Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gagara hallakawa a karon farko.
Aymanul Faris ya kaiwa sadauki Kamaru sara a ƙirjinsa, da takobin Saiful Shiradu.
Cikin tsananin raini da taƙama da jikin tauri wannan sadauki ya haɗe hannayensa a waje guda, sannan ya rintse idanunsa ya doki ƙasa da sawunsa guda. Nan take wani abu mai kama toka ya lulluɓe dukkanin jikinsa.
Sadauki Kamaru ɗan wata ƙabila ce da jikinsu yake da mugun-tauri. Ance babu makamin da yake tasiri a jikinsu muddin suka ƙaddamar da wannan jikin tauri nasu.
Sannan sadauki Kamaru yasha gwada wannan jiki nasa, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, don haka yana da yaƙinin cewa indai da ƙarfe aka ƙera takobi, to, babu abinda zata yi masa.
Takobin Saiful Shiradu tana dira bisa ƙirjinsa yaji wani irin mugun zogi ya shige shi, tamkar ƙarfe aka saka a cikin wuta aka bari yayi zafi sannan aka ɗoɗana masa a ƙirjin.
Sadauki Kamaru ya kwarara uban ihu a lokacin da wannan ƙirji nasa yayi wawakeken tsagu, kuma naman wannan wuri ya gasu sosai.
Cikin tsananin mamaki sadauki Aiys da sadauki Kamaru suka dubi wannan takobi dake hannun Aymanul Faris, suka ganta doguwar takobi ce, ƙarfenta yayi jajawur tamkar garwashin wuta.
Nan take suka sha jinin jikinsu, suka tabbatar da cewa lallai fa wannan takobi ba gama-garin takubba bane, dole sai sun zage dantse idan suna son tsira da rayuwarsu.
Sadauki Kamaru yasa hannu ya murje wannan rauni dake bisa ƙirjinsa, cikin tsananin juriya irin ta mazan ƙwarai, sannan ya dubi sadauki Aiys yayi masa wata inkiya.
Aiys na ganin wannan inkiya ya dako tsalle ya kawowa Aymanul Faris suka a tsakiyar ƙirjinsa da wannan mashi nasa, cikin zafin nama Aymanul Faris ya kauce mashin ya soki iska.
Sai dai kuma, wannan ita ce damar da sadauki Kamaru yake jira. Yana ganin hankalin Aymanul Faris ya tafi akan kaucewa wannan mashi ya daka tsalle ya gabza masa wawan naushi a gefen ƙirjinsa da wannan lafcecen hannu nasa.
Aymanul Faris ya tashi sama tamkar wanda aka harba daga cikin majaujawa ya faɗo a bakin gaɓar wannan teku, saboda ƙarfin wannan naushi na sadauki Kamaru, ji yayi tamkar ƙirjinsa ya goce ya koma gefe ɗaya.
Sadauki Aiys ya daka tsalle daga inda yake tsaye ya kawowa Aymanul Faris suka da wannan mashi dake hannunsa, Aymanul Faris bai ankare ba sai da mashin yazo gab da ƙirjinsa zai soke shi.
Cikin zafin nama irin wanda bai taɓa amfani dashi ba, ya gocewa wannan hari. Mashin sadaukin ya soke ƙasar wannan wuri, da yake a ɗan jiƙe take. Nan take ta daskare tamkar a tsakiyar ƙanƙara take.
Tabbas inda a ce jikin Aymanul Faris ya samu da abinda ya faru da ƙasar, shi ne zai faru da shi.
Kafun Aiys ya zaro mashinsa daga ƙarƙashin ƙasa, Aymanul Faris ya kai masa sara a wuya da nufin ya guntule masa kai.
Amma kafun takobin ta isa wuyansa, Aymanul Faris ya ga an riƙeta. Ba wani bane ya riƙeta ba illa sadauki Kamaru.
Cikin sauri na gaban kwatance tamkar mutum ya taɓa wuta bai sani ba, haka sadauki Kamaru ya saki wannan takobi sannan ya dunƙule hannunsa ya ƙwala ihu.
Ko tambaya babu ka san ƙonewa hannun nasa yayi.
Har a wannan lokaci sadauki Aiys bai gama zaro wannan mashi nasa daga cikin ƙasa ba. Ga dukkan alamu inda yake fuskantar matsala shi ne mashin nasa yana yawan maƙalewa idan ya caki wani abu wanda bai kasance jikin halitta mai rai ba.
Cikin kwanciyar hankali Aymanul Faris ya danƙara masa sara a gadon baya, nan take wannan wuri ya tsage, naman wurin ya gasu sosai.
Aymanul Faris ma bai ankara ba, yaji an doki gadon bayansa da ƙarfi. Nan take ya tashi sama tamkar wanda aka harbo daga cikin baka ya faɗa cikin wannan teku ya nutse a ƙarƙashinta.
Sadauki Kamaru ya ƙarasa wajen Aiys wanda ke kwance a baje yana ta ihu sakamakon mugun zogin dake ratsa shi, tamkar ana zuƙar jinin jikinsa. Kamaru ya dago shi, sannan ya fara shafa masa magani akan wannan rauni nasa.
A gefe guda kuma, fafatawar takobi ce mai zafi tayi nisa tsakanin jaruma Riya da sadauki Saif. Idan kaga yadda suke sarrafa takobi zaka rantse kace waɗannan takubba wani sassa ne na jikinsu.
Tsahon wannan lokaci suna ta fafatawa amma babu wanda ya yiwa ɗan uwansa koda ɗan ƙaramin rauni, saboda tsananin zafin namansu da yadda suke sarrafa waɗannan takubba.
Sadauki Saif ya cika da tsananin mamakin bisa ganin yadda aka samu mutumin da ya kai shi iya sarrafa takobi a duniya. Sannan ransa ya soma sosuwa bisa ganin lokacin da aka shafe ana wannan gumurzu amma ko kwarzane bai yiwa wannan budurwa ba.
A matsayinsa na mutumin da yafi kowa iya sarrafa takobi, kuma ko ba komai wannan na daga cikin dalilan da suka sa sarki Dujalu ya ɗauke shi aiki a wannan tsibiri.
Babban abinda yafi ɗugunzuma masa hankali shi ne, duk wani salon da ya fitowa wannan budurwa da shi, sai yaga ita ma ta iya.
Sadauki Saif tsohon mutum ne, wanda ya jima yana karɓar horo akan takobi.
Saboda wannan dalili dole ne yayi mamaki idan aka ce yarinƴa ƴar shekara goma sha zuwa ashirin ta gagare shi akan abinda ya ɓata tsahon shekara da shekaru yana koyansa.
A fusace Saif ya sauya salon yaƙinsa izuwa wanda bai taɓa amfani da shi ba akan kowa. Tsalle yake yi sama kamar tsuntsu sannan sai yana jujjuya takubban nasa guda biyu a tare tamkar fuka-fukin tsuntsu.
A karon farko sai da ya sami nasarar yankan damtsen hannun jaruma Riya, wannan baƙar riga nata ta yage kaɗan jini ya fara zubowa amma kaɗan-kaɗan.
Sadauki Saif na ganin haka yayi farin ciki a cikin ransa bisa ganin samun wannan nasara. Ya sake dako wannan tsalle yana wannan wasa da takobi nasa.
Kafun Saif ya ƙaraso inda take tsaye, jaruma Riya ta ɗan yi wani gajeren tunani izuwa lokacin da take yarinƴa ƙarama sa'adda sadauki Jarata yake koya mata wasa da takobi.
Tabbas ya koyar da ita irin wannan salo na sarrafa takobi, kuma ya koyar da ita yadda zata kare kanta daga irin wannan salo.
Jaruma Riya ta sha wahala sosai wajen koyon wannan salo da yadda zata kare kanta akai, saboda haka ta ƙware matuƙa akan sa.
Sadauki Saif na ƙarasowa jaruma Riya ta shammace shi, tayi kamar zata yi dama, hankalinsa ya karkata akan daman nata, cikin zafin nama ta goce tayi hagu.
Saif ya wuce ta damanta ba tare da ya cutar da ita ba, ita kuma ta juyo ta hagunsa ta danƙara masa sara akan kafaɗarsa. Nan take wajen ya ɓarke yayi wawan rami. Jini mai yawa yayi tsartuwa daga cikin raunin.
Sadauki Saif ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu wanda ya janƴo hankalin sadauki Kamaru da Aiys waɗanda ke zaune a gefe guda, suna shafawa raunikan jikinsu magani. Jin ihun ɗan uwan nasu yasa suka taso da sauri suka ruga inda yake.
Suna ƙarasowa suka saka jaruma Riya a tsakiya. Sadauki Kamaru ya gama wartsake damatsansa, sadauki Aiys ya gama gyara tsinin mashinsa, sadauki Saif ma ya ɗan dawo hayyacinsa ya gyara riƙe takubbansa guda biyu.
Mutum zai iya cewa rayuwar jaruma Riya tana cikin mugun haɗari saboda koda zata iya kaucewa harin mutum biyu daga cikin waɗannan sadauki, ba zata kaucewa na ukun ba. Sannan harin kowa daga cikinsu shu'umi ne wanda zai iya janyo asarar rai baki ɗaya.
Jaruma Riya ta wulwula waɗannan takubba nata guda biyu, tayi juyi a tsakiyar waɗannan sadaukai guda uku sannan ta fara kallon su ɗaya bayan ɗaya, tana jira taga waye zai fara kawo mata hari.
Kamar haɗin baki waɗannan sadaukai guda uku suka ja baya a tare, sannan suka rugo da gudu zasu turmushe ta a tsakiya. Kamaru yana shirin gabza mata wawan naushi, Aiys yana shirin caka mata wannan mashi, shi kuma, Saif yana shirin fille kanta da sawayenta da waɗannan takubba nasa.
A wannan karon alamun tsoro kaɗan sun bayyana a fuskar jaruma Riya, amma kaifafan idanunta irin na mazan ƙwarai suna nan a yadda suke.
Cikin dakewar zuciya irin ta MACE MAI KAMAR MAZA, jaruma Riya ta gyara riƙe takubbanta sannan ta ware hannayenta biyu tana jiran isowarsu.
Sadauki Kamaru yana isowa ya kawo mata wawan naushi a fuska, cikin zafin nama ta kauce. Sannan ta sake yin alkafira tayi tsalle baya, lokacin da takubban sadauki Saif suka iso, suka sari iska.
Abinda bata sani be shi ne, akwai mashin sadauki Aiys wanda ya taho ta bayanta, ba tare da ta sani ba. Wannan mashi ne shu'umi wanda yana taɓa jikin mutum zai daskarar da mutum ya zamar dashi gunki.
Sannan ga wannan mashi tafe a bayanta, ba tare da sanin hakan ba. Mutum zai iya cewa tabbas ƙarshen jaruma Riya yazo.
Saura ƙiris wannan mashi ya soketa aka ga wani irin jan haske mai kama da wutar-maƙera ya shiga tsakaninta da wannan mashi.
Hasken dake jikin tsinin wannan mashi na taɓa wannan jar-wuta ya soma disashewa yana rage haske, sannan wannan mashi ya tsaya cak, a cikin iska tamkar umarni yake bi.
Cikin tsananin mamaki waɗannan sadaukai guda uku suka juya baya suka hango daga inda wannan jar-wuta take tahowa. Itama jaruma Riya ba'a barta a baya ba, wajen juyawa domin ganin wannan hatsabibi.
Wani kyakkyawan saurayi suka gani ya taso daga ƙarƙashin wannan teku sannan ya nuna hannayensa ga waɗannan sadaukai guda uku. Kallon farko jaruma Riya ta gane wannan saurayi domin kuwa ba kowa bane illa masoyinta Aymanul Faris.
Waɗannan sadaukai suka fara shawarar meye ya kamata su yi, shin su haɗa ƙarfi da ƙarfe su yaƙi Riya ko kuma su afkawa Aymanul Faris?
Sai dai fusataccen Aymanul Faris bai basu damar yanke wannan shawara ba, ya aika musu da wani dunƙulen wuta tamkar ƙwallo.
Kafun wannan dunƙulen wuta ya isa tsakiyarsu wata iska mai ƙarfi tayi jifa da jaruma Riya gefe guda. Su Kamaru suna tsaye cikin tsananin mamaki, wannan dunƙulen wuta ya dira a tsakiyar su.
Kamar an tashi nakiya haka wannan dunƙulen wuta ya fashe a tsakiyar wadannan sadaukai guda uku, yayi jifa da su can gefe nesa da wannan wuri.
Idan mutum ya lura da kyau zai ga cewa jikin waɗannan sadaukai uku ya babbake sosai, don har fatan jikinsu tana saluɓewa. Tabbas wannan hari da Aymanul Faris yayi amfani dashi akan waɗannan sadaukai guda uku babban hari ne.
Jaruma Riya ta rugo da gudu ta rungume Aymanul Faris cikin tsananin nuna soyayya da jin daɗin ceton rayuwarta da yayi. "Nagode masoyina. Tabbas kazo a lokacin da ya dace kuma ka ceci rayuwata, bansan tayaya zan gode maka ba?"
Aymanul Faris yayi murmushi ya janƴe jikinsa daga nata, suka fuskanci juna sosai. "Kada ki damu. Zan kasance mai kare rayuwarki a koda yaushe kamar yadda zan kare rayuwata da ta dukkanin Kuyurun dake ƙarƙashin mulkina."
Jaruma Riya tayi murmushi mai taushi a gare shi ta ce, "Tabbas ban taɓa ganin rana ta farin ciki, irin wannan rana ba. Na farko zan gaji sulken-yaƙin da mahaifina ya mutu ya bar min. Na biyu kuma, masoyina na kwarai ya ceci rayuwata a lokacin da nake buƙatar taimako."
Aymanul Faris yayi mata murmushi mai taushi ya ce, "Zo muje mu ɗakko wannan sulke, mu tafi?" yana faɗin haka ya nufi ƙofar wannan gida mai kama da gidan tarihi.
Caraf jaruma Riya ta kamo hannun shi, a gigice ya juyo ya kalleta. "Me ma'anar hakan? Kizo muje mu yi abinda ya kawo mu." ya bata umarni a nutse.
"Gaggawar me muke, bayan mun riga mun sami nasara akan waɗannan sadaukai? Sannan ai ya kamata mu jira Barban ya ƙaraso ko? " jaruma Riya ta amsa masa.
Aymanul Faris yayi ƴar gajeriyar dariya ya ce, "Tabbas mun gama da waɗannan sadaukai guda uku, amma, har yanzu babban mai gidan nasu bai bayyana ba. Wato, sarki Dujalu. Wannan shi ne dalilin da ya hana Barban bayyana ba."
Suna cikin wannan tattaunawa ne, suka ga yanayin wannan wuri ya soma sauyawa izuwa duhu-duhu, sannan ruwan wannan teku ya soma fantsama yana yin tsiri izuwa sama.
Cikin shirin ko-ta-kwana Aymanul Faris da jaruma Riya suka sake zare makaman yaƙin su, sannan suka ƙurawa wannan ruwan teku idanu wanda yafi ko'ina fantsama.
Kwatsam! Wani irin ƙaton maciji ya ratso ta cikin wannan teku, mai tsananin girma da kwarjini. Macijin ya wangame ƙaton bakinsa tamkar zai haɗiye dukkan abinda ke wannan wuri.
Wani gajeren mutum ya ratso ta cikin bakin macijiya ya fito tamkar wanda ya fito daga cikin ƙofar ɗakin sa, ko,ɗigon ruwa babu a jikinsa. Kai kace ba daga cikin bakin wannan macijiya ya fito ba.
A wannan lokaci ya saka baƙaƙen kaya masu ratsin yalo da beza a hannayensu da kuma ƙafafu. Yana goye da wata gajeriyar sanda a gadon bayansa wanda take walwali da haske lokaci-lokaci.
Kallon farko jaruma Riya da Aymanul Faris suka shaida wannan mutumi, domin kuwa ba kowa bane, illa sarki Dujalu da Barban ya nuna musu a cikin wannan madubin tsafi.
“Ina ganin kamar kunyi gaggawa da kuke tunanin tafiya ɗauko wannan sulke, ba tare da kun ƙarasa hallaka waɗancan dakaru nawa ba. Koda yake ni hakan ma yayi min, tun da zan samu nasarar kama ku, sannan ko ɗaya daga cikin jarumaina bai mutu ba.” inji sarki Dujalu cikin murya mai nuna yarda da kai.
Jin wannan batu nasa yasa Aymanul Faris da jaruma Riya suka daka tsalle suka kewaye shi a tsakiya, jaruma Riya tana wulwula takubbanta guda biyu a cikin iska, shi kuma Aymanul Faris yana ƙaddamar da zanen fuskokin waɗannan aljanu guda goma a cikin wannan ƙarfen takobi.
Sarki Dujalu na ganin haka yayi murmushi kamar dama abinda yake jira kenan, cikin hanzari ya zaro wannan sanda dake ɗaure a gadon bayansa, ya nuna ƙasar wannan tsibiri da ita sannan ya ɗagata sama ya nuna sararin samaniya. Daga nan ya nuna gefe da gefe (yamma, gabas, kudu da arewa) da wannan sanda.
Nan take wani hadari ya bayyana a sama wanda girmansa da faɗinsa ba zai wuce girman wannan tsibiri ba, ya soma yiwo ƙasa-ƙasa. Sannan ƙasar da suke kanta a saman wannan tsibiri ta soma narkewa tana shigewa cikin wannan teku, bangwaye guda huɗu na kowacce ƙusurwa suka soma tasowa da ruwa mai yawa tamkar za'a yi ambaliya suka tunkaro wannan tsibiri.
Ga wannan baƙin hadari dake tahowa daga sama zai danne su Aymanul Faris sannan ga wannan zabtarewar ƙasa da wannan tsibiri yake, ga ruwa mai yawa yana tahowa daga kowanne ɓangare zai haɗe su a tsakiya.
Aymanul Faris da jaruma Riya suka soma guje-guje daga bisa wannan tsibiri, suna neman inda zasu tsaya kada wannan girgizar ƙasa ya haɗiye su.
Inda matsalar take, babu wajen guduwa, wannan tsibiri ƙarami ne sosai sannan ruwan teku da hadarin dake tunkaro shi, yasa su Aymanul Faris daɗa gigicewa.
Kafun su gama ankarewa tuni wannan tsibiri ya gama zabtarewa gaba ɗayansa ya nutse izuwa ƙarƙashin wannan teku. Abin mamaki sarki Dujalu da wannan gidan ajiye makaman yaƙi nasa, suna tsaye daram akan iska. Tamkar waɗanda ke tsakiyar gidajen su, ko alamun faɗawa basuyi ba.
Aymanul Faris da jaruma Riya suka nufi wannan ruwan teku da gudu zasu nutse izuwa ƙarƙashinsa. Aymanul Faris zai iya samar da aljani wanda zai kare shi, to, amma inda matsalar take, shi kaɗai wannan aljani zai ɗauka, ba zai iya ɗaukar su su biyu ba. Saboda Riya bata da irin sirrin dake jikinsa wanda yake hana wuta ƙona shi komai zafinta.
Saboda wannan dalilin ne yasa, ya sallama rayuwarsa da nata, idan suka nutse izuwa ƙarƙashin tekun zasu san tayi.
Kafun su isa cikin ruwan wannan teku, aka ga sun tsaya cak, a cikin iska. Ruwan teku mai sanƴi dake ƙasansu, ya juye ya koma mai ɗumi wanda har wani tiriri yake fitarwa. Wannan hadari dake saƙƙowa ya koma baya da gudu cikin gajimare ƴan uwansa. Ƙasar wannan tsibiri da ta nutse ta fara ɓuɓɓugowa daga cikin ruwan wannan teku tana dawowa yadda take a da.
Tsahon ɗan lokaci, kafun wannan wuri ya dawo kamar yadda yake a da. Ruwan tekun ya dawo ainihin yadda yake, baƙin hadari ya ɓace ɓat, ƙasar wannan tsibiri ta sake wanzuwa.
Cikin tsananin mamaki da kaɗuwa sarki Dujalu ya juya yana dube-dube domin kallon babban matsafin da ya iya tarwatsa masa hare-haren tsafinsa.
***
Yau *12/12/2022*
Babi na gaba zaizo *15/12/2022* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 57: *Mubaya'ar Sarki Dujalu*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
UMAR SANGARU
*
Nan take siffar wani mutum ta bayyana bisa wannan ruwan teku. Sanƴe yake cikin fararen tufafi masu bayar da haske da walwali. Gashin kansa dogo ne sosai, sannan baƙi ne siɗik. Fararen kayan dake jikin nasa dogwaye ne sosai, sun rufe dukkanin wata sura ta jikinsa.
Hakan ne ya ɓoye surar jikinsa, yadda mutum ba zai iya gane murɗaɗɗe ne ko sakakke ba. Idanuwansa na da ban al'ajabi maimakon baƙin idon, wani kore ne kamar na kyanwa.
Su Aymanul Faris suna dira bisa ƙasar wannan tsibiri suka ɗaga kawunan su sama domin ganin wannan matsafi su ma. Ai kuwa suna ɗaga kawunan su suka kalle shi.
Ba wani bane illa KILAWUD BARBAN wanda suka taho wannan aiki tare da shi. Amma, abin mamaki ya sauya musu matuƙa. Wannan siffa da yake cikinta a yanzu, basu taɓa kallonsa da ita ba. Wani irin kwarjini da ƙamshin sihiri irin na matsafan farko na tasowa daga jikinsa.
Tabbas saboda dalilai guda uku ne kawai zasu yarda da cewa wannan shi ne Barban ɗin da suka taho da shi. Dalili na farko shi ne dukda cewa fuskarsa ta ɗan sauya matuƙa amma tana nan a yadda suka santa. Dalili na biyu shi ne irin wannan sutura da take jikinsa kullum, wadda suma da ita suka saba ganinsa. Dalili na uku shi ne, kawo musu ɗauki da yayi a lokacin da suke gab da nutsewa a cikin teku.
Barban ya tankwashe a ƙafafu akan iska tamkar wanda ke zaune akan kujera, ya rufe idanunsa sannan ya taho a hankali ya nufi inda sarki Dujalu ke tsaye.
Sarki Dujalu na ganin haka ya sake zaro wannan sanda tasa, ya gyara riƙeta da kyau. Sannan jikinsa ya soma karkarwa wanda hatta shi kansa bai san dalilin haddasa shi ba.
Dujalu tsohon mutum ne a duniya wanda ya jima sosai yana bincike a fannin tsafi. Idan mutum ya ce sarki Dujalu babu abinda bai sani ba a duniya, bai yi laifi ba. Saboda tsananin yadda yake shige-da-fice a binciken tsafi.
Irin wannan siffa ta Barban, sarki Dujalu ya san ta sarai kamar yadda yasan ƴunwar cikinsa. Saboda gogaggun matsafa ne masu tsananin ban tsoro.
Sarki Dujalu ya ɗaga wannan sanda tashi sama, ya nuna gajimare da ita. Nan take wani baƙin hadari ya taso a daidai saman wannan tsibiri. Waɗansu fararen walƙiya masu kashe idanu suka soma sukuwa a cikin wannan hadari, kafun daga bisani su soma haɗewa a waje guda suna shigewa cikin wannan sanda ta sarki Dujalu.
Murtuƙeƙen walƙiya daga can ƙololuwar sama ya shiga jikin wannan sanda suka haɗe a waje guda, idan ka dubi jikin wannan sanda zaka ga walƙiya wanda ya yi sama har cikin wannan baƙin hadari.
Barban na ganin haka, yayi murmushi. Idanuwansa suka yi koren haske mai ɗaukar hankali musamman a wannan yanayi da wannan tsibiri yake ciki, na ɓuyar rana a cikin hadari.
Baiyi wani yunƙuri na kare wannan walƙiya ta sarki Dujalu ba, wataƙila hakan ta samo asali ne saboda sarki Dujalu bai farmake su da walƙiyar ba.
Tsahon ɗan lokaci wannan farar walƙiya tana sukuwa tsakanin wannan baƙin hadari da wannan tsibiri, kafun sarki Dujalu ya nuna su Aymanul Faris da ita. Tabbas ya san cewa bai isa ya tunkari Barban a wannan lokaci ba, amma idan ya cutar da waɗanda suke tare da shi kamar ya cutar da shi ɗin kansa ne.
Waɗansu irin walƙiya masu yawan gaske suka tunkaro su Aymanul Faris zasu ƙone su. Ai kuwa, yana ganin haka ya fiddo wannan takobi tasa ta Saiful Shiradu ya ƙaddamar da aljanun wuta guda goma, yasa guda biyar suka kewaye shi, guda biyar suka kewaye jaruma Riya.
Dukda haka Aymanul Faris bai aminta da waɗannan aljanu zasu kare su ba, ya sake ƙaddamar da waɗannan jajayen gajimare masu kama da guma-guman wuta. Wata irin jar walƙiya ta fara saƙƙowa daga cikin wannan gajimare tana kewaye jikinsa da na jaruma Riya.
Idan ka hango Aymanul Faris da jaruma Riya daga nesa, zaka gansu tsaye a tsakiyar waɗansu jajayen aljanu masu jiki na wuta, sannan ga jar walƙiya tana ta kewaye jikinsu, kamar kawanƴa.
Rukunin farko na walƙiyar sarki Dujalu tazo ta doki jikin waɗannan aljanun-wuta, dukkaninsu su goman suka ƙwala ihu a tare saboda zogi da raɗaɗin da suka ji. Rukuni na biyu yana dukan jikinsu suka fara tsatstsagewa tamkar zasu tarwatse.
Dama wannan walƙiya da sarki Dujalu ya aiko musu rukuni biyu ce kawai, saboda ya raina ƙarfin sihirin su Aymanul Faris.
Yana ganin haka ya ɗan haɗe fuska cikin jinjina, sannan ya sake ƙaddamar da wata walƙiyar, amma saɓanin na da wannan walƙiya shuɗi-shuɗi ce tamkar ruwan teku.
Tuni jikin waɗannan aljanu na wuta masu kare su Aymanul Faris da ya soma tsatstsagewa, ya koma kamar yadda yake a da. Daɗin waɗannan aljanu shi ne duk irin raunin da aka yi musu, indai suka huta zasu warke.
Barban ya tsaya a cikin iska yana kallon yadda wannan gumurzu zai kasance, yana so yaga iyakacin ƙarfin hadiman Saiful Shiradu wajen kare rayuwar Aymanul Faris da ta Riya, idan sun gagara sai yasa hannu.
Sarki Dujalu ya sake nuna su Aymanul Faris da wannan gajeriyar sanda tasa, nan take shuɗi-shuɗin walƙiya ya tunkaro su Aymanul Faris gadan-gadan. Maimakon hari na farko mai rukunai guda biyu, wannan hari rukunai guda uku ya ƙunsa.
Amma, su Aymanul Faris basu san da hakan ba, daga shi Dujalu sai kuma Barban dake tsaye a cikin iska a can gefe guda.
Waɗannan aljanun-wuta guda goma dake tsaron su Aymanul Faris suka sake dakewa cikin baƙin rai da dakewa irin ta mazan kwarai. Kai da gani ka san cewa sun tsaya tsayin-daka kenan, sai inda ƙarfin su ya ƙare.
Rukunin farko na walƙiyar sarki Dujalu yazo ya doki jikinsu, basu san sa'adda suka ɗan ja da baya ba saboda tsananin zogi da raɗaɗin da ya shige su. A wannan karon tun daga rukunin farko jikinsu ya soma tsatstsagewa.
Lallai wannan walƙiya ta sarki Dujalu mai tsananin ƙarfi ce. Rukuni na biyu yana dukan jikin waɗannan aljanu suka soma fashewa suna tarwatsewa tamkar an saka musu nakiya.
Aljanun-wuta guda huɗu suka tarwatse jikinsu ya bi iska. Sauran na ganin haka suka sake haɗewa a waje guda a wani salo na bayar da kariya.
Wannan rukuni na uku yafi sauran biyu na farkon ƙarfi. Yana zuwa jikin waɗannan aljanu guda shida da suka rage ya tarwatsa jikinsu su ma suka bi iska.
Aljanun-wuta guda goma da Aymanul Faris ya samar duk suka zama matattu a wannan lokaci. Shima sarki Dujalun ya ɗan ji jiki, saboda yayi amfani da kaso mai yawa daga cikin tsafin sa.
Aymanul Faris ya mayar da wannan takobi cikin kufenta, sannan ya sake zarota. Nan take waɗannan aljanu guda goma suka sake bayyana, suka kewaye shi kamar da.
Sarki Dujalu na ganin haka yayi murmushi ya ɗaga wannan sanda tashi sama, ya ruga da gudu kan Aymanul Faris da niyyar su ruguntsume da azababben yaƙi.
Aymanul Faris ya kaɗa ƙarfen wannan takobi, nan take waɗannan aljanu suka ɓace gaba

Please Login or Register in order to submit comment