Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yan uwana muka tattauna akan shiryawa waɗannan jarumai gasanni, nima ina tafe da tawa.
"Saɓanin wannan gasa ta farko da ta kasance ta jarumtaka. Wannan gasa da na shirya amsa tambayoyi ce. Ina tafe da tambayoyi guda huɗu, sannan ina buƙatar a amsa min su dukka huɗun. Idan aka yi haka anyi nasara a wannan gasa ta biyu.
"Waɗannan jarumai sai su turo wanda zai gabatar da wannan gasa, ni kuma zan tura a kirawo min masana da masu ilimi na ƙasata domin a gudanar da wannan gasa. Nagode." Sarki Kayden na zuwa nan a zancensa ya koma ya zauna sannan ya ƙurawa su Marganu idanu.
Caraf Aydenlik ya ce, "Wannan gasa da ni ta dace, domin kuwa nima tsohon manazarci ne shiyasa na keɓe daga cikin mutane naje nayi ta bincike a gefe. Kada ka wahalar da kanka wannan gasa tawa ce."
Marganu ya yi murmushi ya dafa kafaɗar Aydenlik ya ce, "Ko kaɗan bana shakka akanka, tsoho. Fatan nasara!" Yana gama faɗin ya nufi inda Firziyya ke zaune.
Aydenlik ya yi murmushi sannan ya tunkari inda waɗannan sarakuna guda huɗu ke zaune, yana tafiya a hankali.
Mutane dake wannan wuri suka yi shuru tsitt, suka kasa kunnuwa saboda wannan gasa da za'a gudanar tana buƙatar shuru da bayar da hankali tunda kaifafa ƙwaƙwalwa za'ayi.
Sarki Kayden ya tafa hannayensa sau uku, take waɗansu malamai masu dogwayen gemu suka shigo wannan fili. Kowanne daga cikin su riƙe da ƙatoton littafi.
Sarki Wadu yasa waɗansu hadimai suka kawo kujerun zama waɗanda waɗannan malamai da tsoho Aydenlik zasu zauna akai.
Malaman suka zauna akan kujeru guda huɗu dake jere, sannan Aydenlik ya zauna akan guda ɗaya wacce take fuskantar su.
Sarki Kayden ya sake miƙewa tsaye ya fuskanci jama'a ya ce, "Dukkan tambayoyin da zan yiwa wannan tsoho, akwai su a cikin littatafan dake hannun waɗannan malamai sannan akwai amsoshin su. Idan har amsar da ya bayar tayi daidai, waɗannan malamai zasu gani a cikin waɗannan littatafa nasu.
"Idan har mai amsa tambayoyi ya gama shiryawa zan fara zayyano waɗannan tambayoyi da na shirya kamar yadda yake rubuce a cikin waɗancan littatafa..."
Aydenlik ya gyara kwalar rigarsa alamar ya shirya. Sarki Kayden yayi gyaran murya, mutanen dake wannan wuri gaba ɗaya suka yi tsitt.
Marganu, Firziyya da waɗannan sarakuna guda uku suka kasa kunnuwa sosai, suna so su ji waɗannan tambayoyi da Kayden zai zayyano.
"Tambaya ta farko," Kayden ya ci gaba da jawabi. "Wacce halitta ce tafi kowacce halitta ƙanƙanta a duniya?" ya tambayi Aydenlik.
Kowa dake wannan wuri yayi shuru, aka zubawa Aydenlik idanu ana jira ya bayar da amsa.
"Halittar da tafi kowacce halitta ƙanƙanta a duniya, a yankin ƙasashen yamma ake samunta. Ana kiran halittar da 'Suncus' bansan tayaya zan fassara muku sunan ta yarenku ba." inji Aydenlik.
Waɗannan malamai suka duba littatafan dake hannunsu na tsahon yan daƙiƙu, sannan suka ɗago kai suka ce, wannan amsa haka take, daidai ya amsa.
Mutane suka ruɗe da shewa ana ta yiwa ɗan tsohon kirari. Har sai da sarki Kayden ya ɗaga hannu, sannan aka yi tsit.
"Tambaya ta biyu," ya ci gaba. "Wanne makami ne yafi kowanne makami haɗari a duniya a halin yanzu?"
Ba tare da tunani ko wani dogon nazari ba, Aydenlik ya ce, "Makamin da yafi kowanne makami haɗari shi ne, takobin babban sarki Samudul Ansari ce da yake kira SAIF-AL-BARZAK, wacce ya yaƙi dukkanin abokan gabansa da ita."
Malaman suka sake duba littatafansu sannan suka shaidawa jama'a wannan amsa haka take.
"Tambaya ta uku, wanne wuri yafi ko'ina haɗari a duniya" Sarki Kayden ya tambayi Aydenlik.
"Tsibirin Gamsheƙu," inji Aydenlik.
Malamai suka sake tabbatar da amsar wannan tsoho haka take.
Sarki Kayden yayi murmushi kamar yana nuna tambayar da zaiyi ta ƙarshe, mai tsananin wahala ce. Sai da yayi murmushin mugunta sannan ya ce.
"Wace ce sarauniyar kyawu wacce tafi kowacce kyawu a duniya?" ya tambaya.
Aydenlik yayi shuru ya faɗa kogin tunanin mai zurfi. Ba wai bai san amsar wannan tambaya bace, sai domin amsar zata iya kasancewa guda biyu. Sarauniyar kyawun da ya sani tayi zamani ta shuɗe sannan an sake haihuwar mai kama da ita a wannan zamanin.
Abinda yake tsoro shi ne, kada ya ce wadda ta shuɗe ɗinne, kuma amsar wadda take raye yanzu ne.
Kafun kace kobo, Aydenlik ya fara haɗa zufa saboda yadda ƙwaƙwalwarsa take gasuwa. Mutane dake wannan wuri suka yi shuru, suka ƙura masa idanu.
Sarakunan nan guda huɗu suka fara murmushin jin daɗi da samun nasara. Marganu da Firziyya suka yi shuru suna kallon Aydenlik.
Idanun Aydenlik na kaiwa cikin na Marganu ya tuno duk irin kasadar da Marganu yayi a dalilin soyayya. Sannan ya tuno wacce tasa Marganu yayi wannan sadaukarwa.
Tabbas bayan kyawu da Marganu ya gani tattare da wannan gimbiya akwai wani babban sirri wanda yasa ya kamu da mahaukacin sonta, har ya makance ya daina ganin komai idan ba soyayyarta ba.
Aydenlik ya ce, "GIMBIYA ARYA II" yana cewa a ransa, koda ba haka bane amsar Marganu ba zai zargeni ba, saboda ya kusan rasa rayuwarsa akan ta.
Sarki Kayden ya zaro idanu cikin tsananin mamaki, bai taɓa tunanin nazarin Aydenlik ya kai kan gimbiya Jaanu ba. Saboda mutanen da suka san ita ce magajiyar Arya basu da yawa.
A wannan karon waɗannan malamai basu duba littatafan dake hannunsu ba, saboda wannan amsa a kansu take.
Mutanen garin Maban babu abinda suka ƙware akansa face bincike da nazari akan halittun ubangiji. Duk bayanan wani abu da mutum ke buƙata a duniya, indai yazo wajensu zai same shi.
Malamai suka tabbatar da cewa Aydenlik ya amsa dukkanin wadannan tambayoyi guda huɗu daidai.
Jama'a suka ruɗe da shewa. Sarki Wadu ya tashi yayi jawabin bankwana sannan ya sallami dukkanin jama'ar dake wannan wuri, akan cewa za'a haɗu gobe domin ci gaba da wannan gagarumar gasa.
Aydenlik, Marganu da Firziyya suka sake komawa cikin wannan gida nasu. Marganu yana ta wasu-wasi a ransa game da amsoshin da Aydenlik ya bayar. Musamman gimbiya Arya, kwata-kwata bai san wace ce ba.
Amma sai ya ƙudurce a ransa akan cewa zai tambayi tsohon yayi masa bayani filla-filla.
****
Yau *05/01/2023*
Babi na gaba zaizo *07/01/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 68: *ARYA II*
*
DEDICATED TO PRINCESS ZAHRA.
*
COPYRIGHT @Umarsangaru
*
Su Marganu suna komawa gida, Firziyya ta haɗa musu abincin dare ta kawo musu a inda suka saba zama. Ta sakawa kowannensu a cikin kwanon cin abincinsa sannan suka zauna suka fuskanci juna.
Kafun Marganu ya yi loma guda ya dubi tsoho Aydenlik ya ce, "Tayaya aka yi kake bada amsoshi ɗazu cikin kwanciyar hankali, amma da aka zo tambaya ta huɗu sai da ka haɗa zufa kafun ka bayar da amsarta?
"Wacce takobi ce, SAIF-AL-BARZAK? Wane ne Samudul Ansari da naji ka kira shi da babban sarki?
"Wace ce ARYA ta farko, da naji amsar da ka bayar ta ƙarshe ta zamo 'Arya ta biyu?'" Marganu ya tambayi tsohon.
Tsoho Aydenlik ya cire hannunsa daga cikin kwanon abincin dake gabansa sannan ya dubi Marganu ya ce, "Takobin Saif-Al-Barzak babu wanda yasan bayanan komai akanta, saboda duk waɗanda wannan takobi ta yiwa illa sun riga mu gidan gaskiya. Babu inda za'a samu cikakkun bayanai akanta face wajen tsoho Samazan dake yankin birnin Hindu.
"Shi kuma Samudul Ansari wani babban sarki ne da yayi zamani ya shuɗe shekaru aru-aru da suka gabata, idan baka manta ba Isika ya ce mana, makaman yaƙin wannan sarki zasu yi tasiri akanka da shi kansa. To wannan sarki shi ke da mallakin wannan takobi ta Saif-Al-Barzak, kuma a halin yanzu tana ajiye a inda ruhinsa yake.
"Babu mai mallakarta kuma ya sarrafata face wanda ya gaji ruhin wannan sadaukin sarki." Aydenlik na zuwa nan a zancensa ya ɗauki ruwan inibi ya kora, Marganu da Firziyya suka gyara zama saboda a yanzu za'a zo gaɓar da suke buƙatar ji, wato bayanan Arya II.
Aydenlik ya ci gaba, "Arya ta farko, wata gawurtacciyar sarauniya ce da tayi zamani a shekaru masu yawa da suka wuce, sannan ance ita ce matar da Samudul Ansari ya aura. Wannan sarauniya yar wata ƙabila ce wadda jininsu yake da sirri mai ƙarfi wanda har yau, har gobe babu wanda yasan adadin amfaninsa. Amma, yana daga cikin amfanin wannan jini nasu, duk wanda yayi tarayya da wannan jini zai sami ɗaukaka kuma saiya gawurta a duniya.
"Wasu suna cewa wannan yana daga cikin dalilan da suka sa Samudul Ansari ya sami ɗaukaka a duniya kuma harma yayi suna. Koma dai mene, jinin yan ƙabilar Arya yana da ƙarfi wanda hatta manyan bokayen duniya sai da suka yi amanna da haka.
"Arya II: Ita ce wadda ka haukace akanta a shekarun baya, ita ce tasa ka kusa salwantar da rayuwarka a banza. A taƙaice dai, ita ce Gimbiya Jaanu yar sarki Ayubu na birnin Damashkar.
"Kana tunanin a banza ka kamu da ƙaunar gimbiya Jaanu farat ɗaya sannan ka fara kallon dukkanin sauran matan dake duniya a matsayin mazaje?
"Kana tunanin a banza idanuwanka suka makance, baka kalli haɗarurrukan dake kan hanyar zuwa dajin Marsas ba, ka ɗauko fursuna, ka kaita can domin a baka gimbiya Jaanu?
"Shin baka taɓa tunanin dalilin da yasa ka gagara yiwa Jaanu komai ba, a lokacin kuke kan hanyar ku ta dawowa, dukda ka fuskanci baka samu karɓuwa a wajenta ba?
"Wannan kaɗan ne daga cikin sirrin ƙabilar ARYA. Koda Jaanu zata buɗi ta cewa sarki Ayubu ga wanda take so, babu yadda ya iya da ita domin ba zai iya yi mata komai ba.
"Shin ka ta taɓa tunani akan dalilin da yasa Jaanu ta ƙi ka?
"Duk abinda ake buƙata a wajen namiji kana da shi. Ga ka saurayi, kyakkyawa, jarumi kuma ɗan sarki. Babu wadda ba zata yi mafarkin samunka a matsayin mijinta ba.
"Gaskiyar al'amarin shi ne ita kanta Jaanu bata san dalilin da yasa ta tsaneka ba. Abinda kai da ita baku sani ba shi ne, ruhin Jaanu da ruhi guda ɗaya kawai zaiyi tarayya a duniya. Idan ba wannan ruhi ba, babu ruhin da ya isa ya mallaki nata.
"Zamani mai tsaho da ya shuɗe ARYA ta farko tayi rayuwa da jarumi mai RUHIN JARUMTAKA na farko wato Samudul Ansari, kuma dukkaninsu sun sami ɗaukaka sakamakon auren da suka yi.
"BABBAN DALILIN DA YASA JAANU TA TSANEKA SHI NE SABODA BA DOMIN KAI AKA HALICCI RUHINTA BA, RUHIN JAANU DA JARUMI MAI RUHIN JARUMTAKA NA BIYU KAƊAI ZAIYI TARAYYA.
"Shekarun baya ka wahalar da kanka ne kawai, ko me zaka yiwa Arya ba zata taɓa amincewa da kai ba. Koda kuwa mazaje sun ƙare a duniya ba zata aure ka ba. Mijinta guda ɗaya ne kuma shi ne magajin Ruhin Jarumtaka na biyu."
Marganu na gama jin wannan jawabi na Aydenlik yaji wani sabon takaici ya rufe shi. Tun sa'adda Jaanu ta ce bata son shi a wannan tattaunawa daga wannan lokaci ta fita a ransa.
Komai irin son da kake yiwa mace ace ta furta bata sonka, sannan hakan ya janyo sanadiyar mugun yaƙi a birninka dole ne ka tsaneta.
"Ban damu da wace ce ita ba, babbar damuwata a yanzu shi ne yadda zan fille kanta domin ɗaukarwa mahaifina fansa bisa abinda ta janyo aka yi masa." inji Marganu cikin ɗacin rai.
"Shi kuma magajin RUHIN JARUMTAKA na biyu, ba zan taɓa bari ya mallaki wannan ruhi ba, saboda mallakar wannan ruhi yana da mugun haɗari a gare ni." Marganu ya ci waɗannan alwashi.
Tsoho Aydenlik da gimbiya Firziyya suka yi shuru suna kallonsa, irin waɗannan alwashi da yake ɗauka basu da ikon saka baki a ciki.
Gimbiya Firziyya kwata-kwata bata san waye Aymanul Faris ba amma tana yawan jin sunansa a bakin mahaifinta. Amma Aydenlik yasan waye Aymanul Faris sarai da kuma haɗarinsa.
Koda Aydenlik yaga wannan alwashi bai shafe su ba, sai ya fara kawar da maganar. "Gasar da za'a yi gobe, kaine wanda zaka gudanar ko?"
Marganu ya ce, "Kwarai ma kuwa kuma nasan zanyi nasara."
Zuciyar Firziyya ta gama yin fari saboda tsananin farin cikin da take ciki, Marganu ya tsani Jaanu har ta kai matsayin da bai da buri wanda yafi ya fille kanta. Tun da ya tsani gimbiya Jaanu lallai ta gama samun kyakkyawan matsayi a wajensa.
Haka dai su Marganu suka ci gaba da cin abinci a wannan wuri, suna tattaunawa har dare ya soma rabawa sannan suka yi sallama da juna kowa ya shiga ɗakinsa.
Marganu na kwanciya a cikin ɗakinsa, ya gagara barci. Ba komai ne ya hana shi yin barci ba, face tunanin abubuwa guda biyu.
Abu na farko shi ne Aymanul Faris wanda Aydenlik ya ce, shi ne magajin ruhin jarumtaka na biyu. Abu na biyu shi ne tunanin gimbiya Jaanu da maganganun da Aydenlik ya faɗa akanta.
A waje guda ɗaya ya taɓa yin arba da Aymanul Faris, kuma tabbas shi kansa sai da ya tabbatar da cewa Aymanul Faris dabam ne. Bai taɓa kallon jarumi kamar sa ba. Dukda cewa bai taɓa ganin jarumtakarsa ba kuwa.
Babban abinda ya ɓata masa rai shi ne, baisan a ina zai sami Aymanul Faris ba. Ba don komai Marganu ke son fafatawa da Aymanul Faris ba sai domin yana so ya gwada jarumtakarsa akan tasa.
Watannin baya da suka shuɗe ya sami labarin Aymanul Faris da maigidansa Barban sun kai hari birnin Askandariyya da birnin Fairul Faizar.
A yadda yake samun labarin sadaukai jinin Rau'an da Aymanul Faris ya fafata da su, ya fuskanci cewa lallai Aymanul Faris gawurtaccen jarumi ne.
Marganu baisan meyasa ba, tun da yake a rayuwarsa sau ɗaya ya taɓa kallon Aymanul Faris amma yana yawan tsaya masa a rai. Haka kawai sai yayi ta tunanin Aymanul Faris da irin hatsabibancinsa.
Wannan abu yana ɓatawa Marganu rai, sannan yana matuƙar bashi mamaki duk a lokaci guda. Wai shin waye wannan Aymanul Faris ɗin da ya addabi zuciyarsa.
Da farko yayi tunanin ko domin suna soyayya da Jaanu ne, yasa ya tsani Aymanul Faris amma daga baya ya fuskanci ba haka bane. Domin kuwa tun kafun Jaanu ta san waye Aymanul Faris ta san shi, sannan ta san abinda ke ransa.
Amma ahakan bata amince da shi ba. Tabbas kalaman da Aydenlik ya faɗa a ɗazu gaskiya ne, wato ba domin shi aka halicci ruhinta ba. Tabbas wannan shi ne dalilin da yasa ta tsane shi, idan ba haka ba babu wani abu da zai sa ta tsane shi.
Yana cikin tunane-tunanensa ya kai kan Arya ta biyu. Wannan gimbiya ita ce silar taɓarɓarewar komai da komai na rayuwarsa.
Ba don soyayyarta ta makantar da shi ba, da yanzu yana birninsu hankalinsa kwance. Amma tuni aikin gama ya gama.
Marganu yayi tunanin idan suka mallaki wannan takobi yayi amfani da ita ya hallaka sarki Kuffuru da aljaninsa, waɗanne irin abokan gaba zai samu a wannan daula.
Tunda indai ya taka irin matsayin da sarki Kuffuru ya taka, zai tara abokan gaba a wannan daula da ma dukkanin duniya gaba ɗaya.
Lallai akwai gagarumin aiki a gabansa wanda ya zamo dole ya samu lokaci yayi tunani mai kyau akansa, tun kafun lokaci ya ƙure masa. Ma'ana tun kafun ya hau matsayin da sarki Kuffuru ke kai.
Haka dai Marganu ya ci gaba da tunane-tunane a cikin ransa, har barci ya sace shi bai sani ba.
Da sassafe yana farkawa, ya shiga banɗaki yayi wanka sannan ya ɗauko kayan yaƙinsa ya sanya. Ya fito daga cikin wannan ɗaki da ya kwana a cikinsa, inda ya iske Aydenlik da Firziyya zaune suna jiransa.
Marganu ya ɗaga kansa ya dubi inda rana take, yaga ashe tuni gari ya jima da wayewa shi ne bai farka da wuri, kuma ga dukkan alamu su Aydenlik sun jima suna jiransa.
A hankali ya ƙarasa inda suke zaune, bayan sun gama yiwa juna barka da kwana, suka afkawa abinci. Suka ci suka ƙoshi sannan suka tashi suka nufi fada.
Suna isowa fadar suka iske tuni ta gama cika fiye da kowacce rana, ga waɗancan sarakuna guda huɗu a zazzaune bisa kujerunsu. A gefe guda kuma, wani ƙaton tanti aka kafa wanda ga dukkan alamu baƙin mutane aka ajiye a ciki.
Sarki Wadu na ganin su Marganu sun shigo cikin wannan fada, ya tashi ya yiwa jama'a jawabi kamar yadda ya saba, daga ƙarshe ya kirawo sarkin garin Kulsi ya tashi domin ya gabatar da yanayin gasarsa.
Wani narkeken ƙaton mutum dogo kuma kakkaura ya miƙe tsaye, ya fuskanci jama'a ya ce, "Suna na sarki Ardad, ni ke wakiltar garin Kulsi a wannan gasa da aka shiryawa waɗannan baƙin matafiya waɗanda suka ratso ta cikin wannan yanki namu.
"Mu a garin mu bama taƙama da komai face kokawa, shiyasa yanayin gasar da na shiryawa waɗannan jarumai ta shafi wannan al'ada tamu ƙwarai da gaske. Wancan tantin da ake hangowa a baya, ƙanina ne a ciki. Ina so ɗaya daga cikin waɗannan jarumai ya tare shi sannan ya kaishi ƙasa. Indai yayi hakan ya ci wannan gasa da na shirya. Nagode."
Sarki Ardad na zuwa nan a zancensa ya koma ya zauna. Marganu ya dubi Aydenlik da Firziyya ya ce, "Ku koma can ku zauna, yau rana ta ce."
Aydenlik ya risina sannan ya juya ya tafi. Gimbiya Firziyya ta ɗaura hannayenta biyu kan kafaɗun Marganu ta ce, "Masoyina, na san zaka yi nasara. Ka kula min da kanka, rayuwarka ita ce rayuwata."
Marganu ya dubeta ya ce, "Kada ki damu, matata ta gobe. Yadda ba ku bani kunƴa ba, nima ba zan ku ba." Yana faɗin haka ya koma tsakiyar wannan fili ya tsaya.
Wani gagarumin farin ciki ya sake lulluɓe Firziyya taji tamkar kanta zai fashe. A duniya babu abin farin cikin da yafi rayuwa da masoyi.
Marganu na tsaye yaji waɗansu irin taku na tunkaro shi ta baya, cikin kwanciyar hankali ya waiga.
Wani zabgegen ƙaton mutum ya hango yana shigowa cikin wannan fili. Saboda tarin ƙwanjinsa da murɗewar jikinsa har ɗan doro yayi. Yana da zaratan hannaye da lafta-laftan sawaye.
Idanuwansa ko kama da na masu imani basu yi ba. Tun da ya shigo wannan fili ya ƙurawa Marganu idanu.
Yana isowa gaban Marganu ya kwaɓe wata alkyabba da ta lulluɓe jikinsa, nan fa zabgegen ƙato ya bayyana wanda koda a takarda mutum ya kalle shi, dole ne ya razana.
Mutumin da Marganu suka yi kallon kallo na tsahon daƙiƙu, kafun daga bisani ya tako yazo gaban Marganu ya tsaya.
"Suna na Gundalu. Ni ne sarkin ƙarfi na wannan yanki namu gaba daya. Na samu labarin zuwanku shiyasa na shiga wannan gasa domin na hanaku wucewa. Tabbas idan na kayar da kai a wannan gasa, mutanenmu ba za su barku ku wuce ba." inji wannan sadauki da ya kira kansa da suna Gundalu.
Marganu ya yi murmushi ya ce, "Koda kaine sarkin ƙarfi na duniya, ba zanyi shakkar ka ba. Duk jarumin da ya yarda da kansa, babu abinda zaiyi shakka a duniya, indai ina numfashi kuma ina cikin hayyacina, zanyi nasara akanka."
Sadauki Gundalu na jin batun Marganu ya bushe da mahaukaciyar dariya wadda tayi amsa kuwwa a cikin wannan fili. Gundalu ya ɗaga hannayensa sama alamar yana so a fara wannan gasa.
Nan take sarki Wadu ya dubi wani hadimi yayi masa wata inkiya, take hadimi ya fiddo sandunan buga gangarsa sannan ya bugata sau uku.
Gundalu da Marganu suna jin an buga wannan ganga suka ruga da gudu, suka fara kewaye juna. Kowa daga cikinsu yana nazarin ta inda zai fara kaiwa ɗan uwansa hari.
Cikin shammace Gundalu ya kaiwa Marganu wawura da nufin ya kama shi a hannu, Marganu ya daka tsalle baya, Gundalu ya wawuri iska.
Kafun ya sake kawo masa wani hari. Marganu ya taƙarƙare ya gabza masa naushi a ƙirji. Saboda ƙarfin naushin sai da naman wajen yayi rawa.
Sadaukin yayi ihu. Cikin shammata ya kaiwa Marganu naushi a gefen ƙirjinsa na hagu, cikin zafin nama Marganu ya kauce. Sai dai dama wannan dama ita wannan sadauki yake jira.
Yayi amfani da wannan dama ya gabzawa Marganu naushi a ɓangaren ƙirjinsa na dama. Saboda ƙarfin wannan naushi sai da Marganu yayi aman jini ta bakinsa.
Sadauki Guntalu na ganin haka yayi murmushi ya sake gabzawa Marganu wawan naushi a ciki, saboda ƙarfin wannan naushi sai da Marganu yayi tsalle baya, amma bai faɗi ƙasa ba.
Cikin tsananin juriya da jarumtaka ya dake a inda yake tsaye, yana aman jini.
Sadauki Guntalu ya ɗaga hannayensa sama, jama'ar waɗannan garuruwa suka yi ta kuranta shi.
Wannan abu yayi matuƙar ɓatawa Marganu rai, yana matsayin babban jarumi wanda keda burin tarwatsa gawurtattun mutane a duniya. A ce irin waɗannan jarumai marasa asali suna zubar masa da jini?
Cikin tsananin fusata ya kwarara uban ihu sannan ya ruga da gudu kan Gundalu, Gundalu na jin haka ya rugo da gudu shima ya yiwo kan Marganu.
Saura taku huɗu su haɗu suka daka tsalle sama da nufin suyi mugun gamo a sama. Dukda cewa sun kaiwa junansu mugayen hare-hare amma babu wanda ya samu ɗan uwansa.
Sai dai suna dirowa ƙasa, Marganu ya shammaci Gundalu ya kamo hannunsa ta baya ya murɗe. Gundalu ya kawowa Marganu mangara da ɗaya hannunsa amma cikin zafin nama Marganu ya goce.
Marganu ya tattaro ƙarfinsa gaba ɗaya yasa gwiwar ƙafarsa da karfi ya doki ƙashin hannun Gundalu. Nan take ƙashin ya haifar da wata ƙara, alamar ya karye.
Komai tsananin ƙarfin abu indai Marganu ya doke shi da gwiwar ƙafarsa yana iya karyewa. Ta wannan ɓangaren Allah ya baiwa Marganu wannan baiwar.
Sadauki Gundalu ya ɗaga kansa sama ya kurma wawan ihu wanda ya firgita da yawa daga cikin yan kallo.
Kafun ya dawo hayyacinsa Marganu ya sake kamo ɗaya hannun, sannan shima ya aikata masa kamar yadda ya yiwa na farko.
Sadauki Gundalu ya durƙushe ƙasa bisa gwiwowinsa yana kwarara ihu sakamakon tsananin zogin dake shiga jikinsa. Marganu yasa ƙafarsa ya doki ƙirjin Gundalu.
Gundalu ya baje a tsakiyar yashin da ke wannan fili, yana ta kwarara ihun wahala.
Marganu ya ɗaga hannayensa sama alamar yayi nasara. Nan take sarki Wadu ya dubi hadimin dake buga gangunan nan, yayi masa inkiya.
Hadimin ya buga gangar tsayar da gasar sannan aka tabbatar da Marganu a matsayin wanda yayi nasara.
Waɗannan sarakuna da mutanensu gaba ɗaya sai da suka girgiza bisa ganin yadda akayi Marganu ya iya kai Gundalu ƙasa. Saboda sun san waye Gundalu da tsananin ƙarfin damtsensa.
Marganu, Firziyya da Aydenlik suka koma gidansu, Marganu ya sakawa raunikan jikinsa magani suna jiran gari ya waye domin a ci gaba da wannan gasa.
Gari na wayewa kuwa, suka tafi fadar wannan gari. A wannan rana sarki Wadu ya shirya gasar da za'a yi. Bayan kowa ya gama hallara ya tashi jawabi sannan ya faɗi yanayin yadda gasarsa zata kasance.
Yanayin wannan gasa shi ne, wani dogon itace aka kawo mai tsananin tsaho sannan aka ɗaura mutum-mutumi a can ƙarshensa. Saboda tsananin tsahon wannan itace, mutum zai na hango wannan mutum-mutumi ɗan ƙarami tamkar yar tsana.
Aka kawo kwari da baka aka baiwa Marganu, aka ce ya harbo kan wannan mutum-mutumi. Idan ya harbo kan mutum-mutumin yayi nasara a wannan gasa.
Marganu ya yi murmushi ya karɓi wannan kwari da baka, ya saka kibiya guda ɗaya yaja ya ɗame sannan ya ɗagata sama, ya saita wannan mutum-mutumi da kyau sannan ya saki harbi.
Wannan kibiya ta tafi da gudu amma

Please Login or Register in order to submit comment