Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaya daga wannan wuri.
Ya dubi jaruma Riya ya ce da ita, "Ki koma baya faɗa da wannan matsafin yafi ƙarfinki..."
Yana gama faɗin haka sarki Dujalu ya iso inda suke tsaye, jaruma Riya ta daka tsalle gefe ɗaya ta ƙyale su su biyu.
Sarki Dujalu ya kawowa Aymanul Faris duka da wannan sanda dake hannunsa, Aymanul Faris ya ɗaga takobin Saiful Shiradu dake hannunsa ya kare wannan duka. Makaman nasu na haɗuwa a waje guda aka kwararo tsawa da walƙiya wadda tasa ruwan wannan teku yin tsiri izuwa sararin samaniya tamkar zai haɗiye wannan tsibiri.
Jaruma Riya tana tsaye a gefe, fuskarta cike da wasu-wasi gami da kwakwanto duk a lokaci guda. Tana kallon sarki Dujalu dake fafatawa da Aymanul Faris sannan tana kallon gefen da Barban ke tsaye.
Idan mutum ya kalli wanda ke tsaye a gaban Barban a cikin iska, zai cika da tsananin mamaki. Sannan mutum zai gano cewa mamakin dake kan fuskar Riya yana da asali.
Ba wani bane a tsaye a gaban Barban face sarki Dujalu wanda ke fafatawa da Aymanul Faris a lokaci guda.
Sarki Dujalu ya rabe izuwa halittu guda biyu; ɗaya yana fafatawa da Aymanul Faris, ɗayan kuma yana tsaye a gaban Barban a cikin iska suna fuskantar juna.
Fafatawar dake shirin afkuwa tsakanin sarki Dujalu da Barban ga dukkan alamu zata fi ta su Aymanul Faris ɗaukar hankali, saboda gogaggun matsafa ne guda biyu suke shirin fafatawa.
Jaruma Riya ta ma rasa wanne gumurzu ya kamata ta kalla, tsakanin na masoyinta da kuma na su Barban.
Sarki Dujalu ya zaro irin wannan sanduna nasa guda biyu ya nuna Barban da su. A wannan karon maimakon walƙiya ta bayyana, wani irin shuɗin haske ne mai tartsatsi ya bayyana akan iska ya tunkari Barban.
Idan mutum yayi duba izuwa ga inda Barban ke zaune akan wannan iska, zai ganshi zaune ya tankwashe ƙafafu sannan ya rufe idanunsa, kamar ba shi ake kawowa hari yanzu ba.
Duk duniya babu wanda ya san wannan sirri wanda Barban yake amfani dashi, amma ga dukkan alamu baya son buɗe waɗannan idanu nasa masu kama da na kyanwa.
Kafun harin sarki Dujalu ya ƙaraso inda yake, ya ɗan buɗe idanunsa ya kalli shuɗin haske mai tartsatsin, sannan ya sake rufe idanun nasa.
Wani irin koren haske mai kama da hoda ya bayyana akan iska, ya nufi wannan shuɗin haske mai tartsatsi na sarki Dujalu.
Cikin kwanciyar hankali wannan koren haske na Barban ya shige ta cikin wannan hari na sarki Dujalu, kamar ya ratsa babu. Ya nufi sarki Dujalu gadan-gadan.
Wannan hari na sarki Dujalu kuwa, a hankali ya soma dishashewa yana ɓacewa har ya gama ɓacewa gaba ɗaya.
Wannan koren haske mai kama da hoda na Barban ya wuce, kai tsaye, ya lulluɓe jikin sarli Dujalu. Dukda cewa yayi ƙoƙarin kaucewa amma sai da wannan haske ya lulluɓe jikinsa tamkar an watsa masa ruwa mai danƙo.
Abun na gama baibaye jikinsa, ya fara haske da tartsatsi kamar dai yadda harin nasa na farko ya kasance. Sarki Dujalu ya zaro idanu cikin tsananin mamaki.
Barban ya sake buɗe idanunsa ya kalli Dujalu sannan ya ƙifta su. Nan take wannan koren hoda dake jikin Dujalu ya soma zuƙar jinin jikinsa, yana ƙara haske. Lamarin da yasa sarki Dujalu ya fara kwarara uban ihu kenan sakamakon mugun azabar da yake sha.
Cikin ƙarfin hali da jarumtaka sarki Dujalu ya nuna wannan ruwan teku da sandar tsafinsa, yana mai karanto ɗalasiman neman tsari a cikin zuciyarsa.
Faruwar hakan keda wuya, waɗansu duwatsun ƙanƙara masu yawan gaske suka soma tasowa daga cikin wannan teku, suna zuwa suna lulluɓe jikinsa domin su kare shi daga sharrin wannan koren hoda na Barban.
Duk wannan abu dake faruwa Aymanul Faris bai sani ba, domin kuwa, tuni gumurzu mai zafi ya jima da afkuwa tsakaninsa da wannan sarki Dujalu ɗayan.
Tsahon wannan lokaci da suka ɗauka suna wannan fafatawa babu wanda ya yiwa ɗan uwansa koda rauni guda ɗaya. Sarki Dujalu ya cika da tsananin mamakin yadda aka yi ƙaramin saurayi kamar Aymanul Faris ya samu ƙarfin sihiri haka.
Bisa wannan dalili ya soma ƙaddamar da wani gwajin sihiri akan ruhin Aymanul Faris domin shi dai bai yarda da cewa wannan ƙarfin sihiri daga jikin Aymanul Faris yake ba.
Yanayin wannan gwaji nasa shi ne, wata ƙawanyar haske yasa ta kewaye Aymanul Faris, sannan ta ɗinga yin katan-tanwa tana kewaye Aymanul Faris kamar da'ira. Shi kansa Aymanul Faris bai san da samuwar wannan kawanƴa ta haske ba, balle yayi tunanin wani abu.
Abin mamaki lokacin da sarki Dujalu ya samar da wannan kawanƴa farin haske ne da ita, amma, daga bisani ta soma sauyawa izuwa ja-ja ja-ja kalar wuta.
Tuni a wannan lokaci waɗannan duwatsun ƙanƙara da sarki Dujalu ya ƙaddamar sun gama rufe jikinsa gaba ɗaya, kuma sun rufe wannan hoda da ta rufe jikinsa ma.
Wannan hoda na jin wannan sanƴin ƙanƙara ta soma disashewa tana shigewa cikin jikin sarki Dujalu.
Sarki Dujalu yayi murmushi mai nuna yarda da kai da kuma yaƙinin kuɓuta daga mutuwa. Shi kuma Barban saiya sake buɗe waɗannan idanu nasa ya yiwa Dujalu wani kallo sannan ya sake rufe su.
Faruwar hakan keda wuya jikin sarki Dujalu ya soma kumbura kamar ana soya masa a kasko, sarki Dujalu ya soma zare idanu cikin tsananin mamaki. Lallai wannan koriyar hoda da ta shige cikin jikinsa ita ce ta fara yi masa illa.
Sai da ya kumbura ya zamo ƙato yadda ya ninka tsahonsa da kaurinsa sau uku a baya, sannan yayi bindiga ya tarwatse. Maimakon a ga jini da tsoka sunyi fallatsi, kawai ɓacewa aka ga wannan gangar jiki tayi.
Ƙarar fashewar gangar jikin wannan sarki ce ta jawo hankalin jaruma Riya ta juyo ta dubi inda suke. Amma, sai taga wayam, babu kowa a wannan wuri face Barban shi kaɗai dake zaune akan iska.
Barban yayi murmushi domin tun kafun su fara wannan gumurzu yasan cewa wannan Dujalu dake gabansa na bogi ne, asalin Dujalu shi ne wanda ke fafatawa da Aymanul Faris.
Barban ya taho a hankali akan iska yazo daf da jaruma Riya ya tsaye, sannan ya sauƙo ƙasa bisa turɓayar wannan tsibiri yazo kusa da jaruma Riya ya tsaya.
Cikin tsananin mamaki Riya ta kalle shi daga sama har ƙasa. Barban na sanƴe da doguwar riga fara mai bayar da haske da sheƙi, gashin kansa dogo ne domin ya zubo har kan gadon bayansa. Idanuwansa kuma suna bayar da koren-haske mai ɗaukar idanu.
A wannan siffa da Barban yake ciki, jaruma Riya gagara kallon fuskarsa tayi saboda tsananin kwarjinin sa.
Jaruma Riya zata iya rantsewa da ƙololuwar abin rantsuwarta, babu halittar da zata kai Barban kwarjini a wannan zamani. Saboda idan tana kallonsa tamkar ruhinta zai tarwatse haka take ji.
"Kalli abin mamaki a can wurin," inji Barban. Abin mamaki wannan muryar tasa tamkar wani umarni ake sauƙowa jaruma Riya daga mai ikon da bata isa ta bijirewa ba.
Cikin biyayya ta juya inda ya nuna mata. Wani gagarumin abin al'ajabi ne ke faruwa.
Sarki Dujalu suka gani durƙushe a gaban Aymanul Faris cikin wani salo na nuna mubaya'a bisa gwiwowinsa guda biyu, Aymanul Faris na tsaye a gabansa riƙe da takobin Saiful-Shiradu da hannuwansa guda biyu.
"Wannan shi ake kira ƙarfin ruhin Samudul Ansari. Duk duniya babu wanda ya isa ya kalli ƙarfin wannan ruhi, ba tare da ya faɗi yayi biyayya ba. Amma, akwai mutane ƙalilan da zasu iya bijire masa. Sarki Dujalu ya yiwa Aymanul Faris irin gwajin da matsafa keyi wajen ganin ƙarfin ruhin mutum.
"Tabbas tsafin Dujalu ya nuna masa wane ne asalin TAU'RIN don haka dole ne yayi mubaya'a, idan ba haka ba ruhinsa zai iya tarwatsewa." Barban na gama faɗin haka suka tunkari inda su Aymanul Faris da sarki Dujalu suke.
"Ka karɓi mubaya'ata ya kai TAU'RIN?" shi ne abinda suka ji sarki Dujalu ya roƙi Aymanul Faris.
Cikin tsananin mamaki da rashin fahimta Aymanul Faris ya ɗaga kai ya kalli Barban, kamar yana so ya tambaye shi abinda ya kamata yayi.
Barban ya gyaɗa masa kai alamun ya karɓi wannan mubaya'a. Aymanul Faris yasa hannunsa guda ya dafa kafaɗar sarki Dujalu. Nan take sarki Dujalu yaji wani sanƴi a cikin ransa.
Wato, shi Dujalu a cikin tsofaffin mayaƙan ma, shi na dabam ne. Babu irin binciken da baiyi a duniya ba akan abubuwan da suka faru.
Dukda cewa bai rayu a zamanin sarki Samudul Ansari ba, amma, yana daga cikin mutane ƙalilan da suka saurari cikakken tarihin sarkin. Saboda wannan dalili yasan me ake nufi da TAU'RIN sarai.
Sarki Dujalu ya miƙe ya fuskanci Aymanul Faris sosai ya ce, "Nagode. Tabbas zan kasance daga cikin mutanenka daga wannan lokaci..." Kafun ya ƙarasa rufe bakinsa su Barban suka ƙaraso wannan wuri.
Ikon dake tashi a jikin Barban ya bugi jikinsa, yasa dolensa ya nutsu yayi shuru.
Jikin sarki Dujalu na karkarwa da razana ya dubi Barban da su Aymanul Faris ya ce, "Bari na samar mana da tanti domin ina son tattaunawa da kai, ya kai wannan babban matsafi. Idan baza ka damu ba?"
Barban na jin haka yayi murmushi ya tafa hannayensa sau biyu, take wani ƙaramin tanti kore ya bayyana.
"Kafun mu shiga cikin wannan tanti, je ka ɗauko mana wannan sulken yaƙi, ka kawowa wannan yarinƴa abinda mahaifinta ya bar mata." inji Barban. A wannan siffa idan Barban ya yiwa mutum magana, to, kawai umarni ne wanda koda duk duniya zasu taru su hana mutum aiwatarwa, babu abinda zai hana shi yi. Saboda gani zaiyi idan baiyi ba, kamar ya gayyatowa kansa mutuwa ne.
A guje sarki Dujalu ya ruga cikin wannan gidan tarihi zai ɗauko wannan sulke.
"Ya shugaban mu, dan ALLAH ko zaka iya yi mana bayanin wannan siffa da ka koma mai ban al'ajabi?" Aymanul Faris da jaruma Riya suka tambayi cikin haɗin baki.
"Hmm," Barban ya yi guntun murmushi. "Ku jira Dujalu ya dawo domin shima yanzu ya miƙa wuya." Yana rufe bakinsa da ƴan daƙiƙu Dujalu ya dawo wannan wuri a guje a hannayensa biyu yana riƙe da wata rigar yaƙi ta sulke.
Wannan sulke na da ban al'ajabi. Anyi masa tsarin riga gajeruwa mai zane-zanen hotunan mutum-mutumi mayaƙa masu yawan gaske ta bayansa. Sannan ta gaba kuma hoton kan zaki ne wanda ya wangame bakinsa, an kewaye kan zakin, da rubuce-rubucen ɗalasimai.
Idan mutum bai san wannan sulke ba, zaiyi tsammanin gama-garin sulken yaƙi ne.
Sarki Dujalu na ƙarasowa wannan wuri ya zube ƙasa a gaban Barban sannan ya miƙa masa wannan sulke.
Barban ya karɓi wannan sulke yayi murmushi sannan ya miƙawa jaruma Riya.
Idanun jaruma Riya sharkaf da hawayen farin ciki ta karɓi wannan sulke, ta fidda wanda ke jikinta sannan ta saka shi.
Wannan sulke ya zauna a jikin jaruma Riya, kuma ya dace da yanayin jikin nata tamkar dama anyi shi ne dominta.
Jaruma Riya ba tai kama da kowa ba face GAWURTACCIYAR MAYAƘIYA wanda kallonta kaɗai ya isa ya tarwatsa ƙaramar runduna.
Aymanul Faris ya yi murmushi ya matso kusa da ita, ya tayata murnar samun wannan sulke na mahaifinta.
Barban ya yi murmushi ya basu umarnin shigewa cikin wannan tanti gaba ɗayansu, domin muhimmiyar tattaunawa. Nan take duk su huɗun suka tunkari wannan tanti.
****
Yau *15/12/2022*
Babi na gaba zaizo *17/12/2022* da yaddar Allah.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 58: *Dabbobin Daji*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
UMAR SANGARU
*
~Ɓangaren su yarima Marganu
*
"Haba dole nayi mamaki mana," inji Marganu. "Lallai ya kamata na koma cikin wannan daji, na hallaka dukkanin waɗannan dodanni, saboda barin su a raye zai iya janƴo min matsala a gaba."
Tsoho Aydenlik ya gyaɗa masa kai ya ce, "Shin waɗannan dodanni cikin ramuka suka koma, ko kuma cikin kogunan duwatsu suka shiga?"
Marganu ya ce, "Wani ƙaramin tsuntsu ne yazo ya wuce ta saman wannan daji yana wani irin ihu, wanda na ji shi har cikin raina. Jin ihun wannan tsuntsu yasa dukkanin waɗannan dodanni tserewa daga cikin dajin. Bansan ina suka tafi ba, amma fuka-fuki suka cire suka yi ta tashi sama."
"Kash," tsoho Aydenlik ya girgiza kai. "Tabbas saman asalin tsaunin da suke rayuwa suka koma. Babbar matsalar ita ce daga wannan wuri zuwa wannan tsauni nasu tafiya ce mai tsahon..."
Marganu yayi murmushi ya dakatar da tsoho Aydenlik da hannu ya ce, "Babu buƙatar nasan inda suke, ai wuya suka gani, yasa suka gudu daga wannan daji."
Yana gama faɗin haka ya fiddo abinci daga cikin jakar guzurinsa ya fara ci, gimbiya Firziyya tayi saurin matsowa gabansa itama ta saka hannunta a cikin abincin nasa ta fara ci.
Marganu ya ɗago kansa yayi mata wani kallo, amma bai hanata ba suka ci gaba da cin wannan abinci har suka ƙoshi.
Marganu ya miƙe tsaye ya fita daga cikin wannan tanti yana tafiya da ƙyar sakamakon gajiyar dake jikinsa. Cikin sauri Aydenlik da Firziyya suka bishi wajen wannan tanti.
Suna fitowa suka zauna a gaɓar wani ƙaton dutse suka saka wani ƙaton rami a gaba wanda ya cika da korayen bishiyoyi gwanin sha'awa.
"Tsahon wanne lokaci zamu ɗauka a wannan wuri muna jiƴƴar jikin mu." Marganu ya tambayi tsoho Aydenlik.
Aydenlik yayi guntun murmushi ya ce, "Kaine shugaban mu. Duk hukuncin da ka yanke da shi zamu yi amfani."
"Hmm," Marganu yayi murmushi ya dubi Firziyya. "Gimbiyata wacce shawara kika yanke mana?"
Cikin tsananin jin daɗi Firziyya tayi murmushi ta ce, "Ina ganin mu zauna a wannan wuri har zuwa sa'adda zamu ji ƙarfin jikinmu saboda bamu san irin bala'in da zamu tarar a dazuzzukan dake gaba ba. Ko ya ka gani?"
"Wannan shi ne hukuncin da muka yanke, wannan ita ce shawarar da muka tsayar." inji Marganu.
Yana gama faɗin haka ya samar da wani madubin tsafi mai tsananin haske. Madubin nasa ya fara nuno abubuwan dake faruwa a dukkanin faɗin duniya.
A halin yanzu Marganu gogaggen matsafi ne wanda ke sarrafa aljanin da yafi kowanne aljani sarrafa haske, don haka samar da hatsabibin madubin tsafi a wajensa ba wani abu bane.
Kai tsaye Marganu ya ɗan taɓa hoton dake nuna birnin Hirtoliya, wato birnin da mahaifinsa yake mulki a da wanda ya kamata ace yanzu shi ne akan karagar birnin.
Madubin ya ƙara girma ya fara nuna abubuwan da ke faruwa a birnin Hirtoliya. Aydenlik da Firziyya suka matso kusa suna kallon abinda ke faruwa.
Tun bayan wannan mummunan farmaki da sarki Kuffuru ya kaiwa birnin Hirtoliya da tsakiyar dare, gidaje da yawa sun ruguje, rayuka masu yawan gaske sun salwanta, anyi asarar dukiya mai tsananin yawan gaske.
Tsahon wannan lokaci da suka shafe suna ta ayyukan gyara gidajen da suka rushe ne da kuma binne gawarwakin da suka mutu.
Abinda ya farantawa Marganu rai shi ne, basu yi kuskuren ɗaura sabon sarki a wannan birni ba. Wazirin sarki Ratanam aka baiwa riƙo kafun ayi zama na musamman.
Marganu yayi murmushin takaici ya sake shafan wannan madubin tsafi da hannunsa na hagu. Nan take wannan madubi ya nuno musu abinda ke faruwa a ɓangaren su sarki Kuffuru.
Gimbiya Firziyya tana ganin mahaifinta ta ji wani azababben baƙin ciki ya rufeta.
Abin mamaki, ba'a nuno musu abinda ya faru daga fitowar su sarki Kuffuru ba. Abinda kawai aka nuna musu shi ne barin su sarki Kuffuru wannan sansani da suka yada zango a cikinsa.
Don haka basu ga lokacin da sarki Kuffuru ya ƙaddamar da waɗannan sadaukai jinin Infiro ba. Tabbas sarki Kuffuru yana tare da gawurtattun bokaye waɗanda suke ɓoye dukkanin shirye-shiryen sa.
Marganu na ganin sauyin yanayi a fuskar gimbiya Firziyya ya shafi wannan madubin tsafi da hannunsa na hagu, nan take hoton komai ya ɗauke.
Cikin kulawa da soyayya ya dafa kafaɗar Firziyya ta ɗago kanta ta kalle shi, fuskar ta sharkaf da hawayen baƙin ciki.
"Kiyi haƙuri. Ubangiji ya ba ki mahaifi wanda yafi kowa son kansa da abinda zuciyarsa ta raya masa. Idan kika taimaka muka kawar da shi, nayi alƙawarin sadaukar da rayuwata domin ki." inji Marganu cikin kulawa.
"Ka sa a ranka tamkar na taimaka an kawar da shi ne." Firziyya ta ce cikin sheshsheƙa.
Marganu ya yi murmushi ya dubi Aydenlik ya ce, "Wai shin kana riƙe da lissafin kwanakin da muka shafe muna wannan tafiya kuwa? Na ƙosa naga mun isa garin Temisa domin ɗauko takobin Tarwatsa-komai."
Aydenlik ya ɗan yi shuru yana tunani, kafun daga bisani ya amsa. "Ina tunanin kamar makonnin mu biyu muna tafiya fa?"
"Lallai ko akwai sauran tafiya a gaban mu, tsahon wata uku Isika ya ce fa." inji Marganu.
"In dai kuwa haka ne bai kamata mu ɓata lokaci mai tsaho a cikin wannan daji ba." Firziyya ta ce.
Haka dai suka ci gaba da tattaunawa a wannan wuri har magariba ta kawo kai.
Daga wannan rana su Marganu suka ci gaba da zama a cikin wannan daji suna jiƴƴar jikinsu har tsahon mako guda sannan suka gama warwarewa. Washe gari da sassafe Marganu ya basu umarnin ci gaba da tafiya a cikin waɗannan dazuzzuka.
Suna gama kimtsawa suka danna kai, izuwa cikin wannan daji. Har suka fita daga cikinsa suka shigo cikin wannan daji wanda Marganu ya fafata da dodanni ƴan ƙabilar Sedusa.
Abinda yayi matuƙar basu mamaki shi ne tsahon wannan lokaci da suka ɓata a cikin wancan daji, ya kamata a ce waɗannan dodanni sun ruɓe sun fara zamowa ƙasa, tunda sun riga sun zama matattu.
Amma gawarwakin waɗannan dodanni na kwankkwance a ƙasa, babu abinda ya same su. Suna nan a yadda suke, tamkar a wannan rana aka kashe su. Ko wari basu fara ba balle su ruɓe.
Kai tsaye suka wuce wajen ɗaya daga cikin gawarwakin dodannin, Aydenlik ya ɗan gudanar da gajeren bincike akan wannan gawa. Ɗan gajeren lokaci sannan ya juyo ya dubi Marganu.
"Kamar dai yadda na faɗa maka, waɗannan dodanni ɗalasimin-haske baya tasiri akan su. Lallai bayan mun gama kawar da abokan gabar mu, yana da kyau muje har tsaunin da suke rayuwa su ma mu ƙarar da su."
Marganu ya gyaɗa cikin amincewa sannan ya basu umarnin wucewa cikin daji na biyu. Marganu na tafe a gaba, Firziyya a gefensa, shi kuma Aydenlik yana biye dasu a baya, yana dube-dube domin tabbatar da tsaro.
Tsahon rabin sa'a suna ta tafiya sannan suka shigo cikin wannan daji na biyu.
Wannan daji na biyu a cike yake da bishiyoyi dogwaye da ƙanana, sannan akwai kwazazzabai da ƙoramu masu yawan gaske a cikinsa. Akwai tsaunika a cikinsa amma jefi-jefi, sannan akwai ramuka a cikinsa masu yawan gaske.
Marganu, Firziyya da Aydenlik suka tsaya a farkon wannan daji suna ta nazarinsa. Bishiyoyi dogwaye da gajeru. Kwazazzabai da ƙoramai. Tsaunika jefi-jefi. Ramukan dabbobin daji.
"Me kuka fahimta dangane da wannan daji?" Marganu ya tambaye su.
Gimbiya Firziyya ta matso kusa da shi ta ce, "A fahimta ta ni dai, wannan daji duk yadda aka yi akwai dabbobin daji masu yawan gaske a cikin sa. Duba da cewa akwai bishiyoyi da ƙoramai da ramuka a cikin wannan daji. Birirruka da damisa suna rayuwa akan bishiyoyi. Zakuna da kuraye suna rayuwa a cikin ramuka."
Aydenlik ya gyaɗa kai ya ce, "Kwarai kuwa. Nima na amince da wannan fahimta nata."
Marganu ya yi murmushi ya ce, "Kowa ya fara shiri," yana faɗin haka ya fiddo wannan takobi ta haske tasa.
Tsoho Aydenlik ya ƙaddamar da waɗannan duwatsu guda huɗu dake yawo akan hannunsa. Gimbiya Firziyya ta zaro zabga-zabgan takubbanta guda biyu.
Cikin yarda suka fara tafiya a cikin wannan daji. Taku ɗaya... Taku biyu... Taku uku... har taku arba'in, sannan suka ji yanayin wannan daji ya soma sauyawa.
Ganƴaƴen bishiyoyi suka soma zubowa ƙasa, ƙasa ta soma girgiza, ƙura ta soma fitowa daga cikin waɗannan ramuka, ruwan kwazazzabai da ƙoramu suka soma fantsama izuwa sama.
Su Marganu suna ganin haka suka gyara tsayuwa a inda suke, sannan kowa ya gyara riƙe makamin yaƙin dake hannunsa.
Tsahon daƙiƙu arba'in kacal, waɗansu irin damisa suka fara bayyana a saman waɗannan bishiyoyi, jibga-jibgan kuraye da zakuna suka soma firfitowa daga cikin waɗannan ramuka, kadoji da macizai suka fara fitowa daga cikin waɗannan kwazazzabai da ƙoramu.
Marganu ya ɗan haɗe fuska ya dubi su Aydenlik cikin tsananin mamaki. Waɗannan dabbobi dake ta bayyana a cikin wannan daji basu da adadi, tamkar ƙwari ko kuma tururuwa haka suke ta bayyana.
Marganu ya san cewa komai ƙarfinka da ƙarfin shirinka, yana da tsananin wahala kayi nasara akan abokan gabar da suka fika yawa nesa ba kusa ba. Saboda ai ance SARKIN YAWA...
"Kowa ya zaɓi kason da zai ɗauka a cikin waɗannan dabbobin dajin... Na kan bishiya ko na doron ƙasa ko kuma na cikin ruwa?" Marganu ya tambaye su.
Aydenlik ya ce, "Duk hukuncin da ka yanke da shi zamu yi aiki shugaba."
A wannan lokaci waɗannan dabbobi sun gama kewaye su a tsakiya, idan ka hango su daga nesa zaka ɗauka ƙananun tamaru aka jefa a tsakiyar garken shanu.
Marganu ya ɗan yi gajeren tunani na ƴan daƙiƙu sannan ya dubi Aydenlik ya nuna masa sama da hannunsa guda, sannan ya dubi Firziyya ya nuna mata ruwan waɗannan kwazazzabai.
Aydenlik yana iya tashi sama sannan yana jifa da waɗannan duwatsu nasa, Firziyya tana da takubba guda biyu masu tsananin kaifi da tsini. Wannan shi ne tunanin da Marganu yayi ya basu wannan umarni.
Marganu ya ƙaddamar da shuɗin haske a matsayin ƙarfen wannan takobi tasa, yayi kan waɗannan dabbobin daji dake firfitowa daga cikin ramuka wato kuraye da zakuna.
Kimanin kuraye da zakuna guda dubu arba'in suka yiwo kansa da gudu, sawayensu na kartar ƙasa suna haifar da ƙura, suna yin wani gurnani wanda jin sa kaɗai ya isa ya firgita mutum.
Marganu yayi murmushi ya kaiwa waɗanda ke ɓangaren gabas sara da wannan takobi tasa ta haske. Nan take shuɗin haske mai tartsatsi ya fita daga tsinin wannan takobi yayi kansu da gudu.
Wani abin al'ajabi shi ne tartsatsin na ƙara gaba yana ƙara girma da haske, yana zuwa ya shige ta cikin waɗannan dabbobin daji tamkar babu abinda yayi musu. Suka ci gaba da gudu suka sake tunkaro Marganu.
Kafun su iso inda yake da tazarar taku arba'in, jikkunansu suka soma kumbura suna bindiga suna bin iska. Maimakon a ga jini da tsoka sunyi fallatsi, kawai aka ga jikin nasu yana ɓacewa.
Cikin murmushi da yarda da kai Marganu ya sake kaiwa waɗanda ke ɓangaren yamma, kudu da arewa irin wannan sara. Kafun kace me wannan tuni ya hallaka waɗannan dabbobi guda dubu arba'in ɗin nan.
Idan mutum ya dubi yawan dabbobin da suka rage da kuma waɗanda ke shirin afkowa sadauki Marganu, mutum zai iya cewa cikin kaso ɗari Marganu ya kashe kaso goma kawai. Saboda tsananin yawan waɗannan dabbobi.
Marganu yayi murmushin mamaki ya sake ƙaddamar da wani haske mai ja-ja ja-ja a matsayin ƙarfen wannan takobi, ya kai sara dukkanin ƙusurwowin wannan daji.
Nan take wasu dunƙulallun wuta daga sama suka soma dirowa cikin garken waɗannan dabbobin daji. Kamar nakiya ake fasawa haka waɗannan dunƙulallun haske suka soma fallatsa a tsakiyar garken dabbobin, ana jifa da gawarwakin su nesa.
Wannan hari da Marganu ya ƙaddamar babban hari ne, irinsa ake ƙaddamarwa a tsakiyar dubbanin mayaƙa musamman idan aka ga yaƙin babu ci.
Kafun kace kobo, tuni waɗannan dabbobi dake firfitowa daga cikin ramuka sun gama zamowa gawarwaki gaba ɗayansu. Babu su, babu gawarwakin su wannan hari na Marganu ya gama da su gaba ɗaya.
Marganu ya mayar da takobinsa

Please Login or Register in order to submit comment