Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min kafana.
"Amahh!" Ya kira sunan da nasan dai ba nawa bane.
"Amahh kiyi min magana mana."
Yayi magana a raunane,
"Ba zan kuma barin wani ya cutar da lafiyar ki ba" yadda yayi maganar zaka Fahimci har cikin ranshi yake jin zafin abinda ya faru.
Littafin nan na kuɗi ne..
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
     
Page 31

      A yadda yake maganar zuciyar shi kamar zata buga, bai san dalilin da yasa yake jin tashin hankalin tun bai ganta ba, jin ana lallubar kafar shi ya sashi maza ya kai hannun shi tare da riko Ni.
"Wayyo Mehran ciwo na!"
"Amahhh!" Ya kuma kiran sunan da ya rad'a min yau, ban amsa mishi ba, d'aga ni yayi na sake mishi wani irin wahalalliyar kuka, gaba daya ya saka hannun shi ya d'ago Ni, muka fito waje. Jikina da yake kone da wuta babu inda beraye basu ci ba, haka ta riko Ni har waje sosai yana kallona da idanun shi wanda suke kokarin zubda kwallar da ta cika mishi ido yayi sannan ya cincibe ni muka fita daga gidan.

   Kallon Fudail yayi tare da cewa.
"Ina zamu kai ta?"
"Madinatul Mah, akwai shugaban su yana jinyar konar wuta."
       Furza da iskar bakin shi yayi tare da kallon fuskar ta, yace.
"Muje!"

     Keken dokin shi aka kawo mishi ya shigar dani bayan ya taka matakailai din keken, sannan ya badda Umarni a tara mishi dakaru kimananin dubu daya su bi bayan shi shi, kuma tawaga biyu yake bukata. Sannan  su tsaya a gaban shi.

            Sultanah Hoyam da tawagar Fada suka tawo mishi. Yana tsaye, har aka gama tattaro dakarun.
"Mehran!"
"Fudail ka hado min kayan mu!"
"Sultan Aamaan mune sama da kai fa!"
"Darakshan da Zunnoon su rike al'amuran har na dawo!"

Cike da mamaki suke kallon shi Zunnoon da basu tab'a haduwa ba, asalima baya shiga al'amuran mulkin daular yau shi aka bawa damar ya rike daular baki daya.
"Mehran ina magana kana."
"Darakshan kar na dawo na sami ba daidai ba, Ka nuna mishi kome."

     Duk yadda suka so ya saurare su, bai d'aga kai ya kalle su ba. Asalima Fudail yana isowa suka ya shiga keken shi, shi kuma Fudail ya shiga jagorancin bataliyan dakarun baki daya.

     Suna barin masarautan Amir Hood da Sultanah Hoyam suka nufi haramtacciyar fada, tana sane da duk abinda yake faruwa, dan haka zaune take tana bawa wasu kifaye abinci, suka shigo mata a fusace.
"Me kika aikata? Meye alakarki da Yarinyar da kika tura ta?"

        D'ago kai tayi fuskarta shanye da toka, tace musu.
"Maraba da zuwan Munafukan sarari Aminan Boye ga guri ku zauna!"
   
Cike da al'ajabi suke kallonta, a lokaci guda, murmushi tayi sannan tace.
"Shairah basu ruwa!"
Haka ka kawo musu ruwa da butar shayi, tana Cigaba da watsawa kifi abincin. Tare da kallon su,
"Fazilatul nisa meye nufinki? Duk wannan faffutikar da nake sabida ku nake, amma baki gani ba."

     D'ago kai tayi ta zuba mishi ido, na wani lokaci kafin tace mishi.
"Lallai Abba kaso kanka dayawa, koda yake ban ga laifinka ba."

"Akan me zaki tura wata runduna jikin D'ana? Meye yayi miki da ba zaki kyale shi ba, nice nayi miki laifi ba Mehran ba." Murmushi Sultanah Fazilatul nisa tayi tare da zubda kwalla. Ta kalli Narjis kwalla na zuba mata. Sunkuyar da kan su, suka yi suna jinjina qarfin hakurin ta,. Karfin sadaukarwanta. Irin abinda tayi ba kowacce mace bace za tayi.

         Mik'ewa tayi a hankali tare da nufar gaban zanen hoton Sultan Abdus Samad.
"Me yasa ka sani aikata abinda ba zan iya dauka ba, me yasa?"
Kamar yana jinta take tambayar shi. Goge kwallar kan Fuskar.  Juyawa tayi tare da nad'e hannunta a kirjinta.
"Kace kana faffutikar ganin ka inganta mana rayuwa? Kace kana yi ne sabida mu? Toh meye ka ke nufi?"

     Murmushi Hoyam tayi sannan tace mata.
"Zama bawa Jasrah wakiliyar Sultan Mehran, sannan Yanzun hakan Zunnoon shine magajin garin nan kafin Mehran ya dawo, don Allah ki bamu hadin kai yarinyar nan ta fita a rayuwar shi."

                Kallon son kai take musu kiri kiri sun hanata farin cikin ta, sun hanata jin dadin da kowani mutum yake ji, sun tauye mata farin cikin ta, murmushi tayi sannan tace musu.
"Bana da ra'ayin kome daga gare ku, Ita kanta Jasrah ku dauke ta, ku tafi da ita, Ikram itace makamina, itace zata bani abinda nake buƙata.

              Ku kashe ni da rai na ku zata zan zauna a haramtacciyar fada ce, ku binne ki da rayuwata ta ku zata bazan iya tono kai na bane. Har abada babu wannan a tsakanin mu, ku tsimayi jiran wutar fansa wanda zai narka da kowa."

       "Amma me yasa kika tura mishi mace me addini?" Inji Amir Hood, wato mahaifinta ta,

     Cak taja ta tsaya, juyawa tayi tana kallon su, kafin ta fashe da dariya, sannan tace musu.
"Haka nake son ganin Zakina ya farka daga mummunan barci da aka saka shi, haka nake son ganin Jinin Abdus Samad ya farka daga kawayan da Miyagu suka mishi, da ace kinyi abinda ya dace da har abada ba zan iya shiga tsakanin ba, amma son zuciya yayi miki katuttu, sannan ina sane da abinda yake tafiya kin kama ta kin saka an azabtar da ita,toh kin kyauta ki ji tsoron ranar da zan ficce daga nan, wallahi ki fara gudu kiyi gudu karki tsaya nan kusa. Kai ma ka kiyayye abinda zan zo maka dashi..ba iya kai ba har da sauran mutanen da kuke kula kome dan lalata mishi mulkin shi. Kin koya mishi mugun aiki, Allah ya kawo wacce ta koya mishi aiki na gari, zaki yi danasanin laifin da kika aikata. Kina ji kina gani wannan matsayin da kike na Sultanah zai sauka daga kanki zai koma kan wata.."
        Tana gama gaya musu haka ta juya abinda ta barsu a gurin, tun da ta shiga dakinta take kuka, wiwi sabida biyan buƙatar wasu ta sadaukar da rayuwar ta,ta kuntattawa kanta da abinda take so.

   Ta lalata farin cikin ta, da hannunta. Wani irin kuka take lokaci guda, Allah ya kawo mata mai ceto sai dai bata son ta zama butulu, bata son ta butulcewa Ikram bata son ta cutar da ita, idan ta dawo zata sallame ta kawai, ba zai yiwu saboda biyan buƙatar ta yar mutane ta rasa rayuwar ta, ba.

   Ita zata fuskanci GOBEN ta, zata kuma Cigaba da zama har ranar da zanen Qaddara ta zai goge, zata zama me yanci kamar yadda kowa yake dashi amma ba zata bari su salwantar mata da yarinyar ba, duk da wata shashi da zuciyar ta yana bata wasu abubuwa na daban.

     ~~~
Tafiyar wuni guda ne gashi basu fito ba, sai kusan la'asar suka fita dan haka basu shiga garin ba sai ana sallah magarib. Tun kafin su shiga garin aka sanar da shugaban su, ga mayakan SAMAIND nan sun tunkaro  garin,  cikin kaduwa da tashin hankalin ya kalli Alimah yana huci sannan yace.
"Karki yarda na fahimci kina da hannun a zuwan su."
Cikin tsananin Fargaba ta gyada Mishi kai, sai da suka yi sallah sannan Fudail ya gabatar da kanshi tare da abinda ya kawo su,
"Subhanallahi tana ina mara lafiyan?"
"Tana tare da Sultan Aamaan."
Da sauri Suka fito daga cikin masalacin suka nufi wajen gari, kafin kace kwabo, sun iso cikin garin. Gidan shi suka nufa inda aka musu masauki shi kuma Mehran aka bashi wani bangare na saukar baki na garin.

  A daren aka taso mata suka shiga girki na musamman, za a kaiwa dakarun da suke wajen gari,
     Yana rike da hannun ta, kura mata ido yayi tare jin kamar ciwon a jikin shi yake, matse hannun yayi a hankali kamar me mata tausa.
"Har tsawon kwanaki nawa zata dauka a hakan"
Kasa yayi da kan shi sannan yace.
"Allah ya taimake ka, Sultan zata samin kwanaki ashirin da daya zuwa kwana talatin!"

        "Hmm!" Ya fadi a kasan makoshinsa, yana kallon shi ya gama hada maganin, a gurin sakawa ne fa, mutumin yace bai san zancen ba shi zai shi ya saka mata maganin da kanshi, murmushi yayi sannan yace mishi.
"Kayi hakuri, zan dauke ta kamar  Y'ata zan kula da ita, don Allah karka ji."
"Bani maganin"
Babu musu ya mika mishi tare da fita a dakin, a hankali yake zare mata rigar jikinta, tare da shafa mata maganin a gurin ciwon ta, koda ya isa gurin kirjinta ne ya kura mata ido, sannan ya dauke kan shi,  yayi ya shiga shafa mata har, zuwa kan cikinta, yatsar shi ne ya kai kan cibiyar ta, anan ne kome ya kunce mishi.da sauri ya gama shafa mata. Ya maida rigar ya saka mata.

             Haka suka kwana bayan an bata magani wanda bata ma san anayi ba,  sabida doguwar suman da tayi.

          ~~
"Toh wallahi kasan abin yi, domin Fazilatul tana dab da lalata kome." Inji Sultanah Hoyam.
Shiru yayi tare da jan gemun shi yana tuno abinda ya faru, shekaru talatin da bakwai baya. Sabida yasan idan yayi mata magana a lokacin ba zata tab'a yarda bukatar su ta biya ba, amma da yayi mata hikima, bai zata kome zai lalace haka ba, kuma bai tab'a kawowa har yau zata kai tana raye..

              Yayi imani da Allah da bata raye da kome zai zo mishi da sauki, amma kasancewar ta a raye shine ya hana shi samun kan wancan d'an kusun uwar, d'an banza duk hanyar da aka bi sai ya kauce, Insha Allah da zaran ya cika shekara daya dole ya bawa Jasrah daman zama Sultanah ta gaba.

Koda Mehran baya so sai haka ya faru, yaga shegen da ya isa ya hana faruwan Al'amarin.

       "Karki damu, zamu sami abin yi ba zamu tafi a hakan ba, domin itace tayi riba, domin ita ke da Kowani b'angare sabida sanin cewa zata iya samun karfin mulkin da zata iya hana mu walwala yasa barta a gurin.

Babban shirin da zamu yi akan su ba karami bane, dan haka ki saka ido akan shi idan ya dawo, Ni kuma zan tinzira ta, tabar min Jasrah sai na san yadda zamu yi mu tura ta jikin Mehran, ta yadda zata cire mana Ikram a jikin shi."

            Murmushi suka yiwa juna tare da kowa ya kama hanyar shi, a hanyar komawa Fada, itama ta fara nata shirin.
"Mahlika lokacin ki yayi, ba zan tab'a barin wani ya shigo min ba tare da na dakatar dashi ba, wato ga sakarya na tashi a biyu. Babu hmmm Amir Hood kenan dole ka fadi a kasa na."

            Da wannan tunanin ta na cikin gidan.
    Shima a nashi tunanin cewa yake.
"Daga ke har Fazilatul nisa, dole na kawar da hankalin ku, na sami juya zaren azabarina na mulki kamar yadda naso haka tun baya, ba zan tab'a baku damar zama wannan yanayin ba. Har abada Ni zan cigaba da gwara kome,  cikin tsarina. Shima Mehran zan kasance cikin tafin hannu na."

    Kamar yadda itama tayi murmushi, bayan ta gama shirya gadar zare, haka shima ya sake murmushin mugunta tare da aiyana abinda yake shiryawa nan da d'an wani lokaci.

  ~~~
Washi gari
Da kan shi yayi ta bata madara har lokacin bata farka ba, tare da duk da haka yana jin a ranshi kome zai zo mata da sauki, kallon fuskarta yayi tare da dan bakin bakinta, hannun shi yakai kan bakin yana shafawa, tare da shafa kanta, a hankali yana me tausaya mata, tabbas uwa ba zata tab'a kuntatta d'a ko Y'a ba, wani irin zuciya ce a kirjin Maman shi? Wacce irin rashin imani ne a ranta, da har zata saka a yita azabtar da mutum babu tausayi ko jin kai.

Idanun shine yayi jajjur, amma zai dauki mata ki akan wannan abun da tayi. Ba zai tab'a kyale ta ba.

   "Sultan Insha Allah zata sami sauki,  ka rage damuwa kar kai ma ka."  Inji Fudail, Mik'ewa yayi tare da fita daga dakin, ya nufi waje.
Fudail yana biye dashi. Tare da jin Maman Mahlika suna tattauna akan wani abin da ya faru.
"Eh wallahi ance zaki ne wasu sunce damisa ne, amma kuma bamu san me ba, sai dai ya kashe Marwan ya kwashe kayan cikin shi ya cinye."

                  Kallon su yayi tare son jin meke faruwa.
"Wallahi bamu san meye yake faruwa ba, kawai dai ya fara cinye mana dabbobi ne tun wancan watan, yau kuma  ya tab'a dan gidan ladanin garin nan.."
   Saura Pages 9 na gama free book
```Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
     
Page 32

Bai kai ga rufe baki ba wasu mutane uku daga cikin dakarun da suke wajen gari suka iso gurin a guje a bisa Dawaki suna haki.

Sanan suka sauka a kan dawakan tare da kai hannun su gefen kirjina su bayan sun dunkule, suka Gaishe shi sannan biyu suka koma gefe. Babban cikin su ya fara magana.

"Sultan an sami matsala a inda muke!"
"Hmm!"
Yace mishi tare da kafe shi da ido,yana sauraren shi,
"Wani abu da bamu san meye shi ba, wa kashe mana dakaru guda bakwai, yau da asuba."

                   Iskar bakin shi ya furza bayan ya sauke ajiyar zuciya, shafa kan shi yayi yana kallon cikin garin baki daya, sannan ya kalle su. Yace
"Muje naga yadda garin yake."

   Babu musu suka shiga take mishi baya yana tafiya tare da kallon yana yin garin, har suka fara shiga dajin, basu yi nisa ba suka soma jin gurnannin abun,  durkusawa yayi tare da kallon sawun abin. Sannan ya kalli Fudail yace.
"Me kake tunanin yana yin wannan b'arnan?"
"Ina ganin damisa ce!" "Anya zata iya wannan b'arnan a lokaci guda,?" Bai bar Fudail ya karasa magana ba, ya tari numfashin sa.
"Toh Allah manasani."
Juyawa yayi tare da kallon Fudail, sannan ya ce musu, su juya. Har sun fara tafiya ya fara jin takun abin, umartar su yayi tare da hawa bishiya, suka zubawa Sarautar Allah ido, can kamar minti goma sai ga abin ya fito, ƙatuwar damisa. Hauka take sosai a duk lokacin da ta juya gefe da gefen ta, tayi da duba kusurwan kowani bishiy tana noman abu, kallon daya badakaren yayi yaga akwai baka a hannun shi,  makalewa yayi jikin bishiyar sosai ya amshi bakar tare da jan shi da karfi ya sake mata a gadon bayan ta, ihu tayi tare da niman wanda ya harbe ta, ta kuma jera kwarin  a jikin bakar har uku ya harbe ta,  ihu ta saka tare da nausawa daji.

         Basu kuma jin duriyar ta ba suka sauko. Kallon juna suka yi.
"Akwai abinda suka taba mata."

Da haka suka shigo gari tare da yiwa Baban Mahlika bayani, kiran mutanen garin yayi tare da tambayar su, waye ya tab'a damisan nan. Hango wani mutum suka yi ya juya da gudu, take Fudail yabi bayan shi da gudu, tare da saka mishi kafa, ya dauko shi suka dawo. Gaban Sultan Mehran.

      Mika mishi hannun Mehran yayi tare da kallon shi. Babu musu yace musu.
"Tun wancan watan me muka shiga daji ni da yarana, shine muka ga yaran suna ta kiwo toh sun bani sha'awa, shine na kwaso su."

  Kura mishi ido Mehran yayi yana hangon rashin imani akan shi. Kallon Fudail yayi, take ya dauki wasu dakaru suka nufi gidan Mutumin.  Sun sami Kanwar mutumin tana ta wasa da ya'yan Damisan, daukar su suka yi cikin Shegen tsiwa ta kalli Fudail tace.
"Kai me zaku mana da abun wasa na?"

   Wani kallon banza yayi mata tare da sakawa a dauke yaran, ai kuwa ta sha gaban shi.
" Bazasu dauka ba! Waye kai."
Rikota yayan yayi cikin rarrashi yace mata.
"Jiya mun yi baki ne, Sultan Aamaan na SAMAIND yana cikin garin nan ya kawo matar shi jinya dan haka kiyi hakuri, uwar su tana ta kashe mutane."

Tasa keyar shi suka yi, ta rike hannun shi. Jan shi suka yi tare da tafiya dashi, bin bayan su tayi tana kuka. Har kofar gidan su mahlika, tunda ta isa kofar gidan ta ga kusan rabin yan garin suna gurfane, kallon yaran damisar yayi yana kallon mutumin.

        "Ku hukunta shi!" Da gudu ta shigo gurin, tare da rungume yayanta, tana ihu.
"Wallahi ba shi bane ya saka aka dauko su,nice na dauko su. Don Allah ku bar min Yayana don Allah ba zai kuma ba."

"Alhamdulillahi, Sultan mara lafiyan ta farka!"
Kiran Fudail yayi tare da mishi magana a kunne, sannan ya koma cikin gidan.

Yana shiga cikin gidan, yaga yadda nake kokarin tashi zaune. Tsayawa yayi a bakin kofar, tare da kura mata ido, gaba daya ji yaƙe kamar bashi ba, wani irin yanayi yake ji akanta, wanda ba zai iya daukar shi a karamin abu ba, shafa kan shi yayi sannan ya tako kamar mara gaskiya ya iso gaban ta,.ya ja kujera ya zauna yana kallon fuskarta.
Hannun shi ya kai saman kumatunta yana shafawa tare da kallon cikin idanunta.

          Dukar da kai na, nayi ina wasa da hannuna ina kallon farcen hannuna, wanda suka samu nasu azabar, d'ago kai na yayi tare da cewa.
"Meye nufinki?"
Janye kai na nayi,.tare da kallon jikina yadda ya kama magani sosai, sake tambaya na yayi ban d'ago kai na kalle shi ba, asalima dauke kai nayi daga gare shi.
A na uku ne ya fusata tare da mik'ewa yayi wurgi da kujeran tare da daka min tsawa. D'ago kai nayi a hankali ina kallon shi..
"Kin rena ni?"
"Toh ka rabu dani mana, dole sai ka zauna da ni ne, ka tafi kayi rayuwar ka, ka bar ni na koma gurin ahalina na gaji da zama a kasan ka. Ka barni na tafi nayi rayuwa ta da wanda nake so. Yana gab da isowa inda nake.

       Don Allah ka kyale ni, ka barni na."
Buge min baƙi yayi tare da shake min wuya, ilahirin jikin shi rawa yake, idanun shi sun firfito.

   "Kika kuma kira min sunan wani namiji, sai na cire mishi gaban shi na ajiye mishi yayi rayuwa babu gaban shi."

" Na gaya maka ina da wanda nake so na kuma na gaya maka, Noman yana nan zuwa gare ni, sai dai ka kashe mu baki daya, mara imani da tausayi, ka rabu dani mana, dole ne sai na zauna a karkashin mulkin zalincin ka, mugu Azzalumi kawai. Kaje kai da Mahaifiyar ka sai Allah ya bi min hakkina. Ina fama da maraicina kuka rabani da farin ciki na, domin biyar bukatar kanku, baku san kome ba sai zalinci ko Allah madaukakin ya hana kan shi zalinci shi yasa baya zalinci dan shi adalin sarki ne.

  Ku kuma dake dabobbi ne bak..."
Kifa min mari yayi tare da kara min, d'ago Ni tayi tare da hada ni da bango, ya shiga marin bakina, kamar zai watsar min da hakora na.
"A iya kai na kake nuna jarumtar ka me yasa baka fita kasan meye a ke yi a cikin garin ba, kana kiran kanka da suna sarki kana kashe mutanen ka. Hakkin mu ba zai Barka ba."

        Cak ya tsaya yana kallon fuskana, a sanyayye wannan wacce irin rayuwa ce, watsar dani yayi a gurin tare da ficewa ya barni, Alimah tana jin su. Kasa hakuri tayi tare da shigowa dakin tana kallon yadda nake goge bakina, zama tayi tare da cewa.
"Me yasa kike mishi haka? Ko baki san babban mutum bane?"

Kallon ta nayi haka kawai naji a raina bata min ba, bakamar mijinta da yake da kirki ba, ita kuma fuskarta na kalla na Fahimci tana da fuska biyu, dauke kai nayi ban bata amsa ba, dan nima idan naji a raina ko Sultan da aka haifa a mulki sai haka, surutu tai ta min har ta gaji ta fita,

Na bita da harara. Haka na zauna ina nazarin rabona da ibada na, dan haka bayan fitar ta mijinta ya shigo da Fudail.
"Ina son yin sallah"
"Me yasa kike b'ata mishi rai ne?"
"Wa kenan?"
"Sultan Mehran mana!"
Ya faɗa a sanyayye. Yana kallon yadda nake kokarin yin alola.
"Toh sai me dan na b'ata mishi rai? Ba namiji bane shi, ai anyi shi dan na gaya mishi mara dadi da me dad'i, dan haka kai ma ka kara gaba kafin na kalli cikin idanun ka na fesa maka rashin kunya."

    Na fada tare da dauke kai na, zuciya yayi shima ya fita.
"Y'ata ki daina yin haka, Sultan Aamaan yana matukar girmama Al'amarin ki, karki saka shi ya fara jin tsanar wasu matan."

"Baba! Na gaji da zama a kasan mutumin da babu Allah a cikin tsarin shi, Baba na gaji da ganin Mehran baya ibada, me yasa ba zai gane girman Ibada ba, yau da ace Ahlillu kitab ne zan mishi Uzuri, amma musulmi ya haife shi fa, daular da yake mulki a gurin Kawun Annabi ne ya kafata.

    Shi waye da zai barranta kan shi da rahamar Allah, dan haka Ai Cigaba da jin bakakken magana har sai ranar da ya fara sallah. Zan daina mishi wulakancin"
"A'a babu dole a cikin addini karki tilasta shi bayan bai da niyya, ki bari dai idan shi ya bukaci hakan, kusan haramun ne tistalaw ayi addinin Musulunci dole. Karki yi haka, tunda yana jin maganar ki, kiyi kokarin ganin ya fahimci addinin kanta, Insha Allah zai yi yadda kike so."

   Nasiha yayi min a cikin hikima da dabara, sannan ya nuna min illar abinda nakewa Sultan Mehran, tunda a kasar shi nake bai dace na yi ta mishi hawan kawara.

        Ni kuma ina mishi haka ne da haushin Mahaifiyarshi.
.... Daukar yaran damisar nan suka yi tare da kai mata dajin suna bin hanyar da tabi, can suka ganta a yashe, Allah sarki duk da harbin jikinta bai hanata yunkurin mikewa ba, ajiye mata yaran yayi tare da kallonta, cikin dabara da hikima, ya zaga bayanta ya cire mata, kwarin da ya harba mata, sannan suka bar gurin tare da hawa bishiya, suna kallon ta, yaran shiga jikinta suka yi tare da fara shan nono, girgiza jikinta tayi tana lashe kan yaran, har suka gama sha,  suka mike tare da barin gurin.

      Abinda ya faru ya sanya shi kara tausayin Ikram, tabbas itama rabata aka yi da nata rayuwar, shi yasa ta zama wata irin baudaddiyar mutum mara dadin zama. A hankali suka sauko tare da barin dajin, tunda yazo garin jiya bai samu yayi wanka ba, dan haka suna isa gidan Yasaka Fudail ya hada mishi ruwan yayi wanka, sannan ya cire kayan marasa nauyi dai dai da shigar kowa ya saka, tare da ajiye na mulkin yana me jin shi sakayau.

Yana son zuwa duba jikinta dukda abin da tayi mishi, amma zuciyar shi tana hana shi, dan haka ya share batun ta ya cigaba da abinda yake yi, har dare. Kunna wutar itacce aka yi suka zauna a waje kasancewar an fara tunkarar lokacin sanyi kuma suma suna fama da dusar ƙanƙara.

                  Hira Fudail yake tare da Baban Mahlika, sosai ban da shi da yayi zurfi cikin damuwa, domin kuwa hiran da suke tayi mugun tab'a shi wanda kusan dukkan su akan addini ne, sai yake jin babu dadi. Dan haka ya mike tare da musu sallama, ya nufi gidan shi.
"Sultan baka duba Ikram ba?"
Girgiza musu kai yayi sannan ya wuce abin shi.

       "Suna son junan su, amma rashin fahimtar juna yasa suke azabtar da ruhin su!" Inji Baban Mahlika,
"Babu kome a tsakanin su, kawai dai basa jituwa ne amma bana tunanin akwai soyayya a tsakanin su"

   Dariya yayi irinta manyan sannan yace mishi.
"Akwai kauna a tsakanin su, me tsafta kuwa,  dan haka karka yi mamaki suna kaunar junan su, kawai taran miskilai ne ba lallai kowannen su ya fahimci haka ba,sabida yadda suke mu'amalatar junan su, kamar zasu cinye kan su."

      Haka dai yayi shiru, bai ce kome ba, dan yana

Please Login or Register in order to submit comment