Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

SAMUDUL ANSARI!" inji wannan saurayi.
Sarauniya Arya tana jin wannan suna ta baiwa Abu-Sharjas da wannan saurayi umarnin tafiya.
"Yanzu waye zai kula da mahaifina? Ta ya ya zan tafi kogi na bar shi a wannan wuri a galabaice?" inji Samudul Ansari.
"ZAN KULA DA SHI, KU JE KU GUDANAR DA WANNAN BINCIKE KAWAI." inji sarauniya Arya.
Samudul Ansari ya zube a gabanta ya ce, "Na isa na saka gagarumar sarauniya kamar ki wannan aiki?"
"Hmm," sarauniya Arya ta yi murmushi. "Ni ce nace zanyi, kuma zan yi. Rayuwar al'umata tafi tawa muhimmanci, ku je kawai..."
Likita Abu-Sharjas yaja hannun Samudul Ansari, suka nufi hanyar wannan kogi.
Samudul Ansari yana tafiya yana waigowa yana ganin halin da mahaifinsa yake ciki.
Sarauniya Arya ya gani ta rungume mahaifinsa tana bashi wani ruwan magani wanda Abu-Sharjas yake baiwa dukkan masu irin wannan lalura.
Wannan abu da sarauniya Arya tayi yayi matuƙar burge Samudul Ansari. Saboda ƙarfin mulkinta da ikon da take dashi bai sa girman kai ya shige ta ba.
Bayan doguwar tafi suka iso wannan kogi, wanda ruwa keta gudu a cikinsa.
Abu-Sharjas ya tsaya a gaban wannan kogi ya ƙurawa ruwan dake cikinsa idanu, tsahon ɗan lokaci kafun ya fiddo waɗansu irin tufafi daga cikin jakar tsafinsa.
Tufafin guda biyu ne, yasa guda ɗaya ya baiwa Samudul Ansari guda ɗaya. Suka saka wannan tufafi sannan suka fara yawo a cikin wannan kogi suna gudanar da bincike.
"Shin kana ganin irin koren-dafi a cikin wannan kogi?" Abu-Sharjas ya tambayi Samudul Ansari.
Samudul Ansari yayi shuru ya sake ƙurawa ruwan dake cikin wannan kogi idanu. Kamar yana so ya tabbatar da abinda yake kallo ne.
"Tabbas ina ganin irin wannan koren-dafi a cikin ruwan kogin nan." inji Samudul Ansari.
Abu-Sharjas ya gyaɗa kai, sannan suka ci gaba da yawo a cikin wannan kogi suna bincike.
Har sun gaji da yawo a cikin kogin zasu fita kenan, Samudul Ansari ya yi tsalle ya faɗo a gefen Abu-Sharjas sannan ya saka wata ƙaramar wuƙa ya kashe wani ƙaramin maciji.
Hantar cikin Abu-Sharjas ta kaɗa saboda tsananin razana, iyakacin daɗewarsa a duniya, bai taɓa yin arba da irin wannan maciji ba.
Kore ne shar, sannan yana da jajayen idanu. Jikinsa akwai ƙananun ƙayoyi. A taƙaice dai, wannan maciji yana da ban al'ajabi da kuma kwarjini.
Babban abinda ya baiwa Abu-Sharjas mamaki shi ne, kwata-kwata Samudul Ansari bai razana da kallon wannan maciji ba.
Sannan ta ya ya aka yi ya kalli wannan maciji?
Waɗannan dalilai su ne suka tabbatarwa da likita Abu-Sharjas, Samudul Ansari shi ne ɗan-baiwan da yake magana a kai.
"Ga dukkan alamu dai, dafin wannan maciji shi ne abinda ya haddasa guba a cikin wannan ruwa." inji Abu-Sharjas.
Samudul Ansari ya gyaɗa masa kai.
Abu-Sharjas ya bashi umarnin komawa wajen sarauniya Arya domin su gabatar mata da abinda suka samu a cikin wannan kogi.
Suka fito daga wannan kogi sannan suka koma cikin ƙauyen Salwaza inda sarauniya Arya ke zaune tana jiransu.
Tana kallon wannan mataccen maciji ta ja da baya a tsorace saboda tsananin kwarjinin sa.
Bayan gajeren tunani, ta yanke shawarar zuwa wajen gawurtaccen boka Ƙaizadu domin ya gudanar da bincike akan wannan maciji.
Ita, Samudul Ansari da likita Abu-Sharjas suka yi hawa, suka nufi dajin da wannan boka yake rayuwa a cikinsa.
****
Yau *16/02/2023*
Babi na gaba zaizo *18/02/2023* da yaddar ALLAH.
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 86: *Daular Gorgon*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U*M*S
*
Samudul Ansari, sarauniya Arya da Abu-Sharjas suna fitowa daga cikin ƙauyen Salwaza suka yanki daji, suka yi ta tafiya babu dare ba rana. Suka tasarwa dajin Ƙaiz inda boka Ƙaizadu yake rayuwa.
Dama tun kafun su fito wannan tafiya, likita Abu-Sharjas yasa an kafa tantuna masu kyau inda aka killace masu irin wannan lalura wadda bata yi ajalinsu ba, sannan likita Abu-Sharjas ya yiwa jama'a gargaɗi akan su ƙauracewa shan ruwan dake cikin wannan kogi wanda ga dukkan alamu wannan annoba daga cikinsa take.
Sarauniya Arya tana son yiwa Samudul Ansari magana amma ganin baya cikin hayyacinsa sosai, yasa ta dakata.
Suka ci gaba da tafiya har tsahon kwanaki uku, sannan suka iso cikin dajin Ƙaiz.
Wannan daji na da ban al'ajabi domin kuwa babu namun dawa ko kuma tsaunika a cikinsa. Duhuwowi da bishiyoyi ne kawai suka cika dajin.
A tsakiyar wannan daji ne, suka yi arba da wani tafkeken gida wanda aka gina da zallar rassan bishiyoyi masu kaurin gaske.
Daga ganin yanayin wannan gini, mutum zai gane cewa, aiki ne na aljanu.
Ƙofar shiga gidan ta haske ce, bata da mabuɗi ko abin rufewa. Daga gani ka san cewa indai mutum ya shiga wannan gida, to umarni aka baiwa wannan ƙofa ta buɗe.
Boka Ƙaizadu shi ne babban boka na wannan daula gaba ɗaya. Babu matsafin da yafi shi ƙarfin sihiri.
Duk wata buƙata ta sarakunan wannan daula wajensa suke zuwa. Hakan ne yasa ya bunƙasa ya tara dukiya mai yawan gaske sannan ya yi ƙaurin suna.
Samudul Ansari, sarauniya Arya da Abu-Sharjas suka sauƙo daga kan dawakansu, suka tsaitsaya a ƙofar shiga wannan gida.
Abu-Sharjas ya ɗaga muryarsa ya ce, "Barka da wannan lokaci, shugaban matsafa. Babban boka maganin ƙananu, ina mai buƙata yazo wajen mai biyanta! Yau ga sarauniyar birnin Ilam tazo da kanta wajenka domin ka biya mata wata buƙata!"
Abu-Sharjas yana zuwa nan a zancensa ya koma baya ya tsaya.
Wannan ƙofa ta haske fara ta sheƙi da walwali, kafun daga bisani ta tsage. Wani ƙaton mutum ya ratso ta cikinta ya fito.
Boka Ƙaizadu ƙato ne na kwatance amma sai dai ya fara manyanta. Babu riga a jikinsa face wani bante. Gaba ɗaya jikinsa a cike yake da gurayen tsafi.
Boka Ƙaizadu ya ƙarasa inda sarauniya Arya ke tsaye ya yi mata barka da zuwa.
Boka Ƙaizadu babban mutum ne a wannan daula, saboda ƙaurin sunan da yayi da kuma buwayarsa baya risinawa sarakuna.
Idanuwansa na kaiwa kan Samudul Ansari ya zube a gaban Samudul Ansari ya ƙwashi gaisuwa tamkar wanda ya ga wani babban hamshaƙin sarki wanda babu kamarsa a duniya.
Bar batun Samudul Ansari. Sarauniya Arya da likita Abu-Sharjas sai da suka jijjiga.
Boka Ƙaizadu tsohon mutum ne, ana ganin cewa duk faɗin wannan daula babu wanda ya kaishi tsufa. Ba ma su sarakunan da ke mulki yanzu ba.
Hatta iyaye da kakanninsu da suka yi zamani suka shuɗe, boka Ƙaizadu bai taɓa risina musu ba.
Abinda su sarauniya Arya basu sani ba shi ne, shi kansa boka Ƙaizadu ya girgiza saboda ba wai yin kansa bane yasa ya kwashi gaisuwa a gaban Samudul Ansari.
Jikinsa ne kawai ya bi wannan umarni amma zuciyarsa bata so.
Saboda wannan dalili daga wannan lokaci ya soma shakkar Samudul Ansari, ya tabbatar da cewa lallai wanda ke tsaye a gabansa ba ƙaramin mutum bane, kuma ga dukkan alamu shima kansa bai san waye shi ba.
Boka Ƙaizadu ya dubi sarauniya Arya ya kawar da wannan abu daga ransa domin kada su gano wani abu ya ce, "Mu je cikin fadata, mu tattauna. Tabbas na san abinda ke tafe da ku, kuma na san maganin matsalar ku.
"Lallai kun yi babbar dabara da kuka zo wajena da wuri, saboda idan ba mu takawa wannan cuta birki ba, nan gaba sai ta shafe wannan daula gaba ɗaya... Mu je ciki..."
Yana gama faɗin ya juya ya shige cikin wannan fada, Samudul Ansari, sarauniya Arya da likita Abu-Sharjas suka take masa baya.
Lokacin da Samudul Ansari yazo giftawa ta cikin wannan ƙofa sai da ta yi wani haske mai ban al'ajabi wanda ya janyo hankalin boka Ƙaizadu dake can gaba.
Ya juyo cikin sauri ya ƙarewa Samudul Ansari kallo. Daga bisani ya gyaɗa kai bai ce komai ba.
Wannan ƙofa ta haske ita ce take tantance mutane, in dai mutum ya wuce ta cikin wannan ƙofa tamkar boka Ƙaizadu ya samu dukkan bayanansa ne.
Wani lokaci haskenta raguwa yake, idan mutum da mugun nufi yazo, wani lokaci kuma hasken ƙaruwa yake domin ya nuna matsayin mutum da kuma abinda ya taka.
Boka Ƙaizadu bai taɓa ganin wannan ƙofa tayi haske irin na wannan lokaci ba, saboda haka dole ne ya cika da tsananin mamaki.
Boka Ƙaizadu ya zauna akan karagar dake cikin fadar sannan ya baiwa su Samudul Ansari wajen zama a gefen karagar.
"Kun zo ne akan maganar sabuwar cuta wadda ta ɓulla a ƙasar Ilam, shekaran jiya mutum ɗaya ya mutu, jiya mutum ɗari, yau mutum dubu, haka ne?" Boka Ƙaizadu ya tambaye su.
Sarauniya Arya ta gyaɗa masa kai alamun haka ne.
Boka Ƙaizadu ya ci gaba, "Abu-Sharjas jiya kun je cikin wannan kogi wanda ya ratso ta gefen waɗannan ƙauyuka guda uku, shin kun sami wata makama wadda zamu gudanar da bincike akanta, mu gano babban dalilin da ya haddasa wannan cuta?"
Likita Abu-Sharjas ya fiddo wannan koren maciji wanda Samudul Ansari ya kashe a cikin jakar dake rataye a kafaɗarsa ya miƙawa boka Ƙaizadu shi.
Idanuwan boka Ƙaizadu na yin arba da wannan maciji ya ja da baya a tsorace. Idan su sarauniya Arya da likita Abu-Sharjas wannan maciji kwarjini yayi musu, shi ya san wannan maciji sarai.
"Babban boka, mene ne abinda ke faruwa?" sarauniya Arya ta tambaye shi.
Boka Ƙaizadu ya dube su ya ce, "Wannan maciji da kuke gani, ba'a samun sa a ko'ina a duniya face DAULAR GORGONS.
"Wannan maciji sashi ne daga cikin gashin kansu, domin gaba ɗaya gashin dake kansu macizai ne.
"Wannan ƙabila ta Gorgon ana ganin tun daga kafuwar duniya, ba'a taɓa samun shaiɗanu kamar su ba.
"Ɗaya daga cikin waɗannan mutane, na iya hallakar da daula komai girman ta.
"Tabbas ba don muna da ɗan-baiwa [Samudul Ansari] a wannan daula ba, da babu yadda za'a yi mu gano abinda ya haddasa wannan cuta.
"Kuyi sani cewa, duk wani gawurtaccen matsafi da ya yi suna a duniya ya san da zaman wannan ƙabila, kuma tuni hankalin kowa ya fara tashi."
Boka Ƙaizadu yana zuwa nan a zancensa ya nuna wani madubin tsafi da hannunsa, take madubin yayi haske sannan ya soma nuna wata ƙatuwar ƙasa a can tsakiyar duniya.
Daula ce makekiya wadda girmanta zai iya kai zango dubu, tana da tsananin faɗi da kuma yawan ƙasa.
A wannan daula aka nuno garuruwa-garuruwa masu yawan gaske, kowanne gari guda ɗaya girmansa zai iya kai babban birnin Ilam gaba ɗaya.
Aƙalla akwai manyan garuruwa irin waɗannan sama da guda ɗari. Jin wannan kaɗai ya isa yasa mutum, ya tabbatar da cewa lallai wannan daula babba ce.
Ba wai girman daular bane ya baiwa su sarauniya Arya mamaki face mutanen da suka gani suna rayuwa a daular.
Waɗansu irin mutane ne masu girma da faɗin gaske. Mafi yawa daga cikin waɗannan mutane ƴan-mata ne waɗanda ba za su wuce shekaru ashirin zuwa ashirin da ɗaya ba.
Babban abinda yafi basu mamaki shi ne, gashin kan waɗannan mutane, ba gashi bane kamar na sauran mutanen duniya.
Macizai ne kawai keta yawo a matsayin gashi.
Ba wai mutum ɗaya, ko mutum biyu ba. A'a kowa ka gani a wannan daula haka gashin kansa yake.
"Kamar yadda kuka gani," inji boka Ƙaizadu. "Wancan daula tasu babbar daula ce, amma dukda haka wannan daula tayi musu kaɗan, saboda tsananin yawansu.
"A yanzu haka sun fara turo wakilai izuwa sauran dauloli domin su nema musu inda zasu fake.
"Ba wai iya wannan daula tamu bace wannan annoba ta shafa ba, a'a, duk duniya ne.
"Suna so gane wacce daula ce tafi jikkata daga wannan dafi nasu, sai su dawo cikinta su mamaye ta.
"A yadda alƙaluman tsafi suka nuna, wannan daula tamu tafi shan wahala daga wannan annoba.
"Kada ku yi tsammanin iya waɗannan ƙauyuka guda uku, kawai wannan annoba ta shafa.
"Jiya-jiyan nan sauran sarakunan wannan daula, suka zo wajena su ma da irin wannan buƙata ta ku. Na ce musu dai zan yi bincike akai, amma ban sami wani abun kamawa ba.
"Tabbas ba don an tsinci wannan ƙaramin macijin ba, da babu yadda za'a yi mu gano matsalar.
"Yanzu haka, wajen mutum dubu biyu sun mutu a iya waɗannan ƙauyuka kaɗai.
"A sauran ƙasashen wannan daula, wajen mutum dubu talatin ne suka mutu.
"Kun ga kenan, wannan zai janyo hankalin ƙabilar Gorgon izuwa wannan daula domin su zo su mamaye ta."
Koda boka Ƙaizadu yana wannan waje a labarinsa, sai hankalin sarauniya Arya da likita Abu-Sharjas yayi mummunan tashi.
Shi ko Samudul Ansari babu abinda yaji a ransa, saboda baya razana, kuma baida tsoro.
Duk wanda ke rayuwa a wannan daula a wancan zamani, ya san labarin daular dake tsakiyar duniya wadda ƙabilar Gorgon ta mamaye.
Kai, a wancan lokaci idan mutum ya ce ma baya tsoron Gorgon ƙarya yake, saboda yadda ake shakkarsu da kuma yadda labarinsu ya bazu a duniya.
Sau ɗaya wata budurwa ta taɓa fitowa daga wannan daula ta shiga yawon duniya.
Ance wannan budurwa sai da ta hallaka mutane wajen guda miliyan huɗu, saboda duk kogin da ta wuce ta cikinsa ruwan cikinsa guba yake komawa.
Sai da manyan sarakuna da manyan matsafa suka haɗa ƙarfi da ƙarfe sannan suka hallaka ta.
Ance dukda haka sai da ta hallaka fiye da rabinsu.
Wannan yayi matuƙar fusata daular Gorgon suka fara shirye-shiryen afkowa duniya.
Hankalin waɗannan sarakuna ya tashi, bisa dole suka je wannan daula suka bayar da haƙuri tare da kyautar dukiya mai yawan gaske da kuma bayi sannan daular Gorgon ta haƙura.
Tabbas idan daular Gorgon ta bugi ƙirji ta ce zata mamaye wani yanki daga cikin daulolin duniya, babu wanda ya isa ya hana ta.
Boka Ƙaizadu ya lura da tsoron dake kan fuskar sarauniya Arya da likita Abu-Shajras. Yayi matuƙar cika da mamaki bisa ganin cewa Samudul Ansari bai razana ba, dukda cewa ya samu labarin masifar da babu wadda ta kaita a wancan zamani.
Boka Ƙaizadu ya ce a ransa, lallai duk yadda aka yi wannan saurayi ɗan baiwa ne kuma zai sami ɗaukaka a gaba.
Sarauniya Arya ta yi ajiyar numfashi ta ce, "Babban boka, shin wannan cuta dake damun al'umma bata da magani ne? Sannan tayaya za'a yi a ɗauke hankalin Gorgons daga wannan daula tamu?"
Boka Ƙaizadu na jin wannan batu ya duba madubin tsafinsa sannan ya ce.
"Wannan cuta da suka saka ba zata taɓa yayewa ba, face anje saman tsaunin Hajarul Gorgon, an gyara kwanciyar duwatsun Hesheir, sannan an jefe macijiya Ziyazilu da irin waɗannan duwatsu.
"Yin hakan zai sa hankalin Gorgon ya bar wannan daula gaba ɗaya, sannan wannan cuta zata yaye.
"Babu abinda zai sake haɗa su da wannan daula har abada, an rabu kenan."
Koda jin wannan batu sai hankalin Arya da Abu-Sharjas ya sake ɗugunzuma fiye da farko.
Duk wanda ya san labarin Gorgon a wancan zamani, ya san labarin abar da suke bautawa, wato macijiya Ziyazilu.
Hawa kan tsaunin Hajarul Gorgon kaɗai aiki ne, balle mutum ya kashe abinda fiye da mutum miliyan ɗari tara da arba'in suke bautawa.
Amsar wannan batu na boka Ƙaizadu kawai shi ne, BA ZAI YIWU BA. Babu wanda ya isa yayi gangancin zuwa daular Gorgon balle har yayi tunanin kashe abinda suke bautawa.
Sarauniya Arya ta sa a ranta kawai, tabbas gagarumar masifa wadda basu san ƙarshenta ba na tunkaro su.
Cikin dakewa da zuciya irinta mazan jiya, Samudul Ansari ya dubi boka Ƙaizadu ya ce, "Ina so kayi mini izini, zan je daular Gorgon sannan na hau tsaunin Hajarul Gorgon na kashe wannan macijiya!"
Sarauniya Arya tayi caraf ta ce, "Ba ka da hankali ne. Hatta manyan jarumai da suka yi zamani suka shuɗe, basu taɓa kaiwa daular Gorgon wargi ba. Kana tunanin zaka yi nasara akan su ne?
"Ai idan ka kaiwa daular Gorgon wargi, hakan zai sa su fusata su shafe wannan daula tamu gaba daya daga doron duniya!"
Samudul Ansari ya yi murmushi ya ce, "Idan na samu nasarar kashe macijiya Ziyazilu fa? Hakan zai sa dubbannin rayuka su kuɓuta daga mutuwa da ƙunci.
"NA ZAƁI NA SADAUKAR DA RAYUWATA MUDDIN DUBBANNIN RAYUKA ZASU JI DAƊI A BAYANA!"
Koda sarauniya Arya ta ji wannan batu na Samudul Ansari sai jikinta yayi sanyi, daga bisani wani ƙwarin gwiwa ya shige ta.
Boka Ƙaizadu ya ce, in dai ba wannan macijiya aka kashe ba, babu abinda zai hana Gorgons afkowa wannan daula tasu.
Meye zai hana su tashi tsaye, su kare kansu?
Idan suka sami nasarar kashe wannan macijiya, shi kenan wahala ta kau musu.
Koda sarauniya Arya tayi wannan tunani sai ta ji a ranta, ai babu laifi don sun tunkari wannan daula ta Gorgon sun nemawa kansu yanci.
Mutuwar jarumi guda ɗaya, tafi mutuwar ragwaye dubu ɗari.
Sarauniya Arya ta dubi boka Ƙaizadu ta ce, "Shin idan muka hallaka macijiya Ziyazilu, bamu da fargabar komai akan ƙabilar Gorgon!"
Boka Ƙaizadu ya yi murmushi ya ce, "Duk yadda kuke ɗaukar ƙabilar Gorgon sun wuce nan. Matakin samun nasara akan ƙabilar Gorgon guda biyu ne. Idan muka yi amfani da mataki na farko ba mu samu nasara ba, sai mu jarraba na biyun.
Wannan batu na boka Ƙaizadu ba ƙaramin sake ɗugunzuma hankalin Arya da Abu-Sharjas yayi ba.
Duk wannan kasada da zasu ɗauka zuwa saman tsaunin Hajarul Gorgon ace ba lallai bane su sami nasara ba?
"Wanne ne mataki na biyun?" inji sarauniya Arya.
Boka Ƙaizadu ya yi gajeren murmushi ya dubi Samudul Ansari sannan ya dubi sarauniya Arya ya ce, "Sai mun gwada na farkon, idan baiyi ba. Sai a jarraba na biyun!"
Samudul Ansari ya matso gaban boka Ƙaizadu ya ce, "Babban boka. Kayi min izinin tafiya daular Gorgon, tabbas zan je na kashe macijiya Ziyazilu sannan na dawo."
Yana zuwa nan a zancensa ya dubi sarauniya Arya ya ce, "Ya shugabata, ki koma gida, ki ci gaba da tafiyar da harkokin mulki. Tabbas zan je wannan waje sannan zan dawo a raye!"
Boka Ƙaizadu ya yi caraf ya ce, "Ai dole idan za'a je daular Gorgon, sai an je da jinin 'ƙabilar ARYA' domin jinin ne kaɗai zai iya juya duwatsun Hesheir dake saman wannan tsauni.
"Kun ga kenan ta wannan ɓangare tafiya da sarauniya Arya ya zamo dole."
Maimakon sarauniya Arya ta ji tsoro bisa jin wannan batu, wani irin jin daɗi da aminci ne kawai ya shige ta.
Boka Ƙaizadu ya kawo wani ruwan magani mai yawan gaske a cikin wata ƙatuwar randa, ya baiwa likita Abu-Sharjas ya ce, "Ku koma waɗannan ƙauyuka, duk wanda ya kamu da irin wannan cuta ku bashi wannan ruwa ya sha.
"Sannan ku je cikin wannan kogi, ku zuzzuba. Da izinin Ubangiji wannan cuta zata yaye. Fatan mu dai shi ne, kafun su sake juyowa ace mun kashe macijiya Ziyazilu."
Boka Ƙaizadu yana zuwa nan a zancensa ya juyo ya dubi Samudul Ansari da sarauniya Arya ya ce, "Ku je kuyi bankwana da iyalanku da kuma jama'arku, sannan ku dawo nan mu haɗa ku da hadiman da zasu kai ku tsakiyar duniya [daular Gorgon]."
Sarauniya Arya, Samudul Ansari da likita Abu-Sharjas suka yi sallama da boka Ƙaizadu suka fice daga cikin wannan kogon tsafi nasa, suka kama hanyar komawa waɗannan ƙauyuka guda uku.
Suna dawowa waɗannan ƙauyuka suka sake tarar da abin ya sake munana, domin kuwa a wannan lokaci ya kusan mutum dubu huɗu ne suka rasa rayukansu.
Abu-Sharjas ya ɗinga baiwa waɗanda wannan lalura ta jikkata amma bata kashe su ba, ruwan wannan magani wanda boka Ƙaizadu ya bashi.
Wannan ruwan magani yana rage wannan ciwo ainun, amma baya kashe cutar gaba ɗaya.
Sarauniya Arya ta wuce fadar birninta ta tara dukkanin jama'arta tayi bayanin wannan cuta da yadda zasu yi tafiya ita da Samudul Ansari domin nemo maganinta.
Samudul Ansari yana ƙarasawa inda aka kwantar da mahaifinsa ya iske shi, ya sandare jikinsa ya daina motsi sannan idanuwansa suna tsaye cak.
Hakan ne ya tabbatar da Samudul Ansari cewa, mahaifinsa ya mutu.
Samudul Ansari yana da ƙarfin zuciya, ana ganin cewa ba'a taɓa samun mai ƙarfin zuciya kamar sa ba.
A gaban idanunsa mahaifiyarsa ta mutu, bai yi kuka ba.
Mutuwar mahaifinsa tayi matuƙar sosa masa rai, amma dukda haka bai zubar da hawaye ba.
Ya durƙusa akan gawar mahaifinsa idanuwansa sun yi jawur.
Tsahon ɗan lokaci yana durƙushe akan gawar, kafun ya ɗauketa ya goya a gadon bayansa ya juya zai fita daga inda aka ajiye majinyatan domin yaje ya binne gawar.
Sarauniya Arya ya gani ta dawo wannan wuri tare da dakaru ɗari masu yi mata rakiya.
Koda taga Samudul Ansari goye da mahaifinsa kuma ga dukkan alamu mahaifin nasa baya numfashi, sai hawaye masu zafi suka zubo daga idanunta.
Sarauniya Arya da kanta tare da taimakon waɗannan dakaru masu yi mata rakiya, suka taya Samudul Ansari binne gawar mahaifinsa kusa da inda aka binne mahaifiyarsa.
Sarauniya Arya da dakarunta suka can baya suka tsaya, suka ƙyale Samudul Ansari durƙushe a gaban kabarin iyayensa yana yi musu addu'a.
****
Yau *18/02/2023*
Babi na gaba zaizo *20/02/2023*
Chapter 87-100 are still available on WhatsApp.
Contact me, if you want 08136093283 N300 Kadai.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 87: *Wadda nake so*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
U*M*S
*
Samudul Ansari na kammala addu'a a gaban kabarin iyayensa ya miƙe tsaye ya dawo inda sarauniya Arya da dakarunta ke tsaye. A wannan lokaci idanuwansa na cike da ƙwallah.
Komai ƙarfin zuciyar mutum da karɓar ƙaddararsa, idan aka ce ya rasa iyayensa dukkan biyu, sai zuciyar ta karye yayi kuka. Saboda yayi babban rashi wanda ba zai taɓa misaltuwa ba.
Sarauniya Arya ta sallami waɗannan dakaru ta ce su koma fada, aka kawo musu dawakai guda biyu, ita da Samudul Ansari suka hau kan dawakan suka tunkari dajin Ƙaiz inda boka Ƙaizadu yake rayuwa.
Akan hanyar su ta zuwa wannan daji, ba su yi wani magana sosai ba. Sarauniya Arya tayi ta baiwa Samudul Ansari haƙuri bisa wannan rashi da yayi na iyaye.
Wannan abu da sarauniya Arya tayi ya sake burge Samudul Ansari sannan yasa zuciyarsa tayi sanyi matuƙa, yaji tamkar yana tare da iyayen nasa ne.
Suna shigowa cikin wannan daji suka iske boka Ƙaizadu tsaye a ƙofar kogon tsafinsa yana jiransu.
Boka Ƙaizadu ya jajantawa Samudul Ansari wannan gagarumin rashi da yayi, sannan ya fiddo tsohuwar takarda wacce aka

Please Login or Register in order to submit comment