Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kana tunanin kai ɗaya ka isa ka tafi neman Marganu ne, sannan ka tsaya jiran sarki Ayubu, a lokaci guda kuma, ka koma ka ci gaba da tafiyar da harkokin mulkinka?"
Sarki Kuffuru yayi jinjina kai, saboda wannan ba abu bane mai yiwuwa.
Boka Hubbazu ya ce, "Fiddo takobinka a fara wannan aiki..."
"Kafun mu fara wannan aiki," inji sarki Kuffuru. "Ina so ku sanar dani, wannan abu wanda kuka ce, idan na gan shi zan iya faɗuwa a wannan wuri matacce?"
Hubbazu yayi dariyar takaici ya ce, "To, idan muka nuna maka, ka faɗi mataccen fa?"
Sarki Kuffuru yayi shuru maimakon ransa ya ɓaci, kawai ya tunani ya fara cikin nutsuwa. Tsahon ƴan daƙiƙu yana ta tunani, kafun daga bisani ya ɗago ya dubi Hubbazu ya ce.
"Ni fa ba yaro bane. Kuna tunanin akwai baƙin cikin da ban taɓa gani ba a duniya? Sannan ko kuna tunanin zuciyata raguwa ce, wacce zata karaya idan taji labari mara daɗi? Na umarce ku, ku sanar dani wannan sirri, kafun raina ya sake ɓaci."
Boka Hubbazu ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Nayi alƙawarin sanar da kai, wannan sirri, amma bayan mun ɗebo wannan tubali na kwarin Jekish."
Aljani Sheezuwa da boka Hubbazu suka ɓoyewa sarki Kuffuru labarin haɗa kai da ƴarsa Firziyya tayi da Marganu domin a kawo ƙarshen sa. Ba don komai Hubbazu ya ƙi faɗa masa wannan labari ba, sai domin yana so idan aka turawa Marganu wannan sadauki [jinin-Infiro] idan ya kashe shi, sai ya kamo Firziyya.
Sarki Kuffuru zai fi jin daɗi, idan aka ce an kamo masa Firziyya maimakon a sanar dashi wannan butulci da tayi masa.
Koda sarki Kuffuru ya fuskanci cewa su boka Hubbazu ba za su sanar da shi, wannan sirri ba, sai ya dube su ya ce, "Na amince, idan muka ɗebo wannan tubali zaka sanar dani wannan sirri."
Yana gama faɗin haka ya zaro wannan takobi ta Siwod-del-bulod ya ƙaddamar da waɗannan halittu guda talatin ɗin nan.
Sadaukai guda goma. Aljanu guda goma. Dabbobi guda goma.
Boka Hubbazu ya fiddo wani madubi a cikin jakar-tsafinsa ya haska fuskar sarki Kuffuru da shi, sannan ya tashi tsaye, ya tunkari waɗannan sadaukai guda goma masu sanƴe da baƙaƙen tufafi da hular sanƴi wacce ta sauƙo ta ɗan rufe musu fuskokinsu.
Yana zuwa daidai na farkon, ya cire hular sanƴin dake kansa, sannan ya haska wannan madubin tsafi a fuskarsa. Nan take fuskar sadaukin ta rikiɗe ta juye izuwa irinta sarki Kuffuru.
Kamar yadda ya yiwa na farkon, haka ya bi dukkanin waɗannan sauran guda taran su ma yayi musu. Sadaukai guda goma fuskokinsu suka juye izuwa irin na sarki Kuffuru. Ba su da bambancin komai a tsakaninsu, idan ka gansu zaka rantse ka ce sarki Kuffuru ne saboda tsananin yadda suke kama.
Dukkanin su suka zo gaban sarki Kuffuru suka zube ƙasa, suka kwashi gaisuwa cikin biyayya.
Boka Hubbazu ya dubi sarki Kuffuru ya ce, "Ka baiwa waɗannan sadaukai umarnin abinda muka faɗa ma, saboda duk duniya babu mai umartarsu idan ba kai ba."
Sarki Kuffuru ya yi murmushi ya dafa kafaɗar na farkon su ya ce, "Ka tafi izuwa birnin Kufa, ka ci gaba da tafiyar da harkokin mulki kamar yadda na saba. Ka kula da rayuwar ƴata Firziyya ta kowanne hali, saboda ita ɗin rayuwata ce. Bani da kowa a duniya, idan ba ita ba."
Aljani Sheezuwa da boka Hubbazu suka haɗa idanu lokacin da suka ji wannan umarni na sarki Kuffuru, suka yi ajiyar zuciya a tare. Amma, da yake sarki Kuffuru na gaban sadaukai jinin Infiro guda goma baiji su ba.
Kuffuru ya sake ɗaura hannunsa akan kafaɗar na biyu ya ce, "Ka tafi farautar Marganu, ina so ka saro min kansa, da na duk waɗanda suke tare da shi."
Ya zo kan na ukun ya ce, "Ka tsaya a wannan wuri, ka jira zuwan sarki Ayubu, ka hallaka shi."
Koda yazo nan a zancensa sai ya dubi sauran guda bakwai ɗinnan ya ce, "Ku kuma ku tafi farautar duk wani abokin gabata a duniya, ku kashe shi, ku saro min kansa."
Sadaukai jinin Infiro suna gama jin wannan umarni, suka zube ƙasa gaba ɗaya a gaban sarki Kuffuru, cikin biyayya suka amsa.
Waɗannan guda biyu da ya baiwa umarnin zuwa birnin Kufa da inda Marganu yake, suka zaro irin wannan takobi ta Siwod-del-bulod, sannan suka doki ƙasa da sawayensu irin wannan doki mai fuka-fuki ya fito daga ƙarƙashin ƙasa. Suka haye bisa waɗannan dawakai sannan suka tashi sama suka ɓace ɓat.
Sauran guda bakwai ɗinnan suka yi girgiza suka ɓace ɓat. Guda ɗayan nan kuma, sai ya zauna a cikin wannan tanti.
Sarki Kuffuru ya dubi su boka Hubbazu ya ce, "Da ina da kwakwanto a cikin raina, amma, yanzu da naga wannan shiri naku, hankalina ya kwanta. Tabbas waɗannan sadaukai zasu yi maganin duk abokin gaba tawa."
Boka Hubbazu yayi dariya ya ce, "Shiri ya riga ya kammala. Ku zo mu koma wajen abokan tafiyar mu, a ci gaba da tafiya."
Yana faɗin haka ya miƙe tsaye ya fita daga cikin ɗakin, aljani Sheezuwa ya take masa baya.
Kuffuru ya yi murmushi ya mayar da takobinsa cikin kufe, dukkanin waɗannan halittu guda ashirin da suka rage suka ɓace ɓat.
Sarki Kuffuru ya dubi wannan sadauki dake kama da shi, cikin tsananin mamaki. Sadaukin yana tsaye cak, a tsakiyar wannan tanti, ko motsi baya yi tamkar wani gunki.
Bambancin waɗannan sadaukai da sarki Kuffuru kawai shi ne suturar jikinsu baƙa ce, tamkar likkafanin mutanen farkon zamani.
Sarki Kuffuru ya tashi shima ya fice daga cikin wannan tanti.
****
Yau *08/12/2022*
Babi na gaba zaizo *10/12/2022* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 55: *Sarki Dujalu na birnin Hadriyan*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
UMAR SANGARU
*
Barban, Aymanul Faris da jaruma Riya ne zaune a cikin wannan falo sun ƙurawa wata ƙaramar taswira da aka shimfiɗe akan teburi idanu. Abin mamaki wannan taswira ta wani ƙaton gida ne wanda aka gina akan ƙaramin tsibiri a birnin Hadriyan.
An yiwa gidan fasali kamar gidan tarihi. Ƙofar shiga wannan gida guda ɗaya ce jal, sannan akwai zanen hotunan dakaru guda uku kacal masu tsaron gidan. Waɗannan abubuwa su ne kawai a jikin wannan taswira shiyasa bata da girma sosai.
"A cikin wannan gidan," Barban ya fara jawabi. "A cikinsa sarki Dujalu yake ajiye abubuwa masu muhimmaci nasa. Haka itama wannan sulke a cikin wannan gida take ajiye. Kamar yadda kuka gani wannan gida a saman wani ɗan ƙaramin tsibiri aka gina shi.
"Sannan akwai dakarun tsaro guda uku kacal da suke gadi. Za ku iya cewa mutum uku kacal, sun yi kaɗan su yi tsaron wannan gida na kayayyakin sarki Dujalu. Waɗannan dakaru guda uku ba kamar sauran mutane suke ba. Bari na nuna muku yanayin halittunsu ɗaya bayan ɗaya."
Barban na gama faɗin haka ya samar da madubin tsafi a saman wannan taswira, sannan ya shafi madubin da hannunsa na hagu. Nan take yayi haske ya nuna hoton wani zabgegen mutum, dogo kuma murɗaɗɗe.
"Wannan shi ake kira sadauki Kamaru, ga shi dai jikinsa irin na mutane ne amma ruwa-biyu ne. Maigirma Ranganu ya ce, rabin jikinsa na mutum ne, rabi kuma na dodo. Duk faɗin birnin Hadriyan babu sadauki mai tsananin ƙarfin damtse kamar sa, wannan shi ne dalilin da yasa Dujalu ya ɗauke shi aiki a wannan gida."
Yana zuwa nan a zancensa wannan madubin tsafi ya sake nuna hoton wani narkeken ƙato mai riƙe da zabga-zabgan takubba guda biyu masu tsananin kaifi da tsini. Barban ya dube su ya ce.
"Wannan shi ne sadauki Saif. Gawurtaccen jarumi ne. Waɗannan takubba guda biyu da kuka gani a hannunsa tamkar hannayensa haka yake sarrafa su. Indai mutum bai ƙware a iya sarrafa takobi ba, bai isa ya tunkari sadauki Saif da yaƙi ba, domin a cikin daƙiƙa biyar kacal zai iya yin daga-daga da naman mutum."
Madubin tsafin ya sake yin haske ya nuna hoton wani gajeren mutum mai riƙe da dogon mashi. Mashin na da ban al'ajabi, akwai wani ɗan-haske a saman mashin daidai tsininsa.
"Wannan kuma, shi ne sadauki Aiys mai mashin ƙanƙara. Indai ya cakawa mutum wannan mashi dake hannunsa, a take mutum zai daskare ya zamo tamkar gunki. Ba zai sake motsawa ba har abada.
"Wajen yaƙar waɗannan mutane guda uku ana buƙatar sadauki mai tsananin ƙarfin damtse, da mutumin da iya sarrafa takobi har na fitar hankali, sannan da takobi mai sarrafa wuta wacce za'a na amfani da ita wajen narkar da wannan ƙanƙara.
"Ayman kana da tsananin ƙarfin damtse sannan kana da takobin Saiful Shiradu. Idan baka manta ba, na taɓa ce maka ba zamu taɓa samun nasarar sato abu na huɗu ba face mun mallaki wannan takobi. Saboda idan muka yi kuskuren zuwa wannan wuri babu Saiful Shiradu dukkanin mu sai sadauki Aiys ya mayar da mu gumaka.
"Ke kuma Riyalatu a yadda nake samun labarinki, duk faɗin ƙauyen Gazwar babu wanda ya kai ki iya sarrafa takobi. Don ance min hatta sarki Ayubu sai da ya girgiza da yaga yadda kike sarrafa takobi kina kashe masa dakaru, sa'adda ya kawo muku wannan farmaki."
Jaruma Riya da Aymanul Faris suka gyaɗa masa kai alaman haka ne.
Barban ya yi murmushi ya ce, "Saboda haka, jaruma Riya ke za ki gwabza da sadauki Saif mai takubba guda biyu. Kai kuma, Ayman kai zaka tari waɗannan sadaukan guda biyu albarkacin wannan takobi dake hannunka zaka yi nasara akan su.
"Idan babu mai tambaya a cikin ku, sai muyi shirin tafiya." ya tambaye su.
Aymanul Faris yayi caraf ya ce, "Ina da tambaya. Shin sarki Dujalu ba zai san da zuwan mu ba, har ya kawo mana hari?"
Barban yayi murmushi ya ce, "Shiyasa ba zan shiga wannan yaƙi naku ba. Ni ne wanda zai tari sarki Dujalu idan yazo. Sarki Dujalu baya taƙama da komai face ƙarfin sihirin tsafi, ni ne wanda yafi dacewa ya tare shi."
Barban na gama yiwa Aymanul Faris wannan jawabi, ya dafa kafaɗarsa da ta jaruma Riya. Nan take dukkaninsu su uku suka tarwatse suka zamo hoda, a hankali hodar ta ɗinga ɓacewa daga cikin wannan ɗaki har ta gama ɓacewa.
Dama tun kafun wannan tattaunawa, Barban ya gama yin magana da Hajriya akan zasuje wani aiki gobe, kuma su uku ake buƙata.
***
Birnin Hadriyan.
***
Kamar yadda aka riga aka sani wannan daula tana da ƙasashe guda huɗu. Amma, uku daga cikin su ne manƴa - birnin Kufa, birnin Damashkar da birnin Hirtoliya.
Waɗannan birane guda uku muna da bayanan kowanne a cikinsu da sarkin da ya mulkar su. Amma, ba'a taɓa kawo batun birnin Hadriyan ba.
A dukkanin al'amuran waɗannan sarakuna guda uku babu wanda ya taɓa sako sarki Dujalu a cikin sabgogin sa balle a ji bayanan sarkin. Wataƙila hakan ya samo asali ne saboda kowanne daga cikin waɗannan sarakuna ya gama kafuwa da sawayensa baya buƙatar taimakon kowa.
To, idan aka yi duba zuwa ga birnin Hadriyan za'a ga cewa wannan birni ne ƙarami, gaba ɗaya a tsakiyar wani ƙaton daji yake wanda teku ta ɗan ratso ta cikin sa.
Wannan birni shi ne kaɗai a wannan daula wanda ba shi da jahohi ko kuma ƙauyuka. Shi kaɗai yake a haɗe.
Abinda yasa sarki Dujalu baya shiga al'amuran waɗannan sarakuna guda uku shi ne, ko kaɗan ra'ayinsu bai zo ɗaya ba. Sannan shi yafi kowa imani akan tsafe-tsafe da komai. Yana iya shafe kwana da kwanaki a cikin halwar tsafi yana ta bincike.
Sarki Dujalu gajere ne sosai, sannan yana da ƙasumba. Idan mutum ya gan shi a fuska zai ɗauka mutumin kirki ne amma a zuciyarsa ko sarki Kuffuru albarka.
Dujalu ba shi da ɗa ba shi da jika, kai hasalima bai taɓa aure ba. Saboda shi a ganinsa aure da tarawa da mata yana kawowa namijin gaske rauni.
Akwai wata rana da sarki Dujalu yayi bincike akan makomar wannan daula, abinda ya gani a cikin wannan bincike nasa sai da yasa ya fara haɗa zufa a inda yake zaune.
Ba komai ya gani ba face an nuna masa cewa, dukkanin waɗannan manƴan ƙasashe guda huɗu sai sun faɗi ƙasa. Sannan zasu haɗe a waje guda su dawo ƙarƙashin mulkin sarki guda ɗaya.
Abinda ya gagara ganowa shi ne, SHIN ƘARƘASHIN MULKIN WAYE ZASU DAWO? Wannan tambaya ce wacce hatta aljaninsa gagara amsa masa ita yayi.
Tun da Aymanul Faris da Marganu suka bayyana sarki Dujalu bai da aiki kullum face gudanar da bincike akan su da kuma saka musu idanu.
Duk wani motsi na Marganu sarki Dujalu yana kallo, amma sau ɗaya jal, ya taɓa yin arba da Aymanul Faris. Ba'a ko'ina bane sai a lokacin da yake fafatawa da dakarun sarki Ayubu a saman wannan teku.
Sarki Dujalu ba shi da burin da yafi ya mallaki dukkanin ƙasashen dake wannan daula, amma, yasan wannan buri nasa ba zai taɓa cika ba, face ya zamo gawurtaccen matsafin da babu kamarsa duk daular.
Saboda wannan dalili ne yasa kullum a cikin kimtsa kansa yake da ƙarfin sihirin tsafi kala daban-daban.
Bayan wannan sulken yaƙi na sadauki Jarata, sarki Dujalu ya mallaki makaman yaƙi masu yawan gaske.
Sarki Dujalu yana so ya haɗa kai da ɗaya daga cikin waɗannan zaƙwakuran jarumai masu tasowa wanda ga dukkan alamu zasu iya zamowa manƴan gobe a wannan nahiya.
Amma tsahon wata da watanni ya gagara gano da waye ya kamata ya haɗa kai dashi, tsakanin Marganu da Aymanul Faris.
Wani lokacin sai zuciyarsa ta raya Marganu amma kuma sai ya ɗinga ganin aibun Marganu da yawa. Sannan matsalar kuma, babu abinda ya sani akan Aymanul Faris balle yayi tunanin haɗa kai dashi.
***
Ɗan ƙaramin gida ne mai kama da gidan tarihi wanda aka gina a saman wani mitsitsin tsibiri a gaɓar teku, babu kowa a wannan wuri face waɗansu sadaukai guda uku masu tsananin kwarjini da sanƴa firgici a zuciyar mai kallonsu.
Sadauki na farko babu kowanne irin makami a hannunsa, amma, jikinsa a mummurɗe yake ya tara ƙwanji da jijiyoyi kamar me. Hakan ne zai tabbatarwa da mutum cewa, lallai zai kasance mai tsananin ƙarfin damtse har na Allah ya isa
Sadauki na biyu kuma, yana riƙe da zabga-zabgan takubba guda biyu masu tsananin kaifi da tsini. Babu tambaya ka san wannan sadauki ya kasance GOGA a fannin sarrafa waɗannan takubba nasa.
Sadauki na uku ya kasance ɗan gajere mai riƙe da wani dogon mashi mai haske akan tsininsa.
Idan mutum ya ƙarewa waɗannan sadaukai guda uku kallo, ao fuskanci ba wasu bane illa, sadauki Kamaru, sadauki Saif da sadauki Aiys waɗanda Barban ya nunawa su Aymanul Faris a cikin madubin tsafi.
Waɗannan sadaukai guda uku sai kai'-komo suke a wannan wuri, suna kewaye wannan gida. Duk bayan daƙiƙa sai Kamaru motsa jikinsa, Saif ya gyara riƙe takubbansa, Aiys ya sake fiƙe tsinin mashin hannunsa. Saboda shirin ko-ta-kwana.
Dukda cewa tun da suke tsaron wannan gida, ba'a taɓa kawo masa farmaki ba. Amma, kullum a cikin shiri suke.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani! Suka ga mutane guda biyu sun fito daga cikin wannan teku sun tunkaro wannan gida. Wataƙila waɗannan mutane guda biyu ba daga cikin ruwa suka fito ba, domin kuwa, ko ɗigon ruwa babu a jikinsu.
Su biyun sun saka baƙaƙen tufafi masu sheƙi da walwali musamman a cikin hasken rana. Babu abinda mutum zai gani a jikinsu face idanuwansu kaɗai, sun rufe komai da komai nasu.
Idan mutum ya ƙura musu idanu sosai zai fuskanci cewa dole ne su kasance mace da namiji. Saboda ɗaya daga cikin su a mummurɗe yake, alhali, ɗayar kuma a daidai ƙirjinta akwai alamun mama, sannan mazaunata na da tudu.
Sai dai amma, dukkaninsu sunyi shiga ta jaruman ƙwarai. Kowannensu yana rataye da makaman yaƙi. Wannan saurayi yana rataye da zabgegiyar takobi a kafaɗarsa, ita kuma, macen tana rataye da zabga-zabgan takubba guda biyu a gadon bayanta.
Kayan jikin waɗannan mutane guda biyu sun fi kama da irin suturan jikin Aymanul Faris wacce muka gani sa'adda suka je birnin Askandariyya ɗauko lu'u-lu'un sarki Darwazu.
Saboda wannan dalili zamu iya cewa, waɗannan mutane guda biyu ba wasu bane illa AYMANUL FARIS da jaruma RIYA.
Abin tambayar a nan shi ne, ina shugabansu wato Hodon ko kuma Barban.
Su sadauki Kamaru suna ganin su Aymanul Faris suka dubi junansu suka ƙyalƙyale da dariya. Sun kusan shekara uku suna wannan aikin gadi amma ko kadangare basu taɓa kashewa ba, kullum a cikin jiran tsammani suke.
Cikin hanzari sadauki Kamaru ya yayyage rigar jikinsa, murɗaɗɗiyar surarsa ta sadaukai ta bayyana. Tun da su Aymanul Faris suke basu taɓa ganin zabgegen ƙato kamar Kamaru ba.
Saif da Aiys suka zaro makaman yaƙinsu suka ruga da gudu, suka tari su Aymanul Faris suka kewaye su a tsakiya.
Dukda cewa sun kewaye su, amma, basu san wane ne ba. Gaba ɗaya jikin Aymanul Faris da jaruma Riya a rufe yake da waɗannan baƙaƙen tufafi masu sheƙi.
Fuskokin su kuma, irin waɗannan huluna ne masu tsagu a daidai idanu.
Duk wannan abu dake faruwa sarki Dujalu na can zaune a cikin ɗakin tsafinsa yana ganin dukkanin abinda ke faruwa. Dukda cewa akwai sutura mai ɓoye jiki a jikin su Aymanul Faris amma yana ganin fuskokin su, kuma tuni ya riga ya shaida su.
Wannan shi ne dalilin da yasa ya zauna a cikin wannan ɗakin tsafi, yana so yaga yadda wannan gumurzu zai gama kasancewa. Idan Aymanul Faris yayi nasara akan waɗannan dakaru nasa guda uku, to, tabbas zai yanke hukuncin wanda ya kamata ya marawa baya a tsakanin su biyun.
Yana cikin wannan hali ne, wani aljani ya bayyana a gefensa. Aljanin ya kasance zabgegen ƙato mai manya-manyan fuka-fuki. Wannan aljani baiyi kama da komai ba a duniya face hatsabibin boka.
"Wai har yanzu kwakwanto kake akan waye ya kamata, ka yiwa biyayya a cikin manyan gobe na wannan daula?" aljanin ya tambayi sarki Dujalu.
Sarki Dujalu ya dube shi cikin biyayya ya ce, "Kwarai ma kuwa. Har yanzu kwakwanto nake akan su. A ganina Marganu zai fi rinjaye akan wannan yaro mai ƙarfin ruhi. Saboda ta bayyana ƙarara Marganu sadaukin gaske ne mai tsananin ƙarfin damtse irin wanda tunda muke bamu taɓa ganin kamar sa ba, sannan jarumin jarumai ne mai dakakkiyar zuciya wanda baisan tsoro ba. Komai haɗarin wuri Marganu baya tsoron shiga, komai ƙarfin damtsen mutum da jarumtarsa Marganu baya shakkar tunkararsa.
"Babbar matsalar Marganu ita ce, yana fifita soyayya akan komai. Im ba don Marganu ya haukace akan soyayyar gimbiya Jaanu ba, da yanzu yana zaune a birninsu cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. Amma, a yanzu soyayya ta gama lalata masa rayuwa . Marganu yanzu bai ga ta zama ba, face ya gama ɗaukar fansa akan abokan gabarsa.
"Abinda nake tsoro shi ne, kada na haɗa kai da Marganu. Wataran wani abu ya taɓa soyayyarsa ya watsar da ni. Tunda dai ta tabbata babu abinda Marganu ba zai iya yi ba, akan soyayyarsa."
Sarki Dujalu yana zuwa wannan waje a zancensa ya ɗan yi shuru, ya baiwa wannan aljani damar magana.
Aljanin mai suna Amruz ya yi murmushi ya ce, "Duk abinda ka faɗa akan Marganu, haka ne. Tabbas duk wanda ya ɗaura rayuwarsa gaba ɗaya akan soyayya, to, shi kansa baya yarda da kansa. Saboda shi so tamkar guba haka yake. Babban misali a halin yanzu shi ne, soyayyar da Marganu yake yiwa gimbiya Jaanu.
"Zamu iya cewa wannan soyayya ita ce silar tarwatsewar komai na Marganu. Na farko yana matsayin yarima ɗan sarki, amma, ya koma fursuna a gidan yari. Na biyu, tunda Marganu yake ko kwarzane ba'a taɓa yi masa ba, bai taɓa kwana da ƴunwa ba. Amma, sanadiyar soyayyar gimbiya Jaanu sai aka yiwa ƙirjinsa kaca-kaca da raunika, sannan sai da ya kwana uku bai ci komai ba. Na uku, da, Marganu yana da gawurtaccen mahaifi mai son ganin farin cikinsa, amma, a rana guda aka sare kan mahaifin nasa duk a dalilin soyayya.
"Soyayya bata yiwa Marganu komai ba, face haifar masa muguwar hasara da kuma tabo wanda ba zai taɓa gogewa daga cikin zuciyarsa ba.
"Saboda waɗannan dalilai a yanzu, na tabbata Marganu ba zai yarda ya haɗa kai da kowa ba face wanda yayi mugun aminta da shi. Don haka, ta fuskoki da dama haɗa kai da Marganu yana da illoli sosai."
Sarki Dujalu yayi murmushi ya ce, "Wannan haka yake. Shi kuma Aymanul Faris tamkar matsoraci haka nake kallonsa, saboda idan ba matsoraci ba, waye zai tsaya ɓuya. Tunda nake fa sau ɗaya jal, na taɓa kallon gumurzunsa, kuma a gumurzun ma basu ne suka yi nasara ba. Wannan abu shi ne yasa nake ta kwakwanto akan wannan jarumi, anƴa zai iya taɓuka wani abu kuwa?"
Aljani Amruz yayi murmushi ya ce, "Akan Marganu ka kawo hujjoji masu ƙarfi da ma'ana amma akan Aymanul Faris ko hujja guda ɗaya baka kawo ba.
"An faɗa maka faɗa da ɓuya tsoro ne?
"An faɗa maka ƙaramin jarumi ya isa ya shiga husumiyar sarki Darwazu ya fafata da sadaukai jinin Rau'an sannan yayi nasarar sato lu'u-lu'u kuma ya fita lafiya daga cikin birnin lokacin ƙararrawa take kaɗawa?
"Kana tunanin ƙaramin jarumi ya isa yayi ido-da-ido da sarki Fairaz harma yayi masa kashedi?
"Duk tsananin tsaurin ido da rashin tsoro irin na Marganu, da yaje dajin Marsas, babu wanda ya sakawa idanu idan ba Aymanul Faris dukda cewa masoyiyarsa wacce yayi wannan gagarumar tafiya domin ta, tana wurin, kuma dukda cewa sarkin-ɓarayin duniya yana wurin. Kana tunanin a banza Aymanul Faris yayi masa kwarjini?
"Ai a halin yanzu babu abin tsoro da saka firgita kamar tawagar su Aymanul Faris. Saboda babu inda baza su iya shiga ba a duniya?
"Sannan kaje kada ka tsaya ɓata lokacin wajen kallon wannan gumurzu nasu daga nan, zai fi kyau kaje ka hana su ɗaukar wannan sulke.
"Ina ganin kamar ta hakan zaka ƙara fuskantar ƙarfin Aymanul Faris."
Koda sarki Dujalu ya gama jin maganganun hadiminsa akan Aymanul Faris sai jikinsa yayi sanƴi. Tabbas duk abinda wannan aljani ya faɗa gaskiya ne.
Sannan ga dukkan alamu hankalin aljanin yafi kwanciya da Aymanul Faris duba da yadda ya ɗinga yaba shi, sannan ya kushe Marganu.
***
Yau *10/12/2022*
Babi na gaba zai zo *12/12/2022* da yaddar ALLAH.
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 56: *Jarumai Biyu*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
UMAR SANGARU
*
Jaruma Riya ta zaro zabga-zabgan takubbanta guda biyu, ta daka tsalle ta doki ƙirjin sadauki Saif, da shi da itan suka yi sama suka faɗo acan gefe guda. A fusace duk su biyun suka miƙe tsaye suka fara kallon kallo.
Sadauki Kamaru da sadauki Aiys suka saka Aymanul Faris a tsakiya, Kamaru yana jijjiga damatsan jikinsa, shi kuma Aiys yana gyara tsinin mashinsa. Aymanul Faris na ganin haka ya zaro takobin Saiful Shiradu dake ɗaure a kafaɗarsa.
Nan take irin wannan yanayi wanda yake bayyana a duk sa'adda aka zaro wannan takobi ya sake afkuwa a wannan wuri. Baƙaƙen kayan dake jikin Aymanul Faris suka fara haske da sheƙin wuta.
Sadauki Kamaru yayi tsalle ya kawowa Aymanul Faris bangaza da ƙirjinsa tamkar zaki, cikin zafin nama Aymanul Faris ya kauce, Kamaru ya bangaji iska.
Sadauki Aiys ya jehowa Aymanul Faris wannan mashi nasa, a wannan karon ma, Aymanul Faris cikin zafin nama ya kauce.
Waɗannan hari na waɗannan sadaukai guda biyu duk suka sami iska, ba tare da sun sami Aymanul Faris ba.
Lamarin da yasa sadaukan biyu suka fusata kenan, saboda wannan shi ne mahaluƙi na farko da suka

Please Login or Register in order to submit comment