Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zamu yi kewar ki ni da sauran mutanen cikin gidan nan!"

   A hankali na mike tare da mata godiya sannan na fice daga dakin.  A hanyar d'akinta muna hadu ni zan fita shi kuma zai shigo. Kallon juna muke tare da kasa furtawa juna koda da kalmar sannun ce, karshe sai gashi mun tsincin kan mu da kasa bawa juna hanya idan ya kuma gefe nima zan koma gefe,.

.idan ya tsaya zan tsaya karshe ture ni yayi gefe ya shige abin shi ina kallon shi. Wannan wacce irin rayuwa ce haka? Meye nayiwa Mehran da ba zai yafe min ba yake bani wahala har haka? Zan tafi zan yi nesa dashi yadda zai gane bani da laifin da yake zargina, amma tabbas Mehran ya zalince ni sosai. Babu kome Allah zai bayyana gaskiya koda bana tare dashi. Duk tsawon lokacin da na dauka, da fansar da nace zan dauka na ƙasa daukar haka sabida Mehran yau gashi sabida abin da yake da yakinin bai faru ba, ya kirani mazinaciya, karuwa, datti,shara, bolar kowa.

      Share kwalla nayi tare da barin kofar d'akin, na nufi hanyar da zai fitar dani, Fudail muka ci karo.
"Ikram yanzun  ɗan uwanki yake ta niman ki kamar wani karamin Yaro." Murmushi nayi sannan nace mishi.
"Rahil rigima!" Har zan wuce yace min.
"Kiyi hakuri! Kishi yake damun Sultan Mehran, amma kece rayuwar shi."

   Ganin shi muka yi a gaban mu, jikin shi yana kerma.
"Waye kake magana akan shi? Ni Allah yayi min tsari indai ni ne, wannan itace rayuwata? Kishinta nake?" Riko hannuna ya yi tare da jana zai kai ni cikin Kwarkwarorin shi ya tozartani. Sai ji nayi an rike hannuna, tare da fisgo ni. Dukkan mu a tunanin mu Fudail ne. Amma abinda mamaki Amir Rahil ne.

     Cikin b'acin rai,.wanda tunda nake ban tab'a ganin shi ita ba. Fuskar shi har wani jajja jjaa tayi. Ya karasa takowa gaban Mehran ya. ya janyo ne jikin shi tare da sakala hannun sa a kafadana, yana kallon Mehran.

       "Ba zaka wulakantatta ba, matukar ina raye. Muje Salsabila ke kadara ce me tsada baki yi wannan arahan nan da za a tozartaki ba. Dan haka muje cikin Zuri'ar mu kiga yadda ake kaunarki.  Mulki yake yawo a jininka shi yake yawo a jininta. Ya zaka ji idan na gaya maka ita kanta Sultanah ce a kasar Masar!

       Ya zamani idan mace maka ita Sultanah ce a Merocco. Dan haka karka tozarta ta, domin zan iya sare hannunka." Ya faɗa mishi yana kallon cikin idanun sa, juyawa muka yi tare da fita daga gidan baki daya. Kukan da nake rikewa ne yazo min, sosai nayi tare da kifa kai na a kirjin shi.
Har muka isa masaukin su, anan ya ajiye Ni a dakin shi, yayi ta min hira tare da bani labarin abinda zai sani da dariya. Nayi kokarin koran b'acin rai da damuwa, akan fuskana amma a zuciyata kawai ina jin babu dadi. Dan haka nayi ta biye mishi muna ta hira har ya ga nasake ina dariya.

    Tausayi ya bani sabida yadda yake nuna min so ba karya bane, kaunar da yake min yana shimfiɗe akan fuskar shi. Dan haka yake kokarin sai ya sani dariya kota halin k'ak'a.

  ~~~
Har suka bar gidan yana tsaye kamar gumki, idanun shi jajjur.  Dan ji yaƙe kamar an tafi mishi da zuciyar shi, niman faduwa yake. Fudail ya rike shi. Kallon shi yayi sannan yace mishi.
"Sultan MEHRAN! Kayi kuskure babba. Duk abinda za a gaya maka akan Ikram bai dace ka dauka ba, sannan itama kanta taje taji meye ya faru har ka tsane ta haka.

      Mehran ko yanzun haka Nawwas yana jiranka zai maka bayanin abinda ya faru, amma ka sani sai ka cire wannan tsanar da kake mata, tare da fahimtar wacece ita. Sai ka haɗa abinda ya gaya maka da mahaunin hankali matukar kace ba zaka yi haka ba, tabbas yanzun ka fara nadama, domin zaka yi ta kuka har karshen rayuwar ka......
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

38

Kallon Fudail yayi cikin damuwa, amma kuma idan ka kalli yadda ya ɓoye haka zaka iya rantsewa har da Allah babu kome a ranshi, Mehran yana cikin mutanen da Allah yayi musu baiwar ɓoye damuwar su, zai yi wuya ka zauna dasu su ka gane  akwai damuwa a tare dasu  dan yana da irin zurfin cikin nan ne wanda idan ba shi yayi magana ba ba, ba zaka yi yarda ba.

    Sannan yana iya ɓoye abin a ranshi ba tare da ya gayawa kowa ba, yayi ta cin shi ba tare da kowa ya fahimci haka. Ko Fudail yana saurin d'ago shi ne ta hanyar tsananta binciken motsin shi. Wannan d'anyen halin  nashi ba karamin damun Sultanah FAZILATUL gani take kamar da gayya yake k'in faɗa mata, ita bata damu da kanta ba, koda wani zai iya gaya mishi. Amma fir yaki nuna damuwar shi sai dai ya rufe kanshi a daki yayi ta zaman kunci.

   Duk lokacin da ya shiga wannan yanayin, kowa yana shiga damuwa. Shi yasa basu son Ikram tayi nesa da shi. Kuma da alamu haka ce zata faru, tunda ya kasa furta kalmomin da ya dace, gashi nan danginta zasu tafi da ita.

   Juyawa yayi yana kallon waje. Kalmomin Abrad ne yake yawo a kunnen shi.
_Ko mijin da ta aura ba zai iya cewa shi ya dauke abinda kake hari ba! Ka tambaye ta ni na fara kwanciya da ita! Ni na bude idanun ta. Ni na nuna mata yadda namiji yaƙe_

Rintsa idanun shi yayi tare da jin bakin ciki dama da kullum, ji yaƙe kamar ya cire zuciyar shi ya huta, ga baki daya ya tsani kanshi da Abrad ina ma da yana da damar kashe Abrad tabbas sai ya kashe shi.

      "Sultan!" D'aga mishi hannu yayi tare da cewa.
"Bana son ganin shi."
"Amma wannan kuskure ne kake tafkawa, kana kuskure ne babba. Me yasa ba zaka Fahimci yarinyar nan ba? Me yasa ba zaka gane meke faruwa ba, Idan abinda kake zargi haka ne me yasa ba zaka ajiye shi a wani guri na daban ba, kake kuntatta mata da hanyar da bai dace ba! Gaskiya baka mata adalci ba. Shi kenan Allah yasa haka shine mafi alkhairi ga sakon daga Fada Amir Hood ya baka auren jikar shi. Amma sai nan da wata uku zuwa huɗu. Tunda sun sami labarin Ikram an mata bai ko da Amir Rahil. Allah ya tabbatar da alkhairi."

   Daga haka ya juya tare da barin d'akin, tunda ya fara magana bai juya ba, har sai da ya bar dakin sannan ya juya yana kallon kofar tabbas yana son ganinta. Yana son jin meye ta sauke shi. Yana son ganinta kome dare ba zai ya fita da rana tsaka ba, dole ya fita cikin dare ya isa gare ta.  Amma kuma meye makomar shi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da dauke kanshi kasa. Yana shafa kan shi tare da murmushi.

      ~~~
Kasa magana nayi ina kallon yadda Sultanah Amrah take kallon Nimrah, mayar da Nimrah baya nayi. Sannan na tsaya a gaban ta, nace.
"Kiyi hakuri Ummyn, bata da laifi. Kuma nasan ke me adalci ne."
Dakatar da ita tayi ta hanyar d'aga mata Hannun, tare da kura mata ido.
"Ban ce zan mata kome ba, amma ina tsoron abinda Mahaifiyarta tayi mana ne, domin ba lallai bane ta fahimci abinda ta aikata."

  "Insha Allah, Nimrah ba zata aikata kome ba, wallahi ki yarda dani bata da wannan tunanin a ranta ban dai sani ba, amma babu wannan karsashin a ranta."

       Haka nayi ta lallab'a Sultanah  Amrah kafin ta sake jiki, tana kallona daga lokaci zuwa lokaci. Musamman idan ta fahimci na shiga yanayin damuwa,.sai ta ce min.
"Kina son zama da Mehran ne?"
"A'a nafi son zama daku."
"A'a Ikram bamu shiga hakkin ki ba?"
"A'a" nace tare da mik'ewa zan bar dakin domin na tsani hirar da zata kawo min zancen Mehran. Shi yasa bana son zama koda su Izmah ne domin rabin hiran su akan shi suke min.

       A waje na hadu da Rahil ya kawo Abrad, dan haka ban yi mamaki ba, dan nasan yazo gaida Ummyn ne, har cikin gidan ya shiga suka gaisa, sannan suka shiga tattaunawa akai na, wanda duk hiran akan yadda ake shirya min tarb'a da bikin da za ayi mun ni da Rahli.

      Bai ce komai ba, amma daga yadda ya rasa nutsuwar shi har ya gama hiran da ita, muna zaune a harabar masaukin. Zama yayi a kusa dani tare da zuba min ido. Dauke kai na nayi daga gare shi sannan na cewa Rahil.
"Ina son zan sha madara! Amma bana son bayi su kawo min" na fada cikin sakakkiyar murya.

     Mikewa yayi tare da cewa.
"Zauna ki huta mata na, ba zata tab'a wahala ba. Domin ita din sarauniya ce zan kawo miki." Ya faɗa tare da nufar hanyar cikin gidan. Gyara zama nayi sannan na kalle shi.
"Kayi ƙoƙarin raba ni da Mehran, ka dasa mishi k'iyayyana. Sai dai kayi kuskuren mafi girma domin kuwa kayi abinda ba zai tab'a barin ka ba,  daga yanzun daga wannan lokacin ka fara boya, kayi ta gudu karka tsaya.

   Domin tsinin takobin shi sai ya huda kirjin ka. Ka fara gudu karka tsaya inda zai same ka. Nayi danasanin fadawa hannunka, domin babu wanda ya kashe ni da rayuwata sama da kai.

    Babu wanda ya lalata min rayuwa sama da kai. Sannan sauran da yarage kazo zaka lalata min su! Meye nayi maka da zafi? Meye na tsare maka da zafi haka? A sanina ka auri Kanwar Mahaifiyata toh meye kake son daga gare Ni? Amma masu iya magana since idan ajali yayi kira ko ba'a ciwo za aje."

  Daga haka na mike , rike hannuna yayi cikin zafin rai na tsinka mishi mari sannan na wuce abuna, duk akan idanun Amir Rahil ne, ina shiga ya zuba min ido.
"Meye ya haɗa ki dashi? Meye Matsalarki dashi? Yau zan dakatar da shi."
Gudun kar a kuma aikata abinda Ya faru yasani rike shi tare da kallon shi nace.
"Karka damu. Ya wuce na koya mishi yadda ake mutuntawa."

    Murmushi yayi tare da mika min madaran muka shiga zaga gidan, wai duk sabida kar na saka damuwa a raina.

         "Wai dama an miki baiko da wancan basamuden ne?" Kallon shi nayi tare da murmushi kafin nace mishi.o
"Eh amma kuma sawun giwa ya badda na Raƙumi ba" shima kallona yayi sannan yace.
"Ban gane ba?"

Murmushi nayi a karo na biyu, sannan nace mishi.
"Zaka gane mana." Dariya yayi sannan yace min.
"Amma kuma"
"Amma kuma me?" Na tambaye shi,
"Amma kamar kuna son juna da wancan basamuden?"
"Me ka gani?"
"Kin dawo min da tambayana"
"Kamar ya?"
"Kamar yadda na gani da idona"
"Lallai kayi kuskuren"
"Banyi kuskuren ba sai gaskiyar da na hango."
         Kasakai nayi ina kallon shi.kafin nace mishi.
"Babu wata soyayya a tsakanin mu, kawai kana ganin haka ne amma ban ga!"
"Da gaske baki son shi?" Ya tambaye ni, tsayawa nayi ina kallon shi. Tambayar da yayi min iya gaskiyar shi ce, amma kuma bana jin zan bashi amsar wannan tambayar dan haka na juya tare da barin shi a gurin, bakin ruwan da yake gudana a gurin na isa sannan na zauna tare da saka kafana ina nazarin maganar da muka yi da Rahil.  Zama yayi kusa dani, sannan yace min.

"Kiyi hakuri da sakaki surutu da nayi, sai dai kowani mutum me hankali da sanin ya kamata zai so ya ajiye irinki a gefen shi ko badan mu'amalar aure ba, ana bukatar mutum ya ajiye mace irinki na farko zaki bashi garkuwa, na biyu zaki bashi farin ciki a rayuwar shi, na uku kuma..." Murmushi yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Sai nan gaba zaki Fahimci abinda nake nufi"

Girgiza kai nayi sannan na juya tare da kallon cikin ruwan, ina jin babu dad'i domin Allah ya gani son Ƴan uwantaka nake mishi ba son kauna na aure ba, kuma ba zan iya bijirewa iyayen mu ba, tunda abinda suka yanke kenan. Amma ko ya ya bai kamata su zartas da hukuncin haka ba, idan suka yi dubi da ni bakuwa ce a cikin su.

        "Ikram ko na takura miki ne?" Ya tambaye ni cikin damuwa,
"A'a baka takura min ba, sai dai kana da hawa kai" na fada ina kallon shi,
"Toh kiyi hakuri! Ban san yadda zan nuna miki farin cikin da yake raina bane, amma kuma ina jin nutsuwa a zaman mu nan."ya faɗa cikin sanyin murya, duk sai ya bani tausayi, tabbas akwai matsala domin nasan dai ba zan hada maza biyu ba, amma kuma yadda Mehran yayi min ban ji dadi ba, dan haka na juya ina wasa da ruwan.

    Kasa hakuri yayi tare da zama kusadani kamar zai shige jikina, kallon shi nayi kafin nayi magana ya jingina kan shi akan kafadana, tare da riko hannun na, yana me matsawa a hankali.

    ...... Ya saba da ganinta tana sintiri dan haka yau da bai ganta ba, duk sai ya damu dukda ya ganta lokacin da ta fito dakin Sultanah, amma kuma zuciyar shi da ruhin shi suna begen ganinta, ƙwaƙwalwar shi tana yawan hango mishi.wasu abubuwan akanta, dan haka ya mike tare da sauya shiga izuwa kayan dakarun kasar ya fita daga gidan. Gidan bakin dake cikin masarautan ya nufa, tunda ya shigo ya hango yadda suke zaune da Abrad, sai yaji kamar ya koma, amma kuma ya fasa bayan ta gama gayawa Abrad magana yana mamakin yadda take iya sarrafa maza, dan yasan haka kawai ba magana me dad'i ta gayawa Abrad ba. Bayan fitar Abrad, ya hango suna magana da Rahil.

Sam Mehran bai dauki Rahil a wani namiji can ba, amma ganin yadda Rahil din yake ta damunta da surutu sai yaji tsoron kar abinda ta rasa a gare shi ta samu a gurin Rahil tunda soyayya ta tasa kuma idan ta samu a gurin Rahil shi bai da wani abun da zai gwada mata. Suna tafiya yana bin bayan su har gurin ruwan. Duk da bai san meye suke fada ba. Amma kuma tabbas abinda suke fada akwai muhimmanci dan haka ya nace sai yaji abinda suke fadi.

   Bayan ya matso ne yaji lokacin da Rahil yake gaya mata kowani namiji zai so samunta a rayuwar shi. Take hankalin shi ya tashi domin shi ya dace ya fahimci haka, amma baƙin kishin sa Ya saka shi kasa fahimtar kome akan haka. Yana kallon su har ya daura kanshi a kafad'ar ta, a lokacin sai da yaji kamar zuciyar shi zata dirko daga kirjin shi domin babu abinda ya tsana kamar yaga namiji a jikin ta. Yau gashi akan idanun shi wani yake jingina kanshi a kafad'arta. Ji yayi kwallar bakin ciki ya cika mishi ido. Dan haka ya juya tare. Da barin su a gurin tabbas bai da sa'a shi yasa ya rasata a karo na biyu,a da yana tunanin ya sami kanta ko bai gaya mata yana sonta ba, zata iya furta mishi ashe hasashen shi ce, ba tunaninta bane. Bai yarda da abinda Sultanah ta gaya mishi ba sai yanzun da ya gani da idon shi lallai yayi sake d'an zaki ya girma yayi kuskuren barinta ta rayu da wani, da tun lokacin ya kafa gwamnatin shi babu wanda ya isa ya rab'e ta, amma ya zauna sai tsanarta mata amfani da yake ji.

    Da wannan tunanin ya bar masaukin..
Haka kawai naji kamar Mehran ya zo har inda nake dan haka ba juya tare da kallon wani badakare yana tafiya. Haka kawai nake mishi kallon kamar Mehran ne, har na juya zan cigaba da wasa da ruwan sai kuma naji bari na kuma juyawa dan kamar yana kallona, koda na juya yana nan a tsaye. Sannan ya kasa  tafiyar shi.
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
39
Juyawa nayi sabida idanuna da suke min gizo, a hankali kwalla suka cika min ido. Tabbas Matsayin Mehran Babba ce a zuciyata ya, shi yasa na kasa Mantawa dashi.

        Saka hannun shi yayi tare da tare kwallar da take sauka akan fuskana.
"Waye ya tab'a min ke?" Murmushi nayi tare da goge kwallar nace mishi.
"Ina kewar Airan ce, kuma kaga dole nayi kuka domin itace kawai ta rage min gashi ba rasata ga kuma Allah ya bayyana min dangin mu."

"Ikram!" Ya ambaci sunana a hankali yana kallona, sannan yace min.
"Bana raba daya biyun kina tunanin Mehran ne"

Kura mishi ido nayi, da gaske haka ne amma kuma ɗan na karya ta abinda yake tunani a kaina yasani faɗin.
"Tir wannan wacce irin magana ce? Na rasa wanda zanyi tunanin shi sai mutumin da bai da wani amfani a rayuwa ta, kawai dai kana zargina ne, amma idan ba haka ba me zai sani tunanin Mehran."

Cikin fushi na mike zan bar gurin, riko hannuna yayi tare da zaunar dani.
"Kiyi hakuri!" Ya faɗa min a sanyayye, sannan yace min.
"Dole naji babu dad'i, babu namijin da zai so yana yana tare da mace amma zuciyar ta yana ga wani mutum na daban, Kinga kuwa zai cigaba da ganin haka kamar rashin adalci ne."

   Tabbas ya bani haushi amma kuma yana da kyau na tausaya mishi domin gabaki daya ya addabi rayuwata da naci, dan haka na sassauta fushina nayi sannan na zauna ina kallon shi.
"Ke kamar Uwace a gare ni, kin bani kwarin gwiwar da na rasa akan me zaki yi fushi da Ni? Bayan ke bani da wanda zan ƙalla nace shi Masoyina ne. Amma ke kuma na ambace ki da kalmar me tsada da girma,don Allah karki yi fushi da d'an uwan ki."

                Na rasa me zance domin duk wata kalmar da zai yi amfani da ita,rudurduga min zuciya take, duk wata harafin da zai ambata kamar kunawa zuciyata huta yake, gabaki daya sai naji ba zan iya ganin shi cikin rashin nutsuwa ba, zan amshi auren shi duk da ina da zab'i amma kuma shi din zab'in kakanni na ne, hannuna yakai  fuskar shi sannan yana faɗin..
"Ki dube ni da idanun rahama, karki juyawa tayina baya"

   Hawayen da nake b'oyewa ne suna sauko a hankali tare da kura mishi ido, tabbas kome ya kare min dan haka na rike hannun shi tare da cewa.
"Ba zan tab'a juyawa tayin ka baya ba, ina tare da kai kuma zan zauna da kai." Ina gama fadar haka na mike zan bar gurin. Shima mikewa yayi sannan ya saka hannun shi dukka biyu ya rungume ni. Yana shafa bayana. Mehran yana kallon mu. Juyawa yayi tare da barin gidan baki daya. Idan ka ganshi zaka dauka bai da lafiya ne. Hamas shiga Harami ya nemi faduwa, tare da jin wani mugun sanyi ya shige tare da zazzaɓi me mugun zafi.

      Fudail da yaga fitar shi, shine ya fara ganin shi san yana harabar gidan. Ya rike shi zuwa cikin gidan.
"Fudail kirjina zai fashe."
"Sannun Sultan! Ina kaje haka? Ko kamanta kana da ciwon zuciya ne? Gashi a karon farko zaka kashe kanka."

       Ina kasa magana yayi sai juya kai yake, yana jin kamar kirjin zata fashe, a dakin shi aka kwantar dashi.
"Fudail, Ikram" ya faɗa a sanyayye dukda idanun shi a rufe suke amma bai hana shi. Kiran sunan Ikram ba, gabaki daya ya zauce baya gane kome sai sunan Ikram,har akayi sallah magarib da isha Mehran baya cikin hankalin shi. Matan da aka zab'e mishi kuwa kasa hakuri suka yi. Sai da suka magantu.

    Amma haka bai hana Mehran kiran Ikram ba, tun ana zata zafin zazzaɓi ne har suka gane cewa ita din yake bukata, gashi dare yayi sosai. Dan haka suka yi ta fama dashi, daga karshe dai Sultanah da Fudail suka fita har gidan bakin.

       ...... Ina kwance banyi barci ba amma kuma zuciyata babu dad'i dan haka na tashi zaune, naja labulen gadon ina kallon su Nimrah da Izmah, da suke kwance can gefe guda. Kallon su nayi naga suna barcin su. Wato sai kana da nutsuwa kake samun damar barci idan baka da shi kuwa. Kai da barci har abada.

      Buga kofar dakin mu akayi na sauka a gadon sannan na bude tare da kallon Ummyn da Sultanah Fazilatul nisa.
"Ikram! Don Allah zoki taimake mu. Mehran zai mutu." Ban tab'a sanin akwai rudewar da zata sani niman fita daga cikin gidan babu suturar Arziki a jikina ba sai da aka gaya min Mehran zai mutu. Riko hannuna Rahil yayi cikin dakewa sannan yace min.
"Baki da lafiya ne? Dubi yadda zaki fita? Koma ki shirya ina jiranki!"

         Haka nayi kamar yadda yace min, tare muka tafi har da wasu dakarun. Tunda muka shiga cikin harabar gidan, Rahil ya riko hannuna.
"Karki manta akwai alkawarina akanki. Dan haka kiyi kokarin kare girman alkawari."

         Kallon shi nayi domin na kasa Fahimtar me yake nufi, a lokaci guda naji ya fice min a raina. Hawayen da ban san yaushe ya sauko min ba.
"Kasan girman shi a cikin idanuna? Kasan yadda nake  jin shi a raina? Da kasan yadda nake kokarin kyautata mishi ba zaka tab'a sanya min sharadi dan zan ganshi. Ka tsaya a matsayin ka na wanda aka mana alkawari karka tinzira zuciyata izuwa aikata abinda ba zan iya daukar shi ba. Sultan MEHRAN wani shashine na rayuwata. Don Allah karka raba abinda yake a haɗe." Ina gaya mishi haka na shige cikin gidan.

  Na sami Kwarkwarorin shi a bakin kofar, suka gani na suka shiga matsa min a hanyar. Shiga dakin nayi na same shi rike da kirjin shi. "Ikram! Ku kawo min ita" ina shiga matan shi suna shigowa. Tsayawa nayi a bakin gadon ina kallon yadda yake dafe kirjin shi. A hankali na zauna a bakin gadon. Na kai hannuna tare da riko hannun shi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da ƙamƙame ni.

   "Ikram!" Ya kira suna na idanun shi a rufe.
"Na'am Sultan Mehran!" Bude idanun shi yayi sannan yace min.
"Mehran zaki ce, ki ce min Mehran."
"Meke damun ka?" Hannu na yakai bakin shi ya sumbata, sannan yace min.
"Kece ciwo na. Kece magani na" ya fadi haka, kallon sauran matan Fudail da Sultanah suka yi tare da musu alamar su fita.
Fuuuu suka fita daga dakin, ina rike da hannun Mehran, tashi yayi tare da dawowa kan cinya ta, yana sauke ajiyar zuciya.
"Karki tafi! Kunne na yana min kai-kayi, ko zaki susa min"

   Shafa kan shi nayi tare da jin saukar kwalla daga idanun shi akan cinyata.
"Kayi hakuri! Ni zan tafi gobe Insha Allah..sannan ka rungumi matan da aka baka, Insha Allah zaka sami wacce zata fini tsayin daka."

"A wani matsayi kika ajiye Ni?" Ya tambaye ni tare da damke hannuna. Shafa kanshi nayi a hankali tare da jin tashin hankalin a raina.
"Mehran! Kai kamar Uba ne a gare ni, bana son na ganka cikin tashin hankali da damuwa, Mehran ina zaune ne domin kai bayan haka bani da hurumin zama a cikin Masarautan SAMAIND, amma kuma sai naji kunyar abinda ka aikata min. Mehran na tawo da niyyar daukar fansa akan abinda kasa aka aikawa Numan."

    D'ago kai yayi tare da kallona.
_Me yasa ba zaki gane bani da hannun cikin kisar gilla da aka yiwa Mijinki? Me yasa ba zaki gane ban san kome akan kashe shi ba! Nayi kuskuren furta sai na kashe shi amma bani na aikata ba_

      Shiru nayi tare da janye idanuna daga cikin na shi, sannan na cigaba da cewa.
"Haka bai sani ajiye makamina ba, na amshi aikin da ka sani ba. Mehran sai da na gama tsalleke duk wani mataki da iyaka, amma ka juya min

Please Login or Register in order to submit comment