Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin kufenta, bata wuce rabin sa'a bata sha jini ba.
Samudul Ansari na ganin wannan sarki ba zai taɓuka wani abu ba, ya goce cikin zafin nama sannan ya fille kan sarkin.
Gocewar Samudul Ansari da fille kan wannan sarki ya ɗauki lokaci wajen bayani amma kwata-kwata abin bai wuce daƙiƙa sha biyar ba saboda tsananin zafin naman Samudul Ansari.
Gauhan, sarki Mahrus, su Zarifa dake can gefe da kuma sarauniya Arya wadda ke tsaye a saman wannan ganuwa sai da suka cika da tsananin mamaki.
Sarki Mahrus ya dubi Gauhan Ansari ya ce, "Baka da hankali ne, zaka ce mu yaƙi wannan mutumi da ɗaiɗaya? Tabbas idan ba haɗa kai muka yi ba, muma sai yayi mana abinda ya yiwa sarki Jadalu Gorgon..."
Gauhan ya gyaɗa kai alamun amincewa.
Gauhan da sarki Mahrus suka daka tsalle sama suka dira a gefen Samudul Ansari suka saka shi a tsakiya.
Sarki Mahrus ya zaro wani gajeren mashi mai siffar maciji, shi kuma Gauhan ya zaro wata lafceciyar adda.
Ba tare da kace-nace ba, suka afkawa Samudul Ansari da azababben yaƙi.
Gauhan yana kai masa sara da wannan adda, shi kuwa sarki Mahrus yana kai masa suka da wannan mashi dake hannunsa.
Samudul Ansari ya sake a tsayawa a tsakiyarsu yayi ta kare waɗannan hare-hare nasu, ba tare da ya mayar da martani koda sau ɗaya ba.
Gauhan da sarki Mahrus suka cika da tsananin mamaki.
Idan shi sarki Mahrus baisan wane ne Samudul Ansari ba, shi Gauhan ya san shi sama da ƙasa.
Ko a mafarki bai taɓa tsammanin Samudul Ansari yana da horo irin wannan ba.
Abinda bai sani ba shi ne Samudul Ansari da ya sani na da ne, wanda bai mallaki ɓarin-ruhinsa ba.
A yanzu Samudul Ansari ya mallaki ɓarin-ruhinsa wanda ya gama nuna ainihin asalinsa.
Samudul Ansari ya fusata ya shaƙo wuyan sarki Mahrus da ƙarfi, Gauhan ya kawo masa sara, Samudul Ansari yasa ƙotar takobinsa ya doki ƙirjin Gauhan.
Nan take Gauhan yayi sama sannan ya faɗo acan baya.
Samudul Ansari yasa dukkanin ƙarfin damtsensa ya murɗewa sarki Mahrus wuya.
Samudul Ansari yasa wannan takobi ya yanke wuyan sarki Mahrus Gorgon sannan yaje inda kan sarki Jadalu Gorgon ya ɗauko shi, ya haɗa su a waje guda.
Ya cillawa su Gauhan Ansari wanda ke durƙushe acan gefe ya ce, "Ka ɗauki kan waɗannan shashashun ka kaiwa sarauniya Yilan, kace yaro yayi kaɗan sai dai babansa."
Samudul Ansari na gama faɗin haka ya juya zai tafi.
Cikin tsananin fusata Gauhan Ansari ya ɗaga hannunsa sama, takobin da take cikin tauraro ta fito sannan ta dira akan hannunsa.
Gauhan ya kaiwa Samudul Ansari sara da ita.
Wasu jajayen taurari guda biyu suka fice daga tsinin takobin, suka tafi da gudu cikin iska suka doki gadon bayan Samudul Ansari.
Samudul Ansari yayi tsalle sannan ya faɗo a can nesa.
Koda yaga cewa, Gauhan ya karya ƙa'idar da suka ɗaura, sai shima ya zaro Saif-Al-Barzaƙ daga cikin jikinsa.
A zahirin gaskiya, ba wai cikin jikinsa yake soka wannan takobi ba, wannan ruhi yake baiwa ajiyarta.
Amma abinda idanuwa suke nunawa shi ne, cikin jikinsa yake cakata.
Wannan na daga cikin amfanin wannan ruhi, mutum zai iya bashi ajiya a nemi abun sama da ƙasa a sara.
Samudul Ansari ya kaiwa Gauhan sara-mai-tafiya wanda ke ɗauke da sinadarin Jeeish.
Cikin zafin nama Gauhan ya zana wadannan ɗalasimai akan ƙasa, sannan ya ɗauki dungulmayen kawunan waɗannan sarakuna guda biyu da Samudul Ansari ya sare.
A daidai lokacin irin wannan rami wanda muka gani ya bayyana sa'adda wani mutum yake ƙoƙarin hana Samudul Ansari zuwa ɗakin amaryarsa Arya ya sake bayyana.
Gauhan ya faɗa cikin ramin, wanda hakan ya bashi damar kaucewa wannan sara-mai-tafiya na Saif-Al-Barzaƙ.
"Wai yaushe zamuyi maganin irin wannan rami da yake bayyana ne?" Samudul Ansari ya tambayi wannan ruhi.
Ruhin ya ce, "Kaine baka ga damar maganin hakan ba shiyasa, amma idan ka ƙara duba wannan littafi na tabbata zaka samu irin wadannan bayanan."
A daidai lokacin gaba ɗaya rundunar birnin Ilam suka wajen da Samudul Ansari ke tsaye, suka zube a gabansa suka yi mubaya'a.
Zarifa ta rungume shi tana cewa, "Ina sonka, mijina. Na gode da ceton rayuwata da kayi..."
Sarauniya Arya ta sauƙo daga saman wannan ganuwa ta ƙaraso wannan waje a cikin wani ƙasaitaccen keken doki.
Dukkan mayaƙan suka yi tsit suna sauraron jawabin sarauniya.
Sarauniya Arya ta ƙaraso wajen da Samudul Ansari ta dube shi cikin kallo mai cike da yabo da jinjina ta ce, "Daga yau ga sarkin da zai mulki wannan daula gaba ɗaya.
"Tunda an hallaka sarakuna guda biyar, a matsayina na sarauniya guda ɗaya da ta rage na baiwa wannan jarumi kyautar wannan daula.
"Daga yau zamu yaƙi dukkan ma'abota Bankai da suka mamaye sauran garuruwa na wannan daula ƙarƙashin jagorancin Tau'rin...
"Indai akwai Samudul Ansari, babu sauran tashin hankali a wannan daula gaba ɗaya..."
Gaba ɗaya mayaƙan dake wannan wuri, suka ruɗe da shewa sannan suka sake jaddada mubaya'arsu ga Samudul Ansari.
"Da sannu dukkan mutanen duniya zasu risina a gabanmu, su yi mana mubaya'a..." inji wannan ruhi.
Samudul Ansari ya ɗebi wannan runduna ta waɗannan mayaƙa suka afka cikin wannan daula, suka tunkari babban birnin Shaha.
Duk garin da suka zo wucewa da zarar sun riski ɗaiɗaikun mayaƙan Gorgon waɗanda ba'a fita dasu yaƙi ba, ko kuma wadanda suka gudu sai Samudul Ansari ya hallaka su.
Duk garin da suka tarar da tutar Gorgon sai su ƙoneta sannan su kafa tutar Shaha.
Mafi yawancin garuruwan da mayaƙan Gorgon suka ci da yaƙi, sun ruguje sun rushe.
Har suka dangana da birnin Shaha wanda suka tarar gaba ɗaya ya gama rushewa.
A wannan gari sarauniya Arya ta naɗawa Samudul Ansari rawanin mulkin wannan daula gaba ɗaya.
Samudul Ansari da hannunsa ya sake gina birnin Shaha, kyawunsa da girmansa ya ninka na farko.
Samudul Ansari yasa wadannan dakaru dake ƙasansa sake gine wannan daula gaba ɗaya.
Kyawun wannan daula da ƙawatuwarta ya ninka na farko sau goma.
Kai idan kaga wannan daula, zaka ce ba'a taɓa gwabza yaƙi a cikinta ba.
Musamman sarki Samudul Ansari ya shaci wani ƙaton filin-yaƙi a cikin wani ƙaton daji ya saka masa suna 'AJALIN-ABOKAN-GABA'.
Sarki Samudul Ansari ya ayyana Ajalin-Abokan-Gaba a matsayin filin yaƙin da za'a na gwabza duk wani yaƙin da ya taso a wannan daula.
*****
Yau *13/03/2023*
Babi na gaba zaizo *16/03/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 98: *Fusatar Sarauniya Yilan*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
UMS
*
~Daular Gorgon.
*
Kamar yadda mahaifinta ya umarceta haka ta kasance, wato duk wannan gumurzu da aka gwabza a filin yaƙin Nayesh, sarauniya Yilan tana kallo a cikin wani mudubi.
Koda taga Samudul Ansari ya fille kan sarakunanta guda biyu sannan ya faɗawa Gauhan baƙar magana yaje ya faɗa mata, sai zuciyarta ta fara tafarfasa.
Ranta yayi mummunan ɓaci, idanuwanta suka koma koraye dukkaninsu kalar na maciji. Harshen bakinta ya rikiɗe ya koma irin na maciji.
Macizai guda huɗu manya suka bayyana a gashin kanta, suka fara ihu suna rangaji, suna neman abin taɓawa.
Sarauniya Yilan tayi girgiza jikinta ya juye izuwa koren haske sannan ta ɓace ɓat! daga cikin wannan fada.
A tsakiyar wani baƙin daji ta bayyana wanda ke ɗauke da manyan bishiyoyi masu fala-falan ganyaye waɗanda suka sa hasken rana bai wadaci wannan daji ba.
Tana bayyana a tsakiyar dajin tayi kururuwa ta ɗaga maɗaukakan takubbanta sama ta fara tsinewa Samudul Ansari.
"Ziyazilu ta tsine ma ya kai wannan tsinanne [Samudul Ansari]
"Shehunan addinin Bankai su tsine ma ya kai wannan tsinanne [Samudul Ansari]
"Albarkar dake cikin Renin-Yilan ta tsine maka [Samudul Ansari]
"Macizan dake rayuwa bisa kanmu sun tsine maka [Samudul Ansari]"
Sarauniya Yilan tana zuwa nan a zancenta, ta sake kwarara uban ihu wanda ya cika dukkan wannan gaba ɗaya.
Nan take ta ƙwalawa manyan sarakuna guda biyar dake ƙarƙashin mulkinta kira.
"Harsama Gorgon!"
"Najana Gorgon!"
"Ƙulzam Gorgon!
"Aiyni Gorgon!
"Hayara Gorgon!"
Nan take waɗansu irin manya-manyan macizai suka fara fitowa daga ƙarƙashin ƙasa a cikin wannan daji, sannu-a-hankali suka fara kewaye sarauniya Yilan a tsakiya.
Macizan suka fara miƙewa tsaye suna juyewa izuwa siffar mutane.
Harsama, Najana, Aiyni da Hayara duk tsala-tsalan yan-mata ne. Ƙulzam ne kaɗai namiji a cikinsu.
Wani irin iko ya cika wannan waje, inda ace akwai mutum tsaye a gefensu ba zai iya koda ɗaga ɗan yatsansa guda ba, saboda ƙarfin ikon dake tashi daga jikinsu.
Waɗannan mutane guda biyar su ne sarakunan dake daf da matsayin Yilan Gorgon, wato kamar su ne mabiyanta a wannan daula.
Sarauniya Yilan ita ce shugaban wannan daula gaba ɗaya.
Masu bin ta a ƙarfin mulki kuwa, su ne waɗannan sarakuna guda biyar, ana yi musu laƙabi da *BES*.
BES: Kalma ce a yaren wannan daula wadda take nufin biyar.
Kai, ƙarya ne ace BES sun jagoranci yaƙi, ba'a sami nasara ba.
Saboda anyi hakan ba sau ɗaya, ba sau biyu ba, ba sau uku ba... Kamar yadda cin abinci ya zamo ƙa'ida ga kowanne mutum, haka samun nasara a wajen BES yake.
A tarihin wannan daula, ba'a taɓa samun gumurzun da yafi ƙarfin ma'abota Bankai ba, balle har yaje kan sarakunan daular (Ƙananu). Kada ma ka kawo maganar abin yaje wajen BES.
Saboda duk wanda yayi tunanin tunkarar daular da yaƙi, ma'abota Bankai kawai ake tura masa su hallaka shi.
Ba'a taɓa samun wanda ya iya jada da ma'abota Bankai ba, balle har lamarin yazo kan sarakunan wannan daula ƙananu kamar su Mahrus da sarkin birnin Mesa waɗanda Samudul Ansari ya kashe sai shi Samudul Ansari ɗin.
Ga dukkan alamu lamarin Samudul Ansari a wannan daula ya soma ɗaukar zafi, hatta ita kanta sarauniya Yilan ta soma fusata saboda lamarinsa.
Ga shi har ta kai ta ga kiran BES domin tattaunawa akan Samudul Ansari.
Waɗannan mutane guda biyar gaba ɗayansu, suna sanye da korayen tufafi wadanda aka ɗinka da irin wannan auduga mai kaurin gaske.
Korayen tufafin sun lulluɓe ko'ina da ina na jikinsu, yadda ba za ka iya shaida mace ne ko kuma namiji ba.
Babu wani hijabi da ya rufe musu fuska amma saboda ƙarfin ikonsu da kuma kwarjininsu, babu wanda ke iya ɗaga kai ya kalle su, idan ba wanda yake da takobin Bankai mataki na arba'in yayi sama ba.
Waɗannan sarakuna basa bayyana sosai a wannan daula. Mafi yawancin lokuta idan kaga sun bayyana wani abu ne mai muhimmanci ya taso, ko kuma sarauniya Yilan tana so ta gana dasu.
"Akwai abu mai muhimmanci da ya taso wanda yake buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa," inji sarauniya Yilan, lokacin da wadannan mutane suka yi ladab a gabanta suna sauraron abinda take ce musu.
"Zamu tattauna akan abu guda ɗaya - Kuyurul Samudul Ansari, wanda a halin yanzu ya aikata mana laifuka guda uku.
"Hawa kan tsaunin daraja, tsaunin Hajarul Gorgon inda abar bauta Ziyazilu take - laifi na farko.
"Ya kashe ma'abota da dama waɗanda adadinsu yake da yawan gaske - laifi na biyu.
"Ya kashe sarakunan birnin Mesa da birnin Hazram - laifi na uku.
"Kowanne ɗaya daga cikin waɗannan laifuka, maigirma Ziyazilu tayi wadaransu.
"Saboda haka hukunta wannan mutumi ya zamo dolen-dole.
"Ya ya kuke ganin ya kamata a ɓullowa yaƙi dashi tunda har ta kai ga cewa, ya mallaki Saif-Al-Barzaƙ, takobin da jinin Raizam suka ƙirƙiro?"
Koda waɗannan mutane suka ji batun sarauniya Yilan sai suka sunkuyar da kawunansu ƙasa, cikin biyayya suka ce.
"Duk shawarar da kika yanke, da ita zamu aiki, ya shugabar mu!"
Sarauniya Yilan tayi gajeren tunani ta ce, "Shawara guda biyu gare ni," ta ɗan yi shuru ta sake yin gajeren tunani sannan ta ci gaba.
"Shawara ta farko: Mu sake tura masa sarakuna ma'abota Bankai guda uku maimakon da farko da muka tura guda biyu...
"Shawara ta biyu: Ɗaya daga cikin ku, ta ɗebi gagarumar runduna taje ta shafe wannan daula gaba ɗaya...
"Wacce shawara kuke ganin, ya kamata mu ɗauka?" sarauniya Yilan ta tambaye su.
Tsahon daƙiƙu suna tunani akan shawarar da ta dace.
Mafi yawancin lokuta irin haka, sarauniya Yilan tana basu dama suyi tunani sannan su sanar da ita abinda suka yanke.
"Mun zaɓi shawara ta biyu!" inji uku daga cikinsu.
Sarauniya Yilan bata buƙatar jin bakin sauran guda biyu, saboda guda ukun nan sunyi rinjaye.
"Wacce ce a cikin ku, zata je daular Shaha ta saro min kan wannan jarumi?" Sarauniya Yilan ta tambaye su.
"NI" dukkansu suka amsa.
Kai da gani ka san cewa, kowa a cikinsu so yake a ce yaje ya yiwa Samudul Ansari hukunci, saboda sun yadda da ƙarfinsu.
Koda sarauniya Yilan ta lura da cewa, babu wanda a cikinsu zai yarda ya janyewa ɗan-uwansa sai ta ce ayi ƙuri'a.
Bayan kaɗa ƙuri'a ta faɗa kan Aiyni Gorgon, wata kyakkyawar budurwa tafi dukkan sauran kyawu.
Aiyni Gorgon ta daka tsallen murna, ta zaro takobinta Bankai mai mataki na saba'in da takwas ta kwarara uban ihu.
Sauran waɗannan mutane guda huɗu suka tayata murna sannan suka sake rikiɗewa izuwa macizai suka shige cikin ƙarƙashin ƙasa.
Sarauniya Yilan ta dafa Aiyni Gorgon suka ɓace ɓat! daga cikin wannan baƙin daji.
A tsakiyar wani ƙaton sansani suka bayyana wanda babu komai a cikinsa face mayaƙa ma'abota Bankai guda dubu ɗaya da ɗaya.
A wannan waje babu gauraye, dukkan waɗanda suke wajen ma'abota Bankai ne.
Sannan babu wanda ke ɗauke da mai mataki na ƙasa da talatin. Mafi yawancin su daga mataki na talatin ne yayi sama ne.
Ga dukkan alamu waɗannan mayaƙa anyi tanadinsu ne, musamman domin hukunta irinsu Samudul Ansari.
Mayaƙan suna ganin sarauniya Yilan dukkansu suka shiga taitayinsu, waɗanda suke barci suka farka, waɗanda ke zaune suka miƙe.
Dukkansu suka jeru sahu-sahu domin sauraron umarnin sarauniya.
Mafi yawa daga cikin wadannan mayaƙa yan-mata ne, amma sai dai kana ganinsu zaka san cewa, lallai shiryayyu ne.
Sarauniya Yilan da Aiyni Gorgon suka ratsa ta tsakiyar waɗannan mayaƙa suka tunkari wani dogon mumbari dake can ƙarshen sansanin.
A wannan lokaci waɗannan mayaƙa gaba ɗayansu, sun gama jeruwa a sahu-sahu sannan sun ƙame tamkar babu ruhi a jikinsu.
Sarauniya Yilan da Aiyni suna zuwa saman wannan mumbari, suka fara yiwa mayaƙan dake wajen bayani.
"Lokacin da kuka daɗe kuna jira a duniya yazo," sarauniya Yilan ta fara jawabi.
"An samu wani gawurtaccen jarumi da ya aikata mana manyan laifuka har guda uku waɗanda suka sa Ziyazilu da kanta ta bayar da umarnin saro kan wannan mutum dake rayuwa a daular Shaha.
"Mun tura ƙananun sojojinmu amma basu yi nasara ba, dole sai mun tura ku indai muna so mu sare kansa..."
Koda mayaƙan dake wannan sansani suka ji abinda sarauniya Yilan tace, sai suka ruɗe da shewa.
Fiye da shekaru goma sha-biyar, sarauniya Yilan ta ware su daga cikin sauran mutanen wannan daula.
Musamman tasa aka gina wannan sansani domin a ɗinga baiwa mayaƙan horon yaƙi, sannan a ɗinga tsuma su a cikin baƙin dafin maciji.
Saboda haka, idan ka cire ita kanta sarauniya Yilan da kuma BES, babu waɗanda suka kai waɗannan mayaƙa ƙarfi.
Har kirari ake musu da *ASALIN-BANKAI*
Sarauniya Yilan ta ci gaba, "Zamu mutum ɗari uku daga cikinku, su tafi daular Shaha domin mayar da ita tarihi.
"Aiyni Gorgon ita ce zata jagorance ku..."
Koda Aiyni Gorgon taji abinda sarauniya Yilan ta ce sai ta ɗan haɗe fuska ta dubi Yilan ta ce, "Ya shugabata! Wannan daular ce zamu tura mata mayaƙan har guda ɗari uku, kuma nan ma ace asalin-Bankai?
"Gaskiya an raina ƙarfi na..."
Sarauniya tayi murmushi ta dubi Aiyni ta ce, "Ni na san abinda ke ba ki sani ba... Ki bi umarni kawai..."
Aiyni Gorgon ta risina ta ce, "Tuba nake..."
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, sarauniya Yilan da kanta ta zaɓo mayaƙa guda ɗari uku.
Dukkansu aka kawo musu waɗansu irin dawakai waɗanda idanu basu saba kallo ba, aka baiwa kowannensu suka hau.
Sarauniya Yilan ta dube su ta ce, "Su same su a fada, domin yin wannan gagaruman tafiya ta saro kan Samudul Ansari.
Tana faɗin haka, ta dafa Aiyni suka ɓace ɓat!
Waɗannan mahaya guda ɗari uku suka zaburi dawakansu da gudu suka tunkari babbar fadar sarauniya Yilan.
Suna isowa fadar suka iske babu kowa a cikinta face sarauniya Yilan da Aiyni Gorgon.
Sarauniya Yilan tana zaune akan ƙatuwar karagar mulkinta, ita kuwa Aiyni tana zaune a gaban karagar ta risina.
Mayaƙan suka tsaya daga can nesa.
Sarauniya Yilan ta fara yiwa Aiyni jawabin yadda zasu farmaki daular Shaha.
"Za ki raba wannan runduna ta ki izuwa kaso uku - ɓangaren A, ɓangaren B da ɓangaren C.
"Ke da ɓangaren A za ku yaƙi daular ta hanyar amfani da takubban ku...
"Ɓangaren B zasu yi yaƙi da Renin-Yilan dake cikin maɗaukakan idanuwansu.
"Ɓangaren C zasu gurɓata ruwan sha na wannan daula gaba ɗaya.
"Kada ku kuskure ku ce zaku yaƙi daular Shaha da ɓangaren A, idan ba'a filin yaƙin Ajalin-Abokan-Gaba ba.
"Saboda dukkan wasu sassa da dazuzzuka na wannan daula, Samudul Ansari ya riga da ya binne kafi wanda zaiyi matuƙar baiwa dakarunmu ciwon-kai.
"Ku na shigar farkon daular zakuyi sallama da ɓangaren C zasu tafi tekuna, koguna da ƙoramai na wannan daula su gurɓata ruwan shan su.
"Kin ga kenan, hakan zai baiwa rundunar mu kyakkyawar damar cin wannan daula da yaƙi.
"Babu abinda zasu taɓuka matuƙar aka ce, sun rasa ruwan sha.
"Wannan bayani kenan akan yadda za ki ɓullowa wannan yaƙi."
Sarauniya Yilan ta ɗan yi shuru ta sake tattaro hankalin Aiyni Gorgon.
"Shin kin san cewa Samudul Ansari ya hallaka ma'abota Bankai har guda biyu, tun kafin ya mallaki takobin Saif-Al-Barzaƙ?"
Aiyni Gorgon ta gyaɗa kai, "Eh na sani..."
"Ta ya ya kike tunanin za ki yaƙe shi, ki saro kansa. Tun da kinsan cewa yana da takobin Saif-Al-Barzaƙ sannan yana da Tau'rin [ma'ana na II]?"
Aiyni ta ɗan yi shuru tsahon lokaci tana tunani, kafun ta buɗi baki ta ce, "Zan yi amfani da ƙololuwar matakin takobina (Bankai 78)!"
Sarauniya Yilan tana jin haka, tayi murmushi, ta dafa kan Aiyni a wani salo kamar mai saka mata albarka.
Ya kamata a san cewa, duk wani saran Bankai-mai-tafiya da ma'aboci Bankai yayi amfani dashi da mataki na biyar kawai na wannan takobi yayi amfani.
Abinda yasa marigayi sarki Mahrus da sarkin Mesa basu yi amfani da ƙololuwar mataki na takubbansu ba shi ne, sarauniya Yilan bata amince musu da hakan ba.
Zaka iya cewa sarauniya Yilan bata taɓa tsammanin matsayin Samudul Ansari ya kai yadda yake a yanzu ba, sai da ya kashe su Mahrus da sarkin Mesa.
Tabbas a wannan lokaci ta gama fusata iya fusata, sannan ta gama shiryawa domin kawo ƙarshen Samudul Ansari.
Sarauniya Yilan tana gama sakawa Aiyni albarka ta bata umarnin tafiya wannan aiki.
Kafun Aiyni ta miƙe daga inda take zaune, suka ga wani mutum ya shigo cikin wannan fada, ɗauke da dungulmayen kawuna guda biyu.
Saurayi ne wanda kallon farko zaka yi masa, tunanin Gauhan ya faɗo ranka. Koda yake idan ka ƙare masa kallo zaka gane cewa, ai Gauhan ɗin ne.
Sarauniya Yilan ta ɗaga korayen idanunta ta dakawa wannan saurayi harara, take jikinsa ya fara ƙyarma sannan ya zube ƙasa a inda yake, ba tare da ya ƙaraso inda take ba.
"Kai marar kunya!" ta daka masa tsawa. "Uban me ya kawoka fadar nan..?"
Kafun Gauhan ya buɗe bakinsa ya ce wani abu, tuni Aiyni tayi fushi da fushin sarauniya ta zaro takobinta Bankai mai mataki na saba'in da takwas.
Wata koriyar walƙiya wadda ta haskaka wannan daula gaba ɗaya ta bayyana.
Duk wanda ke rayuwa a cikin wannan daula saida ya ga wannan walƙiya.
Lallai lamarin Bankai 78 babban lamari ne.
Jikin Gauhan ya ci gaba da kyarma, Aiyni tana shirin kai masa hari kenan.
Wani irin ƙaramin maciji mai fuka-fuki yazo ya wuce ta saman fadar yana wani irin ihu, wanda da sauraronsa gwamma sauraron aradu a tsakiyar daji.
Sarauniya Yilan tana jin kukan wannan maciji tayi saurin dakatar da Aiyni.
A duk sa'adda ta ji irin wannan kuka na maciji, kira ne daga mahaifinta akan wani babban kuskure da take ƙoƙarin aikatawa.
Sarauniya Yilan ta harari Gauhan da waɗannan idanuwa nata, take wasu sarƙoƙi suka kanannaɗe dukkan jikinsa.
Sarauniya Yilan tasa aka kulle shi a cikin wani ɗaki, kafun taje wajen mahaifinta ta dawo.
Aiyni Gorgon ta mayar da takobinta cikin kufe, sannan tayi sallama da shugabarta ta shiga gaban waɗannan mayaƙa guda ɗari uku, bisa wani ingarman doki suka tunkari hanyar barin wannan daula gaba daya.
Sarauniya Yilan tayi girgiza ta juye izuwa jibgegiyar macijiya sannan ta tunkari dajin da mahaifinta yake domin taji dalilin da ya sa ya kirawo ta.
****
A can birnin Shaha kuwa, tuni Samudul Ansari ya gama sauya komai da komai na wannan daula.
Duk wani abu da zai kawowa wannan daula barazana, Samudul Ansari ya kawar da shi.
Da kansa yake hawa yaje duk inda wani abu zai kawowa daular barazana ya kawar da shi.
Saboda tabbatar da tsaro, Samudul Ansari yayi hawa shi da Zarifa suka shiga dazuzzukan wannan daula suka bibbine wani kafi wanda wannan ruhi ya bashi.
Shi dai wannan kafi amfaninsa shi ne, hana yaƙi a duk inda aka binne shi.
Duk wanda ya yarda yayi kuskuren yaƙi a wajen da aka binne wannan kafi, har abada ba zai iya dawowa wajen ba, face an karya wannan kafi.
Sannan abin ba wai iya kansa zai tsaya ba, hatta ƴaƴansa da jikokinsa sai abin ya shafe su.
Wannan abu, sarki Samudul Ansari bai sanar da kowa ba sai matarsa Zarifa wadda suka fito aikin tare.
Kai, daular Shaha babu inda Samudul Ansari bai binne wannan kafi ba, sai filin Ajalin-Abokan-Gaba.
Ba don komai yayi haka ba, sai domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a wannan daula.
Filin Ajalin-Abokan-Gaba kuma ya

Please Login or Register in order to submit comment