Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

        Hannuna na kai bayan shi tare da shafa bayan a sanyayye, har yayi shiru, matsawa dashi nayo bakin gadon shi dake mun shigo har uwar dakin shi, saka kai shi yayi akan shafaffen cikina.. tare da rungume ni tabaya.
"Don Allah Karki tafi ki barni."
"Rayuwata a cikin ku bata da cikakkun yawa, ina da rayuwa a wani gurin, don Allah karka min dole."

  "Me yasa?" Ya tambaye ni tare da kallon fuskana, rike hannun shi nayi tare da durkusawa a gaban shi, na kai hannun shi kan fuskana.
"Zan tafi! Idan na gama abinda nake yi, ba zan zauna ba akwai wani abu a gaba na, bana son kana rokona. Amma zan bar maka Izmah ka rike min ita Amana kafin na dawo. A'a bar shi na tafi da ita."

           Hada goshin mu yayi tare da zubar hawaye, "don Allah kar ki min haka ina bukatar ki." Kauda kai na nayi tare da cewa.
"Nima ina bukatar ka, amma bai zai hanani tafiya ba, dan na kudiri aniyar tafiya," ganin zai iya damamin lissafi na tab'a wuyar shi tare da mikewa har ya suma, murmushi nayi sannan na gyara mishi kwanciyar shi na fito daga cikin gidan.

          Tunda ga ranar ban kuma samun barci ba, har ranar da za ayi gasar.

   Shiryawa nayi cikin nutsu, sannan na kalli Izmah, nace mata.
"Zaku fita da Sabir, zai wuce dake iyakar kasar nan, insha Allah zuwa dare zan iso. Karki sake kazo na samu baki nan, ki kula da kanki Insha ALLAH zan zo"

    Kai ta gurin Fataken nayi na biya kudin da zasu kaita inda nace, sannan na mika mata kudi da guzurinta, durkusawa nayi na rungume ta, tare da cewa.
"Insha Allah ina tafe."

        Sai da naga tafiyar su, sannan na juya tare da dokin da gudu, na nufi cikin masarautar, gurin shi na nufa, sannan na mika mishi wani abu a kofi, nace mishi.
"Ka juye a gora, zai maka amfani. Idan kaga na lashe gasar kayi ƙoƙarin sha, kafin nan zan tabbatar Raziyana da su Abdullahi sun hadu, sannan zanyi wani abu. Guba ce ka tabbatar kasha na hannunka!"

          Tsoro ne ya kama shi, dan haka na juye mishi a cikin wani karamin goran azurfa, sannan na shirya shi muka fita, koda muka nufi gurin gasar, Niman daya daga cikin yan matan bayin da zasu ciyar da mutane nayi,  mukayi magana, sannan na juya na nufi gurin gasar, tare da maida hankali na. Aka fara, ina yi ina kallon Amir Rahil da yake tsora ce, dan tunda nace mishi guba ne kamar na zuba mishi tafasasshen ruwan zafi, haka yake gumi.

      A hankali gasar yaƙe tafiya, dan haka koda muka tsallake mataki na farko da na biyu duk nice, a hankali mataki da uku dole ko kai ko Raƙumin ka, dole dayanku ya dawo, dan haka ina kai matakin zamu zaga garin nasan za a iya farmaka ta, dan haka na fita da shirina. Juyawa nayi ina kallon Amir Rahil da yake kallona idanun shi jajjur.

Tausayin yan uwantaka yake bani ina son d'an uwana, da dangina, amma ba zan iya zama ba, domin Rayuwata tana wata duniyar ban sani ba, ko zan dawo gare su. Ko kuma su zasu dawo gare ni.

             A hankali na nufi hanyar tare da kad'a linzamin raƙumin, munyi tafiya me nisa aka farmaki ni, dama na san da haka, dan haka duk sai da naga bayan su da takobi, kafin na wuce shigen su. Tafiyar da muka yi tare da zaga birnin ba na wasa bane.

          Dan haka a can ma ban tsira ba, har dai da na tsalleke matakin da zai maidani cikin gari, sannan na tsinci gawar wata matashiyar budurwa, wacce nake da yakinin ba ajima da kashe ta ba, na cire kayana na saka mata, sannan na fito doguwar riga da mayafin fuskana, na daurata akan raƙumin, tare da rubutawa.

   *Amirah Raziyana, Abdullahi, Abdul Rahman,na gama muku aikin ku saura mutuwar Amir Rahil babu wanda zai kuma shan gaban ku, Mun kashe Abubakar da Aliyu, Almustapha mun kad'a shi duniya, domin naji labarin Ya mutu dan haka nasa yanzun gubar da muka bashi ya sha zai fara tasiri ita kuma na gama da Tarihin ta*

   Sannan na kad'a kan Raƙumin ya nufi gari, Ni kuma na nufi inda muka yi da Baba ya ajiye min raƙumin da ya ciro min a garken Amir, sannan na ce mishi.
"Bana zan tafi! Amma zan dawo. Ka koma akan lokaci, domin nasan yanzun haka yasha gubar da na bada a bashi, Baba Insha Allah za a dauki fansar Jinin Almustapha da Abubakar tare da Aliyu, don Allah ka saka mishi ido. Zan dawo amma ban san ki ba, ko tafiyar kenan. Allah ya ƙaddara saduwar."

Na kad'a raƙumin nai gaba na barshi yana tsaye.
"Wacece ke?"

    "Jinin Almustapha! Jinin Mu'allim da Bilqisul Ikram yake huda jikina, Karka damu zan dawo domin kare kimar Mahaifina."
Sannan na kad'a kan Raƙumin muka yi sahara.

   *Amin zan dawo! Ko ban dawo ba jini na zai dawo! Insha Allah zai dawo zai dawo kuma zai dauki fansan da ban dauka ba*

     "Tabbas Allah ya baka yar da tafi maza dubu, cikin hikima ta dauki fansan da ba a tab'a samun wanda yayi haka ba. Sarauniyar mu tazo ta wanzar da adalci Muna jiran dawowar ki. Sarauniyar Jarumai."
Juyawa nayi tare da komawa gari, tun daga shiga garin ya fahimci akwai matsala..
    
   ---- a can filin kuwa yarinyar da Ikram ta bata guba ta saka mishi ta tabbatar mata da cewa, an bata wani ta saka. Dan haka ta kai ta lungu tayi mata barazana da wuka sannan ta   gaya mata gaskiya, dan haka ta karb'i wancan tare da mika mata wani da kuɗi tare da cewa.
"Ki saka mishi wannan!"
"Toh ai zasu kashe ni!"
"Karki damu za a sake ki na miki alƙawarin haka "

       Dan haka bayan fitar su, akayi ta mika musu ruwan, Amirah Raziyana tana kallon lokacin da aka mikawa Amir Rahil ruwan, bata sha nata ba sai da ta tabbatar da cewa ya sha, tare da zuba ido, cikin damuwa yana kallon hanyar da zata  ɓullo.

   Ganin raƙumi ta, dauke da ita. Amma alamar a mace, kasa tashi yayi ya zuba musu ido, yana kallon yadda take kwance, amai ya fara tare da rike kirjin shi. Sauke gawar aka yi tare da ɗaukar takardan jikin gawar, wacce fuskarta babu kyan gani, karanta wasikar akayi tare da mikawa. Magatakardan masarautan ya karanta da karfi. A zabure suka kalle shi. Dakyar Amir Rahil ya iso kan gawar tare da fasa ihun me mugun karfi, yana me rungume gawar, gashi yana aman jini alamar gubar tana ratsa shi, da gudu aka zo aka dauke shi tare da gawar Yarinyar.
"Wayyo Allah na! Salsabila karki tafi ki bar ni."

   Gefe guda kuma aka maka Amirah Raziyana da Abdullahi da Abdul Rahman, aka tafi da su. Domin ana fara magana Abdullahi da Allah ya daura mishi tsoron ya amsa da ya aikata, kome ma aka tambaye shi ya amsa, Raziyana ce taki magana.

            Dan haka aka kai su gidan kaso, tare da maida hankalin kan su.
      ---
Jikin Sultan Mu'allim yayi sanyi da yaji yaran shi har da Yar da yake matukar kauna, tana auren d'an Galadimar kasar, da ita ake haɗa baki aka kashe yan uwanta sabida mulki..

         Sauran Yaran shi kuka suke tare da bashi hakuri, kar ya zafaffa hukuncin Shari'a akan su.
Shigowa Baba yayi tare da mika mishi wata takarda aka amsa sannan ya kalli Sulaiman.

A hankali ya fara karantawa,
```Assalamun Alaikum Kaka na, nasan sakona zai iso gare ka, duk da nasan bana raye! Suna na Bilqisul Ikram Mustapha! Yar d'anka Almustapha! Amir Sulaiman ya san kome akan shi da inda ya zauna! Kaka na gashi bana raye balle naga yadda zaka bi min hakkina da na jinin Mahaifina don Allah ka bi min hakkina karka manta muma muna son rayuwar mu aka raba mu dashi! Ya kai Sultan adali karka manta hakkin mu ne zaka bi```

   Zama yayi tare da kallon Sulaiman ya tambaye shi ya akayi, nan ya gaya mishi kome tare da bashi labarin Auren da Almustapha yayi da sayo Ikram a matsayin baiwa...

           Shiru fadar ya dauka, sannan yace musu.
"A kira min shugaban Shari'a, ya zartas musu da hukuncin da ya dace dasu."
"A'a Sultan! K'iyayyar ba zata kare ba, a sake su. Amma a raba su da jin dadin rayuwar su. A kwace kome nasu. Idan da hali a mai dasu fakirai yadda zasu fuskanci kaskanci a cikin birnin, yadda zasu Fahimci muhimmancin rayuwa domin hassadar su ce ta bayyana musu asalin su "

Inji Sultanah Bilqisul Ikram, tana kuka. Take kowa na fadar yayi na'am da abinda ta faɗa, sannan aka koma kan Amir Rahil. Dan dole aka nufi gidan shi.
An samu yayi aman gubar domin bata da dogon illa.

      ~~~
Gudun da nake bana wasa bane, dan haka na rufe fuskana sai iya idanuna, sai da nayi tafiyar Sa'a biyar da wani abu dan ban tsaya yin sallah ba, sannan na nufi  iyakar inda na sami, Izmah tana kallon hanyar da zai kawo ni, bata san nice ba sai da nace mata.
"Ke Yar masunta!" Dariya me hade da kuka tasaka min sannan na dira akan raƙumin, na durkusa tazo ta rungume ni, tana kukan farin ciki.

      Sallah na gabatar tare da niman abinci naci, sannan nace mata.
"Kinsan Allah, ina kewar wancan sakaran, Sosai domin ya iya kukan banza."
"Matsoracinki. Kinga yadda yake shirme, kai amma wannan anyi sha-sha-sha."

Dariya muka saka sannan muka dauki rakumina, ta haura gaba na zauna a bayanta muna hira muna nufi wata yanki na daban, muna cikin na duniya, ko ina zamu sake fadawa oho....
 
kawo karshen Book one Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641'''
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: Monday-March-2021
*FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

15.
"Bana son wulakancin d'an uwana ne fa, kuma bana da ra'ayin auren miji irin shi, ina da da zab'i amma abinda kakanina suka zab'a min shine zab'i na"

     "Dama duk wannan jarumtar kina da ra'ayin biyayya." Murmushi nayi sannan nace mata.
"Tashi mu nufi wancan yankin."

    ~~~
A hankali yake bude idanun shi, tare da rabawa a kan su, ajiyar zuciya yayi tare da kallon kayan da yake jikin shi, tare da gyara kwanciyar shi.

           Had'iye yawun bakin shi yayi tare da kokarin tashi zaune.
"Kwanta karka motsa, Sannun Rahil!"
Lumshe idanun shi yayi sannan ya kuma buɗe ido.
"Da gaske itace ta mutu?"
Kafin su bashi amsa, sai ganin shi sukayi zai wula, da sauri suka nimo likita, aka shiga ceton rayuwar shi. Tare da kokarin ganin ya dawo hankalin shi.

    Allah cikin ikon shi ya sami barci, ajiyar zuciya suka sauko gaba dayan su.
"Sulaiman shin YARINYAR da ka kawo ce ta mutu!"

       A firgice ya kalle Sultan Mu'allim, kafin yayi kasa da kan shi yana fadin.
"Bani da tabbacin itace ki ba ita ba ce. Sai da yadda na san jinin Almustapha yake yawo a jikin ta, na zata mutu cikin sauki haka ba, Sultan Ikram jinin ka ce, dukda ta hana Ni fada hakan, sabida yadda kome zai zo da sauki."

  Kura mishi ido tayi tare, jinjina al'amarin yarinyar ana niman dangi ita ta shigo dangin, amma ta tafi wacce irin zuciya ce da ita haka? Meke damun ta da kuruciyarta haka? Meye ta saka a gabanta? Me take nima a duniya? Wannan shine tambayar da yayi tawa kanshi domin baki daya, yayi sanyi ya rasa wanda zai bashi amsa, dan haka ya maida hankali akan nazarin abinda Raziyana suka aikata.
     ~~~
Mun shiga garin wanda tun da farko shiga naga rubutun Misra, an rubuta Askandariya. Ajiyar zuciya na sauke tare da niman mayafi ka rufe fuskana tare da saka Kudade Izmah ta rufe nata, itama.

              Sai dai yadda mutane suke kallon mu yasani jin wani iri a raina, muna shiga cikin kasuwar garin, muka gamu da wata mahaukaciya.

     Kura min ido tayi tare da sake baki tana dariya, sannan ta fara magana tana cewa.
"Ai na gaya muku! Zata dawo wallahi ga uwar gijiyata ta dawo, na rantse da Allah itace.". Dake mahaukaciya ce babu wanda ya damu da maganar ta, haka akayi ta ture ta ana wucce.
Ita kuma tana bin mu tare da gayawa jama'a yau ga uwar gijiyatar, har gidan bakin da muka sauka, bata fasa bin mu ba.

   Gashi an hanata shiga, koda muka shiga Izmah tace min.
"Ikram! Mahaukaciyar nan maganarta abin dubawa ce fa, gata can tana dambe da masu gadin gidan."

          D'ago kai nayi tare da kallon ta, sannan nace mata.
"Nima ina nazarin maganarta, kasancewar an tab'a min magana akan kamar mu da Yar sarauniyar wannan garin, kuma ina son na bincika ne ko nan ne dangin Mahaifiyata amma babu fada babu rigima duk abinda zai faru karki damu. Kawai sarauniyar nake son gani."

        "Kina ganin babu wanda zaki markad'a kashin shi! Babu wanda zaki gotar mishi da hannun shi, gaskiya shigowa wannan garin cike yake a kundin tarihin ki. Dan haka babu damuwa za ayi yadda kike so!"

   Ban kulata ba, har dare ya fara na fita daga dakin na nufi waje, kallon Mahaukaciyar nayi.
"Zasu zo su farmake ki, don Allah ku gudu karsu kashe mana ke, muna bukatar ki, kin manta da Ni ce Benazir ce, kin manta baiwar ki me kula da lafiyar ki, karki manta dani, don Allah nice. Da idanun ki na fahimci kece."

Warware mayafin nayi daga fuskana, tana ganin fuskana sai da ta zube a kasa tana kuka tare da cewa.
"Wallahi kece!" 
Mikar da ita nayi tare da cewa.
"Kina magana akan wacece?"
" Amirah Joindatullah!"

            "Kin santa ne?" Na tambaye ta ina murmushi.
"Uwar d'akina ce."

Janta nayi tare da zaunar da ita, muka shiga hira, tana gaya min abinda ya faru, murmushi nayi sannan nace.
"Ba zan d'agawa Sultanah Amrah hankali ba, kawai abinda zan yi zan baki sako ki kai mata, sannan tabbas akwai matsala a tare da ita, yau zamu bar garin nan."

         Komawa cikin masaukin mu nayi na rubuta mata sako ta kaiwa Sultanah Amrah ni kuma na tattara kayan mu, muka bar garin domin bana son abinda zai janyo ayi bore a cikin garin, yin haka shine  zai iya janyonwa a kifar da tsarin mulkin Sultanah Amrah, ni kuma abinda ba zan yafewa kai na ba kenan, indai har mahaifiyata ta bar masarautan ne dan gudun faduwar mahaifiyarta babu amfanin na..... Amma kuma yaushe zan daina gudu. Juyawa nayi tare da zuwa na nime gidan Waziriyar Sultanah Amrah.

     Ajiye mata sako nayi sannan na dauki Yarta budurwa, na fito da ita.

    Nayi tafiya da ita, bayan na rubuta mata.
_Ya zaki ji idan har akace tarihin abinda ya faru ya maimaita akan abinda kike burin ganin ya bunkasa! Kiji yadda uwar da ta rasa basadaukiyar Yarta kuma Sarkin Yakin Kasar ta, idan kika iya fadawa al'ummar kasarki abinda kika aikata da shirinki akan Sultanah Amrah Yarki zata dawo gare ki! Na lashi takobi ba zan tab'a ragawa duk wanda yayi zalinci ba_

Lokacin da ta ga sakon ihu tayi tayi tana cewa.
"Maza ku duba garin karku sake ta ficce min da Y'ata, karku bari na fita da ita"

   Tana fada tana ihu, daga nan kuwa ban mu tsaya ba, itama Yar tana barci, babba budurwa ce dan haka koda muka bar yankin muka kuma nutsa sahara bamu tsaya ba, haka muka kwana muka wuni, sannan muka isa wani gari me suna. Hazb.
*HAZB*
Gari ce wacce take tsakiyar sahara, garin ya kawatu ainun, sai dai muna shiga garin muka fada hannun dakarun garin a matsayin yan gudun hijira, kuma bai zama dole mu kare a haka ba, dole sai a matsayin bayi.

     "Ina kika kawo ni? Ke wacce irin mahaukaciya ce! Wayyo Mama na?" Ta faɗa tana ihu.
Ban mu damu da ihunta ba, sabida tana cika maka kunne, shigowa dakin da aka zubamu aka yi, hasken fitilar ya haska ilahirin jikin ta, wanda take sanye da wata rigar barci ruwan hanta.

       Dariya mutumin yayi tare da komawa yayi ya kira, Mutanen su.
"Don Allah,.Ikram kiyi wani,karsu tab'a lafiyar ta." Inji Izmah,
"Babu abinda zan mata, sabida zunubin mahaifiyarta!"

Na fadi haka dai dai shigowar su, ihun ta yasa na juya gare ta, wato fincikota suka yi tare da danne ta.
"Kuskure ne tab'a macen da bata san hawa ba balle sauka, babba tashin hankalin shine. Karo da zakanya."

Tashi nayi tara da maida kafaa baya kasance sun daure mana hannun mu ta baya, ina tabbatar wa na fito da hannun gaba, nayi kokarin kunce hannun, sannan na daure hannuna da igiya.

    Kallon su nayi sannan na shiga daure wuyar da igiyar dai da na karya musu hannu da kafar su, na kyale su, ashe akwai daya a cikin su da yake rike da wani icce, kafin na ankara sai ji nayi kaina ya bani wata irin sauri kamar an buga karfe sakamakon buga min itaccen da yayi a kaina, ina dafe da keyar da kyar na samu na juya tare da shammatan shi na daki kayan aiki, sannan na mike tare da rufe kofar, na kwanta a gurin.
.  Ina juya kaina da nake ji kamar ba a jikina yake ba, gani nake duniyar tana juya min. Maganar mutane nake ji a rarrabe, bude ido nayi na kuma rufewa.
       
             _Ikram karki bishi! Domin zan kashe shi! Ba iya shi ba duk wanda ya Kuskura ya rab'e ki sai na kashe shi_
_Sultan Mehran! Shi ya turo mu_

_Shi yasa mu mu kashe, shi mu tafi dake!_
_Karku tsaya ku fada ruwa! Sarwat ku fada cikin ruwan_
Fuskar Mehran ce take min gizo, mika hannun nake amma ina, fadawa a cikin ruwan ne ya dawo min, lumshe idanuna nayi, tare da cewa.
"Mehran! Me yasa? Me yasa ka kashe min abokin rayuwa ta? Me yasa baka tsaya  kai na ba? Lallai jininka ya cancanci zubdawa domin fansan na NOMAN"

Daga nan ban kuma sanin meye ya faru ba, sai bude idanuna nayi na gan mu kwal a cikin rana, an shanya mu, Izmah da Nimra suka kuka tare da kiran suna na. Dakyar na bude idanuna, na juya ina kallon su. Dukana dakarun suke tare da kwallo dani.

   "Don Allah kar ku musu kome nice nayi kisar!" Na fada a wahale,
"Lallai kuwa, zamu kashe su, sannan bayan mun kwanta da su."
"Kuskure ne zaku aikata!"
Ina ƙoƙarin zare hannun daga igiyar, wurgo min da wuka yayi tare da cewa.
"Idan kin isa kwace su."
Raina ya b'aci da yadda suke musu, musamman Nimra. Ajiyar zuciya nayi tare da mik'ewa, na naushi wuyar daya daga cikin su, dayan na juyowa na yi maza ka yanke makogaron shi, jini ne ya tartsatsi a ko ina.

    Kallon shi nayi bayan na nufi gaban su Izmah, na tsaya.
"Bana son faɗa! Ku barmu haka zamu tafi ma"

    "Hmm! Tsinanniya zan kyale ki ne?" Murmushi nayi sannan nace mishi.
"Haka ba wani abun damuwa bane domin Ni na yanke hukuncin, dole ka amsa."
Wurga mishi wukar nayi ta wuce bata tsaya ba sai a kirjin shi. Juyawa nayi a hankali, ja konce su. Sanan na riko hannun su. Muka nufi waje, wasu kartin karennuka muka gani, zasu min ihu na rufe kofar.
"Izmah! Koma ki dauko min wuka can, zamu fita."

        A hankali ta koma bayan ta dauko min, muka fita. Na samu suna gurnani. Murmushi nayi sannan nace musu.
"Karku ji tsoron su. Insha Allah zamu fita ku tsaya a bayana."

Dan haka na dauki wukar ''tare da nufar karennuka, da gudu suka rufe min. Cikin ikon Allah ban yi kasa a gwiwa ba, haka kawai nake ganin kamar Mehran ne a gabana, yake bin karannuka.   Cikin wani azabben sauri na caki wuyar shi, kafin dayan na same shi a cikin shi.

    Zuɓewa suka yi suna shure shure, haka muka tsallaka su muka fita daga gidan, niman kaya nayi na bawa Nimra, domin duk wannan ƙaddarar ta faru ne sabida shegen kayan barcinta.

        ~~~
Askandariya.

Zaune take aka ce mata tana da Bakuwar baiwa tazo gurinta. Kasancewar bata hanawa a ganta.
"Ranki shi dad'e! Ta dawo gashi nan tace na baki."

     "Wacece Benazir?"
"Uwar d'akina mana!" Murmushi tayi sannan ta amshi sakon.
_Umma nasan kina kewar Ammyna! Don Allah kuyi kokarin dakatar da waziriyarki! Sannan ki tura sako zuwa Marocco! Kicewa Amir Sulaiman! Kebe Mahaifiyar Matar Almustapha! Wato Gimbiya Joindah! Kuyi zumunci dasu! Sannan ki hukunta Waziriyarki dan itace ta saka a ka sace Ammyna idan na fito zan yake ta jama'ar zasu bata kariya dan haka har nayi tunanin tafiya, sai na dauki Yarta itama taji yadda kika ji! Idan na gama Insha Allah zan dawo gare ku ahalina._
Bilqisul Ikram Mustapha.

      "Ina take?"
"Ai tafi!" Kamar ta fasa ihu, haka ta yasa ta nufi  gidan Waziriyar ta, tana saka kanta tana jin kalaman bakin matar da ta bata yardanta dama da na yaranta biyu. Duk duniya babu wanda zai gaya Mata Nairah nacin amanarta ba zata yarda ba, yau taji da kunnenta.

   "Taya ba zan d'aga hankalina ba, Kuna ganin abinda nayiwa Joindah shine yau ya faru dani, haka na shiga tsakanin su da Sultanah domin na samu yadda nake so dan na fahimci yar ta fara d'ago, abinda nake shirin yi.

    Amma na mata barazana zan kashe mahaifiyarta ko kuma rusa mahaifiyar ta, shine ta tafi ita kuma Uwar na gaya mata ai tabi saurayin da aka cewa ana ganin su tare, wanda kuma karya ce nayi ne domin na rabasu.....

kawo karshen Book one Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641'''
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: kawo karshen Book one Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641'''
#Mai_Dambu

Monday-March-2021
*FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

16

"Kuma duk sharri na mata, ina gab da zama Magajiyar sarauta, (Empress) ace yau an wani gari wata ta sace min Y'a ta da itace zata gaje ni, kuce nayi shiru naci kaniyar shirun,"

   Tafiya yayi da baya kamar zata fadi, tana kallon su. Rike bakinta tayi tana kokarin neman jarumtar da ta rasa lokacin da taji abinda zai tarwatsa mata zuciya.

"Meye nayi miki da zafi Nairah? Meye kika nima kika rasa? Na baki kome na mallaka miki kome?" Ta faɗa cikin kuka me tab'a zuciya, ta ma kasa tsayuwa da kafarta, jingina tayi da bango. Duk da shekaru sun haura mata, amma da zafi mutumin da ka yarda yaci amanar ka.

       "Meye nayi miki? Nairah! Na baki damar kiyi mulki a fakaice, na baki karfin da ban bawa Joindah da Zariha ba, na baki shi
Na baki kome dan kiyi farin ciki." Mikewa tayi tare da zuwa gabanta, ta kife ta da mari.
"Me yasa baki gaya min mulki ne a ranki ba? Me yasa tun tuni baki gaya min kina son kujeran da nake kai ba? Kin san yadda na dauke ki a raina, kin san yadda nake jin girman kaunarki a raina?

   Ke ba yar Uwata ta nesa bace ganinki nake kamar ciki daya muka fito shine zaki saka min da wannan mugun b'arnan! Wani irin laifi na miki haka ban sani ba?"

Goge kwallar ta tayi sannan ta sake murmushi tana faɗin.
"A lokacin da kika shirya kifar dani,sai gashi Allah ya kawo min jikata tayi miki shirme ko? Ba zan kashe

Please Login or Register in order to submit comment