Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muka yi ta zaga gidajen baki har Allah ya nufa muka isa wajen gari.

           A jikin wata itacce na tsaya ina maida numfashin da ya taso min, fada suke na tare da jima junan su ciwo.  Walkiyar da aka yi ne ya sakani ganin yankar da Noman yayi mishi a hannun shi,  shi kuma Noman a gefen kirjin shi, jini na zuba musu, duk da shi Mehran yana tsaye ba tare da ko layi kamar Noman da yayi taurin kai yana son kare martabar SOYAYYAR SHI.
  
Shiga tsakiyar su nayi bayan sun kawowa juna mummunan sara.
"Ya isa! Noman karka manta ina tare da kai, ina sonka amma bayana nufin zan Barka ka hada dantse da Sultan MEHRAN ba, shi din kamar Yaya ne a gare ni, kuma Uban gidana ne."

Juyawa nayi tare da kallon Mehran, na sunkuyar da kaina ba.
"Kayi hakuri! Yayi laifi da ya tako har sansanin ka domin farauta. Sai dai kuma kasan cewa, idan me guri yazo dole me taburma ya nad'e, kayi hakuri."

"Ba zan yi hakuri ba, sai dai ki sallame shi, idan ba haka ba ajalin shine ya kawo shi daulata."
Yana gama fadar haka ya juya tare da barin gurin, kallon Mehran nayi tare da juyawa na isa gurin da Noman yake kokarin faduwa, na rungumo shi, tare da sake kuka me cin rai ina cewa.
"Me yasa ka fara tinkarar shi da yaki? Waye ya gaya maka cewa shi din gama garin mayaki ne? A cikin wannan lardin Noman don Allah karka kuma wannan kasadar."

"Ba zan tab'a bar mishi ke ba ba, wallahi ba zan Barki ba, wallahi ko mutuwa zanyi sai na tafi dake, dan haka ki koma ki shirya akan idon shi zan tafi dake, wannan shine magana ta"

   *Toh fa 🤔☹️ inda ba kasa nan ake gardaman kokuwa*
```Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```

#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
     
Page 39
      _Daga wannan Pagen din insha Allah wanda zai zo shine karshe!_

          Taimaka mishi nayi ya mike tare da kai shi dakin shi, muka shiga bashi taimakon gaggawa, saboda yankan da aka mishi, har jinin ya tsaya, sannan na lalle shi tare da Mik'ewa zan fita yace min.
"Me yasa min fuskar ki?"
Shafawa nayi sannan na ce mishi.
"Babu kome!"
Gyada kai yayi sannan ya koma tare da kwanciya da kanshi yana fadin.
"Kar ki manta da tafiyar mu,"
"Insha Allah! Sai da safe!"
Na juya tare da ficewa daga dakin, ina fitowa waje na hango Fudail.

    A hankali na karasa gare shi, sannan muka nufi cikin garin.
"Me yasa ba zaki iya tafiya ba, ga damar tafiya amma ba zaki tafi ba! Ko kina tsoron Mehran ne kar ya saka a kashe ku?"
Kallon shi nayi na wasu dakikai, sannan na cigaba da tafiya na, tare da kallon gabana.

"Haba Wakiliyar Mehran, me yasa ba zaki amsa min ba?" Ya faɗa cikin raha da Tsokana,
"Tausayin MEHRAN nake ji! Shi ya hana ni tafiya, da tun tuni nayi tafiya ta."
"Ko kema kina son shi ne?"
"Ko kana kishin shine?"
Na fada ina murmushi tare da tsare shi da ido, fisgo ni yayi tare da hadani da jikin wata bishiya, yana kallon fuskana da nake kallon shi babu tsoro.
Kan shi ya sunkuyar zai hada da fuskana nayi maza na kare hakan tare da kai mishi duka.

     "Ni ba kazama bace! Na haɗa jiki da shugaban ka, kuma na hada da kai wannan shine kolokuwar cin fuska da mutuncin Aamaan." Na fisge kai na, tare da mai da  hankali na akan tafiyar da muke.

           Duk yadda yaso su fahimci juna taki asalima kamar bada ita yake ba, ga shegen kwarjinin da tayi mishi.
....
Koda na shiga keb'entaccen shashi, na sami Sultanah Fazilatul nisa a zaune tana kallona, bata ce min kome ba, har zan wuce tace min.
" Me yasa kike rusa shi daga kasa? Abinda kike aikatawa zai ja a dakatar dashi na tsawon shekaru uku zuwa goma.

       Abinda kike bukata ba zai samu ba, idan har kika sake kika bar masarautan nan, tabbas Aamaan zai iya fuskarta tsigewa daga muqaminsa. Tare da mai dashi daya daga cikin masu jiran gado.
     Don Allah Karki janyo min abin kunya da tashin hankali, sannan zai fita daga cikin gidan sarautar har sai ranar ya dawo da martabar shi. Duk da ba laifi bane hukunci ne laifin da ya aikata, na girmama Baiwar shi sama da dattawan Fada.

        Don Allah Karki saka ni asarar duk faffutikar da nayi, domin zasu mai dashi wancan fadar da yake wancan dajin ne. Gashi bai da goyan bayan gwamnatocin shi.

        Bai da goyan bayan mahaifina bai da goyan bayan Hoyam, kuma ba lallai bane sauran mutanen fada su taimaka mishi, don Allah Karki ja min asara biyu."

          Kura mata ido nayi tare da kallon yadda take cikin tashin hankali, sannan nace mata.
"Wai ke meye Matsalarki da Shine? Ina ruwanki dashi ne? Meye nufinki akan shi Ni kam ma zargin ki nake, Wacece mishi ke?"
         Wani irin rugugi garin yayi tare da sake wata irin tsawa, wanda ya haifar da walkiya me shegen haske, tare da haska ko ina,cikin d'aga murya tare da izza me hade da iko tace min.

"Nice Mahaifiyar shi!" Wani irin tsawa aka kuma bugawa me shegen ƙarfi wanda ya saukar da wani irin ruwan sama babu kakkautawa, ta tako gabana tare da kallona.
"Tun daga lokacin da kika iya dukar Jasrah a cikin gidan nan, maganar Uwaisul Qarni ya tabbata zaki zo taimakona!" Da sauri na kalle ta tare da sake baki na.
"Kinyi mamaki ne? Bayan na tabbatar dake ma kin san shi? Ba abin mamaki bane, haka bai wadatar dake ba, sai da kika yi mata duka ta kasa koda amsar kanta. Sannan Ni nasan cewa ke ba daga karamar ahali kika fito ba, amma bansa daga wani ajalin kike ba.

                    Ba zan miki dole ba, sai dai ki sani kece kika kunna fitilar Mehran! Kuma kece kika kashe fitilar Mehran, nasan koda na hanaki ba zaki hanu ba, amma bana cire rai da rahamar Ubangiji, zaki dawo gare mu."

      Har ta isa bakin kofar ta, tace min.
"Ki tuna uwar da aka rabata da D'anta, aka kuma saubanta rayuwar shi domin Muradin rai! Ki tuna irin kukan da uwa take a duk lokacin da aka ce mata D'anta Ya faɗa matsala, ki tuna uwar da take faffutikar rayuwar D'anta ya inganta.

     Nasan nayi laifi mafi girma a rayuwa ta, iya haka idan Ubangiji ya barshi a matsayin hukuncina yayi min gata, Ban tab'a kisan kai ba duk kuwa son mulkina, amma ina ji ina gani aka daura min Sharri yau kimanin shekaru talatin da takwas ina nan! Nagode Ikram!"

     A hankali na duba a azurfan da ya bani, tare da kallon shi a raina ina cewa.
*Ina son ganinka!*
Sanyin da ya kuma dawowa cikin falon ya sani zuɓewa a gurin ina sauke numfashin wahala.
"Jikata!" Da sauri na mike tare da kallon shi. Murmushi nayi sannan na bude baki zanyi magana yace min.
"Nasan ba zaki tab'a fadan Alkhairi ba, abinda ya kawo ko nan min zo ne ki gaya min wato hada miki baki muka yi ko?"

Yayi murmushi sannan yace.
"Ko daya! Sai dai idan kika bar daular nan a cikin kwanakin nan,. Zaki yi ta fadawa hatsari har sai kin dawo gare shi. Zaki fuskanci  meye asalin rayuwa! Zaki yi kokarin ganin kin dawo amma ina daular tayi miki nisa kafin ki cin mishi.

Ina miki murnan sabuwar rayuwar da kika zab'e fatan Alkhairi, a duk lokacin da kika Fahimci tazarar da take tsakanin ku zaki iya nima na, kai ki ambaton Allah kika yi sau uku sannan kika yi tawwasali da fiyayyen halittar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, zaki ganni amma kafin nan. Kamar yadda rubutu baya dama a saman Teku haka zaki ji kome ya tafi.

    Kina zarra da kika gada a gurin Almustapha! Kina da Izza da kika gada a gurin Joindatullah! Jinin Amratu yana yawo a cikin jininki, ki shiga duniya niman nasabarki, nan zaki gane falalar da Allah yayi miki ya ajiye ki a cikn wannan daular."

    Daga hana ya juyar da hannun shi, tsintar kai na ayi a falon, tab'e baki nayi a raina nace.
*Daka hanani magana sai me?ba zan zauna ba*
Gyara kwanciya nayi a gurin ina cewa.
"Yau nasan bani da arzikin kwanan daki" dan haka na yi kwanciya ta.
    ~~~
Tunda ya shigo gidan ya zauna tare da tari, jini ne ya shiga fita ta hancin shi da bakin shi, kafin ya sami damar dafe kahon zuciyar shi da take mishi zafi kamar an kunna wuta. Shigowar da Sultanah Hoyam tayi tare da ganin shi a cikin wannan yanayin, da sauri ta kira Darakshan ya kira mata likitan fadar.

       Ba a bata lokaci ba, aka tawo dashi. A hankali ya shiga duba lafiyar shi,. Ya jima sosai akan shi kafin ya koma kasa tare da saka hannun shi a cikin jinin da yake kasa, murzawa yayi sannan a hankali ya juya tare da kallon Sultanah Hoyam, yace mata.
"Ranki shi dad'e! Ai matsalar da ake samu zuciyar shi ce take ciwo! Akwai abinda yake b'oyewa a ran shi wanda ya haifar mishi da ciwon zuciya. Ku tabbatar ya gaya muku, idan ba haka ba tabbas zaku iya rasa Sultan Mehran har abada, domin ciwon tayi mishi mugun kamu."

             A hankali ya gama musu bayani sannan ya dauki yar jakar shi bayan ya basu maganin da zasu bashi, bayan tafiyar shi itama Sultanah Hoyam ta koma b'angaren ta, aka bar Fudail da Rakshan, suka zauna dashi bai farka na, sai tsakiyar dare. Ruwa suka bashi ya sha sannan ya koma zai kwanta ya kalli Fudail.
"Ina take?"
"Baka da lafiya Mehran, ka kwanta ka huta."
Lumshe idanun shi yayi sannan ya kwanta tare da Cigaba da barcin shi.

         ......
"Me yasa ba zaki zauna dani ba."
Bai tab'a zaton zata iya daukar wani abu ta illata shi ba, sai yanzun da ya gani da idanun shi.
"Me yasa Qurratulain? Mutuwa ta itace fansar ki?" Ya faɗa dai-dai hawaye na zuba daga idanun shi. Jini yana zuba daga kahon zuciyar shi.

      Gashin kanta ya rufe fuskarta, kayan jikinta ya jike da jini jagab.
"Kin san iya adadin lokacin da nayi ina dankon ki? Me yasa Qurratulain bata bincike Ni ba?"

      Shigowar wasu mutane da jajjayen kaya, hannun su rike da takuba, suka mata zasu yi cikin sani irin zafin nama, ya juyar da ita tare da cillata saman kujeran mulkin shi, sannan suka soka mishi takuban su, dukkan su bakwai har sai da takuban ya fito ta kowani kusurwa,  zare wukar da ta soka mishi a kirjin shi yayi tare da tasa wani irin ihu.

Sannan ya watsar da takuban da suka soka mishi, ya juya da wukar yayi ta kashe su, yana gamawa ya isa gaban ta, tare da zuɓewa a gaban. Ya daura kan shi akan cinyarta.
        Garin yayi wani irin Ja, tare da zubar jini ta ko ina, kamar ruwa, hayaki yana tashi a wajen garin, kukan al'umma da na dabobbi ya yawaita, kamar zasu fasawa mutane dodon kunne.
            "Ki sosa min kai na." Hawaye ke zuba daga idanun shi, yana jika cinyar ta, itama kuma hawaye ke zuba mata, tare da fashewa da dariya. Ta ture kanshi, tare da fasa ihun da sai da tagar da suke cikin fadar na glass suka yi ta fashewa, tare da zuɓewa akan gwiwar ta.

      ..... A firgice ya farka tare da dafe goshinsa,. Yana mamakin wannan mafarkin me matukar girma da muni. Sanyin asuba ne yake ratsa jikinsa.

      Ya lumshe idanun shi, tare da jin kiran Sallah daga can nesa, murmushi yayi sannan yana hango yadda take sallah.
  
  ---
A firgice ta farka tare da sauka a gadon ta fito falon da Ikram take zaune itama zufa take,cike da tashin hankali,kallon juna suka yi sannan Sultanah Fazilatul nisa tace mata.
"Kema mafarkin kika yi?"
A tsoro ce tayi tambayar,
Cikin fitar numfashina na kalle ta, sannan nace mata.
"A'a!"
"Eh shi kika yi! Idanun ki basu boye karya, sabida baki iya ba, kin iya boye damuwa ban da karya, mafarkin rushewar daular kika yi ko?"
Ta faɗa cikin kuka tare da kallona.
"Eh!" Na bata amsa a takaice, ina shakkar abinda zai biyo baya.
Juyawa tayi tare da rufe kofar, alola tayi sannan ta gabatar da sallah nafilla, tare da kiran Uwaisul Qarni.

     "Sultanah! Ku barta ta tafi! Karki kuma dakatar da ita, Insha Allah, Allah zai sauya kaddarar shi, amma babu makawa kaddarar su a haɗe take, ƙaddarar shi ya shiga nata, haka kuma na nata ya shiga nashi.

          Zata dawo amma ban san lokacin ba, ban san me zata dawo yi ba, Allah ya sani. Shi zai kawo mana karshen rikicin masarautan nan. Rabo me tsannanin zai dawo da kome a kuma Cigaba da abinda aka dakatar. Shi kuma kiyi hakuri Insha Allah zaki sha mamakin yadda kome zai sauya. Zai baki damar samun D'anki a hankali kuma a hannunki. Karki manta Addu'o'in da kika yi ta mishi a baya shine zaki Cigaba da mishi har zuwa lokacin da rayuwar shi zata yi kyau mafarkin ku da kuka yi Allah ya fahimtar dani wani abu kan shi. Ki barta ta tafi, idan kuka sake ta zauna ba mamaki hakan ya faru ,na barki Lafiya."

             Gyada kai tayi tare da sauke ajiyar zuciya, abu biyu lokaci guda, farin ciki da bakin ciki, bata kuma zazzafa tunani ba ta cigaba da ibadarta kamar yadda ta saba.
     ~~~
Bayan wasu kwanaki abubuwa sun faru, a cikin shi har da mai dani shashin sa, zai sakani a gaba yana kallona, ina juyawa zai dauke kan shi fuskar shi a nanike, tab'e baki nake na cigaba da abinda nake, tunda dan bakin mulki dawo dani Office din cikin gidan yayi tare muke zuwa kuma muke kome, yayi ta wani cin magani kenan.

           Yau saura kwana uku a fara hidimar zab'ar matan da zasu zauna kafin su saba ayi maganar auren shi....
----
*Wayyo Allah na! Labarin nan bai zama dole ya kare 40 ba maybe mu kara koda page 2 ne akan Free Pages din*

```Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Page 40
      *Last free Page"
    Wato tun da na dawo nake lura dashi bai da lafiya, sai dai yaki bani damar fahimtar haka, zan ga wani lokaci yana amai, ina zuwa zai dauke kan shi tare da k'in juyawa ya kalle ni.

         Yau ma da ake ta kawo mishi kayan da zai saka na zab'en  tsaye yake tare da wani farin tsuma, juyawa yayi tare da kallon inda nake tsaye, nima na juya bayana tare da jin ba dad'i.

    "Sultan wannan zai yi kyau! Sosai sannan zai dace da rana irin ta jibi ko Ikram?" Darakshan ya tambaye ni.

     Murmushi nayi sannan nace mishi.
"Zaifi dacewa da wancan itace kalar maza, sannan wannan kuma shigar mutanen Sham ce." D'aga kayan aka yi tare da nuna mishi.
"Bana bukata!" Ya faɗa fuskar shi a haɗe, dole zai min haka, amma kuma bai dame ni ba, haka na wuni suku suku, da magariba ina zaune na saka abinci a gaba, ina kallon shi ya shigo abin shi bai kalle ni ba, sai dai naji yana tari. Koda na isa tare da bashi ruwa buge hannuna yayi sannan yace min.
"Bana bukata!"
"Wai meye nayi maka ne?"
"Baki san me kika yi ba? Toh tashi daga nan"
"Amma Aamaan me nayi da zafi ne rayuwa kowa na da nashi ra'ayin da kuma abinda ya zab'e me yasa kake son tilasta min na zab'i abinda ba zai amfane Ni ba?"
        Idan dutse zai magana Mehran zai yi magana, shan giya yake hankali kwance, har ya fara buguwa kallona yayi tare da nuna ni da yatsar shi. Mik'ewa yayi tare da nufo ni. Mikewa nayi zan gudu ya saka min kafa, na fadi zai juye min ruwan na buge hannun shi tare da mik'ewa.

      Wani irin fada ne ya shiga tsakanin mu, duk da Ni kare kai na nake shi kuma so yake sai ya kai ni bango, take min kafa yayi na maza na sake shi. Ya hada ni da bango. Tare da d'ago kai na.
Kokari yake mu hada idanu amma naki kan shi ya kai wuyana tare da kai baki shi yana sumbatar wuyar.. rike rigar shi nayi tare da ji kamar zan zube ƙasa,

     Matse ni yayi tare da d'ago haɓɓa na, kai fuskar shi yayi nayi saurin rufe idanuna, jin saukar numfashin sa akan fuskana ya sani bude ido na, a hankali. Sai cikin nashi Idanun. Kasa janyewa nayi ina kallon shi da kyau, tare da karanta sakon shi a sanyayye.

   A hankali zaka Fahimci inda ya dosa, tare da duk wani abinda yake tattare cikin idanun shi.
"Mehran! Me kake SO?"
"SO! Ban tab'a son abu na daban ba, dan haka ba zan tab'a yarda naso abinda ba zai kai ni labari ba, kina da damar tafiya duk inda yayi miki. Sai dai alqawari na tabbatacce ne, domin zan kashe shi!"

"Akan me? Nice na dace da mutuwa ba shi ba, karka tab'a min shi.  Domin ba zan tab'a yafe maka ba idan jinin shi ya zuba a banza!" Na fada mishi tare da kwace kai na, daga gare shi. Ina jin kwalla na zubo min.

.....
Washi gari.
Ana gobe zasu yi zaben shima kuma yana na shi shirin, a baya an sa taron sai dare ne, amma ya maida abun yamma, dan haka an Kawata fadar da ko ina gwanin ban sha'awa, tare da gyara ko ina, murmushi nayi ina jin wani irin yanayi yana shiga na, daga nesa yake hangota, yau tafi mishi koda yaushe kyau da kamala, kallon yadda take murmushi iska yana kad'a  rigar jikinta tare da baza gashinta dake baya a zube cikin nutsuwa.

          Lumshe idanun shi yayi tare da tuno sunan da ya kirata da shi a mafarkin shi, dafa kirjin shi yayi tare da sauke ajiyar zuciya yace.
"Qurratulain!!!" Ya kira sunan a hankali, kamar wanda yayi kiran da karfi sai da ta d'ago kanta tana kallon inda yake, tsuke fuskar shi yayi alamar baya kaunar tana kallon shi ma,

     Table baki nayi sannan na dauke kai na, tare da kallon kasa indai wannan mutumin bai daina min tijara ba, zai ga tsiya iya ganin idanun shi. Murguda baki nayi tare da dauke kai na, daga kan shi.

    .....
"Ku saka idanu akanta, ku nutsu ku duba ta inda zai shigo, idan kuka ganshi, ku kashe shi!" Yana gama fadar haka ya juya abin shi. Bin bayan shi da ido Fudail yayi shi kadai yasan meye yake ranshi.

         Ya kuma kara sanin cewa dole ya dauki mataki kan duk wanda zai kawo mishi cikas. Tun tasowar shi yake bauta mishi ba tare Ya tab'a bijire mishi ba, sai dai wannan karon sunyi tarayya akan Abu daya suke so! Kuma ba zai iya hakura da ita ba sabida shi ba, sai dai a rasa kowa wannan shine kudirin shi akan Mehran, ba zai tab'a bari a cutar da shi ba.

    Amma kuma ba zai taba barin shi da Ikram ba, itama ta sami abinda take so shine adalci. Ya kwana da sanin akwai masu son kashe Mehran amma basu sami damar idda nufin su ba, saboda kwarjininsa da kaifin shi. Ya sani ko a cikin taron su na masu kula da lafiyar shi, akwai mutanen da yake zargi,  yazo jikin Mehran ne saboda Sultanah Fazilatul nisa,. Daukar fansa mahaifin shi Rizwan, Darakshan kuma ɗan Amir Fujai,

       Yasan cewa dukkan su Abu daya suka zo yi, amma baya fatan su sami galaba akan Mehran, duk da yasan ba lallai bane su fahimci cewa Mehran bai san kome akan Mutuwar Iyayen su ba, akwai wasu suna nan zuwa kuma yasan fansa zasu zo dauka. Matukar basu so a gobe ba zasu cigaba da tanadin fansa har zuwa lokacin da hakan ya zo musu.
        Duk da yasan mahaifin shi babban mashawarcin Sultan Abdus Samad ne, bai tab'a kawowa har zasu zubda jininshi sabida rashin imani ba, sannan yadda ya kasa fahimtar kome, ance Fazilatul nisa ce ta kashe Sultan Abdus Samad,. Toh meye mahaifin shi yayi aka kashe shi?

  Babu makawa yasan abinda aka shirya ne, kasancewar shi ma shawarci a cikin gidan. Kuma babban Aminin Sultan Abdus Samad. Akwai abinda ya kasa fahimta sam,.sai yanzun ne yake ganin beken shi na zama har na tsawon shekaru kusan ashirin babu wani abinda ya karu dashi.

Ajiyar zuciya ya dauke tare da sunkuyar da kanshi, yana kallon ƙasa.
       --- A shashin Sultanah Hoyam, kuwa rutsa Darakshan tayi tare da gyara zamanta tana kallon shi cikin nutsuwa sannan tace mishi.
" Har yaushe zaka Cigaba da had'iye fansar ka?"
Ta d'aga kafa daya ta daura akan daya cikin wani irin yanayi take kallon shi, sunkuyar da kanshi yayi sannan yace mata.
"Sultanah, ke Mahaifiyarshi ce kuma ban san me yasa kike son lallai sai munyi mummunar alaƙa ba, zai fi kyau ki sare kai na, da cin amanar da kike son nayi."
            Tasowa tayi tare da nufar shi tana shafa fuskar shi, tare da zagaye hannun ta, akan fuskar shi har ta sami damar tab'a mishi agogon karfen shi, zillo yayi mata sannan ta sake murmushi.
"Zaka iya daukar fansan mahaifinka?"
"Zan iya!" Ya faɗa jikin shi yana rawa sakamakon rike shi da tayi, kamar zai fasa ihu, sannan tayi kokarin dai da suka fada gadon, tare da kallon shi. Sannan yace mata.
"Sultanah Hoyam, ki rufa min asiri."
"Zan kara maka matsayi! Sannan kai ma zan fitar da kai na nuna musu kai jinin sune d'a ga Fujai. Idan kuma kaki yarda tabbas sakamakon ba zai mana kyau ba!"
Jikin shi yana rawa, tare da rintsa idanun shi, haka tayi ta aiki da tsarin shi tare da bawa ranta da zuciyarta abinda take kwadayin samun shi, tunda yake ko bayi bai tab'a jin yayi wani abu dasu ba, amma yau ga Sultanah Hoyam tana amshi mishi samartakan shi, tare da sarrafa shi yadda ranta yake so. Gaji sosai, dan akan ta ya fara sanin mace, amma bai tab'a sanin zata iya sarrafa shi har haka ba, idan ya duba yadda ta manyanta.

       Kwanciya tayi a jikin shi tana fidda numfashin wahala, ta kalle shi sannan tace mishi.
"Kana da dadin mu'amala, ban yarda ka ajiye ko baiwa ba, dan yin haka zai iya haifar mana da tarzoma, Ni daya ce a ranka kuma zaka Cigaba da ajiye ni "
Ta fadi haka tana me mik'ewa daga jikin shi, ta nufi ban dakinta tana me gyara jikinta.

                --- tashi yayi tare da barin d'akin, ya saka kayan shi. Sannan ya nufi gidan shi, ya kwanta, kuka ne ya kwace mishi yazo ne daukar fansa mahaifin shi da taimakon Sultanah Fazilatul nisa, ya shigo fadar amma ita bai gaya mata fansa yazo dauka ba, bai san ta yadda zai gayawa mutane abinda ya kawo shi ba, dan bai yarda da kowa ba, sai dai kash wannan tsuhuwar mayyan ta lashe mishi tanadin shi akan matar shi da zai aura.

     Babu wanda yasan cewa yana cikin Amirai na cikin masarautan sai ita,.tabbas akwai dan leken asirin a cikin daular baki daya. Dan haka dole ya sake lalle, kuma zai sake jiki da Sultanah Hoyam domin ya samu daukar fansa mahaifin shi akan D'anta.
~~~
    Yau tun safe ya kasa yin kome kasancewar yau za ayi zaben yan matan da zasu zama matan shi da wanda

Please Login or Register in order to submit comment