
Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi, kamar baya cikin fadan.
"Uku na asuban gobe!" Daga haka ya mike, zai bar fadan.
"Wai kai wani irin mutum ne mara mutunci!"
"Ku kama shi!"
Haka suka kama Mir Rahil, aka fita dashi yana jan Bala'i wa Sultan Mehran.

---
Tunda ya koma yake zirga zirga, tare da zurfaffa tunanin shi, koda baya mu'amala da mutane tabbas yasan ana bin shi da sharri amma yadda ake gudanar da mugun nufin ne bai tab'a tsammanin haka zai faru ba, dan haka ya dauke kan shi kamar bata sane da abinda yake faruwa, a kowane lokaci yana kara fahimtar mutanen da suke zaune dashi musamn dattawan da suke fadar shi, yana kuma kara gane meye matsalar shi dasu.

Na farko dai yasan mulkin da yake kai ne basu so, na biyu basu tab'a tsammanin shi din ba kanwan lasa bane sai da aka bashi mulkin, dan haka yana sane da wannan abun sha yayi sanadin da suke kin shi kamar zasu kashe shi.

Muryan ta yaji tana karatun Suratu baqara, bai san lokacin da ya taka har kofar dakin ba, yana tsaye a gurin har ta tsayar da karatun sauke ajiyar zuciya yayi sakamakon yadda na sami nutsuwa da sauraron muryanta, da karatunta, a sanyayye yake kuma jin yana Samun sauki daga cikin damuwar da yake fama dashi.

Kan shi yana kuma budewa daga cikin duhun da yake fama dashi, a karon farko da yaji yana son ya sami wanda zai taya shi fahimtar rayuwar da yake ciki, sai dai bai san yadda zai fada halin da yake ciki ba, dan dole ya juya baya tare da komawa dakin shi amma tabbas yana cikin damuwar da yake niman abokin hira da raba damuwar shi.

Littafin nan na kuɗi ne
Allah ka jikan Iyayena.
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
     
Page 26
      Shiru  yayi yana kuma nazarin halin da yake ciki. Ga shi nakiya sun sako shi a gaba, gashi yana kuma son sanin waye yake tab'a shi ta hanyar da bai sani ba.

          Dan haka ya dawo gurin cikin abincin shi ya zauna tare da kura mishi ido, kamar yana son gano wani abu a cikin gurin, amma a zahiri ba haka bane tsabar damuwa da tayi mishi yawa ce da tashin hankali.

         Ya rasa ta inda ya rage da mutane suke tab'a shi haka, dan haka ya shiga dakin shi tare da tsayawa yana kallon madubi, kallon kirjin shi yayi wanda yake dauke da ciwon wancar yarinyar, ya jima yana kallon yadda gurin yake sannan ya cire rigar shi ya dubi ciwon ba wani babba bane.

     Amma kuma yana d'an jin zafin shi a jikin shi kad'an kad'an, wanka yayi tare da sake gyara ciwon,kafin ya koma dakin shi ya shirya,tsaf.
      ---ina karatu naji kamshin turaren shi,dan haka sai na kasa fahimtar abinda nake karantawa,dan ina jin kaifin idanun shi a kaina, nutsuwa nayi na cigaba da karatuna har ya gaji ya bar gurin, yana barin gurin ina sauke ajiyar zuciya,  sannan na cigaba da karatun kusan karfe shida na rufe karatun, sannan na fito niman abinda zanyi buda baki dashi, tashi  nayi tare da shiga kitchen ɗin na shiga girki ina gamawa na juye tare da jerawa a tire, na shiga dakina dashi. Sannan na fita daga dakin na nufi babban maajiyin abinci na duba ajiyayyen ya'yan itacce, na hauro sama, ina kallon shi ya harde cikin bakakken kaya, kallon inda yake banyi ba, sannan na shige d'akina, na zauna har lokacin shan ruwa yayi, nasha ruwa. Bayan na idar na nufi ban daki nayi alola, gabatar da sallah nayi sannan na zauna ina azkar har lokacin isha yayi na gabatar tare da sallar tarawee, ina idarwa na kwanta a hankali.

            Ina kwance naji an rufe kofar dakina ta baya, nasan wulakancin Mehran ne, sai ban damu ba.
       ~~
Babu wanda ya san kudirin shi, sai dai kuma bayan ya gama sauraron karatunta,yaji bata motsi a cikin dakin, shine ya rufe ta,sannan ya fita daga gidan, ta baya, wato ta tagar dakin shi ta zura igiya ya sauka. Tare da daukar makamai na balai ya shirya a bayan shi, sannan ya nufi cikin dokar dajin da take bayan gidan shi, wato idan ana maganar farauta toh abinda Mehran yayi kenan, domin abinda yake zargi ne ya faru,mutanen da baya tsammanin zai same su a kusa su ya samu.

    Cikin ban mamaki ya dira musu, suna tsaka da masha'a da yan matan da suka ce shi ya turo du dauke su.  Razane suka mike tare da kallon shi.kowannen su ya dauki makami.

               Bai shirya musu ba dan haka ya sunkuyar da kan shi tare da raba kafar shi d'aya da kasa, yayi wata irin tsayuwa me mugun daukar hankali, irin ta sarakuna, cikin ihu da karaji suka nufe su.

   Nan suka falle da wani irin azabben yaki tare da kaiwa juna sara da suka,  takobin shi ce ta fadi ya kuma saka hannun shi ya zaro Gatari hannun biyu, yake kai musu sara da ita. Idan ran shi ya b'aci ko gaban shi baya gani, d'an batalikin nan cikin rashin mutunci yayi ta girbe halittun Allah, yana gamawa ya jibge su ya zauna akan su.

      Kadawar Bishiya da saukar ganyayyeki yasa shi fahimtar akwai wani gumurzun a gaban shi,mahayi ya gani tare da dokin shi, dan haka bai shirya ba. Dan ya rena mahayin, cikin Sa'a kuwa mahayin ya dauki kwari da bakar shi ya saita daidai kirjin shi, ya sake mishi kwarin cikin wani irin zafin nama, ya shiga kare kanshi, yana falfalawa da gudu, wato yana tun karar mahayin tare da kare kan shi da gatarin hannun shi, cikin Sa'a kuwa aka same shi a gefen cikin shi,da sauri ya kabe amma ina bakin kwarin ya shiga, dan haka yabi mahayin tare da wurga mishi gatarin hannun shi, aikuwa suka fadi can da dokin, sosai, ji yayi kamar wani abu yana yawo a jikin shi, dan haka ya juya da wani irin azabben sauri ya koma gurin da aka yi yakin, ya hango wani akan doki yana gudu. Dan haka ya xari wani karamin wukar shi ya wurgawa mutumin, rigib ya zube daga kan dokin, sannan ya isa gurin Mutumin ya d'aga shi tare da jan linzamin dokin ya daure shi tam, sannan ya nufi tantin dakarun bokin yaga yan mata birjin an gama lalata musu rayuwa,

            A hankali ya fito daga dakin tare da zama, yana jin jikin shi yana kuma ɗaukar bakon yanayin da yake ji kamar daga ciwon da aka harba shi ne. Dan haƙa ya mike tare da umartan yaran su tashi su gyara jikin su, shi Ceton su yazo yi.

          A hankali suka gyara kan su, shi kuma ya haura doki, bai ce musu kala ba suka shiga gaba bin bayan su, dan baya son wani abu ya kuma samun al'ummar shi bayan haka. Mutumin da ya kama yana jan shi, wanda ya harbe shi ne dai bai samu nasarar kama shi ba, har bakin kofar masarautan suka isa, bugawa yayi Dakarun da suke tsaron kofar suka ce.
"Waye?"
"Sultan Aamaan Abdus Samad Aamaan, Mehran!" Jikin su na rawa suka bude kofar, da sauri suka bude kofar, kallon su yayi yana ganin su biyu biyu, bai ce musu kala ba ya wuce. Cikin karfin hali yayi ta taka Yan matan kofar gidajen su, sannan ya juya dakyar ya nufi cikin gidan sarautar, yana jan mutumin nan. A lokacin karfe uku saura da karfi ya kai shi har cikin fadar, ya daure shi da wata makata idan aka tab'a tabbas mutumin nan ya fado mutuwa zai yi dan haka ya shirya mugunta kala kala, sanan ya nufi castle din shi da sauri, dakyar yake bubuga kofar gidan, Rakshan da Fudail suka zo suka bude mishi kofar,  a hankali ya shige yana rike cikin shi. Bai tsaya ba, sai kofar dakin Ikram.

      Jingina yayi tare da bude kofar d'akin.  Ina tsaye dan tunda suka shigo wajen karfe ɗaya suka duba baya nan hankalin su yaso tashi sanin cewa yana fitar dare yasa Rakshan share shi, ganin har karfe biyu bai dawo bane yasa su shiga damuwa dan duk suna kofar babban falon kasa.

         Bude kofar yayi tare da faduwa a jikina, muka zube tare, cikin wani irin fisgar numfashin sa, yace min.
"Sun harbe Ni!"
Ya kai hannun shi saman cikin shi, tare da riko hannuna ya kai kan ciwon, wani irin tsoro ne ya kamani, ban san lokacin da na fasa ihu ba,  tare da kiran su Darakshan da Fudail, sune suka kawo mishi dauki tare da ɗaukar shi zasu fitar dashi.
"Karku kai ni ko ina? Anan zanyi jinya."

   Ya nuna musu saman gadon da nake kwana.
"Mehran!"
"Nace anan!" Ya daka musu tsawa, a sanyayye suka kwantar dashi tare da kallo na.
"Ikram! Ko zaki fita ki koma falon da."
"Ita zata yi jinya na!"
Ya faɗa musu kai tsaye,
"Amma Mehran idan Sultanah Hoyam tazo."
Tari ya fara me dauke da wani irin koren amai,da sauri muka zuba mishi ido, d'aga rigan shi Fudail yayi sai ga tsinin kwarin, bai tab'a ba, suka fita shi da Rakshan, bayan fitar su, ne kiran Lingesa, kawai sai ganin wani mutum da bakakken kaya muka yi a bakin kofar dakina.

                 Tashi yayi dukda yana ganin dishi dishi, bai hana. Shi daukar gatarin da yake k'ugun shi,  da gudu  mutumin yayo kan shi, fisge gatarin hannun shi nayi na tari mutumin, muka fada wani azazzaben yaki a cikin dakin, ban tab'a sanin  wahalar da yake bani koya min yaki yake ba, sai yanzun da abin ya kama nayi.har kamar zan fada kan shi, a hankali ya mike tare da tsayawa a bayana,. Lokacin da mutumin ya kai min wani gawurtaccen sara, na tafi zan fad'i.
Hannun shi ya kai tare da dafe cikina, da sauri na juya ina kallon shi.
"Kuyi irin abinda nake yi!"
A hankali ya maida ni kirjin shi, tare da rike daya hannun nawa tare da nuna mutumin da takobi, kafin yayi mata alamar ta matso, cikin kwarewa da iyawa yake koya min fada tare dashi, dan ya fahimci mutumin da muke yaki dashi.tsohon kashi ne, shi yasa ya hada karfin shi kwarewa ta, muka shiga wani irin fada me mugun cin rai.

   Tunda muka fara, yake cije wa, idan abin ya ciyo shi sai dai naji kanshi a kan wuyana, tare da matse ni a jikin shi, idan ya sake shi kuma mu Cigaba da bagwaza fadan.
        Cikin hukuncin Allah ya daura yakin zuwa wani na daban,wato ana amfani da makami ana amfani da hannun ko kafa, kafin kace kwabo mun.hada mata zafi jin ana shigowa yasa ta buga wani abu abu dakin yayi mugun duhu. Tari muke har suka shigo mana, zuɓewa yayi a bayana, tare da sauke wata irin numfashi, da sauri suka kwantar dashi, aka fara bashi kulawar gaggawa. Ni kuma na shiga kwashe duk abinda aka fasa ina gyara dakin. Ina gamawa, na fita a daren dai dakina ban rintsa ba, har gari ya waye dan masu kula da lafiyar shi basu tafi ba, haka ma Lingesa bai fita ba.

Haka suka kwana suna fama dashi, kasa sahoor har lokaci ya wuce, ina zaune shigowar Sultanah Hoyame ne ya sani mukewa yana kallon ta, bata bi ta kai na ba, ta shige dakin. Tana ihu fitar da ita aka yi, shi kuwa yana kwance kamar gawa.

Sun sami nasarar cire kan bakar, sai dai matsalar an yi amfani da mugun guba ne a jikin bakar, wanda a lokaci guda ya canja mishi halittar shi, jikin shi yayi kore shar. Hatta idanun shi kore yayi, dan haka Sultanah Hoyame tace a daga shi daga dakin a maida shi dakin shi, ko kuma shsshin ta.

"Kiyi hakuri yace ko mutuwa zai kar a fitar da shi daga dakin nan!" Cikin faduwar gaba take kallon shi, Zuciyarta yana zullumi.
"Akan wani dalili?"
"Haka kawai!"

Da sauri ta bar dakin tare isowa inda nake sallah, dukda tasan cewa babu kyau tayi yada zata katse mata sallah da tayi, cikin jin haushi, take kallon ta.

Ina idarwa Naji an rufe ni da duka tana tsine min.
"Makira Tsinanniyar yarinya, meye kika mishi yace a wancan kaskantacciyar dakin zai zauna, meye kika mishi da ya zab'e ki sama da sauran matan da nake tallata miki!"

Janya ake tana ihu tare da cewa sai ta kashe ni, babu digon kwalla a idanuna Asalima kallon ta nake, murmushi nayi mata, Fudail yace mata.
"Sultanah babu abinda yake tsakanin su fa, kawai yafi son zama a dakin ne."

Fisge rikon da suka mata tayi,sannan tace.
"Ki gaggauta warware abinda kika mishi, idan ba haka ba zan kashe ki. Kuma na haramta miki sallah a cikin wannan gidan."

Da sauri na d'ago kai ina kallonta, anan ne nace mata.
"Koda kuka fanshe ni a baiwa baku gaya min bazan yi ibada ta ba, dan haka rayuwata fansa ce ga addina."

"Ku fita da ita! Ku azabtar da ita sama da furucin bakinta."
Haka suka kasa koda motsi ne, suna kallonta.
"Sultanah babu wanda ya isa hukunta Ikram dan tana karkashin Kulawar Sultan Mehran ce!"

Aikuwa ta birkice musu da fada, akan me zasu ki amincewa a fita dani.

Haka ta Karachi masifarta tare da fita daga gidan baki daya,.tun jiya ake abu daya ba a sami makarin karya gubar ba, haka aka shiga niman masu maganin gargajiya.

A lokacin gubar ta fara fadar da jikin shi, dan haka suka yi ta fama dashi.
Wunin ranar an shigo da masu maganin gargajiya sun kai hamsin, gashi an sanar da masarautar da garin baki daya, haka ma iyayen yan matan da aka kwashe sun gayawa Iyayen su ba Sultan Mehran bane, wasu ne da wani dan cikin masarautan, dan hakan iyayen su suka shiga addu'a Allah ya tashi kafad'ar shi, domin kuwa a gurin ceton su ne aka harbe shi..

Littafin nan na kuɗi ne.
Allah ya jikan Iyayena
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
     
Page 27
Daga cikin mutanen da aka tafi da yaran su, sunyi kokarin taimakawa da gudummawar su, na magani amma babu nasara, asalima sai muke ga babu wani canji,

Dan haka na kalli Lingesa nace Mishi.
"Zan sami Hulba da habbatul saudat! Sai y'ay'an zaitun!"

"Zaki samu!" Muka juya zamu fita, finciko Ni, Sultanah Hoyame tayi tare da cewa.
"Idan Sultan MEHRAN ya mutu gawarki ba za'a same ta bama balle ke din."

Ban kulata ba, muka fita, cikin gaggawa nasa aka nika min hulbar, sannan na zuba mata ruwan zafi na sannan na kuma dafa wani hulban da Habbatul saudat tare da garin zaitun, na zuba a wani ƙaramin buta, sannan muka nufi dakin shi, muna zuwa. Ka bude min cikin shi na zuba kwab'abben hulban sannan na saka suka d'aga shi yasha.

Sannan muka koma gefe muna jiran abinda Allah zai yi, kasa nutsuwa nayi na nufi waje nayi Alola tare da gabatar da sallah, sannan na dawo bakina dauke da kirariwa Ubangiji na. Sun bani damar nan da kwana biyu idan babu canji zasu nimo wani taimakon. Dake ana ta jaraba masu maganin, muna gurin Sai ga Narmin da wata matashiyar budurwa, cikin wani irin shiga tazo duba shi. Kus-kus suka yi da Sultanah da Narmin sannan ta kalle mu, kafin tace mana.

"Zaku iya bata guri zata yi aikinta." Kallon ta nayi haka kawai naji raina bai kwanta da ita ba, juyawa muka yi zamu fita sannan na juya na kalle ta, sam bata da gaskiya ko na miskala zarra, haka muka fita ban san me suka yi da Sultanah Hoyam ba itama ta fito.


Tunda suka kawo me maganin nan bana ce ba, amma jikin Mehran babu yadda yake, kullum zata zo da safe, zata zo da dare. Wai tana bashi magani. Haka kawai na shiga dakin tare da d'aga ciwon amadadin gurin ya kame sai ma ya kama ci kamar ana tab'a shi, dan haka bayan tafiyar da dare, kawai na fita har shsshin bayi na samo lalle da kashin shanu, sai Hulba da Habbatul saudat da zaitun. Na saka na hada tare da zuba Mishi ruwan zam-zam wanda na samu a gurin Narmin, sannan nazo na kwab'a na zuba a gurin ciwon.

Idan akwai bakin sihiri sanadin kashin shanuwan nan zai nuna, idan kuma guba ce zata motar gurin, idan kuma dajine ma zai nuna alamar shi, dan haka ina sakawa na tsaya a dakin har asuba na tashi nayi sahoor, sannan na duba ciwon, wasu irin tsutsa suka cika saman maganin, fita nayi na kira Fudail yazo muka kwashe tass, sannan yace min.
"Me ya faru?"
"Kwashe maganin wancan matar nayi, sannan na saka mishi wanda nagada a gurin mahaifina, Insha Allah zuwa gobe da yamma ciwon zai kame, sai dai ina son son Allah a hanata shigowa domin kuwa."

"Baki da lafiya! Ba zai yiwu ba, kawai ki kyale ta tayi abinda taga zata iya! Kema kiyi wanda zaki iya. Bana son kusancin ku yana."

Rike k'uguna nayi tare da sauke gwaron numfashi sannan nace mata.
"Baka da lissafi! Taya ina ganin tana cutar shi zan."
Fisgo ni yayi tare da Hadani da bangon dakin, yana huci duk kowani dakika ji nake kamar zuciyata zata buga idan na fahimci yadda kike kai Gwauro ki kai mari, a gaban Mehran ji nake kamar na kashe kowa na hana shi ganin ki.

Me yasa ba zaki Fahimci yadda zuciyata take kaunark..."
Girgiza kai nayi wani irin kuka yason taso min, na shiga cewa.
"Zuciyarka bata maka adalci ba, bata maka adalci ba, bata maka adalci ba, tuntuni ina da wanda nake kare kaina domin shi, kabawa zuciyarka hakuri akwai wanda yayi

Please Login or Register in order to submit comment