Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga yanzu, ba zan wuce watanni uku ba. Saboda dafin wannan farce da ya shiga jikina."
Cikin tsananin tausayawa Hubbazu ya ce, "Wanne abu ne ya yi maka wannan rauni?"
Aljani Sheezuwa ya ce, "Naje saman ƙwarin Jekish nayi shawaƙi amma kafun na juyo ne, naga waɗansu irin gabza-gabzan tsuntsaye na tasowa daga cikin ramin masu kama da tsuntsayen teku.
"Na gwabza mummunan yaƙi da waɗannan tsuntsaye daƙyar na tsira da rayuwata na gudu, ɗaya daga cikinsu ne ya soka tsinin farcensa shi ne wanda kuka gani yanzu."
Koda su sarki Kuffuru, sarki Darwazu da sarauniya Rauziyya suka ji wannan batu sai suka cika da tsananin mamaki. Lallai ƙwarin Jekish ya cika mai tsananin masifa da bala'i.
Ace duk girman aljani Sheezuwa da ƙarfin sihirin tsafinsa a samu tsuntsayen da zasu ji masa muggan raunika?
****
*TAURON SI = TAURON SEA*
****
Yau *16/01/2023*
Babi na gaba zaizo *19/01/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 73: *Kwarin Jekish (2)*
*
DEDICATED TO PRINCESS ZAHRA.
*
U*M*S
*
Su sarki Kuffuru suna tsaye cirko-cirko suna tambayar aljani Sheezuwa suka ga yanayin sararin samaniya ya soma sauyawa, tamkar gajimare ne ya fara tasowa yana tare hasken rana.
Cikin tsananin mamaki suka ɗaga kawunansu sama, nan take suka fara hango irin waɗannan jibga-jibgan tsuntsaye masu tsananin yawan gaske suna ta ɓullowa daga wannan yanki na Jekish.
Tsuntsaye ne farare sol, masu dogon baki kamar mashi. Sannan suna da manya-manyan fuka-fuki da farata masu cako-cako waɗanda suke amfani dasu wajen ɗaukar abu suyi sama da shi.
Babban abinda ya ɗagawa su sarki Kuffuru hankali shi ne, yawan waɗannan tsuntsaye ɓullowa kawai suke tamkar ƙudajen zuma.
Cikin gaggawa sarki Kuffuru ya zaro takobinsa ta Siwod-del-bulod, sarauniya Rauziyya ta zaro zabga-zabgan takubbanta guda biyu, sarki Darwazu ma ya zaro takobinsa, boka Hubbazu ya samar da ɗalasimin tsafi akan tafukan hannayensa.
A wannan lokaci waɗannan tsuntsaye sun gama cika wannan waje da suke, sai shawaƙi suke tayi a samansu tamkar shaho yana son ɗaukar ɗan tsako.
Boka Hubbazu ya dubi aljani Sheezuwa ya ce, "Ya kai Zuwa, na umarceka da ɗaukar mu gaba ɗaya, ka tashi da mu sama sannan ka tunkari waɗannan tsuntsaye. Tabbas idan muka ce zamu yaƙe su daga ƙasa ba zamuyi nasara ba.
"Saboda a kowanne zasu iya ɗaukar mu da waɗannan farata nasu." Aljani Sheezuwa ya gyaɗa kai cikin cika umarni.
Ya ranƙwafa ƙasa, sarki Kuffuru, sarauniya Rauziyya, sarki Darwazu da boka Hubbazu suka haye gadon bayansa. Shi kuma ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama suka tunkari waɗannan tsuntsaye aka ruguntsume da azababben yaƙi.
Waɗannan tsuntsaye suka kewaye su a sararin samaniya suka yi ta kawo musu muggan hare-hare da bakunan su. Sannan suna fasa wani irin ihu mai tsananin razanarwa.
Sarki Kuffuru da sauran abokan tafiyarsa suka wanzu suna masu kare kansu daga hare-haren waɗannan tsuntsaye, a duk lokacin da takubbansu suka haɗu da bakunan waɗannan tsuntsaye sai kaga tartsatsin wuta mai yawa ya zubo ƙasa tamkar ƙarfe da ƙarfe ya haɗu.
Sannan koda sun sami damar saran jikin waɗannan tsuntsaye, takubban basa yi musu raunin komai tamkar dutse suka sara.
Ko sau ɗaya su sarki Kuffuru basu yi kuskuren bari bakunan waɗannan tsuntsaye ya taɓa jikinsu ba, aka ci gaba da wannan gumurzu har kusan rabin sa'a.
Sarki Kuffuru yana amfani da wannan takobi tasa ta Siwod-del-bulod wajen yaƙar waɗannan tsuntsaye, dukda cewa takobin bata yi musu mummunan illa amma a duk lokacin da ya sari jikinsu sai sun kwaɗa uban ihu sannan su ja baya daga gare shi, ga dukkan alamu wannan takobi tana yi musu rauni ta ciki.
Sarauniya Rauziyya tana amfani da rantsatstsun takubba guda biyu, a duk lokacin da ta sari jikin tsuntsayen sai kaga wurin ya taso, alamar takobin tana musu illa amma akwai wani sirri na musamman wanda yake hana takobin huda jikinsu.
Takobin sarki Darwazu da tsafin boka Hubbazu kwata-kwata basa tasiri a jikin waɗannan tsuntsaye.
Har tsahon rabin sa'a ana ta abu ɗaya tsakanin su sarki Kuffuru da waɗannan tsuntsaye, ko tsuntsu guda ɗaya su sarki Kuffuru basu kashe ba, sannan su kuma waɗannan tsuntsaye basu sami nasarar yiwa ɗayansu rauni ba.
Koda waɗannan tsuntsaye suka fuskanci cewa, basu sami nasara akan su sarki Kuffuru ba sai suka fara kaiwa abin hawansu hari wato aljani Sheezuwa.
Nan take suka raba kansu gida biyu, rabi suna kaiwa aljani Sheezuwa hari, rabi kuma suna kaiwa su sarki Kuffuru hari.
Ai kuwa nan take suka rikita su sarki Kuffuru, saboda gaba ɗaya ƙarfinsu da taƙamarsu yana kan aljani Sheezuwa wanda yake yawo dasu a sararin samaniya a tsakiyar tsuntsayen.
Cikin gaggawa sarki Kuffuru ya kirawo hadiman aljanunsa dake cikin takobinsa ta Siwod-del-bulod, take aljanu guda goma suka bayyana.
Sarki Kuffuru ya basu umarnin afkawa waɗannan tsuntsaye. Aljanun suka zaro takubansu suka afkawa aljanun, amma ba'a ɗauki lokaci ba aka gama dasu. Saboda basa taƙama da komai face ƙarfin sihirin tsafi, su kuma waɗannan tsuntsaye tsafi baya tasiri a kansu.
Kafun a jima wannan gumurzu tuni aka fara cin ƙarfin su sarki Kuffuru saboda waɗannan tsuntsaye sun fisu yawa nesa ba kusa ba, sannan sun fara illata aljani Sheezuwa domin a wannan lokaci sun caka masa farce ya kai sau ashirin.
Jini mai yawa nata ƙwaranyowa daga jikinsa, jiri ya fara ɗibarsa. Boka Hubbazu na fuskantar haka ya bashi umarnin sauƙowa ƙasa saboda idan yaci gaba da gumurzu a sama zai iya hallaka.
Aljani Sheezuwa na dira ƙasa su sarki Kuffuru suka yi tsalle suka sauƙa a kansa, a wannan lokaci waɗannan tsuntsaye sun fara yiwo ƙasa domin yi musu barar shaho.
Sarki Kuffuru ya mayar da takobinsa cikin kufe, sannan ya ɗauki wani ƙaton gungumen itace dake tsakiyar wannan sahara.
Wani ƙatoton tsuntsu na zuwa daidai saman kansa, sarki Kuffuru yayi tsalle ya doki tsakiyar kansa da wannan itace nasa.
Take kan wannan tsuntsu ya yi wata ƙara sannan ya dagargaje jini ya yi fallatsi. Tsuntsun ya faɗi ƙasa matacce.
Sarki Kuffuru na ganin haka ya yiwa su sarki Darwazu busharar lagon waɗannan tsuntsaye.
Babbar matsalar da suka fuskanta ita ce babu irin wannan itace na hannun sarki Kuffuru a cikin wannan daji, sannan koda za'a sami kalar wannan itace da wuya idan zasu iya ɗaga shi saboda basu da ƙarfin damtse irin na sarki Kuffuru.
Sarki Kuffuru ya ci gaba da ragargazar waɗannan tsuntsaye yana dukan tsakiyar kansu, ƙwanya na fantsama, suna ta zamowa gawarwaki.
A ɓangaren su sarki Darwazu kuma, gumurzun babu daɗi saboda yadda waɗannan tsuntsaye suke yawan kai musu bara suna so dauke su, su tashi sama da su.
Sarauniya Rauziyya ce take taɓuka wani abu, domin da zarar ta sari sawayen tsuntsayen sai kaji sun fasa ihu sannan su tashi sama.
Haka dai aka ci gaba da wannan gumurzu, sarki Kuffuru na ta ragargazar waɗannan tsuntsaye, su kuma su sarki Darwazu suna kuɓuta daƙyar daga hare-haren tsuntsayen.
Koda aka shafe sa'a ɗaya ana wannan gumurzu, sai sarauniya Rauziyya da sarki Darwazu suka soma gajiya. Dama boka Hubbazu na laɓe a bayan sarki Kuffuru, saboda ɓarnar da saki Kuffuru ke yiwa waɗannan tsuntsaye basa kawowa Hubbazu hari sosai.
Ana cikin wannan gumurzu wani ƙaton tsuntsu yasa fuka-fukinsa ya mari fuskar sarauniya Rauziyya, take ta gigice ta faɗi ƙasa. Tsuntsun ya buɗe ƙattin sawayensa zai ɗauketa, sarki Darwazu yayi maza yayi tsalle ya shiga tsakani.
Jibgegen tsuntsun ya ɗauki sarki Darwazu a sawayensa tamkar ya ɗauki ɗan tsako, ya tashi ya lulluƙa cikin gajimare, ya ɓace.
Sarki Kuffuru na ganin haka ransa yayi mummunan ɓaci ya ci gaba da dukan kawunan waɗannan tsuntsaye suna mutuwa.
Yana ganin sarauniya Rauziyya ta farfaɗo yasa ƙafarsa ya karya wannan itace, sannan ya cilla mata rabi.
Cikin gaggawa ta ɗauki itacen sannan itama ta fara dukan waɗannan tsuntsaye. Ita da sarki Kuffuru suka ci gaba da ragargazar waɗannan tsuntsaye babu ƙaƙƙautawa.
Sarauniya Rauziyya tana wannan yaƙi sannan tana mamakin yadda aka yi sarki Darwazu ya sadaukar da rayuwarsa domin ya ceci nata.
Wannan ya ƙara mata ƙwarin gwiwa ƙwarai da gaske, ta ci gaba da ragargazar tsuntsayen domin ta samu damar zuwa inda aka kai sarki Darwazu ta cece shi.
Sarki Kuffuru da sarauniya Rauziyya sun mayar da ƙaimi sosai wajen karkashe waɗannan tsuntsaye, wani jibgegen tsuntsu ya taho ta bayansu inda boka Hubbazu ke tsaye.
Yana zuwa ya cakawa boka Hubbazu dogon bakinsa mai kama da algaita, nan take wani wawakeken rami zururu ya bayyana a ƙirjin boka Hubbazu.
Bai san sa'adda ya ƙwarara uban ihu ba, cikin gaggawa sarki Kuffuru ya juya inda Hubbazu yake, koda yaga halin da yake ciki sai ransa ya ɓaci ya tarwatsa tsuntsayen dake wajen sannan yasa hannunsa ya goya Hubbazu a gadon bayansa.
Shi da Rauziyya suka ci gaba da ragargazar waɗannan tsuntsaye babu ƙaƙƙautawa, koda tsuntsayen suka fuskanci cewa, idan suka tsaya aka ci gaba da wannan gumurzu ɗayansu ba zai tsira da rayuwarsa ba, sai suka fara buɗe fuka-fukinsu suna lulluƙawa cikin gajmare suna ɓacewa ɓat.
Kafun shuɗewar rabin sa'a duk sun gama tarwatsewa daga wannan waje, suka ƙyale iya gawarwakin ƴan uwansu da suka mutu.
Sarki Kuffuru da sarauniya Rauziyya suka zube ƙasa suna ta haki, sakamakon mugun wahalar da suka sha.
Sai da suka shafe wata rabin sa'ar suna hutawa, sannan sarauniya Rauziyya ta miƙe ta nufi inda aljani Sheezuwa ke kwance a tsakiyar gawarwakin waɗannan tsuntsayen.
Sarki Kuffuru yasha gabanta ya ce, "Haba uwar matsafa! Ina kuma za kije alhalin yanzu muka gama fafatawa da waɗannan muggan tsuntsayen?"
Sarauniya Rauziyya ta ce, "Zan je na ceci rayuwar wanda ya ceci tawa, hankalina ba zai taɓa kwanciya ba face naga na kuɓutar da sarki Darwazu daga sharrin wannan tsuntsu wanda ya tafi da shi."
Sarki Kuffuru na jin haka gabansa ya sara da ƙarfi, ko ba komai sarki Darwazu yana daga cikin sadaukai-uku ƴan baiwa, waɗanda zasu haɗa ƙarfi-da-ƙarfe su kamo Hodon.
Cikin gaggawa ya kwance boka Hubbazu dake ɗaure a gadon bayansa, ya kwantar dashi ƙasa. Aljani Sheezuwa na ganin uban gidansa cikin mawuyacin hali, ya taso da sauri yazo ya saka masa irin wannan ruwan magani.
Nan take raunin ƙirjin boka Hubbazu ya haɗe, ya dubi su sarki Kuffuru ya ce, "Muyi gaggawar zuwa kwarin Jekish domin idan bamu je da wuri ba, sarki Darwazu zai iya mutuwa saboda wannan tsuntsuwa zata iya baiwa ƴaƴanta shi su cinye."
Aljani Sheezuwa ya ranƙwafa su kuma suka yi gaggawar hawa gadon bayansa, ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama cikin iska sannan ya fara tsala azababben gudu ya nufi inda wannan tsuntsu ya nufa ɗazu.
Aljani Sheezuwa baiyi wata doguwar tafiya ba, ya iso saman wani ƙatoton rami wanda daga samansa mutum bai isa ya hango ƙarshensa ba saboda tsananin zurfi.
Lallai idan ba da halitta mai fuka-fuki ba, babu wanda ya isa ya iya shiga cikin wannan kwari ko shi waye kuwa.
Ba tare da tsoro ko shakkun komai ba, Sheezuwa ya saki fuka-fukinsa ƙasa ya yi ta faɗawa cikin wannan ƙaton kwari.
Iya rayuwar sarki Kuffuru da boka Hubbazu basu taɓa shiga waje mai zurfin wannan kwari ba, domin sai da suka yi sa'a biyu cur suna faɗawa cikin ramin sannan suka dira a ƙasa.
Ƙasar dake cikin wannan rami jajawur ce, sannan ta baibaye komai da komai dake cikin wannan rami.
Sarki Kuffuru, sarauniya Rauziyya da boka Hubbazu suka saƙƙo daga kan aljani Sheezuwa, suka zaro makaman yaƙin su sannan suka fara yawo a cikin wannan ƙwari suna neman sarki Darwazu.
Shi kuma aljani Sheezuwa sai ya buɗe wani ƙaton aljihu a tsakiyar rigarsa, ya fara ɗibar wannan tubali yana sakawa a cikin wannan aljihu nasa.
Su sarki Kuffuru basu yi nisa a cikin ƙaton rami suna nema ba, suka hango wannan tsuntsu kwance a cikin shaɓɓonta tare da kwayayenta, ga sarki Darwazu kwance a gaban wasu ƴaƴanta guda biyu, sai caccakar gadon bayansa suke, jini yana ta zubowa.
Sarki Kuffuru ya dubi su sarauniya Rauziyya yayi musu wata inkiya da idanu. Suna ganin haka suka ja gefe guda suka rakaɓe.
Sarki Kuffuru ya gyara riƙe wannan zabgegen itace dake hannunsa da kyau, sannan ya fara lallaɓawa ta bayan wannan tsuntsuwa yana tafiya a hankali, ba tare da ya bari ta ji motsinsa ba.
Sai da yazo daf da ita sannan ya daka tsalle sama ya rotsa mata wannan itace dake hannunsa, take kan tsuntsuwar ya fashe jini yayi feshi.
Ƴaƴanta na ganin haka suka fara kuka, sarki Kuffuru ya zaro takobinsa duk ya fille musu kai, sannan ya farfasa ƙwayayenta ya ɗauki sarki Darwazu ya koma inda su sarauniya Rauziyya ke tsaye.
A wannan lokaci tuni aljani Sheezuwa ya gama cika aljihunsa da tubalin wannan kwari, don haka sarki Kuffuru yana zuwa ranƙwafawa kawai yayi. Dukkansu suka haye gadon bayansa.
Aljanin ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi dasu sama ya fara tsala azababben gudu, suka nufi saman wannan ƙaton rami.
Ba su yi nisa da fara yin saman ba, suka fara cin karo da irin waɗannan tsuntsaye suna dawowa cikin wannan rami.
Nan fa suka sake kacamewa da sabon gumurzu a sama, domin kuwa tsuntsayen na ƙoƙarin kawar dasu sarki Kuffuru su kuma suna ƙoƙarin ƙwace kansu don kada a jeho su ƙasan wannan kwari.
Sarki Kuffuru da sarauniya Rauziyya suka riƙe waɗannan gabza-gabzan sandunan, sannan muka miƙe tsaye suka fara buge waɗannan tsuntsaye.
Nan fa gawarwakin tsuntsayen suka fara rikitowa cikin wannan rami, aljani Sheezuwa ya samu dama yayi ta tashi sama.
Sarki Kuffuru da sarauniya Rauziyya suka ci gaba da doke waɗannan tsuntsaye suna faɗowa ƙarƙashin wannan rami matattu.
Amma dukda haka sai da waɗannan tsuntsaye suka sake cakawa aljani Sheezuwa irin wannan farce nasu a gadon bayansa, amma dukda ya dake ya ci gaba da tashi har ya fice daga cikin wannan kwari.
Suna dira a gaɓar wannan kwari, waɗannan tsuntsaye suka daina bin su. Boka Hubbazu yayi gaggawar sakawa aljani Sheezuwa wannan magani nasu, a take raunin ya haɗe.
Ba tare da ɓata lokacin komai ba, boka Hubbazu ya baiwa aljani Sheezuwa umarnin ɗaukar su gaba ɗaya ya kaisu muhallin da za'a gina wannan gawurtacciyar kurkuku wacce zasu tsare Barban a cikinta.
Aljani Sheezuwa ya sake ranƙwafawa sarki Kuffuru ya goya Darwazu ya haye kan aljanin, Hubbazu ya take masa baya amma sai Rauziyya ta ƙi ta hau kan aljanin.
Lamarin da yayi matuƙar ɗugunzumawa sarki Kuffuru da boka Hubbazu hankali kenan, sarki Kuffuru ya dubeta ya ce, "Uwar matsafa! Lafiya kika tsaya a wannan wuri muna faman tafiya?"
A hasale sarauniya Rauziyya ta dube shi ta ce, "Kun ce kafun mu ɗebo wannan tubali za'a kawo min Marganu, amma shuru kake ji kamar maye ya ci shirwa?"
Boka Hubbazu ya sauƙo daga kan aljani Sheezuwa yazo daf da ita ya tsaya sannan ya ɗaura hannunsa guda kan kafaɗarta ya ce, "Uwar matsafa! Marganu ya shiga hannuna, nan bada daɗewa ba, za'a kawo min gawarsa har wannan wuri."
Sarauniya Rauziyya ta ture hannun boka Hubbazu daga kan kafaɗarta cikin sauri da hasala ta ce, "Me kace? Kana nufin kun kashe Marganu, idan har kun kashe shi jininsa ba zai yiwa abin bautana daɗi ba, saboda ba zai sha ba. Idan kuwa bai sha jinin Marganu ba, to na saɓa umarninsa.
"Ka faɗa min gaskiya idan har kun kashe Marganu zan yanke alaƙa ta daku daga yanzu, saboda ba zata yi min amfanin komai ba!!!"
Boka Hubbazu na jin haka yayi murmushi ya duba madubin tsafinsa ya ce, "Tsaya hakanan, kada ka sare kan shi." Kamar yana baiwa wani umarni a cikin wannan madubin tsafi.
Yana gama hakan ya dubeta ya ce, "Mun yi sa'a wannan hadimi nawa, bai ƙarasa kashe shi ba, amma yana daf da sare masa kai na bashi umarni ya dakata. Tabbas ina sa ran nan da mako guda wannan hadimi nawa zai iso."
Cikin kallon rashin yarda Rauziyya ta dubi Hubbazu ta ce, "Tayaya zan yarda da abinda kake cewa?"
Hubbazu na jin haka ya haɗe fuska ya ce, "Haba uwar matsafa! Kada ki watsa mana ƙasa a ido mana. Ki duba halin wanda ya ceci rayuwarki yake mana, shin ko domin shi ba zakiyi wannan tafiya ba?"
Koda sarauniya Rauziyya taji abinda boka Hubbazu ya ce, sai jikinta yayi sanyi. Ta yi gajeren tunani sannan ta wuce izuwa inda aljani Sheezuwa yake ta haye gadon bayansa ta zauna a gefen sarki Kuffuru.
Cikin gaggawa ta karɓi sarki Darwazu daga hannun sarki Kuffuru ta fara dudduba raunikan jikinsa tana saka masa magani. Boka Hubbazu ya dawo ya zauna.
Aljani Sheezuwa ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama, ya bar nahiyar kwarin Jekish gaba ɗaya.
*****
Yau *19/01/2023*
Babi na gaba zaizo *21/01/2023* da yaddar Allah.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 74: *Takobin Tarwatsa-Komai*
*
DEDICATED TO WELL-KNOWN ZAHRA.
*
NATURE LOVER
*
~Marganu
*
Tun da asuba aka fara jiwo ihu da gurnani mai kama da na baƙaƙen dabbobin daji na tunkaro wannan gari, sannan wasu irin takun sawaye masu yawan gaske na tunkaro garin..
A firgice Marganu, Aydenlik da Firziyya suka farka daga barci, sannan suka ɗauki makaman yaƙinsu ba tare da sun cewa juna uffan ba, suka rugo fadar sarki Wadu domin sanin abinda ke faruwa.
Suna zuwa fadar suka iske ta cike maƙil da mayaƙa sun sha ɗamara, kowa rataye da zabgegiyar takobi. Sarki Wadu da waɗannan sarakuna guda huɗu na tsaitsaye a gabansu, sun yi jugum-jugum.
Marganu, Firziyya da Aydenlik suna zuwa suka wuce kai tsaye gaban waɗannan sarakuna, Marganu ya dubi sarki Wadu ya ce, "Mene ne abinda yake faruwa, hayaniyar me muke ji a bayan gari?"
Kafun sarki Wadu ya buɗi bakinsa ya baiwa Marganu amsa, sai suka ga wani mahayi ya dawo a guje akan doki.
Cikin gaggawa waɗannan sarakuna guda huɗu suka ruga inda yake, sarki Wadu ya tambaye shi mene ne? Mahayin ya ce, "Ni dai ina kwance saman doguwar bishiyar dake bayan gari, na hango waɗansu halittu masu yawan gaske sun tunkaro wannan gari namu. Halittun sun fi kama da irin waɗannan mutane da suka ƙwace mana garin mu na Temisa a shekarun baya."
Sarki Wadu na jin haka, jikinsa ya fara tsuma saboda tsananin fusata ya juya ya dubi waɗannan sarakuna guda huɗu ya ce, "Ga dukkan alamu waɗannan halittu ne suka gaji da zama a cikin birnin Temisa, suka taso da burin shafe namu biranen. Sannan ina kyautata zaton cewa tuni sun gama cinƴe birnanen ku da yaƙi tunda har suka tunkaro nawa."
Waɗannan sarakuna suna jin abinda sarki Wadu ya faɗa, jikinsu ya fara tsuma su ma saboda tsananin fusata.
A wannan yanki nasu mutum zai iya cewa basu da abokan gaba da suka wuce waɗannan halittu, a karon farko sun tashe su daga cikin asalin birninsu na haihuwa sun koro su ƙauyuka, sannan ace abin bai tsaya iya nan ba har cikin ƙauyukan ma sai an biyo su.
Sarki Wadu ya samar da gagarumar runduna ta sadaukai masu tsananin yawan gaske, dama a duk cikin waɗannan sarakuna guda huɗu babu wanda ya kaishi jin haushin wannan abu da aka yi musu.
Idan ba'a manta ba sarki Wadu shi ne wanda ya nemo sauran ƴan uwansu a uwa duniya, ya basu shawarar dawowa wannan wuri domin su ci gaba da rayuwa.
Saboda wannan dalili za'a iya cewa sarki Wadu yafi dukkanin waɗannan sarakuna guda uku ƙarfin shiri, domin shi kullum a cikin tunanin yadda zai ƙwato birninsu yake.
Sarkin ya dubi mayaƙansa ya ce, "Kuzo mu yi gaggawar zuwa mu tari abokan gaba, domin suna daf da ƙarasowa wannan birni, idan kuwa suka ƙaraso abin ba zai yi mana daɗi ba."
Ko kallon su Marganu bai yi ba, balle ya ce da su wani abu. Kana gani kamar babu ruwansa da su Marganu tunda suka ci waɗannan gasanni guda huɗu.
Sarki Wadu da waɗannan sarakuna guda huɗu suka jagoranci rundunar tarin mayaƙa suka fice daga cikin wannan gari, suka nausa cikin daji mai yawan sahara.
Gimbiya Firziyya ta dubi Marganu ta ce, "Masoyina! Mene ne abin yi a gare mu? Shin zamu taimakawa waɗannan sarakuna ne, ko kuma zamu kama gaban mu?"
Marganu na jin haka ya haɗe fuska ya ce, "Tun da sun nuna basa buƙatar mu, babu ruwan mu da su a yayin wannan gumurzu, abinda zamu mayar da hankali akansa kawai shi ne nemawa kanmu hanya wacce zamu bi mu ƙarasa cikin garin Temisa."
Marganu yana gama faɗin haka ya wuce ya nufi wannan hanya wadda su sarki Wadu suka bi, Firziyya da Aydenlik suka take masa baya.
Sai da suka yi doguwar tafiya a cikin wannan daji mai yawan sahara sannan suka soma hango ƙura na tasowa acan nesa, sannan jini da ƙasa nata gwaurayuwa a waje guda. Ihu da karafkiyar ƙarafa nata tashi.
Koda su Marganu suka ƙara tafiya kaɗan, sai suka hango gumurzu mai zafi na wakana tsakanin su sarki Wadu da waɗannan halittu.
Halittun gabza-gabza ne suna da tsaho da kauri, sannan jikkunansu a mummurɗe suke. Suna riƙe da mahaukatan makaman yaƙi irin waɗanda su Marganu suka daɗe basu gani ba.
Duk inda waɗannan halittu suka saka a gaba, sai dai kaga gawarwakin dakarun sarki Wadu na ta yawo a cikin iska, jininsu yana ta feshi.
Ba su da imani ko kaɗan, in banda ɗaukar rayukar jama'ar sarki Wadu babu abinda suke.
Idan kaga yadda ake wannan gumurzu zaka iya cewa, waɗannan halittu kawai cin zalin dakarun sarki Wadu suke saboda babu abinda za'a kwatanta wannan gumurzu nasu face hakan.
Gawarwakin dakarun sarki Wadu sun cika wannan waje, jininsu kuma tuni ya rina ƙasar wurin.
Marganu, Firziyya da Aydenlik na ƙarasowa wannan wuri suka zaro makaman yaƙinsu suka afkawa waɗannan halittu da mummunan kisa.
Duk inda Marganu ya saka a gaba sai dai kaga kawunan waɗannan halittu na tashi sama, yana barin gangunan jikinsu. Jini kuma yana tsartuwa.
Haka ɓangaren Firziyya ma, shiga kawai take tsakiyar waɗannan halittu tana ta karkashe su da waɗannan zabga-zabgan takubba nata.
Aydenlik kuma, duk inda yayi jifa da wannan dutsen-tsafi nasa, sai dai kaga tarin waɗannan halittu sunyi sama sun faɗo ƙasa.
Shigowar su Marganu wannan yaƙi yayi matuƙar sauyawa yaƙi akala, lamarin da yasa farin ciki ya fara baibaye su sarki Wadu kenan.
Amma abinda basu sani ba shine su Marganu nemawa kansu hanya kawai suke, ba wai taimaka musu ba.
Koda waɗannan halittu suka fuskanci cewa, idan suka ci gaba da tunkarar su yarima Marganu lallai mutuwa zasu yi gaba ɗayansu, sai suka fara guduwa daga ɓangaren su Marganu suna komawa inda su sarki Wadu suke.
Marganu na ganin haka ya baiwa su Firziyya umarnin kutsawa ta cikin waɗannan halittu da ƙarfin tsiya domin su wuce izuwa garin Temisa.
Da yake hankalin waɗannan halittu ba'a kansu yake ba, saboda sun tsorata da ɓarnar da suka yi musu, sai suka yi ta kutsawa suna wucewa gaba ta cikin halittun.
Aka ci gaba da gumurzu tsakanin halittun da su sarki Wadu, jini ya ci gaba da ƙwaranya.
Kafun a jima tuni Marganu, Firziyya da Aydenlik sun fice daga cikin rundunar waɗannan halittu gaba ɗaya, suka ratsa ta cikin garuruwa uku na waɗannan sarakuna suka wuce sannan suka tasarwa birnin Temisa wanda tsakanin su da shi tafiya ce mai tsaho.
Akan hanyar zuwa wannan gari suka yi ta karo da irin rundunonin waɗannan halittu amma cikin sauƙi Marganu yake gamawa da su.
Kafun su isa garin sai da suka fafata da rundunoni wajen guda goma, sannan suka soma hango ƙofar garin.
Irin waɗannan halittu suka gani tsaitsaye a bakin ƙofar shiga, sun yi shiga a wani salo na

Please Login or Register in order to submit comment