Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu irin siffofinsu ba.
Suna da tsaho da kauri, sannan idanuwansu ba kamar na sauran mutane yake ba. Idan mutum ya ce yana da kama da na maciji bai yi laifi ba.
Marganu ya ƙura musu idanu cikin tsananin mamaki kamar yadda suke kallonsa.
Bai yi yunƙurin zaro takobinsa ba saboda bai ga alamun cutarwa a tattare da su ba.
Idan mutum ya ƙarewa waɗannan yan mata guda uku kallo zai fuskanci cewa, ba wasu bane illa su Ileisha Gorgon masu wannan lambu wanda su Aymanul Faris suka zo suka tsinki furannin cikinsa a kwanakin baya.
A hankali waɗannan yan-mata guda uku suka ƙaraso inda Marganu ke tsaye, suka sake ƙare masa kallo.
Babu wadda tafi kallonsa a cikinsu face Ileisha Gorgon.
A zuciyar Marganu ko gezau bai yi ba, dukda cewa ya fara fuskantar waɗannan yan-mata ba asalin mutane bane.
"Ya kai wannan jarumi, wane ne kai? Ya ya aka yi kazo wannan lambu namu, shin kaima ka zo ne domin tsinkar furannin da baba ya shuka?" inji Ileisha Gorgon amma a wannan karon bada wannan yare wanda ta yiwa su Aymanul Faris magana da shi ba, ta yiwa Marganu.
Marganu ya ce, "Suna na Marganu, ban san yadda aka yi nazo wannan wuri ba, nima kawai tsintar kaina nayi a wajen."
"MARGANU?!" inji duk su ukun, kamar suna kwakwanton wannan suna nasa.
Cikin zafin nama yayun Ileisha Gorgon suka zaro takubbansu zasu sare Marganu, amma sai Ileisha ta dube su tayi musu magana cikin wannan yare nasu wanda Marganu bai san me suka ce ba.
Ileisha ta dube shi ta ce, "Ya kai Marganu, kayi sani cewa akwai wanda muke jiran zuwansa a cikin wannan lambu, shiyasa ma muka ɓuya tsahon lokaci babu wanda yasan da zaman mu. A yanzu da muka ganka mun ɗauka kaine wanda muke jira, amma da muka ji sunanka sai muka ji ya saɓa da sunan da aka sanar da mu. Wannan shi ne dalilin da yasa ƴan uwana suka yanke shawarar yaƙar ka, amma na hana su.
"Yanzu idan ka amince zan gudanar da wani ɗan gajeren bincike akanka. Tabbas sakamakon wannan bincike nawa shi ne zai tabbatar mana da asalin ka da kuma waye kai."
Marganu na jin haka ya haɗe fuska ya ce, "Ban gane wannan batu na ki ba, sam-sam?"
Ileisha ta ce, "Idan na gudanar da wannan bincike nawa, zan yi maka cikakken bayani. Abinda muke buƙata kawai shi ne haɗin kanka?"
Marganu ya ce, "Na ji. Faɗa min wanne irin bincike ne, sannan meye zai faru idan sakamakon wannan bincike bai yi daidai da abinda kuke jira ba?"
Ileisha ta dubi Marganu ta ce, "Ɗigon jininka guda ɗaya muke buƙata. Abinda zai biyo bayan wannan bincike kuwa, bamu isa mu yanke hukunci daga yanzu ba?"
Marganu ya ƙura musu idanu yana tunani, kafun daga bisani ya gama yanke shawarar abinda zai yi a cikin ransa.
Daga ganin siffar waɗannan yan-mata ya san cewa lallai gawurtattun mutane ne, kallon su kaɗai ya isa ya razana shi. Ba don shi gawurtaccen sadauki bane, da bai isa ya iya tsayawa a gabansu ba.
Tun da suna maganar akwai mutumin da suke jira, meye zai hana ya basu ɗigon jininsa, wataƙila idan wannan bincike ya dace da shi suke jira, zasu iya dawowa ƙarƙashin ikonsa.
"A ina zan zuba ɗigon jini na?" inji Marganu.
Ileisha tayi murmushi jin daɗin sannan ta fiddo wani farin ƙyalle daga cikin jakarta, ta miƙawa Marganu. Marganu ya karɓa sannan ya zaro ƙaramar wuƙa daga damtsensa ya yanki hannunsa kaɗan, ɗigon jini ya zubo kan wannan farin ƙyalle.
Marganu ya sake miƙawa Ileisha wannan ƙyalle, ta karɓa sannan ta rikiɗe izuwa wata siffa wadda tayi matuƙar baiwa Marganu mamaki.
Gashin kanta ya juye ya koma macizai, idanuwanta sun juye izuwa irin na macizai, harsenta ya koma tamkar dafin maciji. A wannan siffa idan mutum ya kira Ileisha da macijiya yayi daidai.
Ileisha ta kalli wannan ɗigon jini da waɗannan idanuwa nata masu kama da na maciji, sannan ta ɗanɗana jinin da wannan harshe nata, mai kama da na maciji.
Cikin farin ciki tayi wani tsalle mai nuna murna, sannan ta baiwa sauran waɗannan yan uwa nata, su ma suka juye izuwa irin wannan siffa nata, suka kalli wannan jini sannan suka ɗanɗana shi.
Suka sake juyewa izuwa siffar mutane sannan suka zube a gaban Marganu alamun mubaya'a.
Marganu ya dube su cikin rashin fahimta, yana so ya tambaye su.
Ileisha Gorgon ta miƙe tsaye tazo gaban Marganu ta sumbaci hannunsa ta ce, "Suna na ILEISHA GORGON, INA SARRAFA MACIZAI KALA ƊARI!"
Wadda take bin ta tazo ita ma ta sumbaci hannun Marganu ta ce, "Suna na LAILA GORGON, INA SARRAFA MACIZAI ƊARI BIYAR!"
Babbar cikinsu ta zo gaban Marganu ta sumbaci hannunsa ta ce, "Suna na NARIMA GORGON, INA SARRAFA MACIZAI DUBU!
"Daga yau gaba ɗayan mu mun zamo bayinka, masu bin umarninka, da sannu zamu kai ka asalin ɓoyayyiyar daular mu inda zaka iske dukkanin mutanenmu."
Marganu ya dube su ya ce, "Kuyi min bayani, ban gane me kuke nufi ba?"
Ileisha ta risina ta ce, "Ya shugabana, muje cikin gida, idan ka huta kaci abinci zaka fi fahimtar bayanin namu."
Marganu bai yi musu gardamar komai ba, suka shige gaba izuwa cikin wannan gida nasu.
Gida ne ƙarami wanda aka ƙawata musamman domin mutane masu zama a cikin daji.
Wani ƙaramin ɗaki suka kai Marganu, sannan suka kawo masa ƴaƴan itatuwa akan ganye, Marganu ya ɗauki tuffa guda ya fara ci.
Narima da Laila suka fice suka bar shi tare da Ileisha. Marganu na gama cin waɗannan itatuwa ya kishingiɗa tamkar wanda ke kwance a ɗakinsa ya fara barci.
Ileisha na ganin haka ta fara yi masa tausa, har barci mai nauyi ya sace Marganu.
Ileisha ta zauna a gefe ta ƙura masa idanu, tamkar bawa na gadin ubangidansa.
Tsahon sa'a guda da rabi Marganu yana ta sharara barci, kafun ya farka.
Ileisha tana ganin ya buɗe idanunsa tayi sauri tayi masa jagoranci izuwa bakin wani tafki sannan ta bashi umarnin yin wanka a ciki.
Ba tare da tsoro ko fargabar komai ba, Marganu ya cire kayan jikinsa sannan ya faɗa cikin wannan tafki yayi wanka ya fito ya saka kayansa, sannan ya koma cikin wannan ɗaki da su Ileisha suka sauƙe shi a ciki.
Kafun ya isa ƙofar wannan ɗaki ne, ya ga wani farin tsuntsu mai tsananin haske ya sauƙa a gabansa. Tsuntsun ya rikiɗe izuwa siffar aljanin haske Isika.
Isika ya dubi Marganu cikin jinjina ya ce, "Ban taɓa tunanin zaka kai wannan matsayi cikin ƙanƙanin lokaci haka ba. Da a shirina, sai mun hallaka sarki Kuffuru mun mulki wannan daula kamar na tsahon shekaru goma sannan zamu fita neman waɗannan mutane, ban taɓa tunanin zamu haɗu dasu da wuri haka ba."
Marganu ya ce, "Yauwa. Dama ina son ganinka domin nayi maka tambaya akansu?"
"ƘABILAR GORGON!" inji Isika. "Idan ka taɓa jin sunan wannan ƙabila, to su ne!" Yana faɗin haka ya ɓace ɓat!
Marganu ya haɗe fuska kamar baiso aljanin ya tafi ba. Sai dai yana waigawa bayansa yaga ashe Ileisha ce ta fito shiyasa aljani Isika ya ɓace ɓat!
Ileisha Gorgon ta yiwa Marganu murmushi mai nuna biyayya sannan ta yafito shi da hannunta guda, alamar ya shigo cikin wannan ɗaki suna jiransa.
Marganu ya yi murmushin takaici sannan ya nufi cikin wannan ɗaki, kalmar Gorgon tana yawo akansa.
A wannan lokaci zai yi wuya mutum ya taso bai samu labarin ƙabilar Gorgon ba, saboda ta'addancin da suka yi a zamanin da ya shuɗe tun lokacin da babban sarki Samudul Ansari yake raye.
Ance Samudul Ansari ne ya taka musu birki, da sai sun mamaye duniya gaba ɗaya a wancan zamani.
Marganu yana shigowa cikin wannan ɗaki ya hango su Narima Gorgon sun saka wata karagar mulki a tsakiya, suna zaune bisa wasu kujeru guda uku masu fuskantar wannar karaga.
Marganu na ƙarasowa ya zauna kan wannan karaga sannan fuskance su, "Ina jin ku?"
Ileisha Gorgon ta ce, "Bari na yi maka cikakken bayani akan dalilin da yasa muka yi maka mubaya'a. Ya shugabanmu muna buƙatar cikakkiyar nutsuwarka domin ka gane wannan bayani namu, da kuma babban matsayin da zaka taka, idan ka taimaka mana."
Ileisha Gorgon tana zuwa nan a zancenta ɗan yi shuru kamar tana son ta tattaro hankalin Marganu.
Jim kaɗan ta fara jawabi, "Mu ɗin nan da kake kallo dukkanmu ƴan wata ƙabila ce da ake kira Gorgon. Wannan ƙabila tsohuwa ce sosai, sannan tana da ɗumbin tarihi.
"Farkon samuwar wannan ƙabila ta mu, sai da duniya gaba ɗaya ta juya mana baya. Lokacin da bamu da ƙarfi idan banda kashe mu, babu abinda ake. An so a ƙarar da wannan ƙabila tamu gaba ɗaya amma lokaci ƙanƙani muka sami ɗaukaka.
"Tun daga wannan lokaci muke ta ɗaukar fansa akan mutane akan laifin da suka yi mana na karkashe mu, a lokacin da bamu da ƙarfi. A kullum shugabanmu bai da magana kamar cewa, mu nemo waye ISRABIL sannan muyi masa mubaya'a.
"ISRABIL ne kaɗai zai cece mu a duniya, sannan ya dawo da kimar mu. Bamu gane wannan jawabi nasa ba, sai da muka shigo cikin wannan nahiya.
"Wani gagarumin sarki muka tarar mai tsananin ƙarfin sihirin tsafi wanda yafi namu. Kayi sani cewa a wancan zamani, mutum ɗaya daga cikinmu na iya hallakar da gari guda komai girmansa.
"A wannan gari mun zo mun yaɗa baƙaƙen cututtuka masu mugun haɗari waɗanda suka kashe mutane masu yawan gaske.
"Babban abinda ya taka mana birki shi ne wannan sarki, wanda ya kira kansa da suna TAU'RIN.
"Mun gwabza mummunan yaƙi da wannan sarki, an ɗauki lokaci mai tsaho ana fafata wannan yaƙi tsakaninmu da wannan sarki.
"A ƙarshe wannan sarki ya karya wannan ƙabila tamu saboda taimakon wata takobi dake hannunsa. Bisa dole manyanmu suka bamu umarnin guduwa izuwa ainihin daular mu saboda basa so a ƙarar damu.
"Bayan komawar mu daular mu ne, muka samu labarin an ƙarar da dukkanin mutanen ƙabilarmu, sannan wannan sarki yana farautarmu. Amma bai san da zaman wannan daula tamu ba, shiyasa bai zo ba.
"Bayan tsahon lokaci muka samu labarin mutuwar wannan sarki, saboda haka muka shirya tsaf domin shigowa duniya mu ɗauki fansar jinin yan uwanmu da ya zubar.
"Muka haɗa gagarumar runduna mai tarin yawa da ƙarfin gaske, amma kafun mu tafi fatalwar sarkin mu ta bayyana inda ya daka mana tsawa wadda ta firgita mu gaba ɗaya.
"Sarkin mu yace, shin baku da hankali ne? Shin ba nace kada ku kuskura ku bar wannan daula ba tare da ISRABIL ba? Ku na tunanin a banza wannan sarki ya mutu? Shin aka ce muku da ya mutu bai bar magaji ba? Kuyi sani cewa gangar jikinsa ce ta mutu, amma ruhinsa na nan a raye, sannan yana da magaji, idan kuka yi kuskuren barin wannan yanki ba tare da ISRABIL ba, wannan magaji nasa zai hallakar da ku gaba ɗaya.
"Wannan magaji nasa zai fi shi ƙarfi, don haka zai iya gano wannan daula ta ku, idan ya gano wannan daula tamu kuwa, zai hallaka ku gaba ɗaya."
"Cikin rashin fahimta muka dube shi muka ce, to idan muna zaune a wannan daula tamu tayaya zamu gano inda ISRABIL yake har mu kawo shi wannan daula tamu, ya taimaka mana?
"Sarkin mu ya ce, mutane uku daga cikin ku zasu iya shiga duniya su gano waye ISRABIL sannan su kawo shi wannan wuri. Duk ranar da ISRABIL yazo dukkanku kuyi masa mubaya'a, shi ne kaɗai wanda zai kuɓutar daku daga sharrin TAU'RIN da magadansa.
"Muka ce, tayaya zamu gano ISRABIL?
"Sarkin mu ya ce, ɗanɗanon jininsa na dabam ne, sannan kuna ganin cikin idanunsa, wani aminci zai zo ranku. Sarkinmu na gama wannan batu ya ɓace ɓat!
"Mutanen ƙabilar mu suka ware mu, mu uku suka turo mu cikin duniya mu gano waye kai, sannan mu kaika daular mu, ka mulke mu.
"Kamar yadda muke buƙatar taimakon ka, haka kaima kana buƙatar taimakon mu!"
Marganu na jin wannan batu Ileisha wani gagarumin farin ciki ya cika zuciyarsa. Tabbas ya samu babban matsayi wanda kowa yake mafarkin samu a duniya.
Duk hatsabibancin ƙabilar Gorgon ace shi ne shugabansu, ai magana ta ƙare. Babu wanda zaiyi shakka a duniya, babu ƙasar da zata gagare shi.
Marganu ya ayyana a ransa, lallai idan ya mulki wannan ƙabila ya zamo gagarabadau a duniya. Babu wanda zai fi ƙarfinsa.
Abinda kawai ya tsaya masa a rai shi ne, TAU'RIN waye ne TAU'RIN meyasa Gorgons suke tsananin tsoron su?
Ileisha Gorgon ta ci gaba da bayani, "Dukda cewa kaine ISRABIL, ba zaka iya tunkarar TAU'RIN gaba da gaba ba, face mun tsuma ka a cikin tsumin tsafin da sarkin mu ya bari. Wannan tsumawa da zamu yi maka zata ɗauki wajen wata guda...."
Marganu ya gyaɗa kai cikin fahimta, tabbas a halin da ake ciki a yanzu bai kamata yayi wata guda baya nan ba. Saboda wannan dalili zai nemi alfarma a wajensu yaje ya yaƙi sarki Kuffuru, idan ya kashe sarki Kuffuru saiya zo su tafi wannan daula tasu.
"Wane ne TAU'RIN?" inji Marganu.
Ileisha ta risina a gabansa ta ce, "Tau'rin shi ne magajin ruhin jarumtaka na biyu, bayan sarki Samudul Ansari wato shi ne magajin Samudul Ansari..."
Marganu ya yi gajeren tunani ya ce, "Aymanul Faris!!!"
Cikin tsananin mamaki Narima, Laila da Ileisha Gorgon suka kalli Marganu suka ce, ka san shi ne?
Marganu ya ce, "Na san shi amma sama-sama, tun da ya bayyana bai taɓa fitowa fili inda za'a gan shi ba. Kullum yana ɓoye shi a cikin wani wuri mai ƙarfin sihiri."
Narima, Laila da Ilesiha suka yiwa Marganu wani kallo tamkar suna shakkar wannan abu da ya faɗa. Magajin sarki kamar Samudul Ansari ace ya tsaya ɓuya?
Marganu na fuskantar haka yayi murmushi ya ce, "Yana tare da sarkin ɓarayi Barban, duk wata sata yanzu tare suke yi."
Koda suka ji wannan batu na Marganu sai jikinsu yayi sanyi, saboda sun gano cewa su ne waɗanda suka zo wannan lambu suka ɗauki furanni.
Narima da Laila suka kalli Ileisha cikin jinjina, tabbas sun yi kuskure da suka kushe wannan jarumtaka da tayi lokacin da tari Aymanul Faris.
Ileisha Gorgon ta fara murmushi saboda ganin cewa ta tari Tau'rin, sannan bai sami nasara akanta ba.
"Ina alfarma a wajen ku," inji Marganu. "Akwai wani muhimmin aiki a gabana, wanda nake daf da ƙarasawa. Ina so naje na ƙarasar da aikin, sannan na dawo mu tafi daular ku."
Koda su Narima suka ji wannan batu na Marganu sai suka yi shuru, suna tunani. Tsahon ɗan lokaci, kafun Narima ta gudanar da yar-gajeriyar tsatsuba sannan ta dubi Marganu.
"Sarki Kuffuru ya kama abokan tafiyarka - Aydenlik da Firziyya. Ya kashe Aydenlik sannan ya kai masoyiyarka Firziyya gidan kurkuku mafi azaba a duniya..."
Marganu na jin wannan batu jikinsa ya soma tsuma saboda tsananin fusata, wai me sarki Kuffuru yake nufi ne? Haka kawai ya tsane shi, ya saka shi a gaba?
Tabbas idan bai wulaƙanta rayuwar sarki Kuffuru ba, ba zai huce takaicin da ya saka shi a ciki ba.
Marganu ya kwarara uban ihu cikin fusata, jikinsa ya soma ɗaukar haske tamkar rana.
Narima, Laila da Ileisha suna ganin haka, suka risina a gabansa cikin ladabi.
"Ku kaini kogon Rohishmu, domin na sha wani tsumin tsafi." inji Marganu.
Ileisha ta zube a gabansa ta ce, "Ya shugabanmu, wuraren da zamu je a duniya a kayyade suke. Idan muka wuce iyakar mu, RUHIN JARUMTAKA zai iya fusata ya fito farautar mu."
Marganu ya ce, "Shin kogon Rohishmu baya daga cikin waɗannan ƙayadaddun wajaje?"
Narima ta ce, "Za mu iya kai ka wannan waje babu matsala amma idan muka jima sosai, RUHIN JARUMTAKA zai gano mu."
Bayan kai-komo wadannan yan-mata guda uku suka haɗe a waje guda, suka samar da siffar wata jibgegiyar macijiya.
Macijiyar ta wangame ƙaton bakinta, Marganu ya shige ciki sannan ta fara tafiya a cikin wannan ƙaton daji ta tunkari kogon Rohishmu.
****
Yau *11/02/2023*
Babi na gaba zaizo *13/02/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 84: *Cikakken shiryayye: Marganu*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U*M*S
*
Tsahon kwanaki uku cir wannan jibgegiyar macijiya tana ta tafiya a cikin dazuzzuka sannan ta isa bakin kogon Rohishmu. Komai tsananin yawan yan fashin cikin daji da hatsabiban aljanun dake rayuwa a cikin dazuzzuka.
Da zarar sun hango wannan macijiya suke guduwa saboda tsananin kwarjininta da ƙamshin sihirin dake tashi a jikinta.
Kogon Rohishmu dogon dutse ne wanda ya tashi sama har ya soma ƙulewa a cikin gajimare, sannan daga can ƙasa akwai wata ƙofar shiga guda ɗaya mai girma da faɗin gaske.
Abin mamaki wannan ƙofa ba'a kulle take ba, a buɗe take wanwar, amma daga waje mutum ba zai na hango abinde ke can ciki ba, saboda tsananin duhunta.
Wannan jibgegiyar macijiya na zuwa wannan wuri ta sunkuyar da kanta ƙasa sannan ta wangame ƙaton bakinta, tamkar zata haɗiye komai dake wajen. Marganu ya tako a hankali ya fito daga cikin wannan baki nata.
Macijiyar tayi girgiza ta juye izuwa siffar yan-mata guda uku - Narima, Laila da Ileisha Gorgon. Dukkansu suka zube a gaban Marganu, Ileisha ta fiddo wani madubi ta baiwa Marganu ta ce, "A duk lokacin da kake son magana da mu, ka kalli cikin wannan madubi zaka kalle mu. Za mu kasance masu jiran zuwanka domin tafiya daular mu!"
Marganu ya yi murmushi ya karɓi wannan madubi ya saka a cikin jakar guzurinsa sannan yayi sallama da su Ileisha akan cewa idan ya kammala abinda yake yi, zai neme su.
Narima, Laila da Ileisha suka sake haɗewa a waje guda, suka juye izuwa siffar wannan ƙatuwar macijiya, ta risina a gaban Marganu sannan ta juya ta tafi.
Tafiyar wannan macijiya keda wuya, aljani Isika ya bayyana a gefen Marganu ya ce, "Barka dai, ISRABIL!"
Cikin mamaki Marganu ya dube shi ya ce, "Mene ne ISRABIL da naji waɗannan mutane sun damu da sunan?"
"Sunan yana da ma'ana guda biyu," inji Isika. "A harshen baƙaƙen aljanu yana nufin 'tauraruwa mai sa'a' wato wanda yake da tauraruwa mai ƙarfi kenan.
"A yaren ƙabilar Gorgon kuma, yana nufin 'cikakken sarki' ko kuma 'abin bauta'. Tabbas ka samu babban matsayi, mulkin ƙabila kamar Gorgon ba ƙaramin dacewa bane.
"Babu ƙabilar da ta kai su yawa da kuma ƙarfi, ba don takobin Saif-Al-Barzak ba da ba'a karya ƙarfinsu a duniya ba."
Marganu ya gyaɗa kai cikin fahimta ya ce, "Amma mene ne dalilin da yasa suka ce sai sun tsuma ni a cikin tsumin tsafi na tsahon wata ɗaya domin na samu cikakken ƙarfin da zan tunkari TAU'RIN?"
Isika ya ce, "Ban san amsar wannan tambaya ba, amma wataƙila saboda ƙarfin da TAU'RIN yake da ne shiyasa."
Marganu ya gyaɗa kai ya ce, "Wai daular Shaha kam, bata ta riga ta karye ba? Idan ma suka mallaki ruhin kakan nasu, tayaya daular zata sake dawowa kamar da?"
Isika yayi murmushin takaici ya ce, "Wa ya faɗa maka mutanen daular Shaha sun ƙare? Ai tun sa'adda aka fara farautarsu a duniya suka caccanja suna, sannan wasun su suka caccanja kamanni. Ai duk ranar da suka sami labarin wannan daula ta sake tashi zasu koma cikinta, saboda alkhairan dake cikin daular..."
Marganu ya ce, "Waɗanne alkhaire ne a daular Shaha?"
Isika ya sake yin murmushi ya ce, " Duk faɗin duniya, babu inda ya kai daular Shaha albarkar noma, albarkatun ƙasa da ni'imomi masu yawan gaske.
"Masu hasashe na wancan zamani suna ganin cewa, abubuwan da ake nomawa a daular Shaha zasu iya ciyar da duniya gaba ɗaya saboda yawansu.
"Masana kuma suna ganin cewa, karyewar daular Shaha shi ne ya janyowa waɗansu yankunan duniya talauci da kuma yunwa."
Marganu na jin wannan batu yayi wani tunani a ransa, tabbas idan ya mayar da hankali nan gaba zai taka babban matsayi idan ya mulki ƙabilar Gorgon.
"Hmm," Marganu ya yi murmushi ya ce, "Zan taka babban matsayi a duniya. Yanzu mu shiga cikin wannan kogon, na sha tsumin boka Rohishmu domin naje na kawo ƙarshen sarki Kuffuru."
Isika yayi murmushi sannan ya shige gaba, Marganu ya take masa baya suka shige wannan ƙaton kogo.
Ƙato ne mai girma da faɗin gaske wanda gaba ɗaya duhu ya gauraye ko'ina da ina na cikinsa.
Isika ya yi amfani da baiwarsa ya samar da wadataccen haske a cikin wannan kogo wanda ya gauraye ko'ina da ina. Koda allura ce ta faɗi a wannan lokaci mutum zai gan ta saboda tsananin hasken kogon.
Babu komai a cikin wannan kogo face tarkacen kayan tsafi da ƙasusuwan bil'adama, waɗanda suka riga suka fara ruɓurɓushewa.
A can tsakiyar kogon suka hango wata tukunyar tsafi guda ɗaya jal bisa wani tudu. Tun daga nesa wannan ƙarfe na wannar tukunya yana ɗaukar idanu.
Kafun su ƙarasa inda tukunyar take, Isika ya dubi Marganu ya ce, "Ya shugabana! Kada ka manta cewa, ba zaka iya taɓa wannar tukunya ba, face jikinka yana matsayin haske. Idan ba haka kuwa, abinda ya faru da dubbannin bokaye zai faru da kai."
Marganu ya ce, "Ban manta ba, mu ƙarasa kawai."
Suna ƙarasawa Marganu ya dafa wannan hatimi na haske dake kan kafaɗarsa, jikinsa ya juye izuwa haske sannan yasa hannunsa guda ya buɗe marufin wannan tukunya.
Wani irin koren tiriri ya taso daga cikinta, Marganu ya dubi Isika ya ce, "Yanzu wannan ruwa mai zafin zan sha?"
Isika ya ce, "A ido ne zaka ga kamar yana da zafi, amma baida wani zafi..."
Marganu ya gyaɗa kai, yasa hannayensa biyu ya cicciɓo wannan tukunya sannan ya kafa a bakinsa, ya fara shan wannan tsumi dake cikinta.
Kamar yadda Isika ya faɗa haka ruwan tsumin yake, idan mutum ya gan shi a ido, zai ɗauka a tafashe yake, amma mutum yana sha zaiji tamkar ruwa mai ɗan ɗumi yake sha.
Marganu na gama shan wannan tsumi, wani irin gumi ya soma zubowa daga jikinsa wanda ya narkar da dukkan kayan dake jikinsa.
Gaba ɗaya jikin Marganu ya jiƙe sharkaf da gumi, a wannan lokaci babu abinda ya rage a jikinsa face wani gajeren wando wanda bai kai ko gwiwa ba.
Lamba bakwai wadda aka rubuta ta yaren birnin Hindu, ta bayyana a tsakiyar goshin Marganu tsahon daƙiƙu goma kafun ta ɓace ɓat.
Wani irin ƙarfin sihirin tsafi mai ban al'ajabi ya soma ratsawa ta cikin jikin Marganu tamkar gogaggen matsafi irin wanda aka jima ba'a gani ba.
Marganu bai daina jin sauyin yanayi a jikinsa ba, sai da rabin sa'a ta shuɗe sannan ya dawo daidai.
A wannan lokaci Marganu cikakken matsafi ne mai ƙarfin tsafi mataki na bakwai.
A wannan lokaci Marganu cikakken mayaƙi ne mai rantsatstsun takubba guda biyu - takobin haske da takobin tarwatsa-komai.
Abinda ya ragewa Marganu a wannan lokaci, kawai shi ne tunkarar sarki Kuffuru domin kuwa ya gama zamowa cikakken shiryayye.
Yana da ƙarfin sihirin da zai iya tsayawa a gaban Kuffuru su fafata, sannan yana da takobin da zai ga bayan hadimin sarki Kuffuru, aljani Djinn mai jikin duwatsu.
Aljani Isika ya sake zubewa a gaban Marganu domin jaddada mubaya'arsa.
"Mene ne motsin mu na gaba?" inji Marganu.
A wannan lokaci hatta muryar Marganu sai da ta sauya.
Isika ya ce, "Sarki Kuffuru ya hallaka babban hadimi Aydenlik, sannan

Please Login or Register in order to submit comment