Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawowa*
D'ago kai na yayi tare da kallon cikin idanuna, sannan ya hura min iskar bakin shi me dauke da kanshi y'ay'an itacce.

*Me yasa ba zaki Fahimci abinda nake tare da shi ba? Me yasa ba zaki gane girman ki a zuciyata ba? Me yasa kike wahalar da zuciyar da bata dauke da sharri sai Alkhairi?*

     Janye hannuna nayi daga gare shi sannan na dauke kaina zan fita, yayi maza ya riko hannuna, ya juyar dani, bayana yana kwance a kirjin shi, hannun shi ya sarkafe da hannuna ya manna akan cikina, tare da riko daya hannun ya saka akan cikina ya zarge ni a kirjin shi. Kanshi a bisa wuyana, yana sauke ajiyar zuciya akai akai.
_Na tsane ka! Bana son ganinka? Akan idanuna kace bani da daraja! Sannan ka kashe min Mijina! Mehran nice ajalinka, mutuwarka a tafin hannuna yake_

      Na karshe da shashekar kuka, tare da kokarin fita a jikin shi.
"Ki gaya min meye laifina?"

Cikin fushi na kwace kaina, tare da juyawa ina kallon shi.
"Karka kuma takowa inda nake! Me yasa ba zaka gane bana son ganinka a rayuwata ba? Kai abin so ne? Waye ya gaya maka zan tab'a kaunar ka? Toh ko maza sun kare gwara na koma ga Allah babu mijin aure ka fita a rayuwata nace!!!"
Na daka mishi tsawa, ina kuka tare da zuɓewa akan gwiwata, ina kuka.
Shiru yayi sannan ya durkusa a gabana, ya riko hannuna..sannan ya kalle ni cikin damuwa kafin yace min.
"Gashi kiyi yadda kike so dani! Zanyi alfahari idan na mutu a hannun ki, zanyi farin ciki idan mutuwa ta ya zame miki karshen matsalarki! Amma ban miki alƙawarin koda ina raye zan daina bibiyarki ba, wannan shine alkawari na dake"

   Kura Mishi ido nayi, na rasa gane wani irin mutum ne shi da bai damu da kanshi ba, sai dai ya kuntatta maka, banda kuntattawa me yasa zai kore Fudail ya kuma ce min na kashe shi salon yaja min magana..

*200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

28
     Kasa jure idanun shi nayi a cikin nawa, na kai mishi duka a kirjin shi, muryana yana rawa.
"Me yasa?"
Murmushi yayi sannan yace kai bakin shi saman kunne na, ya d'an kama da hakorin shi, rike rigar shi nayi tare da sauke ajiyar zuciya. Sake lasar kasan kunnen yayi na k'amk'ame shi tare da jin wani irin abu yana yawo a jikina kamar an watsa min tsutsa, kark'ada min harshen shi yayi a cikin kunne na, ji nayi kamar zan zube ƙasa, ya kuma rike ni sosai,
Mehran Mugu ne, ba fada dashi bane matsalar.

     Kwana mita, domin a iya haka ya labtar da gangan jikina, ya kuma sani kuka babu fada babu zagi, hancin shi ya shiga gogawa wuyana, yana magana kasar makoshinsa.
"Ba fada zanyi dake ba, kuma ba zan hana ki faɗa dani ba, sai dai ki sani a shirye nake na bawa zuciyarki horon yaki akai na, a shirye nake nayi ta sanya ki kuka akan abinda ba zaki iya bujirewa ba.  Tsaf na shirya yaki da zuciyarki har sai ta nutsu akan Abu daya, sannan zan kyale ki. Mara jin magana kawai." Ya fadi haka tare da hura min iskar bakin shi, wani irin kuka ne ya kwace min domin kafaffuna rawa suke, a hankali ya juya ni tare da saka harshen shi akan fuskana,

  Yana lashe hawayen da suke zuba, tare da cewa.
"Ni zan saka ki kuka! Kuma ni zan lashe kukan nawa, duk abinda zai fito daga gare ki nawa ne!"
"Kyale ni, wallahi babu abinda zai zama naka ,Ni ba kara bace nice ajalin ka" na fada ina kuka.
"Bakin ki yana yawan magana, kuma ina tsoron maganar karta zame miki matsala, harshen ki kamaninki, don Allah ki rage yawan fadar haka. Domin ke baiwa tace."

  Ture hannun shi nayi tare da kallon shi, kuka nake sosai tare da niman guri na zauna, murmushi yake, cikin jin Dadi. Allah ya gani yana son mace me jarumta, yana kuma son ganin mace tana kuka, cikin damuwa kara mata kyau yake balle Ikram da suka shekara uku basu hadu ba, zama yayi a kusa da ita, tare da matse ta a a jikin itaccen da aka yi gwafa da gidan.

         Hannun shi ya saka tare da riko hannun na, yana kallon yadda nake kuka. Tare da kallon yadda nake shashekar kuka. Ita take kukan amma jin hawayen ta yake kamar narkakken  dalma ake diga mishi akan zuciyar shi.

             Kai hannu na ya kai kan kirjin shi, yana kallon yadda na sunkuyar da kaina, tare da kokarin zare hannun daga kirjin shi. Matso dani yayi jikin shi. Tare da d'ago kai na, yana goge min kwallar fuskana.
"Me kike so?"

     Kallon shi nayi tare da kasa cewa kome. Bana iya kallon cikin idanun shi na tsawon mintina, lumshe idanun nayi kwalla suka kuma zubowa.
"Qurratulain!" Ya ambaci sunan daga kasar makoshinsa, yana ji kamar za a kwace mishi ita, gani yake kamar duk wani dakika na duniya kara nesanta shi ake da ita.
"Me kike bukata?"
"So nake na kashe ka" na bashi amsa ina kallon cikin idanun shi. Murmushi me zubin dariya yake yana kallo na, yana shafa fuska ta, tare da kai kanshi saman hancina.
"Har yanzun baki gaya min me kike bukata ba?"
"Na tsane ka"
"Anya kuwa?"
"Bana son ganinka"
"Da gaske?"

    Kokarin ture fuskar shi nayi tare da sake mishi wata irin siririn kuka..
"Yau nayi nasarar saka Jarumar mata kuka ko?"
Mikewa yayi tare da kallon yadda take kuka, murmushi yayi sannan yace mata.
"Ban miki alqawarin zan rabu dake ba, domin zanta bibiyar ƙi" daga haka ya juya barni a gurin ina kuka, wanda idan da zaka tambaye ni me yayi min wallahi ban sani ba, kawai dai ina tare dashi kuma ban san lokacin da nake kuka ba. Hannun shi suna  zuba cikin rigar shi. Fidda su yayi tare da shafa fuskar shi zuwa kan shi yana lashe bakin shi, sannan ya juya bai kuma magana ba, ya bar gidan. Sai da ya fita na sami kaina da yin shiru, ina sauke ajiyar zuciya.

   Wato idan kana niman karfen kafa, ka sami Mehran ka gama kome domin lokaci guda ya zuba min wasu irin matakan tsaro, tare da sawa aka bibiyar kome na, bana fita Izmah da Nimra suke kome, ni ya hanani fita, domin da zaran na fito masu tsaron zasu taso min na koma cikin gidan. Akwai wani bikin da ake a garin SAMAIND wato bikin fitilar wuta, dan haka naso na shiga kasuwa na sayi abinda ake hada abin, amma wad'ancan masu kama da bishiyar su, hana ni fita. Kura musu ido nayi tare da cewa.
"Zan karya kasusuwan ku! Dan haka ku barni nayi tafiya na"
"Idan zaki shekara kina karya kasusuwan mu, ba zamu karya dokar Sultan Mehran ba, mu an kan mishi biyayya bamu damu da rayuwar mu ba"

       Jikina ne yayi masifar sanyi, dan haka na juya tare da zama a kofar dakin mu.
"Ikram!" Juyawa nayi na kalli Izmah,
Tasowa tayi tare da zama a kusadani.
"Ban tab'a ganin mutum me kirki irinki ba, zuciyarki me kyau ne."
"Bar min kewaye kewaye, fadi abin da yake ranki"

     "Sultan MEHRAN!"
"Ai dama nasani" na bude baki zan yi magana kenan Fudail ya shigo da kayan a hannun shi, ya mika mata. Tare da juya kai yana niman Nimrah.
"Wannan fa?"
Murmushi yayi sannan ya kalle ni yace.
"Inji Sultan Mehran!, Wai ku saka kayan zai zo an jima da dare." Yana raba idanun shi, akan kofar mu.
"Ina Nimrah?"
"Tana ciki kuma ai taji ka,, ka mikawa SULTAN Mehran godiya kace mishi Ikram ta amsa cikin mutuntawa. Mun gode"

    Murmushi yayi yana kallon yadda na b'ata rai, kamar bani ba.
"Ikram"
"Me zan maka? Ka dauki kayan tsiyar shi ka maida mishi, jinin mijina ya fi karfin tunanin shi, kar ya kuma kawo min kayan haukar s...."
Had'iye maganar nayi tare da dauke kai na, sabida yadda yake kallona kasa kasa.
"Sultan MEHRAN. Mun gode Allah ya kara maka bud'i da nisan kwana, Ubangiji yayi maka jagoranci akan duk wani abinda ka saka a gaba, Allah ya baka mace ta gari!" Kamar wacce aka watsa min ruwan zafi haka naji Addu'ar Nimrah. Tsaki naja musu sannan na mike zan bar gurin. Ban san ya akayi ba sai ji nayi kamar an ja kafana. Na tafi zan fad'i. Cikin abinda bai kai dakika biyu ba, naji ni a jikin shi tare da d'ago kai muka kalli juna, wani irin tsume fuska yayi wanda ya saka duk suka bar gida, janye jikina nayi tare da b'ata rai.
"Me yasa kake son shige min?"
Tab'e baki yayi tare da kauda kanshi yana wani shan kamshi, kamar wani wanda ya ga abin da baya so.

"Me yasa ba zaka kyale Ni ba?" Na fada da karfi, kauda kanshi yayi tare da kallon kofar shiga gidan, yaga babu kowa. A hankali ya sake ni sannan ya ture ni har jikin kofar shiga dakin.
"Mehran!" Na fada muryana yana rawa, na kira sunan shi. Bakina ya kama, tare da mishi wani irin azazzaben sumbatar da tasani jin kwalla ya zubo min, sabida yadda yake abin wallahi babu tsoron Allah a ranshi. Jin baki na kamar ba ajikina yake ba. Domin kuka tsotsar shi yake yana kuma taune bakina, bai kuma ji a ranshi haka da yake min kuskure ba, domin har harshe na zafi yake min da rad'ad'i, hannun shi kuwa bai fasa yawo dashi a jikina ba, domin jan rigana yake har zuwa sama.

             Ban tab'a ganin shi a irin wannan yanayin ba, domin da ban mamaki abun yake, Mehran ya tsotse bakina lebbe na kuwa har wani yaji yaji yake min, hannun shi da ya tura cikin rigana, yana kokarin cusa hannun shi cikin daurin kirjina, rike hannun shi nayi, ina girgiza kai na, tare da zubda kwalla.  Sai da yaji ina wani irin gurnanin kuka ta cikin wuyana da bakina ya janye bakin shi daga nawa, yana murmushin mugunta da jin dadi a ranshi. Lashe lebben shi yayi kamar wanda aka lasa mishi zuma a bakin. Ya kuma kallona sannan ya juya tare da ɗaukar kayan a inda Izmah ta ajiye, ya mika min.

     "A cikin kasata, a da'irar birnina a cikin garina a cikin farfajiyar mulkina ke har kin isa ki kirani kayan tsiyata?"  Murmushi yayi sannan ya juya har ya isa bakin kofar.
"Bayan sallah isha, zan zo kuma idan." Cizon lebben shi yayi sannan ya sake murmushi, sannan yace.
"Kina sanya Ni magantuwa" sannan ya juya abin shi yabar gidan.

   Zamewa nayi daga tsaye na zauna a kasa, duk zaratan da nake haduwa dasu. Ban tab'a haduwa da makiri, miskili irin Mehran ba, dan mugunta ya gama cinye min bakina, tare da sakani kuka kamar zan shiɗe.

              Shigowar su Izmah suka kalli bakina da yayi ja tare da d'an kumbura.
"Laaa! Amma Sultan Mehran ya iya soyayya, dubi yadda ya cinye miki baki, kai jama'a nima ina tausayin kaina, domin ina kewar Firooz." Ta faɗa tana sake wata irin iska. Murmushi Nimrah tayi tare da gyara zaman gashinta  sannan ta shige dakin.

           
               Kamar zan sake ihu tare da zuba kwalla, ina kallon Izmah sai dariya take, tana kallona tare da cewa.
"Wallahi Sultan Mehran ya miki kankati, domin kuwa shi daya ne yake iya saki kuka tare da ya zane ki ko ya miki kome ba, gashi nan kina kuka wiwi."

            Haka ta gama min wulaqanci, sannan ta shiga magana irinta masu hankali.
"Bilqisul Ikram! Maganar gaskiya ki rage kaifin kalaman ki, domin kuwa zata kai ki ta baro ku, kina gaya mishi maganar da yayi miki, karki manta shugaba ne fa idan ya tsaya a filin yaki dakaru kimananin miliyoyin mutane suke take mishi baya. Ikram Mehran ba kashin yarwa bane, Mehran ba haka kawai yake gabanki ba, Ikram baki da kome a kirjin ki, babu nono baki da abinda lafiyayyen namiji zai ganki yaji a ranshi yaga mace.

    Ikram ki duba yadda rayuwa take tafiya dake, kuma a cikin haka kika yi ta kai mishi farmaki bai tsaya ya duba meye ke tafe dake, ya kalle ki da kyakyawan niyya yana barin fadar shi ya fito sabida ke meye illar shi? Meye laifin shi? Wallahi na rasa gane miki na rasa fahimtar meke damun ki, Ikram idan rayuwar Mehran ne fansar jinin Noman ki tafi ki kashe shi ki huta, wannan wani irin k'iyayya kike mishi?

   Wani irin k'iyayya ne haka ya shiga tsakanin ku? Me yasa baki tuna abinda yayi miki abaya ba kike nuna mishi gundarin k'iyayyar ko dan ganin ya tura a kashe noman ne? Ni kuwa dan Sultan Mehran yace min kar nabi wani wanda nake so zan hakura domin shi din Shugabana ne, kuma Uban gidana ne shi.

    Bana jin dan ya kashe shi tsane shi, idan duniya da gaskiya kamata yayi ki bincike waye Mehran meye Mehran yake yi, me ya faru dashi bayan rabuwar ku baki yi ba, shine faidar dawowarki, kina tsanar Mehran ne kawai Amma duk halin da yake ciki sabida ke ce, Ya hakura da mulkin shi sabida ke, domin da suka ce zasu dakatar da shi idan wani ne kin amincewa zai yi kuma ya nuna musu karfin mulki.

   Amma sai ya juyawa mulki baya, a tsawon shekarun shi kamata yayi ace yana da matar da zata dauke mishi bukatar shi da kewar shi, sai gashi yayi fatali da matan da ake kawo mishi, duk shekara watsi yake da mutane haka kawai ba dan kome ba sai dan yana jiranki ki dawo gare shi."
Kasa da murya tayi tare da rarrafawa gabana ta riƙe hannuna tana kallon fuskana sanan tace min.
"Zunzurutun yana da muradinki ya hana a fitar da kin auri wani namiji. Meye kike bukata yayi miki? Meye kike so yayi miki? Meye nufinki akan shi? Mehran mutum ne guda ba b'ari ba, mutum ne da ya amsa sunan shi.

A shekarun shi kamata yayi ace yana da Kwarkwarorin babu adadi amma yana zaune domin ra'ayin kanshi meye nufin shi da kawo wancan kayan?  Saboda macen da take da daraja ake bawa, amma gabaki daya tunanin ki baya baki lissafin da ya dace kin tsane shi Allah ya baki sa'a da lafiya ki ta tsanar shi. Ba zaki gane illar abinda kike ba sai ranar da kika yanke shawarar da har ki koma ga Allah ba zaki daina kuka ba shine idanunki zai bude.."
*200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

29
"Kyaleta Izmah! Bata ga ni'imar da Allah yayi mata bane, shi yasa take butulce mishi da tasan tarin baiwar da Allah yayi mata da hikimar da ya tsara ba zata tsaya tana musguna mishi ba. Domin na gama nazarin abinda yake tsakanin su ban ga laifin shi ba, sai ma tarin girmama al'amarin ta da yake yi amma baiwar Allah nan ta rintsa idanun ta.

            Meye kike bukata a duniya? Mehran yayi ya kuma amshi hukuncin da kika aikata laifukan da ya dace naki ne amma shi ya amshi laifin akanki, Ikram meye matsalar ki da k'iyayyar da kike mishi, na rasa gane meye ya miki da zafi haka, wallahi ko ni da Mahaifiyata ta miki laifi baki min tsanar da kikewa Mehran. QpAmma kin rufe idanunki a madadin amshi kiran shi kin zauna kina juya halin ki a yadda shi kanshi dole wata rana ya gundura da halinki tir da ma ace Mahaifiyata ce ta haife ki sai nace kin sha mugun hali a nono ne ba a gurin kowa ba, amma abun ai jini yake bi, shi yasa kika dauki kad'an a halin ta."

       Ina jin su ina kuma jin yadda suka sani a gaba da gaya min magana, sabon tsanar shi nake ji a raina. Mehran ya saba kwace min farin ciki na, yau ma ya kwace min kawayena Insha Allah yau zamu yita ya kare ya rabu dani yayi tafiyar shi nagaji da halin shi, duk abinda na samu na farin ciki sai Mehran ya rabani dashi ya saka Ni kuka ya saka zuciyata kunci bai ishe shi ba, yau kawayena da na rabo su da ahalin su. Sune suka juya min baya.

       Kura musu ido nayi tare da sauke kai na kasa, kwalla ne ya zuba min daga idanuna. A hankali na d'ago kai na, zan yi magana kuka ne ya kwace min tare da shashekar kuka, ina jin kamar na had'iye zuciyata na huta.
"Ku koma gurin Mehran!" Na fada musu a tsawa ce, ina share kwalla da take sauka min, ma tsani mutumin nan iya karshen rayuwata. Kuma wallahi ba zan tab'a kyale shi ba sai na ga bayan shi. Haka na shige dakin ba kyale su baki hangame da mamakina.

       ~~~
Merocco.
Ga baki daya tun da aka nime Ikram aka rasa ya koma kamar karamin mahaukaci, yanzun ma a gabanta Sultan Mu'allim yake. Tare da narke Mishi.

"Rahil har yanzun bamu da labarin ta dan ko har aika Sultanah Amrah tayi daga Askandariya, amma babu wani labarin da aka samu. Kayi hakuri ka kara hakuri insha Allah tana bayyana zan aura maka ita."

     Tun bayan tafiyar ta Sultanah Amrah tazo har masarautan tare da tambayar bayanin Ikram, suma suka tabbatar tabbas tazo amma kuma ai nata zauna Kamar yadda suka so ba, dan basu sami labarin ta ba sai bayan tafiyar ta, dan haka suma suke nimanta. Sannan suka daukarwa juna alkawarin matukar aka sami labarin ta, daga kowacce gefe su tabbatar da an tuntube juna. Toh har yanzun dai haka ake ta bincike akanta kuma babu labarin ta.

   Takai har niman masana kuma gogaggun masu iya zanen aka yi tare da zama hotonta ko za a dace. Dan haka aka yi ta rabawa kasuwanni da wasu guraren domin niman ta.

Idanun shi cike da kwalla yacewa SULTAN Mu'allim.
"Don Allah ka taimaki rayuwata, duk duniya bani son wata mace sai Ikram, don ALLAH Sultan ka taimake ni akanta kar na rasa rayuwata"

Tausayin jikan nashi da kuma abinda yaron yake ji yasa shi rike hannun shi, cikin tabbatar da abinda yake nufi yace mishi.
"Ni nake da iko da kai, haka itama ina da iko da ita, dukkan ku a karkashina kuke, don haka babu wanda zai shure dokana da sanin shi, iyayen ku basu shure doka na ba, ku y'ay'an su baku isa ku shure abinda na kafa ba."

   Sake karya wuyar shi yayi tare da kallon shi yace mishi.
"Allah ya taimake ka, nasan ni ina jin tsoron kar ta haɗu da wani namijin ne, ina gudun karta hadu da wani da zai yi nasarar nisanta ta dani ne, Sultan don Allah idan aka ji labarin inda take a barni na wakilce ku, domin na dawo da ita, anan nake son kafa kai na, domin bana son tazo ana dolanta mata ni."
Ya faɗa tare da zubda kwalla, sabida Allah ya gani yana mugun kaunar Ikram, kuma duk rintsi duk wuya sai ya mallake ta, nasiha Sultan Mu'allim yayi mishi sannan ya shafa kanshi ya tabbatar mishi da cewa, yana taya shi da addu'a, sannan Insha Allah Ikram tashi ce.
     ~~~
A wannan lokacin Sultan Abrad ya nime wata yar gwamnar yankin shi me suna Aseelah, kyakkyawar mace ce. Na gaban kwantancen, tunda ya hadu da ita yaji ya manta da Ikram. Dan haka suka baje amarcin su na wani lokaci. Yanzun ya manta da wata Ikram,.sai ma hidimar gaban shi yake da cusa Kanwar shi izuwa Daular su Mehran.

   Dan yaci alwashin ko bai sami damar kashe Mehran ba, sai ya shiga cikin mulkin kasar yayi kane kane, yadda zai ji dadin kuntattawa Mehran tare da takalar shi rigima idan yayi magana ya tinzara, sauran yankunan jazziratul Arab su yaki Mehran. Domin yayi alƙawarin sai ya dagula al'amurran Mehran.

     Dan haka a sauran kwanakin da suka rage zab'en matan sarki ya fara shirya Kanwar shi tare da nuna mata hikimar da zata yi na girki,  tare da kiran manyan masu girki na kasan ana koya mata, duk wani nau'in girki da nuna mata yadda ake girmama al'amarin sarautar SAMAIND.

    "Sultanah!" Murmushi tayi domin tana jin dadin yadda suka fara kiranta da Sultana. Dan gani take dole itace zata lashe gasar. Kuma tayi tafiyar bazata da zuciyar shi. Murmushi tayi sannan tace musu.
"Ina jinki Rubina!" Cikin jin dadi baiwarta Rubina tace.
"Sultanah a yadda zab'en yake matukar kika samu nasarar zama matar da zai aura za a killace ki na wasu kwanaki a gama niman bayanin asalinki, sannan zaki kasance me lura da al'amuran Sultan har kwanakin da zaki yi a killace su cika.

   Sannan ba a son a wannan tsakanin ki kasance dashi ta shamfida, sabida idan kika kasance matar shi ba zai yi daukin ki ba, an fison ki hakura da shi wa Kwarkwarorin da zasu shiga zab'en. Sannan a cikin wannan yanayin babu ruwanki da shiga al'amuran gidan, babu ruwanki da shiga al'amuran  Kwarkwarorin shi, babu ruwan ki da duk abinda zai yi da Kwarkwarorin shi, har ranar bikin ku ya kama a dawo dake masarautan shi."

       "Wannan dokar fa? Tab haka zan hakura da mijin da zan aura gaskiya babu wanda ya isa ya shiga tsakanin mu, domin wallahi ba zan yarda ba." Ta faɗa cikin fada da gatsine, sunkuyar da kai duk bayin suka yi tare da zare idanu.
"Allah ya gani ba zan iya ba, wallahi ba zan iya ganin shi da mace na kasa hakuri ba."

"Sultanah daga ranar da kika zama matar da zai aura, toh zaki iya sauya kundin tarihin masarautan, sannan zaki iya tafiya da ra'ayin kowa ko kuma yi fatali da ra'ayin su, ki kafa naki ra'ayin."
"Kai Rubina idan na zama Sultanah uwar magajin sarauta zan yantaki har na baki me bani shawara na hannun dama na," ta faɗa tare da sake murmushin jin dadi.
"Kai Nagode Sultanah Uwar Magajin sarauta." Murmushi tayi sannan tace mata.
"Karki damu daga yau kuna da damar yin abinda kuke so, har mu tafi SAMAIND."

"Sultanah mun gode! Azizatul Nissah mun gode ainun." Haka tayi ta murna sannan tace mata.
"Toh bayan nan dole zaki daura damara da sauran matan, domin zasu ta kawo miki hari, tare da makirci kala kala, da munafunci. Idan har haka ne toh ba makawa zaki zama me, juyawa tayi tare da kallon sauran bayin sannan tace mata, Sultanah bani kunnen ki" nan suka rad'a munafuncin su , sannan suka kalli juna.

   Murmushi suka yi wanda zai nuna maka akwai wata a ƙasa, kafin suka ci-gaba da tattaunawa.

    ~~~
Ina kwance suka gama shiryawa, tare da dauke kaina akan su, dan naga ba karamin dukiya bane a jikin kayan, musamman rigunan aka dinke su da duwatsu lu'lu'u, sai azurfa da aka makala a wuyar hannun rigar, tare da saka musu digon karfe zinari. Sunyi kyau. Lumshe idanuna nayi amma kayan ne akan idanuna. Tsaki naja, sannan na juya baya abuna.

        "Ikram! Ki tashi ki shirya mana." Inji Izmah,
"Kar wata ta min magana." Na fada a fusace, murmushi suka yi kafin suka shirya dan tunda nayi sallah isha nake zaune a gurin, kuma babban damuwar su na tashi na shirya. Amma fir naki. Juya baya nayi abinda daga kallon da suke min na rashin mutunci. Ya jima a bakin kofar shiga cikin dakin, murmushi sukayi tare da d'an dukawa suka gaishe shi, sannan suka daga d'akin. Kamshin turaren shi ne ya fahimtar dani yana cikin ɗakin.

          A hankali ya zare alkyabar shi ya ajiye a jikin

Please Login or Register in order to submit comment