Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kofar d'akin, sannan yayi zaman raƙumi a bayana, yana kallona, fuskar shi babu walwala.
"Ki tashi"
Banza nayi dashi tare da kin motsi. Gyara zaman shi yayi tare da rungume gwiwar shi, yana kallon yadda nake kwance.
"Bana son gardama." Banza nayi dashi a karo na biyu,  iskar bakin shi ya furza. Sannan yayi shiru. Ina jin idanun shi a kai na, ji nake kamar zane ni yake yi, kasa jure idanun shi nayi na tashi tare da kallon shi ina murguda mishi baki.
"A daina cinye ni da ido!"
"Hmm!" Ya faɗa a kasar makoshinsa, tare da lashe bakin shi, alamar haka a jikin shi yake.
"Ni dai ka fita min a d'akin"
Kamar da dutse nake magana yaki ko motsi, tare da sake murmushin jin dadi.
"Don Allah ka fitar min a daki."
Wani irin mayyen kallo yake bina dashi, kamar kura taga d'anyen nama, tare da lasar leben shi ba kasa,wanda nake hango yadda take rawa, tsoro ne ya sani mik'ewa da sauri tare da shiga ban ɗakin, bai damu ba sai ma sake murmushin da yake alamar yarinyar ta fara laushi daga horon idanu. Wanka na fito, yana inda na barshi bai matsa ba.

     Tura baki nayi tare da hararan inda yake, sannan na fara gyara jikina, haka na gama shiryawa fuskana ban yi mishi kome ba, ina gamawa ya kalli inda kayan yake sannan ya kalle ni.
"Ni bazan saka ba!"
Na fada kamar zanyi kuka, murmushi yayi sannan ya gyara zama. Shi yana kallon ta, ai maganin biri karen maguzawa, dan haka ba zai tab'ata ba balle tayi tunanin dan jikinta yake tab'ata ko daya, shi kawai dole ne ayi yadda yake so, idan mutum yaki zai ji a jikin shi.  Yadda ya zuba min ido ya sani kwashe kayan daga cikin dakin zuwa ban daki. Ban fito ba sai da na shirya, sannan na fito ina yatsina fuska.

      Murmushi yayi sannan ya janyo alkyabar shi ya saka, tare da kallona. Nufin shi na daure mishi igiyar, kallon shi nayi baki sake ban san lokacin da na kwashe da dariya ba. Ina kallon shi.
"Nice zan zo na daure maka zaren alkyabar?"
Murmushin gefen baki yayi tare da nad'e hannun shi a kirjin shi yana me kallona da ido.
_Yau duk abinda zaki yi sai kin daure min shi domin nafiki rigima dan mulki nake ji yau_ ya faɗa a ranshi.
*Ni ba zan daurewa makashina alkyabar ba, matukar zan daure maka toh ba makawa sai na shake ka*

Na fada a raina ina murmushi, takowa nayi tare da kallon fuskar shi, domin nasan matukar na isa gurin sai wuyar shi ya gaya mishi.
_Bilqisul Ikram! Kome zaki yi ina shirye dake! Ina jiranki_ ya faɗa yana murmushin mugunta.

Takowa nayi na isa gaban shi na saka hannuna da niyyar daure mishi igiyar, yadda na sarkafe tare da zarga mishi zaren, sai da ya matse ni da kirjin shi har ina jin yadda numfashina yana wani irin kamar zai fasa Kirjina.
"Mehran!""""
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

30
A razane na kira sunan shi, tare da jan numfashina dakyar, kan shi ya kai wuyana tare da sake min wani irin numfashi me hade da nishi, k'asa k'asa yace min.
"Hmm! Na iya nima" d'ago kai nayi tare da kallon shi.
"Hmmm!" Ya kuma cewa, alamun dai ma mishi abinda ya sani, kamar zan fashe da kuka haka na daura mishi sannan ya sake ni, muka fito daga cikin ɗakin.

     A hankali muka fito daga gidan, muna tafiya bai damu da yadda ake kallon mu ba, tare da kallon yadda mutane suke hidimar su na bikin ranar, duk da tafiyar kurame muke haka bai hanani jin wani irin nutsuwa ba, duk inda muka wuce shagali ake, ashe ni ce ma nake damuwa dasu domin kuwa jama'a kowa hidimar gaban shi yake, har muka isa inda ake ta soya kayan ciye ciye, kallon shi nayi ina son tambayar shi su Izmah, amma ganin yadda bai bani fuska ba ya sani jan bakina nayi shiru.

  Tsayawa yayi tare da kallon inda ake sayar da wani, wani abu kamar panke, abin yayi min kyau, muna tsayawa a gurin wasu matasa suka kalle mu. Tare da cewa.
"Keeee! Kyakkyawa, idan zaki ci gashi."
Satar kallon shi nayi da wutsiyar ido, mika min panken matasan suka yi.  Ni kuma dake ina son na b'ata mishi rai kawai na amshi panken tare da sake murmushin mugunta. Faucewa yayi tare da wurga da abin a kasa yana hararar Matasan. Cikin isgilanci suka ce mishi.

"Dalla malam mun ga kayan aiki kace zaka hanamu, yan mata kinyi mana! Kuma gaskiya muna sonki." Cikin murmushin jin dadi na bude bakina zanyi magana, ya cire hular alkyabar da ta hana mutane fahimtar shi, kamar wanda ake jiran ya cire gabaki daya mutanen gurin suka sauke wuta, kallon su yayi tare da girgiza kanshi yana fadin.
"Ku watsa!"
Jikin su yana rawa suka shiga watsawa, baki daya gurin ya zama babu kowa sai shi da dakarun shi.

   Shi kanshi me sayar da panken jikin shi rawa yake, dan kamar zai sake fitsari.
"Darda bashi jakar tsaba nan!"

      Ajiyewa mutumin jakar kudin  sannan ya koma gefe yana faɗin.
"Ka zubawa Amirah Ikram abinda take bukata"
"Ba zanci ba, baba ka rike amadadin kashe maka kasuwa da aka yi" murmushi mutumin yayi tare da cewa.
"A'a Amirah wannan dukiyar ta isheni, koda zan shekarar goma banyi sana'a ba wannan zai ishe ni, nagode sosai Sultan Ubangiji ya kare rayuwar ka." Ya zuba min abin tare da mika min. Ganin yadda yake damun sai naci ya sani karb'a ina kallon Sultan.

           Dauke kanshi yayi tare da hango Jasrah tare da wasu bayinta, dan ta hango mu. D'ago kai nayi dan mishi magana naga hankalin shi yana kan ta, ajiye tasar nayi tare da mik'ewa na tsaya a gefen shi. Har Jasrah ta iso gurin.
"Sultan MEHRAN kai ma kafito kallon wasan ne, Barka da kasancewa da kai a wannan lokacin."
Murmushi yayi sannan ya kalle ni, tare da kallonta. Nad'e hannun nayi a kirji ina kallon su.
"Ikrammmmm! Bake bace aka ce kin bi saurayi ba." Satar kallon shi nayi naga fuskar shi babu wani abu na sauyi, murmushi nayi tare da cewa.
"Eh laifi ne?"
Dariya tayi sannan tace.
"A'a ba laifi bane, amma shi Sultan Mehran ya san cewa kuskure ne babba macen da take kasar ikon Sultan Mehran ta bijire mishi, duk da kuwa Sultanah Fazilatul nisa, tayi kokarin d'aga miki daraja kika zab'i bin saurayi koda yake ba laifi bane tunda matsayinki na bawa ce."

        Murmushi nayi tare da matsawa jikin shi sosai, sannan nace mata.
"Eh Toh wannan ra'ayinku ne, ra'ayin shi ya gaya min, ban sani ba ko akwai wani abu bayan haka Mehran."
  Yadda na shiga jikin shi tare da manne mishi.  Kura min ido tayi tare da kasa cewa kome, murmushi nayi mata tare da janyo hannun shi ka makala a k'uguna, ina murmushin jin dadi.

Kasa jure ganin mu a haka tayi kawai, kamar wacce aka ingizo ta zata fadi a jikin shi itama, kayi maza na ture shi baya ita kuma ta fadi a jikina, murmushi nayi mata sannan nace mata.
"Sannun karki ji kome, zan tare ki, Mehran ne dai baki isa ya tare ki ba."
Ya ture ta, bayinta suka tawo da sauri suna ce mata.
"Sannun Amirah,"

   Kallon mu yake cikin jin dad'i, a ranshi, amma kuma ba zaka tab'a ganin wannan abun akan fuskar shi. Tasowa tayi tare da d'aga hannun ta zata mare ni, rike hannunta nayi tare da cewa.
"Ki duba kwayar idanuna baki isa ba, Amir Zuhair bai isa ba balle kakan ku Amir Hood, ni dince ban sauya ba." Na wurgar da hannunta tare da jan hannun shi muka bar gurin, ina murmushi, muna karawa gaba na kalle shi cikin jin haushi na ja alkyabar shi na rufe kan shi, duk da kuwa ya fini tsayi.
"Wallahi ni ba dan kai kayi fada na ba, nayi ne dan ra'ayina, kuma ka mayarda hulan kanka."
Na fada ina tura mishi baki.

    Share ni yayi tare da wuccewa abin shi, a ranshi yana faɗin.
*Magulmaciya zaki gama gulmarki! Amma tabbas yau naga abinda kike boyewa ina jiranki,*

      Haka muka yi ta zaga garin har kusan tsakiyar dare sannan ya dawo dani gida, tun muka iso yaga ina hamma, zama yayi tare da kallon yadda nake kokarin shiga daki yayi, ganin zan gudu na barshi ya sashi finciko ni.
"Ni barci nake ji!"
Zaunar dani yayi tare da saka kaina gefen kafadar shi, bai ce min kome ba, bai kuma nemi nayi magana ba, hannun shi a cikin nawa, yana murza yatsuna. a hankali har barci ya dauke ni me karfi.

            Yana zaune a gurin, har aka fara kiran sallah farko, kafin ya dauke ni zuwa cikin ɗakin ya kwantar dani, ya ja min bargo. Tare da shafa fuskana, sannan ya juya ya fita daga dakin. Dake na gaji sosai ban ma san har ya kawo ni dakin ba, sai da Nimrah ta tashe ni daga barcin sannan na mike a hankali na nufi ban daki nayi alola, bayan na idar da sallah ne na kalle su.

   Sun sayi abinci, tare da zama suna hirar yadda suka sha yawo da Fudail, ban saka baki a maganar su ba, sai da naji suna cewa.
"Amma naji ance kamar an samu yar karamar rikici, tsakanin Amirah Jasrah da tawagar Sultan Mehran, wai da gaske ne?". Bude idanuna da yake cike da barci nayi sannan nace.
"Ki tambayi Aamaan Mehran,!"
"Kai Ikram amma baki da kunya kowa Sultan Mehran yake kiran shi ke kuma Aamaan Mehran, sai kace sa'arki!" Tab'e baki nayi sannan nace mata.
"Aamaan Abdus Samad kike magana akan shi." Na fada tare da dauke kaina ina murmushin mugunta, dan naga yadda suka gwalallo idanu waje, na kuma sake samun damar na kwafta rashin mutunci a silalle.

"Wai Aamaan Abdus Samar kuke faɗa?' kasa amsa min magana ta suka yi suna kallona, tare da cewa.
"Dama haka kike baki da mutunci?"
"Gado nayi a gurin Wancan d'an bakirin" na fada ina murmushi,

Watsewar zabi sukain tare da min fatar shiriya, dan ganin mahaukaciya suke min.
~~~
Karyawa Mehran yake bini bini yana sake murmushi, gyara zama Sultanah tayi sannan tace.
"Sultan dina anya baka fara soyayya ba?"
Ya kuma sake murmushi a karo na babu adadi, yana daukar soyayen kwai ya saka a bakin shi yana me sake murmushi me sauti.
"Fudail meye gaskiyar magana yau kimanin kwanaki masu yawa bana ganin shi da maraici,idan ya dawo kuma zai ta sake murmushi wacce barauniyar ce tayi sa'ar sace zuciyarshi?"

     Kallon juna suka yi tare da dauke kai.
"Nifa kamar uwace! Idan baku gaya min wacece ita ba waye zai gaya min?" Ta tambaye su. Sake kallon juna suka yi kafin suka shiga kallonta an rasa wanda zai gaya mata gaskiyar maganar.

    Murmushi tayi sannan ta cigaba da cin abincin ta, tana me cewa.
"Ikram itace mafarkinka, ba zanyi mamaki idan nace maka nasan tana cikin lardin nan ba, amma kuma ban san me ya dawo da ita ba, dan nasan dai haka kawai ba zata zo ba sai dan daukar...." Zuba mata ido yayi tare da rike cokalin hannun shi da mugun karfi har sai da ta lankwashe.
 
    "Karka damu! Ni ba a zalimar mutum bace, ina bawa kowa ra'ayin shi." Matsanancin kunya ce ta kama shi, tare da kasa kallon kallonta. "Toh Fudail idan Shugabanka yayi aure kai waye zaka aura?" Diriricewa yayi ya kasa tsayuwar guri guda, sai kallon gefe da gefe.
"Nimrah" Mehran ya faɗa a sanyayye, kamar bashi yayi maganar ba, da sauri Fudail ya bar falon.
"Dawo nan! Kayi min bayani daga ina take."
"Sultanah tare suke da Ikram!"  Inji Darda,
"Hmm!" Ta faɗa tana murmushi, Mehran kan kasa cin abincin yayi, duk ya takure guri guda.

       "Bari na baka guri" ta faɗa tana murmushi, "hmm" yace mata, tana jinjina wannan karfin halin shi, toh ya yake yi da Ikram dan hira tsakanin mafadaciya da Miskili irin Ikram akwai matsala, dan kowanen su gwani ne akan halin shi, zafi da sanyi zasu haɗu guri daya, murmushi tayi a karo na biyu. Sannan ta shiga d'akinta. Tana zama tana son ganin Uwaisul Qarni, dan haka ta shiga addu'a kafin can tayi imani da Allah sannan ta ambaci sunan shi.
               Cikin hukuncin Ubangiji ya bayyana a gaban ta, a saman fatar damisa. Yana murmushi.
"Ikram!"  Cikin girmamawa tace mishi.
"Barka da warhaka Baba na, eh itace!" Kallon tausayin yayi mata tare da girgiza kai, tare da cewa.
"Kiyi ta addu'a, Allah ya taikaita tashin hankalin da yake tare da alaƙar su."  A hanzarce tace mishi." Akwai damuwa ne?" "Idan Ubangiji ya so al'amarin shi, babu makawa sai ya faru, duk abinda yazo muku, ku amshe shi da hannun bibiyu, a duk inda ƙaddara take, toh yana da kyau bawa ya amshe shi hannun bibiyu, Wani al'amarin dole sai Ubangiji kadai zai warware miki shi, SOYAYYA ce me tattare da kalubalen rayuwa, soyayya ce da kema idan baki yarda da Allah zaki iya shiga al'amarin Ubangiji, soyayya ce me cike da raunin zukatan al'umma. Soyayya ce da zata kashe masoya ta kuma raya makiya, ban tab'a ganin irin wannan al'amarin ba, duniya cike take da kalubale, rayuwa cike take da tashin hankali. Wallahi babu wanda ya isa goge zanen ƙaddarar da ya zana. Dan haka karki yarda ki shiga wannan lamarin." Hawaye ne ya zubo mata, tana faɗin. "Yanzun babu hanyar da zan dakatar da wasu abubuwan?" Murmushi yayi sannan yace mata. "Eh mana! Kin isa ki aikata abinda Allah ya ƙaddara? Baki isa ba? Baki da ikon tafiyar da rayuwar wasu, kiyi addu'a, kiyi hakuri karki yarda wani abu ya shiga tsakanin wutar da zata kono a tsakanin wasu, karki yarda wasu su fahimci cewa akwai wutar da ya kama a cikin gidan ki." Ya faɗa tana tsare ta da idanu, kasa tayi da kai. "Nasan kina kaunar Ikram, dole wata rana zaki iya Mantawa da wannan tunanin, nasan zaki iya juyawa kome baya domin wani dalili, ina tausayawa lokacin da wasu abubuwan zasu juyawa wasu dalilai baya, na tausayawa tafiyar da za ayi ta a cikin tsananin zafin sahara, babu ruwa babu Uzuri, rayuka zasu koka zuciya zata kasa jure kome, tunani zai tsaya cak. Mafita zata yi ƙaranci, ba lallai bane na riski wannan yanayin, bai zama tilas na san lokacin ba. Domin lokacin tafiya na ya kusa, zan tafi baki daya." Ya faɗa a sanyayye, yana me juya kanshi ya ce mata.
"Idan irin wannan lokacin ya riske ki, kiyi kokarin maida alamarinki ga Ubangiji, Insha Allah Ubangijin zai amsa miki kuma zai kawo miki ɗauki, karki yarda a juya miki nazarin ki. Insha Allah zaki yi farin cikin samun Ikram a rayuwarki."

Gaba daya ta rasa abin cewa, ita kanta tausayin kanta da kanta take ji, dan haka har ya tafi bata iya fahimtar kome ba, sai hawayen da take zubdawa.....
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

31

Ita kanta bata san iya adadin lokacin da ta dauka tana kukan  tashin hankali da damuwa wanda bata san daga inda zai ɓullo mata ba, alola ta mike tayi tare da gabatar da sallah nafilla, ta jima tana kaiwa Allah kukanta,  kafin ta fito daga dakin. Sam bata jin dadin ranta, tana fitowa ta sami Shairah da Narjis suna magana akan zab'en da za ayi, da yadda ake shirya bikin domin Fudail ya gabatar musu da wasu abubuwan da  za ayi. Suna ganin Sultanah suka yi shiru.
"Meye Mehran ya sauya a cikin tsarin?" Shiru suka yi tare da kallon shi.
"Sultanah dama ya ce a cire maganar lallai sai anyi gwajin budurci ne?" Shiru tayi sannan tace musu, "babu wanda zai goge abinda aka kafa, dole yabi tsarin masarautan" ta faɗa musu,  "amma Sultanah!" Suka fadi haka lokaci guda. D'aga musu hannu tayi sannan tace musu. "Dokar masarautan ce,bai isa ya take ta ba, ko Ni da na haife shi ban da ikon karya dokan balle shi din banza, doka ce babu wanda zai karya ta"
"Toh Sultanah" haka ta zauna bata ce musu kome ba, ita dai wallahi da ana sauya ƙaddara tabbas da ta sauyawa Ikram da Mehran, sam ta rasa mafita lumshe idanu tayi tana nazarin me ya dace tayi ba tare da ya shafi rayuwar su ba. Sannan taya Ikram zata kashe masoya ta raya makiya. Ga baki daya ta rasa tunaninta. Dafe goshin ta tayi kamar wacce take fama da ciwon kai. Nan kuwa ƙwaƙwalwar ta ne yake aikin hargitsa mata lissafi.

  ~~~
Shiru suka yi tare da kallon Mehran, kafin suka shiga kallon shi an rasa wanda zai gaya mishi dalilin kiran shi fadar, asalima duk sun razana da yadda yake muxurai.
"Sultan MEHRAN yana da uzuri fa!" Fudail ya gaya musu, "kai d'an mashawarta waye yayi dakai?" Murmushi Fudail yayi sannan yace mishi. "Darakshan! Bani da abinda zance maka, amma wata rana zaka biya ladan aikin ka" sannan ya kuma duban mutanen fadar yace musu. "Wani dalili kuke niman Sultan Mehran?"
"Shi Sultan Mehran bai da bakin Magana ne inji Sultanah Hoyam?" Ta kalli Mehran, wanda kanshi yake sunkuye yana matsa hannun shi, kamar baya fadar. Kuma har ila yau sun kasa fadar abinda yasa suka nime shi, kasancewar ya zabga musu gargadi tun lokacin yakin da yankunan jazziratul Arab suka nemi shiga musu, ya dakatar.
Dayawan su dattijai ne, da suka manyanta amma kasuguman munafukai ne. Dan haka da gayya yaki magana kuma dole sune zasu fadi dalilin da yasa suka kira shi, amma kuma babu wanda yake da zarrar bude baki yayi magana.

        Abin dariya sai wannan ya zunguri wannan, shi kuma ya zunguri na kusa dashi haka sukai tayi, karshe Amir Hood ne yayi shahadar kuda ya mike tare da cewa.
"Jiya Jasrah ta gaya min cewa taga Sultan Aamaan Mehran da wata mace wacce taci mutuncin shi a cikin masarautan nan, sannan ta keta Alfarmar masarautan nan akan idanun kowa bayan ta kasance daya daga cikin fadar nan, shin Sultan Aamaan Mehran ya yarda da ita ne har ya iya yafe mata, ko ba saurayi ta bi ba? Sannan kuma ba girman SULTAN Mehran bane yana yawo cikin gari da kaskantacciyar baiwa a cikin jama'arsa,  kar Sultan Mehran ya manta yana cikin dokar hana fita ne me yasa zai karya doka ko ya manta akwai Amirorin da suke jiran ya bada kayan bikin fitilar al'ada a kai musu, amma anga kaya masu daraja a jikin Ikram da kawayenta shin wata irin matsayi take dashi haka? Sannan abisa al'ada ba a yarda wani sarki ya auri macen da tayi mu'amalanci wani namijin ba, kuma ta bayyana ƙarara Ikram namiji tabi, sannan kuma dokar masarautan nan ne, babu batun auren bazawara ko karuwa mafi munin lalacewa ace Sultan Aamaan Mehran ya kwana a gidan ƙaruwai, wannan Zubewar mutuncin masarautan nan ne, mafi munin abu ace Sarki Guda ya kwana a gidan Ƙaruwai? Don Allah ku duba wannan lamarin"
   
                Lumshe idanun shi yayi yana jin kalmar karuwa da ya danganta Ikram dashi, jin yadda kalmar take dukar shi kamar ana saka bulalar k'aya karfe. Idanun shi yayi jajjur. Mikewa yayi tare da sauka akan kujeran shi dake fadar,.Yasaka kai zai fita daga fadan."kai waye da zamu yi magana ka mana shiru?" Suka daka mishi tsawa,  wannan shine girman kuskuren da suka aikata mishi, dan haka ai ance shiru ma magana ne, dan haka ya fice daga fadan. Tunda yake babu wanda ya tab'a gaya mishi abinda ya saka shi bakin ciki sama da kowa ba, dan haka koda ya koma gida, Daki ya wuce ba tare da kalli inda Sultanah take, tunda ya shiga dakin bai kuma fitowa ba, domin kuwa baya son magana, fahimtar haka da Sultanah tayi yasa ta hana kowa yayi wani abun da zai saka ayi hayaniya ko wani magana me karfi.

      A bakin Fudail suka ji labarin abinda ya faru, tashi tayi tare da shiryawa tayi zata fadar Fudail ya ce mata. "Sultanah a halin da yake ciki baya son karin damu, matukar zaki nufi fadar toh ba makawa kin lalata kome, dan haka ki zuba ido kiga abinda ya shirya. Yakin masarautan nan Sultan Aamaan Mehran ba zai iya shi daya ba, sannan kuma ke idan kika shiga mishi zasu iya aikata wani abu kuma su makala miki, ni tsorona daya karsu kaiwa Ikram hari domin kuwa zasu aikata haka kuskuren da zasu damu da kansu." Ya fadi haka a raunane, domin yasan haka ce zata faru. Idan ba wani ikon Allah bane ya hana faruwan haka.
     Numfashi ta sauke tare da kallon shi tace mishi.
"Ina Ikram din take?"
"Tana wajen garin SAMAIND!" "Toh ka kai mata dauki mana, ko a tura mata dakarun da zasu kula da lafiyarta ".

"Karku fara haka!" Ya fadi hakan lokacin da ya fito daga dakin, yana me shirin barin gidan.
"Akan me?"
"Ba mace kawai bace ita!" Yana gaya musu haka ya ficce daga gidan baki daya, can wajen gidan ya nufa, dan baya son abinda zai tinzira zuciyar shi. Cikin yanayin bakin ciki yake kallon dajin, da yadda kome yake zaune cikin tsarin Ubangiji da ikon shi, yau yayi danasanin kasancewar shi daya daga cikin gidan sarautar ƙasar shi.

        Damuwa tayi mishi yawa, bai san ta lokacin da ya b'ata a gurin ba, kuma ba zaka tab'a tsammanin yana gurin ba, dan ya saje da gurin baki daya, ya rasa inda zai cusa kanshi. Dan haka da ya gaji da zama ya mike zai dawo gida ne ya hadu da Fudail yana niman shi, kallon juna suka yi sannan yace mishi.
"Sun kaiwa Ikram hari"
Rab'a gefen shi yayi tare da barin guri a hanzarce ya isa gidan, kayan shi ya sauya sannan ya dauki gatarin shi ya nufi wajen gari.

      Gani yake dokin da yake  kai bata gudu, duk da kuwa saurin da yake yi bai hana shi ganin nisan gidan da Ikram take ba, jike kamar ya cire zuciyar shi ya gulla tsabar tashin hankalin, koda ya isa ya sami dakarun da suke kula da lafiyar ta, duk an kashe su, yana shiga ya same ta zaune akan saman gawarwakin mutanen da ta kashe, jini na d'iga daga gefen cikinta. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tako a hankali,yana murmushi ganin yadda take rike da takobin salon shi ta dauka, wato tayi kujera da mutanen.

     Ganin su Izmah da Nimra a gefe bakin su a fashe ne ya sashi kallon su da son karin bayani.
"Muna zaune suka shigo, wai ance su kashe Ikram, shine tace inji waye? Sai suka ce mata Sultan Aamaan Mehran, ya umarce su, suka kasheta.mu kuma muka ce karya ne ba zaka tab'a sakawa a kashe ta ba, shine suka rufe mu da duka, daga nan ne ta ce su kyale mu ita ta yarda a kashe ta. Shine kawai suka juya kanta da dukka.

          Har da janya, bayanta ma jini na zuba. Ganin sun kama mu zasu shigar da mu d'akin ne domin kudirin su, shine ta fara kashe su, wallahi bana son naga tana kashe mutane haka, dabi'ar tai mata yawa, mace ce kuma hakkin jini ba zai tab'a barinta ta huta na." Izmah ta karshe maganar cikin kuka da tashin hankali.
"Ikram bani takobin" ya mika mata hannu, bata d'ago kai ba, balle ya saka rai zata amsa mishi, a hankali ya taka har gaban ta, ya saka hannu ya tab'a kafad'arta, biyo shi tayi tare da zubewa a jikin shi. A kidime ya d'ago kanshi, tare da kai hannun shi bayanta, yaji wuka a suke a bayan ta, a hankali ya zare wukar.
                Kallon Fudail yayi

Please Login or Register in order to submit comment