Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwai ƙwarangol da yawa na mutane a zuzzube, wasu sun gama ruɓurɓushewa sun zamo ƙasa, wasu kuma da saura.
"Wannan shi ne BIRNIN SHAHA wanda Samudul Ansari ya gina da hannunsa domin mutanensa na baya su amfana..." inji Barban.
Yana gama faɗin haka, ya ƙarasa bakin ƙofar shiga birnin ya murɗa wata kuba. Nan take ƙofar tayi ƙara mai sautin gaske sannan ƙura ta fara tashi daga jikinta a lokacin da ta fara buɗewa.
A hankali, a hankali ƙofar ta gama wangamewa gaba ɗaya. Aymanul Faris da jaruma Riya suka hango kyawawan gine-ginen dake cikin wannan birni masu tsananin kyawu.
Dukda cewa a zamani mai tsaho aka gina waɗannan gidaje amma zai yi wuya a samu gidajen da zasu kaisu kyau a wannan zamani. Amma da yake ƙura ta gama lulluɓe komai da komai na wannan gari, su Aymanul Faris basu kalli kyawun gidajen ba.
Barban ya sake dafa kafaɗar Aymanul Faris da ta Riya, nan take suka ɓace daga wannan wuri suka bayyana a sararin samaniya a tsakiyar wannan birni. Daga wannan wuri da suke tsaye, suna iya hango komai da komai dake cikin wannan birni, da yake a sararin samaniya suke.
Birnin Shaha: Babban birni ne wanda aka tsara gine-ginen shi izuwa unguwa-unguwa ma'ana kowacce unguwa da yanayin gine-ginenta da kuma yadda aka fasalta ta.
Saboda tsananin girman wannan birni koda za'a dunƙule birnin Kufa, Hirtoliya da Damashkar a saka a cikinsa, ba za su wuce rabinsa kawai ba.
Mutum bai isa ya iya fasalta kyawun wannan birni da girmansa ba, sai dai kawai a ce ya ninka daular sarki Kuffuru a girma sau biyu ko sau uku.
A tsakiyar wannan birni suka hango wani babban ginin gidan sarauta wanda saboda tsananin girmansa zai iya kai rabin birnin Hirtoliya.
Ginin na da tsaho sosai domin har ya soma shigowa cikin gajimare, sannan anyi hikima sosai wajen gina gidan sarautar.
Daga tsakiyar gidan sarautar an gina wani ƙaton gunki na wani sadaukin mutum wanda ke tsaye riƙe da zabgegiyar takobi, gaba ɗaya jikin gunkin da zallar ɗanƴen zinari kore aka gina shi.
Fuskar gunkin a rufe take da baƙin mayafi yadda mutum ba zai iya gane wane ne ba. Yamma da gunkin kaɗan, an gina wata ƙasaitacciyar fada da irin wannan koren zinari wanda aka gina wannan gunki da shi.
Tun da su Aymanul Faris suke basu taɓa ganin irin wannan kyakkyawan gidan sarauta ba. Na farko ƙaton gaske ne, sannan anyi masa kyakkyawan gini, sannan an gina shi yanki-yanki.
Tabbas duk sarkin da ya mulki wannan birni zai ji tamkar duniya gaba ɗaya yake mulka saboda tsananin girman wannan birni da kuma al'umar da zai iya ɗauka. Aƙalla zai ɗauki kamar mutum miliyan ɗari uku zuwa sama.
Barban ya sake dafa kafaɗar Aymanul Faris da ta Riya suka sake ɓacewa daga saman wannan birnin sannan suka bayyana a bakin ƙofar shiga birnin Shaha.
Barban ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Babban jarumi! Idan ka mayar da hankali, nan gaba kaɗan kaine sarkin da zai mulki wannan babban birni mai dumbin tarihi."
Yana gama fadin haka ya nufi cikin wannan birni, Aymanul Faris da jaruma Riya suka take masa baya.
Aymanul Faris na shigowa cikin wannan birni, ƙwaƙwalwarsa ta fara juyawa. Waɗansu irin tunane-tunane waɗanda suke kama da abubuwan da suka faru a baya suka fara yawo a cikin kansa.
Bisa dole ya nemi waje ya tsaya, domin yaji yake tamkar kansa zai yi tsawa ko kuma ƙwaƙwalwarsa ta samu matsala.
Jaruma Riya tana shigowa wannan gari, taji wani irin sauyin yanayi a jikinta. Ita kanta bata san matsalar mece ce ba, amma kwata-kwata jikinta bai aminta da wannan gari ba. Kamar ace mutumin da aka haife shi a yankin da yake da sanyi ne, aka ɗauko shi aka kawo shi wuri mai zafi, haka ta ɗinga ji.
Barban na jin sun tsaya a baya ya juyo ya dube su, koda yaga halin da suka shiga sai ya dawo baya da sauri, ya tsaya a gaban Aymanul Faris sannan ya ɗaura hannunsa guda akan Aymanul Faris.
Nan take wani irin koren haske mai kama da irin wannan haske na cikin idanunsa ya soma fitowa daga cikin hannun Barban, yana shigewa cikin kan Aymanul Faris.
Hasken na fara shiga cikin kansa, Aymanul Faris ya fara dawowa cikin hayyacinsa wannan abubuwa da suke yawo a kansa masu kama da mafarki suka daina.
Barban ya sake ƙarasawa gaban jaruma Riya ya tsaya, sannan itama yayi mata kamar abinda ya yiwa Aymanul Faris. Take duk su biyun suka dawo cikin hayyacinsu sannan suka dubi Barban alamar suna so yayi musu bayani.
Barban ya ce, "Wannan shi ne abinda sarki Samudul Ansari yake jiyewa jama'arku tsoro. Kamar yadda ya saba gargaɗar mutanenku akan cewa kada su kuskura su yi yaƙi a cikin wannan gari, duk ranar da suka yi yaƙi a garin kuwa, wani babban bala'i zai bayyana.
"Wannan sauyin yanayi da kuka ji a jikin ku, ba komai bane face wannan bala'i da yake magana akai. Wannan bala'i shi ne abinda ya hana mutane zama a cikin wannan gari, babu mai iya kawar da shi face wanda ya mallaki ruhin Samudul Ansari."
Barban yana gama faɗin ya shige cikin wannan birni, cikin tsananin mamaki da kalle-kalle Aymanul Faris da Riya suka take masa baya.
Duk inda suka wuce a cikin wannan birni sai dai su ga ƙasusuwan bil'adama waɗanda suka gama ruɓurɓushewa suna komawa ƙasa. Cikin takaici suke kawar da kai sannan su wuce.
Suka yi ta ratsawa ta cikin wannan birni, suka yi ta wuce wurare da yawan gaske masu tsananin kyawu, har suka iso kasuwar wannan gari.
Kasuwa ce makekiya wadda aka ƙawatata sosai, a wani ɓangare dabam nata aka gina manya-manyan rumbuna waɗanda sarakuna suke ajiye abinci.
Su Aymanul Faris suka wuce wannan kasuwa sannan suka tasarwa wannan fada gadan-gadan, duk da cewa nisan dake tsakaninsu da wannan fada mai tsaho ne amma sai Barban yayi amfani da ɗalasimin tsafinsa ya kaisu har ƙofar shiga wannan fada.
Tsayawa fasalta kyawun wannan fada zai ɗau lokaci mai tsaho kafun a kammala. Barban ya sake murɗa wata kyakkyawar kuba, wannan ƙasaitacciyar ƙofa ta soma buɗewa a hankali.
A hankali wannan ƙofa ta gama buɗewa inda su Barban suka hango kayayyaki irin na gidan sarauta masu tsadar gaske. Babu abinda yafi jan hankalinsu idan ba wannan karaga da take tsakiyar fadar ba. Mutum bai isa ya ce ga abinda aka ginata da shi ba.
Ba su wani ɓata lokaci a wannan wuri ba, suka wuce izuwa cikin wani ƙaton ɗaki wanda aka gina a ƙarƙashin wannan fada. Suna shigowa cikin wannan ɗaki, wani azababben zafi ya doke su.
Barban ya nunawa Aymanul Faris wata ƙofa da aka rufe wacce ga dukkan alamu ƙarƙashin wannan ɗaki zata kai mutum, ya ce, ya buɗe. Aymanul Faris yayi gaggawa ya buɗe ƙofar inda ya hango matattakalar bene tayi ƙasa.
"Ayman! Ka bi waɗannan matattakalan benen, zasu kai ka bakin ramin da aljani Nara yake rayuwa a ciki. Mu zamu jiraka daga wannan wuri saboda kai kaɗai zaka iya jure zafin cikin wannan wuri, albarkacin takobin daraja dake tare da kai." Barban ya baiwa Aymanul Faris umarni.
Barban da jaruma Riya suka koma gefe guda suka tsaya, shi kuma Aymanul Faris kai tsaye ya ƙarasa bakin wannan ƙofa yasa hannunsa guda ya buɗeta.
Matattakalar bene mai yawan gaske ta bayyana, yasa ƙafafuwansa ya tattaka ya nufi ƙasa.
Aymanul Faris na shigowa cikin wannan ɗaki yaga ko'ina wuta ce ke tashi daga cikin ɗakin tamkar maƙera. Amma bisa mamaki babu abinda wannan wuta take yi masa, tamkar ba'a cikin ɗakin yake ba.
A nesa kaɗan ya hango wani ƙaton rami, wanda wuta ke tashi daga cikinsa lokaci-lokaci. Kamar yadda ya karanta a tarihi bakin wannan ƙaton rami ake zuwa a tsaya idan ana so aljani Nara ya bayyana, saboda haka ya ƙarasa bakin wannan rami ya tsaya sannan ya zuba idanu.
Wuta mai tsananin yawan gaske tayi feshi daga ƙarƙashin wannan rami, sannan ta soma haɗewa a hankali tana bayar da siffar aljani Nara.
Aljani Nara komai na jikinsa da wuta aka halicce shi, baya rayuwa a ko'ina face tsakiyar wuta. Shi ne wuta, wuta ita ce shi.
Jikinsa na gama haɗewa ya matso kusa da Aymanul Faris suka fara kallon kallo. Wannan shi ne karo na farko da Aymanul Faris ya taɓa kallon aljani Nara ido-da-ido.
"TAU'RIN! Kayi haƙuri bisa ga dukkan abinda ya faru a baya, na rasa rayuwar mahaifinka da jama'arka da kayi." Wannan shi ne abinda aljani Nara ya fara cewa.
Aymanul Faris ya haɗe fuska ya ce, "Shin ka san cewa laifi ka aikata, a lokacin da ka tafi ka barmu aka zo aka yaƙe mu, alhalin kana da ƙarfin da zaka iya gamawa da dukkanin abokan gabar mu?"
Aljani Nara ya ce, "Kayi haƙuri lokacin da wannan yaƙi ya afku, mahaifinka ya riga da ya sadaukar dani a matsayin hadiminsa a wannan lokaci ni ba hadiminsa bane. Bani da dalili guda ɗaya wanda zai sa na shiga wannan yaƙi, idan kuwa nayi kuskuren shiga, hadiman waɗannan sarakuna zasu kai ƙarata wajen sarkin aljanu.
"Mahaifinka mutum ne wanda yasan abinda yake yi, tabbas ba don ya faɗi a wannan yaƙi ba, babu yadda za'ayi ka haɗu da Barban harma ya ceci sauran jama'arka. Kayi sani cewa ba don Barban ya ceci jama'arku ya ɓoye su a wannan birni ba, da yanzu tuni an gama kashe su gaba ɗaya."
Aymanul Faris ya gyaɗa kai ya ce, "Mene dalilin da yasa ake kirana da suna Tau'rin? Sannan idan har kai ba hadimin mahaifina bane a yanzu, mene ne dalilin da yasa ka dawo wannan birni da rayuwa?"
Aljani Nara ya ce, "TAU'RIN: Suna ne wanda ake kiran dukkan wani magajin Samudul Ansari da shi, wato kamar matsayi ne za'a ce. A zamanin da mahaifinka yake raye shi ne Tau'rin ɗin wancan zamanin, a yanzu kuma kaine.
"Dalilin da yasa nake zaune a wannan birni shi ne saboda ni ne hadimin da Samudul Ansari ya wakilta a lokacin da yazo mutuwa, a matsayin wanda zai na yiwa dukkan magajinsa hidima. Mahaifinka ya nuna bai damu dani bane, shiyasa na fita a al'amuransa."
Cikin fahimta Aymanul Faris ya gyaɗa kai sannan ya ce, "Shin kana da labarin ARYA II?"
"Kwarai kuwa!" inji Nara. "Nafi kowa farin ciki da soyayya ta shiga tsakaninku tun daga yanzu. Zamanin da mahaifinka yake raye, ba'a haifi Arya ba. Saboda wannan dalili aljanu da yawa suke ce min, mahaifinka ba zai taɓa gadon wannan ruhi ba.
"Amma kai gashi tun baka fara manyanta ba, har ka haɗu da Arya sannan har soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninku. Tabbas kaine wanda yake da dama ɗari bisa ɗari ta mallakar wannan ruhi amma sai ka mayar da hankali.
"Hankalina yafi kwanciya da kai saboda haka zan mayar da hankali sosai wajen taimakonka domin ganin wannan ruhi ya zamo mallakinka.
"Kayi sani cewa akwai wani sirri wanda mai girma Samudul Ansari ya sanar dani a lokacin da zai mallaka min wannan takobi dake hannunka, tabbas sanin wannan sirri ne ya sa na karɓi wannan aiki sannan nayi rantsuwa da rayuwata akan zan tsaya tsayin daka wajen ganin waninku ya mallaki wannan ruhi."
Aymanul Faris ya sake haɗe fuska ya ce, "Wanne irin sirri ne wannan?"
Aljani Nara ya ce, "Ba zan taɓa sanar da kai wannan sirri ba, face kana daf da mallakar wannan ruhi."
Aymanul Faris na shirin sake tambayarsa kenan, ya ce, "Muje wajen su Barban tun ɗazu suke jiranka har sun fara ƙosawa."
Yana faɗin haka ya juye izuwa ɗan ƙaramin tsuntsu mai jan gashi, tsuntsun ya taso daga cikin wannan wuta sannan yazo ya sauƙa akan kafaɗar Aymanul Faris.
Aymanul Farisa ya kalli tsuntsun yayi murmushi sannan ya fito daga cikin wannan ɗaki, ya nufi inda su Barban suke tsaye. Yana zuwa ya ce musu ga aljani Nara akan kafaɗarsa.
Suna jin haka suka ɗunguma gaba ɗayansu suka kama hanya, suka fice daga cikin wannan gidan sarauta.
Barban ya kirawo aljanu guda biyu, ya hau kan guda ɗaya, ya baiwa Riya guda ɗaya. Aymanul Faris kuma, wannan jan tsuntsu ake kan kafaɗarsa ya juye izuwa jibgege ya haye kansa.
Nan take suka tashi sama suka lulluƙa cikin gajimare, basu yi nisa da wannan tafiya ba, irin wannan mugun jiri ya sake bugan Aymanul Faris da Riya suka kwanta akan aljanun kamar sumammu.
Suna farfaɗowa suka tsinci kansu a tsakiyar wannan fada ta sarki Ranganu. Aljanin ya sake nuna musu waɗannan kujeru suka zazzauna, sannan ya dubi wannan tsuntsu dake kan kafaɗar Aymanul Faris yayi masa bayanin yadda wannan aiki zai kasance.
Aljani Ranganu na gama yiwa wannan aljani bayani, ya fiddo wata taswira ya baiwa aljanin sannan ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Wannan aiki ku uku zakuje ku aiwatar da shi. Wato kai, Riya da aljaninka. Ina so na zauna da Barban domin mu tattauna akan maƙiyanmu."
Yana gama faɗin haka ya basu umarnin tafiya. Irin wannan jiri ya sake ɗibar su, suka zube ƙasa sumammu.
****
Yau *12/01/2023*
Babi na gaba zaizo: *14/01/2023* da izinin ALLAH.
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 71: *Ileisha Gorgon*
*
DEDICATED TO PRINCESS ZAHRA.
*
UMAR M*S
*
Lokacin da su Aymanul Faris suka farfaɗo sai suka tsinci kansu a bakin wani ƙaton daji mai mummunan yanayin hazo, saboda tsananin kaurin hazon dake wannan daji, basa iya hango abubuwan dake cikin dajin sosai. Suna ganin komai dishi-dishi.
Cikin tsananin mamaki jaruma Riya ta dubi Aymanul Faris ta ce, "Masoyina wai shin wannan dajin zamu shiga a irin wannan yanayi da yake ciki?"
Kafun Aymanul Faris ya buɗe bakinsa ya ce wani abu, wannan tsuntsu dake zaune akan kafaɗarsa ya rikiɗe ya koma siffar aljani Nara. Ya dube su ya ce, "Ina zuwa."
Yana faɗin haka ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama ya shige cikin wannan daji mai yawan yanayi na hazo, ya buɗe bakinsa ya fara fesar da wuta tamkar tsohon jegari.
Wata irin azababbiyar wuta mai kama da narkakkiyar wutar dutsen wuta ta soma sauƙa a cikin wannan daji. Nan take wani irin jan hayaƙi ya soma tashi daga cikin dajin.
Sai da aljani Nara ya gama kewaye wannan daji sau uku sannan ya sauƙo ƙasa kusa da su Aymanul Faris ya tsaya. Ba su ce dashi uffan ba, dukkaninsu suka zubawa wannan jan hayaƙi idanu.
A hankali wannan hayaƙi ya soma lafawa, waɗansu irin gabza-gabzan bishiyoyi suka soma bayyana a cikinta. Bishiyoyi ne masu tsaho da kaurin gaske, babu inda mutum zai same su a duniya idan ba irin wannan daji ba.
"Na karya asirin dake ɓoye lambun Gorgon, shiyasa kuka ga wannan lambu ya bayyana. Waɗannan bishiyoyi sune katangar da ta rufe wannan lambu nasu. Bari na samar mana da hanya, mu shiga cikin lambun mu tsinko waɗannan furanni tun da naga gaba ɗaya halittun barci suke."
Aljani Nara yana gama faɗin haka ya nufi waɗansu manya-manyan bishiyoyi guda biyu, yana zuwa gindin bishiyoyin ya sake buɗe bakinsa ya hura musu wannan azababbiyar wuta tasa. Take suka kama da wuta sannan a hankali suka soma juyewa izuwa toka.
Tsahon kusa daƙiƙu ɗari takwas da arba'in waɗannan bishiyoyi suka ɗauka suna ƙonewa, kafun su gama zamowa toka sannan suka zube a wannan wuri.
Cikin tsananin farin ciki Nara ya juyo ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Hanya ta samu, kuzo muje mu ɗauko abinda ya kawo mu."
Yana faɗin haka ya shige cikin wannan ƙaton lambu, Aymanul Faris da jaruma Riya suka yi ajiyar zuciya sannan suka bi bayansa.
Lambu ne mai girma da kyawun gaske. Gaba ɗaya ƴaƴan itatuwan dake cikin wannan lambu nunannu ne, babu ruɓaɓɓu ko kuma ɗanƴu.
Sannan akwai furanni masu kyawun gaske kala-kala, wasu farare, wasu koraye, wasu ruwan ɗorawa.
Haka kuma akwai ƙananun ƙoramu waɗanda ƙananun kifaye keta iyo a cikinsu. A taƙaice dai wannan lambu kyakkyawan gaske ne, hatta iskar dake kaɗawa a cikin wannan lambu ta dabam ce.
Aymanul Faris da jaruma Riya suka tsaya kalle-kalle da dube-dube, babu abinda yafi jan hankalin Riya kamar waɗansu korayen furanni dake can gefe guda.
Ji take kamar ta ruga da gudu ta tsinko su, ta kawowa masoyinta wanda ke tsaye a gefenta. Amma Riya bata kasance mai karambani ba, wataƙila akwai wani sharri a jikin waɗannan furanni wanda bata sani ba.
Wannan shi ne dalilin da ya hanata zuwa tsinko waɗannan furanni. Haka dai suka yi ta ratsawa ta cikin wannan lambu suna tafiya a hankali, don kada ƙarar takun sawayensu ta tashi Gorgons daga barci.
Kusan daƙiƙu ɗari tara da wani abu suna ta dube-dube a cikin wannan lambu sannan suka hango waɗannan fararen furanni waɗanda suka zo nema.
Babbar matsalar ita ce ga inda aka shuka waɗannan furanni ga ɗakin da Gorgons suke barci, motsi kaɗan zai iya haddasa sauti wanda zai tashe su daga wannan barci.
Idanun Aymanul Faris na yin arba da waɗannan furanni, yaji wani aminci a ransa. Babu buƙatar a yi masa bayani yasan tabbas su ne abinda zasu bayyanar masa da asalin surar masoyiyarsa.
Aymanul Faris ya nuna musu waɗannan furanni ya ce, "Ga abinda muka zo nema can, kuzo muyi gaggawar zuwa mu tsinko su. Tabbas idan muka mayar da hankali, ko tashi daga barci ba za su yi ba."
Aljani Nara ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Ka daina ɗaga murya idan zaka yi magana, sautin muryarka zai iya tashinsu daga barci. Mu gaggauta zuwa wancan wuri mu tsinko waɗannan furanni."
Aljani Nara na gama faɗin haka ya fara sanɗa a hankali, ya tunkari wannan yanki wanda aka cika da irin waɗannan furanni. Aymanul Faris da Riya suka take masa baya a hankali.
Ba su jima ba, suka ƙarasa bakin ƙofar shiga wannan wuri. Abin mamaki ƙofar shiga wurin a buɗe take, ga dukkan alamu basu jima da amfani da wurin ba.
Aymanul Faris ya baiwa Riya umarnin shiga wannan lambu domin tsinko furannin. Cikin kwanciyar hankali da nutsuwa Riya ta tunkari ƙofar shiga wannan wuri.
Tana daf da wucewa ta cikin wannan ƙofa, aljani Nara yayi tsalle da nufin ya tureta gefe domin akwai abinda ya gani a bakin wannan ƙofa ita da Aymanul Faris basu gani ba.
Amma ina, kafun ya ƙarasa inda take tuni ta wuce ta cikin wannan ƙofa.
Wata iska mai ƙarfi ta kaɗa a cikin wannan daji. Waɗannan manya-manya-manyan bishiyoyi da suka kewaye dajin, ganyayen su suka kaɗa da ƙarfi suka haifar da gagarumar ƙara mai kama da ƙarar aradu.
Aljani Nara ya dubi Riya cikin takaici ya ce, "Mun tafka babban kuskure da bamu gudanar da bincike kafun wucewa ta cikin wannan ƙofa ba. Tabbas akwai ɓoyayyun igiyoyin sihiri da suka ƙuƙƙule a wannan wuri, waɗanda mutum yana taɓawa irin wannan ƙara zata afku."
Aymanul Faris ya dube shi ya ce, "Yanzu mene ne abin yi?"
"Ta yi gaggawar tsinko waɗannan furanni, domin kuwa daga kowanne lokaci daga yanzu, waɗannan halittu zasu iya farkawa daga barci." inji Nara.
Aymanul Faris yayi gaggawar sanar da Riya wannan umarni da Nara ya bashi.
Cikin gaggawa jaruma Riya ta ƙarasa cikin waɗannan furanni, ta saka hannunta guda ta tsinko masu yawa daga cikinsu.
Furannin na barin jikin uwarsu, irin wannan ƙara wadda ta afku daga farko ta sake afkuwa.
Jaruma Riya ta rugo da gudu ta kawowa Aymanul Furannin, cikin gaggawa ya karɓe su ya saka a cikin jakar guzurinsa.
Nan take dukkaninsu su uku, suka juya da gudu da nufin fita daga cikin lambun.
Sai da suka zo bakin ƙofar da suka shigo, saura ƙiris su fita daga lambun. Irin waɗannan bishiyoyi suka tsirowa daga ƙarƙashin ƙasa suka tare musu hanya.
Aljani Nara na shirin sake ƙonesu kenan, suka ji motsi a bayansu. Cikin tsananin mamaki suka juya da baya domin ganin abinda ya haddasa wannan motsi.
Wata kyakkyawar budurwa suka gani tsaye a bayansu sanye da koriyar riga mai beza kamar jelar maciji ta ƙasa. Gashin kanta kore ne sidik sannan a gauraye yake da baƙi-baƙi.
Idanuwanta masu tsananin kwarjini tsaye cak akan su Aymanul Faris. A tsakiyar goshinta akwai zanen ƙatuwar macijiya mai jan dafi.
"Suna na ILEISHA GORGON, su wane ne ku?" inji wannan tsaleliyar budurwa cikin wani irin yare wanda su Aymanul Faris basu taɓa jin irinsa.
Sai da aljani Nara ya fassara musu abinda tace sannan suka gane.
Aymanul Faris ya ce, "Ko mun faɗa mata mu su waye, bai da amfani. Muyi shirin guduwa kawai saboda yaƙi da waɗannan halittu sai cikakken shiryayye."
Ayman yana gama faɗin haka ya zaro takobinsa ta Saiful-Shiradu, irin wannan yanayi ya sake afkuwa. Aymanul Faris ya ƙaddamar da aljanu guda goma na wutan nan.
Ya sa guda huɗu suka ɗauki jaruma Riya suka tashi sama da ita, sannan suka ɓace ɓat.
Aymanul Faris ya dubi Nara ya ce, "Kayi gaggawar barin wannan wuri, kafun wannan hatsabibiya ta fara yaƙar mu."
Aljani Nara na jin wannan umarni ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Tabbas zan bi umarninka amma a duk lokacin naga faɗan na faman fin ƙarfinka zan bayyana."
Yana fadin haka ya ɓace ɓat! Aymanul Faris ya saka waɗannan aljanu guda shida suka kewaye shi, ya riƙe takobin Saiful-Shiradu da hannu biyu sannan ya ƙurawa wannan budurwa mai suna Ileisha Gorgon idanu.
Koda Ileisha taga abokan tafiyar Aymanul Faris sun gudu an barta da shi, su kaɗai, sai ranta ya ɓaci. Idanuwanta suka soma sauya launi suna komawa irin na maciji.
Gashin dake kanta ya fara motsi yana ƙara girma, siffofin macizai suka fara bayyana a cikinsa. Wannan shi ne abinda ke faruwa a duk lokacin da ɗan ƙabilar Gorgon ya fusata.
Aymanul Faris na ganin haka ya gyara riƙe takobinsa sannan ya dubi aljanun dake kewaye da shi yayi musu magana da yaren tsafi, nan take dukkaninsu suka ɓace ɓat.
Ileisha ta zaro wata zabgegiyar takobi mai siffar maciji ta rugo da gudu kan Aymanul Faris tana wani irin ihu mai kama da na maciji.
Aymanul Faris ya tsaya cak a inda yake, idanuwansa na tsaye a kanta. Kafun ta iso inda yake ta taka wani ƙaramin tudu tayi tsalle sama ta kawo wawan sara a wuya, da nufin ta tsinke masa kai.
A wannan lokaci idan mutum zai dubi wannan budurwa zai ganta tamkar macijiya, saboda bata da wani bambanci da macijin.
Aymanul Faris ya saka takobinsa ya kare wannan sara nata, takubbansu na haɗuwa a waje guda aka kwararo wata uban tsawa. Dajin gaba dayansa yayi girgiza.
Aymanul Faris da Ileisha Gorgon suka ruguntsume da azababben yaƙi a cikin wannan lambu, suka yi ta kaiwa junansu sara da suka cikin baƙin nama, juriya da bajinta.
A duk sa'adda takubbansu suka haɗu a waje guda, sai an kwararo gagarumar tsawa wacce zata sa wannan daji gaba ɗaya yayi girgiza.
Ileisha gawurtacciyar jaruma ce wacce ta iya yaƙi sosai, dukda cewa Aymanul Faris ya samu gagarumin horo na yaƙi amma ko rabin Ileisha baiyi ba.
Babu abinda ke ƙwatarsa daga sharrinta face tsananin zafin namarsa da kuma jarumtakarsa.
Haka dai Aymanul Faris da Ileisha suka yi ta gwabza yaƙi har tsahon rabin sa'a, ba tare da ɗayansu ya yiwa ɗan uwansa rauni ba.
Lamarin da yayi matuƙar ɓatawa Ileisha rai kenan, saboda wannan shi ne bil'adama na farko da ɗan

Please Login or Register in order to submit comment