Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 51: *Taswirar Barban*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
UMAR SANGARU
*
Aljani Sheezuwa ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "Lallai kai Kuffuru ka fi kowa sauri, kawai daga ganin Hodon sai kace aje a kamo shi? Inda ace Hodon zai kamu cikin sauƙi haka, da zai kai wannan lokaci yana sata?
"Na farko Barban yana tare da aljanin da yafi kowanne aljani ƙarfin sihiri a duniya. Na biyu ba ku gina kurkukun da za'a kulle shi a cikin ta ba. Waɗannan abubuwa guda biyu su ne zasu hana mu zuwa kamo Hodon a yanzu.
"Kuffuru, idan baka manta ba, nace bazan amsa maka waɗannan tambayoyi guda biyu da kayi ba, face kun gama haɗuwa SADAUKAI UKU. Tambayoyin naka su ne mene ne dalilin da yasa Barban ya bari aka samar da taswirarsa? Wanne tubali za'a gina wannan kurkuku da shi? Ku nutsu da kyau ku ji wannan bayani nawa.
"Duk duniya babu wanda ya isa amsa wannan tambaya akan dalilin da yasa Barban ya bari aka samar da taswirarsa face shi kansa. Wataƙila yana so yayi amfani da wannan dama ne wajen nuna ƙarfinsa a duniya, wataƙila kuma yana so yayi amfani da wannan dama ne domin ya bayyana kansa ga idon duniya. Amma ko kaɗan bana tunanin yayi haka ne domin ya miƙa wuya.
"Tubalin da za'a gina wannan kurkuku da shi kuma, duk duniya babu inda ake samunsa face kwarin Jekish. Wannan tubali ragowar wani ƙaton dutse ne, da ya yi bindiga ya narke. Ruwan dutsen ne ya haɗu a waje guda ya samar da wannan tubali. In dai kuka sami wannan tubali aka gina wannan kurkuku dashi, kuma aka kulle Barban a ciki. Duk duniya babu wanda ya isa ya fiddo shi daga ciki.
"Shin kun san a ina wannan kwarin Jekish yake?" Aljani Sheezuwa na zuwa nan a zancensa ya ɗan yi shuru ya baiwa su sarki Kuffuru dama ko zasuyi tambaya. Tsahon ɗan lokaci shuru babu wanda yayi tambaya.
"Kwarin Jekish, na can yankin birnin Auzur wanda yayi iyaka da yankin Dilikem. Daga wannan wuri zuwa kwarin Jekish tafiya ce ta kusan watanni goma. Koda akan aljani mutum zaiyi wannan tafiya saiya shafe waɗannan watanni goma, amma daɗinta shi ne, har mutum ya isa wannan wuri ba zai haɗu da komai na sharri ba.
"Babbar matsalar ita ce babu wanda ya san mene ne a cikin kwarin Jekish. Saboda haka dole ne muyi taka-tsantsan idan muka je wannan wuri."
Sarki Kuffuru, sarauniya Rauziyya da sarki Darwazu suka fara kallon juna cikin tsananin mamaki, ko sunan wannan kwari basu taɓa ji ba, ballantana su san haɗarurrukan dake cikinsa.
"Ina da tambaya," inji sarki Darwazu. "Idan muka je wannan kwari, tayaya zamu iya ɗebo wannan tubali mai yawa wanda zai isa a gina wannan kurkuku?"
Aljani Sheezuwa yayi murmushi ya ce, "Tare zamuyi tafiyar, sannan ni ne zan ɗebo wannan tubali. Akwai wata tambayar?"
Tsahon ɗan lokaci suka yi shuru. Aljani Sheezuwa yayi gyaran murya ya ci gaba da bayani.
"Aljanin dake tare da Hodon yafi ƙarfin ifritu. Kuyi sani cewa ifritu ba su da yawa a duniya, kowanne ifritu yana da makami na musamman wanda zai hallaka shi a duniya. Amma, ga aljanin da yafi ƙarfin ifritu babu makamin da zai iya kashe shi, face ƙarfin ruhi wanda babu kamarsa a duniya.
"A taƙaice dai, ina so na sanar da ku cewa ba zamu iya kashe wannan aljani dake tare da Barban ba, face Kuffuru ya mallaki RUHIN SAMUDUL ANSARI. Da wannan ƙarfin ruhi ne kaɗai zai iya amfani wajen tarwatsa ruhin wannan aljani."
Sarki Kuffuru na jin wannan batu yaji wani abu a cikin ransa, ya tabbatar da cewa kamo Barban ba ƙaramin aiki bane. "Meye amfanin gina wannan kurkuku, idan har bamu kamo Barban ba. Nake ga ai kamar wahalar banza ce. Me zai hana mu fara tunkarar mallakar wannan ruhi daga yanzu, idan yaso bayan mun mallaki ruhin sai muyi tunanin gina wannan kurkuku?" inji sarki Kuffuru.
Aljani Sheezuwa yayi murmushi ya ce, "Ba zaka gane bane. Shi wannan aiki da kake kallo, dole ne a bi komai daki-daki. Gina wannan kurkuku shi ne aiki na farko, daga nan sai tarwatsa ruhin wannan aljani. Kana tunanin mallakar ruhin sarki Samudul Ansari zaiyi sauƙi ne?"
Sarki Kuffuru ya murtuƙe fuska ya ce, "Shi kenan. Na amince."
Lokacin da wannan madubin tsafi yazo wannan wuri, sai boka Biu Lin yasa hannunsa yaja abinda ke faruwa gaba, inda aka nuno sarki Kuffuru, sarki Darwazu, boka Hubbazu da sarauniya Rauziyya zaune bisa aljani Sheezuwa suna ta tsala azababben gudu a cikin gajimare.
Sarki Ayubul Zairiy ya dubi wannan boka cikin tsananin mamaki ya ce, "Me sarki Kuffuru yake shiryawa?"
Boka Biu Lin ya dube shi ya ce, "Sarki Kuffuru da waɗannan mutane sun haɗa kai domin kamo Barban. Sun samar da taswira mai ƙarfin gaske wacce zata bi diddigin Barban. Na san zai yi wuya ace kun san wannar sarauniya, ba wata bace illa sarauniya Rauziyya. Duk wanda ya samu labarin gumurzun da ya faru a kurkukun-mutuwa zaiyi mamaki idan aka ce masa sarauniya Rauziyya da sarki Kuffuru sun haɗa kai.
"Kuyi sani cewa sarki Kuffuru ya kashe sarki Ratanam, sannan ya ɗauki yarima Marganu ɗan sarki Ratanam ya kaiwa shi wannan sarauniya. Wannan shi ne dalilin da yasa ta amince suka haɗa kai da sarki Kuffuru a yadda suka nunawa duniya, amma dole nasan akwai ɓoyayyen sirri.
"Wannan kuma, ɗan ƙabilar Adbenchan ne. Sarki Darwazu sunan sa, ƙasar Askandariyya yake mulki..." Kafun wannan boka ya ƙarasa jawabinsa sarki Ayubu ya dakatar dashi da hannu.
"Mene ne ma'anar nuna wannan abu da yake faruwa a cikin wannan madubin tsafi?" sarki Ayubu ya tambaye shi.
Boka Biu Lin ya ɗan haɗe gira, kafun daga bisani ya amsa masa. "Dole ne ku tafi farautar wannan taswira, kuyi ta bin su sarki Kuffuru a baya har zuwa inda ya dace, ku farmake su ku kwaci wannan taswira. Saboda a halin yanzu babu taswirar da za'a samar ta nuna ainihin inda Barban yake face wancar ɗin."
Sarki Ayubul Zairiy ya zaro idanu cikin mamaki ya ce, "Ah haba! Wannan abu zai yiwu kuwa? Sarki Kuffuru mai aljanin duwatsu. Sarauniya Rauziyya mai aljani Barzasa. Ga wannan baƙon sarkin. Ga boka Hubbazu mai ƙarfin sihiri. Ga wannan aljani dake tare dasu. Anƴa zamu iya kwato wannan taswira daga hannunsu kuwa?"
Boka Biu Lin ya yi dariya ya ce, "A ɓangaren ku, ga ka nan kana da aljani Jizid. Ga boka Ruguzan jikan Shashamu. Sannan ga sarkina Kim Sam, babu abinda kuka sani akansa. Uwa-uba gani nima zanyi muku rakiya gani nake daidai muke da su."
Koda sarki Ayubu yaji wannan batu sai hankalinsa ya ɗan kwanta amma da yake yasan waye Kuffuru har a wannan lokaci, bai gama samun nutsuwa ba. Amma, ga dukkan alamu wannan boka ma zai kasance mai tsananin ƙarfin sihiri duba da yadda yake sarrafa tsafi kamar kayan gidansu.
Sarki Kim Sam ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Mu a wannan nahiya tamu, ba kamar wajajen ku bane. Mu ba ma sarrafa aljanu, mun fi yin imani akan sihirtattun makamai masu firgitarwa. Zan iya ce muku tunda nake a rayuwata bai fi sau uku na taɓa yin ido-da-ido da aljani ba. Tun da yanzu mun haɗa kai zan zayyane muku dukkanin ƙarfin sihirina da ƙarfin shiri na.
"Kamar yadda na faɗa muku da farko, a wannan nahiya bama sarrafa aljanu. Ni wani sihirtaccen mashi na sihiri nake sarrafawa. Komai yawan runduna ta mayaƙa idan na shiga cikin su da wannan mashi sai na ragargaza su. Komai duhun waje idan na shiga da wannan mashi sai yayi haske. Sannan bugu-da-ƙari wannan mashi nawa yana iya rikiɗa ya zamo jibgegen shaho na hau kansa ya kaini duk inda nake so a faɗin duniya."
Sarki Kim Sam na zuwa nan a zancensa ya fiddo wani mashi dake ɗaure a gadon bayansa ya nunawa shi su sarki Ayubu. Mashi ne dogo mai haske da walwali kamar fitila.
Boka Biu Lin yayi murmushi ya ce, "Haka ne. Ni kuma abubuwa guda biyu nake sarrafawa. Na farko wata dardumar tsafi ce, na biyu kuma wata isga ce ta tsafi. Wannan darduma tawa tana iya ɗaukar mutane komai yawansu ta kai su waje. Wannan isga tawa kuma, komai ƙarfin sihirin mutum kafun ya iso inda nake da tafiyar mako guda zata nuna min. Kuyi sani cewa tun kafun kuzo wannan birni namu, na riga na kalle ku sannan na kalli abinda ke tafe da ku.
"Saboda haka bin bayan su sarki Kuffuru ba zai bamu wahala ba, abinda kawai zai wahalar da mu shi ne tayaya zamu iya sace wannan taswira, batare da sun sani ba?"
Sarki Ayubul Zairiy ya gyaɗa kai ya ce, "Shin za mu iya ƙwatar wannan taswira da ƙarfi?"
Boka Biu Lin ya ce, "Ya danganci yanayin yadda damar tazo mana. Idan muka ga tazo da sauƙi sai mu ɗauketa cikin ruwan sanƴi. Idan muka ga tazo da wahala sai mu gwada ƴar ƙwanji."
Sarki Ayubu ya yi murmushi ya ce, "Lokaci yayi da zan nunawa sarki Kuffuru ainihin waye ni."
Sarki Kim Sam da boka Biu Lin suka yi murmushi. Sarki Kim Sam ya shafi wani wuri a jikin wannan mashi nasa, nan take mashin ya rikiɗe ya zamo jibgegen shaho. Kim Sam ya dubi sarki Ayubu ya ce, "Kaine abokina sarki, zo mu zauna akan wannan mashi domin yin wannan gagarumar tafiya." Ayubu na jin haka yayi murmushi ya ƙarasa wurin wannan ƙaton shaho ya haye kansa, sarki Kim Sam ya zauna a gefensa. Abin mamaki dukkansu su biyun suka zaune ɗare-ɗare akan shaho ba tare sun takura ba.
Boka Biu Lin yayi murmushi shima ya samar da wannan darduma tasa, ya kira boka Ruguzan suka zauna su biyu akanta. Ba tare da ɓata wani lokaci ba, wannan ƙaton shaho da wannan darduma suka tashi sama cikin iska suka ratsa ta rufin wannan fada suka fice suka bayyana a cikin gajimare. Daga bisani suka fara tsala azababben gudu na gaban kwatance suka nufi yankin kwarin Jekish wato inda su sarki Kuffuru suka nufa.
A wannan rana sarki Ayubul Zairiy da sarki Kim Sam suka ƙulla ɗamarar kamo Barban su ma.
***
Rana na daf da faɗuwa Barban ya gama yiwa jama'ar dake cikin wannan fada bayani akan shirye-shiryen su na sake kafa daular Shaha, yana gama bayanin ya sallami dukkanin jama'ar dake cikin fadar sannan shima ya juya ya fice daga cikin fadar, ya nufi wannan gida da su Aymanul Faris.
Yana zuwa ya samu tuni an gama shirya abincin dare bisa wani ƙaton teburi. Aymanul Faris da jaruma Riya suna zaune su biyu rak a cikin ɗakin cin abincin, jaruma Riya sai nuna masa soyayya take.
Aymanul Faris na ganin Barban ya shigo ɗakin yaji daɗi a ransa, saboda ko ba komai zai ɗan huta da kalaman jaruma Riya. Shima Barban ganin su da yayi su biyu a cikin wannan ɗaki yasa yaji daɗi a ransa. Saboda a wannan rana zai sanar da Aymanul Faris aikin da zasu yi na huɗu, sannan ta fuskoki da dama ayyukan sun shafi jaruma Riya.
"Kai Ayman! Alƙawarin da kayi yau ɗin nan ya burgeni ba kaɗan ba. Maigirma Ranganu ya ce na sanar da kai cewa, shima yana ra'ayin wannan buri naka. Ya ce a faɗa maka zai taimaka maka sosai wajen ganin wannan buri ya cika. Sannan ya kawo min bayanan abun hari na huɗu."
Barban na zuwa nan a zancensa Aymanul Faris yayi murmushin jin daɗi bisa jin cewa aljani Ranganu zai taimaka masa wajen cikar wannan buri. Amma, da ya tuno maganar Barban ta ƙarshe sai ya ɗan haɗe fuska ya dubi inda jaruma Riya ke zaune. Wato kamar yana so ya ce mata ta tashi ta fita tunda zasu tattauna akan abinda bai shafe ta ba.
Koda Barban ya fuskanci haka sai yayi murmushi ya dube shi, "Kada ka damu, na san da cewa tana wannan wuri shiyasa na kawo batun wannan aiki na huɗu saboda aikin ya shafe ta matuƙa, kuma zan iya cewa kusan domin ita zamuyi wannan aiki. Sannan dole sai da ita da wannan takobi ta Saiful Shiradu wannan aiki zai kammala."
Aymanul Faris da jaruma Riya suka dubi juna cikin tsananin mamaki. "Ban gane me kake nufi da wannan aiki ya shafe ni ba?" jaruma Riya ta tambayi Barban.
Barban ya yi guntun murmushi ya ce, "Kada ki damu, idan nayi miki bayani za ki gamsu. Wai shin ina sulken yaƙin mahaifinki wanda mahaifiyarki ta ba shi a matsayin kyauta lokacin aurensu?"
"Sulken yaƙin mahaifina kuwa?" inji jaruma Riya ta ɗan yi shuru tana tunani, Barban da Aymanul Faris suka zuba mata idanu sannan suka bata dama tayi ta tunani har kusan rabin sa'a sannan ta numfasa ta ce.
"Ah na tuna... Lokacin da nake yarinƴa ƴar shekara goma sha-uku tabbas ina ganin wani sulken yaƙi a jikin mahaifina mai ban al'ajabi. Amma ban taɓa tambayarsa bayanan wannan sulke ba, kuma bai taɓa fada min komai akan sulken ba. Ban san yadda akayi ya rasa wannan sulke ba, kuma ban taɓa tambayarsa ba."
Barban ya sake yin guntun murmushi ya ce, "Wannan sulke shi ne abinda zamu je mu ɗakko na huɗu. Kina son jin bayanan wannan sulke da kuma inda yake a halin yanzu?"
Cikin farin-ciki da kaɗuwa jaruma Riya ta ce, "Tayaya zan ƙi jin bayanan abinda mahaifina ya bar min. Ai sai inda ƙarfina ya ƙare akan mallakar wannan sulke nasa."
"Tabbas haka nake son ji, yanzu sai ku saurara da kyau domin jin darajojin wannan sulke." inji Barban.
"Shi dai wannan sulke," ya ci gaba da bayani. "Wani maƙeri ne dake rayuwa a birnin Hindu ya ƙera shi. Wani bafatake dake cin kasuwannin tsibirurruka yazo wannan tsibiri da shi, matar sadauki Jarata, jaruma Wahiba ta kalle shi ya burgeta ta saya masa.
"Wannan sulke ba kamar sauran kayan yaƙi yake ba, maƙerin da ya ƙerashi ya zuba basira sosai wajen samar da sulken. Komai kaifin takobi da tsininta bata tasiri a jikin wannan sulke, sannan komai ƙarfin naushin ƙato baya ratsawa ta cikin wannan sulke. Kai, ko ruwan kibbau ake mutum zai ratsa ya wuce lafiya matuƙar aka ce akwai wannan sulke a jikinsa. Kaɗan daga cikin falalolin wannan sulke kenan.
"A ina wannan sulke yake a halin yanzu? Kuyi sani cewa, maƙerin da ya ƙirƙiri wannan sulke ba'a ƙashin kansa ya ƙera shi ba. Wani gawurtaccen sarki ne dake rayuwa a birnin Hadriyan yayi hawa da kansa yaje har ƙasar Hindu yasa wannan maƙeri ya samar masa da wannan sulke. Ance shi wannan maƙeri ya amince zai samar masa sulken da farko, amma da ya kammala sai suka samu saɓani akan ladan wannan aiki. Kwatsam kuma! Wannan baƙon attajiri yayi arba da wannan sulke, nan take yayi masa tayi mai kyau.
"Wannan maƙeri ya amince karaf ɗaya, saboda maƙudan kuɗin da wannan attajiri ya saka masa.
"Sarkin birnin Hadriyan yayi baƙin ciki matuƙa bisa ganin cewa duk tsahon tafiyar da ya shafe daga birninsa zuwa wannan birni na Hindu amma ace bai samu biyan buƙata ba. Saboda wannan dalili daga wannan lokaci yake ta farautar wannan sulke.
"Ance babu irin farmakin da bai kaiwa wannan attajiri ba, amma baiyi nasara ba. Saboda wannan attajiri yana da tsari sosai a jikinsa. Dukda haka SARKI DUJALU na birnin Hadriyan bai haƙura ba.
"Da ya samu labarin wannan sulke yana tsibirin Gazwar sai ya fara shiri yana zuwa a matsayin bafatake yana leƙen asiri domin gano wanda ya mallaki wannan sulke. Daƙyar da siɗin goshi ya gano inda sulken yake."
Barban na zuwa nan a zancensa ya dubi Aymanul Faris da jaruma Riya ya ce, "Bari na nuna muku yadda aka yi wannan sulke ya salwanta daga hannun sadauki Jarata." Yana faɗin haka ya nuna wani madubin tsafi dake jikin bango da hannunsa na hagu.
Nan take wannan madubin tsafi yayi haske sannan ya nuna hoton duniya, ya nuna hoton teku, ya sake zuƙowa ya nuna hoton wani ƙaramin tsibiri wanda keda ƙananun gidaje da gonannaki akan sa.
Abin mamaki wani saurayi ne keta noma a cikin wannan gona. Rana tayi yamma tana daf da faɗuwa. Wannan saurayi na niyyar tashi daga wannan aiki kenan, wani baƙon mutumi yazo wannan gona tasa. Wannan mutumi sanye yake cikin alkyabba irinta attajiran larabawa. Gajere ne sosai sannan yana da ƙasumba. Kana ganin fuskarsa kaga mutumin kirki wanda ko kaɗan baiyi kama da masu mugunta ba.
Wannan saurayi na ganin wannan mutumi ya jefar da fartanƴar dake hannunsa ya ruga inda mutumin ke tsaye. Yana zuwa ya gaishe da mutumin.
"Alaji. Lafiya ka kawo min ziyara har gonata da kanka?" inji wannan saurayi.
Jaruma Riya tana ganin wannan mutumi ta shaida shi, domin kuwa ba wani bane illa sadauki Jarata mahaifinta wanda ya haife ta. Wannan gajeren mutumi ne basu gane wane ne shi ba, amma sai suka zubawa wannan madubin tsafi idanu.
Wannan bafatake ya hanga izuwa bayan sadauki Jarata ya hango wata rigar sulke ajiye a saman bishiya, sai farin ciki ya kama shi.
"Nazo duba shinkafar da muka yi magana akanta ne." inji mutumin. Ga dukkan alamu dama ya ɗan saba da sadauki Jarata.
Jarata ya yi murmushi ya juya da nufin nunawa wannan mutumi wannan shinkafa, kawai sai yaji wannan mutumi ya shaƙo wuyansa ta baya, sannan ya shaƙa masa hodar banju. Nan take Jarata ya bingire a wannan wuri yayi ta sharara barci, wannan mutumi ya ƙarasa gindin wannan bishiya wanda wannan sulke yake kanta, ya ɗakko sulken, sannan ya doki ƙasa da sawunsa guda, nan take ya tashi sama tamkar daga cikin majaujawa aka harba shi. Ya ɓace a cikin gajimare.
"Wannan mutumi da kuka gani ba wani bane illa sarki Dujalu na birnin Hadriyan, kamar yadda kuka gani, shi ne wanda ya sace wannan sulke na sadauki Jarata." inji Barban.
Jaruma Riya ta ɗan haɗe fuska cikin fusata ta ce, "Amma, saboda me mahaifina bai faɗa mana wannan labari ba?" Barban da Aymanul Faris suka yi shuru basu ce da ita komai ba, saboda basu san amsar da zata dace da wannan tambaya ta ta ba.
"Yaushe zamu ɗauko wannan sulke, kuma a ina yake a halin yanzu?" jaruma Riya ta sake tambayar Barban.
Barban ya dubi Riya cikin nutsuwa ya ce, "Ban san a ina wannan sulken-yaƙi ba, kuma bansan ranar da zamuje wannan birni ba. Amma, yau da dare nake tunanin aljani Ranganu zai kawo min bayanan komai."
Barban na zuwa nan a zancensa Hajriya ta shigo cikin wannan falo, don haka sai dukkaninsu suka ja baki suka yi shuru. Barban da Aymanul Faris suka gaishe da ita, sannan aka ci gaba da cin abincin dare.
***
Yau *01/12/2022*
Babi na gab a zaizo *03/12/2022* da izinin ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 52: *Sadauki ma'aboci Isik*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
UMAR SANGARU
*
Farin haske ne mai kama da tauraruwa mai wutsiya keta tsala azababben gudu a cikin sararin samaniya, yana giftawa ta saman birane, tekuna da tsaunika. Tsahon ɗan lokaci yana ta wannan gudu kafun daga bisani ya iso saman wani ɗan ƙaramin gari.
Yana zuwa saman wannan gari haskensa ya ragu ainun, a hankali ya rabe gida uku, sannan ya sake rikiɗewa izuwa halittu guda uku ta waɗansu mutane suka faɗo ƙasa. Abin mamaki waɗannan mutane sun kasance maza guda biyu da kuma mace guda ɗaya.
Idan mutum ya ƙare musu kallo zai fuskanci cewa ba wasu bane illa yarima Marganu, gimbiya Firziyya da tsoho Aydenlik.
"Mun zo gari na farko daga cikin waɗannan garuruwa guda uku, shiyasa kuka ga mun saƙƙo ƙasa ba tare da shiri ba. Babu sihirin tsafin dake aiki a wannan wuri saboda mugun-kafin dake wurin." inji Aydenlik.
Marganu da Firziyya suka gyaɗa kai cikin fahimta, Aydenlik ya wuce gaba suka take masa baya suka nufi wannan gari na farko da suke hangowa daga nesa.
Tafiyar taku arba'in kacal suka yi suka iso ƙofar wannan gari wanda aka yi shi da baƙin ƙarfe. Babu ko mai gadi guda ɗaya a wannan wuri amma ƙofar a kulle take da wani zabgegen kwaɗo.
Marganu ya yi murmushi ya fiddo wannan takobi ta mahaifinsa, ya ɗagata sama. Nan take wani jan haske ya bayyana a daidai inda ƙarfen takobin yake.
Marganu ya sari wannan kwaɗo da ita, take jan hasken nan ya ratsa ta cikin kwaɗon ya rabe gida biyu ya zube a ƙasa. Aydenlik da Firziyya suka yi murmushi, Marganu ya juyo ya dube su a lokacin da ya buɗe wannan ƙofa.
Ƙofar tana gama buɗewa Marganu ya kunna kai izuwa cikin garin, Aydenlik da Firziyya suka take masa baya. Marganu na riƙe da wannan takobi ta haske, shi kuma Aydenlik waɗannan duwatsu guda huɗu na tsafi su ne suke yawo akan tafin hannunsa na hagu. Gimbiya Firziyya kuma waɗannan takubba nata

Please Login or Register in order to submit comment