Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko tsoron komai ba, Marganu, Aydenlik da Firziyya suka bi bayan wannan sarki, suka shigo cikin wannan gari na huɗu.
Garin ƙaton gaske ne, sannan a cike yake da gidaje barkatai tamkar tantuna a sansanin mayaƙa. Mafi yawancin gidajen da farar ƙasa irin ta gari na uku aka gina su.
Su Marganu sun cika da tsananin mamaki bisa ganin dukkanin mutanen wannan gari wadanni ne, babu wanda ya kai ƙugun gimbiya Firziyya a tsaho.
Lallai duniya na da faɗi a wannan gari, ga shi dai mutanen gajeru ne amma suna rayuwarsu cikin farin ciki domin da dama daga cikinsu basu san da cewa akwai mutane irinsu Marganu a duniya ba.
Kai tsaye sarki Wadu ya ja su Marganu har fadar birninsa sannan yasa aka kaisu wani ƙerarren gida dake gefen fadarsa, akan cewa zai tura a kirawo waɗannan sarakuna guda huɗu domin gudanar da wannan gasa.
Su Marganu suka tare a cikin wannan gida, cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. Abinda suka sani kawai shi ne babu wanda ya isa ya iya cutar da su a cikin wannan gida matuƙar suna cikin hayyacin su.
Tsahon mako guda sarki Wadu bai neme su ba, sannan sau ɗaya kawai ya taɓa zuwa wajen su. Da yazo ɗin ne ya shaida musu cewa, waɗannan sarakuna guda huɗu na nan tafe kuma zasu iso a cikin mako guda domin gudanar da waɗannan gasanni.
Wannan shi ne dalilin da yasa su Marganu suka saki ransu a cikin wannan gida, suka ci gaba da rayuwa har tsahon wannan mako guda.
A tsahon zaman da suka yi a cikin wannan gida, basu taɓa cin abincin mutanen sarki Wadu ba. Duk abinda aka kawo musu basa ci sannan basa sha, face abinda suka taho da shi kawai.
A duk lokacin da suka gaji da zama a cikin wannan gida sai su tafi bayan wannan gari suyi ta kallon ni'imomin Allah.
A ranar da mako guda ta cika ɗin ne, sarki Wadu ya turo musu wani hadimi wanda zai jagorance su izuwa fadar birninsa sannan hadimin ya shaida musu cewa waɗannan sarakuna guda huɗu ne suka iso.
Koda su Marganu suka ji haka sai suka yi farin ciki, suka ce hadimin yaje ya jira su a ƙofar gida.
Ba tare da ɓata lokacin komai ba, su Marganu suka gama kimtsawa sannan suka fito ƙofar wannan gida inda suka iske wannan hadimi tsaye yana jiran su.
Hadimin ya nufi cikin gidan sarautar garin wadda bata da nisa da wannan gida da aka sauƙe su. Marganu, Aydenlik da Firziyya suka take masa baya.
Ba su yi wani dogon tafiya ba suka shigo cikin wannan fada, wadda aka tsara gininta sosai. Daga can nesa suka hango sarakuna guda huɗu a zazzaune kan kujeru sunyi ado da alkyabba.
Tun daga nesa aka fara kallo-kallon tsakanin su da su Marganu. Har suka ƙaraso inda waɗannan sarakuna ke zazzaune sannan suka tsaya.
" Barkan ku da zuwa," inji sarki Wadu dake zaune a tsakiya. "Waɗannan su ne abokanai na, sarakunan waɗannan garuruwa guda uku dake gaban wannan gari nawa. Ɗazu suka ƙaraso, sannan na riga na sanar dasu cewa, kun amince a shirya muku waɗannan gasanni domin samun sulhu a tsakanin mu.
"Bisa wannan dalili yasa sarakunan suka nemi dama na basu daga yau zuwa gobe domin su yi kyakkyawan nazari akan gasar da ta dace kowanne daga cikin su ya shirya. Saboda haka nake so na sanar da ku cewa kuje ku gama kimtsawa gobe, zamu fara gudanar da gasanni."
Marganu yayi murmushi ƙarewa waɗannan sarakuna guda uku kallo, sannan ya kama hannun Firziyya suka juya suka fita daga wannan fada, Aydenlik ya take musu baya.
Washe gari da sassafe fadar wannan gari ta cika ta batse da tarin al'umma, har da mutanen sauran waɗannan garuruwa guda uku sai da suka zo domin ganin jaruman da suka iya ratsowa ta cikin garuruwa uku na farko da kuma muggan dazuzzuka masu mugun haɗari.
Wani tafkeken fili aka gina a tsakiyar wannan fada, wanda koda ƙatti ashirin zasu yi kokawa a cikinsa baza su takura ba. An kewaye filin da gajeren gini wanda dole sai mutum ya daka tsalle zai iya tsallake shi.
Gaba ɗaya filin a kewaye yake da tarin ƙananun kujeru waɗanda mutanen waɗannan garuruwa suka gama cike su, ko'ina mutum ya duba babu abinda zai gani face mutane ratata.
A gefe guda kuma, an gina wani tudu mai ɗan tsaho, a saman tudun an gina karagun mulki guda huɗu waɗanda sarakunan nan suka zauna akansu. Taro ya gama cika taro. Kowa da kowa ya hallara amma banda Marganu, Aydenlik da Firziyya.
Bayan ɗan lokaci sarki Wadu ya tura wani hadimi yaje ya taho dasu. Jim kaɗan da dawowar wannan hadimi aka ga su Marganu sun bayyana a tsakiyar wannan tafkeken fili.
Marganu bai sanya riga a jikinsa ba, sai wata ƙaramar falmara da ta zagayo daga kafaɗarsa zuwa ƙugunsa. Yana rataye da takobin mahaifinsa a kafaɗarsa sannan zabgegiyar takobinsa na ɗaure a gadon bayansa.
Wannan shiga da yayi ta fiddo murɗaɗɗiyar surar jikinsa ta sadaukai wacce ta yiwa mutanen dake wannan wuri kwarjini ainun, har da su kansu waɗannan sarakuna kuwa.
Gimbiya Firziyya kuma doguwar riga ta sanya jajawur wacce aka tsagata daga tsakiya. Kamar kullum tana rataye da zabga-zabgan takubba guda biyu a gadon bayanta.
Tsoho Aydenlik na nan kamar yadda aka san shi, babu abinda ya canja daga jikinsa. Illa iyaka gemunsa kawai ya yiwa ƙunshi ja.
Ganin su Marganu a cikin wannan gagarumar shiga yasa waɗannan yan kallo ruɗewa da ihu, saboda jaruman sun yi matuƙar burge su.
Sarki Wadu ya ɗaga hannu sama, nan take wajen gaba ɗaya ya sake yin tsitt! Sarkin ya fara jawabi da cewa.
"Mutanen garin Wadanni, garin Wrisa, garin Maban da garin Kulsi barkan ku da wannan rana. A yau kamar yadda kuke gani muna da baƙin mutane, jarumai, matafiya waɗanda hanya ta ratso da su izuwa wannan yanki namu.
"Kamar yadda alƙaluma suka shaida mana waɗannan mutane sun fafata mugun artabu da mutanen garuruwa guda uku na farko, sannan sun kashe na kashewa sun bar na bari.
"Lallai sun yi bajinta sosai ya kamata a jinjina musu. Daga cikin adalcinmu da son zaman lafiyarmu da kuma rashin son ganin jini na zuba a banza, yasa na tara waɗannan abokai nawa muka gudanar da zama ta musamman akan yadda zamu ɓullowa waɗannan baƙin jarumai.
"Godiya ga abun bauta. Mun yanke shawara mai kyau, kuma naje da kaina na tari waɗannan jarumai nayi musu tayin wannan shawara kuma an dace sun amince.
"Lallai waɗannan jarumai sun zaɓi hanya mai kyau wadda ake bi wajen raba gardama da zubar da jini. Kowanne ɗaya daga cikin mu zai miƙe tsaye ya faɗi irin gasar da ya shiryawa waɗannan jarumai.
"Daga yau za'a fara gudanar da wannan gasa, har zuwa tsahon kwanaki huɗu. Watau kowacce rana za'a yi gasa guda ɗaya kenan.
"Idan har an fahimci zancena ina so sarkin birnin Wrisa ya tashi ya gabatar mana da irin gasar da ya shirya, sannan waɗannan jarumai su zaɓi mutum ɗaya daga cikinsu wanda zai jarraba ta. Nagode."
Sarki Wadu na gama wannan jawabi nasa, ya koma kan karagar mulkinsa ya zauna. Wani dogon sarki ƙato mai sanye da walkin fatar damisa ya miƙe ya fuskanci jama'a.
"Suna na sarki Amu mai mulkin garin Wrisa. A yankin garin mu bamu san komai ba, im banda farauta. Wannan yasa gasar da na shiryawa waɗannan jarumai ta shafi farauta ƙwarai da gaske.
"Yau da asuba na tura an kawo mini manya-manyan damisa guda biyu, yanzu haka suna tsare a cikin keji. Tsarin wannan gasa shi ne, ina so ɗaya daga cikin waɗannan jarumai ya yaƙi waɗannan damisoshi nawa guda biyu sannan ya fille min kansu ya gabatar dasu a gare ni. Nagode."
Mutane suna jin kalaman sarki Amu suka ruɗe da shewa. Lallai wannan gasa da yazo da ita zatayi daɗin kallo.
Sarki Wadu ya sake ɗaga hannu sama aka yi tsitt sannan ya dubi su Aydenlik ya ce, "Yanzu sai ku yanke shawara a tsakanin ku akan wanda zai jarraba wannan gasa ta sarki Amu?"
Marganu ya gyaɗa kai ya dubi su Firziyya ya ce, "Ya kuka ce?"
Caraf gimbiya Firziyya ta tari numfashinsa ta ce, "Zan jarraba wannan gasa kuma zan yi nasara."
Cikin tsananin mamaki Marganu ya dube ta ya ce, "Gimbiya gwabza yaƙi da dabbobin daji ba kamar gwabza yaƙi da mutane bane, sannan a irin wannan lokaci idan ba kiyi nasara ba, sulhun da muka ɗaura da waɗannan mutane zai iya warwarewa mu yaƙe su!"
Gimbiya Firziyya tayi murmushi cikin kafiya ta ce, "Ka yarda dani masoyina, zan yi nasara. Ka yadda dani!"
Aydenlik ya dubi Marganu ya ce, "Tun da ta ce zata iya mu barta kawai, idan bata yi nasara ba sai mu yaƙi waɗannan arnan daji."
"Idan ba kiyi nasara ba," inji Marganu. "Sannan wannan ya zamo silar da waɗannan arnan daji zasu faɗa min baƙar magana, ba zan yafe miki ba."
Gimbiya Firziyya tana jin gabanta yayi wani mugun faɗuwa. Me Marganu yake nufi da ba zai yafe mata ba.
Hawaye mai zafi ya zubo daga idanunta guda ta dubi Marganu ta ce, "Tun kafun mu zo wannan gari sai da kasa muka ɗaukar maka alƙawari akan kowanne ɗaya daga cikin mu zai karɓi gasa guda ɗaya. Don na karɓi wannan gasa sai ka kafa min sharaɗi wanda idan ban cika shi ba, nasan mutuwa zan yi?"
Marganu na jin wannan batu na ta yaji kunya ta ɗan rufe shi, tabbas bai kyauta mata ba. Amma ko ba komai, shi shugabanta ne kuma masoyinta, duk abinda ya ce mata dole shi zatayi.
"Kiyi haƙuri da abinda na faɗa," inji Marganu cikin tattausan harshe. "Ki je ki yaƙi waɗannan damisoshi da dukkanin ƙarfin ki, lallai zan yi alfahari dake idan kika sami nasara."
Gimbiya Firziyya tana jin wannan batu na Marganu taji wani irin ƙwarin gwiwa ya shigeta, ta rungumi Marganu sannan ta zare waɗannan takubba nata guda biyu ta shiga tsakiyar wannan fili.
Marganu da Aydenlik suka fice daga cikin wannan fili, suka ƙyale gimbiya Firziyya ita ɗaya jal. Suka koma kan waɗansu kujeru guda biyu acan gefe guda suka zazzauna.
Koda jama'a suka ga an ƙyale kyakkyawar gimbiya guda ɗaya a cikin wannan fili, sai suka ruɗe da shewa suka zuba idanu sosai domin ganin bajintar ta.
Sarki Amu yayi murmushi ya kirawo wani hadimi ya bashi umarni. Hadimin ya ruga jim kaɗan ya dawo cikin wannan fili ɗauke da wani ƙaton amalanke wanda aka ɗaurawa ƙaton keji mai ɗauke da gabza-gabzan damisoshi guda biyu.
Hadimin na zuwa tsakiyar wannan tafkeken fili ya tsaya cak, ya kalli Firziyya yayi murmushin mugunta sannan ya zagayo ta bayan wannan keji, ya ja wata murtuƙeƙiyar igiya.
Waɗansu ƙofofi guda biyu dake gaban wannan keji, suka buɗe. Waɗansu irin damisoshi guda biyu suka fito daga cikin kejin. Wannan hadimi yayi sauri ya ja wannan amalanke nasa suka fice daga cikin filin, suka ƙyale gimbiya Firziyya da waɗannan damisoshi guda biyu.
Irin waɗannan damisoshi Firziyya bata taɓa ganin kalar su ba, saboda babu irin su a wancan nahiya da take rayuwa.
Farare ne sol, sannan jikinsu yana da layi baƙi-baƙi. Idanuwansu kuma, koraye ne masu ban al'ajabi da ɗaukar hankali. Haƙoran dake cikin bakunansu fiƙaƙƙu ne, waɗanda zasu iya kama duk abinda suka ciza.
Jikin su a gine yake da tarin tsokoki, kai da gani kasan zasu yi ƙarfin na gaban kwatance.
Koda waɗannan damisoshi suka yi arba da gimbiya Firziyya, sai suka dako tsalle inda take tsaye, suka sakata a tsakiya sannan suka fara kewaye ta.
Gimbiya Firziyya ta zaro takubbanta guda biyu ta riƙe su da kyau sannan ta ɗinga nazarin dukkanin motsin waɗannan damisoshi.
****
Yau *02/01/2023*
Babi na gaba zaizo *05/01/2023* da yaddar ALLAH.

su.
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 67: *Muguwar Gasa*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga MAL. ZAHRA.
*
UMAR SANGARU
*
Marganu ya dubi Aydenlik ya ce, "Kai wadancan dabbobin akwai ɗaukar hankali, tunda nake ban taɓa ganin irin su ba."
Aydenlik ya ce, "A yankin da yafi kowanne zafi suke rayuwa babu irinsu a yankunan da muke rayuwa..."
Kafun Aydenlik ya rufe bakinsa waɗannan damisoshi guda biyu suka dako tsalle sama, suka kawowa gimbiya Firziyya bangaza da nufin su haɗata a tsakiya su turmushe.
Cikin zafin nama ta karkata jikinta, damisa ta farko ta wuce, sannan ta sa takobinta ta yanki gadon bayan guda ɗayar kuwa da kaifin takobinta guda.
Nan take wani lafcecen yanka ya bayyana a gadon wannan damisa, jini yayi tsartuwa. Ta rafka wani uban ruri wanda ya cika wannan fili gaba ɗaya da amsa kuwwa.
Jaruma Firziyya ta tsaya a bayan waɗannan damisoshi guda biyu, takobinta guda ɗaya tana ɗigar da jini. Mutane suka ruɗe da shewa suna mata jinjina bisa wannan gagarumar jarumtaka da tayi.
Jaruma Firziyya ta kalli inda su Marganu suke tayi musu murmushi, nan take su ma suka mayar mata da martani. Take ta ji wani sabon kuzari ya sake shiganta. Murmushin Marganu kaɗai yana nufin komai a wajen Firziyya.
Waɗannan damisoshi guda biyu suka ja da baya, suka dako wani wawan tsalle sama da nufin su bangajeta ta faɗi ƙasa. Cikin zafin nama irin na farko ta sake gocewa, guda ɗaya ta wuce, ɗayar kuwa ta doki gefen kafaɗar Firziyya.
Saboda ƙarfin wannan damisa sai da gimbiya Firziyya taji tamkar allon kafaɗarta ya goce. Ba ta san sa'adda tayi ƙara ba.
Waɗannan sarakuna dake zaune acan nesa suka dubi junansu suka yi murmushi. Gimbiya Firziyya na ganin haka ranta ya ɓaci, ta ruga da gudu ta fuskanci wannan damisa ta farko wadda ta jiwa rauni a gadon baya.
Wannan damisa na ganin haka, ta rugo da gudu kan Firziyya itama. Sawayenta na kartar ƙasa suna haifar da gagarumar ƙura, tana wani irin ruri mai sanya tsoro da firgici. Saura taku bakwai su haɗu wannan damisa ta daka tsalle sama ta ware hannayenta guda biyu, sannan ta wangame ƙaton bakinta da nufin ta yiwa Firziyya ƙwaf ɗaya.
Jaruma Firziyya ta tale sawayenta guda biyu tayi ƙasa, wannan damisa ta wuce ta samanta.
Sai dai wannan damisa na dira aka ga kayan cikinta na zazzagowa ƙasa, jini yana ta zuba tamkar ana ambaliya. Nan take wannan damisa ta zube ƙasa a wannan wuri matacciya.
Ashe lokacin da wannan damisa tazo giftawa ta saman kan Firziyya tasa takobinta ta farke cikin damisar.
Mutane suka ruɗe da shewa bisa ganin wannan gagarumar bajinta da jaruma Firziyya tayi. Marganu ya yi murmushin jinjina ya dube ta, nan take suka haɗa idanu.
Wannan damisa na ganin an kashe yar uwarta tayi wani irin ruri wanda yasa dukkanin jama'ar dake wannan wuri sake yin shuru. A fusace ta rugo da gudu kan Firziyya kamar yadda ta farko tayi.
Jaruma Firziyya na ganin haka, ta tsaya cak a inda take tsaye sannan ta mayar da takubbanta cikin kufe. Mutane na ganin haka suka fara ihu mai nuna cewa, lallai wannan jaruma tayi ganganci.
Aydenlik ya dubi Marganu ya ce, "Shin jaruma Firziyya ta shiryawa mutuwa ne? Me take taƙama da shi wanda zai sa ta mayar da takubbanta cikin kufe, ta tsaya a gaban wannan ƙatuwar damisa? Shin ta kasance basadaukiya ce?"
Marganu ya ce, "Nima ban san komai ba, amma yau zamu ganewa idon mu, idan har ta kasance basadaukiya. Amma maganar gaskiya bana so na rasa Firziyya daga yanzu, sannan idan ta sami nasara zanyi mata magana akan wannan ganganci da tayi."
"Hmm" Aydenlik ya yi murmushi. "Anya za tayi nasara kuwa?"
A daidai wannan lokaci da su Aydenlik ke ta wannan tattaunawa akan waɗannan karagu guda huɗu kuma, bushewa kawai ake tayi da dariyar mugunta. Ba wasu bane ke ƙyatata wannan dariya face waɗannan sarakuna guda huɗu.
"Wai dama har yanzu da akwai irin waɗannan jarumai masu wannan ganganci a duniya?"
"Na tambaye ku mana, idan suka faɗi wannan gasa sulhun da muka ƙulla da su ya warware?"
"Amma ai tayi ƙoƙari da ta iya kashe guda ɗaya, wataƙila hakan ne yasa girman kai ya shigeta har take ganin zata iya nasara akan wadannan damisa koda kuwa bata tare da takubba?"
"Hmm, ku barta kawai lallai a yau zamuga yadda za'a yi kaca-kaca da namanta bata san ƙarfin waɗannan damisoshi bane."
"Bari dai mu gani." Haka dai waɗannan sarakuna suka ci gaba da tattaunawa akan yadda haɗuwar Firziyya da wannan ƙatuwar damisa zai kasance.
Saura ƙiris wannan damisa ta isa inda Firziyya ke tsaye ta daka wawan tsalle sama kamar yadda damisa ta farko tayi. Ƙiris ya hana wangamemen bakinta ya haɗiye kan Firziyya amma sai Firziyya ta goce cikin zafin nama, ta shaƙo wuyan wannan damisa suka fara kokawa.
Gimbiya Firziyya ta shaƙe wuyan wannan damisa da kyau, ita kuma wannan damisa tayi ta kartar jikin Firziyya da faratan hannunta domin ta samu ta ƙwaci kanta. Amma ina, ta riga ta shiga hannu.
Kafun kace me, tuni ta fara yiwa gimbiya Firziyya ƙananun rauninka a jikinta waɗanda suke zubar da jini da kuma zogi. Dukda cewa a shaƙe take kuwa.
Nan fa wannan faɗa nasu ya fara daɗin kallo, domin duk girman wannan damisa sai ga ta a hannun Firziyya tana ta ƙoƙarin ƙwace kanta amma ta kasa ƙwatar kan nata.
Basadaukiya Firziyya. Ƴar sadaukin sarki Kuffuru. Gimbiya mai ɗalasimin dusar ƙanƙara, Gandiz.
Waɗannan sarakuna guda huɗu suka yi ƙuri da idanu, suna kallon tsantsar jarumtaka irin ta ƴaƴan sadaukai. Haka a ɓangaren su Marganu da Aydenlik ma, kallon Firziyya suke cikin tsananin mamaki. Lallai a wannan rana ta tabbatar da cewa ita ƴar sarki Kuffuru ce.
Koda gimbiya Firziyya taga wannan damisa tana faman ɓata mata lokaci, kuma raunikan da take ji mata a jikinta sun fara yawa sai ranta ya ɓaci. Ta saki wuyan wannan damisa sannan tayi wuf ta kamo bakinta.
Hannunta guda ya kama haɓar ƙasa, guda kuma ya kama haɓar sama. Nan take ta fara ƙoƙarin ɓare bakin wannan damisa da ƙarfin tsiya.
Nan fa suka sake ruguntsumewa da sabon kokawa su faɗi nan, su tashi can. Firziyya na ƙoƙarin ɓara bakin damisar, ita kuma damisar na ƙoƙarin ƙwace kanta.
Duk mutanen da ke wannan wuri sai da suka cika da tsananin mamakin wannan jarumtaka da Firziyya keyi, da dama daga cikinsu sai da suka fara yi mata kirari da jinjina saboda tayi matuƙar burge su.
Da ƙyar da siɗin goshi, gimbiya Firziyya ta samu damar murɗewa wannan ƙatuwar damisa wuya. Ƙarar kakkaryewar ƙasusuwanta ya cika wannan wuri.
Kafun gawar wannan damisa ta gama zuwa ƙasa, gimbiya Firziyya ta zaro takubbanta cikin zafin nama ta fille kan damisa sannan ta riƙe shi da hannu guda.
Ta yi dungure izuwa inda gawar guda ɗayan ma take, ta fille kanta sannan ta mayar da takubbanta cikin kufe, ta ɗauki dungulmayen kawunan waɗannan damisoshi ta gabatar dasu a gaban sarki Amu.
Mutane suka yi tayi mata jinjina bisa wannan gagarumar jarumtaka da tayi. Marganu da Aydenlik suka yi ta yi mata tafi, wanda yasa gagarumin farin ciki ya lulluɓe ta.
Sarki Amu ya taso da kansa ya karɓi waɗannan dungulmayen kayuka sannan ya shaidawa cewa jaruma Firziyya tayi nasara a wannan gasa ta farko.
Sarki Wadu ya tashi yayi jawabin bankwana sannan ya sallami dukkanin jama'a akan cewa sai gobe za'a sake haɗuwa domin gudanar da gasa ta biyu.
Kowa da kowa ya watse, sadauki Marganu da su Firziyya suka sake komawa cikin wannan gida nasu.
Firziyya ta haɗa musu abinci mai kyau, suka zauna a tsakiyar wani ƙaton ɗaki suka fara ci.
"Wa ya koya miki faɗa da damisa?" Marganu ya tambaye ta.
Firziyya tayi murmushi ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce, "Fita farauta yana daga cikin abubuwan da nafi muradi a birnin mu. Na sha gwabza yaƙi da muggan dabbobin daji sannan na kashe su, na saro kansu na tsire a cikin jeji ba tare da kowa ya sani ba."
"Hmm," Marganu yayi murmushi. "Tabbas yau waɗannan sarakuna sun jijjiga, wannan jarumtakar ace ta matata ce, ya ya suke tsammanin tawa zata kasance?"
Gimbiya Firziyya tana jin wannan batu daga bakin Marganu wani farin ciki ya lulluɓeta, taji tamkar an tsamota daga cikin wuta an saka ta acikin ƙanƙara.
Lallai a wannan lokaci ta gama fuskantar cewa Marganu ya kamu da tsananin ƙaunarta, wannan abu kaɗai ya isa yasa farin ciki a zuciyar Firziyya har zuwa ƙarshen rayuwarta.
"Waye zai yi gasar da zasu saka gobe?" Marganu ya tambaye su.
Aydenlik ya risina ya ce, "Ya shugabana, mu ji yanayin yadda wannan gasa zata kasance mana. Idan ta jarumtaka ce kai zaka yi ta, idan kuwa ta shafi tsafi da ƙwaƙwalwa ce sai ka barni nayi."
Marganu ya ce, "Lallai haka za'a yi."
Haka dai suka ci gaba cin abinci suna ta hira har dare ya soma sannan kowa yaje ya kwanta. Marganu yaga gimbiya Firziyya tana son shigowa cikin ɗakin da yake saida ya daka mata tsawa sannan ta bar wurin.
Gimbiya Firziyya ta shiga cikin ɗakinta ta zauna a bakin gado tana ta tunanin irin wannan hali na Marganu. A ce kyakkyawar budurwa kamarta, mai kyakkyawan jiki da diri mai dimauta duk wani namijin da ya kalleta, ace ko kaɗan Marganu baya sha'awarta?
Idan a haɗuwarsu ta farko tsoron sarki Kuffuru ya hana shi biya mata buƙatarta, ai yanzu yana da kyakkyawar dama wacce zai iya yi mata dukkan abinda yake so. Tun da a halin yanzu idan aka kirata da sunan matarsa, ba'ai laifi ba.
Gimbiya Firziyya ta fara kwakwanton anya Marganu yana da cikakkiyar lafiya kuwa?
Abinda bata sani ba shi ne, Marganu namijin gaske ne. Abinda yayi imani da shi shine maza basa tarawa da mata a filin daga. Sannan tun daga tasowarsa har zuwa girmansa bai taɓa saduwa da mace ba.
Mahaifiyarsa ta sha ja masa kunne akan kada ya kuskura yayi jima'i har sai yayi aure. Wannan na daga cikin dalilan da suka sa kwata-kwata Marganu ya fita a sabgar mata, babu abinda yafi mayar da hankali akansa face karɓar horo da juriya irinta mazajen ƙwarai.
Washe gari bayan sun farka daga barci, suka yi kalaci kamar yadda suka saba, sannan suka sake komawa fadar wannan birni inda aka gwabza gasa jiya.
Marganu da Aydenlik basu sauya kayan da suka saka jiya ba, amma ita kuma Firziyya ado ta caɓa na gaban kwatance. Idan ka ganta a cikin wannan sutura ba zaka yi tsammanin ita ce ta hallaka muggan dabbobin daji guda biyu ba, saboda tsananin kyawunta.
Mutanen waɗannan garuruwa da suka kalli Firziyya a cikin wannan shiga sai da ta ɗauke hankalin fiye da rabi daga cikin su. Basu da buƙatar tambaya ita kam, ba zata yi gasa a wannan rana ba.
Gimbiya Firziyya ta zamo tamkar kyakkyawan fure a tsakiyar ciyawi, hatta waɗannan sarakuna guda huɗu sai da suka ji sanyi a ransu sakamakon ganin kyawunta kuma sai da suka ji inama a ce su ne suka mallaketa.
Sarki Wadu ya miƙe tsaye ya yiwa jama'a barka da zuwa sannan ya ci gaba da cewa, "Kamar yadda muka alƙawarta jiya, yau zamu ci gaba da wannan gasa. A yau sarki Kayden ne zai gabatar mana da tasa gasar. Muna jira..."
Sarki Wadu na zuwa nan a zancensa ya koma kan kujerarsa ya zauna, wani sarki mai yawan dogon gashi ruwan ɗorawa ya miƙe tsaye ya fuskanci jama'a ya ce.
"Barka da wannan lokaci, dukkanin jama'ar da ke wannan wuri, ni sarki Kayden ina yi muku barka da wannan lokaci. Kamar yadda ni

Please Login or Register in order to submit comment