Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙabilarsu ya gagara hallakawa a cikin daƙiƙu tamanin kacal.
Cikin tsananin fusata ta ja da baya, suka yi kallon-kallo da Aymanul Faris sannan ta sake rugowa kansa.
Saura ƙiris su haɗu ta daka tsalle sama, ta zaro idanunta tayi masa wani wawan kallo. Nan take wani irin farin haske mai kama da hayaƙi ya fito daga cikin idanunta yayi kan Aymanul Faris.
Saura ƙiris wannan haske ya taɓa Aymanul Faris wani aljanin-wuta ya bayyana a tsakani, ai kuwa hasken na taɓa shi ya sandare a wajen ya zamo gunki.
Cikin tsananin mamaki wannan budurwa ta kalli Aymanul Faris, domin shi ne mutum na farko da wannan mummunan hari bai yi tasiri akansa ba.
Cikin takaici ta sake afkawa Aymanul Faris da mummunan yaƙi, waɗannan macizai dake kanta suna ta wani irin ihu tamkar zasu ci babu. Lokaci-lokaci suna wangame bakunansu suna kaiwa Aymanul Faris sara amma basa samunsa saboda baƙin zafin namarsa.
Tun da Aymanul Faris yake gumurzu a duniya, bai taɓa fafata baƙin gumurzu kamar wanda yake fafatawa da wannan shaiɗaniya ba.
A hannunta akwai takobi, gashin kanta macizai ne, sannan idanuwanta ma kaɗai masifa ne domin zasu iya mayar da mutum gunki. Shi kuma babu abinda yake taƙama da shi face wannan takobi dake hannunsa da kuma zafin namar sa.
Koda aka sake nutsawa ana wannan yaƙi sai hankalin Aymanul Faris ya fara tashi. Idan ace ɗaya daga cikinsu ce take wahalar da shi haka, ya ya gumurzun zai kasance idan da dukkanin su uku yake fafatawa?
Aymanul Faris ya tuno cewa fa, a kowanne lokaci daga yanzu ƴan-uwan wannan shaiɗaniya zasu iya kawo mata ɗauki. Su haɗu su uku su hallaka shi. Saboda wannan dalili ya fara shawarar abinda ya kamata ya yi.
A wannan lokaci Ileisha ta gama fusata iya fusata, jikinta ya fara komawa kore-kore yana ɗaukar samfurin maciji.
Ta cizgo silin gashi guda uku daga cikin gashin kanta ta jefowa Aymanul Faris su. Nan take gashin nata suka soma rikiɗewa suna komawa manya-manyan macizai.
Suka tunkaro Aymanul Faris da gudu da nufin su sare shi. Aymanul Faris ya zaro takobinsa ya yi tsalle ya fille kawunan waɗannan macizai da kaifin takobinsa.
A tare kawunan nasu suka tashi sama sannan suka faɗo gaban Ileisha Gorgon. Koda taga dungulmayen kawunansu sai ta rintse idanunta ta fara ƙwala wani irin ihu mara daɗin ji, wanda yake cika dukkan wannan lambu da amsa kuwwa.
Aymanul Faris na ganin haka ya fara shawarar guduwa, domin ga dukkan alamu wannan budurwa ƙoƙari take ta kirawo ƴan uwanta.
Ai kuwa, ba'a ɗauki lokaci ba, yan mata guda biyu suka fito daga cikin wani ɗaki suka rugo inda wannan budurwa Ileisha ke tsaye.
Ƴan matan sun fi Ileisha Gorgon kwarjini da cika ido da kuma ban tsoro. Idanuwansu tsaye cak akan gawarwakin waɗannan macizai da Aymanul Faris ya kashe.
Kafun su ƙaraso wannan wuri, aljani Nara ya bayyana a gaban Aymanul Faris ya caka hannayensa a cikin ƙasa, wani wawakeken rami ya bayyana. Aljani Nara ya busa wuta cikin wannan rami daga bakinsa.
Nan take gagarumar wuta mai tsananin zafi da tartsatsi ta soma fantsama a cikin wannan ƙaton wannan rami, tana yin sama tana ƙasa, tana biyayya a gaban aljanin wuta.
Aljani Nara ya kamo Aymanul Faris ya goya shi a gadon bayansa sannan ya daka tsalle ya faɗa cikin wannan ƙaton wanda ke cike maƙil da wuta.
Gangar jikinsa tana faɗawa cikin wannan rami ta saje da kalar wutar dake cikin ramin, ya ɓace ɓat a cikinta.
Ileisha Gorgon ta dubi yan-uwanta ta fashe da kuka ta ce, "Ku duba fa ku gani, sun zo har gidanmu, sun kashe mana ƴaƴa sannan sun saci furannin da baba ya shuka."
Suna jin haka suka murtuƙe fuska suka kewaye Ileisha a tsakiya suka ce, "Amma dai kin ji kunya, bil'adama zasu shigo hannunki su gudu? Tabbas inda ace baba yana raye da ba zaiyi alfahari dake ba."
Suna gama faɗin haka suka koma cikin wannan ɗaki nasu, suka bar Ileisha Gorgon durƙushe akan gwiwowinta tana ta rusa kuka.
"Na rantse da kabarin mahaifina sai na farauto wannan jarumi, na hallaka shi. Komai daren-daɗewa kuwa." Wannan shi ne alwashin da Ileisha Gorgon ta ɗauka na kawar da Aymanul Faris.
Sa'adda wannan wuta da Nara ya haddasa ta ɗauki rabin sa'a tana ci, sai wani jan hayaƙi ya soma tashi daga cikinta yana shigewa cikin sararin samaniya.
Hayaƙin na gama shigewa cikin sararin samaniya ya soma gudu, ya bar yankin wannan daji gaba ɗaya. Gudun da wannan hayaƙi yake mai ban al'ajabi ne.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya shafe tafiya mai tsahon gaske ya sauƙa akan wani faffaɗan dutse mai ƙaton kogon dutse bisa kansa.
Abin mamaki wannan hayaƙi na sauƙowa bisa wannan dutse, siffar aljani Nara da Aymanul Faris ta fara bayyana a cikinsa.
Jim kaɗan aljani Nara da Aymanul Faris suka bayyana a saman wannan dutse a ƙofar shiga wannan kogo.
"Aiki mai kyau," inji Aymanul Faris.
Aljani Nara ya yi murmushi ya ce, "Babban jarumi tabbas kayi ƙoƙari da ka iya yaƙar waɗannan halittu kuma basu yi nasara akan ka ba. Kayi sani cewa shi kansa Samudul Ansari abinda yasa yayi nasara akansu shi ne, da wata zabgegiyar takobi yayi amfani ya yaƙe su."
Cikin tsananin mamaki Aymanul Faris ya dubi Nara ya ce, "Shin kana nufin kace bayan wannan takobi dake hannuna, maigirma Samudu yana amfani da wata takobi?"
Aljani Nara ya ce, "Kwarai ma kuwa. Ai wannan takobi dake hannunka zata taimaka maka ne kawai a yayin da kake ƙoƙarin mallakar wannan ruhi, a duk lokacin da aka ce wannan ruhi ya shiga jikinka, bata da sauran amfani. Zaka samu gawurtacciyar takobi wadda a zamanin da aka kusa yin yaƙin duniya dominta."
Aljani Nara yana gama faɗin haka ya shiga cikin wannan kogon dutse, Aymanul Faris ya ƙarewa wajen kallo sannan shima ya kunna kai izuwa cikin wannan kogon dutse.
Yana shigowa cikin kogon dutsen ya hango waɗannan aljanu nasa guda huɗu da yasa su ɗauki Riya su tafi da ita, zazzaune sun kewaye Riya a tsakiya a wani salo na bayar da kariya.
Jaruma Riya tana hango masoyinta ta rugo da gudu, ta rungume Aymanul Faris a ƙirjinta sannan ta sumbace shi ta ce, "Barkan mu da kuɓuta daga hallaka. Koda na tsahon daƙiƙa guda hankalina bai kwanta ba, saboda banga dawowarka ba."
Aymanul Faris ya yi murmushi ya janye jikinsa daga nata ya ce, "To ai gani na dawo ko?" Riya ta gyaɗa kai.
Aymanul Faris ya dubi Nara ya ce, "Yanzu tayaya zamu koma fadar sarki Ranganu domin gabatar masa da waɗannan furannin?"
Aljani Nara yana shirin bashi amsa kenan, siffar Barban cikin haske ta bayyana a wannan wuri ta dafa su gaba ɗaya suka ɓace ɓat.
****
Yau *14/01/2023*
Babi na gaba zaizo *16/01/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 72: *Kwarin Jekish (1)*
*
DEDICATED TO ZAHRA.
*
U*M*S
*
~Ɓangaren sarki Kuffuru.
*
Sarki Kuffuru na fitowa daga cikin wannan tanti da suka gama tattaunawa da su boka Hubbazu, ya kirawo sarki Darwazu da sarauniya Rauziyya gefe guda, ya sanar dasu cewa sun gama dukkanin shirye-shirye a wannan lokaci zasu ci gaba da tafiya.
Sarki Darwazu da sarauniya Rauziyya suka amince da wannan shawara ta sarki Kuffuru, basu ɗau wani lokaci ba suka gama kimtsawa dukkaninsu. Sarki Kuffuru ya ce a bar komai kamar yadda yake a wannan sansani, saboda akwai baƙin da zasu zo bada daɗewa ba.
Ba tare da sake ɓata lokacin komai ba, aljani Zuwa ya ranƙwafa dukkaninsu suka haye gadon bayansa. Ya yunƙura cikin taƙama da ƙarfi ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi dasu sama cikin iska sannan ya fara tsala azababben gudu ya tunkari yankin Dilikem inda kwarin Jekish yake.
Sarki Kuffuru ya yi shuru akan wannan aljani, ya sunkuyar da kansa ƙasa yana tunani. Wanne irin shiri yarima Marganu yake yi masa? Meye zai faru idan sarki Ayubu ya samu nasara akan mutum-mutumin da ya bari? A halin yanzu ina Barban da Aymanul Faris waɗanne irin mugun tanadi suke yi masa tunda sun mallaki takobin da shuwaganninsu suke taƙama da ita?
Waɗannan su ne abinda sarki Kuffuru yake ta tunani a cikin ransa. Sarki Darwazu ne kawai ya lura da wannan hali da sarki Kuffuru ke ciki. Don haka sai ya dafa kafaɗarsa ya ce, "Ya shugabana, mene ne abinda ke damunka naga ka zauna kayi shuru?"
Sarki Kuffuru ya ɗago kansa ya ce, "Babu komai, kawai ina tunanin ƴata ce." Sarki Darwazu ya gyaɗa kai sannan ya ci gaba da kallon hanya.
Tsahon kwanaki uku suna ta tafiya akan wannan aljani cikin sararin samaniya, ko sau ɗaya basu yada zango ba. A cikin waɗannan kwanaki kullum sarki Kuffuru a cikin mummunan tunani yake.
Shi kansa sai da ya cika da tsananin mamaki kuma zuciyarsa ta fara raya masa anƴa babu wani mummunan abu dake faruwa kuwa?
A ranar kwana na uku da yammaci ne, ba zato suka ga sarauniya Rauziyya ta yanki jiki ta faɗi daga kan wannan aljani. Ba don sun riƙota da sauri ba, da tuni ta faɗo ƙasa.
Idanuwanta suka rufe ruf, jikinta ya daina motsi tamkar wacce ta suma.
Boka Hubbazu ya samar da ruwan sihiri mai sanyi ya soma yayyafa mata, tsahon lokaci amma bata farfaɗo ba.
Sarki Darwazu ya soma yi mata fifita amma duk a banza bata farfaɗo daga wannan suma ba. Shi ko sarki Kuffuru yana zaune a gefe, yana ta nazarin wannan hali da ta shiga.
Sai da aka ɗauki rabin sa'a ana ta abu ɗaya, sarauniya Rauziyya ta ƙi farfaɗowa daga wannan suma da tayi.
Har su sarki Kuffuru sun fara shawara domin sauƙa a wani daji domin duba halin da ta shiga. Ba zato aka ji tayi attishawa sau uku, sannan ta buɗe idanunta ta kalle su.
Sarki Darwazu ya matso kusa da ita ya ce, "Ya ke uwar matsafa, mene ne abinda ya faru gareki, lokaci guda muka ga kin suma?"
Cikin kaɗuwa da razana sarauniya Rauziyya ta dube su ɗaya bayan ɗaya ta ce, "Tabbas ba zan iya ci gaba da wannan tafiya ba, saboda an nuna min wani mummunan abu a cikin wannan suma da nayi. Tun da ba daga wannan lokaci amfanina a wannan tafiya zai fara ba, ina so kuyi min alfarma naje na kawar da wani abu mai muhimmanci.
"Nayi muku alƙawari zan dawo a duk lokacin da na gama kawar da wannan uzuri."
Koda su sarki Kuffuru suka ji wannan kalamai na sarauniya Rauziyya sai hankalinsu ya ɗugunzuma. Basu san wanne uzuri ne zata tafi aiwatarwa ba, idan yaƙi ne fa, wanda ya janyo aka kasheta ko kuma aka illata ta. Lallai tafiyar sarauniya Rauziyya a wannan hali da suke ciki, ba zata haifar musu ɗa mai ido ba.
Sarki Kuffuru ya fara wasu-wasin anya ba kuɓutar Marganu aka nuna mata ba kuwa.
Boka Hubbazu ya dubeta cikin nutsuwa ya ce, "Haba uwar-matsafa. Wanne uzuri ne zai taso miki wanda zai hanaki wannan tafiya da muke mai muhimmanci? Kiyi sani cewa a duk lokacin da muka kai ƙarshe, za ki samu babban alheri."
Rauziyya tayi murmushin takaici ta ce, "Abin bautana, ya sanar dani cewa bai samu jinin da yake buƙata ba, wato jinin yarima Marganu. Sannan ya sanar dani cewa Marganu na nan a raye, sa'adda aka zo yanka masa jininsa akwai waɗanda suka zo suka cece shi.
"Tun ina yarinƴa ƙarama zuwa girma na, mai girma Barzas bai taɓa bani umarni na ƙi cikawa ba. Tabbas a yanzu ya zamo wajibi a gareni, na farauto Marganu a duk inda yake a faɗin duniya naje gaban wannan gunki namu na yanka shi!"
Boka Hubbazu ya dafa kafaɗarta ya ce, "Haba uwar matsafa. Ni na ɗauka wani mummunan abu ne har hankalina ya soma tashi. Marganu da mahaifinsa nawa suke gaba ɗaya? Ki kwantar da hankalinki zanyi mana maganin wannan taƙadarin jarumi a lokaci na ƙarshe."
Cikin rashin fahimta Rauziyya ta ce, "Ban gane abinda kake nufi ba?"
Boka Hubbazu ya sake dubanta cikin nutsuwa ya ce, "Marganu baya taƙama da komai face sa'a da ƙarfin damtse. Kiyi sani cewa sa'adda kike daf da hallaka shi, a lokacin da yayi miki wannan muguwar ɓarna a birninki, sa'a ce kawai ta ƙwace shi.
"Tun kafun ki gano cewa Marganu yana raye, ni na rigaki ganowa. Kuma tuni na riga nayi maganinsa. Ina mai tabbatar miki da cewa, kafun mu ɗebo wannan tubali za'a kamo Marganu a kawo mana shi har wannan wuri da muke. Daga wannan lokaci zamu yi miki uzuri, ki koma ƙasarki ki yanka shi sannan ki dawo."
Sarauniya Rauziyya ta ƙurawa boka Hubbazu idanu tsahon lokaci, kafun daga bisani ta haɗe fuska ta ce, "Ta ya ya zan yarda da abinda kake cewa?"
Kafun boka Hubbazu ya ce wani abu, sarki Kuffuru ya dubeta ya ce, "Na turawa yarima Marganu Infiro guda ɗaya wanda nake da tabbaci akan zai sami nasara akansa."
Sarauniya Rauziyya tayi shuru ta faɗa kogin tunani mai zurfi. Daga bisani ta amince akan hadimin sarki Kuffuru zai kamo Marganu ya kawo mata shi.
Daga wannan lokaci suka ci gaba da tafiya a sararin samaniya, babu dare ba rana. Ba sa yada zango face ƙarshen wata ko kuma wata lalura ta musamman har tsahon watanni takwas.
Lokacin ne suka iso cikin wani irin yanki mai mugun yanayi na zafi. Babu hazo ko gajimare, rana ta ƙwale a sararin samaniya tamkar zata gasa halittun dake ƙasa.
Aljani Sheezuwa ya saki fuka-fukinsa ƙasa ya dira a tsakiyar wani gabjejen daji mai yawan sahara. Yana sauƙowa ya baiwa su sarki Kuffuru umarnin sauƙowa daga kansa.
Suna sauƙa ya dube su ya ce, "To, kamar yadda kuka ji yanayi ya sauya. Wannan yana nuni da cewa mun iso yankin dake tsakanin Auzur da Dilikem inda ƙwarin Jekish yake.
"Tun kafun mu fito wannan tafiya na sanar da ku cewa, akan hanƴar zuwa wannan wuri babu abin hatsari ko guda ɗaya, kuma kun ga haka. Sannan na sanar da ku cewa, babu wanda ya san bala'in dake cikin wannan ƙwari na Jekish domin babu wanda ya taɓa shiga ya fito da ransa.
"Bisa wannan dalili ne, naga ya kamata mu sauƙa a cikin wannan daji domin naje ni ɗaya nayi shawaƙi a saman wannan ƙwari, wataƙila ko na iya kallo mana wani abu, domin mu san irin shirin da zamu yi.
"Sanin abinda zaka tunkara a yaƙi yafi rashin saninsa. Ko ya kuka ce?"
Gaba daya su sarki Kuffuru suka amsa da cewa, lallai ka kawo shawara mai kyau.
Aljani Sheezuwa yayi sallama da ubangidansa sannan ya buɗe fuka-fukinsa ya lulluƙa a cikin gajimare ya ɓace ɓat.
Sarki Kuffuru, sarki Darwazu, boka Hubbazu da sarauniya Rauziyya suka kafa tanti a tsakiyar wannan sahara sannan suka shige cikinta, suka fiddo abinci suka fara ci.
Sarauniya Rauziyya ta dubi Hubbazu ta ce, "Yaushe ne wannan hadimi da kuka aika ya kamo Marganu zai dawo? Kuyi sani cewa watannin mu kusan takwas fa muna tafiya, wai shin har a wanne wuri zaije yayi farautar Marganun?"
Koda jin wannan tambaya sai boka Hubbazu yayi murmushi ya ce, "Ki kwantar da hankalin ki kuma kada ki samu damuwa. Kiyi sani cewa Marganu da kika sani na da ne, a halin yanzu Marganu bijimin sadauki ne wanda tunkararsa sai cikakken shiryayye.
"Marganu ya fara gadon sirrukan tsafin mahaifinsa saboda haka kama shi ba abu ne mai sauƙi ba." Yana gama faɗin haka ya ci gaba da cin naman dake gabansa.
Sarauniya Rauziyya ta murtuƙe fuska ta ce, "Tabbas idan wannan hadimi da kuka aika, ya gagara kamo Marganu babu abinda zai hanani tafiya da kaina domin kamo shi."
A hasale sarki Kuffuru ya dube ta ya ce, "Wai shin kin raina ƙarfin shirin mu ne? Kada ki manta mu ne muka kamo Marganu da hannunmu sannan muka damƙa shi a hannunki. Mahaifin Marganu kansa ma, yaronmu ne ballantana kuma ɗansa. Duk abinda Marganu zai zamo a duniya bai wuce matsayin ƙaramin ƙwaro a wajen mu ba.
"Ki sani cewa idan har hadimin da muka aika ya kamo Marganu ya gagara, tofa kema ba za ki iya kama shi ba..." Sarki Kuffuru ya ƙarasa maganarsa ƙasa-ƙasa.
Sarauniya Rauziyya ta fusata tana shirin tasowa kan Kuffuru kenan, sarki Darwazu ya riƙota ya ce, "Haba uwar matsafa! Kada maganar ƙaramin jarumi ta sa ki warware alƙawarin da muka ƙulla mana."
Sarki Darwazu ɗan ƙabilar Adbenchan ne, mutanen ƙabilar sarauniya Rauziyya suna shakkarsu ba kaɗan ba. Wannan magana da Darwazu ya faɗa mata sai ta dawo hayyacinta.
Sarki Kuffuru ya kishingiɗa a cikin wannan tanti ya fiddo madubin tsafinsa ya shafe shi da hannun hagu, madubin tsafin yayi haske sannan ya fara nuno abubuwan da ke faruwa a birnin Kufa.
Wannan sadauki mai kama da sarki Kuffuru sak, aka nuno zaune akan karagar mulki yasha alkyabba. Idan ka gan shi sai ka rantse kace sarki Kuffuru ne saboda babu abinda ya bambanta su.
Mutumin na tafiyar da harkokin mulki kamar sarki Kuffuru, idan mutum bai sani ba sai ya ce sarki Kuffuru ne kawai a wannan birni.
Babban abinda ya damu sarki Kuffuru shi ne ko sau ɗaya ba'a nuno masa ƴarsa Firziyya ba. Hakanne yasa ya fara wasu-wasi akan cewa ina wannan ƴa tasa ta shiga.
Tabbas yayi babban kuskure da ya fito wannan tafiya, ba tare da ya tsaurara matakan tsaro akanta ba.
Ko kaɗan hankalin sarki Kuffuru bai kai akan cewa zata iya haɗa kai da yarima Marganu ba. Abinda ya raya a ransa shi ne wani wajen dabam kawai taje domin taga baya nan.
To, amma idan baya nan ai wannan hadimi da ya tura yana matuƙar kama da shi, kuma zaiyi wuya ace Firziyya ta gano cewa ba ainihin shi ɗin bane tunda komai da komai nasu yana kama hatta yadda suke tafiyar da mulki kuwa.
Koda yaga cewa irin binciken akan irin waɗannan abubuwa zai iya haifar masa da damuwa, sai ya kashe madubin tsafin sannan ya mayar da shi cikin aljihunsa sannan ya tashi ya fice daga cikin wannan tanti.
Boka Hubbazu na ganin ya fita ya miƙe tsaye ya biyo bayansa da sauri.
Sarki Kuffuru na fitowa daga wannan tanti ya fara tafiya a cikin wannan sahara, ba tare da sanin inda ya dosa ba. Bai yi nisa sosai ba, ya hango wani baƙin abu na tahowa daga sama da gudu.
Cikin shirin ko-ta-kwana sarki Kuffuru ya zaro takobinsa ya riƙeta da hannu biyu, abin ya ci gaba da matsowa a hankali.
Jim kaɗan wani shirgegen mutum ya faɗo gaban sarki Kuffuru a galabaice. Mutumin yana sanƴe da baƙaƙen tufafi waɗanda idan sarki Kuffuru zai tuna irinsu ne a jikin sadaukan da ya baiwa aiki a watannin baya wato Infirons.
Sarki Kuffuru na ganin fuskar wannan sadauki ya shaida shi domin kuwa mai kama da shi ne.
Ganin wannan sadauki a galabaice yasa hantar cikin sarki Kuffuru ta kaɗa domin kuwa baisan wanne daga cikinsu bane.
Idan wanda ya aikawa Marganu ne fa, ace Marganu ya samu nasarar jifa da shi. Matsaloli guda biyu zasu faru, Marganu na raye sannan sarauniya Rauziyya zata tafi ta barsu.
A fusace sarki Kuffuru ya dakawa sadaukin tsawa ya ce, "Kai kuma daga ina?!"
Sadaukin ya cire hular sanyin dake kansa ya zube ƙasa gaban sarki Kuffuru ya ce, "Ni ne wanda aka baiwa alhakin kula da sarki Ayubu, haƙiƙa na fafata ƙazamin yaƙi da wannan sarki amma ga dukkan alamu tun kafun mu fara wannan yaƙi ya riga ya gano ni. Saboda takura min yayi da abubuwan da na bana so, har ya sa na kirawo ɗalasimin tsafinmu wanda ya sa guguwa mai ƙarfi tayi jifa dani da shi."
Cikin tsananin fusata sarki Kuffuru yasa takobinsa ya fille kan wannan sadauki yana cewa, "Zancen banza kenan, duk wannan ƙarfi naka ace sarki Ayubu ya gagareka hallakawa?"
Takobin sarki Kuffuru na taɓa wuyan sadaukin ya juye izuwa haske, sannan ya shige cikinta.
A lokacin ne boka Hubbazu ya ƙaraso wurin da yake tsaye a guje, ya tambaye shi abinda ya faru.
Sarki Kuffuru ya harare shi, sannan ya kwashe komai ya zayyane masa. Boka Hubbazu ya gudanar da gajeruwar tsatsuba daga bisani ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "Sarki Ayubu ya hallaka!"
"Kamar ya kenan?" inji sarki Kuffuru. "Ba ka ji labarin da na faɗa maka bane?"
Boka Hubbazu ya ce, "Sarki Ayubu da ɓataccen aljaninsa sunyi shiri akan wannan jifa da hadiminka zaiyi zai kaisu wani wuri ƙasaitacce a duniya. Wuraren guda huɗu ne; birnin Hereza, tsaunin Rawas, dajin fatalwa da tekun TAURON SI.
"Dukkanin waɗannan wajaje guda huɗu masu mugun haɗari ne, kuskuren sarki Ayubu guda ɗaya zai iya sa wa ya rasa rayuwarsa gaba ɗaya.
"Amma dukda haka ka tura wannan hadimi naka da ya dawo, yaje waɗannan wajaje guda huɗu ya dubo halin da sarki Ayubu yake. Idan ya mutu ya kawo mana gawarsa, idan kuwa yana da sauran rai ya ƙarasa shi."
Cikin amincewa sarki Kuffuru ya gyaɗa sannan ya sake fiddo wannan hadimi ya bashi wannan umarni.
"Mene ne dalilin da yasa har yanzu wanda muka tura wajen Marganu bai dawo ba?" sarki Kuffuru ya tambayi Hubbazu.
Boka Hubbazu ya nemi waje ya zauna a cikin wannan sahara sannan ya ce, "Kamar yadda na faɗawa Rauziyya a ɗazu, Marganun da muka sani na da ne. A yanzu Marganu cikakken matsafi ne.
"Kamar yadda kake taƙama da aljani Djinn, haka shima yake taƙama da aljani Isika wanda mahaifinsa ya riga ya sadaukar masa."
Cikin tsananin mamaki sarki Kuffuru ya zaro idanu ya ce, "Marganu ya mallaki aljani Isika? Lallai idan ban takawa Marganu birki ba, nan gaba zai zamo min ciwon ido."
Boka Hubbazu ya ce, "Shi ne dalilin da yasa kaga har yanzu wannan hadimi bai dawo ba. Wataƙila fafatawa suke tayi da Marganu wataƙila kuma har yanzu bai gano ainihin inda Marganu yake ba."
Cikin takaici sarki Kuffuru ya ce, "Ina fatan a komawarmu ba zamu ɓata lokacin da muka yi yanzu ba, saboda ayyukan da suke gabana suna da yawa."
Boka Hubbazu ya ce, "Akwai babban sirri a jikin Infirons, lallai ina da tabbaci akan cewa wanda muka aikawa Marganu sai yaga bayansa. Mu jira kawai na san har nan za'a kawo mana gawar Marganu."
Boka Hubbazu na zuwa nan a zancensa suka hango aljani Sheezuwa ya sauƙa a tsakiyar wannan daji. Cikin tsananin sauri suka ruga inda yake, sannan suka ƙwalawa su sarauniya Rauziyya kira.
Dukkaninsu su huɗu suka ƙarasa inda wannan aljani ke durƙushe, sai dai suna zuwa suka iske aljanin yana ta aman jini.
Ga wani abu ƙato mai kama da farcen tsuntsu cake a gefen ƙirjinsa, jini yana ta malalowa daga wajen.
Aljani Sheezuwa ya bingire a ƙasa yana kakarin mutuwa, sarki Kuffuru da sarki Darwazu suka yi hanzari suka zaro wannan abu da ya lume a ƙirjinsa.
Boka Hubbazu da sarauniya Rauziyya kuwa, suka haɗa masa magani da ƙarfin sihiri suka bashi yasha, sannan suka yayyafawa wannan rauni dake kan ƙirjinsa.
Jini ya daina zubowa sannan wannan rauni ya haɗe. Bayan dogon lokaci aljani Sheezuwa ya dawo hayyacinsa.
Boka Hubbazu ya dube ya ce, "Ya kai Zuwa. Mene ne abinda ya faru gare ka?
Aljani Sheezuwa ya ce, "Ya shugabana haƙiƙa tawa ta ƙare. Iya daɗewar da zanyi a duniya

Please Login or Register in order to submit comment