Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ƙarasa inda gawarwakin suke, ya fiddo kibiyoyinsa ya goge jinin a jikin fatan damisoshin sannan ya mayar da kibiyoyin cikin ƙuttunsu.
Barban ya dube shi ya ce, "Ba ma buƙatar ka gwada mana wannan baiwa ta ka, mun riga da mun san cewa waye kai, da kuma ƙwarewarka a fannin harbi."
Oksu yayi murmushi ya ce, "Komai na buƙatar tabbatarwa, tabbas yanzu kun tabbatar da cewa zan iya!"
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, suka ci gaba da tafiya a cikin wannan daji, har suka fice daga cikinsa.
Tsahon sa'o'i cir suna tafiya sannan suka iso wannan waje wanda Aymanul Faris da Barban suka sauƙo a ɗazu daga fadar aljani Ranganu.
Suna zuwa wannan waje Barban yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak! Aymanul Faris da Oksu ma suka tsayar da dawakansu.
Barban ya sauƙo daga kan dokinsa sannan ya basu umarnin sauƙowa su ma.
Suna sauƙowa Barban ya dafa su su biyun, take jikinsu ya zamo haske su biyun suka ɓace ɓat!
A tsakiyar fadar sarki Ranganu suka bayyana inda suka iske shi, zaune akan karagar mulkinsa kamar yadda suka bar shi.
Ranganu ya dubi Oksu daga sama har ƙasa sannan ya basu umarnin zama akan waɗannan kujeru.
Kai tsaye suka ƙarasa kan waɗannan kujeru suka zazzauna.
Ranganu ya dubi Oksu ya ce, "Barka da zuwa. Da fatan sun sanar da kai aikin da zaka yi mana, kuma ka amince?"
Saboda ƙarfin ikon sarki Ranganu, Oksu ji yake tamkar a gaban wani abu mai cikakken iko yake.
A hankali ya gyaɗawa Ranganu kai, alamun ya amince.
Ranganu ya yi murmushi ya ce, "Da kyau. Yanzu sai ka biyo ni izuwa ɗakin tsafina domin na tsumaka a cikin tsumin tsafina!"
Ranganu yana gama faɗin haka ya miƙe tsaye, ya shiga cikin wani ɗaki dake gefen wannan fada tasa. Barban, Aymanul Faris da Oksu suka take masa baya.
Ɗaki ne ƙatoton gaske wanda aka cika da manya-manyan tuƙwane masu ɗauke da ruwan zafi launi daban-daban.
Wani irin tiriri na fita daga cikin tukwanen mai ban tsoro da nuna tsananin zafin da suka ƙunsa.
A tsakiyar wannan ɗaki suka iske sarki Ranganu tsaye yana jiransu.
Oksu yana ganin waɗannan tukwane gabansa ya sara saboda yana tsoro kada ace cikinsu za'a saka shi.
Abinda ya kwantar masa da hankali shi ne, ƙarfin ikon sarki Ranganu da Barban. Idan yana kallonsu wani aminci yake ji, wanda yake sawa yaji kamar ba zasu yaudare shi ba.
Ranganu ya ƙarasa bakin wata ƙatuwa tukunya mai ɗauke da shuɗin ruwa ya buɗe marfinta. Wani irin mugun tiriri ya tashi sama.
"Ya kai Oksu ka matso gaban wannan tukunya sannan ka dafa ta da hannunka..."
"Ehye?" inji Oksu cikin razana.
Barban ya ƙaddamar da korayen idanunsa sannan ya dubi Oksu ya ce, "Ba ka ji abinda aka ce ma ba?"
A cikin wannan siffa idan Barban yayi magana, umarni ne kawai wanda mutum ko yana so ko baya so saiya bi.
Kai tsaye Oksu ya ƙarasa gindin wannan tukunya sannan ya dafata da hannunsa kamar yadda aka umarce shi.
Wani shuɗin haske mai kama da gajimare ya bayyana a gabansa sannan ya lulluɓe jikinsa.
Hasken ya ɗinga disashewa a hankali, har ya gama disashewa inda gangar jikin Oksu ta ɓace ɓat daga wannan waje.
A cikin wannan tukunya ta bayyana inda ta soma dagargajewa tamkar alli.
Ranganu ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Ka je ka taho mana da masoyiyarka Riya, lokacin tafiya ya kusa. Yau ɗaya ga watan Yuni!"
Aymanul Faris yayi murmushi ya so ya risina a gaban Ranganu amma sai jikinsa ya ƙi bin wannan umarni.
Aymanul Faris yayi girgiza jikinsa ya juye izuwa wuta ya ɓace ɓat!
Barban ya yi murmushi ya ce, "Dama yana iya juyewa izuwa wuta ne?"
Ranganu ya ce, "Wannan shi ne ikon Samudul Ansari! Komai nasa na wuta ne!"
***
A tsakiyar unguwar Barbanul Kuyr Aymanul Faris ya bayyana. Yana bayyana mutanen wannan unguwa wanda da yawa daga cikinsu yan asalin ƙauyen Gazwar ne, suka fara zubewa ƙasa suna gaishe da shi.
Aymanul Faris ya wuce kai tsaye izuwa wannan gida nasu jaruma Riya, yana karɓar gaisuwar jama'a har ya iso wannan gida.
Da shigowarsa cikin gidan, yayi kiciɓus da jaruma Riya tana fitowa.
A gigice tayi tsalle ta rungume shi, cikin tsananin farin ciki. Kallon Aymanul Faris yafi wa jaruma Riya komai.
Aymanul Faris ya janye jikinsa daga nata sannan ya nuna waɗansu kujeru dake bayansu ya ce, mu zauna a can.
Cikin sauri suka ƙarasa wurin suka zazzauna.
Aymanul Faris ya dubeta cikin nutsuwa ya ce, "Ba kya tunanin yin aurenmu da wuri zai janyo wata matsala?"
"Kamar matsalar me kenan?" inji jaruma Riya.
Aymanul Faris ya gyara zama ya ce, "Har yanzu ba mu gama fuskantar alƙiblarmu ba. Akwai abubuwa da yawa waɗanda suke gabanmu sannan suke buƙatar mayar da hankali sosai domin gamawa da su!"
"Kamar waɗanne abubuwa kenan?" inji jaruma Riya.
Aymanul Faris ya ce, "Abu na farko shi ne mallakar ruhin babban sarki Samudul Ansari... Abu na biyu shi ne sake kafa daular Shaha mai zaman kanta kamar yadda take a da... Abu na uku shi ne kare wannan daula daga abokan gaba... Abu na huɗu sare kan sarki Kuffuru da sarki Ayubu mahaifin gimbiya Jaanu...."
"Hmm," jaruma Riya tayi murmushi. "Sai nake ganin waɗannan abubuwa kamar ba wata matsala bace... Cikakken namiji shi ne wanda yake da mata kuma yake kula da ita. Aure a wajen namijin duniya, ba wani abu bane face cikar lafiyarsa da kuma samun nutsuwarsa.
"Shin baka ganin idan aka ce kana da aure, zaka fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali wanda zai sa ka ɗinga gudanar da komai naka yadda ya dace...?"
Aymanul Faris yana tunanin waɗannan maganganu da ta faɗa masa.
"Alƙiblar mu ɗaya, ra'ayinmu ɗaya, burinmu ɗaya. Duk inda kake ina nan ina tare da kai. Shin baka tunanin zamu fi jin daɗin tarayya idan akace muna sanin juna." inji jaruma Riya.
Aymanul Faris yayi shuru yana tunanin waɗannan maganganu jaruma Riya.
Tabbas duk abinda ta faɗa gaskiya ne. Mutun baya taɓa cika mutun face yana da mata. Sannan daga wannan lokaci duk Aymanul Faris zaije suna tare.
Tun suna yara ƙanana suke karɓar horo a wajen mahaifinta a tare, saboda haka sun shaƙu sosai.
Babu abinda yafi dacewa dasu a wannan lokaci face aure, saboda zumuncin dake tsakaninsu ya ƙara ƙarfi sosai.
"Sannan nima bani ce na cewa mama ayi mana aure ba," inji jaruma Riya. "Muna tsakiyar tattaunawa kawai ta ce min, lokacin da za'a daura mana aure ya kusa."
"Hmm," Aymanul Faris yayi murmushi ya ce, "Wannan ba matsala ba ce. Bin umarnin mama shi ne burina..."
A daidai lokacin ne Hajriya ta shigo cikin wannan falo sanye da doguwar riga ruwan toka.
Aymanul Faris yayi saurin durƙusawa ya gaishe da ita kamar yadda ya saba. Hajriya ta zauna a gefensu suka sake fuskantar juna.
"Na ji kamar kuna tattaunawa akan aure da za'a yi muku ko?" inji Hajriya.
Jaruma Riya ta ce, "Eh, abinda muke tattaunawa kenan..."
Hajriya tayi guntun murmushi ta ce, "Shin kun amince gaba ɗaya?"
Aymanul Faris da Riya suka dubi juna suka yi murmushi sannan suka gyaɗa kai a tare alamun sun amince.
Hajriya ta fuskance su da kyau ta ce, "Zan faɗa muku dalilin da yasa nace ayi auren nan da wuri, ku bani nutsuwarku..."
Aymanul Faris da Riya suka yi tsit sannan suka kasa kunnuwansu sosai.
"Kasancewa ta matar Hasanul Jalwar jikan Samudul Ansari na san sirruka da dama waɗanda ba ku sani ba.
"Shin ko kun san cewa sarki Samudul Ansari ba sarauniya ARYA ya fara aure ba?"
Aymanul Faris da jaruma Riya suka dubi juna cikin tsananin mamaki.
"Na san cewa ba ku san ƙa'idojin mallakar ruhin jarumtaka ba?
"Kuyi sani cewa mijina yayi nisa sosai kuma ƙiris ya hana ya mallaki ruhin jarumtaka, abinda ya tsayar da shi shine rashin samun ARYA II.
"Mijina yaje har cikin kogon da aka ajiye ruhin jarumtaka sannan yayi ido-da-ido da ruhin, amma sanin cewa babu jinin ARYA II a jikinsa yasa bai ɗauki wannan ruhi ba.
"Ƙa'idojin guda uku ne; na farko shi ne zamowa cikakken mutum. Na biyu shi ne kasancewa a cikin zuciyar ARYA. Na uku shi ne dole ne mutum ya kasance yana da kusanci sosai da wannan ruhi.
"Shi cikakken mutum shi ne wanda yake da mata sannan yake da cikakkiyar lafiya.
"Kasancewa a cikin zuciyar ARYA, yana nufin dole mutum ya kasance yana soyayya da ARYA, sannan ya taɓa jin ɗumin jikinta a nasa.
"Kusanci da wannan ruhi kuma, yana nufin dole ya kasance mutum yana da jinin Samudul Ansari a jikinsa gaba da baya.
"Sarki Samudul Ansari ya auri wata mace dabam, kafun ya auri ARYA.
"Hasanul Jalwar ya aure ni, dukda cewa ban kasance ARYA ba, sannan yana neman wadda zata kasance ARYA domin itama ya aureta.
"Kaima, dole ne ka auri Riyalatu. Idan yaso daga baya sai ka auri ARYA!"
Aymanul Faris da Riyalatu suka yi shuru suna tunanin waɗannan maganganu da Hajriya ta faɗa musu.
Daga can Aymanul Faris ya ce, "Na gode sosai yake ummina da kika sanar dani wannan sirri. Sannan ban ga laifinki ba, da kika ce nayi aure daga yanzu...
"Dama nazo ne domin na ɗauki Riyalatu, muje mu gudanar da aikin ƙarshe da ita. Wanda muna kammala shi, zan tafi ɗauko wannan ruhi."
"Ah lallai aurenku ya kusa." inji Hajriya.
Aymanul Faris ya ɗan risina ya ce, "Idan mun kammala wannan tattaunawa, ina so kiyi mana izini mu tafi domin gabatar da wannan aiki...?"
Da wannan Aymanul Faris da mahaifiyarsa suka yi sallama, akan cewa suna kammala wannan aiki, zasu dawo a ɗaura musu aure.
Aymanul Faris ya dafa kafaɗar jaruma Riya, irin wannan wuta ta baibaye jikinsu suka ɓace ɓat!
****
Yau *04/02/2023*
Babi na gaba zaizo *06/02/2023* da yaddar ALLAH..
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 81: *Farmakar sarki Raja*
*
Dubun Godiya Ga Masoya...
*
U*M*S
*
Aymanul Faris da jaruma Riya suka bayyana a tsakiyar fadar sarki Ranganu, inda suka iske Barban da Oksu zaune a gaban Ranganu yana tayi musu ƙarin bayanai akan wannan aiki da ke gabansu.
Ranganu yana ganin sun bayyana ya nuna musu waje ya ce su zauna. Babu musu suka zazzauna.
Ranganu ya dubi Riya ya fara sanar da ita tsare-tsaren wannan aiki da yadda zasu gudanar da shi, har dai ta gane komai da komai.
"Yau uku ga wata, tuni sarki Raja ya fito wannan rangadi nasa, kamar yadda muka tsara gobe ne zai isa garin Duhamul, saboda haka yau za ku je ku kwana a can." inji Ranganu.
Jaruma Riya ta ce, "Ya shugabana, shin wannan tafiya mu nawa ne zamu yi ta? A bayanan da kayi mini baka sanar dani mu nawa zamuje ba?"
Ranganu yayi murmushi ya ce, "Ku uku za ku je. Ke, Aymanul Faris da Oksu. Ke da Aymanul Faris za ku farmaki dakarun sarki Raja ku hallaka su, daga nan shima sai ku afka masa ku kashe shi. Oksu shi ne wanda zai harbe inuwowin sarki Raja daga nesa!"
Jaruma Riya ta gyaɗa kai cikin fahimta. Ranganu ya sake cewa, "Idan babu mai tambaya a cikinku, za mu sa hadiman mu su ɗauke ku, su kai ku garin Duhamul domin ku jira wayewar garin gobe."
Caraf Oksu ya ce, "Ta wacce hanya sarki Raja da mutanensa zasu ɓullo? A ina zan laɓe domin samun harbo waɗannan inuwowi nasa?"
Sarki Ranganu yayi murmushi sannan ya nuna bangon wannan fada tasa, bangon yayi haske sannan ya nuna hoton yankin birnin Duhamul gaba ɗaya.
Garin Duhamul ƙaramin gari ne wanda aka gina shi gaba ɗaya a cikin sahara, yanayin gidajen garin yana matuƙar kama da na mutanen birnin Hindu. Wataƙila hakan ya samo asali ne saboda garin a cikin birnin Hindu yake.
A bayan wannan gari akwai wata doguwar hanya da ta ratso ta cikin wani ƙaramin daji mai yawan duwatsu jefi-jefi.
Wannan hanya ita ce wadda ake bi, a shigo wannan gari ko kuma a fita.
Aljani Ranganu ya nunawa Oksu wani ƙaton dutse dake can nesa da wannan hanya, ya ce, "A saman wannan dutse za ka kwanta, sannan dole ka kashe waɗannan inuwowi a lokacin da suke daf da shiga wannan gari!"
Oksu ya gyaɗa kai alamun ganewa.
Aljani Ranganu ya nuna wata ƙatuwar bishiya dake kusa da wannan hanya ya ce, "Ayman da Riyalatu a jikin wannan bishiya za ku ɓuya da zarar Oksu ya harbe waɗannan inuwowi zaku fito ku afkawa dakarun sarki Raja da kisa, ku na gama kashe su zaku haɗa ƙarfi da ƙarfe ku yaƙi sarki Raja.
"Idan ku ka sare kansa, sai ku ɗakko wannan makulli. Daga wannan lokaci Barban zai bayyana domin yayi muku jagora zuwa wajen tsoho Samazan domin jin cikakkiyar hikayar sarki Samudul Ansari.
"Kada ku manta daga wannan lokaci zamu sanar da ku hanyar zuwa inda wannan ruhi yake, sannan idan mutum bai saurari wannan hikaya ba, babu yadda za'ayi ya mallaki ruhin!"
Aymanul Faris, jaruma Riya da Oksu suka gyaɗa kai cikin fahimtar wannan bayani na aljani Ranganu.
Ranganu ya nuna wannan bango da hannunsa, take hoton garin Duhamul ya ɓace ɓat!
"Ku shirya, yanzu zamu tura a kai ku garin Duhamul domin jiran wayewar garin gobe!" inji Ranganu.
Nan take ya nuna Aymanul Faris, Riya da Oksu da hannunsa guda, wani farin haske ya baibaye jikinsu suka soma ɓacewa a hankali, kafun su ɓace daga cikin wannan fada gaba ɗaya.
****
A tsakiyar wannan gari wanda Ranganu ya nuna musu a madubin tsafi suka tsinci kansu. Oksu ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Tau'rin! A ina zamu kwana?" Don a wannan lokaci rana na daf da faɗuwa.
Aymanul Faris ya ɗaga kansa sama inda ya hango wani gida, a saman gidan an rubuta 'OTEL' Aymanul Faris ya ce, ga can inda zamu kwana.
Yana faɗin haka ya wuce ƙofar wannan gida inda wani mutum ke zaune a cikin wata rumfa tare da takardu tirim a gabansa, yana ta rubuce-rubuce.
"Barka! Ɗakunan kwana muke buƙata?" inji Aymanul Faris.
Mutumin ya ɗago kansa a hankali ya kalle su ɗaya bayan ɗaya sannan ya basu umarnin zama akan wasu kujeru.
Tsahon daƙiƙu kafun ya yafito Aymanul Faris da hannunsa guda, Aymanul Faris ya matso kusa.
"Ɗakuna nawa kuke buƙata?" inji ma'aikacin.
Aymanul Faris ya ce, "Ɗakuna uku!"
Ma'aikacin ya duba wani ɓangare daga cikin wani littafi dake hannunsa ya ɗago kai ya ce, "Ɗakuna guda biyu rak! suka rage."
Aymanul Faris ya yi gajeren tunani ya ce, "Ba matsala!"
Ma'aikacin ya ce, "Ku bamu bayananku domin a tanadar muku ɗakunan. Ya ya sunanku? Daga ina kuke?"
Aymanul Faris ya ce, "Suna na Ayman, wancar sunanta Riya, wannan kuma sunansa Nasim. Dukkaninmu daga birnin Damashkar muke." Aymanul Faris ya ɓoye sunan Oksu saboda wani dalili na musamman.
Wannan ma'aikaci ya fara rubutu akan wata takarda, ga dukkan alamu ciketa yake. Yana gama cikewa ya ɗakko wani makulli ya baiwa Aymanul Faris.
"Ɗaki mai lamba ta 246 da ɗaki mai lamba ta 247." inji ma'aikacin.
Aymanul Faris ya karɓi makullan sannan ya tashi ya shige cikin wannan otel, Riya da Oksu suka take masa baya.
Suka yi ta wuce ɗakuna har suka iso bakin waɗannan ɗakuna waɗanda wannan ma'aikaci ya faɗa musu.
A ƙofar shiga waɗannan ɗakuna ne fa, gardama ta ƙarƙe a tsakaninsu. Inda jaruma Riya ta bi ta dage akan dole sai sun kwana a ɗaki ɗaya da Aymanul Faris.
Shi kuma ya ce, sam wannan abu ba zai yiwu ba.
"A ɗaki ɗaya zamu kwana, ni da wannan maharbin..." inji Aymanul Faris.
Oksu ya dube shi ya ce, "Tun ina yaro ƙarami, ba na kwana da kowa a ɗaki. Ni ɗaya nake barci na. Har na girma nayi aure, ban taɓa kwana da matata a ɗaki ɗaya ba. Ina ganin zai fi dacewa ku kwana ku biyu, ko ba komai ku masoyan juna ne!"
"Ka ji magana!" inji jaruma Riyalatu cikin farin ciki.
"Hmm," Ayman yayi murmushi. "Sai dai nayi barcina a nan."
Jaruma Riya tana jin haka ta haɗe fuska sannan ta juya ta nufi ƙofar fita daga wannan otel ɗin.
A gaggauce Aymanul Faris ya ruga ya riƙota sannan ya dawo da ita inda Oksu yake, suka shiga cikin ɗaki ɗaya. Shima Oksu ya shige cikin nasa.
Ɗaki ne ƙaton gaske wanda aka ƙawata ainun. Akwai gadon barci guda ɗaya ƙato da kujerun zama na alfarma.
Aymanul Faris yaje ya kwantar da jaruma Riya kan wannan gado, yayi kamar zai kwanta a gefenta amma sai yayi wuf ya koma kan wannan kujera ya kwanta.
Har jaruma Riya tayi niyyar tasowa taje ta same shi, amma sai wani tunani yazo kanta, kawai ta koma ta kwanta ta fasa zuwa. Kwanaki kaɗan suka rage a ɗaura musu aure, ana yi musu aure komai zai zo.
Washe gari da sassafe Aymanul Faris yana farkawa yaga jaruma Riya acan nesa daga inda yake, tana saka sulken yaƙi. Waɗansu ƙananan kaya ne a jikinta waɗanda suka bayyanar da kyakkyawar surarta.
Tun da Aymanul Faris yake tare da ita, bai taɓa ganinta a irin wannan hali ba.
Tabbas jaruma Riya, cikakkiyar budurwa ce mai kyawun dirin jiki wanda Aymanul Faris yake ganin ko ARYA ba zata nuna mata komai ba.
Ganinta a cikin wannan hali yasa Aymanul Faris yaji wani sanyi a ransa, sannan yayi sauri ya rufe idanunsa tamkar barci yake saboda baya so ta gane ya kalleta a haka.
Abinda bai sani ba shi ne, dama dalilin da yasa tayi hakan kenan. Saboda ta nuna masa baiwar da take da a kyawun jiki.
Jaruma Riya ta gama rufe dukkan jikinta da wannan sulke, sannan ta nufo inda Aymanul Faris yake.
Tana zuwa ta sunkuya ta sumbaci goshinsa domin ta tashe shi daga barci, Aymanul Faris ya buɗe idanunsa ya dubeta.
"Ka tashi gari ya waye!" inji Riya cikin soyayya.
A gaggauce Aymanul Faris ya tashi saboda baya son surutu a wannan lokaci, shima yayi wanka ya sako kayan yaƙinsa.
Oksu ya shigo cikin wannan ɗaki nasu suka yi kalaci sannan suka fice daga cikin wannan otel gaba ɗaya.
Ba su yarda sun bi hanyar da jama'a suke bi sosai ba, domin gujewa yan leƙen asiri.
Da yake wannan gari ɗan ƙarami ne, kafun a jima tuni sun fice daga wannan gari sun hau kan wannar hanya.
Suna zuwa kan hanyar suka yanki daji suka yi ta tafiya. Nan ma basu yi nisa sosai ba, suka hango wannan ƙaton dutse da aljani Ranganu ya nunawa Oksu ya ce a samansa zai kwanta domin harbin waɗannan inuwowi.
Oksu ya gyara kwari da bakansa sannan ya yi sallama da su Aymanul Faris ya nufi kan wannan dutse.
Aymanul Faris da jaruma Riya suka nufi gindin wannan ƙatuwar bishiya wadda suke hangowa a can nesa.
"Yanzu idan wannan maharbin bai samu nasarar harbo waɗannan inuwowi ba, ya ya kenan?" jaruma Riya ta tambayi Aymanul Faris.
Aymanul Faris ya ce, "Sarki Raja zai gudu mana. Amma ni dai na ɗau alƙawari tun da nazo wannan wuri, da wannan makulli zan koma, koda ta kama naje babbar fadar birninsa kuwa!"
"Ba sai ta kai ga haka ba," inji jaruma Riya.
Suna ƙarasawa gindin wannan bishiya suka hau kanta, suka ɓuya a cikin duhuwar ganyaye. Oksu ma ya haye can saman wannan dutse, sannan ya ɗana kibbau guda uku akan bakarsa ya saita wannan hanya yana jira.
Tsahon rabin sa'a cur, suna jira sarki Raja da mutanensa basu ɓullo ba.
Rabin sa'a na cika, suka soma jiwo sukuwar dawakai daga can nesa.
Aymanul Faris ya zaro asalin takobinsa (ba Saiful Shiradu) ba. Itama jaruma Riya ta zaro zabga-zabgan takubbanta guda biyu ta riƙe su da kyau.
Jim kaɗan wata runduna ta mayaƙa masu yawan gaske ta bayyana. Gaba ɗayansu sanye suke cikin sulken kala ɗaya. A tsakiyarsu kuma, wani basarake ne tafe.
Sarki Raja gabjejen ƙato ne yana da tsaho da ƙauri. Fuskarsa a cike take da ƙasumba, yayi wani rawani irin nasu na ƙasar Hindu. Kayan da suke jikinsa a wannan rana na sarauta ne, kasancewar rangadi ya fito.
Waɗansu sadaukai guda uku masu baƙaƙen ƙaya na take masa baya, duk inda yasa sawunsa yana ɗaukewa zasu saka nasu.
Fuskokinsu a rufe suke da baƙin rawani, mutum ba zai ga fuskokinsu ba.
Kowanne ɗaya daga cikinsu yana rataye da zabgegiyar takobi wadda take walƙiya a cikin hasken rana.
Wannan runduna ta ci gaba da tafiya akan wannan hanya tana tunkarar birnin Duhamul, har suka kusa iso wannan ƙatuwar bishiya.
Ba zato ba tsammani! Aka ji sauƙar kibiyoyi daga can sama.
A fusace sarki Raja ya juyo, ai kuwa sai yayi arba da waɗannan mutane uku dake take masa baya, durƙushe bisa gwiwowinsu.
Ga kibiya a soke a ƙirjin kowanne ɗaya daga cikinsu. Sarki Raja ya kwarara uban ihu cikin takaici. Ya zaro zabgegiyar takobinsa sannan ya kwaɓe alkyabbar dake jikinsa.
Ya bayyana babu komai a jikinsa face wani dogon wando da kuma wani abun wuya wanda aka saka wannan makulli a ƙarshensa.
Sarki Raja ya dubi waɗannan inuwowi nasa ya ga suna mutuwa a hankali. Wannan abu yayi matuƙar bashi mamaki.
Saboda gudun irin wannan ɓacin rana yasa ya haɗa musu wani tsumi suka sha, wanda kowanne irin makami aka aiko musu sai dai ya ratsa ta cikin jikinsu kamar haske. Ya ya aka yi waɗannan kibiyoyi suka huda jikinsu?
Sannan sarki Raja yana da wani kafin tsafi a jikinsa wanda yake bashi damar jiwo tahowar abu, tun kafun abun ya ƙaraso da taku arba'in. Ya ya aka yi bai ji tahowar waɗannan kibiyoyi ba?
Kafun ya samu amsar waɗannan tambayoyi nasa, aka ga waɗansu jarumai guda biyu sun dako tsalle daga saman bishiya sun faɗa tsakiyar dakarunsa, sun hau su da sara da suka cikin baƙin zafin nama da bajinta.
Waɗannan dakaru na ganin haka suka yi kukan kura suka zaro makaman yaƙin su suka tari wadannan jarumai, aka soma baƙin gumurzu. Waɗannan jarumai guda biyu ba wasu bane illa Aymanul Faris da jaruma Riya.
Nan fa Aymanul Faris da jaruma Riya suka yi ta kashe waɗannan dakaru babu ji abu gani. Duk inda suka saka a gaba sai dai kaga gawarwaki na zubewa ƙasa. Jini ya fara fallatsi da feshi, sassan jikin bil'adama suka soma yawo a sararin samaniya tamkar ruwan samansu ake.
Daga bisani kuma, waɗansu irin kibbau masu shegen tsini suka soma sauƙowa cikin wannan filin yaƙi suna karkashe dakarun sarki Raja.
Kafun a jima tuni an haɗawa dakarun sarki Raja zafi, ta ko'ina zubar da su ake tamkar ganyayen bishiyoyi a lokacin bazara.
Sarki Raja na tsaye a gefe guda, yana ta kallon yadda wannan gumurzu yake gudana. Kamar yana so yaga iyakar ƙarfin su Aymanul Faris ne.
Kafun sa'a guda ta cika, tuni su Aymanul Faris sun gama zubar da waɗannan dakaru, saura kuma sun ruga cikin daji da gudu domin ceton rayuwarsu.
Ya rage saura sarki Raja kaɗai da su Aymanul Faris sai kuma gawarwakin da suka cika wannan fili.
Cikin tsananin fusata sarki Raja ya dakawa su Aymanul Faris tsawa ya ce, "KAI! Su waye ku? Me kuke nema?"
Aymanul Faris ya ce, "Rayuwarka muke so ka bamu, idan zaka kashe kanka a yanzu,

Please Login or Register in order to submit comment