Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

guda biyu ta zaro.
Wannan gari na farko yana da bambanci da dukkanin garuruwan da su Marganu suka taɓa zuwa. Abu na farko wannan gari babu sanƴi ko kaɗan a cikinsa sannan gidajen garin yawanci da laƙa aka gina su. Wannan wuri baiyi kama da ko'ina a duniya ba face nahiyar baƙaƙen fata.
Jaruman guda uku suna tsakiyar tafiya suka jiwo takun sawayen mutane da yawa sun durfafo su ta baya, cikin hanzari suka tsaya sannan suka waiga.
Nan take suka hango gungun waɗansu tarin sadaukai baƙaƙen fata gabza-gabza kamar mutanen farko. Dukkaninsu sun yiwa fuskokin su zane-zane da abubuwa kala-kala. Suna riƙe da makaman yaƙi iri dabam-dabam. Adadin mutanen zai kai dubu huɗu da ɗoriya.
Marganu, gimbiya Firziyya da Aydenlik suka haɗe bayansu a waje guda. Lokacin da waɗannan mutane suka gama kewaye su, suna ta wani irin ihu mai tsananin firgitarwa.
Tsoho Aydenlik ya wulwula waɗannan duwatsu guda huɗu dake kan tafin hannunsa, ya jefi waɗannan arnan-daji da guda ɗaya. Ɗan ƙaramin dutse ne amma yana barin tafin hannunsa ya warwatsu ya zamo duwatsu masu yawan gaske, daga bisani suka soma ƙara girma suna tsaho suna bayar da siffar mashi.
Kafun su iso inda waɗannan arnan-daji suke, tuni sun gama zamowa masuna dogaye masu tsananin tsaho da tsini. Yawansu kuma, zai kai yawan waɗannan arnan-daji don haka kowanne mashi saiya tunkari arne guda.
Wataƙila waɗannan arnan-daji basu kalli wannan hari na tsoho Aydenlik ba, domin kuwa babu wanda ma ya kalli waɗannan masun balle su yi ƙoƙarin kare kansu. Har waɗannan masu suka zo daidai wuyansu zasu tsire su, sannan kowanne arne ya harari mashin da ya tunkaro shi.
Abin mamaki kamar umarni suka baiwa waɗannan masun, nan take suka juya da baya suka haɗe a waje guda suka bayar da siffar ƙaton dutse, dutsen ya tafi da gudu zai doki kan Aydenlik.
Cikin hanzari ya jefi da dutsen da irin waɗannan duwatsu dake yawo akan hannunsa, nan take dukkansu duwatsun biyu, suka kumbura suka fashe. Sannan suka bayyana a tafin-hannun Aydenlik.
Aydenlik ya yi murmushi sannan ya dunƙule duwatsu guda biyu a waje ɗaya, ya sake jifan waɗannan arnan-daji da su.
A wannan karon kuma, waɗannan duwatsu waɗansu irin jibga-jibgan tsuntsaye suka dawo masu cako-cakon farata. Tsuntsayen suka tafi da gudu suka karci fuskokin arnan-dajin dake gaba, jini yayi feshi daga fuskokin su. Waɗanda ke tsaye a baya cikin fusata, suka harari tsuntsayen. Nan take waɗannan tsuntsaye ma, suka haɗe a waje guda, suka sake zamowa waɗannan duwatsu guda biyu, suka koma kan Aydenlik da gudu.
Kafun ya ankara tuni sun doki kansa, nan take yayi tsalle baya ya faɗo ƙasa a galabaice. Bakinsa da hancinsa da kuma kansa suka fashe jini ya fara zubowa. Marganu da jaruma Firziyya na ganin dukkanin abinda ke faruwa.
A fusace jaruma Firziyya ta rintse idanunta, ta kira ɗalasimin ƙabilar Gandiz. Nan take farar dusar ƙanƙara ta fara saƙƙowa wannan wuri, tana lulluɓe waɗannan arnan-daji. Duk wanda wannan dusar ƙanƙara ta taɓa sai kaga ya sandare a inda yake tsaye.
Jaruma Firziyya ta daka tsalle ta fille kan mutum biyar daga cikinsu, sannan ta saƙƙo a tsakiyar su da nufin tayi amfani da wannan dama ta karkashe su gaba ɗaya.
Bisa mamaki taga wannan dusar ƙanƙara tana tashi a jikinsu tamkar iska na hura ƙura. Ai kuwa take suka dawo hayyacinsu suka kewaye ta.
Jaruma Firziyya ta cika da tsananin mamakin yadda aka yi wannan dusar ƙanƙara ta sake waɗannan arnan daji da wuri. A ƙa'ida idan ɗan ƙabilar Gandiz ya ƙaddamar da wannan ɗalasimi, dusar ƙanƙarar tana iya ɗaukar sa'a bakwai kafun ta ɓace.
A baya mun ga lokacin da wannan dusar ƙanƙara ta ɓace daga jikin waɗannan arnan-daji dake shirin sare kan Marganu, amma hakan ya samo asali ne sakamakon bayyanar waɗannan aljanu da suke bautawa.
To, amma dole ne ta cika da tsananin mamaki idan aka ce wannan dusa ta tashi daga jikin waɗannan arnan-daji kamar iska ce ta hure ta. Amma, da tuno cewa ai babu abinda ta sani akan waɗannan arnan-daji sai hankalinta ya ɗan kwanta.
Komai ƙarfinka da ƙarfin shirinka, idan baka san sirrin abokin karawarka ba. Ba ka isa kayi nasara akansa farat ɗaya ba.
Jaruma Firziyya ta sake rintse idanunta ta kira wannan ɗalasimi, wannan dusar ƙanƙara ta sake zubowa kan waɗannan arnan-daji suka sake sandarewa a waje guda. Ta sake fille kan mutum goma daga cikin su.
Kafun ta sake wani yunƙuri na sake afka musu, tuni wannan dusar ƙanƙara ta sake ɓacewa daga cikin su.
Jaruma Firziyya tayi murmushin takaici domin ta tabbatar da cewa wannan ɗalasimi ba zai taɓa yin tasiri akan waɗannan arnan daji ba. Saboda haka ta zaro takubbanta guda biyu ta kwarara uban ihu ta afka musu da sara da suka.
Marganu da tsoho Aydenlik suka tsaya a gefe suka zuba mata idanu, suna so su kalli jarumtakar ta. Ba don komai Marganu ya ƙi shiga wannan faɗa nasu ba, sai domin yana so yaga iya ƙoƙarin da kowa zai iya a cikin wannan tafiya.
Lallai Marganu yayi lissafi mai kyau. Idan kana tare da mutum yana da kyau ka san ƙarfinsa da ƙarfin shirinsa. Musamman a irin wannan yanayi da yake ciki na son ɗaukar fansa.
Jaruma Firziyya ta wanzu a tsakiyar waɗannan arnan-daji ta ci gaba da saransu da sukarsu. Duk inda tasa gaba sai dai kaga kawunan bil'adama suna tashi sama kamar giginƴa. Marganu da Aydenlik suka cika da tsananin mamakin yadda take sarrafa waɗannan takubba nata.
Duk irin wannan ɓarna da gimbiya Firziyya take saiya zamo na banza domin tamkar ƙaro waɗannan arnan-daji ake saboda tsananin yawansu. Lamarin da ya fusata gimbiya Firziyya kenan, ta tsaya cak, ta daina saran waɗannan arnan daji, ta ɗaga waɗannan takubba nata guda biyu sama.
Sannu-a-hankali ta fara karanto ɗalasiman tsafi a cikin ranta, tana tofawa waɗannan takubba. Jim kaɗan wannan dusar ƙanƙara ta fara saƙƙowa amma bisa waɗannan takubba nata, kafun kace me sun fara zamowa farare tamkar wannan dusar ƙanƙara.
Marganu, Aydenlik da waɗannan arnan daji sai suka zuba mata idanu, suka yi kasake suna kallon ikon ALLAH.
Wannan dusar ƙanƙara na gama saƙƙowa, gimbiya Firziyya ta kaiwa waɗannan arnan-daji da takobin dake hannunta na dama. Abinda mamaki tazarar dake tsakanin su zata kai taku goma amma sai wani siririn layi mai tsananin sanyi ya fita daga tsinin takobin, ya tunkari waɗansu arnan daji hamsin dake tsaye a nesa.
Wannan siririn layi na iso su, ya ratsa su ya wuce. Suka ji wani irin sanƴi mai shegen bala'i ya buge su. Kafun daga bisani ƙasusuwan kafaɗunsu suka fara ɓaɓɓallewa suna karyewa.
Wannan abu ya ɗauki lokaci wajen bayani amma daga saran zuwa ɓallewar ƙasusuwan a cikin daƙiƙu goma komai ya faru. Sadaukai guda hamsin suka zube ƙasa suna ihun wahala.
Ƴan uwansu na ganin haka suka kwarara uban ihu, suka rugo da gudu kan gimbiya Firziyya zasu gididdiba ta da makaman yaƙin su.
Gimbiya Firziyya tayi murmushi ta kai sara gabas, yamma, kudu da arewa. Nan take irin waɗannan sirarun layuka guda huɗu suka fita daga jikin wannan takobi nata suka ragargaji ƙasusuwan waɗannan arnan-daji. Mutum ɗari biyu suka sake zubewa ƙasa. Wato wannan sara nata, mutum hamsin yake illatarwa.
Cikin fusata da baƙin naci irin na arna, waɗannan arnan-daji suka sake yunƙurowa zasu afkawa Firziyya. Murmushi kawai tayi ta sake aika musu da irin wannan sara guda bibbiyu a jere.
Wannan karon mutum ɗari huɗu ne suka zube ƙasa suna ta ihu. A wannan lokaci bai wuce mutum ɗari hudu bane kacal, suka rage daga cikin waɗannan arnan daji ba. Koda suka ga babu haza, kuma idan suka tsaya abinda ya faru da na farko shi zai faru dasu. Sai suka juya da baya suka ruga da gudu suka koma cikin gidajensu.
Marganu ya yi dariya ya dubi gimbiya Firziyya cikin jinjina ya ce, "Da kyau mace mai kamar maza. Tabbas kin cancanci kasancewa a cikin rundunata. Naso ace kun bani dama na gwada takobina a kansu. Amma bari muje gari na biyu, na ɗauke muku, ku barni da su kawai."
Gimbiya Firziyya ta yiwa Marganu murmushi mai taushi sannan ta mayar da takubbanta guda biyu cikin kufe, ta dawo bayansa ta tsaya.
Marganu ya ɗora hannunsa akan kafaɗarta cikin soyayya ya dubi cikin idanunta ya ce, "Lallai yau kin burge ni, kuma tun daga yanzu na fara alfahari da samunki a cikin tafiyata. Wannan 'ƙarfin iko' naki zai taimaka sosai da sosai wajen ganin bayan abokan gaba ta."
Gimbiya Firziyya tayi murmushi ta kamo hannun Marganu ta sumbace shi ta ce, "Hmm. Wannan kaɗan ne masoyina. Tabbas zan ci gaba da zage damtse wajen ganin ci gaba da samun yabo a wurinka."
Marganu ya yi murmushi kawai ya juya ya nufi cikin wannan gari na arnan-daji. Aydenlik da gimbiya Firziyya suka take masa baya.
Ana kallon-kallo tsakanin su Marganu da waɗannan arnan-daji suka wuce. Tun daga nesa suka soma hango gari na biyu na waɗannan arnan-daji.
Tsakanin wannan gari na farko da na biyun babu wani bambanci, yanayin gidajen nasu da komai duk ɗaya ne. Abinda ya ɗan bambanta shi ne gari na biyun yafi yawan gidaje da tarin al'uma.
Su Marganu suna ƙarasowa baƙin ƙofar wannan gari suka hango wani mutum guda ɗaya a tsaye, yana ganinsu ya ruga da gudu cikin wannan gari saboda yanayin jikinsu baiyi masa kama da komai ba face gawurtattun jarumai.
Marganu ya yi murmushi ya ce, su jira su a wannan wuri saboda tabbas yasan zasu dawo.
Ai kuwa tsahon rabin sa'a kacal aka ɗauka, wannan ƙofa ta gari na biyu ta buɗe. Waɗansu irin gabza-gabzan mutane suka fara fitowa daga cikinta. Saboda tsananin yawansu mutum bai isa ya ƙirga daga kallo ɗaya ba.
Dukkaninsu sun shafe fuskokinsu da baƙin shuni, suna ɗauke da mahaukatan makaman yaƙi kamar zasu ci babu.
Marganu ya dubi Aydenlik da gimbiya Firziyya ya ce, "Kamar yadda na baku umarni a ɗazu, waɗannan arnan dajin rabona ne. Ku koma gefe ku zuba mana idanu."
Aydenlik da Firziyya suka yi murmushi suka koma gefe suka tsaya. Shi kuwa Marganu saiya zaro wannan mariƙin takobi wanda ba shi da ƙarfe ya ɗaga shi sama.
Koda waɗannan arnan daji suka ga mutane biyu sun ware sun barsu da mutum ɗaya, kuma maimakon ma ya fiddo makamin yaƙi, mariƙin takobi ma kaɗai ya fiddo sai suka fara bushewa da dariyar mugunta.
Cikin hanzari suka kewaye Marganu, mutum arba'in daga cikinsu suka jeho masa masu da kibbau masu tsananin tsini.
Marganu ya tsaya cak a inda yake tsaye, baiyi yunƙurin komai na kaucewa waɗannan makaman yaƙi nasu ba. Hannunsa kawai ya ɗora akan hatimin hasken dake kan damtsensa ya rintse idanu.
Saura ƙiris waɗannan makamai su dira a jikinsa, kawai aka ga wani irin haske mai ban al'ajabi na tashi daga jikinsa tamkar rana a tsakiyar sararin samaniya.
Duk mashi ko kibiyar da tazo sai kaga ta gifta ta cikin jikinsa kamar ta cikin hayaƙi ta wuce. Haka waɗannan masu guda arba'in ɗinnan suka gama wucewa ta cikin jikin Marganu amma ko kwarzane basuyi masa ba.
Maimakon waɗannan arnan daji suyi mamaki, kawai sake fiddo waɗansu makaman yaƙin suka yi, suka sake jifansa. Abinda ya faru da farko dai shi ne ya sake faruwa.
Sai da akayi hakan har sau uku sannan waɗannan arnan-daji suka ɗan dakata. Mutum hamsin daga cikinsu suka zare zabga-zabgan takubba suka ruga da gudu kan Marganu zasu gididdiba shi.
Kaico! Ashe basu san dama haka Marganu yake buƙata ba. Yana ganin sun tunkaro shi, ya ƙaddamar wannan takobi tasa ta haske. Wani koren-haske mai kashe idanu ya bayyana a daidai ƙarfen wannan takobi.
Cikin kwanciyar hankali Marganu ya kaiwa iska sara da wannan takobi. Nan take waɗansu korayen ɗigo-ɗigon masu yawan gaske suka fita daga cikin wannan takobi suka nufi waɗannan arnan-daji.
Maimakon su tsorata ma, dariya suka soma yi saboda sun raina wannan hari nasa.
Marganu ya sake ɗaga wannan takobi ya sauya kalar hasken da take bayarwa daga kore, ya mayar dashi shuɗi. Ko kallon waɗannan sadaukai guda hamsin bai sake yi ba saboda yana da tabbaci akan wannan hari da ya kai musu.
Waɗannan korayen ɗigo-ɗigo suna iso waɗannan arnan-daji suka soma kumbura suna bayar da haske mai kashe idanu. Kafun kace me sun soma ɗaukewa waɗannan arnan-daji idanu, bisa dole suka soma kawar da idanunsu ga barin kallon ɗigo-ɗigon.
Sai dai wannan shi ne kuskuren da zasuyi na ƙarshe a rayuwar su. Kowanne ɗigo saiya ɗauki samfurin makamin dake hannun kowanne arne daga cikin arna hamsin ɗinnan. Sannan suka cake su.
A take mutane guda hamsin daga cikin arnan-dajin nan suka zube ƙasa matattu.
Sauran na ganin haka suka zaburowa Marganu gaba ɗayansu. Har a wannan lokaci Aydenlik da Firziyya suna can gefe guda a tsaye suna kallo.
Marganu ya ɗaga wannan takobi tasa sama, shuɗin haske ya tashi sama daga jikin wannan takobi. Yayi ta tafiya a sama, har ya tokare da gajimare.
Faruwar hakan keda wuya, waɗansu taurari masu yawan gaske suka soma bayyana a saman waɗannan arnan-daji. Abin mamaki kamar yadda waɗannan arnan daji baza su ƙirgu ba, haka su ma waɗannan taurari saboda yawan su.
Cikin tsananin mamaki waɗannan arnan-daji suka tsaitsaya suna kallon waɗannan taurari. Jim kaɗan waɗannan taurari suka soma ɗaukar kalar shuɗi suna bayar da haske kamar wannan takobi.
Marganu ya mayar da wannan takobi mazauninta ya ɗaureta, sannan ya juya ya nufi inda su Aydenlik suke tsaye, fuskarsa cike da murmushi da yaƙinin samun nasara.
Arnan daji na ganin haka suka fusata, suka sake zabura da gudu zasu afkawa Marganu.
Kash! A daidai lokacin waɗannan taurari suka soma sauƙowa ƙasa-ƙasa suna zuwa daidai ƙirajen waɗannan arnan-daji. Duk tauraron da yazo daidai ƙirjin arne, sai yayi haske mai ƙarfi, daga bisani yayi bindiga ya tarwatsa ruhinsa.
Kafun ka ce me, tuni waɗannan taurari sun tarwatsa ruhin waɗannan arnan-daji gaba ɗaya.
Aydenlik da gimbiya Firziyya suka dubi wannan takobi ta Marganu cikin tsananin mamaki.
"Wai dan ALLAH wannan takobi ba zata iya hallaka Shiyyu Djinn ba?" gimbiya Firziyya ta tambayi Marganu.
"Dukda cewa mahaifinki ne amma ba ki san ƙarfin aljaninsa ba," Aydenlik ya amsa mata. "Dutse yana tarwatsewa, amma na tabbata haske baya iya narka dutse."
Marganu yayi murmushi ya ce, "Kada kayi mamakin ta akan ganin wannan takobi tawa, wai nan ma da ƙananun ƙwari ake gwabzawa ne shiyasa."
Yana faɗin haka ya wuce ta cikin gawarwakin waɗannan arnan-daji, Aydenlik da Firziyya suka take masa baya.
Cikin kwanciyar hankali suka ratsa ta cikin wannan gari na biyu, suka wuce shi lafiya. Suna fitowa daga cikin sa suka hango gari na uku.
Wannan gari na uku saɓanin waɗannan garuruwa guda biyu, shi ya fito dabam. Yanayin gidajensa da tsarinsa baiyi kama da na waɗannan garuruwa guda biyu ba.
Yawanci gidajensa da farar ƙasa aka gina su, sannan anyi musu ado da ƙasar tsibirin Jiliy. Wata ƙasar gini ce mai sheƙi da ɗaukar idanu.
Kafun su iso wannan gari da tazarar taku arba'in, suka iso wani wuri wanda aka yiwa ado da irin wannan farar ƙasa ta gini. Sannan akwai waɗansu ƙarafu kamar mariƙan takubba a kakkafe a cikin wurin.
Idan mutum zai wuce ta cikin wannan wuri, dole sai ya bi a hankali idan ba haka ba kuwa, zai iya taka waɗannan ƙarafu. Dukda cewa su Marganu basu san mene ne a wannan wuri ba, amma jikinsu yana basu lallai waɗannan ƙarafu zasu iya kasancewa wata hanƴa ce ta shiga wani bala'i.
"Tunda ya zamo dole sai mun ratsa ta cikin wannan wuri, ina mai baku umarnin kada ku kuskura ku taka ɗaya daga cikin waɗannan ƙarafu, domin jikina sam bai yarda dasu ba." Marganu ya basu umarni.
Yana gama basu wannan umarni ya sa ƙafafunsa a cikin wannan wuri yana ratsawa ta tsakankanin waɗannan ƙarafu, ba tare da ya bari sawunsa ya kusanci ɗaya daga cikin su ba.
Aydenlik da Firziyya suka biyo bayansa a hankali, suna ratsawa ta cikin waɗannan ƙarafu, har suka kusa fita daga cikin su.
Kwatsam! Ba zato wani irin mugun santsi ya ɗebi Aydenlik ya tafi ƙasa zai faɗi cikin ƙarafun nan, cikin gaggawa ya kai hannayensa da nufin ya tallafi kansa da jikin Firziyya. Da yake da ƙarfi ya taho, nan take duk su biyu suka faɗi kan ƙarafu.
Wasu ƙofofi daga cikin ƙarƙashin ƙasa suka buɗe, gangar jikin Aydenlik da ta Firziyya suka faɗa cikin su. Kafun Marganu yayi wani yunƙuri tuni sun sake rufewa kamar da. Kai kace ba su ne suka buɗe yanzu ba.
Marganu ya daka tsalle ya fice daga cikin waɗannan ƙarafu. Sawayensa suka dira a bakin ƙofar shiga wannan gari.
Yana fitowa daga cikin ƙarafun ya juyo ya dubi cikin waɗannan ƙarafun yana nazarin tayaya zai iya kuɓutar da abokan tafiyarsa?
Tabbas idan yace zai koma cikin waɗannan ƙarafu, akwai yiwuwar shima su kama shi.
Marganu ya ƙaddamar da idanuwansa na haske, ya duba cikin waɗannan ramuka wanda su Aydenlik suka faɗa. Bisa mamaki sai ya gansu wayam, babu komai a cikin su.
Wannan abu yayi matuƙar baiwa Marganu mamaki, to, wai shin ina suka shiga ne?
***
Yau *03/12/2022*
Babi na gaba zaizo *05/12/2022* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 53: *Ƙabilar Dodanni: SEDUSA*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
UMAR SANGARU
*
Tsahon ɗan lokaci Marganu yana ta tunani, kafun daga bisani ya yanke shawarar abinda ya kamata yayi. Tun da basa cikin waɗannan ramuka, to, ko shakka babu suna cikin wannan gari na uku na arnan daji.
Saboda wannan dalili yasa Marganu, ya ƙarasa bakin ƙofar shiga wannan gari yasa takobinsa ya ɓalleta sannan ya kunna kai izuwa cikin wannan gari.
Tun daga shigowarsa cikin wannan gari ya fuskanci cewa lallai akwai gagarumin bikin dake gudana a cikin wannan gari, saboda dalilai guda biyu. Dalili na farko shi ne babu mutane sosai a cikin unguwanni, sannan yana jiwo tashin bugun ganguna daga can nesa.
Lallai duk yadda akayi waɗannan mutane suna can wajen bugun waɗannan ganguna. Zuciyarsa ta soma raya masa anƴa ba irin abinda mutanen sarauniya Rauziyya keyi, waɗannan arnan-daji ke shirin yi akan su Aydenlik ba?
Koda Marganu ya raya hakan a cikin ransa, sai ya gyara zaman makaman yaƙinsa ya ruga da gudu cikin wannan gari inda yake jiwo wannan bugun ganguna.
Tsahon rabin sa'a yana ta gudu amma bai iso wannan wuri ba, lamarin da ya bashi mamaki kenan. Ya sake zage damtse yayi ta gudu amma har tsahon wata rabin sa'ar sannan ya soma hango cinciridon mutane masu yawan gaske a tare a waje guda.
Mutanen da ya hango rataye a saman wani dogon gini su ne suka sa jikinsa ya fara tsuma da karkarwar fusata. Ba wasu bane illa Aydenlik da Firziyya. Anyi musu wani irin wawan ɗauri, kansu yana kallon ƙasa, sawayensu kuma suna kallon sama.
A ƙasansu an ajiye waɗansu manya-manyan kasko guda biyu, wani murjejen ƙato na tsaye a kusa da su riƙe da wani dogon mashi, yana ƙoƙarin huda kawunansu da wannan dogon mashi dake hannunsa.
Aydenlik da Firziyya sun gama galabaita iya galabaita. Bakunansu sun bushe saboda tsabar ƙishirwa.
Wannan narkeken ƙato ya ɗaga mashin dake hannunsa zai cakawa Aydenlik a tsakiyar kansa. Ba zato aka ga gilmawar wata takobi ta haske kamar walƙiya. Duk mutanen dake wannan wuri basu kalli mai wannan takobi ba, sannan gilmawar nata bai wuce daƙiƙu biyar ba ta ɓace.
Ba zato kuma, aka ga kan wannan sadauki dake riƙe mashin nan ya guntule ya faɗi ƙasa.
Nan take dukkanin waɗannan mutane dake wannan wuri suka fara kalle-kalle suna dube-dube amma basu ga kowa ba.
A fusace wasu sadaukai guda goma suka sake rugawa da gudu kan su Aydenlik zasu halaka su, amma wannan gilmawar takobi ta haske aka sake gani. Waɗannan sadaukai guda goma, gaba ɗaya kayukansu suka guntule su ma suka zube ƙasa.
Waɗannan arnan-daji suka tsaya zuru-zuru suna kalle-kalle cikin tsananin razana. Komai jarumtakarka da rashin tsoron ka, idan aka ce baka ganin abokin karawarka dole ne ka razana.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani! Aka ga gangar jikin wani saurayi ta fara bayyana a cikin wani haske mai ban al'ajabi. Kai kace rana ce ta saƙƙo wannan wuri saboda tsananin hasken.
Bisa dole waɗannan arnan daji suka soma kawar da idanunsu ga barin kallon jikin saurayin, saboda yadda yake ɗauke musu idanu. Ji suke tamkar rana suka ƙurawa idanu.
Jim kaɗan surar yarima Marganu ta gama bayyana a matsayin haske a tsakiyar waɗannan arnan-daji. Zaka iya cewa a wannan karon Marganu baiyi kama da kowa ba, face aljanin-haske wanda da kallonsa gwanda mutum ya ƙurawa rana idanu a lokacin da take tsakiyar sararin samaniya.
Cikin kwanciyar hankali Marganu ya ƙarasa inda aka ɗaure su Aydenlik da Firziyya yasa hannayensa biyu ya tsitstsinke igiyoyin da suka ɗaɗɗaure su.
Waɗannan arnan daji basu da ikon kallon abinda ke faruwa saboda basu isa su kalli Marganu a wannan hali da yake ciki ba.
Lallai a wannan rana an gama fusata Marganu, kuma ya shirya tsaf domin koya musu hankali.
Marganu na durƙushe yana yayyafawa gimbiya Firziyya ruwa a fuskarta, yaji wucewar wata zabgegiyar takobi ta cikin ƙirjinsa. Tabbas ba don a wannan lokaci yana cikin jikin haske ba, da tuni wannan takobi ta farke shi.
Amma, bisa mamaki wannan takobi kamar iska ta sara ta wuce babu abinda ta yiwa Marganu.
A fusace ya juya ya kalli wanda yayi masa wannan sara, inda yayi arba da shugaban waɗannan arnan-daji. Wani zabgegen ƙato ne mai faffaɗan ƙirji, yana riƙe da zabgegiyar takobi a hannunsa.
Wannan ƙaton mutumi baya iya kallon jikin Marganu sosai, yana yawan kawar da kansa ga barin kallon jikin Marganu. Ko shakka babu, tarar aradu yayi da ka domin kada yaransa su ce ya gaza.
Marganu ya murtuƙe fuska, yasa hannunsa guda ya zabgawa wannan mutumi mari. A take wani farin haske mai kama da farar-wuta ya kama fuskar wannan arne. Kafun ka ce me tuni ta ƙone tayi baƙi.
Baisan sa'adda ya fara kwarara uban ihu ba, ya juya da gudu izuwa inda mutanensa ke tsaitsaye amma duk ya kawo masa ɗauki shima hannunsa ne yake kamawa da wuta.
Suna ji, suna gani Marganu ya zame musu ƙadangaren bakin tulu. Babu yadda suka iya da shi.
Haka ya kammala zubawa Firziyya da Aydenlik ruwa suka farfaɗo, amma, suka gagara miƙewa koda zaune saboda ɗan-karen dukan da suka sha a hannun waɗannan arnan daji.
Lamarin da ya sake fusata Marganu kenan, saboda an taɓa masoyiyarsa, abar ƙaunarsa.
Ya samar da takubban haske guda uku ya aikawa waɗannan arnan-daji. Kamar tsuntsaye masu fuka-fuki haka waɗannan takubba suka je kan waɗannan arnan-daji suka fara yin kaca-kaca da namansu.
Kafun cikar daƙiƙu ashirin masu kyau, sun kashe wajen arna dubu da ɗoriya. Sauran na ganin haka suka firgice suka ruga da gudu izuwa cikin gari suka bar su Marganu a wannan wuri.
Marganu ya ɗauki Firziyya da Aydenlik ya nufi hanƴar da zata fitar dashi daga cikin wannan gari.
Tsahon sa'a guda cir ya ɗauka yana wannan tafiya kafun ya baiwa wannan gari na arnan-daji baya. Yana fitowa daga cikin garin ya shiga cikin wani ƙaramin daji ya kafa tanti, ya saka Aydenlik da Firziyya a ciki domin yayi jiƴƴarsu.
Marganu ya ƙarewa yanayin jikinsu kallo, yaga ya kumbura sosai sakamakon mugun dukan da suka sha. Saboda wannan dalili ya sa ya shiga cikin wannan daji, yana neman wata itaciya wacce zai dafa ya shashshafa musu ruwanta.
Kusan rabin sa'a yana ta kewaye-kewaye amma baiga wannan

Please Login or Register in order to submit comment