Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a raina babu makawa zaki bukaci gani na,

          Idan da namiji ne tuni yayi abinda ya kawo shi, dan nasan ya kawo ki ne ki kashe Rahil, sai dai zuciyar mace ba irin na namiji bane, mace tana da taushin. Ban san sunanki ba?"

     "Bilqisul Ikram Mustapha!" Cikin wani irin sauri ta d'ago kai tare da rawan jiki, tace min.
"Matso na ganki!" Tana kai hannunta fuskana, alamar bata gani, shafa fuskana take son yi dan haka na matsa kusa da ita.

             "Ina iyayenki?" Ta tambaye ni, "sun rasu!"
"Daga ina kike?"
"Gezira!"
Ajiyar zuciya ta sauke, sannan tace min.
"Me kike bukata a cikin wannan gidan?"
"Me yasa suka kashe miki Yaranki?"
Hawayen da suke zuba tare da tuttukowa daga idanunta ya sani fahimtar kome.
"Yanzun me kika fahimta akan Sauran dakunan?" Na tambaye ta, girgiza min kai tayi sannan tace min.
"Kasancewar nice matar shi ta farko, kuma yar kasar Habasha, kuma ina zuwa ban jima ba, Yayan shi Sultan Khabir ya rasu, sai aka bashi sarauta, ganin haka ne yasa yaran shi suka fusata me yasa ba zaa bawa Mahaifiyar su magajiyar sarauta ba(Which mean Empress)

                 Sai suka fusata har itama Ummu Kulsum din taji babu dad'i, su kuma sunyi nazarin gidan da tafito ne, ba wasu bane kuma idan aka basu magajiyar sarauta, basu da Addini dan haka suka zab'i Mu'allim, lokacin ina goyon Cikin Almustapha, anyi rikici karshe aka tsayar da magana idan ta gana takaba zata aure shi kuma ya amince.

     Sanin cewa musulunci bai haramta ba yasani saukar da kaina, har Allah ya sauke ni lafiya, lokacin na haifi Almustapha, a hankali sai mutum suka fara kokuwar ganin ai tunda na fito a cikin gidan da suke da karfin mulki a nahiyar Afirka, dan haka suka fara bani goyan bayan a bani Sultanah, shi kuma Sultanah ana iya samun shi ta karfin mulki,. musamman idan kin hada nasaba da manyan masarautu a jininki, sai Allah ya sanya aka fada abin daidai kai na. Kuma aka duba tarihin kasar mu, babu kowa nawa da yayi bauta, mulki aka haife mu muka taso cikin shi.

    Dan haka suka bani, tun daga lokacin aka fara farautar rayuwar Almustapha, har na haifi Abubakar, sha'anin mulki dole sai kayi takatsantsar, dan haka duk ta yadda naga mijina zai kauce ina tsaya mishi domin ina da ilimin addini sosai, shima kuma haka, Ikram. Har na haifi Aliyu, ana samun matsala a cikin gidan nan sai da na haifi Raziyana, na sami sauki lokacin Mu'allim ya auri Baiwar shi. Itama ta haifi yara maza Abdullahi da Abdul Rahman, anan aka zafaffa k'iyayyar da ake acikin masarautan.

         Cikin hukuncin Ubangiji, sai gashi yarana sune Jarumai ko yaki aka tafi sune suke dawowa da tuta, tun Almustapha yana da shekara sha biyar ya fara fita yaƙi, kuma ya jagoranci yaki na fitar hankali, har ya kai matakin shekara ashirin da biyar, su uku suke fuskarta yaki, kowacce iri ne, Allah yayiwa Almustapha baiwar iya fahimtar lamarin yaki, yayinda Abubakar yayi tafiya har kasar ruma, yayi ilimin yadda ake sarrafa, nakiya, shi kuma Aliyu ya kware a iya leken asirin abokan gaba, yara Uku sai suka zama kaf nahiyar Afirka su ake kwantaccen dasu.

   Idan suka fara yaki har saka maza gudu suke."
Murmushi tayi wanda ya fidda mata yan lub'anta, sannan ta cigaba da bani labarin.
"A hankali yarana suka kawo ka, Ana cikin nima musu auren Yar Daular Askandariya, aka wayi gari ya tafi farauta daga nan ba a kuma ganin shi ba sai kayan aikin shi. Muna cikin wannan halin Abubakar da yayi tafiya zuwa kasar Sham, a hanyar dawowa ya rasu, Kinga bude wancan akwatin, zaki ga rubutun su kowa ya iya Rubutu, kuma sun ajiye min tarihi."

              Haka na bude tare da daukowa naga sunan Almustapha, gabana ne ya fadi. Sakamakon ganin rubutun Abba na,.kallonta nayi ina jin hawaye na zuba min, tabbas akwai ranar da na tab'a ganin shi yayi rubutu, sannan ya juya zoben hannun shi wanda yake da wani abu a bayan shi ya kunna wuta ya kona bakin abun ya manna a jikin Takardan. Sai daga alamar wancan da na gani a gurin shi.

    "Bayan mutuwarsu, dan haka Muka kama Aliyu muka aura mishi yar gidan Abu Ayyub, shekaran su goma sha biyu, aka kona su, Allah ne ya nufa Rahil zai yi nisan kwana, aka samu baban shi ya fidda shi daga cikin gidan, ya turo shi waje! Har yau ba a san suwaye suka musu kawanya ba."

Fesar da kukan nayi sannan nace mata.
"Me kike so nayi musu?"
"A hukunta su idan an same su, idan kuma ba a same su ba, Allah zai hukunta su."

     Mikewa nayi sannan na taku daya biyu, nace.
"Idan aka musu shara'a a fada, zasu sami sassauci, hukuncina dai dai take da hukuncin Shari'ar Muslunci. Idan ka kashe a kashe ka idan ka tab'a a tab'a ka, matukar jini Ya tsaga dole hukuncin ya haura kansu."

           Ina gama fadar haka na fice daga cikin gidan, na nufi gidan Sulaiman, ina shiga na shiga sumar da  dakarun shi, har na isa cikin dakin shi, yana kwance nayi kwance kwance na zuba Mishi duka akan cikin shi. Da gudu ya farka.

"Yau nazo na ji bayanin daga bakin ka, saura sati biyu na gama abinda ya kawo ni, idan kuma kayi karya, zan datse kofar numfashin ka."

   "Wai Ni kam wani irin masifa ce ya sani kwaso ki?" Ya fada yana dukan kanshi.
"Waye ya kashe Almustapha da yan uwanshi." Zaro ido yayi sannan ya rufe bakin shi. Yace min
"Kasancewar kin tab'a Bala'i zan gaya miki, amma zaki mutu"
"Karka damu, a jini na yake wasa da mutuwa,! Gaya min"

    "Almustapha nina fitar dashi daga kasar baki daya na kai shi iyakar kasar nan bayan mun shiga Algers, domin Amirah Raziyana tana son zama mace ta farko da ta mulki kasar nan, ba zata tab'a samun damar haka ba, dole sai takawar da yayunta, Ni da Almustapha mun taso abokan amana, ba zan iya gani a kashe shi babu dalili ba, dan haka koda na kai shi Algers sai na samu nayi mishi dalilin da ya manta da kome nashi amma kafin nan ya gaya min cewa. Ko bude ko bi jima zai dawo, idan bai dawo ba Allah zai kawo jinin shi.

     Dan haka ina jin haka na buge kanshi ya fad'i, sannan na yiwa bayin shi barazana da zan kashe su. Sanan daga baya na hana shi da wani mutumin da shi kanshi Almustapha bai sani ba, yayi ta bibiyar rayuwar shi, har aka ce min ya sauka a gezira. Amma ban tab'a zuwa ba, wannan shine zunubin da na aikata, sai Abubakar kuma, Babu ruwan mu a cikin mutuwar shi, domin an hanya tasaka aka kashe shi wannan kan ba ita daya bane har da Abdullahi, Mutuwar Aliyu ma haka har da su. Domin Umma da ta ga lallai Mulkin gidan ya koma kishi a tsakanin zubda jini ta hana mu shiga cikin maganar gidan.

          Bayan haka toh mun fara jin ƙishin ƙishin, Sultan zai yi murabus, kuma ana zargin Amir Rahil zai bawa, shine na kawo ki."
         Kukan da nake ya kura min ido.
"Wacece ke?"
"Bilqisul Ikram! Yar Amir Almustapha Mu'allim!  Idan na kashe ka na b'ata kome, zan Barka a raye domin Rahil kuma, zan dawo kamar yadda nace, .maka amma  zan karasa aikin da azo yi sai dai ba gawar Amir Rahil bane, gawan mutanen da suka yi wanka da jinin Ahalina zan bar su. Domin akwai sauran aikina."

   Juyawa nayi na fita daga gidan, nayi kuka nayi danasanin kuntatta mishi, ashe dan uwana ne,nake ta bashi azaba, shi yasa suka ki bashi tarbiyyar sarauta...

   Haka har na isa gidan, ban kuma kwanciya ba, domin a duk lokacin da na kwanta bana iya barci, sabida Rahil gani nake kamar ina rufe idanu na zasu far mishi.

....
A hankali har kwanakin da za ayi gasar ya shiga zuwa, kamar na san ana shiri a kaina, ranar na dauke shi har gidan Amira Raziyana,  tun da Samir ya ganni, ya mike zai kama haushi kamar kare. Na sha hannuna a bakina.
"Shiiiii! Bana son haushi kamar kare, ka zauna nazo magana ne da Umma ta, Amirah Raziyana, Barka da dai."  Komawa nayi kusa da ita tana zaune cikin mulki.

         Kallona take cikin tashin hankal, zama nayi tare da cewa.
"Kamar yadda aka saka mutane bakwai a kashe Abubakar, sai mutuwar Aliyu aka saka mutane biyar, sabida mulki."
"Ke....karya!"
Dukar bakin shi nayi, sai da ta razana, sannan nace mishi.
"Da Farko ba da kai nake ba, amma ka nace sai kayi magana, ki kuma na tsani katsalandan, jibi zamu yi gasar tunawa da Almustapha da Abubakar, tare da Aliyu. Nasan ana shiri akai na,  Raziyana. Zan karasa aikin da nazo, kamar yadda kika saka wasu kuka sai na saka ki kuka, mulkin da kike bukata kuma sai na san yadda na haramta miki shi. Sannan na dawo kan Jahilin d'anki na kona shi kamar yadda aka kona Abubakar da Aliyu, ki godewa Allah da baki da hannun a b'acewar Almustapha, da yanke miki hannun zanyi. Mulkin kuma kina ji kina gani za a haramtawa ahalin ki baki daya har karshen rayuwar ku. Ke ba iya ke ba. Hatta Yaranki sai....

```BOOK one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```

#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: Monday-March-2021
*FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

14
SAMAIND
A hankali ya d'ago kanshi, tare da kallon Darakshan wanda yake sanye Da Kayan alfarma. Kallo daya yayi mishi sannan ya maida kan shi kan Abinda yake yi.
"Sultan MEHRAN! Ana gayyatarka fada, domin."

"Da kuka Fahimci shine Kusar Yakin ku ko?" Inji Fudail, a fusace Darakshan ya juya kan Fudail.
"Kai kare!" Bai rufe baki ba sai da hakoran shi biyu suka sauka a kasa, sakamakon naushin da bai san lokacin da ya amsa daga basamuden hannun Mehran ba.

  Kamar bashi yayi dukar ba, ya koma mazaunanin shi, yana cigaba da aikin shi.
"Kace yana zuwa!"
Inji Fudail, juyawa yayi cikin fusata yana kallon Fudail.
"Rakshan ba gaba da gaba ba, ko ta baya sai ka shirya, Sultan Mehran murucin kan dutsen ne bai fito ba sai da ya shirya, zaka iya gayawa iyayen farautar ka yana tafe."

           Fita yayi sannan Fudail ya gayawa Sultan Mehran dalilin da yake tunanin shi zai sanya su nemi shi. Daukar kofin shayi yayi sannan yace mishi.
"Kana gani akan yakin da basu san mafarin shi bane zasu kirani!"
Ya tambaya yana kallon Fudail.
"Eh Sultan! Sabida kowa yasan kai ne kawai zaka iya jagoranta yakin da mutane dari kacal ayi nasara da Iznin Ubangiji, sannan basu da takamaiman Sarkin Yakin da zai jagoranci SAMAIND, shi yasa suke ganin kamar kai ne mafita."

     Ajiye kofin yayi tare da mik'ewa yana me nad'e hannun shi a kirjin shi.
"Ikram!..." Shiru yayi tare da dauke kan shi dan Fudail zai ce ya kira sunan ta.
"Sultan kana magana ne?"
Tab'e baki yayi sannan yace.
"Me kake gani akan hakan?" Ya tambayi Fudail, murmushi yayi sannan yace.
"Sultan MEHRAN, hadakar mayakan ne na yankin larabawa, sannan sun ninka Dakarun SAMAIND sau biyar, bayan haka kuma mace ce take jagorantar matakan Sakeenatu binti Abu Waqqas!"

       "Tana da aure?" Ya tambaya a sanyayye,
"Bata dashi!"
"Daga ina take?"
"Daga Bahrain!"
"Ta tab'a soyayya?"
"Bata tab'a ba, domin itace Sarkin yakin kasar su."

"Ya ka gani idan aka gyarota, a saukakke an fasa yaƙin, idan ta kama ma, zamu hada shimfid'a duk ba laifi bane!" Ya faɗa cikin sanyin murya, wanda zai nuna maka cewa yasan me yake yi.

"Sultan!!" Fudail ya kira sunan shi a tsora ce,
"Na zata ka barranta kanka ga aikata irin wannan abin? Sultan naga zallar soyayyar Ikram a idanun ka, yanzun zaka dauki nauyin bawa wata halittar ka, gaskiya ina taya Ikram mugun kishi da akan ka aikata haka, gwara mu faffata yaki."

    Murmushi yayi sannan, ya cigaba da abinda yake, tsakanin da Allah ya hango kishin akan Fuskar Fudail, bai damu da hakan ba, sai can bayan awa daya ya shirya cikin riga doguwa, tare da saukar da gashin shi bayan shi.

        Rigar farar ce babba har kasa take jan kasa, a hankali suke ratsa bishiyoyin har suka isa cikin fadar, ana ganin shi sai da suka mike, wannan girman dai da Allah ya bashi yana nan tare dashi, kwarjinin shi da kamalar shi tana nan zube a kan fuskar shi.

      Nutsuwa da kamun kai yana nan a jinin shi, zama yayi tare da kallon su. Duk suka yi tsuru tsuru, suna kallon juna. Wasa yake da hannun shi yana kasa.

    "Yarona Mehran! Baka ji labarin anyi gobara bane, har Yar Amir Hood ta rasu, sai kuma batun yakin da yake tunkaro mu."

    Mikewa yayi tare da had'a hannun shi guri guda, murmushi yayi sannan yace musu.
"Toh meye nawa a cikin abinda yake tinkarar Daular mu? Naga dai anyi min iyaka da mulkin baki daya, dan haka kowa tasa ta fusheshi, ku nimo wata mafita Ni babu ruwana."

     "Amma wannan wani irin magana ce? Akan me ba zaka taimakawa kasar ka ba, karka manta duk abinda ya faru da kai talakawa zasu yi kuka?" Inji Amir Hood,
"Toh ina ruwana da kukan takalawan? Ko ance muku Ni sakarai ne da zan kashe rayuwa ta sabida ku? Dan haka wannan matsalarku ce ba tawa bace.

  Dan haka babu abinda ya dame ni lokacin da zaku cire ni baku yi tunanin talakawan ba? Kuka cire ni basu sani ba toh uwar me zanyi wa rayuwar su? Dan haka babu abinda ya dame."
.yana gama fadar haka ya juya tare da Bar fadar.
"Aamaan!" Cak ya tsaya sakamakon jin muryan Sultanah Hoyam.
"Kazo ayi magana daya da kai !"
"Da farko dai bani na gayyato kai na ba, sai na biyu ba zan shiga hurumin fada ba, na uku kuma karku kuma gayyato ni, domin zan sare kan duk wanda ya kirani na ajiye a kofar mashigar masarautan nan!"

Daga haka ya saka kai ya fita abun shi.
"Meye yake nufi?"

"Har yanzun yana cikin halin rabuwa da wancan me idanun kifin ne, dan haka ku kyale shi nasan waye shi" inji Mir Jazib,

       ~~~
Yana sane yaki shiga cikin maganar yakin, domin zasu tattaro su daura mishi nauyi ne, a gefe guda kuwa turawa yayi aka kira Mishi Sakeenatu binti Abu Waqqas,  da har tayi gardama amma jin an ce mata Sarkin Samaind ne kuma matashi ne da bai tab'a aure ba yasa ta shiryawa ta fito har inda yake zaune a cikin tantin shi.

Tana shigowa ya mika mata hannun, babu musu ta rike nashi tare da kallon shi. Mazauni yayi mata akan cinyar shi, tare da sake mata murmushi, a hankali ta kai hannunta kirjin shi, tana kallon fuskar shi.
"Sultan MEHRAN! Ya gayyace ni, tantin shi, nasan ba haka kawai zai bukaci hakan ba. Kuma nasan garin SAMAIND cike take da yan mata da kyawawa."

        A hankali ya zare wukar da yake gefen cikin ta, ya wurga can gefe.  Sannan ya kuma gyara mata zama a jikin shi.
"Dakatar da yakin da kika fito nake son kiyi."

Ya fadi haka yana zare mata mayafin samar kayanta. Lumshe idanun shi yayi.

   Duk da tafi wancan mahaukaciyar diri, baya jin kome akanta kuma ba zai iya mata kome ba, kallon kirjinta yayi tare da kai kanshi wuyar ta, yana shinshina turaren ta.
"Me yasa baki amfani da miski? Yana da dad'i a jikin mace"

"Sultan MEHRAN, yana da bukatar mace ne?" Ta tambaye shi shi.

D'ago shanyayyun idanun shi yayi akanta, tare da hura mata iskar bakin shi, sannan ya shiga bi da ita, amma bawai dan ya fahimci ita din bace a gaban shi, gizon da Ikram take mishi a jikinta yasa shi kara rikicewa. Ture ta gefe yayi sabida jin zata saka mishi karfe a jikin shi, ya juya da sauri ya kamata. Tare da rike rigar jikinta, zai yaga.
"Bana son tozartaki! Dan haka zan baki damar ki janye yakin da kika zo yi, ko kuma nayi miki mafi munin abinda zai sanya ki bukaci kashe kanki, a yanzun haka dakaruna miliyan daya sun zagaye ku baki daya.

          Dan haka shawara tana gare ki, idan yayi miki to idan bai miki ba, zamu kuka haduwa gobe Insha Allah."
Juyawa yayi zai fita yayi wani irin tsalle ta rungume shi. Sai da tayi nasarar hada bakin su guri guda. Bata kyale shi ba, sai da suka dangana da shimfid'ar shi.

     Cikin sauri da tashin hankalin, take kokarin kare kanshi, inda suka shiga fada kamar wasu karnuka, sai da ya kai da ta raba kanta da kayanta, sannan ta samu damar yaga rigar shi. Tana me hada jikinsu waje daya.

          Kan shi ya kau fuskar ta, a tunanin ta, sumbatar ta zai yi. Sai aka sami akasanin haka, domin mayafi yaja tare da rufa mata kirjinta sannan ya mike a kanta.
"Wallahi tallahi, yadda ka jefani cikin wannan yanayin, sai na ana d'aya Daga cikin matan ka, haka ka shirya gani na nan da mako me zuwa!"

   Tsayawa yayi tare da d'an waiwayawa tare da kallon bayan shi kad'an, sannan ya gyara rigar shi yana faɗin.
"Ku tattara yanaku yanaku, ku bar yankina"

      Yana fadan haka ya fita abun shi, dukar shimfid'ar tayi tare da cewa.
"Wallahi sai na same ka."

      Kad'a dawakan su, suka yi tare da barin gurin, baki daya. Suka nufi SAMAIND, yana lura da  yadda Fudail yake cika yana batsewa, murmushi yayi cikin son jin bakin Fudail yace mishi.
"Sakeenatu binti Abu Waqqas, akwai cikar halitta, gaskiya mace ce ta shaidawa duniya. Naji dadin alakata da ita"

  
         "Allah sai ya bi mana hakkin mu" ya faɗa kamar zai yi kuka, yana kallon Mehran, tab'e bakin shi yayi domin haka ya zame mishi kamar jiki ko halitta.
"Ni dai naji dadin alakata da ita"

"Chaaaaa!"  Fudail yacewa dokin shi dan ba zai iya kayan Bakin cikin Mehran ba. Haka suka iso cikin garin, tare da nufar hanyar gida, koda suka shiga gidan, kowa kama gaban shi yayi.

          ~~~
Misra..

     "Kin san me? Na gaji don Allah mu yadda zango mu huta." Inji Izmah, dan ta gaji.
"Karki damu ga can garin Misra muna hangowa kibari mu shiga garin"
      "Wallahi ba zan iya kaiwa har haka ba!" Ta faɗa tana kuka, sauka muka yi gefen hanya, sannan na kafa mana tanti, muka zauna dabino da ruwa muka sha, sannan muka shiga hira.

"Akwai soyayyen nama, da Baba ya bani!" Ta wurga min kunshin namar, budewa nayi na fara kallon shi sannan na dauki daya na ci, na mika mata itama taci. Tana dariya, sallah nayi tare da kallonta, duk sai ta diriri ce tace min.
"Ina jin kunyar yadda kike Ibadar ki! Kuma tafiya ta haɗa mu, baki tab'a kyama na ba."

"Wannan ba matsala bane dan Addinin mu ba daya bane, babu inda aka ce ka saka wani addini dole"  murmushi tayi sannan tace min.
"Kina da saukin kai kome naki a warware yaƙe!"
Murmushi nayi tare da cewa.
"Kwanta ki huta, idan babu fada hannun masu sayar da bayi ba, munyi Arziki."
Na fada mata ina gyara kwanciya na, murmushi tayi tare da zuwa kusa dani, ta kwanta tare da rike Ni,.

            A hankali barci me nauyi ya dauke ta, ni kuma na fito daga tantin na zauna ina kallon garin Misra, daga nan ban san inda zamu kuma nufa ba.

     Nazarin nake amma kuma ban fahimci kome ba, sai da na shiga tantin muka kwanta.  Mafarki nake me dauke da ban mamaki.

   Dan daga kwanciyar nawa na fara mafarkin.
Bude idanun nayi cikin gajiya da mafarkin na tashi zaune, dan ban fahimci kome ba.
Alola nayi na tadda sallah, ban kwanta ba, sai da aka asuba yayi anan na sami damar barci me nauyi.

            Mafarkin Noman nayi cikin jini, ina kallon aka sare kanshi. Ihu da nayi ne ya saka ni farkawa, na tashi ina ajiyar zuciya.kai na ne ya sara min, a hankali na mike tare da nufar hanyar waje inda Izmah take zaune.
"Izmah" juyowa tayi tana murmushi, ajiyar zuciya nayi tare da kallon ta, fitowa nayi tare da kallon ta haɗa wuta tana, gasa wani abu.

   "Me kika sa mana?" Na tambaye ta,
"Zomo tun d'azun na fita can akwai lambu shine naji kamshin kasa nabi kamshi sai naga suna bayi ne! Anan na ga zomon na kama mana shi."

      Zama nayi tare da tankwashe kafaffuna, ina kallonta tare da had'iye yawun na. Dariya take nace mata.
"Don Allah Karki ja min rai"
Na fada a shagwaɓe,
D'aga min gira tayi tare da, cizon bakinta tana murmushi, tace.
"Zan baki Amma sai kin min alkawarin bani labarin ki"  girgiza mata kai nayi sannan nace mata.
"Kiyi hakuri na manta wasu abubuwan masu muhimmancin, duk ranar da na tuna zan baki mamaki"

           "Babu damuwa." Ta faɗa min, tana gama gasawa. Ta mika min dukka, dan haka na raba mana biyu, na mika mata wanda yafi girma, girgiza kai tayi tare da dawowa kusa dani, ta daura kanta a kafadana tana murmushi.
"A da ina tunanin idan muna shiga cikin al'umma zaki wulakanta ni, sai gashi kin rike Ni kamar jininki, kina kare lafiya ta, da hakkina. Nagode Salsabilan Amir Rahil."

Dariya muka saka tare da kallon juna, muna ci muna tab'a hira.....
```Two three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: Monday-March-2021
*FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

13
Ina gama fadar haka na riko hannun shi muka bar gidan, sannan muka fita waje ya kalle ni a tsora ce yace.
"Yanzun me kika aikata?" Banza nayi dashi yana kuma tambaya na nace mishi.
"Yadda zata yi gunduwa gunduwa da namarka na mata magana"

"Me yasa kike son tashin hankali ne? Ba kome ake samar dashi da fada ba, kin fahimta." Ya fadi haka kamar zai fasa ihu. Kallon shi nayi sannan nace mishi.
"Sai kayi kuma!"
Na wuce abuna,muna shiga falon shi ya fisgo ni tare da had'a Ni da bango..yana kallon cikin idanun na.
"Me yasa baki san tsoro ba?" Bin hannun shi nayi da wani irin kallo, ya sashi sake ni yana jefa min tambayar renin hankali,
"Abubuwan da ya dace naji tsoron su basu nan, na gaya maka kanwata da aka kashe ta sanadin fyade ko kuma mahaifiyata da aka tsince ta a bakin kogi cikin jini!

     Ko na baka labarin yadda aka kashe min mijina? Meye ne ban gani ba? Meye kake son na gani da zanji tsoron na boya a bayan wani kato ina rawan jiki? Da ace an haife ni a rangwanta tabbas kashe kai na zanyi da bakin cikin duniya na huta, sai Allah ya taimaka ina da zuciya a...."
Tattausar leben shi naji akan nawa.

          Wanda suke jike da sanyi, cikin nutsuwa yake sumbatar bakina, rike rigar jikina nayi da mugun karfi, ina kallon kwayar idanun shi.
*Amir Rahil! Matashin dan shekara ashirin da biyar, kyakyawan saurayi wanda ake ji dashi a cikin Amirai na kasar Maroko, Yarimar da yafi kowani Yarima ina ado da tsari! Tausayi yake bani*

Wannan shine abinda Zuciyata take fada min, tabbas tausayi da kasancewar mu jini daya, yana cikin tashin hankali, dan haka ban hana shi sukuni ba, sai dai yadda naga yana shirin ganin ya wuce gaba da bakin ne na nemi dakatar dashi ta hanyar tura mishi goshina, bakin shi ya sauka akan goshina.

       Wani irin rungume ni yayi tare da kara matse ni yana sauke shashekar kuka.
"Kinji dadinki ke jaruma ce, gashi ko takobin ban iya rikewa ba, me yasa bani da karfin zuciya haka?"

   

Please Login or Register in order to submit comment