Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aikin ɗauko wannan sulke na yaƙi wanda muka baiwa Riya.
"Lallai idan muka kammala aiki na ƙarshe a cikin nasara, za muje wajen mahaifiyar Aymanul Faris da mutanen birnin Shaha gaba ɗaya domin gabatar musu da manufofin da suka sa muke waɗannan ayyuka da kuma irin masifu da bala'in da zasu biyo baya idan ba'a mallaki wannan ruhi da wuri ba.
"Wannan aiki da zamu gudanar na ƙarshe shi ne, ƊAUKO MAKULLIN TASKAR SAMUDUL ANSARI A BIRNIN HINDU, wanda zamuyi amfani da shi wajen buɗe rijiyoyin ƙarƙashin ƙasa da sarki Samudul Ansari ya ajiye ruhinsa a cikinsu.
"Shi dai wannan sarki ana kiransa da suna Raja, babban sarki ne a wancan nahiya. Yadda aka yi ya mallaki wannan makulli kuwa, abu ne wanda yazo da rainin hankali.
"Lokacin da sarki Samudul Ansari ya fuskanci cewa ƙarshensa ya kusa zuwa, sai yayi wata tafiya izuwa cikin wani ƙaton teku inda yayi nutso izuwa ƙarƙashin tekun, ya isa bakin wata rijiya ya buɗe marufinta ya ajiye wannan makulli a ciki.
"Babu wanda ya san yadda aka yi sarki Raja ya gano inda aka ajiye wannan makulli da kuma yadda aka yi ya mallake shi. Amma an tabbatar da cewa wannan makulli yana hannunsa.
"Babu wanda ya san meye zaiyi da wannan makulli tunda dai bai kasance jinin Samudu ba, sannan bai isa ya je inda wannan kogon dutse yake ba.
"A kullum da kowanne lokaci wannan makulli yana ɗaure a wuyansa, baya rabuwa da makullin, dare da rana yana tare da shi.
"Kai ko barci yake ko kuma wanka wannan makulli na ɗaure a jikinsa.
"Sarki Raja yayi rantsuwa da abin dogaronsa cewa, ba zai taɓa rabuwa da wannan makulli muddin yana numfashi.
"Saboda haka dole idan muna so mu raba shi da wannan makulli, sai mun sare kansa.
"Birnin Hindu babban birni ne a duniya wanda yake da tarihi mai girman gaske. Birni ne wanda ya tara dubban mayaƙa masu ƙarfin damtse da iya yaƙi.
"Idan ka cire birnin Sin zai yi wuya ka samu birnin da ya kai Hindu tarin al'umma da girman ƙasa.
"Saboda wannan dalili ba zamu shiga birnin Hindu kai tsaye, mu kaiwa sarki Raja hari ba.
"A duk ƙarshen shekara yana wata fita izuwa ƙasashen dake ƙarƙashin mulkinsa domin ganin yadda ake tafiyar da harkokin mulki.
"A cikin ƙasashen dake ƙarƙashin mulkinsa akwai wata ƙasa da ake kira Duhamul, wannan wani ƙaramin birni ne a tsakiyar wata sahara, kafun a je wannan birni sai an yi doguwar tafiya.
"A wannan waje zamu yiwa sarki Raja kwantan-ɓauna, lokacin da suka zo wucewa shi da tawagarsa Ayman da abokan aikinsa zasu fito su afka musu da yaƙi.
"Lallai za'a gwabza mummunan yaƙi wanda hatta ni kaina bansan ƙarshensa ba, amma a ƙarshe rundunar mu zata yi nasara da yaddar abin bauta.
"Da zarar mun kammala wannan aiki, Ayman kai da Hodon za ku kaiwa tsoho Samazan dake cikin kogon dutse a yankin birnin Hindu ziyara domin sauraron hikayar Samudul Ansari da sarauniya Arya.
"Daga wannan lokaci za ku dawo wannan waje nawa, na sanar da ku motsin mu na gaba wanda nake tunanin tafiya izuwa kogon Samudul Ansari ne.
"Shin akwai mai tambaya a cikin ku ko kuma neman ƙarin bayani?"
Lokacin da aljani Ranganu yazo nan a zancensa, sai yayi shuru ya baiwa Aymanul Faris da Barban dama domin su yi tambaya.
Tsahon ɗan lokaci suna ta tunani da nazarin waɗannan maganganu da ya zayyane musu. Kamar ba zasu ce komai ba, daga can sai Aymanul Faris ya numfasa ya ce.
"Shin wannan kogon dutse yana da ƙofa mai zaman kanta ne wadda take amfani da makulli wajen buɗewa?
"Ita kuwa takobin Saif-Al-Barzaƙ da ake maganarta tana wanne wuri a halin yanzu?
"Nifa tun da maganar kogon Samudul Ansari ban ma san ta wanne ɓangare kogon yake ba?"
Aljani Ranganu na jin tambayoyin Aymanul Faris ya yi murmushi ya ce, "Amsar tambayarka ta farko ita ce, a bakin shiga wannan kogo ba ƙofa bace irin wadda ka sani. Wata ƙofa ce ta haske wadda aka yiwa siffar ƙwarangol, a daidai ƙirjin sa akwai alamar wurin saka makulli. Wannan ita ce amsar tambayarka ta farko.
"Amsar tambayar ka ta biyu ita ce, a halin yanzu takobin Saif-Al-Barzak tana cikin wannan kogo na Samudul Ansari, tana kusa da inda aka ajiye wannan kwalba wanda aka saka ruhinsa a ciki. Wannan ita ce tambayarka ta biyu.
"Amsar tambayarka ta uku ita ce, idan baka manta ba sa'adda muke kallon yarima Marganu a cikin madubin tsafi lokacin da yake dawowa da mahaifiyarka izuwa dajin Marsas, mun ga ya shiga cikin dajin Djinn.
"Idan baka manta ba a wannan daji na Djinn, mun ga ya iso wata mararraba ta waɗansu hanyoyi guda biyu - ɗaya ta nufi kudu ɗaya kuma arewa.
"Marganu ya nufi hanyar arewa wadda ta sada shi ta dajin Shiwazu har dai ya iso dajin Marsas muka yi musanya.
"To, ka sani cewa, wannan hanya da ta nufi nufi kudu ita ce zata sada mutum da muggan dazuzzuka huɗu waɗanda suka yi iyaka da kogon Samudul Ansari.
"Masifu da bala'in dake waɗannan wurare shi kansa Samudul Ansari sai da ya yiwa magadansa gargaɗi a cikin wasiƙar da ya bari, lokacin da zaiyi ƙaura.
"Saboda wannan dalilai muka ga ya dace duk wanda yake so ya zama cikakken Tau'rin mu bashi dama, domin ya kimtsa kansa.
"Har yanzu da sauranka tukunna, ba zaka iya wuce waɗannan dazuzzuka guda huɗu a haka ba.
"Idan muka sami nasarar ƙwato makullin dake hannun sarki Raja zanyi maka bayanin yadda zamu kimtsa ka da sihirin tsafi wanda zai baka damar jure wahalar da zaka sha a cikin waɗannan dazuzzuka.
"Da fatan ka fuskance ni?"
Aymanul Faris ya gyaɗa kai alamar ya fahimci abinda Ranganu ya sanar da shi.
Barban ya numfasa ya ce, "Ya shugabana! Ina neman ƙarin bayani akan yadda wannan gumurzu na mu da su sarki Raja zai kasance?"
Aljani Ranganu na jin haka yayi murmushi ya ce, "Yadda gumurzun zai kasance shi ne, yau ashirin da takwas ga watan Mayu.
"Ranar huɗu ga watan Yuni sarki Raja zai yi wannan fita da ya saba. Yadda zamu farmake shi, shi ne, sarki Raja yana fita wannan rangadi da yake yi da dakaru dubu uku kacal.
"Kasancewar a yankin ƙasarsa yake, baya shakkan komai daga abokan gabarsa ko kuma masu masa tawaye. Wannan yasa yake fita da dakaru yan ƙalilan.
"Aymanul Faris kaɗai zai iya tarwatsa wannan runduna ta sarki Raja amma ba ma buƙatar hakan, saboda idan ya fuskanci gumurzu zai fi ƙarfinsu akwai sihirin da yake ya zamo shaho ya gudu daga waje.
"Saboda wannan dalili muka tsara yadda zamu kai wannan farmaki daki-daki.
"Sarki Raja yana da waɗansu dakaru guda uku dake take masa baya, kullum da koda yaushe suna tare basa rabuwa.
"A matsayina na gawurtaccen matsafi naje da kaina na kallo waɗannan dakaru guda uku, sannan na gudanar da bincike akan su gaba ɗaya.
"Waɗannan dakaru guda uku, ba mutane bane. Inuwar sihirin sarki Raja ne, matuƙar aka ce an hallaka waɗannan dakaru guda uku tamkar an ci ƙarfin sarki Raja ne, ba zai iya rikiɗewa izuwa wannan shaho ba.
"Saboda wannan dalili muka tsara yadda zamu hallaka waɗannan dakaru guda uku cikin ruwan sanyi, ba tare da sarki Raja ya ankara ba.
"Domin yana ankara zaiyi wata girgiza waɗannan dakaru su ɓace su shiga jikinsa, indai suna jikinsa ba za'a taɓa samun nasara akansa ba.
"Mataki na farko: muna buƙatar ƙwararren maharbi wanda zai iya harbo waɗannan dakaru guda uku daga nesa, sannan cikin zafin nama ba tare da sarki Raja ya ankare ba.
"Wannan maharbi ba wani bane illa Oksu, dake rayuwa a birnin Zerina.
"Mataki na biyu: muna buƙatar afkawa sauran dakarunsa cikin gaggawa mu hallaka su, ya zamana cewa cikin ƙanƙanin lokaci ya rage saura shi kaɗai.
"Mataki na uku: shi ne, dole ne Aymanul Faris da Riya su haɗa kai, su yaƙi wannan sarki su biyu. Saboda idan su ka ce da ɗaiɗaiya zasu yaƙe shi, ba zasu yi nasara ba.
"Kai ana ganin cewa, sarki Kuffuru ne kaɗai zaifi sarki Raja ƙarfin damtse, nan ma tsammani ake ba'a tabbatar ba.
"Yanzu ku koma birnin Darul Barban ku gama tattaunawa da su Hajriya akan wannan aiki, idan kun gama sai ku dawo nan, mu sanar da ku hanyar da za'a bi a riski wannan maharbi [Oksu]."
Lokacin da Ranganu yazo nan a zancensa sai Aymanul Faris da Barban suka yi ajiyar zuciya a tare, lallai wannan aiki da zasu je yana da mugun haɗari.
Kuskure kaɗan na nufin rasa wannan makulli gaba ɗaya.
Koda aljani Ranganu ya fuskanci cewa duk a cikinsu babu wanda zai ce wani abu, sai ya basu umarnin tafiya izuwa birnin Darul Barban domin sanar da su jaruma Riya wannan aiki.
Barban ya dafa kafaɗar Aymanul Faris suka ɓace ɓat, daga cikin wannan fada.
****
Yau *28/01/2023*
Babi na gaba zaizo *30/01/2023* da yaddar Allah.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 78: *Yaudara*
*
SADAUKARWA GA MASOYA...
*
U*M*S
*
~Kuffuru.
*
Sai da aljani Sheezuwa yayi tafiya ta tsahon mako uku a sararin samaniya sannan ya sauƙa a tsakiyar wani ƙaton daji wanda manyan tsaunika gudu huɗu suka kewaye. A tsakiyar tsaunikan kuma, ƙatoton fili ne fetal tamkar gwadawa aka yi aka bar shi.
Aljani Sheezuwa na sauƙa a ƙasan wannan daji, ya fara amai ɗin jini da tari mai tayar da hankali.
Cikin gaggawa boka Hubbazu da sarauniya Rauziyya suka fiddo magani suka bashi ya sha, tarin nasa ya lafa sosai amma dukda haka bai daina ba.
Aljani Sheezuwa ya dube su ya ce, "Daga wannan lokaci tawa ta ƙare, wannan dafi ya gama cin jikina. Kowanne lokaci daga yanzu ƙarfin jikina raguwa zai nayi, har zuwa sa'adda zan bar duniya.
"Yanzu zan sanar da ku yadda za'a gina wannan kurkuku kafun muyi sallama na koma ƙasar da matayena suke rayuwa a cikinta.
"Kamar yadda na sanar da ku abubuwan da ake buƙata wajen kamo Barban sun haɗa da: sadaukai uku ƴan baiwa, gina wannan kurkuku da kuma kawar da aljani Ranganu daga doron duniya.
"Mun samu nasarar haɗa sadaukai uku, sannan mun samu nasarar ɗebo tubalin Jekish, bayan kammala gina wannan kurkuku abinda zaku mayar da hankali akansa shi ne hallaka wannan aljani wato Ranganu.
"Bayan kun hallaka Ranganu salin-alin zaku kamo Barban ba tare da fargaba ko tsoron komai ba.
"Ba zan kai lokacin da zaku zo wannan gaɓa ba, saboda haka a lokacin wajen boka Balwaz zakuje yayi muku bayani.
"Ga tubalin gina wannan kurkuku amma babu mai iya ginata duk faɗin duniya, idan ba magini Gidr ba. Mai gidana Hubbazu zai yi muku bayanin inda Gidr yake a halin yanzu.
"Na bar ku lafiya muyi sallama irinta waɗanda baza su sake haɗuwa ba!" Aljani Sheezuwa yana zuwa nan a zancensa ya karkato aljihunsa duk ƙasar wannan tubali da ya ɗebo ta zubo a wannan wuri ta taru a waje guda.
Koda su sarki Kuffuru suka ga haka sai tausayin Sheezuwa ya lulluɓe su. Sun shaƙu dashi sosai a wannan tafiya, kuma ko ba komai shi ne wanda ya buɗe musu hanyar da zasu bi su kamo Barban.
Bayan ɗan lokaci suka yi bankwana da juna. Hubbazu yana kuka Sheezuwa yana kuka saboda sabo, amma a haka Sheezuwa ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama ya bar wannan wajen gaba ɗaya.
Tsahon daƙiƙu suna alhinin rabuwa da shi, kafun daga bisani sarauniya Rauziyya ta sake yankar jiki ta faɗi sumammiya, kamar yadda ta taɓa yi a watannin baya.
Sarki Kuffuru, sarki Darwazu da boka Hubbazu suna ganin haka hankalinsu yayi mummunan tashi, saboda basu san meye zasu faɗawa Rauziyya ba idan ta farfaɗo.
Ko shakka babu wani saƙo mai muhimmanci ake sanar da ita, wanda idan ba su yi sa'a ba zata iya tafiya ta barsu.
A wannan gaɓa da suke wadda wannan aiki da suka ɗauko yake daf da fara ɗaukar zafi. Daga lokacin da aka ce sun fara amfani da wannan taswira lallai aikin ya ɗauko zafi.
Sarki Kuffuru ya dubi Hubbazu ya ce, "Mene ne abin yi? Har yau wanda muka tura ya hallaka Marganu bai dawo ba, sannan ba mu sake jin ɗuriyarsa ba?
"Meye zamu faɗawa sarauniya Rauziyya idan ta farfaɗo?"
Boka Hubbazu yayi murmushi ya fiddo madubin tsafinsa ya duba shi, ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "Nan da rabin sa'a kacal, za'a kawo Marganu wannan wuri a raye."
Sarki Kuffuru ya yi dariyar mugunta ya ce, "In dai kuwa hakane, babu abinda zai sa sarauniya Rauziyya ta tafi ta barmu. Kuma lallai da kaina zan yiwa Rauziyya rakiya wajen ganin an hallaka Marganu a gaban idanuna!"
Sarki Darwazu ya yi murmushi ya ce, "Lallai nima da ni za'a je domin ganin faɗuwar wannan yaro mai karambani."
A daidai lokacin ne sarauniya Rauziyya ta farfaɗo daga wannan suma da tayi, tayi attishawa sau uku sannan idanuwanta suka buɗe a hankali.
Sarki Kuffuru, sarki Darwazu da boka Hubbazu ƙirjinsu ya soma bugawa da ƙarfi saboda ganin irin tashin da sarauniya Rauziyya. Idanuwanta sun sauya matuƙa baƙin dake cikin idanun, ya ƙarun ainun tamkar zai mamaye dukkan idanun.
Sarauniya Rauziyya ta miƙe tsaye daga inda take zaune, ta dubi su Kuffuru a hasale ta ce, "Kun gagara hallaka Marganu. Jinin Marganu shi ne abinda abin-bautana ke muradi amma kusan shekara guda a ce ban kai masa ba, lallai wannan abin kunya ne a gareni.
"Saboda haka zan yanke wannan tafiya tawa daga wannan wuri, zan je da kaina na farauto Marganu... Zan dawo gareku a duk lokacin da na kammala..."
Sarauniya Rauziyya tana zuwa nan a zancenta, waɗansu fuka-fuki guda biyu suka fito daga gadon bayanta tamkar tsuntsuwa ta fara kaɗa su tamkar zata tashi sama.
Boka Hubbazu ya ce, "Uwar matsafa! Ki dakata Marganu na isowa wannan wuri bada daɗewa ba, kuma a raye. Zamu ba ki shi kije ki yanka shi sannan ki dawo."
Rauziyya tana jin wannan batu ta juyo ta harari boka Hubbazu da waɗannan idanu nata, nan take ta fara karkarwar sanyi saboda irin ƙarfin sihirin da ya gani a cikin idanun.
Saura ƙiris sarauniya Rauziyya ta tashi sama kenan, suka ga wani bijimin sadauki ya sauƙo wannan wuri sanye da baƙaƙen tufafi irin na sadaukan Infiro.
Sadaukin na goye da wani saurayi akan kafaɗarsa wanda aka ƙullewa hannu da sawaye da murtuƙa-murtuƙan igiyoyi.
Saɓanin sadaukan Infiro da sarki Kuffuru ya samar, wannan sadauki fuskarsa a rufe take gaba ɗaya, babu yadda za'a yi mutum ya iya shaida fuskar tasa.
Sarki Kuffuru da sarauniya Rauziyya suka kalli wannan saurayi dake kan kafaɗarsa da kyau, ba wani bane illa Marganu.
Wani abin al'ajabi shi ne, sarki Darwazu yana kallon saurayi yaga ko kaɗan baya kama da Marganu.
Sarki Darwazu ɗan ƙabilar Adbenchan ne, su ne asalin tsafi. Ba kowanne irin gama-garin tsafi bane yake tasiri a kansu ba.
Boka Hubbazu wani saurayi daban yasa aljaninsa ya kamo domin ya yaudari su sarki Kuffuru su ɗauka Marganu ne.
Wannan Infiro da ya dawo da Marganu ba asalin Infiro bane, wani hadimin Hubbazu ne shiyasa ya rufe fuskarsa gaba ɗaya.
Da yake hankalin sarki Kuffuru yana kan wannan bogin Marganu da aka kawo musu, kwata-kwata bai lura da wannan ba.
Sarki Darwazu tsafi baya tasiri akansa sosai wannan yasa ya kalli wannan yaudara da boka Hubbazu ya shirya musu.
Amma sai yaja bakinsa yayi shuru bai sanar da su sarki Kuffuru ba, saboda dalilai guda biyu.
Dalili na farko shi ne idan har ya sanar dasu wannan ba yarima Marganu bane, babu abinda zai hana sarauniya Rauziyya tafiya. Idan sarauniya Rauziyya ta tafi basu san ranar dawowar ta ba, sannan dalilin da ya hana Infiro kamo Marganu zai iya janyo ajalin Rauziyya gaba ɗaya.
Dalili na biyu shi ne alaƙar dake tsakanin boka Hubbazu da sarki Kuffuru zata karye, idan kuwa wannan alaƙa ta karye waye zai nuna musu hanya, tunda babu Sheezuwa. Tabbas dole ce tasa Hubbazu ya yaudare su ta hakan, amma daga baya dole zai san yadda zaiyi ya hallaka Marganu.
Waɗannan su ne dalilan da suka sa Darwazu ya ja bakinsa yayi shuru bai tona wannan yaudara da boka Hubbazu yayi musu ba.
Waɗansu baƙaƙen hawaye masu kama da hawayen farin ciki suka zubo daga idanun sarauniya Rauziyya ta ruga da gudu ta karɓi Marganu daga hannun wannan sadauki.
Sadaukin na miƙa mata Marganu ya juya ya tashi sama, cikin gajimare ya ɓace ɓat.
Wannan abu yayi matuƙar baiwa sarki Kuffuru mamaki, ya ya za'a yi shi da hadiminsa ace ya dawo daga aikin da ya saka shi sannan baice da shi komai ba?
Amma saboda ganin yadda sarauniya Rauziyya ke farin ciki yasa Kuffuru bai ce komai ba.
Sarauniya Rauziyya ta shaƙe wannan saurayi dake hannunta wanda yake cikin siffar sadauki Marganu, saurayin ya fara kakarin mutuwa farar kumfa ta fara zubowa daga bakinsa.
Sarauniya Rauziyya tayi murmushi, wannan baƙi dake cikin idanunta ya fara sheƙi. Ta zaro harshen dake cikin baƙinta shima ya gama juyewa izuwa baƙi ƙirim ta sokawa shi wannan saurayi mai siffar Marganu a cikin bakinsa.
Nan take wannan saurayi ya yi wata irin ƙara sannan ya sandare a waje ɗaya, jikinsa ya yi laushi ƙwarai da gaske sannan ya suma.
Sarauniya Rauziyya tayi murmushi ta goya shi a gadon bayanta, ta ɗaure shi tamau da igiyar tsafi. Ta dubi boka Hubbazu cikin kallo mai cike da jinjina tace, "Nagode."
Boka Hubbazu ya ce, "Kada ki damu, yanzu kije ki yanka shi sannan ki dawo, muna wannan wuri muna jiranki..."
Sarauniya Rauziyya ta fara kaɗa waɗannan fuka-fuki nata zata tashi sama, sarki Kuffuru yayi sauri ya ce, "Nima son ganin yadda za'a yanka Marganu."
Boka Hubbazu ya ce, "Nima ina so naje na gani..." Ba don komai ya ce haka ba, sai domin yana so yaje wannan wuri inda za'a yanka wannan saurayi domin yayi wani siddabaru wanda zai hana aljani Barzas jin ɗanɗanon wannan jini.
Sarki Darwazu ya san duk abinda ke faruwa saboda haka baya so yaje wannan wuri, don idan yaje aka yanka wannan saurayi a gaban idanunsa, daga baya sarki Kuffuru da sarauniya Rauziyya suka gano wannan yaudara da aka yi abin ba zai yi masa yadda yake so ba.
"Zan jira ku a wannan wuri, domin nayi gadin wannan tubali!" inji sarki Darwazu ya nemi dabarar da zaiyi wajen ganin bai bisu ba.
Sarki Kuffuru, sarauniya Rauziyya da boka Hubbazu suka amince da wannan shawara ta sarki Darwazu, bai kamata su tafi su bar wannan wuri babu mai gadi ba.
Boka Hubbazu ya samar da wata darduma ta tsafi da shi da sarki Kuffuru suka haye kanta, suka tashi sama cikin iska. Sarauniya Rauziyya ta buɗe waɗannan fuka-fuki nata ta bi bayansu.
Sarki Darwazu ya nemi waje ya zauna a cikin wannan daji, ya shiga tunanin yadda abubuwa zasu kasance.
Sarki Kuffuru, sarauniya Rauziyya da boka Hubbazu suka ci gaba da tsala azababben gudu a cikin gajimare. Wannan saurayi mai siffar Marganu na kwance a gadon bayan sarauniya Rauziyya.
Abin ka da gawurtattun matsafa kafun kace kobo, tuni sun yi tafiya mai nisan gaske. Sarauniya Rauziyya ce akan gaba, domin duk tafi su gudu. Tamkar tsuntsuwa haka take kaɗa waɗannan fuka-fuki nata.
Lallai sarauniya Rauziyya gawurtacciyar matsafiya ce da duniya ta daɗe bata gani ba.
Kusan sa'a goma sha huɗu suna tafiya a cikin gajimare sannan suka saki fuka-fukinsu suka sauƙa ƙasa a saman wani gabjejen tsauni.
Sauƙarsu keda wuya waɗannan fuka-fuki na sarauniya Rauziyya suka koma cikin gadon bayanta, ta goya Marganu a gadon bayanta ta tunkari cikin birninta, sarki Kuffuru da boka Hubbazu suka take mata baya.
Jama'ar birninta suna ganin ta dawo ɗauke da yarima Marganu sai suka ruɗe da shewa, suka yi ɗaukar duwatsu suna jifan wannan saurayi wanda a zatonsu Marganu ne.
Sarauniya Rauziyya ko fadar birninta bata tunkara ba, ta wuce wannan gidan bauta inda gunki Barzasa yake.
Tuni wannan birni nata an gama ɗauka. Sarauniya ta dawo tare da jarumin da ya gudu lokacin da ake daf da yanka shi.
Mutane suka yi ta tururuwa suna zuwa wannan gidan bauta domin ganin yadda za'a kawo ƙarshen wannan taƙadarin jarumi wato Marganu.
Kafun ka ce me wannan, tuni wannan gidan bauta ya cika ya batse da waɗannan arnan daji.
Sarauniya Rauziyya ta kwantar da wannan saurayi akan wannan tudu wanda suka saba kwantar da mutane, idan zasu yi layya da jininsu.
Gaba ɗaya mutanen da ke cikin wannan gida suka durƙusa kan gwiwowinsu kamar yadda suka saba a duk lokacin da za'a yi yanka.
Sarki Kuffuru da boka Hubbazu suka tsaya a bayanta suna ganin abinda take aikatawa.
Boka Hubbazu yana wani irin wuridin tsafi a cikin ransa domin hana aljani Barzas jin ainihin ɗanɗanon wannan jini saboda idan ya kuskura ya bari ya ji ɗanɗanon jinin zai gano cewa ba Marganu bane, idan kuma suka gano haka tabbas tasa ta ƙare.
Sarauniya Rauziyya ta karanto wannan karatun yanka kamar yadda suka saba, ta zaro wata ƙatuwar wuƙa ta ɗaura akan wuyan wannan saurayi ta ɗaga ta kalli sama.
Idanuwanta suka kai kan dungulmin kan wannan gunki wanda har a wannan rana ba'a gyara shi ba, ta dadara wannan wuƙa a wuyan saurayin wanda a duk zatonta yarima Marganu ne.
Tsahon daƙiƙa sha biyar jini bai fito ba, duk da cewa wuyan nasa ya yanku kuwa.
Daƙiƙa sha biyar ɗin na wucewa, jini mai yawan gaske ya soma malalowa daga wuyan wannan saurayi tamkar an yanka shanu.
Rauziyya ta saita wuyansa da ƙoƙo na farko, yana cika ta saita da ƙoƙo na biyu, a haka sai da ta cika ƙoƙuna guda huɗu.
Suna gama cika ta juyota dubi su boka Hubbazu tayi murmushi ta ce, "Na gode... Tabbas yanzu ne nake da cikakkiyar damar tafiya wannan gagarumin aiki..."
Sarki Kuffuru ya yi caraf ya ce, "Ai nima mutuwar Marganu zata amfane ni ba kaɗan ba... Dama wannan saurayi ya riga ya gama rayuwarsa a duniya... Wanda ya zaɓi soyayya kam dama?"
Sarauniya Rauziyya tayi murmushi ta dubi jama'arta ta ce, "Abin bautarmu ya samu jinin 'ISRABIL' wanda ya daɗe yana nema. Nan ba da daɗewa ba, darajar wannan ƙabila tamu zai ɗagu a duniya.." A cikin yarensu tayi wannan magana.
Jama'arta suna jin haka suka ruɗe da shewa, suka yi tayi mata jinjina saboda ba'a taɓa samun gagarumar sarauniya wadda tayi suna kamarta a tarihin ƙabilar ba.
Sarauniya Rauziyya ta kai su sarki Kuffuru fadarta, suka kwana biyu suka huta.
Rannan da yammaci sai suka yi zama ta musamman domin tattaunawa akan yadda zasu gina wannan gawurtacciyar kurkuku wadda zasu tsare Barban a cikinta.
Sarki Kuffuru ya ce, "Hubbazu! Boka Sheezuwa ya sanar da mu cewa kaine wanda zaka sanar da mu inda zamu samu magini Gidr wanda zai gina mana wannan kurkuku wadda zamu kulle Barban a cikinta."
Boka Hubbazu ya yi guntun murmushi ya ce, "Gidr a wani ƙaramin yanki yake rayuwa a yankin birnin Hindu, cikin wani ƙasaitaccen birni wai shi Bahzam. Babu abinda yake tsolewa Gidr idanu idan ba dukiya ba, hakan ne yasa ya tara dukiya mai yawan gaske saboda aikinsa akwai tsada sosai.
"Gidr shi ne wanda ya gina fadar sarki Raja, fadar da ake ganin duk faɗin duniya babu wanda ta kaita ginuwa (ba wai tsaruwa ba).
"Idan muna son mu haɗu dashi dole ne muje birnin Bahzam, mu bashi kyautar dukiya mai yawan

Please Login or Register in order to submit comment