Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bane, lumshe idanun ta, Fazilatul tayi. Uwace kawai zata iya daukar nauyin tashin hankalin D'anta.

        Murmushi tayi sannan tace mata.
"Idan na saka aka kashe ki, kamar na bawa makiya dama su kalubanci Mehran ne, idan na barki a raye su din da suka turo ki sune ajalinki.

      Itama Mahaifiyarki da take ta faffutikar, ganin ta turo ki hmm cutar dake zata yi domin amfanin dake za ayi idan bukata ta biya zaki sha mamaki."

       Nuna mata Hanyar fita tayi, jikinta a sake, sabida bakin cikin abinda take ji take gani, Alhamdulillahi tana tare dashi ko babu kome zata zame mishi garkuwa.

      Fita tayi ta nufi dakin da ya kwana, ta kira shi yana zaune ya kurawa guri guda ido, zama tayi sannan tace mishi.
"Kayi hakuri!"
Wani karamin murmushi yayi wanda bai kai Zuci ba, ya ce mata.
"Nagode!"
"Taso muje ka karya;"
Babu musu ya mike suka fita dashi.
---
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Yanzun ta ya aka yi gobara ta cinye Y'ata da jama'ar ta?" Take ya fara wani irin girgiza, kafin ya fadi.
Jasrah itama kuka take tare da ihu, Goggonta.
Dakyar aka fitar dasu daga filin gidan da ya kone murus, ana kai shi gidan shi ya sake murmushi, tare da cewa.
"Kome ya kammala min"

       Dariya suka saka shida Jasrah tare da kamanta abinda suka yi a gaban jama'a, suna dariya tare da cewa ai an yarda dasu.
         ~~~
Bude idanu nayi ma ganin a saman rumfa, da sauri na duba naga Izmah, ajiyar zuciya na sauke tare da shafa kanta, ina faɗin.
"Duk wuya duk rintsi sai na baki garkuwa!"

     "Sarauniyar barci, kin farka?"
D'aga labulen nayi sannan na ce mishi.
"Eh amma yaushe aka dauko mu?" Dariya yayi sannan yace min.
"Karki damu da haka? Zaki ji kome a hankali."

     Mika min abinci yayi na kalli abincin sannan naki dauka!
"Kina tunanin ko na saka guba ne?"
"Ai nasan ba zaka zuba guba dan ka kashe ni ba, aiko dan cikar Muradin ka zaka barni a raye."

  "Toh tunda kin yarda da haka kici mana!"
"Zanci kai, Abokiyar tafiya ta nake tunanin bata cin abincin irin wannan"
"Toh yayi kyau. Tunda haka ne bari akwai wani nama sai ki bata."

           Murmushi nayi sannan na cigaba da cin abincin.
"Ban san sunan ka ba, lokacin sallah yayi?"
"Taya kika san lokacin yayi."
Murmushi nayi mara sauti sannan nace mishi.
"Ka duba sararin samaniya, rana ta raba tsakiya."
"Toh Malama!
Haka muka yi ta musayan kalaman har muka iso garin, kallona yayi sannan yace min.
"Daga yanzun zan miki aika kuma zai zo har inda kike, domin nayiwa Amir Rahil alkawarin zan kawo mishi sabuwar baiwa, kiyi amfani da wannan damar ki kashe min shi.

    A sanyayye yadda kowa ba zai kawo hakan ba a ranshi, ina son kiyi aikin nan da wata uku, ki shiga jikin shi yadda babu wanda zai iya fahimtar kome."

    Gyada mishi kai nayi, sannan muka shiga cikin birnin da ake kasuwanci, kamar ba gobe. Gaskiya garin yayi min kyau, dan haka ina kallon shi har aka nufi gidan sarautar kasar damu.

    "Karki manta kiyi abinda ya kawo ki karki yi tunanin fadawa wata damuwar da zata saka mu hadu a fada."

       Gyada mishi kai nayi, tare da jin son garin da yanayin garin yana shiga na, sai da muka ratsa wani gida, muka ci abinci, sannan muka nufi fadar kasar.

     An shiga damu, har cikin fadar musamman yadda muka yi shiga na tukurun bayi, muna zuwa muka zube a gaban wani dattijo, wanda yake buga mulki kamar me,

        "Amir Sulaiman, har ka dawo daga tafiyar da kayi?" Wani a gefen zubewa gaban Mutumin sannan ya ce mishi.
"Sultan Mu'allim na dawo daga tafiyar da nayi, da fatan zaka saka amshe ni hannun biyu biyu"
Ya faɗa cikin taushin murya.

        Kallon shi wasu daga cikin yan fadan suka san halin shi, kallona suke, sannan wasu suka dauke kansu.
"Yarinya daga wani yanki na duniya kike?"
.kallon shi nayi sannan na sunkuyar da kaina, domin ya bani damar magana.
"Daga yankin Afirka ta Tsakiya."
"Meye sunanki!"

"Salwah!"
Kallona suka yi kafin suka ce, min.
"Ita kuma wannan wadar ba?"
"Jasmin"
Na fada a takaice, ina me sunkuyar da kaina.

"Ku kaita shashin bayi kafin a kaita inda zata zauna. wato shashin Sultan Rahil"
"Yanzun za ayi yadda kace"
Haka suka tasa keyar mu, har shashin bayi, muna shiga suka shiga mana dariya, ban yi mamaki ba, sai dai ita Izmah sai ya zama kaman cin zarafin ta suka yi..dan haka na rike hannun ta.

      Nuna mana inda zamu zauna akayi sannan aka bamu abinci, na saka hannu zamu, fara ci wata cikin yan matan dakin, tana sanye da jan kaya. Ta kai min duka.
Ban kulata ba,. Na turawa Izmah abincin cikin tsoro ta fara ci, sake kawo min dukka tayi na buge kafarta tare da kai mata duka, sai da kashin kafar yayi tsawa.

"Wayyo Allah! Kafana!"
"Ba rigima nazo nima ba, kowa dan haka ku shiga hankalin ku, nasan halin ku na bayi, dan haka kar wata ta kuma d'aga min murya. Dan zan karya kasusuwan ku!"

"Toh mafadaciya! Sake mata kafarta, ki shirya a kaiki shashin Amir Rahil."
"Toh!" Na sake kafar sannan muka fara cin abincin, muna gamawa na mike tare da nufar hanyar ban daki nayi wanka da alola, ganin na fito zan gabatar da sallah duk sai jikin su yayi masifar sanyi, suka shiga kallon juna ina idarwa nacewa Izmah.
"Muje na taimaka miki kiyi wanka!"
Haka na taimaka mata tana gamawa na fito, nuna mata gurin kwanciya nayi sannan nace mata.
"Ke Yar masunta, duk wacce tayi miki shirme kiyi mata yadda kuke watsawa kifi koma a ruwa. "
Da sauri matar ta leko tana kallona, cike da mamaki rabonta da taji murya irin na shi kusan shekarar ashirin da biyar kenan, ajiyar zuciya ta sauke sannan na fito ina tafiya tana waige na. Har muka fito shashin,.wato akwai wata dabi'a da Abba yake yi, a duk lokacin da ya shiga damuwa, zaka samu ya kai hannun shi baya, yana tafiya. Wannan dabi'ar nakanyi lokaci zuwa lokaci.

       Amma ban maida shi ya zama abin dogara na ba, kawai yau na tsinci kai na dayin haka ne, aikuwa ina yi naga abun mamaki, domin duk inda muka wuce Ni ake bi da ido. Da gudu wani mutum yazo ya janyo Ni bayan wani lungu. Zuɓewa yayi a gabana, tare da cewa.
"Ban san ki ba, amma tabbas jinin Ahalin Mu'allim yana yawo a jikin ki, wacece ke?"

      Kallon rashin fahimta nayi nashi sannan na juya tare da nufar matar, har muka isa gidan da zata kai ni.

Babban gidane me dauke da manyan dakaru, a hankali na shiga bin bayanta na sami dakarun gidan dukkan su a tsaye, wai ana wasa da Amir Rahil. Sai ihu suke suna tafa mishi.

Shi kuma ya rufe fuskar shi da farin kyale yana niman su, ashe ita matar ta koma gefe, dan laifina a katse wannan haukar.ni kuma ban lura ba, sai ji nayi an kamani tare da sake wata zazzakar murya kamar ba namiji ba.
"Ahah na kama waye?"
Hmm, mara mutuncin kawai sai ji nayi ya kai hannun shi kan nonona ya matsa tare da dumbular shi. Har cikin raina naji zafin abin ban san lokacin da na murɗa hannun shi tare da buga shi da kasa sai da ya fasa wata irina kara, sake juya kan hannun nayi zan karya.
Suka samun takobin akan wuyana.
"Kin san waye kika daka?"
Zubur ya mike tare da zare idanu, yana me cire kyallen a fuskar shi, sannan ya kura min ido.
Gefen bakin shi yana fidda jini, sauke wata irin numfashi yayi, tare da kallon yadda nake fusace.
"Durkusa! Ki bashi hakuri kafin a hukuntaki!"
"A'a barta kawai, a gaban waye ta kayardani? Shin kun gani ne?"

Girgiza mishi kai suka yi sannan ya fashe da dariya kafin ya kira su dukkan su duka koma baya tare da cewa.
"Kunsan m....
Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: Monday-March-2021
FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

07
"Toh tunda babu wanda yaga lokacin da ta makani da kasa a manta batun, kuganta sai kace wata namiji, dan haka muje muji meke tafe da ita."

Ya basu hannu suka tafa, sannan ya zo inda nake tare da goge jinin bakin shi yana faɗin.
"Hmm! Zan miki afuwa sai kin bani hakuri?"
"Hakuri?"
Na kuma tambayar shi, kallon masu tsaron shi yayi sannan ya kane musu ido, yace musu.
"Ko ba haka ba?"
"Eh ki bada hakuri sai mu kyale ki"
Ganin suna b'ata min lokaci nacewa matar.
"Ko zaki taimaka ki kai Ni shashin yarima Rahil!"
Cikin wani irin jin dadi ya gyara kwalar rigar shi, tare da kallon na ya nuna min kanshi da hannun shi yana faɗin.
"Gani nan"
Kallon shi nayi cikin mamaki nace mishi.
"Kai?"
"Baki yarda bane?"
Ya kuma dawo min da tambayar yana gyara hannun rigar shi, alamar shine fa, takaici ya sani cewa.
"Toh yanzun naji nayi laifi kayi min afwa"
"Na miki! Amma da sharadi!"
Kallon shi nayi sannan nace mishi.
"Name fa?"
"Zaki nuna min wani abu ne me laushin da na tab'a."
Suke fuskana nayi tare da kaiwa kafarshi wani mugun taku, sai da yayi ihu. Sannan na kyale shi.
"Baka da da'a ne? Ina mace kana tambayana abinda ka tab'a a jikina ai sai a rena ka" na fada mishi kasa kasa.

       "Kuma haka ne fa," yana kallon mutanen shi. Sannan ya gyara muryan shi yana faɗin.
"Wacece ke? Kuma waye ya turo ki?"

    Da sauri matar tazo sannan tace mishi.
"Sunanta Salwah daga tsakiyar Afrika, Amir Sulaiman ne ya kawo maka ita"

   "Salsabila! Sunanta daga yau. Dan tafi dacewa da sunan. Sannan mu shiga daga cikin gidan."
      Ya faɗa tare da goya hannun shi a baya, abun sai ya bani mamaki da dariya, wato shima yana yi, share batun nayi har muka shiga cikin gidan, muna shiga muka sami ana ta aiki, haka yayi ta bin bayin yana make musu duwawun su, tare da zuba musu dundu a baya.

      Da zafi amma haka suke dariya, ya kai kan wani dattijo kenan na buge ganin shi sai da ya saka kara.
"Toh kuma meye nayi miki?"
Ya faɗa a shagwaɓe, har idanun shi yana kawo kwalla,

   "Wannan abun da kake babu kyau rashin da'a ce, Allah bai baka mulki dan ka wulakanta rayuwar wasu ba, Allah ya baka ne dan ka sama abun tausayawa a gare su ka Fahimta?"

    Fuuuu ya wuce abinshi yana kuka. Kallona suka yi dukkan su, tare da cewa.
"Mun gode!"

       Share su nayi tare da nad'e hannuna a kirjina ina kallon gidan, yadda suke aiki. Babu juyawa ina tsaye har sai da yamma tayi sannan ya fito sanye da kananun kayan mutanen ketare.
"Ke zo nan" ya kirani.
Ba musu na isa gaban shi, kallon shi nayi sannan yace min.
"Don Allah yaushe zan fita daga wannan yanayin? Ni ina son nayi rayuwa kamar kowa amma kullum Kaka rufe Ni yake yi! Kisan sabida me?"

  Kallon ko ina yayi sannan yace min.
"Sabida yaran Kaka Uku maza kashe su ake yi, An kashe Kawuna Almustapha! Sannan an kashe Me bin shi Abubakar! Sai Abba na sa ake kashe shi a shekara goma da suka wuce. Kuma sabida mulki ne, don Allah dube ni fa, ina son nayi rayuwa kamar kowa amma an hanani, Kinga kisan yadda zaki yi mu fita cin kasuwan  dare don Allah!"

Ya faɗa a shagwaɓe, kamar zai min kuka.
Kallon shi nayi tare da hango yar tusar jakin da yake kunnen shi sak da na Abba na. Murmushi nayi sannan nace mishi.
"Ban san yadda zaka fita daga gidan nan ba, kayi hakuri Amir Rahil!"

     Kamar ya saka kuka haka ya kalle ni, sannan ya dauke kanshi kafin can ya sake min kuka. Har da ihu, share shi nayi tare da juyawa na fita daga gidan. Na nufi hanyar gidan da nafito.

Ina juya labarin da ya bani.
"Zaki iya tafiya da kome yadda kike so! Idan ma zaki iya shiga jikin shi duk ba laifi, amma maganar gaskiya bana son aikina ya wuce wata uku."

         Juyawa nayi na kalli mutumin sannan nace mishi.
"Ba a min dole aiki tunda nice nace zanyi toh a zuba min ido."

                    Kallona yayi sannan ya share tare da nufar hanyar shi na daban, nima nufi gidan nayi. Ina shiga na hango Izmah a kwance a tsakar dakin babu kaya, kowa yana harkan gaban shi. Da sauri na isa gaban ta, tare da cire mayafina na rufe ta dashi, sannan na kalle ta tana kuka. Irin wanda aka tozarta.

          Taune bakina nayi ina kallon matan da suke tsaye tare da rike bulala sannan daya daga cikin su tana faɗin.
"Eh munga Wada ce kuma tana da kayan mamaki shine muka duba ko tana da budurcin ta har yanzu."  Fashewa tayi da kuka tare da rungume ni.
"Ki mai dani Gulsana, na hadaki da Ubangijin ki!"

      Matse kanta nayi a kirjina, ina tuna alkawarin da na dauka a raina.
_Ya Allah kamar yadda ka Hadani ƙaddara da wannan Baiwarka Ya Allah ka bani ikon kare lafiyarta daga duk wani abin cutarwa daga nesa ko kusa_

"Ban san me yasa mutanen duniya suke da zalinci a ransu ba, hmm" nayi wani irin murmushi. Sannan na dauke ta tare da ajiyeta a saman gadon mu, duk da tana da zuri amma dake zuciyata tana zafi bana jin kome a raina.

    Rufeta nayi sannan na koma na rufe kofar d'akin, tare da kashe wutar dakin da gayya, ban tab'a sanin cewa zan iya wannan b'arnan ba, sai da aka kwashi awa daya da rabi, sannan na koma gurin kwanciya ta, lokacin sunyi ihu har sun godewa Allah, sabida na rufe tagogin dakin. Sannan na koma nayi kwanciya ta a gefen Izmah, raina a b'ace.

   Haka na kwana ina kallon duk wani motsinta, kiran sallah farko ya tadda Ni nayi alola da gabatar da sallar asuba, ina idarwa nayi mata wanka, sannan na nufi gurin amsar abincin. Anan me bada abincin take tambayar yan dakin mu.
"Me ya faru daku ne haka?"
Kallona suka yi tare da ganin yadda nake hada abincin mu. Sannan na dauki tire na jera.

     Nazo zan wuce wasu kartin mata suka sha gabana, sunkuyar da kai Masu bamu abincin suka yi. Ajiye abincin nayi sanan na mikar da hannuna kashin hannun suka yi kara.
"Cikin girma da Arziki ku bani hanya na wuce, idan ba haka ba, al'adu zasu fiki daraja." Na fada ina murmushin mugunta.

"Toh me zai hana karamar yarinya!" Dariya nayi sannan na kalle su, rufeni suka yi da dukka gabaki daya dakin yayi shiru, sai karan sautin duka kawai yake tashi, a hankali na mike tare da ture su na dauki abincin mu, na fashe da dariya.
"Bana rena mutum, sabida ban san baiwar da Allah yayi mishi ba."

              Nayi tafiya ta, kamar danyen nama haka suke ta zuɓewa a kasa.

         "Kunga Yarinyar nan Shaidaniya ce! Idan kuka Cigaba da tab'a ta zaku fuskanci tashin hankali. Dan haka ku kyaleta horarriya ce, tasan me take yi." Inji wani me tsaron shashin bayin.
Zama nayi na kalle ta, sannan na bata abinci. Kallon yan dakin mu nayi suna ta ficewa a hankali kamar munafukai, sannan na kalle Izmah, nace mata.
"Meye ke damunki?"
Cikin zubda kwalla tace min.
"A cikin matan nan ne akwai wata me halitta biyu! Itace ta dauke min kimata, Ikram haka tayi ta saduwa dani tun bayan fitar ki, Don Allah ki nema min guba nasha na rantse da abin bauta gwara Firoz yaji labarin mutuwa ta akan yaji labarin abinda ya."

         "Mutuwa ba ita bace karshen wasu abubuwan, ita din mafarin wasu abubuwan ce, a cikin matan da na daka bata cikin sune!". Kuka take tare da rike Ni tace min.
"Bata nan, daga wani daki take zuwa."

              "Lallai sun tab'a me tsada, kuma zasu biya a furashi me tsadar biya, dan haka zan fita idan nafita zan kai kamar minti goma, zan dawo."
"Ina jin tsoro!"

     "Kina tare dani, Ni kuma ina tare da Allah,tsoron me zaki ji? Kwantar da hankalinki, zanyi kome cikin tsarina." Na gaya mata bayan na gama bata abinci sannan na gyara mata kwanciya, na kalle su babu kowa a dakin. Fitowa nayi sannan, na fita abuna.

            Tsayawa nayi a waje tare da jiran wani lokaci, ina nazarin abinda zan musu. Har na kwashe mintotin, sannan na kuma shiga cikin gidan, ina zuwa na sami kofar a rufe an bar mutum daya a waje, tun daga nan na fara cin ƙwallon Ubanta, har muka shiga cikin dakin.  Sun bankare ta ita kuma Yar iskan tana tsaye da surar maza.
     Rufe dakin nayi tare da jan wani katako na karya. "Hmmmm!" Nace musu, sannan na nufe su. Da farko sun zata zan ji tsoron karka su rufa min ne, ya sani tsayawa, nan kuwa gyara zaman katakon nayi.

    Sai da na karya hannun da suka rike ta, ita kuma mata mazan nayi mata dukar kare dangi a gabanta, sannan na juya abuna, na kula da lafiyar Izmah, bude kofar aka yi.

     Masu kula da shsshin mu ne suka shigo, nan suka tambaye ni, murmushi nayi sannan na nad'e hannuna a kirjina.
"Toh me zan ce muku? Kun barwa bayi damar suyi yadda suke so! Sannan a cikin gidan da mata suke kun bar mata maza tana rayuwa. Ku gyara ko na gyara kowa zama a cikin gidan nan."

          Murmushi nayi sannan na juya na cigaba da abinda nake, ina gamawa na juya tare da kallon Izmah, fita aka yi da matan sam na manta da Amir Rahil.

      ~~~
Kallon su yayi tare da cewa.
"Hanyar yanzun Salsabila bata zo ba? Ku duba min ko tazo"
"Ran shi dad'e! Bata zo ba."

Kasa zama yayi ya kuma sake tuma tsalle can, zai kai musu duka. Kamar wanda ya tuna ya meda hannun sa baya. Tare da kallon su.
"Yallabai kaci abincin ka."
"Kaniyar Abincin! Da shegen kwalkwal dinka, maza wuce da fuskar shi kamar abinci. Yarinyar zaku."

"Amir ga Almirah Laylah tana zuwa."
"Kuce ta tafi bana son ganin ta."
Haka kuwa suka hanata shiga cikin gidan, ya daura daya akan daya, yana jiran Ikram, har rana ya fadi bata zo ba, sai yaji babu dad'i kawai ya share ba tare da ya kuma nuna damuwar shi ba.

     Washi gari
Haka na tashi tare da kammala kome, sannan na rike hannun ta, muka nufi gidan Amir, tun a hanya take tambaya.
"Ina zamu?"
"Inda aka kawo ni aiki."
"Me yasa yau sai dani?"
"Karki damu, hakkin kula da lafiyar ki yana wuyana ne!"
Muna isa aka bude kofar, yana tsaye hannun shi goye a bayan shi. Kamar sakarai haka yazo ya tsaya min.
"Yanzun don Allah abinda kika yi ya dace, ki ajiye mutum kama na baki zo ba, gaskiya baki kyaita min ba."

Wallahi baya had'iye yawu, haka yake ta magana kamar na zubda kwalla, Izmah kuwa dariya ya bata. Hannun nakai bakin shi, tare da cewa.
"Ya isa haka!"
Lumshe idanun shi yayi tare da kallo na, gabaki daya ya tawo zai zube min a jiki tuni na kauce na bashi hanya ya zube a kasa.
"Ke mahaukaciyar ina ce? Amir Rahil kika sake ya fadi."

Mutumin ya faɗa da gudu rike da bulalar shi, sai da na bari ya tawo na mishi kwaf daya. Na gyara wuyana tare da cewa.
"Duk wanda ya ce zai min hawan kawara Ni kuma zan shayar dashi nono uwarshi!"
Mika mishi hannu nayi ya mike tare da kade jikin shi.
"Waye yace muku itace ta sani na fadi? Salsabila babu ruwanta da kome ko?"

Ya kalle ni yana murmushi, tare da wangale min baki, sha-sha-sha kawai. Na fada a raina, sam bai da wata Izza irinta me mulki, sakarai lamba daya shine wannan amma kuma son shi masu aikin shi suke, Ni kuma....

```BOOK one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```

#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: Monday-March-2021
*FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

08
"Sakarai kawai" na fada da harshen swahili, juyawa wani dattijo yayi tare da cewa.
"Kema kin iya swahili ne?"
Kallon juna muka yi da Izmah sannan muka sake murmushi, muka ce mishi.
"Eh!"
Ai kuwa muka shiga hira dashi sama dama, duk da nikan ba sosai nake magana ba, amma Izmah kamar taga yan uwanta, haka suke hira. Kamar wani dolo ya tawo gurina ya tsaya.

Wangale min baki yayi irin hee (😬) zunzurutun bakin ciki kamar zan mutu, dan har da kai hannun shi kafadana yana dariya, da gudu ya jani muna nufi bayan gidan shi, kamar babban mutum haka suka shirya mishi gurin lambune, muna zuwa ya ture ni na zauna sannan ya zauna tare da cewa.
"Bani labarin garin ku"
Ina ƙoƙarin mikewa ya daura min kanshi akan cinyata, yana faɗin.
"Duk wanda kika ganshi anan yayi zama na amana da iyayena ne. Salsabila! Daga ganinki naji zuciyata ta kamu da kaunarki! Kuma naji ina kaunar na gaya miki halin da nake ciki.

     Duk da kowa da yadda zai dauki rayuwar shi, amma rayuwata ta tana da muhimmanci a gurin kakanina.

          A cikin dakin su mahaifina na, saura Autar su Abba ne yanzun Amirah Raziyana, babu kowa duk sun kare.

    Sultan Mu'allim Abdulkarim, shine cikakken sunan kakana, yana da mata biyu, da Kwarkwarah daya. Sultanah Balkisu Ikram itace uwargidan shi, sai Amaryan shi Ummu Kulsum, matar tsohon sarkin nan garin ne, me suna Ahmad.

    Yana da yara maza hudu, da mata biyu,
Yaran Balkisu sun Hada da Almustapha shine babba, Abubakar me bi mishi sai Aliyu, Abbana kenan, sai Autar su Raziyana.

          Dakin Ummu Kulsum, akwai yara maza huɗu mata biyu, Sulaiman shine babban, sai Usman da Yahya, sai Isah.

           Khalilah itace ke bin Isah  da Nana A'ishah, dakin kwarkwarah shi kuwa akwai. Kamaliyah a yaki aka kawowa Sultan Mu'allim, tana da yara Biyu Abdullahi da Abdul Rahman, , Sultanah Balkisu Ikram, yar kasar Habasha ce, daga garin Minalik, mahaifinta sarki ne a can.

     Dan haka..."
Barci ya cigaba da yi, naji zafin barcin shi gaskiya dan naso jin karshen Labarin shi, amma haka na hakura tare da dauke kai na..
  
Sakarai barci yayi abin shi fa, haka na gama duba ko ina na gidan ban ga kome ba, ina tsaye a bakin kofar fakon aka yi sanarwar Sultan Mu'allim ya zamo ganin jikan shi.

       Durkusawa nayi tare da gaida shi. A hankali ya taka har gaban Amir Rahil, wanda yake barci saman kilishi, shafa kanshi yayi sannan ya kalle ni. Kai na a sunkuye.
       "Yar nan! Don Allah Karki cutar dashi. Bai da laifi ko daya, naji ance tunda kika zo kike dukar shi, don Allah karki kuma ɗan nasan ba zai bari a hukunta ki ba, tunda har ya iya gayawa mutane baki mishi kome ba. Toh dan Allah karki mishi kome, idan turo ki aka yi Ni na dace da hukuncin ki ba bashi ba."

   Cikin girmamawa na ce mishi.
"Allah ya taimake ka, wallahi babu kome a raina, ina haka ne dan na tuna mishi nauyin da yake kan shi, kayi hakuri ba zan kuma ba."

    Mikewa kakan yayi sannan ya tawo gaba na,yana faɗin.
"Jikana amana ne a gare ki, gashi nan yana kwance kuma barci yake yi don Allah."

        Sake matse hannun na nayi cikin wani irin yanayi, sannan nace mishi.
"Insha Allah!"
Sannan ya fita daga gidan, kallon Amir Rahil nayi kamar na rufe shi da duka. Haka nake ji, sabida ina zaman lafiya an kuma kara min nauyin shi. Lokacin Sallah yana yi na wuce nayi sannan nazo na amshi abinci na kira Izmah da ta sami Abokan hira sai hira suke abun su.

          Zama nayi muka fara cin abincin, muna hira nan take gaya min tana son zama da Iyalan tsohon nan dan taga da tafi sakewa dashi, a duk lokacin da suke Yaren swahili. Kallon shi

Please Login or Register in order to submit comment