Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hanya?"
Wannan saurayi na jin batun wannan sarki ya zaro takobinsa sannan ya durƙusa bisa gwiwowinsa alamun mubaya'a.
"Ni ne Gauhan Ansari daga yau, nayi mubaya'a ga Gorgon. Zan taimaka wajen ganin kun ƙwace wannan daula..." inji saurayin.
Waɗannan sarakuna suka dubi junansu suka gyaɗa sannan ɗaya daga cikinsu ya ce, "Kai baka kishin ƙasarka ne... Mene ne dalilin da zai sa kayi mana mubaya'a alhalin mun zo wannan daula ne domin mu ƙarar da kowa (har iyalenka da mahaifanka)"
Gauhan ya ce, "Bani da kowa a duniya face masoyiyata Zarifa. Ni indai za ku bani auren Zarifa sannan ku bani mulkin birnin Ilam, zan taimaka muku wajen ganin kun ƙwaci wannan daula cikin ruwan sanyi.
"Babu wani lungu da saƙo na wannan daula da ban sani ba, babu wanda ya kaini iya haɗa tuggu. Tabbas za ku ji daɗin tarayya da ni."
Waɗannan sarakuna guda biyu, suka yi ƙus-ƙus na tsahon ƴan-daƙiƙu kafun ɗaya daga cikinsu ya ƙarasa gaban Gauhan ya dube shi.
"Tabbas kayi shawara mai kyau, yaro. Idan ka taimaka muka ƙwaci wannan daula kamar yadda kake faɗa zamu baka auren wannan yarinya.
"Batun baka mulkin birnin Ilam muna da sharuɗɗa. Idan ka cika waɗannan sharuɗɗa, ba iya birnin Ilam ba, wannan daula gaba ɗaya zamu mallaka maka."
Cikin tsananin farin ciki Gauhan ya ce, "Ina so naji waɗannan sharuɗɗa naku, ni kuma zan kasance mai cika su. Bani da buri a rayuwata da ya wuce mulkar wannan daula!"
Sarkin ya yi murmushi ya ce, "Muna so kayi mana bayanin wane ne Samudul Ansari... Sharaɗi na farko kenan.
"A ina zamu riski wannan mutumi sannan ta ya ya zamu hallaka shi, cikin ruwan sanyi... Sharaɗi na biyu.
"Waɗanne hanyoyi kake ganin ya kamata mu bi wajen ganin bayan wannan mutumi...
"Idan ka amsa waɗannan tambayoyi daidai kuma muka bi su, muka samu nasara tabbas zamu baka kyautar wannan daula gaba ɗaya..."
Koda Gauhan ya gama jin batun wannan sarki, sai yayi shuru yana ta tunani.
Kamar ba zai ce komai ba, daga can sai ya numfasa ya ce.
"Samudul Ansari, mutum ne wanda zai iya yin komai akan ya ceci rayuwar talakawa.
"Jarumi ne shi na kwatance amma yana da rauni guda ɗaya.
"Wannan rauni nasa ba komai bane, illa yana da tsananin tausayi.
"Wannan tsananin tausayi nasa, za'a iya amfani dashi wajen kama shi a hannu."
Gauhan yayi musu bayani a haka, saboda kada su ga kamar yana kurara Samudul Ansari.
Gauhan ya ci gaba da bayani, "A halin yanzu Samudul Ansari yana cikin sansanin mayaƙa tare da sarakunan wannan daula guda shida.
"In dai aka samu nasarar raba shi da waɗannan sarakuna, hakan zai rage masa ƙarfi sosai a wannan yaƙi harma a samu nasarar kashe shi ko kuma a kama shi.
"Ni zan iya zuwa cikin wannan sansani nasa waɗannan sarakuna guda shida su juya masa, indai suka juya masa baya zai kasance a wannan yaƙi shi ɗaya jal.
"Zan yi amfani da wannan dama na baku dama, ku yaƙi waɗannan sarakuna.
"In dai muka karya waɗannan sarakuna guda shida tamkar mun sami nasara akansa ne, domin su ne masu taimaka masa."
Wannan basarake na jin haka ya gyaɗa kai, cikin fahimta ya ce, "Tabbas ta wannan hanya zamu iya ganin bayan wannan jarumi. Babu yadda zai iya ja damu, matuƙar aka ce mun ƙwaci wannan daula sannan ba zai iya guduwa mana ba, saboda zamu mamaye dukkan daular.
Wannan shi ne yadda aka yi Gauhan Ansari ya ƙulla yarjejeniya da mutanen ƙabilar Gorgon akan cewa zai kawo kan Samudul Ansari, su kuma zasu bashi kyautar wannan daula.
Gauhan shi ne wanda ya kaiwa Samudul Ansari hari, sa'adda yake hanyarsa ta zuwa ɗakin Arya domin more amarci.
Zaka iya cewa, wannan ɗaukaka da Samudul Ansari ya samu Gauhan yafi kowa a duniya baƙin ciki saboda yasan cewa abu ne mawuyaci yayi nasara akan Samudul Ansari a haka.
To, dama Gauhan mutum ne mai tsananin hikima da hangen nesa.
Yayi tunanin haka zata iya faruwa, shiyasa ya baiwa waɗannan sarakuna shawarar sare kan waɗannan sarakuna guda shida na wannan daula, indai aka ce babu waɗannan sarakuna guda shida tamkar sun ci wannan daula ce.
Idan kuwa aka ce wannan daula tana ƙarƙashin ikonsu babu yadda za'ayi Samudul Ansari ya samu nasara akan su.
Don ance sarkin yawa... yafi sarkin ƙarfi.
A taƙaice dai, Gauhan Ansari ya haɗa kai da waɗannan sarakuna ne domin ya baiwa ma'abota Bankai damar kashe su cikin sauƙi.
Wannan shi ne shirin Gauhan Ansari wanda waɗannan sarakuna guda biyar da suka juyawa Samudul Ansari baya basu sani ba.
***
~Filin Yaƙi, birnin Wabisal.
***
Sarakunan daular Shaha guda biyar da mayaƙansu, suna ta murna bisa ganin Gauhan ya kare su daga sharrin Bankai.
Waɗannan sara-mai-tafiya guda hamsin da ma'abota Bankai suka aiko, taurarin Gauhan sun tarwatsa su.
Ma'abota Bankai suna ganin haka, suka ɗaga takubbansu sama, farin hayaƙi ya soma ɓulɓula daga takubban nasu guda goma yana tafiya cikin gajimare.
Sannu-a-hankali farin hayaƙi mai ɗan yawa ya taru a cikin gajimaren, ya soma haɗewa a waje guda yana bayar da siffar macijiya [Mesa]
Suna ganin haka suka sake aika irin waɗannan sara-mai-tafiya guda hamsin kan su Gauhan.
A wannan lokaci, ba wai iya faifan haske ne ya tunkaro su Gauhan ba.
Har da wannan sabon gajimare wanda ya bayyana sakamakon ɓulɓular farin hayaƙi daga takubbansu, shima ya dawo saman su Gauhan ya tsaya.
Gauhan ya sake saran iska da wannan takobi ta hannunsa, lamarin da yasa irin waɗannan taurari suka sake bayyana kenan.
Kafun su haɗu wannan hadiri mai siffar maciji ya soma rugugi yana komawa kore, wasu irin macizai suka fara sauƙowa daga cikinsa suna wangame bakunansu suna haɗiye waɗannan taurari na Gauhan.
Lamarin da yayi matuƙar ɗugunzuma hankalin waɗannan sarakuna guda biyar da mayaƙansu kenan.
Waɗannan gabza-gabzan macizai suna gama haɗiye taurarin, Gauhan ya zube ƙasa kan gwiwowinsa tamkar wanda aka zarewa laka.
Daga bisani jikinsa ya soma yin hazo-hazo yana ɓacewa, har ya gama ɓacewa.
Kai da gani ka san cewa, waɗannan taurari su ne ƙarfinsa, yanzu kuma an cinye su.
Wannan abu fa yayi matuƙar ɗugunzuma hankalin waɗannan sarakuna fiye da kowanne lokaci, saboda abin dogaron nasu baya nan.
A daidai lokacin ne, waɗannan saran takobi-mai-tafiya suka ƙaraso inda suke.
Nan fa suka fara tarwatsa mutane, suna saran jikinsu tamkar ana yanka tsakiyar tuffa.
Waɗannan mayaƙa gaba ɗayansu suka tarwatse suna guje-guje da iface-iface saboda basu taɓa ganin hari irin wannan ba.
Kafun a jima wannan hari ya kashe wajen mutum dubu biyar, sannan ya raunata mutane da yawa daga cikin mayaƙan.
Sarakunan ƙabilar Gorgon suka baiwa waɗannan ma'abota Bankai ɗin umarnin daina kai irin wannan hari, suka baiwa wani kaso daga cikin mayaƙansu umarnin afkawa maƙiya.
Mayaƙa dubu casa'in suka zaburi dawakansu da gudu, suka yi kan dakarun waɗannan sarakuna guda biyar suna kwarara uban ihu, suna ɗaga takubba masu siffar maciji sama.
Koda waɗannan sarakuna guda biyar suka ga haka, sai suka yi farin ciki suka baiwa dakarunsu afkawa mahaya guda dubu casa'in ɗinnan.
Sai da aka kwana bakwai cir ana gwabza wannan yaƙi, sannan aka karya dakarun waɗannan sarakuna guda biyar.
Aka kashe da yawa daga cikinsu, sauran kuma aka kama su a matsayin bayi.
Waɗannan sarakuna guda biyar dukkansu suka durƙushe kan gwiwowinsu alamar sun yi mubaya'a.
Jim kaɗan waɗansu taurari guda biyar suka bayyana a daidai wuyan kowanne daga cikinsu.
Sarakunan suna ganin waɗannan taurari suka soma kuka, saboda sun gano abinda ke shirin faruwa.
Take waɗannan taurari suka juye izuwa takubba masu kaifi, suka fille kan waɗannan sarakuna guda biyar.
Gauhan ya bayyana riƙe da kan waɗannan sarakuna a hannunsa. Ya gabatar da su ga waɗannan sarakuna sannan ya sake jadda mubaya'arsa.
A wannan rana Gorgon suka ci daular Shaha da yaƙi, tare da taimakon Gauhan Ansari wanda ya ɗaura waɗannan sarakuna a bayan kura.
Inda ace suna tare da Samudul Ansari da abin ba zai rincaɓe haka ba.
Waɗannan manyan sarakuna guda biyu suka ƙaraso gaban Gauhan Ansari suka dube shi a hasale suka ce, "Ina Samudul Ansari, ya ya aka yi bamu kalle shi ba har aka kammala wannan yaƙi?"
Gauhan Ansari ya yi dariyar mugunta ya ce, "Ya tsorata ya gudu, ya ɓuya a birnin matarsa, birnin Ilam."
Sarakunan suka yi dariya, suka ce, "Ya shiga hannu..."
A wannan waje suka yada zango, gari yana wayewa suka afka manyan biranen wannan daula guda biyar suka kafa tutocinsu.
A wannan rana daular Gorgon ta ƙwaci wannan daula ta Shaha, ta mamaye manyan biranen daular guda biyar, ya rage saura birnin Ilam kaɗai.
Dole mutane suka yi mubaya'a suka koma bayinsu, duk wanda yayi gardama su kashe shi.
Rana guda masu yanci suka koma marasa yanci.
Kaɗan daga cikin mutane ne, suka tsere izuwa birnin Ilam amma a tsorace.
***
~Daular Gorgon.
***
Abin mamaki, tun sa'adda sarauniya Yilan ta baiwa mutanen birnin Mesa da birnin Hazram umarnin saro kan Samudul Ansari.
Lokacin da mayaƙan suka tafi izuwa daular Shaha sai ta bayar da umarni ga dukkan wannan daula cewa, a fara horon yaƙi domin gagarumin yaƙi wanda aka daɗe ba'a gani ba yana nan tafe.
Mutanen wannan daula suka yi ta mamaki, saboda basa ganin akwai wanda ya isa yaja dasu a wannan zamani.
Sa'adda ɗaya daga cikinsu ma, ta shiga duniya da ƙyar aka kawar da ita.
Ya ya abin zai kasance idan aka ce mayaƙan birnin Mesa da Hazram aka tura?
Sannan ace mutum ɗaya kacal aka basu umarnin kashewa?
Shin wanne irin hatsabibi ne wannan mutumi?
Sarauniya Yilan ba tace da su komai ba, amma hatta ita kanta ma, sai da ta ɗauko maɗaukakan takubbanta ta ci gaba da baiwa kanta horo.
Ya kamata a san cewa, waɗannan takubba dake hannun sarauniya Yilan babu maɗaukaka kamar su duk faɗin daular.
Duk wanda ke kan matsayinta yana gadon irin waɗannan takubba.
Sarauniya Yilan ita kaɗai mahaifinta ya haifeta, sannan ba wai ya mutu bane ta gaje shi.
Murabus yayi daga kan mulki ya bata, saboda tsananin jarumtakarta da kuma baiwar da take da.
Mafi yawancin lokuta sarauniya Yilan tana tare da wannan mahaifi nata suna tattaunawa akan al'amuran mulki.
Zaka iya cewa, mahaifinta shi ne wanda yake ja mata kunne akan Samudul Ansari.
Saboda ya san abinda ita bata sani ba.
Koda sarauniya Yilan ta samu labarin yadda jama'arta suke yawan mamaki akan umarnin da take bayarwa sai ta ziyarci mahaifinta wanda ya keɓe kansa daga cikin wannan gari ya koma can bayan gari, yana gudanar da halwa a cikin ɗakin tsafinsa.
Koda mahaifinta yaji abinda ke tafe da ita sai yayi ajiyar zuciya ya ce, "Duk faɗin duniya babu wanda ya isa ya tsayar da mu. Mun fi ƙarfin kowa.
"Amma a halin yanzu babbar masifar da magabatanmu suke jin tsoro ta bayyana.
"Kawar da Tau'ron [ma'ana na II] daga duniya babban masifa ne a gare mu!"
Sarauniya Yilan ta ce, "Ya kai abbana!
"Muna da Renin-Yilan!
"Muna da Bankai!
"Muna sarrafa baƙin dafi wanda zai girgiza duniya gaba ɗaya!
"Mene ne wannan Tau'rin ɗin yake taƙama da shi, wanda zai girgiza mu?"
Mahaifin nata ya sake yin ajiyar numfashi sannan ya fiddo wani tsohon littafi nasa ya buɗe shafin farko.
A wannan shafi na farko akwai hoton wani dattijon mutum mai irin wannan gashin kai nasu.
A ƙasan hoton an rubuta sunansa kamar haka; sarki SADUSA ƙarni na takwas.
Mahaifin nata ya dube ta ya ce, "Tun zamanin sarki Sadusa a ƙarni na takwas an sha tattaunawa akan Tau'rin a majalisa, saboda babbar illar da zai haifarwa da wannan ƙabila tamu."
Yana faɗin haka ya buɗe wani shafi wanda ke ɗauke da maganar sarki Sadusa ta ƙarshe.
"KU NEMO 'ISRABIL' SHI NE KAƊAI WANDA ZAI CECE KU DAGA SHARRIN TAU'RIN!"
Mahaifin nata ya dubeta sannan ya sake buɗo shafi na gaba wanda ke ɗauke da bayanan sarkin da yayi zamani a ƙarni na bakwai da kuma wasiyyar da ya bar wa na baya.
"ISRABIL NE KAƊAI ZAI CECE KU DAGA SHARRIN TAU'RIN!"
Sai da mahaifinta ya buɗo wasiyyoyin wajen sarakuna guda ashrin da biyar duk wasiyyarsu guda ɗaya.
Dukkansu suna magana akan ISRABIL domin kare su daga sharrin Tau'rin.
Lamarin da yayi matuƙar baiwa sarauniya Yilan mamaki kenan.
Tun da take a rayuwarta yau ne rana ta farko da ta fara jin wannan kalma "ISRABIL"
Wane ne shi?
A ina yake?
Ta ya ya zai kare wannan daula tasu?
Waɗannan tambayoyi ne da take da buƙatar sani.
"Wane ne shi? meyasa magabatan mu suke bayar da wasiyyar mu nemo shi?" sarauniya Yilan ta tambayi mahaifinta.
Mahaifin nata yayi murmushi sannan ya mayar da wannan tsohon littafi ya ajiye, ya sake jawo wani sabo wanda bai koɗe sosai ba.
A jikin bangon wannan littafi an rubuta ISRABIL da yarensu.
Ya buɗe wannan littafi, ya ɗan duba abinda ke cikin littafin, kafun ya ɗago kai ya soma yi mata jawabi.
"Kamar yadda kalmar Tau'rin take ɗaukar ma'ana guda biyu, haka kalmar ISRABIL take ɗaukar ma'ana guda uku.
"Ma'ana ta farko wadda dukkan duniya ta sani shi ne, sunan wata dabbar daji dake rayuwa a yankunan ƙanƙara.
"Ma'ana ta biyu wadda manyan matsafa da aljanu suka sani shi ne, tauraruwa mai sa'a wato kamar mutum wanda yake da tauraruwa mai ƙarfi wadda take bashi sa'a.
"Ma'ana ta uku wadda babu wanda ya santa face mu sarakunan wannan daula (waɗanda suka shuɗe, da waɗanda suke kai) shi ne, HASKE MAƊAUKAKI ko kuma kishiyar Tau'rin!"
Sarkin na zuwa nan a zancensa ya buɗo wani shafi wanda ke kusan ƙarshen wannan littafi ya nunawa Yilan.
Shafin na ɗauke da hoton macijiya Ziyazilu, a ƙasan ta anyi rubutu kamar haka:
"IN DAI KUN AMINCE NI CE ABAR BAUTAR KU, TO KU NEMO SARKIN KU WANDA YA DACE DA MULKAR KU!"
Sarkin ya dubeta ya ce, "ISRABIL, mai girma Ziyazilu take nufi..."
Cikin tsananin mamaki sarauniya Yilan ta dubi mahaifin nata ta ce, "Ya kai abbana! Baka amsa min tambayar da nayi ma ba. Wane ne ISRABIL?"
Mahaifin nata yayi murmushi sannan ya dubeta cikin nutsuwa ya ce, "Bari nayi miki bayanin wannan mutumi kamar yadda na fassara miki ma'anar sunan nasa.
"ISRABIL: Mutum ne wanda haske yake yawo a cikin jinin jikinsa da kuma jijiyoyinsa.
"Wannan mutumi yana iya juyar da jikinsa izuwa haske, yadda zai kare kansa da dukkan hare-haren da aka aiko masa.
"Ziyazilu ta ce min, karagar da aka gina a fadar wannan daula tamu, ISRABIL ne zai zauna akan ta.
"Shin kin san dalilin da yasa ake cewa ISRABIL ne kaɗai zai kare mu daga sharrin TAU'RIN?"
Sarauniya Yilan ta girgiza kai ta ce, "Wannan shi ne dalilin da yasa na taso da kaina nazo wajenka domin ka fayyace min?"
Sarkin ya sake yin ajiyar zuciya ya ce, "Tau'rin wuta ne! Shi kuma ISRABIL haske ne!"
Sarauniya Yilan ta ce, "Me hakan yake nufi kenan?"
"Bayani da baki ba zai fassara waɗannan kalmomi face idanuwanki, sun yi arba da su...
"Tau'rin da wuta yake mu'amala. Shi kuma ISRABIL da haske yake mu'amala.
"Ba za ki gane wannan bayani nawa ba, amma ina so ki kalli gumurzun da za'a fafata gobe tsakanin rundunar mutanenmu da kuma mutanen birnin Ilam wanda shi ne kaɗai ya rage mu gama mamaye wannan daula..."
Haka dai sarauniya Yilan da mahaifinta suka ci gaba da tattauna har tsahon ɗan lokaci, sannan suka yi sallama ta koma birnin ta.
****
Yau *09/03/2023*
Babi na gaba zaizo *11/03/2023* da yaddar ALLAH.
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 96: *Dodon Gorgon*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U~M~S
*
Tuni labari ya gama cika birnin Ilam cewa, mayaƙan Gorgon sun sami nasara a wannan yaƙi da aka gwabza a filin yaƙin birnin Wabisal. Sun karya waɗannan sarakuna guda biyar sannan sun mamaye ƙasashen su.
Birnin Ilam ne kaɗai yayi saura, su kammala mamaye wannan daula.
Labari ya riski mutanen garin Ilam cewa, mayaƙan Gorgon na ta shirye-shiryen afkowa wannan birni domin su cishi da yaƙi kamar yadda suka ci sauran garuruwan guda biyar.
A wannan rana Samudul Ansari, Zarifa da sarauniya Arya suna zaune a cikin fadar ƙasar suna tattaunawa akan wannan yaƙi wanda zai iya ɓallewa a kowanne lokaci.
Sarauniya Arya da Zarifa sun sunkuyar da kawunansu ƙasa suna sauraron jawabin da Samudul Ansari yake musu.
Bayan sarauniya Arya da Zarifa, akwai ɗaiɗaikun mutane a cikin fadar waɗanda suka haɗa da sarkin yaƙi da manyan masu faɗa a ji na ƙasar.
"Tabbas sarakunan wannan daula sun yi babban kuskure da suka amince da Gauhan, domin yana daga cikin manyan dalilan da suka sa garuruwansu suka faɗi.
"Tabbas yaƙin da zamu gwabza da waɗannan mutane, sai yafi wanda suka gwabza da dakarun waɗannan garuruwa guda biyar, saboda dodonsu ya bayyana.
"A wannan yaƙi ina so dakarun mu, su yi amfani da dabarun yaƙi guda biyu.
"Na farko, kada ɗaya daga cikinsu yayi kuskuren tunkarar ma'aboci Bankai, saboda yaƙi da ma'aboci Bankai tamkar yaƙi da duniya ne.
"Na biyu, a duk sa'adda yaƙi yafi ƙarfin mu, kada su yi tunanin guduwa, su jajirce lallai zamu kauda ma'abota Bankai daga wannan daula..."
Lokacin da Samudul Ansari yazo nan a zancensa sai suka ga wani mahayi ya shigo cikin wannan daula, dakarun sarauniya Arya mutum goma na kewaye da shi domin kada yayi wani motsi.
Samudul Ansari na ganin mahayin ya baiwa waɗannan dakaru dake kewaye dashi, umarnin tsayawa a can baya.
Dakarun suka bi wannan umarni, suka tsaitsaya a can baya, shi kuma mahayin ya ƙaraso gaban Samudul Ansari ya tsaya.
Ba tare da ya sauƙo daga dokinsa ya fiddo wata wasiƙa ya damƙawa ita Samudul Ansari sannan ya juya ya tafi.
Samudul Ansari ya koma kan karagar mulki ya zauna gefen sarauniya Arya.
Waɗannan dakaru da suka rako wannan manzo, suka take masa baya suka fice daga ckin wannan fada gaba ɗaya.
Mutanen dake cikin wannan fada suka matso gaban Samudul Ansari domin jin abinda wannan wasiƙa ta ƙunsa.
Samudul Ansari ya warware wannan wasiƙa a hankali sannan ya soma karanta abinda ke cikinta kamar haka:
"Wasiƙa daga sarki Mahrus Gorgon zuwa ga sarauniya Arya da ƙasƙantaccen jarumin dake tare da ita [Samudul Ansari]
"Ya ke wannan sarauniya ina mai farin cikin sanar dake cewa, duk gudunki ba za ki taɓa tserewa inuwarki ba.
"Mun yaƙi sauran sarakunan wannan daula yan-uwanki, mun sare kan kowanne daga cikinsu sannan mun tsire shi a fadarsa.
"Mun kafa tutocin mu a wannan daula, yanzu haka wannan daula tana ƙarƙashin ikon mu.
"Birnin ki ne kaɗai ya rage, shima muna shirye-shiryen zuwa mu mamaye shi.
"Tun da kin nuna mana, ke matsoraciya ce ba ki kasance jaruma ba, zamu ba ki zaɓi guda biyu waɗanda zasu jawo sulhu a tsakanin mu.
"Zaɓi na farko shi ne, ki sa a saro mana kanki, sannan a kawo mana kan naki har nan birnin tarayya, birnin Shaha.
"Zaɓi na biyu shi ne, ki sa a saro mana kan Samudul Ansari sannan ki kawo shi har wannan babban birni da hannuwanki sannan ki zube ƙasa a gabanmu, kiyi mubaya'a.
"Idan kika aikata ɗaya daga cikin waɗannan zaɓuɓɓuka, sulhu ya shiga tsakanin mu dake.
"Ƙin aikata ɗaya daga cikinsu kuwa, yana nufin janyo fushin mu wanda zai sa muyi gayya mu ruguza wannan birni naki gaba ɗaya.
"Wasiƙa daga sarakunan Gorgon masu burin sare kan Samudul Ansari..."
Samudul Ansari yana zuwa nan a karatun wannan wasiƙa, ya ɗago kansa ya dubi sarauniya Arya.
Maimakon a ga damuwa da razana a fuskar sarauniya Arya, kwata-kwata, babu.
Wani irin ƙwarin gwiwa ne da rashin tsoro akan fuskarta.
Zaka iya cewa sarauniya Arya tafi kowa sanin wane ne Samudul Ansari, saboda a gaban idanunta ya farkar da babban ruhi, sannan har zuwa wannan lokaci ita ce kaɗai tayi arba da wannan arba da babban ruhin ido-da-ido.
Indai har wannan ƙarfin iko da kamalar da taji a wannan lokaci gaskiya ne, to babu abinda zata yi shakka.
Samudul Ansari ya dube ta ya ce, "Ba zamu yi ko ɗaya daga cikin waɗannan zaɓuɓɓuka da suka bamu ba.
"Babu abinda ke tsakanin mu da ma'abota Bankai, idan ba kisa ba.
"Tabbas zamu kawo ƙarshen su..."
Samudul Ansari ya dubi sarkin yaƙin wannan birni ya ce, "Kaje ka haɗa kan dukkanin dakarun mu, su tafi bayan gari filin yaƙin Nayesh.
"Ku rubuta wasiƙar raddi, ku aikawa waɗannan sarakuna sannan ku sanar da su cewa, muna jiransu a wannan filin yaƙi na Nayesh!"
Samudul Ansari na zuwa nan a zancensa ya fice daga cikin wannan fada gaba ɗaya, Zarifa ta take masa baya.
Wannan sarkin yaƙi ya risina a gaban sarauniya Arya sannan ya tashi shima ya fice daga cikin fadar.
Bai tsaya a ko'ina ba, sai a tsakiyar sansaninsu wanda ke cike da mayaƙa maƙil.
Wasu suna wasa makaman yaƙinsu, wasu kuma suna ƙara baiwa kansu horo.
Gaba ɗaya dakarun ƙasar ba zasu wuce mutum dubu ɗari tara ba, amma bayan kammala wannan yaƙi wanda yayi sanadiyar rugujewar waɗannan garuruwa guda biyar, akwai mayaƙan da suka rugo cikin wannan birni suka sake haɗewa da wannan runduna.
Duka-duka dai, mayaƙan ba za su wuce mutum miliyan ɗaya da rabi ba.
Sarkin yaƙin na ƙarasowa ya tara dukkanin mayaƙan a waje guda, sannan ya sanar da su wannan umarni da Samudul Ansari ya sanar da shi.
Nan take mayaƙa suka tabbatar masa da cewa, zasu cika wannan umarni na zuwa filin yaƙin Nayesh domin tarar abokan gaba.
Sarkin yaƙin ya rubuta wasiƙa, sannan ya baiwa wani soja ya bashi umarnin kaita babban birnin tarayya na wannan daula - birnin Shaha.
Wannan soja ya karɓi wasiƙar sannan ya zaburi dokinsa da gudu ya nufi ƙasar.
***
Gauhan Ansari da wadannan sarakuna guda biyu suna zazzaune a cikin wani ƙaton falo suna tattaunawa akan yadda wannan yaƙi zai kasance, wani badakare ya shigo cikin falon ya sanar da su cewa ga can manzo daga garin Ilam.
Cikin gaggawa Gauhan da waɗannan

Please Login or Register in order to submit comment