Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabbatarwa mutane cewa kaje can ba. Ya ya aka yi haka?" inji Gauhan cikin izgili.
Samudul Ansari yayi guntun murmushi ya ce, "Ba don dawowa da wata alama naje can ba. Naje can ne domin neman magani kuma an dace..."
Gauhan ya yi dariyar mugunta ya ce, "Idan ka isa, ka kare dakarun wannan matar taka daga sharrin ma'abota Bankai gobe..."
"Hmm," Samudul Ansari ya sake yin murmushi. "Mu haɗu a filin daga. Tabbas kai da waɗannan sarakuna kun kama hanya wadda ba zata ɓulle ba."
Gauhan na jin wannan batu na Samudul Ansari ya zaro wata zabgegiyar takobi a gadon bayansa, ya ɗagata sama.
Nan take waɗansu jajayen taurari masu launin jini suka soma bayyana a saman kansa.
"Da wannan takobi zan ƙarar da ma'abota Bankai gobe, kuma da wannan takobi zan kunyata ka..."
Samudul Ansari ya yi dariya ya kama hannun sarauniya Arya da hannun Zarifa suka bar wannan waje, saboda baya so baƙaƙen maganganu su soma shiga tsakaninsa da Gauhan waɗanda zasuyi sanadiyar yaƙi a tsakanin su.
Waɗannan sarakuna suka tara dukkanin dakarunsu suka shaida musu cewa, daga wannan lokaci basa ƙarƙashin Samudul Ansari zasu karɓi umarni daga Gauhan a gobe.
Da wannan suka janye hankalin dukkanin dakarunsu ga barin ɓangaren Samudul Ansari suka dawo ɓangaren Gauhan.
Sarauniya Arya ta tara dakarun ƙasarta waɗanda su suka fi kaɗan daga ciki, ta shaida musu cewa, umarnin Samudul Ansari zasu bi a wannan yaƙi.
Saboda shi ne kaɗai wanda zai iya kuɓutar da wannan daula daga sharrin ma'abota Bankai.
Mayaƙanta suka tabbatar mata da cewa, lallai zasu bi wannan umarni da ta basu.
Waɗannan sarakuna babu yadda ba'a bi da su ba, domin su dawo hanyan amma sun ƙi.
Hatta Ƙaizadu sai da ya bayyana da kansa ya ja musu kunne amma sun ƙi yarda.
Dare na soma tsalawa, Samudul Ansari ya tunkari ɗakin da sarauniya Arya ke zaune tana jiransa.
Dama tun bayan magriba suka yi sallama da juna, akan cewa zata je ta gyara kanta saboda a wannan dare zasu more amarci.
Idan suka more amarci Samudul Ansari zai farkar da wannan ruhi dake cikin jininsa.
Saura taku arba'in Samudul Ansari ya isa wannan ɗaki, yaji an shaƙo shi ta baya, sannan an ɗaga shi sama an doka da ƙasa.
Wanda yayi masa hakan, ya zauna akan ruwan cikinsa.
Cikin gaggawa Samudul Ansari ya taso suka fara kokawa, su faɗi nan su tashi can.
Koda Samudul Ansari ya fuskanci manufar wannan mutumi, yana ƙoƙari ne ya hana shi zuwa wajen matarsa domin farkar da jininsa saiya doki ƙirjin mutumin.
Saboda ƙarfin dukan sai da mutumin ya yi tsalle ya faɗo acan baya.
Samudul Ansari ya zaro Saif-Al-Barzaƙ dake gadon bayansa. Takobin tayi haske ta haskaka dukkan wannan waje.
Samudul Ansari yayi arba da wannan mutumi wanda ya rufe fuskarsa da baƙin rawani.
Cikin tsananin fusata Samudul Ansari ya aika masa da sara-mai-tafiya yana cewa, "Ba zaka sake kawo min farmaki ba, daga yau."
Dukda cewa fuskar mutumin a rufe take amma saida alamar tsoro ƙarara ya bayyana a cikin idanunsa, ya zaro wata sanda a gadon bayansa yayi rubutu akan ƙasa.
Take wani ƙaton rami na sihiri ya bayyana, ya daka tsalle ya faɗa cikin wannan rami.
Wannan ita ce babbar sa'ar da yayi, ba don haka ba, da tuni wannan sara-mai-tafiya ya aika shi lahira.
Ƙaton rami da ya faɗa ciki, ya koma ya haɗe.
Samudul Ansari yayi murmushi ya mayar da takobinsa cikin kufenta sannan ya ƙarasa turakar sarauniya Arya inda ya iske abinci wajen kala ashirin a jibge suna jiransa.
Shi da amaryarsa suka ci suka ƙoshi sannan suka shige banɗaki suka yi wanka.
Abinda Samudul Ansari ya fuskanta a jikinsa shi ne, tun sa'adda ya tunkari sarauniya Arya a matsayin mijinta yake jin wani sauyi a jikinsa.
Lokacin da suka kwanta kan gado, ya tara da ita kuwa, sai ɗakin gaba ɗaya ya sake gaurayewa da wani sabon duhu dukda cewa a cikin duhu suke amma wannan duhu wanda ya bayyana a wannan lokaci ya ninka na farkon sau arba'in.
Tun da Samudul Ansari yake a rayuwarsa bai taɓa jin daɗi irin na wannan lokaci ba, saboda sarauniya Arya mace ce mai baiwar ni'ima wadda mijinta zaiyi matuƙar ɗimaucewa idan ya tara da ita.
Tsahon daƙiƙu talatin, kafun wannan duhu gaba ɗaya ya yaye. Wani irin farin haske ya gauraye ɗakin gaba ɗaya.
Sarauniya Arya tana kwance lulluɓe da wani farin bargo.
A wannan lokaci taje tayi wanka sannan ta sake gyara jikinta. Kai har barci ma ya saceta bata sani ba, saboda tsananin yadda take farin ciki.
Babu matar da zata kwana da Samudul Ansari ba tare da ta kamu da tsananin ƙaunarsa ba, saboda namijin gaske ne.
Wannan farin haske na bayyana sarauniya Arya ta buɗe idanuwanta a hankali, a tsakiyar wannan ɗaki ta hango Samudul Ansari zaune ya tankwashe sawayensa.
Bata yi yunƙurin tasowa daga kan wannan gado ba, kawai ƙura masa idanu tayi tana jira taga abinda zai faru tunda ya farkar da jininsa.
Wani irin iko wanda tunda take a rayuwarta bata taɓa jin mai kama da shi ba.
Dukda cewa ita sarauniya ce, amma saida taji wannan lokaci ta zamo tamkar baiwa wadda dole ne tayi biyayya ga wannan iko idan ba haka kuwa, ruhinta zai tarwatse yayi daga-daga.
Bisa dole ta miƙe tsaye sannan ta risina a gaban wannan iko dukda cewa bata kalli mai ikon ba.
Wannan baƙin hayaƙi ya sake bayyana a cikin wannan ɗaki, Samudul Ansari na ganin hayaƙin ya miƙe tsaye.
Siffar wannan mutumi ta bayyana wanda muka gani ya kira a saman tsaunin Hajarul Gorgon sa'adda yake fafatawa da ma'abota Bankai.
Wannan halitta bata numfashi, bata baƙin ciki, bata farin ciki, kai zaka ce bata motsi ma, saboda kamar gunki haka take tsaye shirim a gaban Samudul Ansari.
A wannan lokaci, asalin surarta ya bayyana yadda mutum zai iya ƙare masa kallo.
Mutumin dogo ne sosai, fasali da zubin jikinsa tamkar Samudul Ansari.
Abinda ya bambanta su da Samudul Ansari shi ne, wannan halitta bata kamanni kamar na mutane.
Komai na jikinta a lulluɓe yake da baƙin hijabi.
Daga sama har ƙasa wata doguwar baƙar alkyabba ce a jikinta mai samfurin kayan yaƙi.
A kansa kuma, wata irin hular sanyi ce mai zubin hular ƙarfe amma da auduga mai kauri aka ɗinka ta.
Wannan hular sanyi ta zamo tamkar shingen-tsafi wadda ya ɓoye fuskar sa.
Sarauniya Arya tana arba da wannan siffa ta zube ƙasa a tsakiyar wannan ɗaki.
"NI ARYA ƳAR SARKI HARUN NAYI MUBAYA'A GA TAU'RIN..." inji sarauniya Arya.
Abin mamaki ita kanta bata san sa'adda ta furta waɗannan kalmomi ba.
Waɗannan su ne kalmomin da duk wanda yayi arba da wannan halitta yake furtawa a duk lokacin da ta fito da ainihin siffarta.
Ƙarin bayani: Ba lallai bane mutum yayi mubaya'a ga wannan halitta musamman ma, idan ba'a cikin ainihin siffarta yake ba.
Halittar ta durƙusa a gaban Samudul Ansari cikin tsananin biyayya tamkar bawa a gaban shugabansa ta fara magana a cikin wata irin murya.
Muryar bata da kaushi, bata da taushi, bata nuna farin ciki sannan bata nuna baƙin ciki. Akwai iko na musamman a cikinta wanda yake sawa dole mutum ya nutsu ya saurareta.
"AN HALICCE NI DOMIN NAYI BIYAYYA [A GARE KA]
"NUMFASHINA SHI NE BIYAYYA [A GARE KA]
"ABINCINA SHI NE BIYAYYA [A GARE KA]
"RUWAN SHA NA SHI NE BIYAYYA [A GARE KA]
"BARCINA SHI NE BIYAYYA [A GARE KA]"
Wannan halitta na gama faɗin waɗannan kalmomi ya sake juyewa izuwa baƙin hayaƙi, sannan ya cikin jikin Samudul Ansari ta idanuwansa.
Samudul Ansari yayi shuru tsahon daƙiƙa ɗari da arba'in, har wannan baƙin hayaƙi ya gama shigewa izuwa cikin jikinsa.
Nan take gaba ɗaya jikinsa ya sauya.
Murɗewar jikinsa a yanzu ta ninka na da sau uku.
Ƙarfin damtsensa na yanzu ya ninka na da sau arba'in.
Wani kwarjini ya bayyana a gare shi wanda duk sarakunan duniya babu mai rabinsa.
A wannan siffa da Samudul Ansari yake, babu wanda ya isa ya tsaya a gabansa su yi cacar baki.
Babban sarki ne, wanda bin umarninsa ya zamo dole.
Sarauniya Arya ta zube a gaban Samudul Ansari cikin biyayya ta ce, "Ni sarauniya Arya nayi mubaya'a ga Tau'rin."
Sarauniya Arya ita ce mutum na farko da tayi arba da ainihin siffar Tau'rin (ma'ana na II) kuma ita ce mutum na farko da ta fara yiwa wannan ruhi mubaya'a.
Samudul Ansari ya taka da sawayensa ya ƙarasa inda take, ya sa hannayensa biyu ya ɗagota tsaye, ya rungumeta a ƙirjinsa yana cewa, "Nagode da wannan kyautatawa da kika yi min.
"Tabbas a yanzu na zamo cikakken shiryayye wanda zai kawar da ma'abota Bankai..."
Muryar Samudul Ansari tayi matuƙar sauyawa, ta ƙara kaushi da iko. Idan yana magana tamkar umarni ake sauƙarwa.
"Ina da magana," inji wannan ruhi wanda ke jikin Samudul Ansari.
Ya kamata a san cewa, wannan ruhi da ya shiga jikin Samudul Ansari yana da hankali da tunani nasa na kansa.
Saboda wannan dalili zasu iya tattaunawa da Samudul Ansari, ba tare da kowa ya sani ba.
Wannan na daga cikin amfanin wannan ruhi, wato ganawa da ma'abocinsa ba tare da kowa ya sani ba.
Wannan ruhi yana iya hango abu, nisan tafiyar zango metan. Komai zurfin teku, yana hango abinda ke can ƙasan ta.
Komai tsananin duhun waje, baya yiwa idanunsa wani abu.
Yafi ingarman doki gudu, yafi maridin aljani tashi sama, yafi kifi iya nutso a cikin ruwa.
Kai, amfanin wannan ruhi ba zai faɗu da baki ba, sai dai wanda ya mallake shi yasan abubuwan da yake kawai.
"Ina jin ka?" Samudul Ansari ya baiwa ruhin amsa.
Ruhin ya ce, "Mu koma ƙofar birnin Ilam, domin nan ne yafi dacewa mu yaƙi abokan gabar mu..."
"Meyasa?" inji Samudul Asari.
Kai tsaye wannan ruhi ya ce, "Saboda an riga an rubuta cewa, ba zamu samu nasara a wannan waje ba. Akwai wani munafuki wanda yake so ya tarwatsa wannan daula gaba ɗaya kuma shi ne zai yi sanadiyar rashin nasarar da za'a samu gobe."
"Ya kake so a yi kenan?" inji Samudul Ansari.
"Gobe da sassafe zamu janye daga wannan filin yaƙi, muje mu jira abokan gabar tamu a birnin Ilam..." inji ruhin.
"Idan muka janye kamar fa mun gaza ne, za'a iya mana dariya..." inji Samudul Ansari.
"SARKI BAYA TAƁA DURƘUSAWA...
"DURƘUSAWA WADA BA GAJIYAWA BANE...
"DA SANNU DUKKAN SARAKUNAN DUNIYA ZASU YI MANA MUBAYA'A!!!"
Kada dai manta, duk wannan tattauna take gudana tsakanin Samudul Ansari da wannan ruhi, sarauniya Arya dake gefe bata ji. Saboda daga shi sai wannan ruhi suke jin maganar juna.
"Shi kenan, zamu janye daga wannan yaƙi... Amma akwai yiwuwar samun nasara a ƙofar birnin Ilam kuwa?" inji Samudul Ansari.
"Ɗari bisa ɗari ma kuwa!" inji wannan ruhi.
Samudul Ansari ya koma kan wannan gado ya kwanta, Arya tana jin ya dawo ta sake hawa kan wannan gado ta kwanta a gefensa itama.
Samudul Ansari ya dubeta ya ce, "Mun gama yanke shawara zamu janye daga wannan yaƙi gobe, zamu koma ƙofar birnin ki, mu jira abokan gaba...!"
"Shawara?" inji sarauniya Arya. "Yaushe kuma da waye ka yanke shawarar?"
Samudul Ansari ya ce, "Yanzu ni da ruhina..."
Sarauniya Arya tayi gajeren tunani ta ce, "Amma akwai yiwuwar samun nasara acan kuwa?"
"Ɗari bisa ɗari..." inji shi.
Sarauniya Arya ta gyaɗa kai, sannan ta kwanta akan ƙirjinsa suka ci gaba da barci, har gari ya waye sannan suka yi wanka, suka kimtsa suka fito.
Gaba ɗaya sai da wannan sansani suka gane cewa, lallai babban sarki ya bayyana.
Babu wanda ya iya haɗa hanya da Samudul Ansari, da zarar sun haɗa hanya da mutum sai kaga mutum ya kauce ko kuma ya risina cikin biyayya, ba tare da sanin cewa ya risina ba.
A can cikin wani ɗaki kuwa, Gauhan ne zaune yana ta kukan takaici, yana dukan ƙasa da hannayensa biyu.
Yana cewa, "Ya aka yi haka? Ya ya aka yi ban hana Samud tarawa da yar-ƙabilar ARYA ba?"
Haka dai, ya ci gaba da takaici yana kuka bisa wannan ɗaukaka da Samudul Ansari ya samu.
Kai tsaye Samudul Ansari da sarauniya Arya suka ƙarasa sansanin dakarun ƙasarta, inda suka iske Zarifa tsaye a gabansu tana basu horon-yaƙi.
Tana ganin mijinta, ta ƙarasa gabansa ta risina cikin biyayya ta gaishe da shi.
"Ina son ki tara mana dukkanin waɗannan dakaru, saboda akwai wani saƙo mai muhimmanci da muke son mu sanar da su..." inji Samudul Ansari.
Zarifa ta risina cikin biyayya sannan ta koma ta tara dukkanin waɗannan dakaru a waje ɗaya.
Sarauniya Arya taje da kanta ta tsaya a gaban dakarun ta ce.
"Zamu janye daga wannan sansani, zamu koma ƙofar birnin mu. Tun da sun nuna basa buƙatar mu, abinda yafi mana shi ne, mu je mu kare birnin mu..."
Koda dakarunta suka ji wannan umarni, sai hankalin da yawa daga cikinsu yayi mummunan tashi.
A yadda ake ƙiyasi yawan abokan gabar da suke tafe, zai ninka su sau biyu ko sau uku.
Ya ya su da suka fi kaɗan ace su zasu fara janyewa.
Wannan yaƙi da yawa daga cikinsu suna ganin kamar fitowar banza kawai suka yi, amma sun yi imanin cewa baza su taɓa samun nasara ba.
Koda sarauniya Arya ta fuskanci halin da mayaƙanta suke ciki, saboda jin wannan umarni sai ta dube su ta ce.
"Muna tare da Tau'rin, ko ba komai shi zai kare wannan daula gaba ɗaya..."
Wannan batu ya kwantarwa wasu daga ciki hankali, amma wasu sun amince ne kawai domin suna so su ga zahirin ƙarfin Samudul Ansari.
"Nan da cikar sa'a biyu, nake so mu gama haɗa komai da komai namu, mu bar wannan sansani..." inji sarauniya Arya.
Mayaƙanta suka amsa mata da na'am zasu bi wannan umarni.
Sarauniya Arya ta koma wajen su Samudul Ansari da Zarifa suka fara tattaunawa akan sabon al'amarin.
Gauhan ya fito daga cikin wannan ɗaki da ya kulle kansa a ciki, tamkar ba shi ne yayi kuka da baƙin ciki bisa ɗaukakar Samudul Ansari ya samu ba.
Ya wuce tsakiyar wannan sansani inda aka sauƙe waɗannan sarakuna guda biyar, ya shiga cikin ɗakin da suke.
Bayan sun gama gaisawa Gauhan ya ce, "Nan da sa'a uku da rabi, mayaƙan ƙabilar Gorgon zasu ƙaraso wannan filin yaƙi, saboda haka kuzo muje mu fara shirin tunkarar su."
Ba tare da wani ɓata lokaci ba, waɗannan sarakuna suka bi wannan umarni da ya basu.
Koda suka ga rundunar sarauniya Arya ta janye daga wannan filin yaƙi sai suka fara yi musu dariyar mugunta, suna faɗa musu baƙaƙen maganganu.
Wannan ko kaɗan bai damu sarauniya Arya da mutanen ba, saboda sun san abinda su waɗannan sarakuna basu sani ba.
Gauhan gagara tsayawa yayi a gaban Samudul Ansari saboda bai isa yayi gaba-da-gaba da kwarjinin sa ba.
Amma dukda haka sai da ya faɗawa Samudul Ansari baƙar magana wadda ta ƙona masa rai, yaji kamar ya ƙaddamar masa da Saif-Al-Barzaƙ mai tafiya amma sai wannan ruhi ya hana shi.
Kafun cikar rabin sa'a tuni dakarun su Samudul Ansari sun bar wannan sansani gaba ɗaya.
Saboda tsananin yawan dakarun waɗannan sarakuna guda biyar, zaka iya cewa babu abinda ya ragu daga cikinsu dukda cewa mayaƙan Ilam sun janye.
Mayaƙa suka jeru a layi sahu-sahu suna jiran isowar abokan gaba.
Gauhan da waɗannan sarakuna guda biyar, suka tsaitsaya a gaban mayaƙan cikin gagarumar shiga ta yaƙi.
Gauhan ƙato ne na kwatance yana da tsaho da kauri sannan murɗaɗɗe ne sosai.
A wannan rana alkyabba irin ta mayaƙa ya saka ruwan-toka wanda ta bayyana tsahonsa.
Yana riƙe da zabgegiyar takobi mai zane-zanen taurari akan ƙarfenta.
Wannan takobi da ita Gauhan yake yaƙi, tun daga farkon fara gumurzunsa har zuwa wannan lokaci.
Tsahon rabin sa'a kacal, suna jira kafun su fara hango baƙar guguwa ta turnuƙe sararin samaniya a can nesa.
Ƙarar takun sawayen mayaƙa mai matuƙar razanarwa ta cika wannan waje gaba ɗaya.
Waɗansu irin mutane gabza-gabza suka fara bayyana acan nesa, dukkansu sanye da baƙaƙen tufafi.
Suna tafiya suna ihu da kirari suna wasa gashin kansu.
Wannan runduna ta mayaƙa ita ce, rundunar Gorgon [birnin Mesa da birnin Hazram] waɗanda sarauniya Yilan ta turo suyi farautar Samudul Ansari sannan su kai mata kansa.
Koda waɗannan sarakuna guda biyar suka hango yawan abokan gaba da kuma makaman yaƙin dake hannunsu, ai sai suka razana.
Kada ma ka kawo batun mayaƙansu waɗanda ke tsaye cirko-cirko.
Rundunar Gorgon suka tsaya a can nesa, suna ihu da ambaton sunan Samudul Ansari.
Waɗansu mahaya biyu daga cikinsu ya sako linzamin dawakansu suka zo tsakiyar wannan fili, suka tsaitsaya.
Gauhan ya dubi waɗannan sarakuna guda biyar ya ce, "Ku zo muje mu tattauna da waɗancan mutanen, don jin abinda ke tafe da su..."
Yana gama faɗin haka ya sakarwa dokinsa linzami, ya tunkari inda mahayan suke.
Waɗannan sarakuna guda biyar, suka take masa baya, jikinsu yana karkarwa.
Suna isowa inda mahayan suke aka yi kallon-kallo. Kafun ɗaya daga cikin Gorgon ɗin ya fara magana.
"Muna kira a gare ku, ku nuna mana inda Samudul Ansari yake.
"Muna kira a gare ku, ku zubar da makaman ku sannan kuyi mubaya'a ku zamo bayin mu.
"Muna kira a gare ku, ku dawo ADDININ BANKAI."
A hasale Gauhan ya dubi mutumin ya ce, "Zancen banza kenan! Sarki baya taɓa zamowa bawa face ya kasance sakare.
"Ƙarya kuke ku zo, har ƙasashen mu sannan ku mayar da mu bayi. Ƙarya ne.
"Mai ƙarfi ya ci..."
Sarakunan guda biyu, suka dubi Gauhan suka yi murmushi sannan suka juya suka koma cikin rundunar su.
Cikin tsananin tsorata waɗannan sarakuna suka dubi Gauhan suka ce, "Mene ne dalilin da yasa za ka faɗawa waɗannan mutanen baƙaƙen maganganu alhalin kamar da sulhu suka zo mana?"
Cikin tsananin fusata Gauhan ya dubi sarakunan ya ce, "Amma kun ji kunya... Manyan sarakuna kamar ku, su tsaya jin tsoro...
"Lallai ba ku dace da mulki a wannan daula ba, ni ne wanda yafi kowa dacewa ya mulke ta..."
Yana zuwa nan a zancensa suka ji ƙarar busa ƙaho daga cikin rundunar abokan gaba, alamar an basu umarnin afkawa su Gauhan.
Gauhan da waɗannan sarakuna suka juya cikin sauri suka koma cikin rundunar su.
Maimakon mayaƙan Gorgon su afko gaba ɗayansu, kawai mutane goma aka gani sun fito daga cikin rundunar suka tsaitsaya a gaba.
Nan take kowannensu ya zaro takobi mai siffar maciji wadda aka fi sani da BANKAI.
Cikin gaggawa suka aikawa su Gauhan saran takobi-mai-tafiya guda biyar-biyar.
Fai-fan haske guda hamsin suka fice daga takubban waɗannan mayaƙa, suka yiwo kansu Gauhan gadan-gadan zasu karkashe su.
Gauhan ya zaro wannan takobi tasa, shima ya sari iska da ita.
Nan take irin waɗannan taurari masu launin jini suka bayyana da yawa akan iska, kowanne tauraro guda ɗaya saiya haɗe da faifai guda ɗaya suka gwabzawa.
Iskar wannan wuri ta fara ƙugi, ƙasa ta soma girgiza.
Wannan yanayi ya addabi dakarun su Gauhan.
Cikin tsananin mamaki waɗannan sarakuna, suka dawo bayan Gauhan suka tsaitsaya.
Ba su taɓa zaton ya kai haka ba. Lallai ga dukkan alamu zai iya kuɓutar dasu daga sharrin ma'abota Bankai.
Sun tafka babban kuskure, basu san wane ne Gauhan ba, kuma basu san irin shirye-shiryen da yayi musu ba.
****
Yau *06/03/2023*
Babi na gaba zaizo *09/03/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 95: *Wasiyyar Sarakunan Gorgon*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra <3
*
U-M-S
*
~Sa'a guda, kafun ɗaura auren Samudul Ansari da sarauniya Arya.
*
Runduna ce ta mayaƙa masu tsananin yawan gaske tafe a cikin wani ƙungurmin daji mai yawan manyan tsaunika da kwazazzabai.
Kowannensu na zaune bisa ingarman doki suna ta kutsawa ta cikin wannan daji, babu tsoro ko kuma alamun shakku akan fuskar ɗaya daga cikinsu.
Duk da cewa idan ka lura sosai, zaka fuskanci cewa, wannan daji da suke ciki ba yankin ƙasar su bane, saboda babu mutum ɗaya da ya san hanya da wata taswira suke amfani suna kutsawa.
Kai, ƴan-fashi ko hauka suke idan suka hango wannan baƙar runduna guduwa suke izuwa cikin daji su ɓuɓɓuya saboda tsananin yawan rundunar da kuma kwarjininta.
Sannu-a-hankali wannan runduna ta fice daga cikin wannan daji mai yawan kwazazzabo, ta shigo cikin wani daji mai dogayen itatuwa da kuma manya-manyan koguna.
A gaban wannan runduna akwai manyan sarakuna guda biyu masu sanye da baƙaƙen tufafi mai kaurin gaske wanda aka ɗinka da irin wannan auduga wanda muka gani a jikin waɗannan mayaƙa guda biyu ma'abota Bankai da suka gwabza yaƙi da Samudul Ansari a saman tsaunin Hajarul Gorgon.
Suna shigowa cikin wannan daji, ɗaya daga cikin sarakunan ya ɗaga hannunsa sama, ya bayar da umarnin a tsaya.
Nan take kowa yaja linzamin dokinsa aka tsaitsaya.
Sarkin ya fiddo wata taswira daga cikin jakar tsafinsa ya dubata ya ce, "Saura tafiyar wuni guda cir, mu iso daular Shaha inda abin-harin mu Samudul Ansari yake.
"Kada dai a manta, umarnin sarauniya shi ne: A kamo wannan mutumi ko kuma a cizgo mata kansa."
Wannan basarake na gama faɗin haka, ya sake sakarwa dokinsa linzami suka afka cikin wannan daji, amma a wannan lokaci basa gudu sosai.
Tsahon sa'a guda suna ta tafiya a cikin wannan daji, kafun su yi kiciɓus da wani saurayi tsaye shi ɗaya a tsakiyar hanyarsu tamkar wanda ke jiran su.
Saurayin yana sanye da riga da wando na mayaƙa, sannan yana rataye da zabgegiyar takobi a gadon bayansa.
Cikin tsananin fusata wannan runduna tayi turjiya ta ba zato, sannan waɗannan sarakuna suka fiddo hoton wani mutum dake cikin wani madubi nasu suka duba shi da kyau.
Suka tabbatar da cewa, wannan wanda ke tsaye a gabansu, ba shi ne wanda suke nema ba.
"KAI!" ɗaya daga cikin waɗannan sarakuna ya dakawa wannan saurayi tsawa.
"Wane ne kai? Me kake taƙama da shi da har zaka tarewa ma'abota Bankai

Please Login or Register in order to submit comment