Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sam bana jin dadin kusancinsa dani, an haka dai na daure muka shiga cikin gidan, har cikin gidan, nan aka kuma buɗe sabon hira, duk idanun shi yana kai na, tare da kasa cewa kome. A hankali muke satar kallon juna, sabida yadda muke da d'an tazara a tsakanin mu, murmushi nayi sannan na kalle shi, shima murmushi yayi tare da kallon na, yana min magana da idanu. Girgiza kai yayi tare da nuna min Izmah, lumshe idanuna nayi tare da gyada mishi kai.
 
        A hankali muke tare da kallon Izmah da take kallon mu, mik'ewa yayi tare da kallon Umma yace..
"Zamu tafi umma!"
"Toh mun gode Sultan Mehran!" Murmushi tayi sannan ta bishi da addu'a, haka ya fita tare da kallon inda nake, dauke kai nayi tare da cewa.
"Allah ya kai mu lafiya"
Haka suka tafi,ina jin a raina  tausayin shi yana rinyana, sunkuyar da kai nayi, wato tunda suka fita yaja tunga ya tsaya, duk ya rasa me zai ce, can kuwa yacewa Fudail.
"Hmm, baka yi mantuwan ba?"
Dake shima ya harbo jirgin shi, sai yace mishi.
"Ban manta kome ba, sai dai ko kai?"
"Hmm! Ina jin kam nayi mantuwa a cikin gidan."
"Toh na kira maka Ikram sai ka saka ta ta dauko maka abin."
"Hmm! Manta kawai mu tafi dare yayi" haka suka  suka bar gidan babu wani armashi a fuskarshi.

        ----
Tunda suka tafi muke hira da Umma take min bayanin abubuwan da zanyi amfani dashi a cikin daren zuwa gobe da safe, sai kuma yadda take buƙatar nayi wasu abubuwan, kama daga tafiya na, kasa magana nayi ina kallon ta, har ta gama.

   ~~~
Da asuba su Abrad suka iso, garin SAMAIND ta jirgin ruwa, babban masauki aka tanadar musu, sannan suka kwanta Huce gajiyar su. Amma Allah ya gani baya ta matar shi,.Ikram ce yake bukata a lokacin. Dan haka ya kwanta da mafarkai akanta, washi gari suka shirya tsaf sannan aka ɗauki Azizatul Nissah aka tafi da ita su kuma suka take mata baya,

   A hankali ya'yan shuwagabannin yankunan da suka yi ta wucewa, wurin hatsi Sakeenatu binti Abu Waqqas ta iso, itama ta wuce sannan. Nima banyi tsammanin zan sami tawaga ba, aka turo na fito.  Haka na fita sanye da wata rigar da aka kawo mintin daga Masarautan Sahara, tare da shigar alfarma wanda idan ka ganin zaka Fahimci lallai tabbas na fito daga babban masarautan,haka muka nufi cikin masarautan.

   ***
Cikin shigar alfarma yake kallon yan matan da suke zuwa, har ya cire rai da zata shigo, domin ya kalli Fudail ya kai sau bakwai, kafin aka sanar cewa ga Amirah Bilqisul Ikram daga Masarautan Sahara.

    Yadda aka kawo ni tare da fitowa na, Yasaka zukatar mutane dayawa ya girgiza, dan haka na sunkuyar da kaina, tare da nufar inda aka ajiye mana kujerun mu,  su Izmah da Nimra suna kallona, Idanun Abrad kuwa ya kur akan Ikram, yarinyar ta kuma girma da kyau, sai wani sheki take, ga wani shegen annurin da take fitarwa, a gurin dai ta zame mishi fitilar shi.

            Haka yayi ta kallonta tare da jin cewa tabbas ya mallake ta, kowa kuwa haka zai kuma tinzira zuciyar su ga yaki ne sai ya amshi abin shi, dan haka ya sauke ajiyar zuciya, tare da yarda da cewa, dole ya kawo karshen Labarin. Domin koda taci kome bazata zama matar sarki ba sai Kanwar shi.

    A ɓangaren Mehran kuwa hankalin shi a tare yake.
A ranshi kuwa tambayar kanshi yake.
_Wani irin Girma kike dashi ne a zuciyata Ikram?_

Ya kasa samun amsar domin kuwa, ya gama lallubar kome....
*Ana dara ga dare yayi.....*
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

34
MEROCCO

Da sauri wani Bafade ya shigo tare da zuɓewa a gaban Sultan Mu'allim, tare da sadda da kanshi, jikin shi yana rawa.
"Huzaif lafiya?" Amir Sulaiman ya tambaye shi,
"Allah ya taimaki Sultan, An sami inda Ikram take."

Jikin Rahil na rawa ya taso kamar zai fada kan Huzaif yace mishi.
"A ina? Tana ina ne? Waye ya bada labarin ganinta? Ina yaƙe?"
Yayi tambayar jikin shi yana rawa,
"Tana SAMAIND!" Ya faɗa a sanyayye, kallon kallo aka shiga yi da dattawan fadan, bakin shi na rawa yace mishi.
"Me ta jeyi a can?"

"Ta shiga cikin zab'en matan sarki da..." Wani irin duhu ya gani tare da jin faduwar gaba, kaman zai zube kasa, haka ya kasance dashi. Idanun shi da suke cike da kwalla, yake lumshe su. Rike shi aka yi tare da shafa kanshi. Amir Sulaiman yake yana kallon shi.

   Tausayin Amir Rahil suke gabaki daya ya sussuce musu.
"Nifa kawai ku tashi muje, kar mukara dan wallahi ba zan barwa kowa ita ba. Don Allah ku tashi mu tafi."  Haka suka wuce dashi cikin gidan, nan suka shiga tattaunawa daga nan suka ajiye maganar yadda zasu tinkari SAMAIND ba tare da sun sami matsala ba.

        Duk da sun so ba zasu tafi da Amir Rahil ba, amma suka hakura domin matukar suka ce ba zasu tafi da shi ba, zasu iya samun labarin ya mutu. A yanzu ma ya aka kare dashi. Dan haka zasu tafi dashi. Sai dai sun san ba tafiyar yau bane dole su hakura sai gobe.

   A ranar aka kuma tura wani bafade har askandariya. Domin kuwa idan ba haka ba babu wanda zai kaiwa Sultanah Amrah labarin.

   ~~~
SAMAIND.

Shiru gurin taron yayi kafin Fudail ya fara musu bayani kamar yadda ake yi, tare da nuna musu inda kayan abincin yake zasu diba. Sannan aka saka musu lokacin da zasu fara aikin.  Haka kowa yaje ya dauki nashi cikin ladabi. Sai dai yaran shuwagabannin yankunan ne basu da dad'i.

       Domin magana suke gaya min, dan haka ban damu ba. Na nufi inda zan dauki nawa kayan aikin ne na samu sun kwashe kome. Juyawa nayi tare da kallon su, sannan na tafi na dauki ruwan da duka bari,  haka na dauka tare da dawowa na rufe shi. Sai dariya suke min tare da kallona, ban damu ba ban kuma ji a raina zan fadi ba.

Fitowar Sultanah ya saka mutane dayawa mik'ewa cikin tashin hankali da dimuwa, cikin su har da Amir Hood, tare da Sultanah Hoyam. Zama tayi a inda Fudail ya ajiye mata kujeran domin kallon yadda ake gabatar da abubuwan. Awa daya ya wuce sannan aka kuma samun awa biyu yazo.

A lokacin kowa ya fara alaman ya gama abincin, ina kallon su.

      Mik'ewa suka yi nima haka, sannan Fudail yazo ya fara kwashe abincin yana kaiwa ana jerawa, tare da saka tambarin gidajen su. Da aka zo kaina suka dauki ruwan,.
"Me yasa haka?"
"Bani da zab'i."
"Baki tunanin zaki fadi!" Murmushi nayi mishi sannan nace.
" Allah zai tsaya min,Nasara a jini na take." Na fada mishi.
Juyawa yayi gurin sauran ya musu magana sannan ya wuce.

    An fara gabatar da abincin da kuma tambayar kowa yadda suka hada, babu laifi wannan karon sunyi bazata, domin idan kaci abincin wannan ,.ka kuma cin na wannan sai kaji na wannan yafi na wancan. Haka ayi ta jingina musu musamman iyayen su. Ruwa ka gabatar mishi , kallona yayi cikin tuhuma.
Sunkuyar da kai nayi, sabida yadda ake dariya daga manyan gurin har zuwa yaran su, sai Sultanah Fazilatul nisa ce ta kalle ni, Fudail yace min.
"Ikram muna jin hujjar ki na kawo ruwa a madadin abinci."

Mikewa nayi  tare da rike hannuna, sannan nace Mishi.
"Mulki ba iya abinci yake bukata ba ga talakawa, suna bukatar tsaro da kula da hakkokin su, sannan dole duk wacce zata kasance matar sarki ta kasance me tunanin rayuwar al'umma, babu wanda zai fito daga sahara ka dauki abinci ka bashi, sannan kayi tunanin zai yi rayuwa cikin nutsuwa.

   Ruwa yake bukata, kana bashi ruwa tamkar ka warware mishi duk wani abinda ya dauko ne daga can.
Sannan muhimmanci ruwa Yasaka ake mishi kirarin ruwa abokin aiki, duk  abinda zaka yi dole sai ka bukaci ruwa a cikin shi. Hatta masana kiwon lafiya su tabbatar da cewa. Kaso mafi yawa a jikin mutum ruwa ne, sai jini dan adam ba zai iya rayuwa babu ruwa ba, kamar yadda zai iya rayuwa babu abinci matukar akwai ruwa zai iya samar da abinci.

      Ba zaka gane baiwar da Ni'imar da Allah yayiwa Ruwa ba sai ka shiga sahara babu ruwa dai abinci nan zaka ga mutane da yawa suna mutuwa, amma idan da akwai ruwa zaka samu zasu kai labari duk lokacin da zaka ci abinci dole ka bukaci ruwa, dukda dashi ake sarrafa abincin, wannan shine dalilina na amfani da ruwa a cikin tsarina."

      Shiru kowa yayi musamman yan matan da suke ganin kamar sun lashe zab'en, sai juyawa suke suna kallona, wato nayi abinda basu iya ba, bayan an gama wannan sai aka bukaci mu dafa shayi. A tare muka tashi. Da haka iya ganyen shayin ne sai zuma.

   Tashi nayi tare da nufar Lambun da yake gurin na tsinko ganyayyekin masu kyau da kamshi, sannan na fara dakawa a hankali ina maida hankalina akan abinda nake, a cikin ganye akwai janye minnan nas, akwai ciyawar lemo,.akwai ganyen citta, da ganyen kanumfari, sai ganyen na'ana dan haka duk na dake su, sai ganyen ciyawar lemo ne ban saka ba, na barshi sai da shayin na dauko dafuwa na saka, a hankali kamshin ya cika gurin su kansu yan matan kallona suke kamar zasu yi ihu.

           Dan haka ina gamawa na zuzzuba a cikin kofunan sannan kuma na d'iga musu zuman,a hankali aka yi ya kai na sauran kafin aka zo kaina, suna zuwa Fudail yace.
"Sannun da ƙoƙari." Murmushi nayi mishi sannan suka wuce da shayin, kai na a sunkuye na zauna,.ina jiran sakamakon. Kamar yadda aka raba na kowa haka aka kai nawa ya dauka a hankali yana kallon yadda na sunkuyar da kaina.

                    A hankali ya kurb'a, dadda'ar d'and'ano da kamshi me gamsar da zuciya Yasaka shi d'ago kai yana kallona, kurb'an shayin yayi sanan ya kuma kallon yadda kowa yake shan shayin cikin gamsuwa, musamman Abrad da yake jifar Ikram da kallon duk da bata san yana yi ba.

              A hankali suka tashi suka fara bayanin su,.duk kusan abu daya suka yi dan haka ina mik'ewa nace musu.
"Gabaki daya ganyayyekin da nayi amfani dashi yana magani. Domin dukkan su, ana mana abinci da shi. Sannan ita kanta wannan shayin idan mura ta dame ka, aka hada maka kana sha da Yardan Ubangiji zaka ji sauki sosai, shi yasa na hada shi sabida nasan dayawa ana fama da ciwon mura. Kasancewar muna yankin da take da yawan dusar ƙanƙara. Ita kanta maganin sanyi ce."

           Zama nayi domin sun yarda da abinda na faɗa, can aka kuma zuwa da wani bayani. Inda Darakshan ya kawo bayanin kamar haka.

    "Kasancewar kina matsayin Sultanah sai sarki ya tafi yaki, kuma bai talakawa babu abinci a tare dasu, kayan abincin su ya kare, gashi Sultan bai bada Umarnin a raba ba, sabida haka ke a baki tunanin me zaki iyawa talakawa?

Sai manomin da yayi noma tare da saka tsammanin abincin shi zai kai labari, sai aka wayi gari d'an shi bai baida lafiya kuma yana da saniyar shi na hud'a, dan haka sai ya saka.saniyar shi da abincin shi a gaba wane zai sayar?

Sai na uku, mutane uku  sunyi laifi kuma ba a san waye mai laifin ba, dan haka sarki ya basu wasika akan su tafi can wajen gari su bawa dakarun. Sai kafin su isa sai aka fara ruwan sama, dan haka sai fada ta kama su. Har takai sun sake wasikar su a sunyi musayan wasikar, daya kuma yana rike da wasikar shi. Dan haka da suka isa gurin dakarun sai suka maida abinda ya kawo su, sannan aka amshi wasikar dayan su, aka duba..su kuma aka yanke musu hukuncin kisa? Bayan kuma daya ne mai lafiyan shin taya zaku gano me laifin?"

        A hankali Sakeenatu binti Abu Waqqas ta mike sannan tace.
"Idan Sultan bayan ba zan tab'a dukiyar masarauta ba, sabida babu hurumina a cikin wannan yanayin.
Na biyu kuma manomi zai sayar da saniyar shine domin  lafiyar d'an shi.
Na uku kuma a kashe su dukkan su biyu, domin koda za a tsananta binciken ba za a gane ne gaskiya ba. Wannan shine hujjata."

Azizatul Nissah ta mike sannan tace.
"Bazan yi katsalandan ga shiga harkan tallafawa talakawa ba, ai daman tun kafin a fara yaki dole zasu bukaci su tanadar da kayan abincin su.

   Na biyu manomi zai iya sayar da saniyar shi domin idan ya sayar da abinci bai da abinda zai ci,saniyar kuma ba zata isha shi ba.
Na uku, wanda za a kashe shine wanda yazo da wasikar."dafe kai Abrad yayi. Sabida sam amsar ba haka ban.

       A hankali akayi ta tafiya har aka zo kaina.
"Idan muka duba dalilin da yasan manomi zai fidda kayan abincin shi da saniyar shi ba ƙaramin lalura bane, domin abincin nan idan yayi tattalin shi zata kai shi har kafin faduwar damina me zuwa, dan haka babu hujjar sayar da saniya, abincin zai raba gida biyu ya sayar da rabi tunda yayi noman a wadacce, saniyar kuma da ita yake aikin nomar idan ya sayar da ita bai da wanda zai miki kwaftu, saboda dan shi bai kai wanda zai iya noma ba, shi kuma karfin shi ya kare.
Kuyi min hakuri na fara da amsar manomi ne..

A matsayina na Sultanah, aka wayi gari Sultan Mehran ya tafi yaki kuma bai ce min kome ba dangane da al'ummar shi, gashi akwai kayan abinci a cikin Baitul Malin masarautan! Zan duba soyayyar su da kaunar su ga Sultan Mehran,.zan saka ayi ta diban abinci cikin dare ana kai musu kofar gidajen su, domin ya rage musu zaman dar-dar da suke yi. Bayan nan idan suka gani washi gari addu'o'in su itace kashin bayan dukkanin mulkin shi da nasarar shi.

Sai batun masu laifi, akwai wani dabi'a na mai laifi ban sani ba ko wasu sun fahimci haka, amma idan mutum ya aikata laifi yana iya fin kowa firgice, sannan da zaka saka kanka a kirjin shi bugun zuciyar shi yafi na kowa, sannan abinda na Fahimta shine Mai laifin da ya fahimci shi za'a kashe shine ya dauke wasikar wancan,  badan kome ba yasa ni fadar haka sai dan hujjar da nake da ita. Duk yadda akayi mutane biyu da suke jajjayan nan sun bude wasikar su..shi na ukun su bai san meke faruwa ba, dan haka su biyu sun san meye a cikin wasikar su.daya ne za a kashe ba dukkansu ba."

"Shin ko Ikram zata gaya mana taya zata iya gane mara gaskiya, duk da, sun kafe akan cewa wasikar su ne?" Amir Hood ya min tambayar.
Dan mik'ewa nayi tare da gaishe shi, sannan nace mishi.
" Bayyana nayi bayanin domin mara gaskiya duk inda yake zaka iya d'ago shi, idanun shi yana yawan budewa, sannan shi kansa baya iya tsayawa guri guda ba,  jikin shi kuwa rawa yake yi, tsoro takan zame mishi shimfid'a akan fuskar shi. Bayan haka yafi kowa zakewa da rantsuwa."

       Na fada sannan na zauna sai lokacin na kalli Mehran da ya haɗa ya dunkule hannun shi, yana kallona, fuskar shi ta bayyana farin cikin shi. Dayawan dattawan gurin magana daya suke, yarinyar yayi kokari tana da basira.

Murmushi nayi ina me jin dadin nasarar da na samu, a hankali.suka yi ta bayyana mana sakamakon mu, karshe dai aka bankad'o tafiya na da nayi shi ya saka ban samun damar tsayawa a.matan shi sai suka barni a shugaban Kwarkwarorin shi. Mikewa Fazilatul nisa tayi sannan tace musu.
"Wannan sakamakon bai yi ba, dan haka Ikram itace matar Mehran, ko kuma allura ta tono garma..,
*Toh fa wata sabuwa....*
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

35
Cikin fusata Sultanah Hoyam ta mike tare da kallon ta, cikin fushi mara iyakata tace mata.
"Wacece ke da zaki saka mana ,doka Mu kuma mu bi?"

Murmushi tayi tare da gyara zama sannan ta kalli Ikram tace mata.
"Kin cika duk wata sharudan da ake bukata, dan haka kece yau zaki gana da Mehran! A matsayina na mahaifiyar shi, na baki shi gudan shi ba b'ari ba."

   Kallonta gabaki daya Emiraters councilors din, suka yi domin abinda suke gudu kenan shigar Fazilatul nisa cikin harkokin Masarautab,. Tunda da suka ji labarin bata mutu ba suka san cewa tabbas tana raye ne domin fansar ta, dan haka suka mike tare da kallon ta, kafin suka ce.
"Mun amince Yaran mu zasu zama Kwarkwarorin shi, sanan muna rokon Sultanah arzikin karta bawa Ikram karfin da zata juya a kalar masarautan."

        "Karya ne,  Mehran d'ana ne dan."
"Bani da lokacin ki, Ita wancan Yarinyar nake da Muradin a bata matsayinta! Ko kuma hmm!" Fazilatul ta sake murmushin mugunta.
Cike da mamaki nake kallon ta, domin dai nasan tana da nata Muradin idan ba haka ba, me zai saka ta kafe akai na.
"Toh an bar mata matsayinta a bisa sharadi guda uku! Sharadi na farko dole ta kasance budurwan! Sharadi na biyu dole ta kasance yar da tafito daga Masarautan? Sharadi na uku karmu kama ta da wani kuskure ko muji labarin wani mugun abu yafito idan ba haka ba. Hmm!" Yayi wani irin murmushi hade da kumshe bakin shi, yana kallon ta.

    Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Insha Allah! Na yarda da Allah kuma na yarda da ita, kuma Allah zai bamu sa'a."

Ta faɗa tana murmushi.
"Shin wai ince wannan kika tsayawa? Wannan kika tsayawa? Lallai kina bukatar nazari. Amma lokaci zai nuna mana."

   Takowa tayi daga sama, inda take zaune ta tawo har inda yaƙe,  sannan tace mishi.
"Mir Umdatuddawla ko kana da matsala da ita ne? Dan naga Yarka Yasmin kake taya kishi! Duk wanda yayi magana tabbas yayi magana ina da yakinin Yar shi yake tsayawa kishi, dan haka kowa ya zuba ido."

         Shiru duk suka yi tare da sunkuyar da kai, sannan ta juya kai ta kalle ni.
"Daga ranar da kika amshi matsayinki na Sultanah ina son ki shiga binciken sanadin mutuwar Abdus Samad, idan kika amshi ragamar Sultanah ina son ki bincika mike faruwa a cikin masarautan nan! Idan kika yi haka zaki taimakawa mijinki gurin bincike! Kina da damar tuhumar me yasa aka dakatar da mijinki akan muqamin sa? Bayan nan kuma ina rokon adalci daga gare ki na bi min hakkina akan kazafin da aka min. Ina tayaki murna."

      Daga haka ta juya daga gurin taron, tana me jin dadin ta wanke abinda yake ranta, tabbas tasan ba zasu iya dakatar da matsayin Ikram ba, kodan tsira da mutuncin su. Sannan ba zasu so asirin da suke aikatawa ya fito fili ba, dan haka ta barsu da tashin hankali. Domin kuwa matukar suka barta tayi magana. Zata iya fadar abinda zai daure su har karshen rayuwar su, dan haka suka yi farin ciki barin ta gurin dan tana magana da yawa, duk yan matan an kira su tare da karrama su.. sannan aka kirani daga karfe aka bani kyautar da yafi nasu, bayan na amsa ni dasu Izmah da Nimra muka bar gurin.

         Takawa Abrad yayi har gurin Mehran, ya kura mishi ido sannan ya mika mishi hannun, cikin girmamawa yace mishi.
"Kana ta farin ciki zaka auri budurwa ko? Koda yake naji an cire gwajin budurci. Domin wasu yan matan zawarawa ne, idan kuma dattawan masarautan ka suka ji labarin Sarki Abrad ya tab'a kwanciya da ita fa? Hhhh koda yake shima wancan ai sauran Abrad ya samu.

    Ka tambaye ta, tun bata kai haka ba, na saka mata girmana jikinta kuma ta dauke ni cif. Dan haka kasan dole sai ta cika sharadin budurci ko kuma hukuncin kisa ya haura kanta. Itama zata so na rufa mata asiri dan haka ka ajiye a ranka zaka fara jin kararrawan tashin hankali. Matukar ina raye Ikram tawa ce ni daya."

             Kura mishi ido Mehran yayi tare da sunkuyar da kan shi kasa, yana jin kamar ya dauki takobin shi ya dauke mishi kai cikin tashin hankali yake murza hannun shi, kafin ya d'ago kanshi yana murmushi yace mishi.
"Zan iya cewa haushin ka rasata yasa ake gaya min magana haka ba. Dan haka babu damuwa koda a gidan ƙaruwai na samo ta, tabbas zan zauna da ita."

      Cikin fusata ya kalli Mehran sannan yace mishi.
"Tabbas zaka yi kuskuren da ba zaka manta ba, domin zan kashe duk wanda yake tare da ikram, domin ita mallaka ta ce"
"Ina ga baka tab'a kowa Askandariya ka tambayi ina Yar uwan matanka take ba ko? Zanga yadda zaka iya hada kazamtar da kake shirin aikatawa."

Daga haka ya juya tare da barin gurin, domin jin kirjin shi yake kamar zata fashe, yana shiga ya hango ikram daga nesa, wani irin tausayin kan shine ya kama shi. Meye laifin shi da kaddarar ta yake walagigi dashi? Me yasa ba za'a barshi ya huta da ita ba, sai tashin hankali da damuwa. Kura mata ido yayi yaga yadda take dariya da farin ciki. Ji yayi wani kamar zai fashe da kuka domin kuwa yana hango yadda Abrad ya kwanta da ita, tare da hango Yadda Numan yayi ta juya ta a shimfid'ar shi.

  Wato maza biyu sun keta mishi alfarman shi, sunci mutuncin shi sama da yadda ake cin mutuncin wani a duniya, da takalmi suka dauka suka dake shi da shi ba zai mishi ciwo irin wannan da Abrad yayi mishi ba, ji yayi duk wata alfarmar da yake dashi ya tsinke gani yake kamar duk wata mutuncin shi sun tsinka mishi. Duk da yasan tayi aure baya jin haka yayi mishi ciwo kamar yadda Abrad ya nuna mishi ya kwanta da ita..mafi kololuwar ɓaci rai da ya tab'a ji a ranshi kenan.

    Dan haka ya bar abin a ranshi kafin yasan mafita.

  ***
Had'iye yawun Abrad yayi tare da juyawa yana kallon taron jama'a da suke watsewa. Ba dai Ikram Yar Joindah bace?

  . tabbas idan yarta ce ta haramta mishi, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun me yasa haka ya faru dashi. Lallai dole ya dakatar da kome ya tsaya Domin rusa Mehran da ya ikram, idan ba haka ba tabbas zai yi biyu babu, ya kwadaitu da jikin Ikram, dan haka koda zai mutu ya dawo wallahi sai ya shiga ya mata faca faca da ruwan jikin shi.

    Wannan shine tunanin da ya tsaya a ranshi, dan haka yayi wucewar shi zuciyar shi daya..yana haduwa da Nawwas ya gaya mishi abinda ya faru. Ba karamin kaduwa Nawwas yayi na, tare da cewa.
"Wallahi baka da kirki!  Me kake shirin aikatawa? Yarinyar da babu aure a tsakanin ku shine zaka shirya mata mugun makirci haka..toh wallahi zan gaya mata gaskiyar abinda kake shirin aikata mata domin ta farga daga abinda kake shirin aikata mata ai wannan rashin imani ne idan kanwarka aka yiwa haka ba zaka ji dadi ba, dan haka wallahi dai na gaya mata idan ban sami ganinta ba zan gayawa Mehran dan yaji abinda kake shirya musu.. son kan ka yayi yawa toh wallahi ba zan tab'a barin ka, ka lalata musu rayuwa ba, tunda kai kana da naka rayuwar!"

    "Nawwas ni kake gayawa Magana? Toh naga wanda ya isa ya dakatar da ni." Ya faɗa da karfi, nan fada yaso kaurewa a tsakanin su, dakyar wasu daga cikin dakarun suka raba su.

Cikin fushi Nawwas yace mishi.
"Wallahi ina sane da kome da ka aikata, kyale ka nayi kawai amma wannan karon zaka sha mamakin abinda zai faru."

           Cikin mugu mugun fargaba ya kalli Nawwas, sannan ta

Please Login or Register in order to submit comment