Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saboda tsahon dake tsakanin sama da ƙasa sai da ta shafe daƙiƙa ɗari da arba'in kafun ta caki tsakiyar kan wannan mutum-mutumi, mutum-mutumin yayi tsalle baya sannan ya faɗo tsakiyar wannan fili.
Sarki Wadu da sauran sarakuna guda huɗun nan suka ruga suka ɗauko shi, ai kuwa sai suka ga Marganu ya lashe wannan gasa.
Nan take sarki Wadu ya sanar da jama'a cewa waɗannan baƙin matafiya sun yi nasara, sannan gobe da safe za'a yi sallama dasu a ɗaura su akan hanyar zuwa garin Temisa.
Mutane suka yi farin ciki sannan suka watse. Su Marganu ma suka koma cikin gidansu da nufin washe gari zasu zo ayi sallama da su sarki Wadu.
****
Yau *07/01/2023*
Babi na gabaaizo *09/01/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 69: *Kyakkyawan Fure*
*
DEDICATED TO *PRINCESS ZAHRA*
*
(The man with the ADVENTUROUS MIND)
*
Barban na zuwa nan a labarinsa ya kurɓi shayin dake hannunsa sannan ya dubi su Aymanul Faris ɗaya bayan ɗaya ya ce, "Idan na gama da ayyukan da suke gabana, birnin Ranayes zan koma na ci gaba da gudanar da rayuwata a can."
Sarki Dujalu na jin haka ya risina ya ce, "Ya shugabana, ina neman alfarma a wajenka. Dan Allah ina so ka zauna a cikin birni na domin na samu tubarrakin ka?"
Barban ya yi gajeruwar dariya ya ce, "Ban taɓa zama a cikin birnin wani sarki ba, saboda duk wanda na zauna a cikin birninsa kamar na shafa masa kashin-kaji ne. Masu farautata a duniya suna da tsananin yawan gaske, tabbas idan aka samu labarin na zauna a ƙasarka zaka fuskanci matsala.
"Kada ka damu. Abinda yasa kaga mun karɓi mubaya'arka shi ne saboda naga babu wata manufa a cikin ranka. Tabbas ka kama turba mai kyau, wadda nan gaba zata mulki duniya gaba ɗaya." inji Barban.
Sarki Dujalu na jin wannan batu na Barban ya sake risinawa ya ce, "Ban isa na ja da umarninka ba, sarkin matsafa. Amma alfarmar da nake nema ta biyu ita ce, ina son mu dinga ganawa lokaci-lokaci domin muna tattaunawa."
Barban ya yi guntun murmushi ya ce, "Wannan babu laifi, a duk lokacin da muke son ganinka zamu turo maka da ɗan saƙo, ka ji?"
Sarki Dujalu ya risina ya ce, "Nagode."
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, Barban da sarki Dujalu suka yi sallama da juna. Barban ya dafa jikin Aymanul Faris da jaruma Riya nan take suka zamo farin hayaƙi ya ɓace ɓat.
****
Daga wannan lokaci Aymanul Faris da jaruma Riya basu san abinda ya sake faruwa ba, kawai sai buɗe idanunsu suka yi suka tsinci kansu a tsakiyar wata ƙawatacciyar fada mai kyawun gaske.
Kallon farko Aymanul Faris ya yiwa wannan fada ya shaidata amma ita jaruma Riya bata fahimci komai ba. Wannan fada ba fadar kowa bace face fadar aljani Ranganu ubangidan Barban.
Aljani Ranganu na zaune bisa wannan karaga tasa sanye da baƙaƙen tufafi. Idan mutum ba ƙare masa kallo yayi ba, ba zai gane cewa aljani bane saboda kyawun siffarsa.
Ranganu ya nunawa su Aymanul Faris waɗansu kujeru dake gefe guda ya ce su zauna. Dama tuni Barban kam, na zaune akan ɗaya daga cikin su.
Ba tare da gardamar komai ba, Aymanul Faris da jaruma Riya suka zauna akan waɗannan kujeru suka fuskanci aljani Ranganu wanda ke zaune akan karagar mulkinsa.
Ranganu ya yi gyaran murya ya ce, "Babu buƙatar na gabatar da kaina a gareku, tun da kun riga kun sanni. Ina so nayi amfani da wannan dama a lokacin da kai Aymanul Faris ka mallaki takobin mahaifinka, ita kuma Riya ta mallaki sulken yaƙin mahaifinta domin na sanar da ku shirye-shiryen mu.
"Tun daga yanzu dai, kun fara fuskantar abubuwan da muke ɗaukowa asalin su mallakinmu ne, amma aka yi mana zalunci aka raba mu da su.
"Tabbas a halin yanzu abubuwa sun fara dagulewa, sarki Kuffuru na daf da ɗebo tubalin da zasu gina kurkukun da za'a kulle Barban a ciki.
"Sadauki Marganu na daf da mallakar gawurtacciyar takobi wadda zaiyi amfani da ita wajen yaƙar sarki Kuffuru. Tabbas idan Marganu ya gama da sarki Kuffuru kan mu zai juyo.
"Ba ma shakkar sadauki Marganu amma sanin cewa shi ne ISRABIL dole ne mu tattauna akansa.
"Ayman, a cikin sarakuna guda uku da mahaifinka yayi maka wasiyya da kashe su, an kashe guda ɗaya, saura guda biyu. Sannan na biyun nasu ma ana gagarumin shiri domin hallaka shi amma bai sani ba.
"Ina ganin kamar a halin yanzu ba zamu tattauna akan waɗannan sarakuna guda uku ba. Tunda an kashe ɗaya, sannan ɗaya ana shirin kashe shi, ɗayan kuma anyi jifa dashi uwa-duniya har yanzu babu wanda ya sake jin ɗuriyarsa.
"Abinda zamu tattauna akai, shi ne Marganu ko kuma ISRABIL.
"ISRABIL: Kalma ce da baƙaƙen aljanu suke kiran tauraruwa mai sa'a da ita. Tabbas Marganu ya cika ɗan sa'a wanda sa'a take bibiyarsa.
"A ilimin taurari na baƙaƙen aljanu sun tabbatar da cewa, Marganu sai ya zamo babban sarki a wannan daula.
"Marganu ya yi rantsuwa da ƙololuwar abin rantsuwarsa cewa sai yaga bayan dukkan wanda yake da hannu a kisan mahaifinsa.
"A lissafin abokan gabarsa sarki Kuffuru shi ne na farko, sai sarki Ayubu mahaifin Jaanu da kuma kai Aymanul Faris.
"Kuyi sani cewa Marganu ya fara tunani akan halin da zai shiga idan aka ce, ya hallaka sarki Kuffuru sannan ya haye kan karagar mulkinsa. Ma'ana ya fara tunani akan shirye-shiryen da zai yiwa abokan gabarsa.
"Tauraruwar yarima Marganu tana da ƙarfi sosai, tabbas zai iya ganin bayan sarki Kuffuru. Idan kuwa ya kashe sarki Kuffuru tabbas shi ne zai mulki wannan daula gaba ɗaya.
"Marganu yana tare da mutane masu ƙarfin ƙwaƙwalwa da baiwar tunani musamman ma aljaninsa. Tabbas idan Marganu ya zamo sarki a wancan daula zai addabi duniya."
Aljani Ranganu na zuwa nan a zancensa, Aymanul Faris da jaruma Riya suka fara kallon juna cikin wasu-wasi, kwata-kwata basu fahimci wannan zance nasa ba.
Sau ɗaya suka taɓa yin arba da Marganu kuma ko cacar baki mai kyau basu yi ba. Akan wanne dalili zai saka su a cikin jerin abokan gabarsa?
Ranganu na fuskantar haka ya yi murmushi ya ce, "Abinda nake nufi shi ne, abokan gabarmu suna daf da zamowa gawurtattun mutane a duniya. Mu kuma har yanzu ko ayyuka guda goma na farko bamu kammala ba.
"Tabbas nayi zama na musamman nayi nazari akan waɗannan ayyuka guda goma, na rage wasu daga ciki. Yanzu ayyuka guda shida kacal zamu gudanar sannan Aymanul Faris ya tafi farautar ruhin kakansa.
"Mun riga mun kammala guda huɗu, yanzu guda biyu ne kacal suka rage. A nazari na sauran ko daga baya zamu kammala su.
"Tabbas idan ba kyakkyawan shiri muka fara daga yanzu ba, nan gaba za'a iya samun matsala.
"Ni da Hodon bamu da matsalar komai amma babu waɗanda muke dubawa kamar kai Aymanul Faris da sauran mutanenku.
"Abinda yasa mahaifinka ya sadaukar da rayuwarsa domin sake gina shi kasan ba ƙarami bane. Ina nufin sake kafa daular Shaha.
"Babban dalilin da yasa na rage waɗannan ayyuka da zamu gudanar shi ne, ina so ace a lokacin da sadauki Marganu ya kwace wannan daula ta sarki Kuffuru lokacin nake so ace mun mallaki wancan daula mu ma.
"Saboda ko mun so ko mun ƙi, Marganu nan gaba zai zamo babban maƙiyi a gare mu. Abinda aka yiwa Marganu ba zai taɓa yafewa ba, kuma shi mutum ne mai faɗa da cikawa.
"Ni nasan abinda ku baku sani ba, shiyasa na damu da wannan magana ta Marganu kwarai da gaske." Aljani Ranganu na zuwa nan a zancensa ya fiddo wani littafi ya baiwa Aymanul Faris.
"Wannan littafin bayanai ne akan ruhin da zaka mallaka nan gaba, idan ka samu zama ka duba bayanan ruhin." yace.
Ranganu ya dubi Riya ya ce, "Shin a al'adar ƙabilarku, mata nawa ya dace namiji guda ɗaya ya aura?"
Jaruma Riya ta dubi Ranganu cikin rashin fahimta ta ce, "Ban gane abinda kake nufi ba?"
"Zan fayyace miki komai," inji Ranganu. "Akwai wani babban ruhi wanda aka halicce shi musamman domin magajin Samudul Ansari. Wannan ruhi da magajin ruhin Samudul Ansari kaɗai zaiyi tarayya a duniya.
"Kiyi sani cewa duk wanda ya mallaki ruhin Samudul Ansari idan ba da wannan ruhi yayi tarayya ba, wannan ruhi ba zai na zama a cikin jikinsa ba. Saboda haka, dole ne magajin Samudul Ansari ya nemo wannan ruhi sannan yayi tarayya da shi.
"A binciken da gudanar da kuma yadda tarihi ya tabbatar mana, wannan ruhi wanda ya dace da magajin Samudul Ansari yana cikin birnin Damashkar. A taƙaice dai, gimbiya Jaanu ce.
"Idan har ya zamo dole Aymanul Faris ne, magajin Samudul Ansari to dole yana buƙatar gimbiya Jaanu a matsayin abokiyar rayuwarsa. Idan ba haka kuwa, a banza zai rasa wannan ruhi.
"Kun fi ni sanin tashin hankali da bala'in da jama'arku zasu shiga idan suka sake ɓata tsahon lokaci basu koma asalin yankin su ba." Ranganu ya ƙare yiwa Riya bayani.
"Kana nufin ka ce, dole sai Aymanul Faris ya auri Jaanu?" inji Riya. Daga jin muryarta ka san azababben kishi ne ke tasowa daga cikin zuciyarta.
Bata jira aka bata amsa ba, ta tashi ta fita daga wannan fada ta bar su, su uku a zaune.
Aymanul Faris ya ce, "Kada ku ga laifinta, soyayyata ta shiga ranta matuƙa. Kun san mata da kishi..."
Aljani Ranganu ya dakatar da Aymanul Faris da hannunsa guda ya ce, "Ka bar batun wannan jarumar tunda mun riga da mun isar da mata da saƙo. Yanzu saura a bata umarni ta sanar da mahaifiyarka dukkanin abinda muka sanar da ita. Yana da kyau su san matsayin ARYA daga yanzu, kada daga baya suzo su sani a samu matsala.
"Ayman! Aiki na biyar babu buƙatar mu sanar da Barban ya sanar da kai. Ina so mu tattauna ido-na-ganin-ido.
"To, kamar yadda na sanar da kai a baya, kyawun gimbiya Jaanu rabi ne kawai. Sauran akwai wani hijabi na sihiri da ya lulluɓe shi.
"Kayi sani cewa tun sa'adda kuka yi arba da ita a cikin wannan turaka nata, a karo na farko na haduwarku. Ruhinta ya kamu da tsananin ƙaunarka saboda yaga abinda yasa aka halicce shi domin sa.
"Tun daga wannan lokaci bata da aiki, idan ba tunanin ka ba. Kullum sai ta zubar maka da hawayen tausayi. Jaanu ba zata taɓa samun sukuni a ranta ba, face ka zamo mijinta.
"Kayi sani cewa yadda take tsananin ƙaunarka, baka ƙaunarta haka. Shin ka san dalilin da yasa?"
Cikin tsananin mamaki Aymanul Faris ya girgiza kai, alamun bai sani ba.
Aljani Ranganu ya ci gaba da bayani, "Saboda baka taɓa yin arba da asalin surarta ba, surar da kake gani a yanzu ba ainihin na ta bane. Tun daga lokacin da aka haife ta hadiman sarki Samudul Ansari suka ɓoye ainihin kyawunta saboda kada mutane su ankara da cewa ita ce, magajiyar ARYA.
"Tabbas idan baka yi arba da asalin surar Jaanu ba, ba zaka ƙaunaceta kamar yadda sarki Samudu ya ƙaunaci ARYA ta farko ba. Ta ya ya za'a yi gimbiya Jaanu ta dawo ainihin surarta?
"A kudancin duniya, a wani yanki tsakanin daular Shaha da daular Jerawa akwai wani ɓoyayyen lambu wanda duk duniya babu wanda yasan da zamansa idan ba aljanu masu irin ƙarfin sihirin tsafina ba.
"Wannan lambu mallakin waɗansu irin halittu ne waɗanda suka yi zamani a wannan yanki, lokaci mai tsaho da ya shuɗe.
"A cikin wannan lambu akwai waɗansu irin furanni da waɗannan halittu suka shuka. Su dai waɗannan furanni nasu, suna da tsananin ban al'ajabi.
"Binciken mu na tsafi ya tabbatar mana da cewa, waɗannan furanni nasu suna maganin dukkanin wani sihiri a duniya.
"Idan har muna so mu cire wannan hijabi wanda aka saka a fuskar ARYA, dole sai mun je wannan lambu mun tsinko irin waɗannan furanni nasu munzo mun bata.
"Indai idanunta suka yi arba da waɗannan furanni, tabbas wannan hijabi zai yaye. Daga wannan lokaci ruhinka da nata zasu haɗu a waje guda, babu abinda zai raba ku a duniya face mutuwa.
"Wannan shi ne dalilin da yasa nasa aka kawo ku wannan fada, domin na sanar da Riya wannan babban sirri, sannan kaima na sanar da kai matsayin Jaanu a rayuwarka.
"Kafun mu je wannan lambu, muna buƙatar rantsatstsiyar takobi, da rigar sulke mai ƙwarin gaske sannan da aljanin wuta guda ɗaya wanda zamuyi wannan tafiya tare da shi.
"Bari nayi muku bayani dalla-dalla dangane da amfanin kowanne abu daga cikin abubuwan da na ambata yanzu.
"Kamar yadda na faɗa muku, wannan lambu da zamuje mallakin waɗansu irin halittu ne da basu kasance mutane ko aljanu ba. Bari na muku irin tsarin jikin waɗannan halittu a madubin tsafi domin naji daɗin yi muku bayaninsu."
Aljani Ranganu na zuwa nan a zancensa ya tafa hannayensa sau uku, wani ƙaton allon tsafi ya bayyana a tsakiyarsu. Ya nuna allon tsafin da tafin hannunsa na hagu.
Nan take siffar waɗansu irin halittu guda uku suka bayyana akan allon tsafi. Gaba ɗayan su yan-mata ne kyawawan gaske, abin sai wanda ya gansu.
Abinda ya bambanta su da mutane shi ne, akansu ba gashi bane, macizai ne masu yawan gaske a matsayin gashi. A tsakiyar goshinsu akwai zane-zanen macizai kala-kala.
Waɗannan halittu sun fi kama da bil'adama saboda haka, ba za'a kira su da aljanu ba.
"Idan kun taɓa jin sunan ƙabilar 'GORGON'," inji Ranganu. "To, waɗannan ne. A shekarun baya sun fara addabar duniya da kashe-kashe, sai da sarki Samudul Ansari da manyan sarakuna guda huɗu suka haɗa kai sannan suka kawar dasu.
"Waɗannan guda ukun da kuka gani, su ne suka yi saura daga cikin ƙabilar kuma su ma ɓuya suka yi a wannan ɓoyayyen lambu, ba don haka ba da tuni Samudul Ansari ya kashe su.
"Waɗannan halittu suna da mugun haɗari ga duniya, domin sa'adda suke zalunci ance komai girman alƙarya ɗaya daga cikinsu na iya hallakar da ita.
"Kamar yadda kuka kalli gashin kansu macizai ne maras iyaka, haka ma dafin dake cikin bakunansu basu da iyaka. Babu irin dafin da waɗannan halittu basu da. Komai girman kogi ko kuma teku suna iya saka masa dafi wanda zai hallaka duk wanda yasha ruwan sa.
"Duk abinda waɗannan halittu suka zarewa waɗannan idanu nasu a take zasu mayar da gangar jikinsa gunki, idan zaku ziyarci garuruwa da yawa da waɗannan halittu suka ci a yaƙi a shekarun baya, za ku tarar da gumaka waɗanda har yau ɗinnan suna tsaye a inda suke. Wannan na daga cikin ayyukan wannan ƙabila.
"Amfanin aljanin wuta a wannan aiki da za ku je shi ne, wannan lambu da waɗansu irin itace masu ƙwarin gaske aka gina shi, waɗanda komai ƙarfin ƙarfe bai isa ya huda su ba, sannan komai tashin da aljani zaiyi a sararin samaniya bai isa ya tsallaka su ba.
"A binciken da na gudanar na tsafi na gano cewa, irin wutar da aljani Nara ke sarrafawa zata ƙona waɗannan itace har ku iya shiga inda wannan furanni suke, ku tsinko. Saboda haka tafiya wannan lambu da aljani Nara ta zamo dole.
"Wannan shi ne amfanin da aljanin wuta zaiyi a cikin wannan aiki da zakuje, wato samar da hanya wacce za'a bi a shiga cikin wannan lambu."
Aljanin na zuwa nan a zancensa ya nuna takobin Saiful-Shiradu dake ɗaure a kafaɗar Aymanul Faris ya ce, "Amfanin wannan takobi a cikin wannan aiki shi ne, tana iya samar da mutum-mutumi guda goma hadimanta.
"A duk lokacin da waɗannan halittu suka zare muku idanunsu, Aymanul Faris zai iya waɗannan aljanu nasa su shiga tsakaninku da bala'in dake cikin idanun nasu.
"Kun ga kenan hakan zai sa su yi ta mayar da waɗannan mutum-mutumi gumaka. Wannan zai ba ku damar yaƙar su cikin kwanciyar hankali. Wannan shi ne amfanin wannan takobi a cikin wannan aiki da za ku je.
"Amfanin jaruma Riya kuwa, ita ce kaɗai zata iya tsinkar waɗannan furanni ba tare da sun yayyanka hannayenta ba. Mutanen Gorgon dake rayuwa a cikin wannan lambu sun yiwa waɗannan furanni wani sihiri.
"Duk wanda yayi kuskuren kai hannunsa zai tsinko su, a take zasu juye izuwa wuƙaƙe su yi kaca-kaca da naman hannunsa. Albarkacin wannan sulke da jaruma Riya ta samu, duk wani kaifi ko tsini ba zaiyi tasiri a jikinta ba, komai ƙarfinsa da sihirin dake jikinsa kuwa.
"Wannan shi ne taƙaitaccen bayani akan wannan aiki da zakuje.
"Ayman! Ka je ka rarrashi Riya domin kuwa yanzu tana zaune a ƙofar shiga wannan fada tana ta rusa kuka. Ka bata haƙuri akan abinda muka sanar da ita, tabbas ƙaddara ce ta riga fata. Mu kanmu ba mu so haɗa zuri'a da ɗaya daga cikin su sarki Kuffuru ba, amma babu yadda muka iya tunda an riga an rubuta."
Akwai tambayoyi da yawa da Aymanul Faris yake son yiwa wannan aljani amma tunda ga umarnin da aljanin ya bashi, bai da ikon tsayawa. A hankali ya miƙe tsaye daga kan wannan kujera sannan ya nufi ƙofar fita daga wannan fada.
Kafun ya isa bakin ƙofa ya jiwo muryar Ranganu, "Idan kaje ka sanar da ita dukkan abinda muka tattauna yanzu, wato maganar zuwa lambun Gorgon domin tsinko kyawawan furanni."
Aymanul Faris ya gyaɗa masa kai, sannan ya fice daga cikin wannan fada.
Yana fitowa ya hango jaruma Riya zaune akan wani ɗan tudu ta sunkuyar da kanta, hawaye na ta zubowa daga cikin idanunta daki-daki.
Aymanul Faris na ganin haka, yaji tausayin jaruma Riya ya lulluɓe shi. Saboda tabbas da gaske take matuƙar ƙaunar shi.
Saboda wannan dalili Aymanul Faris ya ƙudurce a ransa, komai wuya, komai rintsi ba zai taɓa watsawa Riya ƙasa a ido ba. Zai ƙaunaceta kamar yadda take ƙaunarsa.
A hankali Aymanul Faris ya ƙarasa inda take zaune, sannan ya ɗaura hannunsa guda ya dafa kafaɗarta. Jaruma Riya ta ɗago kanta, idanuwanta sun yi jajawur saboda wannan kuka da ta daɗe tana yi.
Aymanul Faris na ganin haka tausayinta ya sake kama shi, ya sunkuyar da kansa ƙasa.
Jaruma Riya ta goge hawayen idanunta ta ce, "Abinda wannan aljani ya faɗa gaskiya ne?"
Aymanul Faris ya ɗago kansa, idanuwansa cike da ƙwalla ya ce, "Kiyi haƙuri. Ƙaddara ta riga fata. Babu yadda muka iya da abinda ƙaddara tazo mana da ita."
Jaruma Riya ta gyaɗa kai a hankali, sannan ta rintse idanunta hawaye ya zubo ta ce, "Ka faɗa min gaskiya, shin dama can kana ƙaunar Jaanu a cikin ranka?"
Cikin tsananin tausayawa ya dube ta ya ce, "Kamar yadda kika sanni tun ina yaro ƙarami, bana ƙarya bana taɓa yarda da ƙarya. Kamar haka ne a yanzu, duk abinda zan faɗa miki gaskiya ne.
"Babu dalili guda ɗaya da zai sa na kamu da soyayyar gimbiya Jaanu, saboda na farko ba ƴar ƙabilarmu ba ce, sannan bata kasance jaruma ko basadaukiya ba.
"Bugu da ƙari mahaifinta shi ne wanda ya tarwatsa farin cikin sauran mutanenmu, sannan shi ne mutumin da ya kashe mahaifina.
"Inda ace mun kasance azzalumai da gimbiya Jaanu da dukkanin wani wanda ya haɗa jini da sarki Ayubu kisan gilla mai muni zamuyi masa.
"Maganar gaskiya ita ce, lokacin da muka je yin garkuwa da gimbiya Jaanu. Sa'adda nayi arba da ita sai da naji wani sauyin yanayi a jikina, duk tsahon lokacin nan da muka shafe ina tunanin abin nan.
"Tabbas ban gano mene ne ba, sai a yanzu da su Ranganu suka yi mana bayani. Ni ne jarumin da ruhin Samudul Ansari ya zaɓa a matsayin magajinsa, wannan shi ne dalilin da yasa gimbiya Jaanu ta shiga raina farat ɗaya.
"Babu yadda ban yi ba, wajen ganin na cire sonta daga cikin raina amma na gagara saboda tuni ruhina da nata sun haɗu a waje ɗaya.
"Kiyi haƙuri tunda wannan abu bai saɓawa al'adar ƙabilar mu, wato auren mace sama da guda ɗaya. Amma nayi miki alƙawari kece matata ta farko sannan kece wadda zan fara sani ƴa mace.
"Ina ganin idan nayi miki haka, za ki gane na martaba soyayyarki sannan nafi ƙaunarki akan gimbiya Jaanu." Aymanul Faris na zuwa nan a zancensa jaruma Riya ta rungume shi sannan ta sake fashewa da sabon kuka.
Haka dai Aymanul Faris ya wanzu yana ta kwantarwa jaruma Riya hankali sannan yana lallashinta, abin ka da wadda ta haɗu da abin ƙaunarta nan take ta saki ranta ta ma manta da wannan batu na ɗazu.
Aymanul Faris ya kwashe duk abinda suka tattauna da su Ranganu ya samar da ita, wato batun zuwa wannan lambu.
Ba don komai jaruma Riya ta amince za'a yi wannan tafiya da ita ba, sai domin yadda take tsananin ƙaunar Aymanul Faris, da kuma tsananin tausayin mutanen ƙabilarsu waɗanda mallakar ruhin Samudul Ansari zai dawo musu da martabar da suke da ita a baya a idon duniya.
A daidai wannan lokaci da Aymanul Faris ya gama shawo kan jaruma Riya suna ta shan soyayyarsu, a birnin Darul Barban kuwa, wani Barban ɗin ne zaune tare da mahaifiyar Aymanul Faris yana ta yi mata bayani.
"...sannan idan ba ki manta ba, ita ce ta ceci rayuwarki a hannun mahaifinta a lokacin da suke daf da sare miki kai?" shi ne abinda muka ji wannan Barban ɗin ya faɗa.
Hajriya ta share hawayen idanunta ta ce, "Babu komai tunda abin ya riga ya zamo haka. Idan ma muka ce ba zamu haɗa kai da wannan yarinya ba, gaba dole mu wannan abu zai dama.
"Babu komai na amince. Fansar da zamu ɗauka akan mahaifinta ba akanta ba, lallai wannan yarinya ta kasance mai tsananin adalci..."
Barban bai jira Hajriya ta gama rufe bakinta ba, yana jin cewa 'ta amince' ya dafa kafaɗarta ya ce, "Nagode" Sannan ya ɓace ɓat.
****
Yau *09/01/2023*
Babi na gaba zaizo *12/01/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 70: *Ziyara zuwa birnin Shaha*
*
DEDICATED TO PRINCESS ZAHRA.

*
U*M*S
*
Aymanul Faris da jaruma Riya na rungume da juna cikin tsananin farin ciki, Barban ya fito daga cikin wannan fada yazo inda suke zaune ya dube su ya ce, "Mai girma Ranganu, ya bamu umarnin zuwa birnin Shaha domin ɗauko aljani Nara a yi wannan tafiya da shi. Saboda haka ku zo mu tafi can."
Aymanul Faris na jin umarnin Barban ya janye jikinsa daga na Riya sannan ya kamo hannunta ya jawo ta suka zo gaban Barban suka tsaya. Barban ya karanto ɗalasiman tsafi a ransa sannan ya dafa kafaɗar Aymanul Faris da ta jaruma Riya.
Nan take irin wannan mugun jiri ya sake ɗiban su Aymanul Faris suka zube ƙasa kamar sumammu. Daga wannan lokaci basu san abinda ya sake faruwa ba.
Lokacin da suka buɗe idanunsu sai suka tsinci kansu a ƙofar shiga wani ƙatoton birni wanda tun da suke a rayuwarsu ba su taɓa zuwa birni mai girman shi ba. Ƙofar shiga wannan birni kaɗai abar dubawa ce, domin kuwa mutum ba zai na hango ƙarshenta ba face ya ɗaga kansa can sama.
Gaba ɗaya garin a kewaye yake da wata irin katanga wadda aka gina da wani irin tubali mai ban mamaki, yana da haske kamar na jar zinari amma yana da laushi kamar yashi. Katangar ma kaɗai, tana da tsananin tsaho kamar husumiya. Gaba ɗaya ƙura ta lulluɓeta yadda mutum bai isa ya gane irin tubalin da aka ginata dashi ba.
A bakin ƙofar shiga wannan gari

Please Login or Register in order to submit comment