Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sarakuna suka miƙe tsaye sannan suka fito daga cikin falon, suka tunkari inda sojan ke tsaye.
Gauhan ya karɓi wannan wasiƙa ta raddi, ya karanta abinda ke cikinta sannan ya fassarawa waɗannan sarakuna ta yaren da zasu gane.
Koda waɗannan sarakuna suka ji abinda ke cikin wannan wasiƙa sai suka fara tsuma, saboda tsananin fusata.
Ɗaya daga cikinsu ya zare takobinsa ya sare wannan soja da ya kawo wannan wasiƙa.
Cikin gaggawa suka fice daga cikin wannan fada, suka tunkari babban sansanin mayaƙansu wanda ke can bayan wannan gari.
Idan mutum ya kalli wannan sansani daga nesa, zai cika da tsananin mamaki saboda dakaru ne birjik keta ayyuka dabam-dabam.
Mutum zaiyi kwakwanto anya waɗannan dakaru ne suka gwabza yaƙi yan-kwanaki da suka shuɗe kuwa?
Saboda yawansu bai ragu koda kaɗan ba.
Koda yake idan mutum yayi duba izuwa wannan yaƙi da suka gwabza a kwanakin baya, zai fuskanci cewa, kawai ta-more suka yi.
Ko ɗaya daga cikinsu waɗannan sarakuna guda biyar basu sami damar hallakawa ba, saboda tsananin hatsabibancinsu da kuma yadda suka shiryu tun kafun su zo.
Sarakunan suna isowa suka haye saman wata doguwar ganuwa, sannan suka busa wani ƙaton ƙaho wanda yasa dukkan waɗannan mayaƙa dawowa hayyacinsu sannan suka jeru a ƙasa domin sauraron umarni.
Sarki Mahrus ya ce, "Mutanen birnin Ilam sun bijirewa sulhun da muka kai musu.
"Su da kansu sun nemi damar gwabza yaƙi da mu.
"Saboda wannan dalili gobe da safe, zamu afka cikin wannan gari nasu.
"Muna so a kawo mana kan Samudul Ansari da kan sarauniya Arya. Wannan shi ne umarnin mu."
Mayaƙa suka yi kururuwa dama abinda suke son ji kenan, sun shigo wannan daula ne domin takubbansu su sha jini.
Nan take suka fara fiddo makaman yaƙinsu daga cikin wuraren ajiya.
Waɗanda suka lalace a jefar dasu, waɗanda suke buƙatar kuɗa kuma aka fara kuɗa su.
Kafun gari ya waye gagarumar rundunar Gorgon tare da ma'abota Bankai guda goma sun gama kimtsawa.
Waɗannan sarakuna guda biyu da kuma Gauhan Ansari, suka shige gaba suka jagoranci rundunar suka tunkari filin yaƙin Nayesh.
***
A filin yaƙin Nayesh gari ya wayewa su Samudul Ansari. Sun gama hallara dukkaninsu, a wannan rana za'a yi ta ta ƙare.
Samudul Ansari da Zarifa na tsaye a gaban wannan runduna.
Sarkin yaƙi da sauran manyan mayaƙa na wannan ƙasa, suna tsaitsaye a bayansu.
Ita kuwa sarauniya Arya tana tsaye acan saman wani dogon gini a can baya, tana hango abinda ke faruwa.
Samudul Ansari yayi shiga ta yaƙi mai tsananin kwarjini.
Babu riga a jikinsa amma akwai wani gajeren wando a kunkuminsa wanda ya tsaya iya gwiwowinsa kawai.
Yana rataye da Saif-Al-Barzaƙ a gadon bayansa.
Idanuwan Samudul Ansari na bayar da kwarjini, kamala, nutsuwa da tsantsar jarumtaka.
Zarifa na tsaye a gefensa, ita ma tayi shiga ta yaƙi mai matuƙar ban al'ajabi.
Sauran mayaƙan su kuma, sun yi shiga ta fararen tufafi gaba ɗayansu.
Tsahon ɗan lokaci suna tsaitsaye, kafun su hango mutum kwance akan doki na tunkaro su.
Cikin gaggawa Zarifa taje ta riƙo linzamin dokin ta ƙaraso.
Koda aka sauƙe wanda ke kwance akan dokin, sai suka gane cewa ba wani bane illa wannan manzo da aka aika da wasiƙar raddi.
Zuciyar Samudul Ansari ta soma tafarfasa saboda tsananin baƙin ciki da fusata.
"Mu bamu kashe musu manzon da suka aiko ba, amma su sun kashe mana namu!" inji Samudul Ansari.
Kafun ya rufe bakinsa suka hango fai-fan haske masu tsananin yawan gaske na tunkaro su.
Waɗannan fai-fai na haske, su ne saran Bankai-mai-tafiya.
Tabbas idan suka iso rundunar su Samudul Ansari ba ƙaramar ɓarna zasu yi musu ba.
"Ina da magana..." inji wannan ruhi.
Samudul Ansari na jin haka ya zaro takobinsa ta Saif-Al-Barzaƙ ya ce, "Ina jinka..."
Ruhin ya ce, "Saif-Al-Barzaƙ zata iya kare kowanne hari na takobin Bankai, koda kuwa takobin ta kai mataki na casa'in da tara ne..."
"Ba wannan nake so naji ba, ta ya ya zan kare mutanenmu daga wannan hari dake tunkaro su yanzu?" inji Samudul Ansari.
Ruhin na jin haka, ya miƙa hannunsa guda ya damƙi ƙarfen takobin Saif-Al-Barzaƙ.
Wani baƙin hayaƙi ya ɓulɓulo daga hannunsa ya shige cikin ƙarfen takobin.
"Saran takobin Saif-Al-Barzaƙ guda ɗaya mai tafiya, zai tarwatsa dukkan waɗannan ƙananun hare-haren." inji wannan ruhi.
Kada dai a manta cewa, irin wannan tattauna dake gudana tsakanin Samudul Ansari da wannan ruhi babu mai jin ta face su biyu.
Samudul Ansari ya gyaɗa kai a hankali, sannan ya sari iska da Saif-Al-Barzaƙ da ƙarfi.
Nan take wani ƙaramin fai-fai mai baƙin haske ya fice daga tsinin takobin, ya tunkari waɗannan fai-fai da ma'abota Bankai suka aiko.
Abin mamaki ficewar wannan fai-fai daga tsinin takobin Samudul Ansari bai wuce girman tafin-hannu sau uku ba.
Amma yana ƙara gaba, yana ƙara girma.
Kafun ya iso inda fai-fan ma'abota Bankai yake, ya kusan girman da'ira mai kamu metan.
Saran ya ratsa ta cikin waɗannan ƙananun fai-fai na ma'abota Bankai sannan ya wuce.
Nan take dukkansu suka bi iska suka tarwatse.
A wannan rana sun haɗu da ubansu.
Wannan shi ne karo na farko da aka samu takobi wadda ta iya tasiri akan harin Bankai-mai-tafiya, tun lokacin da aka ƙirƙiro Bankai.
Fai-fan da Samudul Ansari ya aika ya ci gaba da tafiya, har ya riski rundunar su Gauhan wanda suka kusa isowa wannan filin yaƙi.
Cikin tsananin razana da zafin nama, Gauhan da waɗannan sarakuna guda biyu suka daka tsalle daga kan dawakansu suka kaucewa wannan sara.
Saran ya ratsa ta cikin dakarunsu, yayi ajalin da yawa daga ciki sannan ya raunata wasu, da ƙyar aka sami waɗanda suka tsere masa.
Waɗannan sarakuna guda biyu suna haki, suka dubi Gauhan suka ce, wannan wanne irin hari ne?
"Saif-Al-Barzaƙ aka turo domin tai mana sallama!" inji Gauhan.
"Fatan dai, kun taho da manyan makaman yaƙi waɗanda zasu kare mu daga sharrin wannan takobi?" ya ƙara da cewa.
Sarakunan guda biyu suka haɗe fuska a tare sannan suka zaro asalin takubbansu na Bankai.
Sarki Mahrus na riƙe da takobin Bankai mai mataki na arba'in da shida, shi kuma ɗaya sarkin wanda ke mulkin birnin Mesa yana riƙe da takobi mai mataki na arba'in da tara.
A wani salo na mayar da martani, su ma suka sari iska da waɗannan takubba dake hannunsu a tare.
Fai-fan iska irin wanda aka jima ba'a gani ba, suka fice daga takubbansu suka tunkari rundunar su Samudul Ansari dukda cewa basa ganin rundunar kuwa.
Fai-fan suna tafiya suna ƙugi suna tarwatsa dukkan wani abu wanda ya shigo gaban su.
Rundunar waɗannan sarakuna ta sake haɗuwa a waje guda suka ci gaba da tafiya.
Samudul Ansari na tsaye ya hango waɗannan fai-fai dake tafe acan nesa, albarkacin idanuwan wannan ruhi.
Samudul Ansari ya yi murmushi sannan ya caka takobin Saif-Al-Barzaƙ a cikin ƙasa.
Wata irin katanga mai girma da faɗin gaske ta bayyana acan kusa da waɗannan fai-fai da suke tunkaro su, fai-fan suna dukan jikin wannan katanga suka zube ƙasa.
Daga bisani wannan katanga tayi girgiza ta ɓace ɓat.
Ya kamata a san girman Bankai mai matakin arba'in zuwa sama.
Bankai mai mataki na arba'in zuwa sama, iyakacin sarakunan daular Gorgon ne keda mallakinta.
Ba wai rundunar mayaƙa ba, komai girman gari da yawan jama'arsa, saran wannan takobi yana iya hallakar da su.
Amma yau ga shi, cikin kwanciyar hankali Samudul Ansari ya hana waɗannan sara ƙarasowa inda yake.
Wai nan ma, ba ma sara guda ɗaya ba, sara guda biyu!
Sannu-a-hankali rundunar su Gauhan ta ƙaraso wannan wuri.
Koda suka yi arba da yawan dakarun su Samudul Ansari sai suka bushe da dariyar mugunta.
Saboda sun ninka su a yawa sau uku ko sau huɗu.
Babbar barazanar su a wannan yaƙi shi ne Samudul Ansari.
To, amma ai ance sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi.
Gauhan, sarki Mahrus da sarkin Mesa suka shigo tsakiyar wannan fili suka tsaitsaya.
Sarkin Mesa ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, "Ya ku jama'ar wannan gari, kuyi sani cewa kun tafka babban kuskure da kuka ƙi bin umarnin mu.
"Ku daina tunanin za ku samu nasara akan mu, wannan babban kuskure ne.
"Tabbas kun fusata mu, kun nuna mana cewa bamu kai ba.
"Saboda haka, ba iya mamaye wannan gari naku zamuyi ba face ruguza shi.
"Sai mun kashe kowa, mun ƙona komai, tabbas wannan gari naku sai ya zamo turbaya..."
Sarkin na zuwa nan a zancensa yayi kururuwa ya ɗaga takobinsa sama, rana ta doki ƙarfenta take ta fara fitar da koren-launi.
Mayaƙan dake bayansu suka ruɗe da shewa.
Nan take shi da su Gauhan suka juya dawakansu suka koma da baya.
"Ina da magana..." inji wannan ruhi.
"Ina jin ka..." Samudul Ansari ya bashi amsa.
"Zan kawo maka dukkan tattaunawar da zata gudana tsakanin su Gauhan akan dabarun yaƙi da zasu yi mana.
"Saboda bana so mu ɓata lokaci mai yawa akan wadannan ƙananun sarakunan!" inji wannan ruhi.
"Da kyau... Hakan yayi..." inji Samudul Ansari.
Gauhan da waɗannan sarakuna suna komawa cikin rundunarsu suka tsaitsaya suna shawara akan dabarun yaƙin da ya kamata su ɓullo dasu wajen samun nasara.
"Koda zamu kai musu hari guda ɗari na Bankai-mai-tafiya, ba za su yi musu komai ba... Saboda wannan takobi zata kare su daga sharrin namu...
"Wacce dabara kuke ganin ya kamata mu ɓullo musu da ita, wadda zata bamu damar hallaka su cikin sauƙi.
"Tun da mun fi su yawa, sannan mun fi su ƙarfi, abin dogaronsu guda ɗaya shi ne Samudul Ansari..."
Waɗannan sarakuna suna jin abinda Gauhan ya faɗa suka yi shuru suna ta tunani.
Tsahon ɗan lokaci kamar ba za su ce komai ba, daga can sai sarki Mahrus ya numfasa ya ce.
"Mu rarraba dakarun mu izuwa kaso huɗu. Kaso na farko zasu tsaya a ɓangaren gabas, kaso na biyu ɓangaren arewa, kaso na uku ɓangaren yamma, kaso na huɗu ɓangaren kudu.
"Kowanne kaso zamu haɗa su da ma'abota Bankai guda goma.
"Waɗannan kaso guda huɗu zasu yi ta haɗawa abokan gaba muggan hare-hare a lokaci guda.
"Abin dogaron nasu guda ɗaya ne, kuma bai isa ya kare su a lokaci guda ba..."
Sarkin Mesa ya dubi sarki Mahrus Gorgon ya ce, "Tayaya haka zata yiwu bayan gaba da gaba za'a gwabza wannan yaƙi?"
Sarki Mahrus ya yi guntun murmushi ya ce, "Wannan shi ake kira dabarar yaƙi samfuri na uku.
"Da zarar an haɗu da juna a tsakiya, abinda rundunar mu zata mayar da hankali akansa shi ne, wannan dabarar yaƙi..."
Gauhan ya yi murmushi ya ce, "Wannan dabara taka, babu ja-in-ja tayi. Da ita zamuyi amfani a wannan yaƙi, kuma dole zamu sami nasara.
"Bayan rundunar mu ta gama kewaye abokan gaba... Ni da ku zamu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu yaƙi Samudul Ansari.
"Komai ƙarfinsa, idan muka haɗu a waje guda zamu iya kashe shi..."
****
Advertisment: Follow/Like MATSAFAN DUNIYA littafin yaƙi.
****
Yau *11/03/2023*
Babi na gaba zaizo *13/03/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 97: *Wane yaro, sai dai babansa*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
U~M~S
*
Duk wannan tattaunawa da ta gudana tsakanin Gauhan Ansari da waɗannan sarakuna guda biyu akan dabarar yaƙi samfuri na uku, Samudul Ansari yana ji. Wannan na daga cikin manyan amfanin wannan ruhi, ɗauko magana daga nesa ya kawowa ubangidansa.
"Ta ya ya zamu kare mayaƙanmu daga wannan dabarar yaƙi samfuri na uku, sannan mu kare kanmu daga hare-haren da zasu aiko mana. Tun da sun ce zasu haɗa kai su yaƙe mu?" Samudul Ansari ya tambayi wannan ruhi.
"Kayi duba izuwa bayanan Saif-Al-Barzaƙ, sakin-layi na sha-biyu." inji wannan ruhi.
Samudul Ansari yana jin abinda ruhin ya ce, yayi shuru yana tunani izuwa lokacin da ya karanta wannan littafi mai ɗauke da bayanan wannan takobi wadda Nurbas ya bar masa.
Tsahon daƙiƙu yana tunani kafun ya tuno abinda aka ce a sakin-layin.
"Zan iya samar da samfurin Saif-Al-Barzaƙ guda dubu casa'in?" inji Samudul Ansari.
Ruhin ya ce, "Ƙwarai ma kuwa. Abinda ake buƙata shi ne, daƙiƙu guda metan domin baiwa hadiman wannan takobi dama su samar da waɗannan samfuri."
Samudul Ansari yana jin haka ya baiwa hadiman wannan takobi umarnin dake rubuce a sakin-layi na sha-biyu.
A dai-dai wannan lokaci ne, aka busa wani ƙaton ƙaho daga cikin rundunar su Gauhan suka baiwa mayaƙansu umarnin afkawa su Samudul Ansari ƙarƙashin irin wannan dabarar yaƙi wadda Mahrus Gorgon yazo da ita.
Mayaƙan suka kwarara uban ihu, suka zaro makaman yaƙinsu sannan suka yiwa dawakansu ƙaimi suka ruga da gudu kan rundunar su Samudul Ansari.
Samudul Ansari ya yiwa rundunar abokan gaba kallon nutsuwa, kafun ya baiwa jama'ar dake tsaitsaye a bayansa umarni da hannunsa.
Dakarun suka zaro waɗansu irin garkuwowi sannan suka harhaɗu a waje guda, suka bayar da katanga mai girman gaske da waɗannan garkuwowi nasu.
Babu yadda za'a yi jama'ar Gorgon su shiga tsakiyar su, idan ba waɗannan garkuwowi suka tarwatsa ba.
Samudul Ansari ya dubi Zarifa da waɗansu mayaƙa guda arba'in zaƙwaƙurai dake tsaitsaye a bayansa ya basu umarnin tarar abokan gaba.
Ba tare da tsoro ko shakkun komai ba, Zarifa da waɗannan zaƙwakuran dakaru dake bayanta suka sakarwa dawakansu linzami suka tunkari runduna mai tsananin yawa da mugun haɗari.
Zarifa ta zaro waɗansu irin takubba guda biyu daga gadon bayanta. Takubban basu da tsaho sannan basu da faɗi sosai, sai dai kaifi biyu suke da sannan suna da tsananin tsini.
Waɗannan mayaƙa guda arba'in dake bayanta kuwa, wasu suka zaro takubba, wasu masu, wasu wasu kwari da baka. Babu irin makamin da babu a hannunsu.
Samudul Ansari ya dubi mayaƙan dake tsaitsaye a bayansa ya ce, "Duk wuya, duk rintsi, kada ku kuskura ku bari waɗannan mayaƙa su karya waɗannan garkuwowi naku.
"Nan da cikar daƙiƙu ɗari da sittin zan tarwatsa su duk wannan yawa nasu..."
Waɗannan mayaƙa suna jin wannan umarni suka amsa masa.
Samudul Ansari ya ɗaga wannan takobi ta Saif-Al-Barzaƙ sama, hasken rana ya doketa.
Nan take ƙarfenta ya soma ɓacewa yana sajewa da hasken rana, har ya gama ɓacewa ya saje da hasken rana.
Zarifa da waɗannan dakaru guda arba'in, suna haɗuwa da rundunar su Gauhan suka ruguntsume da azababben yaƙi.
Kowanne ɓangare suka wanzu suna masu kaiwa junansu sara da suka cikin zafin nama.
Zarifa da waɗannan dakaru guda arba'in sun kasance zaratan jarumai masu tsananin ƙarfi da iya yaƙi.
Duk inda suka sa a gaba sai dai kaga mazaje suna zubewa ƙasa matattu.
Duk tsananin horo da ƙarfin shiri irin na mayaƙan Gorgon saiya zamo na banza, sun gagara taɓuka wani abu.
Musamman ma, Zarifa tafi ci wa waɗannan mayaƙa tuwo a ƙwarya.
Duk inda ta sa a gaba sai dai kaga tana girbar mazaje da waɗannan wuƙaƙe dake hannunta.
Abinda Samudul Ansari ya fuskanta a wannan yaƙi shi ne, kwata-kwata rundunar Gorgon bata mayar da hankali sosai wajen yaƙar su Zarifa ba.
Abinda suka mayar da hankali akansa shi ne, rabuwa izuwa kaso huɗu domin saka rundunar su Samudul Ansari a tsakiya.
A wannan lokaci sun gama rabewa izuwa kaso guda uku, kaso ɗaya ne ya rage, kuma shi ne wanda su Zarifa suke ta kashewa babu ƙaƙƙautawa.
Zarifa da waɗannan dakaru suna cikin ragargazar waɗannan dakaru, suka ga waɗansu fai-fai masu yawan gaske sun sauƙo wannan wuri da suke.
Cikin zafin nama Zarifa ta daka tsalle gefe guda, sannan ta juya ta dubi daga inda waɗannan fai-fai suka taho.
Waɗansu mutane ta gani guda goma tsaitsaye riƙe da takubba masu siffar maciji [Bankai]
Waɗannan fai-fai na haske da suka aiko masu yawan gaske, sai da suka hallaka wasu daga cikin dakarun dake bayan Zarifa.
Mutanen suka juyo inda Zarifa ke tsaye, suka aiko mata da Bankai-mai-tafiya guda goma a tare.
Ƙarfin gudun saran Bankai-mai-tafiya yafi gaban tunanin mutum, komai zafin naman jarumi indai aka aiko masa wannan sara, kafun ya ankara zasu riske shi sannan su aika shi ƙiyama.
Saura ƙiris saran su riski Zarifa, waɗansu irin takubba na haske suka soma sauƙowa daga ƙasa sannan suka shiga tsakaninsu.
Saran Bankai-mai-tafiya guda goma suka doki waɗannan takubba, take suka zube a ƙasa gaba ɗayansu.
Waɗannan takubba da suka shiga tsakanin Zarifa da waɗannan ma'abota Bankai ɗin, basu da launi, tamkar ruwa haka suke.
Amma suna da tauri na gaban misali.
Samudul Ansari dake tsaye a can baya, ya motsa hannunsa guda.
Nan take waɗannan takubba suka tafi da gudu suka shige ta cikin jikin waɗannan mayaƙan Gorgon ɗin, waɗanda adadinsu zai kai dubu arba'in da ɗoriya sannan suka shige ta cikin mayaƙa ma'abota Bankai guda goma da suka aikowa Zarifa waɗannan muggan hare-haren.
Kamar ruwa aka watsa musu haka waɗannan takubba suka ratsa ta jikinsu sannan suka wuce baya.
Sai dai gaba ɗaya dakarun ƙamewa suka yi a inda suke tsaye, ruwan jikinsu gaba ɗaya ya ɗauke ya daina gudana. Sun mutu.
Iska mai ƙarfi na kaɗawa suka fara zubewa ƙasa kamar shara.
Babu rauni a jikinsu, babu rauni a cikin jikinsu amma ruwan jikinsu ya ɗauke gaba ɗaya.
Wannan shi ne karo na farko da Samudul Ansari yayi amfani da sinadarin ruwa dake cikin takobin Saif-Al-Barzaƙ ya hallaka ma'abota Bankai da ita.
Cikin tsananin mamaki kowa dake wannan wuri ya juya ya dubi wannan takobi dake hannun Samudul Ansari.
Duk takobin da zata iya hallaka mutane sama da dubu arba'in a lokaci guda, lallai ta cika abar tsoro da jinjinawa.
Gauhan da waɗannan sarakuna guda biyu, hankalinsu yayi mummunan tashi.
In dai aka ci gaba a haka, wannan takobi sai ta ƙarar da kowa dake wannan fili, hatta su kansu ba zata ƙyale su ba.
Ana tsaitsaye cikin wannan mamaki ne, irin wannan takubba na haske suka sake sauƙa a cikin ɓangaren dakarun dake kudu.
Wani jan haske mai launin jini, ya gilma ta tsakiyar su da sauri.
Wajen dakaru dubu tamanin suka sake zubewa ƙasa matattu.
Koda jama'ar dake filin wannan yaƙi suka ga haka, sai jama'ar Samudul Ansari suka ruɗe da shewa.
Mayaƙan Gorgon kuma suka fara ihun azaba.
Gauhan ya dubi waɗannan sarakuna guda biyu ya ce, "Ku zo muje mu tari Samudul Ansari, idan ba haka kuwa, duk saiya ƙarar da mu a wannan yaƙi..."
Sarakunan suna jin haka suka gyaɗa kai a tare, sannan suka tunkari inda Samudul Ansari ke tsaye.
Sauran mayaƙan su kuwa, suka fara guduwa suna komawa bayansu domin su kare su daga sharrin takobin Saif-Al-Barzaƙ.
Abunda basu sani ba shi ne sunyi gudun banza domin kuwa tuni hadiman wannan takobi [Saif-Al-Barzaƙ] sun rubuta sunayensu a cikin waɗanda zasu isa ƙiyama a wannan rana.
Suna tsakiyar gudu, manya-manyan duwatsun ƙanƙara suka soma dira a tsakiyar su.
Duwatsun suka soma yin nakiya suna bindiga, wani irin azababben sanyi ya fara daskarar da jinin jikin waɗannan dakaru suna mutuwa.
Kafun su Gauhan su ƙarasa gaban Samudul Ansari tuni ya hallakar da duk yawan dakarunsu dake wannan filin yaƙi.
Wasu ruwan jikinsu aka tsayar, wasu kuma jinisu aka gurɓata, wasu kuma jinin jikinsu aka daskarar.
Wannan na daga cikin kaɗan daga cikin sharrukan Saif-Al-Barzaƙ akan abokan gaba.
A fusace Gauhan da waɗannan sarakuna guda biyu suka ƙarasa gaban Samudul Ansari suka tsaitsaya.
Gauhan ya dube shi cikin rashin tsoro ya ce, "Tabbas ka samu nasarar karya dakarun mu, amma baka cika jarumi ba. Tun da ƙarfin sihirin aljanu kayi amfani ka kashe su!"
Samudul Ansari yayi guntun murmushi ya ce, "Maciyi amana ma, har yana da bakin magana? Ai bani ne na fara amfani da rantsatstsiyar takobi ba, hatta su kansu ma'abota Bankai da wacce irin takobi suke yaƙi?
"Tun da har kun ce haka, na yarda zan ajiye takobin Saif-Al-Barzaƙ a gefe, kuma zaku ajiye waɗannan takubba naku.
"Mu yaƙi da baiwar da Ubangiji yai mana!"
Waɗannan sarakuna guda biyu suna jin abinda Samudul Ansari suka yi dariyar farin ciki, suka ce, mun amince.
Suna faɗin haka suka cilla takubbansu sama cikin gajimare, takubban suka saje da kalar samaniya suka ɓace ɓat.
Gauhan ma ya cilla tashi sama, take wata tauraruwa ta bayyana a sama, takobin nasa ta shige cikin jikinsa.
Shi kuwa Samudul Ansari, kansa ya cakawa wannan takobi ta Saif-Al-Barzaƙ take takobin ta shige cikin jikinsa ta ɓace ɓat!
"Da ɗaiɗaya zamu gwabza wannan yaƙi, ko kuma zaku tarar min a lokaci guda?" inji Samudul Ansari.
Gauhan ya dubi waɗannan sarakuna ya ce, "Da ɗaiɗaya zamu yaƙe shi..."
Nan take suka sanar da Samudul Ansari wannan shawara da suka yanke.
Samudul Ansari na jin haka ya ware hannayensa biyu ya ce, "Ina jira waye zaizo mu fara gwabzawa..."
Sarkin birnin Mesa yayi tsalle cikin gaggawa ya dira a gaban Samudul Ansari.
A tare suka zaro waɗansu takubba waɗanda basu kasance masu amfani da aljanu ba, sannan suka afkawa juna da azababben yaƙi.
Sarkin birnin Mesa ya wanzu yana kaiwa Samudul Ansari muggan sara da suka cikin baƙin zafin nama tamkar jikinsa bai kasance jini da tsoka ba.
A cikin daƙiƙa biyar yana iya kaiwa Samudul Ansari sara sau biyu ko ma fiye.
Shi kuwa Samudul Ansari saiya dinga kare hare-haren wannan sarki, cikin kwanciyar hankali ba tare da yayi wani motsi na kirki ba.
Kai da gani ka san cewa, dama kawai ya baiwa wannan sarki domin ya gama abinda zaiyi kafun ya afka masa.
Tsahon ɗan lokaci sarkin birnin Mesa nata kaiwa Samudul Ansari, ba tare da ya samu nasarar koda lakutar jikinsa ba.
Lamarin da yayi matuƙar bashi mamaki kenan, kuma ya girgiza shi.
Duk wanda yake da muƙamin sarki a birnin Mesa ana bashi wani gagarumin horo na yaƙi wanda duk duniya babu inda ake karɓar horon idan ba can ba.
Saboda tsananin horon yaƙin nasu, komai yawan runduna mutum ɗaya jal a cikinsu yana iya tarwatsa ta.
Bayan wannan, takobin da ke hannun sarkin bata amfani da aljanu amma akwai albarkar macijiya Ziyazilu a tattare da ita.
Indai suka zarota daga

Please Login or Register in order to submit comment