Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana faɗin.
*Magulmaciya zaki gama gulmarki! Amma tabbas yau naga abinda kike boyewa ina jiranki,*

      Haka muka yi ta zaga garin har kusan tsakiyar dare sannan ya dawo dani gida, tun muka iso yaga ina hamma, zama yayi tare da kallon yadda nake kokarin shiga daki yayi, ganin zan gudu na barshi ya sashi finciko ni.
"Ni barci nake ji!"
Zaunar dani yayi tare da saka kaina gefen kafadar shi, bai ce min kome ba, bai kuma nemi nayi magana ba, hannun shi a cikin nawa, yana murza yatsuna. a hankali har barci ya dauke ni me karfi.

            Yana zaune a gurin, har aka fara kiran sallah farko, kafin ya dauke ni zuwa cikin ɗakin ya kwantar dani, ya ja min bargo. Tare da shafa fuskana, sannan ya juya ya fita daga dakin. Dake na gaji sosai ban ma san har ya kawo ni dakin ba, sai da Nimrah ta tashe ni daga barcin sannan na mike a hankali na nufi ban daki nayi alola, bayan na idar da sallah ne na kalle su.

   Sun sayi abinci, tare da zama suna hirar yadda suka sha yawo da Fudail, ban saka baki a maganar su ba, sai da naji suna cewa.
"Amma naji ance kamar an samu yar karamar rikici, tsakanin Amirah Jasrah da tawagar Sultan Mehran, wai da gaske ne?". Bude idanuna da yake cike da barci nayi sannan nace.
"Ki tambayi Aamaan Mehran,!"
"Kai Ikram amma baki da kunya kowa Sultan Mehran yake kiran shi ke kuma Aamaan Mehran, sai kace sa'arki!" Tab'e baki nayi sannan nace mata.
"Aamaan Abdus Samad kike magana akan shi." Na fada tare da dauke kaina ina murmushin mugunta, dan naga yadda suka gwalallo idanu waje, na kuma sake samun damar na kwafta rashin mutunci a silalle.

"Wai Aamaan Abdus Samar kuke faɗa?' kasa amsa min magana ta suka yi suna kallona, tare da cewa.
"Dama haka kike baki da mutunci?"
"Gado nayi a gurin Wancan d'an bakirin" na fada ina murmushi,

Watsewar zabi sukain tare da min fatar shiriya, dan ganin mahaukaciya suke min.
~~~
Karyawa Mehran yake bini bini yana sake murmushi, gyara zama Sultanah tayi sannan tace.
"Sultan dina anya baka fara soyayya ba?"
Ya kuma sake murmushi a karo na babu adadi, yana daukar soyayen kwai ya saka a bakin shi yana me sake murmushi me sauti.
"Fudail meye gaskiyar magana yau kimanin kwanaki masu yawa bana ganin shi da maraici,idan ya dawo kuma zai ta sake murmushi wacce barauniyar ce tayi sa'ar sace zuciyarshi?"

     Kallon juna suka yi tare da dauke kai.
"Nifa kamar uwace! Idan baku gaya min wacece ita ba waye zai gaya min?" Ta tambaye su. Sake kallon juna suka yi kafin suka shiga kallonta an rasa wanda zai gaya mata gaskiyar maganar.

    Murmushi tayi sannan ta cigaba da cin abincin ta, tana me cewa.
"Ikram itace mafarkinka, ba zanyi mamaki idan nace maka nasan tana cikin lardin nan ba, amma kuma ban san me ya dawo da ita ba, dan nasan dai haka kawai ba zata zo ba sai dan daukar...." Zuba mata ido yayi tare da rike cokalin hannun shi da mugun karfi har sai da ta lankwashe.
 
    "Karka damu! Ni ba a zalimar mutum bace, ina bawa kowa ra'ayin shi." Matsanancin kunya ce ta kama shi, tare da kasa kallon kallonta. "Toh Fudail idan Shugabanka yayi aure kai waye zaka aura?" Diriricewa yayi ya kasa tsayuwar guri guda, sai kallon gefe da gefe.
"Nimrah" Mehran ya faɗa a sanyayye, kamar bashi yayi maganar ba, da sauri Fudail ya bar falon.
"Dawo nan! Kayi min bayani daga ina take."
"Sultanah tare suke da Ikram!"  Inji Darda,
"Hmm!" Ta faɗa tana murmushi, Mehran kan kasa cin abincin yayi, duk ya takure guri guda.

       "Bari na baka guri" ta faɗa tana murmushi, "hmm" yace mata, tana jinjina wannan karfin halin shi, toh ya yake yi da Ikram dan hira tsakanin mafadaciya da Miskili irin Ikram akwai matsala, dan kowanen su gwani ne akan halin shi, zafi da sanyi zasu haɗu guri daya, murmushi tayi a karo na biyu. Sannan ta shiga d'akinta. Tana zama tana son ganin Uwaisul Qarni, dan haka ta shiga addu'a kafin can tayi imani da Allah sannan ta ambaci sunan shi.
               Cikin hukuncin Ubangiji ya bayyana a gaban ta, a saman fatar damisa. Yana murmushi.
"Ikram!"  Cikin girmamawa tace mishi.
"Barka da warhaka Baba na, eh itace!" Kallon tausayin yayi mata tare da girgiza kai, tare da cewa.
"Kiyi ta addu'a, Allah ya taikaita tashin hankalin da yake tare da alaƙar su."  A hanzarce tace mishi." Akwai damuwa ne?" "Idan Ubangiji ya so al'amarin shi, babu makawa sai ya faru, duk abinda yazo muku, ku amshe shi da hannun bibiyu, a duk inda ƙaddara take, toh yana da kyau bawa ya amshe shi hannun bibiyu, Wani al'amarin dole sai Ubangiji kadai zai warware miki shi, SOYAYYA ce me tattare da kalubalen rayuwa, soyayya ce da kema idan baki yarda da Allah zaki iya shiga al'amarin Ubangiji, soyayya ce me cike da raunin zukatan al'umma. Soyayya ce da zata kashe masoya ta kuma raya makiya, ban tab'a ganin irin wannan al'amarin ba, duniya cike take da kalubale, rayuwa cike take da tashin hankali. Wallahi babu wanda ya isa goge zanen ƙaddarar da ya zana. Dan haka karki yarda ki shiga wannan lamarin." Hawaye ne ya zubo mata, tana faɗin. "Yanzun babu hanyar da zan dakatar da wasu abubuwan?" Murmushi yayi sannan yace mata. "Eh mana! Kin isa ki aikata abinda Allah ya ƙaddara? Baki isa ba? Baki da ikon tafiyar da rayuwar wasu, kiyi addu'a, kiyi hakuri karki yarda wani abu ya shiga tsakanin wutar da zata kono a tsakanin wasu, karki yarda wasu su fahimci cewa akwai wutar da ya kama a cikin gidan ki." Ya faɗa tana tsare ta da idanu, kasa tayi da kai. "Nasan kina kaunar Ikram, dole wata rana zaki iya Mantawa da wannan tunanin, nasan zaki iya juyawa kome baya domin wani dalili, ina tausayawa lokacin da wasu abubuwan zasu juyawa wasu dalilai baya, na tausayawa tafiyar da za ayi ta a cikin tsananin zafin sahara, babu ruwa babu Uzuri, rayuka zasu koka zuciya zata kasa jure kome, tunani zai tsaya cak. Mafita zata yi ƙaranci, ba lallai bane na riski wannan yanayin, bai zama tilas na san lokacin ba. Domin lokacin tafiya na ya kusa, zan tafi baki daya." Ya faɗa a sanyayye, yana me juya kanshi ya ce mata.
"Idan irin wannan lokacin ya riske ki, kiyi kokarin maida alamarinki ga Ubangiji, Insha Allah Ubangijin zai amsa miki kuma zai kawo miki ɗauki, karki yarda a juya miki nazarin ki. Insha Allah zaki yi farin cikin samun Ikram a rayuwarki."

Gaba daya ta rasa abin cewa, ita kanta tausayin kanta da kanta take ji, dan haka har ya tafi bata iya fahimtar kome ba, sai hawayen da take zubdawa.....
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

31

Ita kanta bata san iya adadin lokacin da ta dauka tana kukan  tashin hankali da damuwa wanda bata san daga inda zai ɓullo mata ba, alola ta mike tayi tare da gabatar da sallah nafilla, ta jima tana kaiwa Allah kukanta,  kafin ta fito daga dakin. Sam bata jin dadin ranta, tana fitowa ta sami Shairah da Narjis suna magana akan zab'en da za ayi, da yadda ake shirya bikin domin Fudail ya gabatar musu da wasu abubuwan da  za ayi. Suna ganin Sultanah suka yi shiru.
"Meye Mehran ya sauya a cikin tsarin?" Shiru suka yi tare da kallon shi.
"Sultanah dama ya ce a cire maganar lallai sai anyi gwajin budurci ne?" Shiru tayi sannan tace musu, "babu wanda zai goge abinda aka kafa, dole yabi tsarin masarautan" ta faɗa musu,  "amma Sultanah!" Suka fadi haka lokaci guda. D'aga musu hannu tayi sannan tace musu. "Dokar masarautan ce,bai isa ya take ta ba, ko Ni da na haife shi ban da ikon karya dokan balle shi din banza, doka ce babu wanda zai karya ta"
"Toh Sultanah" haka ta zauna bata ce musu kome ba, ita dai wallahi da ana sauya ƙaddara tabbas da ta sauyawa Ikram da Mehran, sam ta rasa mafita lumshe idanu tayi tana nazarin me ya dace tayi ba tare da ya shafi rayuwar su ba. Sannan taya Ikram zata kashe masoya ta raya makiya. Ga baki daya ta rasa tunaninta. Dafe goshin ta tayi kamar wacce take fama da ciwon kai. Nan kuwa ƙwaƙwalwar ta ne yake aikin hargitsa mata lissafi.

  ~~~
Shiru suka yi tare da kallon Mehran, kafin suka shiga kallon shi an rasa wanda zai gaya mishi dalilin kiran shi fadar, asalima duk sun razana da yadda yake muxurai.
"Sultan MEHRAN yana da uzuri fa!" Fudail ya gaya musu, "kai d'an mashawarta waye yayi dakai?" Murmushi Fudail yayi sannan yace mishi. "Darakshan! Bani da abinda zance maka, amma wata rana zaka biya ladan aikin ka" sannan ya kuma duban mutanen fadar yace musu. "Wani dalili kuke niman Sultan Mehran?"
"Shi Sultan Mehran bai da bakin Magana ne inji Sultanah Hoyam?" Ta kalli Mehran, wanda kanshi yake sunkuye yana matsa hannun shi, kamar baya fadar. Kuma har ila yau sun kasa fadar abinda yasa suka nime shi, kasancewar ya zabga musu gargadi tun lokacin yakin da yankunan jazziratul Arab suka nemi shiga musu, ya dakatar.
Dayawan su dattijai ne, da suka manyanta amma kasuguman munafukai ne. Dan haka da gayya yaki magana kuma dole sune zasu fadi dalilin da yasa suka kira shi, amma kuma babu wanda yake da zarrar bude baki yayi magana.

        Abin dariya sai wannan ya zunguri wannan, shi kuma ya zunguri na kusa dashi haka sukai tayi, karshe Amir Hood ne yayi shahadar kuda ya mike tare da cewa.
"Jiya Jasrah ta gaya min cewa taga Sultan Aamaan Mehran da wata mace wacce taci mutuncin shi a cikin masarautan nan, sannan ta keta Alfarmar masarautan nan akan idanun kowa bayan ta kasance daya daga cikin fadar nan, shin Sultan Aamaan Mehran ya yarda da ita ne har ya iya yafe mata, ko ba saurayi ta bi ba? Sannan kuma ba girman SULTAN Mehran bane yana yawo cikin gari da kaskantacciyar baiwa a cikin jama'arsa,  kar Sultan Mehran ya manta yana cikin dokar hana fita ne me yasa zai karya doka ko ya manta akwai Amirorin da suke jiran ya bada kayan bikin fitilar al'ada a kai musu, amma anga kaya masu daraja a jikin Ikram da kawayenta shin wata irin matsayi take dashi haka? Sannan abisa al'ada ba a yarda wani sarki ya auri macen da tayi mu'amalanci wani namijin ba, kuma ta bayyana ƙarara Ikram namiji tabi, sannan kuma dokar masarautan nan ne, babu batun auren bazawara ko karuwa mafi munin lalacewa ace Sultan Aamaan Mehran ya kwana a gidan ƙaruwai, wannan Zubewar mutuncin masarautan nan ne, mafi munin abu ace Sarki Guda ya kwana a gidan Ƙaruwai? Don Allah ku duba wannan lamarin"
   
                Lumshe idanun shi yayi yana jin kalmar karuwa da ya danganta Ikram dashi, jin yadda kalmar take dukar shi kamar ana saka bulalar k'aya karfe. Idanun shi yayi jajjur. Mikewa yayi tare da sauka akan kujeran shi dake fadar,.Yasaka kai zai fita daga fadan."kai waye da zamu yi magana ka mana shiru?" Suka daka mishi tsawa,  wannan shine girman kuskuren da suka aikata mishi, dan haka ai ance shiru ma magana ne, dan haka ya fice daga fadan. Tunda yake babu wanda ya tab'a gaya mishi abinda ya saka shi bakin ciki sama da kowa ba, dan haka koda ya koma gida, Daki ya wuce ba tare da kalli inda Sultanah take, tunda ya shiga dakin bai kuma fitowa ba, domin kuwa baya son magana, fahimtar haka da Sultanah tayi yasa ta hana kowa yayi wani abun da zai saka ayi hayaniya ko wani magana me karfi.

      A bakin Fudail suka ji labarin abinda ya faru, tashi tayi tare da shiryawa tayi zata fadar Fudail ya ce mata. "Sultanah a halin da yake ciki baya son karin damu, matukar zaki nufi fadar toh ba makawa kin lalata kome, dan haka ki zuba ido kiga abinda ya shirya. Yakin masarautan nan Sultan Aamaan Mehran ba zai iya shi daya ba, sannan kuma ke idan kika shiga mishi zasu iya aikata wani abu kuma su makala miki, ni tsorona daya karsu kaiwa Ikram hari domin kuwa zasu aikata haka kuskuren da zasu damu da kansu." Ya fadi haka a raunane, domin yasan haka ce zata faru. Idan ba wani ikon Allah bane ya hana faruwan haka.
     Numfashi ta sauke tare da kallon shi tace mishi.
"Ina Ikram din take?"
"Tana wajen garin SAMAIND!" "Toh ka kai mata dauki mana, ko a tura mata dakarun da zasu kula da lafiyarta ".

"Karku fara haka!" Ya fadi hakan lokacin da ya fito daga dakin, yana me shirin barin gidan.
"Akan me?"
"Ba mace kawai bace ita!" Yana gaya musu haka ya ficce daga gidan baki daya, can wajen gidan ya nufa, dan baya son abinda zai tinzira zuciyar shi. Cikin yanayin bakin ciki yake kallon dajin, da yadda kome yake zaune cikin tsarin Ubangiji da ikon shi, yau yayi danasanin kasancewar shi daya daga cikin gidan sarautar ƙasar shi.

        Damuwa tayi mishi yawa, bai san ta lokacin da ya b'ata a gurin ba, kuma ba zaka tab'a tsammanin yana gurin ba, dan ya saje da gurin baki daya, ya rasa inda zai cusa kanshi. Dan haka da ya gaji da zama ya mike zai dawo gida ne ya hadu da Fudail yana niman shi, kallon juna suka yi sannan yace mishi.
"Sun kaiwa Ikram hari"
Rab'a gefen shi yayi tare da barin guri a hanzarce ya isa gidan, kayan shi ya sauya sannan ya dauki gatarin shi ya nufi wajen gari.

      Gani yake dokin da yake  kai bata gudu, duk da kuwa saurin da yake yi bai hana shi ganin nisan gidan da Ikram take ba, jike kamar ya cire zuciyar shi ya gulla tsabar tashin hankalin, koda ya isa ya sami dakarun da suke kula da lafiyar ta, duk an kashe su, yana shiga ya same ta zaune akan saman gawarwakin mutanen da ta kashe, jini na d'iga daga gefen cikinta. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tako a hankali,yana murmushi ganin yadda take rike da takobin salon shi ta dauka, wato tayi kujera da mutanen.

     Ganin su Izmah da Nimra a gefe bakin su a fashe ne ya sashi kallon su da son karin bayani.
"Muna zaune suka shigo, wai ance su kashe Ikram, shine tace inji waye? Sai suka ce mata Sultan Aamaan Mehran, ya umarce su, suka kasheta.mu kuma muka ce karya ne ba zaka tab'a sakawa a kashe ta ba, shine suka rufe mu da duka, daga nan ne ta ce su kyale mu ita ta yarda a kashe ta. Shine kawai suka juya kanta da dukka.

          Har da janya, bayanta ma jini na zuba. Ganin sun kama mu zasu shigar da mu d'akin ne domin kudirin su, shine ta fara kashe su, wallahi bana son naga tana kashe mutane haka, dabi'ar tai mata yawa, mace ce kuma hakkin jini ba zai tab'a barinta ta huta na." Izmah ta karshe maganar cikin kuka da tashin hankali.
"Ikram bani takobin" ya mika mata hannu, bata d'ago kai ba, balle ya saka rai zata amsa mishi, a hankali ya taka har gaban ta, ya saka hannu ya tab'a kafad'arta, biyo shi tayi tare da zubewa a jikin shi. A kidime ya d'ago kanshi, tare da kai hannun shi bayanta, yaji wuka a suke a bayan ta, a hankali ya zare wukar.
                Kallon Fudail yayi sannan yace mishi. "Maza ka koma ka dauko keken dokin" da gudu ya fita, tare da kallon su Izmah da suke kuka. Kamar me,  gani yake kamar Fudail baya dawowa, kamar yayi kuka haka yake ganin ta, dan ma ya tab'a wuyarta yaji tana raye, amma zubar jinin yana d'aga mishi hankali. Dan haka ya kalli Izmah da itace zata iya bashi amsa Nimrah kan tsoro ya cinye ta baki daya. "Basu kira sunan wani ba?" Shiru tayi tana nazarin abinda suka fada tare da kallon shi, girgiza kai tai tare da cewa. "A'a" shiru yayi tare da sake wata tsaki sabida ganin har yanzun  Fudail bai iso ba ji yaƙe kamar ya kurma ihu, dan haka ya dauke ta cak zai fita da ita sai ga Fudail nan.
"Afwa Sultan Mehran, dakyar suka barni na fito!" Ya kalli Izmah sannan yace musu.
"Ku fito!" Ya juya tare da bin bayan Mehran, yana fita aka bude kofar keken ya sakata a kujeran sannan ya juya tare da riko hannun Izmah ta shiga sannan ya kalli Fudail da yake rike da Hannun Nimrah da take kuka.
"Ina da abin yi!" Ya gaya musu a gaggaucce, da sauri sauri itama ta shiga cikin keken, hawa dokin shi yayi, Fudail ya hau gaban dokin.

      Basu B'ata lokaci ba suka nufi masarautar, inda dakarun suka nemi hana Keken shi kasancewar Sultan Mehran yana baya, ganin shi ya dawo gaba duk suka zube akan gwiwar su. Tare da niman afwa. Nufar gidan Mehran yayi da ita, shi kuma Mehran ya nufi gidan likitan masarautar yana shiga yayi karo da Amir Hood.

   "Zo muje ka duba min mara lafiya!"  Ya faɗa a sanyayye, ko kallon Amir Hood bai yi ba,shima likitan haka, bai kalli inda Amir Hood yake ba, zasu fita yace.
"Aamaan ba dai akan karuwar na bace kake damuwa?"
Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Bani da lokacin ka!" Suka fita a fusace, Amir shima ya fita daga gidan yana jin lallai dole ya kashe Ikram, wannan itace bakar kaddarar da aka ce zata shigo masarautan. Kuma ya fahimci haka ne tun daga ranar da Sultan Aamaan ya saka aka hukunta Zuhair, sannan bayan an konata Aamaan ya dauke ta suka yi balagoron har Madinatul Mah, wannan yasa shi kara fahimtar haka akanta. Amma baya fatan abubuwan da ya aikata su biyayya har yarinyar ta sani.

   ~~~
Tunda likitan ya isa gidan yake famar bata kulawa har ya dinke ciwon jikinta, Mehran yana tsaye akanta tare da sintiri, idan kana gidan sai ka fahimci yadda Mehran ya dawo, bayan wani lokaci likitan ya fito yana faɗin.
"Insha ALLAH zata samu sauki, sannan a kula da bayanta da kuma cikin ta."
"Zata ji sauki nan da sati biyu?" Mehran ya tambaya a dame,
"Eh Toh ya danganta da yanayin jikinta ne" rike bakin shi yayi sannan ya kalle shi, yace.
"Babu wani matsala bayan Ciwon jikinta?'
"Babu gaskiya"
"Mun gode!" Inji Sultanah,
Yana fita ta shiga dakin tare da kallon ikram, zucuyarta a raunane yake akan Yarinyar, amma tsoron goben D'anta take, tana gudun abinda zai je ya dawo mishi. Ikram itace ta dace da Mehran, amma idan ta duba yadda rayuwar su take, zai yi wuya kome bai faru ba, tana jin ciwon yadda kome ya cab'e mishi .
      
Shigowar shi da yayi ne ya sata dauke kanta daga Ikram.
"Naji kama tambayar zata sami lafiya nan da sati biyu. Meye kike nufi?"
"So nake ta shiga cikin zab'en matan da za ayi."
"Akan me?" Zuba mata ido yayi sannan ya sake murmushi.
"Sabida ta zauna a matsayin shugaban Kwarkwarorin na!"
"Yarinyar da take da sa'ar ce zata zauna a kwarkwarah? Hmm!.....
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

32

Ta tambaye shi tare da kallon shi,bakin shi ya gaza furta kome, sai zare ido yake.
"Mehran ba zan hanaka abinda kake so ba, amma ya girman hatsarin shi a rayuwarka, iya yanzun ma an fara samun matsala ina kuma ta shiga harkokin cikin masarautan? Ka duba abinda nake nufi akan Ikram kayi hakuri ka rabu da ita, bata da Sa'a a rayuwarka. Idan so ne a duniyar nan babu wanda ya kai ni sonka da kuma kaunarka da Ikram, amma dole ce Kanwar naki zata sani na iya dauke kai na daga Ikram, don Allah ka rabu da ita"

      Girgiza mata kai yayi, sannan ya juya tare da barin d'akin,  numfashi ta sauke sannan ta kalli yadda ikram take barci cikin wahala, kafin ta juya ta fita. A gaskiya bata kin Ikram amma halin da zata jefa rayuwar shi ce take jin tsoron Allah akan haka, kuma tasan zai yi wuya ya rabu da ita, shi yasa take jin kamar ta kori ikram idan taji sauki ko kuma ta saka a a lalata mata jarabawar da zasu yi.

               Amma kuma idan ta tuna yadda yarinyar ta b'ata lokaci tana zaune da Mehran sai taji jikinta yayi mugu mugun sanyi, taji bata da wani hanyar da zata iya cutar da ikram, sai dai kuma ba zata iya daukar kasadar barin shi ya zauna da ikram ba, Allah ya gani ba zata yarda da wannan tunanin ba, gwara duk abinda zai faru ya faru, amma tabbas zata raba su Insha Allah. Dan haka ita zata zauna da ikram har ta warke ta kuma maida ita garin su ta gaji yanzun son D'anta take bata jin zata bar shi ga kowa.

     ***
Kura musu ido yayi tare da cewa.
"Akan me zaku ce min Sultanah ta hana a cire al'adar duba al'urar mace? Gaskiya ba zai yiwu ba a cire shi ko kuma."

"Indai akan ikram ce kake wannan zakewar ba dai kai ka ba, domin haka da zaka aikata shi zai sanya kowa ya zargi wani abu daga gare ta, dan haka ka ɗauke kanka akan Ikram ko kuma na sanya a fidda ita daga Masarautan nan baki daya." Inji Sultanah, shafa kanshi yayi tare da kallon kasa, tabbas yana tinzira ta, domin bata tab'a juyawa muradin shi baya ba, sai wannan karon.

"Shi kenan, amma ba zan lamunci kasawa ba, dan wallahi idan aka min kuskure za a ga mugun tashin hankali.".ya fadi haka a zuciye, sannan ya bar gurin su....

   ..~~~ a cikin wannan yanayin aka fara shirya abubuwan da za ayi, duk da kuwa an fara tarb'an baki daga yankunan kasar. Musamman y'ay'an gwamnonin shi, Sakeenatu binti Abu Waqqas da Azizatul Nissah, sune kawai suka rage basu iso ba. Gefe guda kuwa zamu iya cewa Alhamdulillahi domin jikin Ikram ya d'an samu sauki, sai dai bata iya jure tsayuwa ko kuma wani abun da zai sanya ta zauna na wani lokaci. Sannan wani karin tashin hankali yadda take wasu abubuwan kamar tab'abb'iya, domin zata iya daukar wasu lokuta bata yi magana ba, idan kuma ka bata abinci zata na kallon shi kamar taga dodo, dan haka wannan yanayin ya sanya shi shiga tashin hankalin da ya kasa fahimtar kome. Itace dai yake sakawa a gaba da tunanin halin da zata kasance.

      Ganin haka yasa Sultanah ta kuma niman Uwaisul Qarni, sunyi magana sosai har ya gaya mata cewa.
"Ku godewa Allah da iya haka ne ya same ta, domin ban da Allah ya taimaka na bata  addu'o'in kwanaki ba da wallahi sai abin yafi haka, dan haka ku kai mata wannan, sannan karki zata abinda kike bukata zaki samu, karki kuma yunkurin rabasu, hakan kuskuren ne babba, karki nunawa Ubangiji wayonki, shi da ya had'a su shi yasan yadda zai yi da kowannen su. Dan haka kar na kuma jin kin ce zaki raba su, domin wani tunanin dake ranki."

     Da wannan yayi mata sallama, tare da barin gurinta,  haka ta kai wannan ruwan addu'o'in dakin Ikram ta bata, sai da ta shanye sannan ta fita. "Anne meke damun tane?" Ya tambaye ta ranshi a jagule, ajiyar zuciya ta sauke sannan tace mishi. "Jini yake bibiyarta, amma Insha Allah idan tayi barci ta farka zata ji sauki wasu abubuwan."  Kasa jure bayanin da Sultanah tayi mishi, dan haka ya juya ya bar gidan. Bai tsaya ba sai

Please Login or Register in order to submit comment