Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

likita Abu-Sharjas ya bashi wannan ƙatuwar kwalba wadda wannan sarki (da bai sunansa ba) ya bashi.
Duk wanda aka baiwa ruwan cikin wannan kwalba, da zarar ya sha saiya warke daga wannan cuta gaba ɗaya.
Samudul Ansari, sarauniya Arya da likita Abu-Sharjas suka zage damtse suka yi ta baiwa marasa lafiya ruwan wannan magani suna warkewa.
Kafun cikar sa'a uku, tuni al'umar waɗannan ƙauyuka gaba ɗaya sun gama warkewa daga wannan cuta.
Samudul Ansari, sarauniya Arya da likita Abu-Sharjas suka yi hawa suka zagaye wannan daula gaba ɗaya suka rarraba wannan magani.
Har suka iso cikin wannan birni wanda suka haɗu da su Nurbas.
Jarumi Nurbas na kwance a cikin ɗakinsa, ya kusa mutuwa don a wannan lokaci zaka iya cewa numfashin da suka rage masa a ƙirge suke.
Shima kansa ya fidda rai ga rayuwa.
Samudul Ansari yayi gaggawar ɗura masa wannan magani ya sha, ai kuwa take ya warke.
Bayan Nurbas ya gama yiwa Samudul Ansari godiya ya ce, "Tabbas zan biyaka ladar wannan aiki da kayi mini, amma sai nan gaba kaɗan..."
Samudul Ansari yayi murmushi ya ce, "Ni ban ceci rayuwarka domin ka biyani da wata dukiya ba..."
A wannan daula gaba ɗaya sai da aka san wane ne Samudul Ansari, jarumin da yayi tafiya izuwa waje mai mugun haɗari a duniya ya samo maganin annoba.
Kafun kace kobo, tuni Samudul Ansari ya fara yin farin jini a zuƙatan waɗannan jama'a gaba ɗaya.
Samudul Ansari da sarauniya Arya suka sake hawa irin waɗannan dawakai nasu, suka tasarwa dajin Ƙaiz inda boka Ƙaizadu yake.
Saboda gudun waɗannan dawakai, gajeriyar tafiya kawai suka yi, suka isa cikin dajin.
Suna shigowa cikin dajin suka yi arba da boka Ƙaizadu tsaye yana jiran su.
Bayan kammala gaisuwa Ƙaizadu ya shige gaba suka biyo shi a baya.
Suna shigowa cikin kogon Ƙaizadu ya basu wajen zama. Sannan ya kawo musu abin taɓawa.
****
Yau *27/02/2023*
Babi na gaba zaizo *02/03/2023* da yaddar ALLAH.
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 91: *Mataki na biyu*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U * M * S
*
Ƙaizadu ya dubi Samudul Ansari ya ce, "Tun kafun ku tafi wannan tafiya, na san cewa ba za kuyi nasara ba!
"Saboda babu wanda ya isa yayi arba da Ziyazilu idan ba sarauniya Yilan da manyan sarakunanta guda biyar ba!
"Babban dalilin da yasa na tura ku daular Gorgon shi ne, haɗuwa da wannan ƙaton jirgin ruwa wanda ke ɗauke da mutanen sarkin ƙabilar AZBIN.
"A zahirin gaskiya sarkin ƙabilar Azbin shi ne kaɗai wanda ke ɗauke da maganin wannan cuta, kuma shi ne kaɗai yake da bayani akan ruhin Samudul Ansari (Tau'rin ma'ana na II).
"Kun ga kenan haɗuwa da sarkin ƙabilar Azbin yazo mana har da ribobi guda biyu; maganin wannan cuta da kuma bayanin Tau'rin..."
Sarauniya Arya ta ɗan dakatar da Ƙaizadu da hannu ta ce, "Babban boka! Ba wannan bayanan muka zo ji ba, kayi sani cewa nan da cikar makonni uku, mayaƙan Gorgon [ma'abota Bankai da waɗanda basu da] zasu shigo duniya farautar Samudul Ansari.
"Mun zo ne domin kayi mana cikakken bayani akan saƙonnin da ya kawo guda biyu don ya ce a wajenka kaɗai zamu samu cikakken bayanin.
"Sannan sai ka sanar da mu batun MATAKI NA BIYU wanda wannan sarki ya ce, da shi ne kaɗai zamu iya yaƙar ƙabilar Gorgon."
Ƙaizadu na jin wannan batu yayi dariya sannan yayi shuru yana tunani tamkar mai sauraron wani abu.
Daga bisani ya ce, "Sarkin ƙabilar Azbin ya sanar da ku a saƙon sa na farko cewa, mataki na biyu ne kawai zaiyi tasiri wajen yaƙi da ƙabilar Gorgon sannan ni ne wanda zai yi muku bayanin wannan mataki, haka ne?"
Samudul Ansari da sarauniya Arya suka gyadawa Ƙaizadu kai alamun haka ne.
Ƙaizadu ya gyara zama sannan ya soma yi musu bayani.
"Ni da mai gidana [sarkin ƙabilar Azbin] mun san cewa ba zaku taɓa samun nasara a mataki na farko ba, wannan yasa bamuyi gaggawar sanar da ku mataki na biyu ba, domin mai gidana yana so ya jarraba jarumtakar Samud sannan yana so ya nunawa ƙabilar Gorgon ƙarfinsa.
"Mun sami nasarar wannan aiki, ƙabilar Gorgon ta ga ƙarfin Samud sannan hatta sarauniyarsu sai da ta girgiza.
"Ina so ku bani aron kunnuwanku domin ku saurari bayanin mataki na biyu wanda zai yi matuƙar girgiza duniya..."
Ƙaizadu ya ɗauki wani abin sha a cikin kofin dake gefensa ya kurɓa sannan ya ci gaba da zayyano bayani.
"Wannan mataki na biyu mai gidana [sarkin ƙabilar Azbin] ya kira shi da suna 'gamayyar jini' guda biyu domin samun mafita.
"Mutanen ƙabilar Gorgon suna da bambanci sosai da sauran mutanen duniya.
"Babban manazarci na ƙabilar Azbin ya taɓa kama ɗaya daga cikin waɗannan halittu sannan ya gudanar da kyakkyawan bincike akansa.
"Manazarci ya ce, jinsin Gorgon suna ɗauke da nau'in jini mai matakin [L]
"Wani irin nau'i ne wanda duk duniya babu mai irinsa face waɗannan halittu.
"Kwanakin bayan nan, manazarcin ya sanar da sarkin ƙabilar Azbin cewa, duk duniya babu jinin da zai iya karya 'nau'in L' idan ba jini mai 'nau'in M' ba.
"Mun yi bincike duk faɗin duniya, babu jini mai nau'in M.
"Saboda wannan dalili dole sai an samar da wannan jini, idan har ana so a karya ƙabilar Gorgon daga duniya.
"Bayan gudanar da doguwar bincike ƙabilar Azbin ta gano cewa, jini mai nau'in H idan ya haɗu da jini mai nau'in J zai bayar da jini mai nau'in M..."
Lokacin da boka Ƙaizadu yazo nan a batunsa sai yayi shuru, ya kurɓi wannan sha dake hannunsa.
Sarauniya Arya ta dube shi ta ce, "Ya kai wannan boka, ba mu gane wannan bayani naka ba, shin zaka iya yi mana komai dalla-dalla?"
Ƙaizadu yayi murmushi sannan ya ci gaba, "Sarkin ƙabilar Azbin ya sanar da ni sakamakon binciken da wannan manazarci yayi.
"Sarkin ya ce, duk duniya mutane guda biyu ne, suke da nau'in H da J wanda babu wani gauraye a cikinsa.
"Idan har ya zamo dole ana so a yaƙi Gorgons, to ya zamo dole waɗannan mutane guda biyu su auri juna.
"Ɗaya daga cikinsu wanda ya kasance namiji yana da jini mai nau'in H, da zarar nau'in H ya haɗu da nau'in J. Wani bijimin sadauki zai bayyana amma ba'a wannan zamani ba.
"Shima wannan namiji (mai nau'in H) zai gawurta a wannan zamani, sannan zai fi ƙarfin dukkan abokan gabar sa.
"Wannan shi ne mataki na biyu. Ina fatan kun gane bayanai na?"
Samudul Ansari ya ce, "Mun gane wannan batu naka amma a kaikaice. Kamata yayi ka fito ka bayyana komai yadda zamu gane..."
Ƙaizadu yana jin wannan batu yayi murmushi, ya ɗan yi shuru kamar ba zai ci gaba da wannan bayani ba.
Daga bisani ya yi ajiyar zuciya ya dubi sarauniya Arya da Samudul Ansari ya ce, "Ke ce wadda ke ɗauke da asalin jini mai nau'in J. Kai kuma kaine wanda ke ɗauke da jini mai nau'in H.
"Haka binciken masana ya tabbatar..."
Koda jin wannan batu sai ƙirjin Samudul Ansari ya buga da ƙarfi. Me wannan boka yake nufi kenan?
Kenan ana nufin shi ne zai auri sarauniya Arya?
A lokacin tunanin Zarifa ya faɗo masa a rai, nan take zuciyarsa ta buga da ƙarfi.
A duniya idan ka cire uwa da uba, Samudul Ansari ya san babu wadda take ƙaunarsa kamar Zarifa.
Saboda tsananin yadda Zarifa take matuƙar ƙaunarsa Samudul Ansari yayi rantsuwa akan cewa, ita zai fara aure.
Tabbas wannan lalura da ta bijiro zata iya dagula masa lissafi.
A ɓangaren sarauniya Arya, tsananin farin ciki take. Saboda ta kamu da tsananin ƙaunar Samudul Ansari amma bata taɓa sanar da shi ba, dukda cewa kuwa, abin na damun ta.
Bata taɓa tsammanin zata mallake shi da wuri haka ba.
Sarauniya Arya ji take tamkar kyautar wannan duniya gaba ɗaya aka bata.
Babu abinda yafi daɗi a duniya, kamar rayuwa da masoyi.
Ƙaizadu ya ci gaba da bayani, "Wannan jini da sarkin ƙabilar Azbin yake magana akai wanda idan ka same shi, wannan ruhi zai dawo jikinka sannan ya zamo inuwarka a yayin da kake gwabza yaƙi, shi ne jini mai nau'in J wanda sarauniya Arya ce kaɗai take da irinsa.
"Tabbas idan ka sake yin gaba-da-gaba da ma'abota Bankai, ba tare ƙarfin wannan ruhi ba, mutuwa zaka yi.
"Ku duba irin sharrin waɗannan takubba nasu. Wai hakan iya mai mataki na biyar da mai mataki na shida ne.
"Kowanne sarki daga cikin waɗannan sarakuna guda ɗari, yana da takobin Bankai mai mataki na arba'in.
"Idan har masu mataki ƙasa da goma, sun wahalar da kai haka; ya ya kake tunanin haɗuwar ka da masu mataki sama da na arba'in?"
Koda Samudul Ansari yaji wannan batu sai jikinsa yayi sanyi, ya tabbatar da cewa lallai yana buƙatar sarauniya Arya indai yana so ya samu nasarar ƙarar da shaiɗancin Gorgon.
Samudul Ansari ya sunkuyar da kansa ƙasa yana tunani. Abinda ya faɗo masa a rai shi ne, tunanin Zarifa.
Tun kafun su yi tafiya izuwa daular Gorgon mahaifinta ya ɗauke ta, ya tafi da ita izuwa wajen sarkin ruwa domin a bata magani.
Sa'adda suka dawo da maganin wannan cuta, ba su sami Zarifa a wannan daula ba.
Wannan abu yayi matuƙar ɗugunzumawa Samudul Ansari hankali, amma saboda ganin yadda jama'a suke warkewa daga wannan cuta sai zuciyarsa tayi sanyi.
Samudul Ansari ya ajiye magana akan cewa da zarar sun kammala 'mataki na biyu' zai shiga duniya nemanta.
Ko a mafarki bai taɓa tunanin cewa wannan mataki na biyu zai kasance aure tsakaninsa da Arya ba.
Tabbas abubuwa sun dagule, ta ya ya zai ce zai tafi neman Zarifa a wannan hali da ake ciki, wadda babbar daula kamar Gorgon take farautar sa?
Tabbas mafita guda ɗaya ce, kawai ya auri Arya idan yaso daga baya zai iya tafiya neman Zarifa.
Zuciyar Samudul Ansari ta daka masa.
Samudul Ansari bai taɓa ɗaukar rantsuwa bai cika shi ba, tabbas idan ya auri Arya kamar ya saɓawa wannan rantsuwa da yayi ne.
Ƙaizadu ya dubi Arya ya ce, "Shin kin amince za ki auri Kuyurul Samudul Ansari domin kuɓutar da wannan daula tamu daga sharrin ma'abota Bankai?"
Sarauniya Arya ta ɗago kai ta yiwa Samudul Ansari wani irin kallo wanda ba za'a kwatanta shi da komai ba, face kallon soyayya.
Ƴan daƙiƙu ta gagara cewa komai, ga dukkan alamu kunyar bayar da amsa take.
"...domin ceto al'umma ta, ƙasata da daula ta na amince!!!" inji sarauniya Arya.
Ƙaizadu yayi murmushi kamar da can ma, ya san wannan amsa zata bayar.
Ƙaizadu ya yi ajiyar zuciya ya dubi Samudul Ansari ya ce, "Kaifa, ka amince zaka auri sarauniya Arya domin kuɓutar da daular mu?"
Ƙaizadu ya yiwa Samudul Ansari wannan tambaya ce kawai, amma yana da tabbaci a cikin ransa ɗari bisa ɗari Samudul Ansari zai amince.
Ko babu komai Samudul Ansari zai fi kowa amfanuwa da wannan aure, domin daga wannan lokaci ya zamo mijin sarauniya.
Kuma zai farkar babban sirri wanda ke cikin jininsa wanda zai bashi kyautar wannan ruhi wanda yake kira a duk lokacin da faɗa baiyi masa daɗi ba.
Daƙiƙu masu tsaho Samudul Ansari yana ta tunani, kafun daga bisani ya numfasa ya ce, "Zan yi shawara zuwa da dare tukunna."
Ƙaizadu yana jin wannan batu gabansa ya faɗi, ya dubi Samudul Ansari ya ce, "Shawara? da su waye kenan?
"Shin ka san cewa, yanzu haka mayaƙan ƙabilar Gorgon kimanin mutum ɗari na tafe suna tunkaro wannan daula ta mu?
"Shin ka san cewa a cikin waɗannan mayaƙa akwai ma'abota Bankai guda hamsin ga kuma ƙarin waɗannan sarakuna guda biyu?
"Yana da kyau mu gama tattauna wannan magana anan, nan da cikar kwanaki biyu a ɗaura muku aure!"
Samudul Ansari ya dubi Ƙaizadu cikin nutsuwa ya ce, "Na san girman alƙawari. Akwai wadda muka yi alƙawari da ita akan cewa zan aureta, ina so na cika wannan alƙawari, kafun a yi aurena da Arya!!!"
Ƙaizadu yana jin wannan batu ya ɗan cika da tsananin mamaki, kafun daga bisani ya ce, "Wace ce?"
"ZARIFA!" inji Samudul Ansari kai tsaye.
"Hmm," Ƙaizadu ya yi murmushi, ya duba wani kasko dake gabansa ya ce, "Sarkin ƙabilar Azbin dama yayi tunanin haka, shiyasa ya tura babban hadimi ya nemo Zarifa da mahaifinta, kuma an dace wannan hadimi ya samo su sannan yana dawowa.
"Gobe-goben nan muke kyautata zaton zai ƙaraso!"
Samudul Ansari ya ce, "Idan suka ƙaraso goben, aka ɗaura aurena da Zarifa, na amince zan auri Arya!!!"
Tab! Wannan kalma ta ƙarshe da Samudul Ansari ya faɗa ta saka zuciyar sarauniya Arya yin fari. Wani gagarumin farin ciki ya lulluɓe ta.
Hawayen farin ciki suka zubo daga idanunta.
Samudul Ansari ya dubeta yayi ajiyar zuciya sannan ya dubi Ƙaizadu ya ce, "Mun gama tattauna wannan magana, abinda ya rage yanzu shi ne ka sanar da mu saƙo na uku, wanda wannan sarki ya ce, sharuɗɗa ne guda uku waɗanda ya zamo dole mu bi domin yaƙi da ƙabilar Gorgon!"
Ƙaizadu ya sake kurɓar wannan abun sha nasa sannan ya dubi Samudul Ansari ya ce, "Sharaɗi na farko da sarkin ƙabilar Azbin yake magana akai shi ne, DOLE KA ZAMO BABBAN SARKI NA WANNAN DAULA GABA ƊAYA.
"Sharaɗi na biyu, dole KA SAMU WANNAN RUHI A MATSAYIN MAI TAIMAKA MAKA A WANNAN YAƘI.
"Sharaɗi na ƙarshe, dole ne ka mallaki takobin da aka ajiye a cikin rijiyar Barzaƙ dake tsakiyar tekun birnin Rasha."
Cikin tsananin mamaki Samudul Ansari ya dubi Ƙaizadu ya ce, "Ta ya ya zan zamo sarki na wannan daula gaba ɗaya, alhalin ban kasance jinin sarauta ba?
"Ta ya ya kake tunanin sarakunan waɗannan daula gaba ɗaya zasu yarda su dawo ƙarƙashin iko na?"
Samudul Ansari ya girgiza kai sannan ya ci gaba, "Shin idan na auri sarauniya Arya zan samu wannan ruhi a matsayin mai taimaka min?
"Kayi sani cewa tekun birnin Rasha yafi kowanne teku a halin yanzu haɗari, ta ya ya wani mutum zai je can, yayi nutso izuwa ƙarƙashin tekun sannan ya shiga cikin rijiya sannan ya ɗauko takobi.
"Inda ace babu wani bala'i dake tunkaro mu, da da sauƙi amma a halin yanzu a kowanne lokaci daga yanzu mutanen Gorgon zasu iya dira a wannan daula tamu.
"Me kake tunanin zai faru idan ma'abota Bankai suka shigo wannan daula alhalin bana nan?"
Ƙaizadu yana gama jin waɗannan tambayoyi na Samudul Ansari yayi murmushi ya sake kurɓar wannan abun sha nasa sannan ya fara bayani da cewa.
"Kada ka damu da cewa yaushe wannan daula zata dawo ƙarƙashin mulkinka, kayi sani cewa bala'in da ma'abota Bankai zasu haifar a wannan daula zata sa dukkan sarakuna su yi maka mubaya'a saboda kaine kaɗai wanda zai cece su.
"Tabbas sai ka mulki wannan daula gaba ɗaya, wannan abu an riga an rubuta saura ya faru kawai.
"Amsar tambayarka ta biyu, duk ranar da aka ce ka sadu da sarauniya Arya wannan ruhi zai shiga cikin jikinka.
"Kayi sani cewa, dama can wannan ruhi naka ne, abinda yasa ya fita a jikinka shi ne yana buƙatar ka zamo babban mutum kafun ya dawo jikinka.
"Duk wanda ya auri ƴar ƙabilar Arya tabbas saiya zamo babban mutum a duniya.
"Ba kai zaka je birnin Rasha domin ɗauko wannan takobi ba, akwai wani jarumi wanda ya tafi ɗaukota saboda mallakin mahaifinsa ne.
"Sarkin ƙabilar Azbin ya sanar da ni cewa, ranar aurenka da sarauniya Arya wannan jarumi zai baka kyautar wannan takobi saboda akwai alherin da ka taɓa yi masa.
"Idan ka fuskanci bayanai na zaka iya tafiya, gobe da safe kai da sarauniya Arya ku fita bayan gari ta ɓangaren yamma tabbas zaku hadu da su Zarifa."
Ƙaizadu na zuwa nan a zancensa Samudul Ansari da sarauniya Arya suka cika da tsananin mamaki.
Samudul Ansari yayi shuru bai sake tambayarsa komai ba. Saboda waɗannan al'amura ne da suke buƙatar lokaci ba wai yawan bincike ba.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, Samudul Ansari da sarauniya Arya suka yi sallama da boka Ƙaizadu suka fice daga cikin wannan kogon tsafi nasa.
Gari na wayewa Samudul Ansari da sarauniya Arya suka fito bayan ƙauyen Salwaza ta ɓangaren yamma inda Ƙaizadu ya ce zasu haɗu da su Zarifa ta wajen.
Zuciyar Samudul Ansari cike fal da farin cikin sake saduwa da masoyiyarsa.
Ita kuwa sarauniya Arya ƙaguwa tayi taga wace ce Zarifa wadda ta samu kyakkyawan matsayi a zuciyar Samudul Ansari wadda ba domin waɗannan ƙa'idoji ba, da Samudul Ansari ba zai aureta ba.
Tsahon ɗan lokaci suna tsaye suna ta jira, kafun daga bisani su soma hango mutane guda biyu a can nesa.
Sannu-a-hankali mutanen suna ƙara matsowa suna ƙara girma, Samudul Ansari suka soma gane su.
Waɗannan mutane guda biyu, uba ne da kuma ƴarsa.
Uban na zaune akan doki, ita kuma yar tana riƙe da linzamin dokin suna tunkaro wannan ƙauye.
Tun daga nesa Samudul Ansari ya gane cewa, ba wata bace wannan budurwa illa masoyiyarsa Zarifa.
Ai kuwa suna kusa isowa Samudul Ansari ya taka da sawayensa yaje har inda suke, ya gaishe da wannan dattijo sannan ya rungume Zarifa a ƙirjinsa.
Sarauniya Arya ta tsaya a can baya kawai, ta ƙura musu idanu.
Tsahon ɗan lokaci suna ƙanƙame da juna, kafun Samudul Ansari ya janye jikinsa daga nata, ya tambayeta ya jiki?
A wannan lokaci Zarifa ta gama warkewa daga wannan cuta.
Koda Zarifa ta hango kyakkyawar budurwa wadda ba za tafi ta shekaru ba a bayan Samudul Ansari sai ta cika da tsananin mamaki.
"Wancar wadda kuke tare da ita, wace ce?" ta tambayi Samudul Ansari.
"Sarauniyar birnin Ilam, sarauniya Arya." inji Samudul Ansari.
Koda Zarifa da mahaifinta suka ji wannan batu na Samudul Ansari sai suka cika da tsananin mamaki.
Cikin gaggawa suka ƙarasa inda Arya ke tsaye suka kwashi gaisuwa.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, suka sake ɗungumawa suka koma cikin ƙauyen Salwaza.
Tun da Zarifa ta dawo, sarauniya Arya ta fuskanci cewa, Samudul Ansari ya fara baya-baya da ita.
Lamarin da yasa hankalin ta ya soma ɗugunzuma kenan, bisa dole ta nemi mafita.
Zama tasa aka shirya musu ita, Samudul Ansari, Zarifa da mahaifin Zarifa.
Sarauniya Arya ta dube su ta basu labarin abubuwan da suka faru. Tun daga fitowarta wannan rangadi, yadda suka gano wannan cuta, yadda suka je daular Gorgon tare da Samudul Ansari domin juya waɗannan duwatsu, haɗuwarsu da sarkin Azbin da bayanin mataki na biyu.
Koda su Zarifa suka gama jin wannan labari, sai suka cika da tsananin mamaki sannan suka sallamawa jarumtakar Samudul Ansari suka tabbatar da cewa lallai ya cika ya zamo wanda zai kare wannan daula tasu.
Wani azababben kishi ya rufe Zarifa jin cewa, Samudul Ansari dole ne yayi mata biyu wato dole ne ya auri Arya.
Abinda yasa Zarifa bata nuna wannan kishi nata a fili ba, abubuwa guda biyu ne.
Abu na farko shi ne tana tsananin tsoron sarauniya Arya, ko ba komai Arya sarauniyarta ce duk abinda tace a yi a wannan birni, dole ne a yi shi.
Abu na biyu shi ne yadda wannan aure da zasu yi ya shafi kimar wannan daula gaba ɗaya. Tabbas idan Samudul Ansari bai auri sarauniya Arya ba, akwai yiwuwar wannan daula gaba ɗaya ta karye.
Samudul Ansari ya dubi mahaifin Zarifa cikin girmamawa ya ce, "Baba! Ina so a saka mana rana, ni da yarka Zarifa..."
Mahaifin Zarifa ya yi murmushi ya ce, "Meye zai hana ku bar batun wannan aure, sai bayan wannan yaƙi?"
Samudul Ansari ya ce, "Saboda bani da tabbacin zan tsira da rayuwata a wannan yaƙi, sannan akwai alƙawari mai girman gaske tsakanina da ita.
"Tun da ance ya zamo dole na auri sarauniya Arya, meye zai hana na fara auran yarka kafun na auri sarauniyar..."
Bayan kai-komo mahaifin Zarifa ya saka rana wadda za'a ɗaura auren Samudul Ansari da Zarifa.
Sarauniya Arya tasa aka yi shela dukkan wannan daula gaba ɗaya.
Mutane suka cika da tsananin farin ciki saboda tsananin yadda suke ƙaunar Samudul Ansari.
Tun sa'adda Samudul Ansari yayi wannan tafiya ya samo musu maganin wannan annoba, suke tsananin ƙaunarsa a zuƙatansu.
*****
Yau *02/03/2023*
Babi na gaba zaizo *04/03/2023* da yaddar Allah.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 92: *Auren Ƴan-mata Biyu*
*
***HIKAYAR SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U
*
M
*
S
*
Tuni labari ya gama gauraye dukkan wannan daula cewa, mayaƙan Gorgon na tafe izuwa wannan daula domin su mamaye ta, hankalin jama'a yayi mummunan tashi.
Wasu suka fara tunanin hijira, wasu kuma suka fara addu'o'i wajajen ababen dogaronsu domin su kare su daga sharrin ma'abota Bankai.
Babbar matsalar da jama'a suka fuskanta shi ne, matsawa da sarakunansu suka yi wajen ganin an haɗa runduna-runduna na mayaƙa masu yawan gaske, waɗanda za'a yi amfani dasu wajen wannan yaƙi.
A ganin waɗannan sarakuna, guduwa daga biranensu a wannan lokaci ba shi ne mafita ba. Idan har ba su tsaya sun kare daular su ba, akwai yiwuwar nan gaba ma'abota Bankai su yi tunanin kaiwa wata daular hari.
Idan aka ci gaba a haka kuwa, duk inda suke a duniya wataran za'a ritsa da su.
Kafun kace me, a wannan daula an haɗa gagarumar runduna mai tsananin yawan gaske.
Ana shirye-shiryen tafiya wannan yaƙi aka ɗaura auren Samudul Ansari da Zarifa.
Da yake hankalin mutane a tashe yake, ba'a yi wani biki na a zo a gani ba.
Ƙaizadu ya yiwa Samudul Ansari gargaɗi akan cewa, kada ya kuskura ya fita wannan yaƙi ba tare da ya tara da sarauniya Arya ba.
Bisa dole Samudul Ansari ya sake yin aure a karo na biyu, kafun a fita wannan yaƙi.
Dukkanin waɗannan bukukuwa da aka yi, basu yi wani armashi ba, saboda hankalin jama'a yana kan wannan yaƙi da za'a gwabza.
Amma,

Please Login or Register in order to submit comment