Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mazauninta sannan ya juya wajen da Aydenlik da Firziyya suke. Abinda ya gani shi ne yayi matuƙar bata masa rai.
Jaruma Firziyya tana tsakiyar waɗannan kadoji da sauran halittun ruwa, tana ta saransu gami da sukarsu. Duk inda tasa a gaba sai dai kaga sassan jikin halittun na yawo a cikin iska, jininsu kuma yayi ta malala a wannan wuri tamkar daga cikin teku yake ƙwaranyowa.
Firziyya jarumar gaske ce mai tsananin zafin nama da iya yaƙi, idan mutum yaga yadda take ta hallaka waɗannan halittu zaiyi zaton aljana ce.
Babbar matsalar dabbobin dake rayuwa a cikin wannan daji shi ne, basu da iyaka. Suna mutuwa sannan suna jin raunika amma yawansu ya wuce tunanin mutum.
Jaruma Firziyya ta kashe, ta kashe har ta gaji amma ko rabinsu bata ƙarar ba. Har a wannan lokaci ƙara ɓullowa suke daga cikin waɗannan kwazazzabai da ƙoramu.
Tana cikin gumurzu da dabbobin kenan, taji wata ƙatuwar jela ta doki gadon bayanta da ƙarfi. Saboda ƙarfin wannan duka sai da ta tashi tamkar daga cikin baka aka harbata.
A cikin wani ƙaramin tafki ta faɗo sannan ta nutse izuwa cikinsa. Bata kai can ƙarshen wannan tafki ba, wani abu ya sake dukanta ta sake tashi sama ta faɗo a can nesa a wajen wannan tafki.
A galabaice Firziyya ta miƙe zaune sannan ta buɗe idanunta. Ai kuwa wata zabgegiyar macijiya ta gani acan nesa ta kanannaɗe jikinta tana furzar da dafi daga cikin bakinta.
Jikin macijiyar jajawur ne amma yana da ɗiso-ɗison baƙi wanda ya ƙara mata kwarjini. Idanuwanta kuma tamkar baƙar tawada haka suke saboda tsananin baƙi.
Macijiyar ta saki jikinta a hankali ta nufo inda Firziyya ke zaune, bakinta na fesar da wannan dafi, idanuwanta a tsaye cak akan Firziyya. Waɗannan idanu nata idan ta sakawa mutum su, zaiji tamkar za'a janƴe shi cikinsu.
Cikin dakewa da jarumtaka Firziyya ta miƙe tsaye sannan ta sake zaro waɗannan takubba nata guda ta fuskanci wannan fuskanci. Tabbas Firziyya ba ƙaramar jaruma ba ce, domin bambancin ta da wannan macijiya tamkar bambancin dake tsakanin ƙaton ƙadangare ne da malam buɗa-littafin.
Macijiyar na ƙarasowa gaban Firziyya suka fara kallon-kallo cikin nutsuwa. Firziyya ta ƙurawa idanun wannan macijiya idanu, dukda cewa ji take a jikinta tamkar za'a janƴeta izuwa cikin idanun.
Firziyya bata da ikon juyawa baya da gudu domin wannan macijiya zata iya amfani da jelarta da dokota ƙasa, sannan idan tace zata tsaya fuskantar wannan macijiya gaba-da-gaba zata watso mata dafi ta hallaka ta.
Saboda waɗannan dalilai guda biyu yasa Firziyya yin tunanin abinda ya kamata tayi. Tsahon dakiƙu ashirin kafun ta yanke shawarar abinda ya kamata tayi.
Ɗalasimin ƙabilar Gandiz ta ƙaddamar a wannan wuri, dusar ƙanƙara mai tsananin yawan gaske tamkar ruwan sama ta soma sauƙowa wurin. Kwazazzabai da ƙoramun wannan wuri duk suka ƙafe, suka zamo ƙanƙara. Dukkan halittun dake fitowa daga cikinsu suka daskare.
Kai tsaye wannan dusar ƙanƙara ta fara sauƙa akan wannan macijiya dake tsaye a gaban jaruma Firziyya tana shirin kawo mata farmaki. Maimakon jikin wannan macijiya ya daskare kamar yadda sauran halittu suka daskare.
Wani irin hayaƙi ne ya fara tashi daga jikin wannan macijiya tamkar gobara a ruwa. Kai da gani babu tambaya ka san cewa wannan dusar ƙanƙara babu abinda zata yi mata.
Wannan hayaƙi ya ci gaba da tashi a wannan wuri, ya cike wurin gaba ɗaya yadda mutum ba zai na ganin abinda ke faruwa ba. Wannan macijiya tayi amfani da wannan dama ta kawowa jaruma Firziyya da wangamemen bakinta.
Jaruma Firziyya bata san abinda ke faruwa ba, sakamakon wannan hayaƙi mai kauri da ya lulluɓe wannan wuri. Amma Marganu yana ganin komai albarkacin waɗannan idanu nasa na haske kuma wannan shi ne dalilin da yasa ya fusata.
A ɓangaren Aydenlik kuwa, duk tsananin yawan waɗannan dabbobi da zarar ya jefe su da dutsen-tsafinsa guda sai kaga kibiyoyi masu yawan gaske sunje sun caccake su. A tsakiyar iska Aydenlik ya tsaya ya fuskanci waɗannan halittu. Shi ba'a ƙasa ba, kuma ba'a sama ba.
Waɗannan halittu sun rasa yadda zasu yi dashi, in banda kashe su babu abinda yake. Damisosin kawai fitowa suke daga kogunan bishiyoyi sun ƙi ƙarewa su ma. Aydenlik ya kashe, ya kashe har ya gaji amma sun ƙi ƙarewa.
Yana tsaye a tsakiyar iska yana ta kashe damisosi da birirrukan kenan, yaji wata ƙatuwar halitta ta yiwo tsalle daga ƙasa ta doke shi. A galabaice ya faɗo kan ƙasa sannan ya waiga da baya da sauri saboda jin ƙarar sauƙar wannan halitta a bayansa da sauri.
Wani ƙaton gwaggon biri ya gani baƙi ƙirim, dogo mai murɗaɗɗen jiki. Idanuwansa kamar garwashi saboda tsananin jan su. Wannan gwaggon biri ya tunkaro inda Aydenlik ke zaune yana wani irin taku mai haifar da ƙaramar girgizar ƙasa a wannan daji.
Aydenlik ba shi da ikon kare kansa daga sharrin wannan gwaggon biri, sakamakon muguwar faɗuwar da wannan gwaggon biri yayi masa.
Marganu na ganin komai kuma wannan shi ne dalilin da yasa ya sake fusata. Dole sai yaje ya ceci abokan tafiyar nasa guda biyu, idan ba haka ba kuwa, Firziyya tana fuskantar barazanar haɗiya daga wannan macijiya. Aydenlik yana fuskantar barazanar wannan ƙaton gwaggon biri.
Ba zato! Waɗansu dabbobi dabam suka fara fitowa daga cikin waɗannan ramuka waɗanda suka fi waɗannan zakuna da kuraye bala'i. Marganu na ganin haka ya murtuƙe fuska, ya dafa wannan hatimin haske dake bisa damtsen hannunsa na hagu.
Nan take jikinsa ya juye izuwa haske, waɗannan dabbobi suka ɗinga rugowa da gudu suna bangazarsa, amma tamkar babu suke bangaza. Babu abinda ya samu Marganu wucewa ma suke ta cikin jikinsa.
A wannan siffa da Marganu yake ciki babu abinda zai iya ratsawa ta cikin jikinsa face waɗannan makaman yaƙi da aljani Isika ya lissafa masa.
Cikin kwanciyar hankali ya daka tsalle yasa takobinsa, ya raba wannan macijiya gida biyu wacce take shirin haɗiye jaruma Firziyya. Takobinsa ta haske ta ratsa ta cikin gangar wannan macijiya, ai kuwa ta rabe gida biyu gangunan jikin nata suka faɗi a gefe.
Jaruma Firziyya ta ɗaga kanta ta kalli Marganu cikin tsananin mamaki, amma a wannan siffa da yake ciki bata isa ta ɗauki lokaci mai tsaho tana kallonsa ba, saboda tsananin hasken dake jikinsa.
Marganu ya ruga da gudu ya nufi inda wannan gwaggon biri yake, kafun ya ƙarasa wajen da tazarar taku bakwai, ya daka wawan tsalle yasa ƙafafuwansa biyu ya doki ƙirjin wannan biri.
Duk tsananin jarumtaka da dakewa irin ta wannan biri sai da ya ja baya saboda tsananin ƙarfin damtsen Marganu.
A fusace wannan biri ya yiwo kan Marganu, yana wani irin gurnani tamkar zai ci babu. Marganu na ganin haka yayi murmushi ya aika masa da wawan sara da wannan takobi dake hannunsa.
Wani irin kaifi ya fice daga tsinin wannan takobi tamkar haske, haka yaje ya fille kan wannan biri. Kan nasa ya guntule ya faɗi ƙasa, gangar jikinsa ta tafi ƙasa a hankali a itama.
A wannan lokaci waɗannan dabbobi sun sake ƴanƴame jaruma Firziyaya a tsakiya, sannan waɗanda ke kan bishiyoyi da doron ƙasa suna shirin afkowa Marganu da Aydenlik.
Marganu ya tabbatar da cewa in dai suka ce zasu tsaya yaƙi da waɗannan dabbobi zasu shekara basu ƙarar da su ba saboda tsananin yawansu.
Saboda wannan dalili yasa ya matsa kusa da Aydenlik yasa hannunsa guda, ya doki gefen wuyan tsohon take ya sulale ƙasa sumamme. Marganu ya cicciɓe shi, ya goya a gadon bayansa, sannan yayi ta ratsawa ta cikin waɗannan dabbobi ba tare da ya taɓa koda guda daga cikinsu ba, kuma koda sun kawo masa hari ma basa samun jikinsa saboda ya riga ya juye izuwa haske.
Marganu ya ƙarasa kusa da Firziyya itama ya sumar da ita, sannan ya saɓa ta a kafaɗarsa ya ratsa ta cikin waɗannan dazuzzuka ya fice daga cikin wannan daji, ba tare da ya sake wani yunƙuri na cutar su ba.
Dukda cewa suna biye da shi da gudu. Suna zuwa ƙarshen wannan daji, dukkaninsu suka ruga da gudu suka koma da baya suka koma muhallinsu.
****
Yau *17/12/2022*
Babi na gaba zaizo *19/12/2022* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 59: *Ƙaurud'Dusa*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
UMAR SANGARU
*
Marganu na barin cikin wannan daji na biyu, ya kwantar da Aydenlik da Firziyya a ƙasa sannan shima ya nemi waje ya zauna. Tsahon rabin sa'a suna hutawa sannan suka dawo hayyacin su. Aydenlik da Firziyya suka miƙe zaune suka fuskanci Marganu.
"Kai wancan dajin bala'i ne," inji Aydenlik. "Dabbobi sai ka ce ƙwari?"
Gimbiya Firziyya tayi murmushi ta ce, "Nahiyar baƙaƙen fata kenan, duk duniya babu inda ya kai su yawan dabbobin daji. Ba don muna tare da sadauki ma'aboci Isik ba da mun jima da zama gawarwaki."
"Hmm," Marganu ya yi murmushi. "Ku tashi mu ci gaba da tafiya, abubuwan al'ajabi dai yanzu muka fara kallon su a cikin wannan tafiya ta mu. Bari mu je cikin garin Temisa ku gani!"
Marganu na gama faɗin haka ya miƙe tsaye ya gyara ɗamararsa, sannan ya wuce gaba suka bi shi a baya da sauri suka tunkari wannan daji na uku wanda ko alamunsa basa hangowa.
"Babban jarumi, baka tunanin ya kamata mu aikawa da birninka saƙon cewa kana nan a raye, sannan zaka dawo ka hau karagar mulkinka? Saboda kada su ɗaura wani akan karagar mulkin, muje mu tunɓuke shi rana-tsaka a ga kamar mun yi zalunci?" inji Aydenlik.
Marganu ya ɗan yi gajeren tunani ya ce, "Tabbas ka kawo shawara mai kyau, tsoho. Barin mutanen Hirtoliya a cikin duhun ina raye ko bana raye zai iya sa wa suyi tunanin na riga na mutu. Tunda ansan cewa babu mahaluƙin da ya taɓa shiga kurkukun mutuwa da kurkukun azaba-uku ya fito a raye.
"Amma idan na aika musu da wasiƙa na san cewa, zasu ci gaba da jira min wannar karaga har na koma na hau kanta. Komai tsananin daɗewar da zan yi kuwa, tun da sun san cewa mahaifina ba mulkin zalunci yake yi musu ba."
"Idan muka yada zango a gaba, ka rubuta wasiƙa da kanka da kuma sa-hannunka mu bayar da ita ga hadimin-aljani ya kai can." inji Aydenlik.
Marganu ya gyaɗa kai cikin yarda da wannan shawara ta Aydenlik.
Gimbiya Firziyya ta dubi Marganu ta ce, "Wai shin bayan mun kawar da mahaifina daga mulki, kuma mun kawar da sarki Ayubu, meye shirinka na gaba?"
Kai tsaye Marganu ya ce, "Zan kawar da Aymanul Faris ɗinnan wanda ya janƴo gimbiya Jaanu ta ƙi karɓar soyayyata."
"Daga nan kuma fa?" ta sake tambayarsa.
Marganu ya ɗan haɗe fuska ya dube ta, "Zan zamo babban sarki." ya amsa mata a taƙaice.
Gimbiya Firziyya tana shirin sake tambayarsa kenan, Aydenlik ya rigata yin magana. "Gaskiya yana da kyau, mu gudanar da kyakkyawan bincike akan wannan Aymanul Faris ɗin, saboda marigayi mahaifinka ya sha bani labarinsa yana cewa, akwai yiwuwar Aymanul Faris nan gaba zai iya zamowa gawurtaccen mutum."
"Gaskiya dai kam," inji Marganu. "Ko ni kaina na cika da tsananin mamaki sa'adda na fara yin arba da shi a cikin dajin Marsas. Tabbas akwai babban sirri tattare da Aymanul Faris ɗinnan wanda hatta shi kansa bai sani ba."
Aydenlik ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Tabbas ina so naga wannan Aymanul Faris ɗin, ko don yadda Marigayi ya dinga bani labarinsa."
Marganu ya ce, "Bari mu gama da abubuwan da muka saka a gaba, zamu mayar da hankali a kansa."
Haka dai suka ci gaba a cikin wannan daji suna tattaunawa akan abubuwan da suka a gaba, sannan suna ɗan kawo maganar Aymanul Faris jifa-jifa.
Tsahon kwanaki uku cir suka ɗauka suna wannan tafiya, sun yada zango sau huɗu, sannan suka iso cikin wannan daji na uku wanda yayi iyaka da garuruwa huɗu na gaba.
Wannan daji na uku babu komai a cikin sa face manƴa-manƴan tsaunika masu yawan gaske. Babu kogi ko kwazazzabo. Babu manƴan bishiyoyi, kawai iya waɗannan tsaunikan ne.
Ba tare da tsoro ko shakkun komai ba, su Marganu suka danna kai cikin wannan daji. Suka yi ta tafiya ba tare da sun haɗu da ko ƙatuwar dabbar daji guda ɗaya ba.
Wannan abu yayi matuƙar basu mamaki ace duk girman wannan daji, babu manƴan dabbobi a cikinsa? Tabbas akwai babban dalilin da ya haddasa hakan.
Suna cikin tafiya suka iso gindin wani ƙaton tsauni wanda da wuya a samu na biyunsa a cikin wannan daji. A jikin tsaunin akwai wani ƙaton kogon dutse mai tsananin zurfi wanda mutum ba zai na hango komai dake cikinsa ba, face duhu.
Suka ɗan tsaya a bakin kogon suka ƙare masa kallo cikin al'ajabi, sannan suka juya suka ci gaba da tafiya.
Basu yi nisa da barin gindin wannan tsauni ba, suka soma jiwo wasu manƴan takun sawu na fitowa daga cikin wannan kogo. Saboda ƙarfin takun har ƙasa ce ke girgiza.
Bisa dole suka tsaitsaya suka juyo suka fuskanci wannan tsauni. Kowannensu ya sake zaro makamin yaƙinsa don sun tabbatar da cewa duk halittar dake fitowa daga cikin wannan kogo zata yi bala'i.
Tsahon daƙiƙu ɗari biyu da hamsin sannan wani irin zabgegen ƙaton dodo ya fito daga cikin wannan kogo. Dodon dogo ne sosai domin zai iya kai rabin wannan tsauni a tsaye.
Jikin wannan dodo gaba ɗaya ƙwarangol ne, kansa rafkeke ne sannan idanuwansa jajawur ne. Bakinsa kuma tamkar ƙatuwar rijiya saboda tsananin faɗi. A hannayensa kuma, yana riƙe da zabga-zabgan sunguma guda biyu masu cako-cako.
Wannan dodo bai yiwa Marganu kama da komai ba face, SEDUSAWA. Marganu ya ayyana a ransa duk yadda aka yi wannan dodo shi ne shugabansu, domin ya ninka su a girma sau uku. Sannan sunguman dake hannunsa guda biyu ne maimakon nasu guda ɗaiɗaya.
Marganu, jaruma Firziyya da Aydenlik suka tsaitsaya a gaban wannan ƙaton dodo. Shi kuma dodon ya tsaya a gabansu ya ɗaga waɗannan ƙattin sunguma nasa, aka fara kallon-kallo.
"Kada ku kuskura ku ce zaku yaƙi wannan dodo da ƙarfin sihirin tsafi, saboda ba zai yi tasiri akan sa ba. Yana ɗaya daga cikin irin waɗannan dodanni da na fafata da su a baya." Marganu ya basu umarni ba tare da ya kalle su ba.
Aydenlik ya mayar da duwatsun tsafinsa guda huɗu, ya dubi Marganu ya ce, "In dai kamar yadda ka bamu labari haka ne, makaman yaƙin dake hannunmu baza su yiwa wannan dodo komai ba. Abinda ya kamace mu kawai shi ne muyi tunanin ƙwace wannan sunguma dake hannunsa."
Jaruma Firziyya ta dube shi ta ce, "Kare kan mu zamuyi da makaman ba wai yaƙarsa ba.." Bata ƙarasa rufe bakinta ba, suka ga wannan dodo ya dako wani wawan tsalle ya kawo musu duka da waɗannan sunguma dake hannunsa.
Cikin zafin nama suka daka tsalle gefe guda, sungumin farko ya dira bisa ƙasa, na biyun ya sauƙa akan wani ƙaramin tsauni take yayi daga-daga da shi.
Kafun su Marganu su sake dawowa hayyacinsu tuni ya sake kawo musu duka cikin zafin nama.
Da yake Marganu ya fi su zafin nama shi ya fara kaucewa harin dodon, jaruma Firziyya ma ta kauce, amma kafun tsoho Aydenlik ya ankara tuni ya sauƙe masa duka a kafaɗa.
Saboda ƙarfin dukan wannan dodo sai da Aydenlik ya nutse izuwa cikin ƙasa iya kafaɗarsa ne a waje.
Ba don Aydenlik tsohon mayaƙi bane kuma ya sha maganin tsari sosai da tuni wannan sungumi ya tarwatsa shi.
Marganu da Firziyya suna ganin abinda ya faru da Aydenlik suka sha jinin jikinsu, sannan suka dubi juna suna tunanin wanne irin salo ya kamata su fitowa wannan dodo da shi.
Wannan ƙaton dodo ya sake dako irin wannan tsalle nasa ya sake kawo musu duka a tare da waɗannan sunguma dake hannunsa. Marganu da Firziyya suka kauce, sunguman suka doki ƙasa da ƙarfi.
Nan take gagarumar ƙura ta lulluɓe wannan wuri sannan suka haifar da wawakeken rami.
Kafun wannan dodo ya zaro sunguman nasa daga ƙarƙashin ƙasa tuni Firziyya ta ƙaddamar masa da ɗalasimin Gandiz.
Farar dusar ƙanƙara mai yawan gaske ta soma sauƙa akan dodon tamkar ruwan sama.
Gaba ɗaya jikin wannan dodo yayi fari fat tamkar wanda aka yiwa fenti. Maimakon wannan dusar ƙanƙara ta daskarar dashi, kawai sai yayi girgiza ya watsar da ita.
Sakamakon wannan dusar ƙanƙara dake sauƙa a wannan wuri tasa duhu ya ɗan lulluɓe wurin, sannan kuma ga wannan ƙura da dodon ya haddasa. Uwa-uba kuma jikin wannan dodo ya saje da kalar wannan dusar ƙanƙara dake sauƙa a wurin, wannan yasa gimbiya Firziyya ta daina kallon abinda ke faruwa a cikin dajin.
Bata san hawa ba, bata san sauƙa ba, taji tahowar zabgegen sungumi daga saman kanta. Bata kallon wannan sungumi balle ta samu ikon kauce masa.
Saura ƙiris wannan sungumi ya sauƙa a tsakiyar kanta, wanda kuma yana sauƙa zai tarwatsa ta gaba ɗaya. Ta ji an doki ƙirjinta da ƙarfi, dukan ne yasa tayi sama ta faɗo gefe guda.
Ba don anyi mata wannan duka ba, da tuni sungumin wannan dodo ya dira a kanta yayi fallatsi da namanta.
Jaruma Firziyya ta tashi zaune a galabaice ta juya ta dubi inda wannan dodo yake domin ganin wanda ya kawo mata ɗauki.
Sadauki Marganu ta gani durƙushe bisa gwiwowinsa yasa hannayensa biyu ya tare wannan sungumi na wannan dodo.
Dodon ya saka ƙarfinsa gaba ɗaya domin ya danna Marganu ƙasa, shi kuma ya tattaro ƙarfinsa gaba ɗaya ya tare wannan sungumi ya hana shi ƙarasawa kansa.
Nan fa kwanjin jikin Marganu suka taso, jijiyoyin jikinsa suka kumburo. Idanuwansa suka kaɗa suka yi jawur, fuskarsa kuma ta fara gatsinewa tamkar zata zazzago saboda tsananin wahalar da yake sha.
Tabbas Marganu gawurtaccen sadauki ne mai tsananin ƙarfin damtse har na Allah ya isa. Wannan sungumi dake hannun wannan dodo, idan za'a ajiye a ƙasa sai ƙarti huɗu sun taru zasu iya ɗaga shi, amma Marganu ya tare shi.
Koda aka ɗan ɗauki lokaci a haka, sai bakin Marganu da hancinsa suka fara zubar da jini sakamakon muguwar galabaitar da yake sha a hannun wannan dodo. Saboda nauyin wannan sungumi da kuma ƙarfin wannan dodo.
Jaruma Firziyya ta fara kukan takaici saboda ganin wahalar da masoyinta Marganu yake sha sakamakon ceton rayuwarta da yayi.
Babban abinda ya dameta shi ne sakamakon wannan muguwar duka da yayi mata, ba zata iya miƙewa ta kai masa ɗauki ba.
Marganu ba shi da ikon kaucewa wannan sungumi domin gaba ɗaya ƙarfinsa ya gama tafiya akan tare wannan sungumi, da zarar ya zamewa wannan sungumi wannan dodo zaiyi amfani da ɗaya sunguminsa yayi masa wawan duka.
Sannan kuma wannan dodo ya fara cin ƙarfinsa domin jinin dake zuba daga cikin bakinsa da hancinsa ya soma yin yawa.
Jaruma Firziyya ta miƙe tsaye cikin tsananin juriya ta lallaɓa ta bayan wannan dodo, ta rugo da gudu ta fara hawa kansa, ba tare da ya sani ba.
Wannan dodo gaba ɗaya jikinsa na ƙwarangol ne, saboda haka baya jin halitta a jikinsa sosai. A wannan lokaci ya gama mayar da hankali wajen danna Marganu da wannan sungumi dake hannunsa saboda haka bai ma lura da wani abu na hawa jikinsa ba.
Jaruma Firziyya ta ci gaba da gudu akan jikin wannan dodo tamkar ƙadangare na hawa bango, har ta iso kan kafaɗarsa ba tare da ya ankara ba.
A wannan lokaci ne ya soma lura da cewa akwai wani abu akansa. Kuma a lokacin tuni ƙasusuwan kafaɗun Marganu sun soma amsawa suna shirin ɓallewa saboda nauyin wannan sungumi yafi ƙarfinsa.
Wannan dodo na shirin juyo da kansa domin ganin abinda ke kansa kenan, jaruma Firziyya ta daka wawan tsalle sama, ta zaro takubbanta guda biyu. Tana zuwa daidai kan wannan dodo ta caka su a cikin kunnuwansa guda biyu.
Nan take takubban suka shige cikin kan dodon sannan suka haɗe da juna a tsakiyar ƙwaƙwalwarsa. Dodon ya taƙarƙare ya kwarara wani irin mahaukacin ihu wanda yasa dukkanin tsaunikan dake cikin wannan daji amsawa, tamkar zasu tashi sama.
Dodon ya saki waɗannan sunguma dake hannunsa ya saka hannunsa guda ya cafko Firziyya ya ɗagata sama, ya wulwulata a cikin iska sannan yayi jifa da ita jikin wani tsauni.
Sannan yasa ƙafarsa guda ya doki ƙirjin Marganu da ƙarfi. Firziyya da Marganu suka tafi da gudu a cikin iska, zasu fyaɗu a jikin wani ƙaton tsauni wanda ko shakka babu jikinsu yana haɗuwa da tsaunin zasu dagargaje.
Dukkaninsu sun fita a hayyacinsu balle su yi tunanin sarrafa jikinsu su kare kansu daga sharrin haɗuwa da wannan tsauni.
Kafun su haɗu da tsaunin waɗansu manyan duwatsu suka zo suka shiga tsakaninsu, gangunan jikinsu suka sauƙa akan duwatsun a hankali.
Wannan ƙatoton dodo yayi ta kwarara ihu a cikin wannan daji wanda ya addabi komai da komai dake cikin dajin, har da su kansu su Marganun.
Duwatsun wuta suka soma ɗaukar zafi suna bindiga suna fesar da laba (lava) wanda ya fara gudu a cikin wannan daji tamkar ruwan kogi.
Duk abinda wannan ruwa ya taɓa sai kaga ya narkar da shi saboda tsananin zafi.
Cikin hanzari da kaɗuwa Marganu ya goyi Firziyya a gadon bayansa, ya ruga da azababben gudu a cikin wannan daji. Aydenlik ya samar da dutse mai faɗi ya hau kansa ya bi bayan Marganu.
Wannan ruwan wuta ya saka su a gaba suka yi ta gudu, tamkar ruwan zai cinƴe su amma a haka suka ci gaba da gudu iyakar ransu.
Da kyar da siɗin goshi Marganu da Aydenlik suka samu suka fita daga cikin wannan daji, ruwan wuta (lava) ya narkar da komai dake cikin wannan daji na uku har da shi kansa wannan ƙatoton dodo.
A ƙofar shiga waɗannan garuruwa guda huɗu Marganu, Aydenlik da Firziyya suka yada zango domin jiƴƴar jikinsu sakamakon mugun azabar da suka sha a hannun wannan shirgegen dodo.
Tanti guda uku Aydenlik ya samar musu, kowa ya shiga cikin tantinsa. Bayan kowa ya gama gyagygyara raunikan jikinsa, barci mai nauyi ya sace su.
Washe gari da sassafe da suka farka suka fito daga cikin waɗannan tantuna nasu, suka zauna dukkansu a waje ɗaya suna cin abincin safe.
"Jiya da dare banyi barci ba," Aydenlik ya fara jawabi. "Bincike na gudanar akan wannan shirgegen dodo da muka fafata da shi a daji na uku.
"Wannan dodo ɗan ƙabilar Sedusawa ne, sannan idan bai kasance shugaba a wannan ƙabila ba zai iya kasancewa mataimaki.
"Sunan sa ƘAURUD'DUSA."
Marganu ya ɗan ɗago kai ya kalli Aydenlik, cikin wani irin kallo mara ma'ana. Mutum zai iya cewa Marganu mamakin yadda Aydenlik ya ɗauki lamarin waɗannan dodanni da muhimmanci yake.
Saboda a yawancin lokuta Aydenlik yafi kowa kawo maganar waɗannan dodanni.
Marganu na shirin yin magana kenan, suka jiwo ƙarar buɗe wannan gari wanda suka yada zango a ƙofarsa. Cikin sauri suka juya da baya domin ganin abinda ya buɗe ƙofar garin.
****
Yau *19/12/2022*
Babi na gaba zaizo *22/12/2022* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 60: *Ƙabilar Aswad*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
MAL. UMAR SANGARU.
*
~Ɓangaren Aymanul Faris da Barban.
*
Suna shigowa cikin wannan tanti suka cika da tsananin mamaki domin daga waje ne yake tanti, amma ta ciki wata ƙasaitacciyar fada ce mai ban al'ajabi.
Tsayawa fasalta kyawun wannan fada kuwa, ɓata lokaci ne kawai. Barban ya tunkari wata ƙatuwar karaga ta mulki ya zauna, Aymanul Faris, jaruma Riya da sarki Dujalu suka zauna akan waɗansu ƙananun kujeru guda uku a gaban wannan karaga suka fuskanci juna.
Barban ya tafa hannayensa sau uku, faratan abinci da kofunan

Please Login or Register in order to submit comment