Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

doki ƙasa da ƙarfi.
Har a wannan lokaci sarauniya Arya bata farfaɗo daga wannan suma da tayi ba.
Tsahon daƙiƙa sittin kacal Samudul Ansari yana hutawa, ya fara jiwo ƙarar busa ƙaho daga can saman wannan tsauni.
Ga dukkan alamu wannan mayaƙi ne, wanda ya jeho sarauniya Arya yake ƙoƙarin kirawo dakarun ƙasar.
Samudul Ansari yana jin haka, ya goya sarauniya Arya akan kafaɗarsa sannan ya fara gudu yana neman hanyar da zai fita daga wannan daula gaba ɗaya.
Tabbas sanin da suka yiwa ƙabilar Gorgon kaɗan ne.
Idan ace ma'abota Bankai (mataki na biyar da mataki na shida) ne suka wahalar da su haka, ya ya abin zai kasance idan suka haɗu da mai mataki na goma ko ma fiye?
Jim kaɗan da fara busa wannan ƙaho, mutane guda dubu ɗaya suka bayyana.
Kowanne daga cikinsu na rataye da takobin Bankai mai mataki na tara.
Waɗannan mutane su ne masu tsaron wannan tsauni, a duk lokacin da aka kawowa tsaunin hari, su ne masu kare shi.
Wannan yasa aka basu Bankai mai mataki na tara.
A dai-dai lokacin ne Samudul Ansari ya iso bakin wani ƙaramin tafki wanda ruwansa yake faɗawa cikin wani ƙaton rami.
Samudul Ansari ya kalli wata tsohuwar ƙaramar kwale-kwale wurge acan nesa kaɗan da tafkin.
Cikin sauri ya ɗauko wannan kwale-kwale ya saka ta a cikin wannan ruwa, sannan ya shiga cikinta ya saka sarauniya Arya a gefensa ya kwantar da ita.
Ya tura kwale-kwalen gaba a cikin wannan ruwa, sannan ta fara tafiya ta tunkari wannan ƙaton rami wanda mutum ko hauka ke damunsa ba zai yi tunanin faɗawa ba.
A daidai lokacin ne mayaƙa ma'abota Bankai guda tara suka ƙaraso wannan wuri.
Koda suka ga Samudul Ansari ya tsere sai ransu ya ɓaci, biyu daga cikinsu suka zare takubbansu, suka sari wannan ruwa da su.
Nan take waɗansu korayen macizai manya, suka shiga cikin wannan ruwa suka bi bayan Samudul Ansari da gudu.
Samudul Ansari na ganin haka, ya ƙarawa kwale-kwalen nan gudu. Kafun macizan su iso inda yake, tuni wannan kwale-kwale ta faɗa cikin wannan wawakeken rami.
Samudul Ansari ya kwanta akan sarauniya Arya sannan ya baje hannayensa ya kamo ƙarshe da ƙarshen wannan kwale-kwale, kada iska tayi jifa dasu; shi da Arya.
Kusan rabin sa'a suna faɗawa cikin wannan rami sannan suka faɗo cikin wani ƙaton teku mai girma da faɗin gaske.
Ko'ina ka duba ruwa ne, babu ko alamar ƙasa balle mutum yayi tunanin samun abinci.
Samudul Ansari ya tashi zaune ya ci gaba da tuƙa wannan kwale-kwale ya nausa cikin wannan teku, ba tare da ya san inda ya dosa ba ma.
Yana tafe yana takaicin rashin samun nasarar da suka yi. Musamman ma, idan ya tuna da cewa, wannan annoba fa zata ci gaba da hallakar da mutanensu ne.
Sai yaji kamar ya juya da baya ya koma amma sai zuciyarsa ta gargaɗe shi.
Gwabza yaƙi da ma'abota Bankai guda dubu, gwara mutum ya zare takobi ya ce zai yaƙi duniya gaba ɗaya.
Sannu-sannu Samudul Ansari yana tafe bisa wannan teku, ya soma hango wani baƙin abu a cikin duhun hazon wannan teku.
Ya ci gaba da matsawa kusa da baƙin abun, inda ya fuskanci cewa, ashe ƙatoton jirgin ruwa ne irin wanda tun da yake bai taɓa kallon irinsa ba.
Koda Samudul Ansari ya yi arba da wannan jirgi sai farin ciki ya lulluɓe shi, ya miƙe tsaye ya fara ƙwalawa na cikin jirgin ihu.
A daidai lokacin ne sarauniya Arya ta farfaɗo daga wannan suma da tayi, har a wannan lokaci babu kaya a jikinta.
Lokacin ne Samudul Ansari ya samu ya yiwa kyakkyawan jikinta kallo mai kyau.
Arya mace ce ta gaban kwatance, bayan baiwar kyawun fuska, surarta ta ya mace tana da tsananin kyawu da ɗimauta tunanin mutum.
Samudul Ansari ya yi sauri ya kawar da idanunsa daga kanta saboda wata kunya da ta rufe shi.
Ya cire doguwar rigar dake jikinsa ya bata ta saka, ya rage daga shi sai gajeren wando wanda ya tsaya iya cinyoyinsa kawai.
Samudul Ansari mutum ne dogo amma baida ƙiba sosai. Jikinsa a cike yake da ƙwanji tamkar jera masa su akayi.
Zaratan hannayensa na ɗauke da jijiyoyi masu nuna alamun ƙarfin damtse na gaban misali.
Wannan ƙatuwar jirgin ruwa dake gabansu ta tsaya, wani dogon mutum ya fito wanda zaiyi biyun Samudul Ansari a tsaho ya fito daga cikinta ya tsaya.
Idanuwan mutumin ruwan ɗorawa ne, sannan a goshinsa akwai ƙaho guda biyu waɗanda suka kwanta akan kansa tamkar gashi.
Yana sanye da sulken yaƙi mai tambarin masarauta.
Kwale-kwalen Samudul Ansari ta ƙarasa jikin wannan ƙaton jirgin ruwa a hankali.
Wannan mayaƙi ya nuna musu wani tsani ya ce, su hawo kan wannan jirgin ruwa.
Samudul Ansari da sarauniya Arya suka kama wannan tsani, suka shigo cikin jirgin ruwan.
Wannan badakare mai sulken masarauta ya ƙare musu kallo, sannan ya ce.
"Sarki yana buƙatar kallon ku..."
Yana gama faɗin haka, ya buɗe wata ƙofa a jikin wannan jirgin ruwa wanda ya fito daga cikinta ya shige ciki yana mai yafito su Samudul Ansari.
Samudul Ansari da sarauniya Arya suka dubi junansu.
"Mu je ciki muga wane ne wannan sarki, ga dukkan alamu bada cutarwa suka zo ba..." inji Samudul Ansari.
Yana faɗin haka ya shige cikin wannan ƙaton jirgin ruwa, sarauniya Arya ta take masa baya. Tana so tayi masa tambaya akan yadda suka tsira daga saman wannan tsauni da kuma yadda ya ceci rayuwarta sa'adda take faɗowa daga saman tsaunin.
***
Yau *25/02/2023*
Babi na gaba zaizo *27/02/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 90: *Sarauniya Yilan*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
SADAUKARWA GA MASOYA...

*
U * M * S
*
Samudul Ansari da sarauniya Arya suna shigowa cikin wannan jirgi, suka tsinci kansu a tsakiyar wani waje ƙato tamkar tsakiyar wani gari.
Haƙiƙa wannan jirgin ruwa ƙaton gaske ne. Akwai gidaje ƙanana, shagunan kasuwa, wuraren wasanni, kai har wajen horon yaƙi akwai.
Mutane suna ta harkokinsu a cikin wannan jirgi tamkar ba a tsakiyar teku suke ba. Kai ka ce a cikin garinsu suke.
Amma sai dai duk inda mutum ya duba zai yi arba da dakaru birjik suna bayar da tsaro. Mafi yawancin dakarun irin wannan sulke na wannan mayaƙi ne a jikinsu.
Abinda ya baiwa Samudul Ansari da sarauniya Arya mamaki shi ne, gaba ɗaya mutanen dake cikin wannan jirgi irin gashin wannan mutumi ne dasu.
Wato akan kowa akwai ƙaho guda biyu waɗanda suka kwanta akan kan nasu tamkar gashi.
Tun da suka shigo cikin wannan jirgi aka ƙura musu idanu, babu wanda ya ce dasu uffan.
Wannan mayaƙi ya ci gaba da yi musu jagoranci suna nausawa cikin wannan jirgi.
Saboda girman wannan jirgi sai da suka shafe rabin sa'a suna tafiya a cikinsa sannan suka iso ƙarshen jirgin inda aka gina wani ƙaton ɗaki da zallar dutsen zinari.
Waɗansu mayaƙa guda biyu na tsaye a ƙofar wannan ɗaki suna gadi.
Mayaƙin da ya yiwa su Samudul Ansari jagora yaje wajen waɗannan mayaƙa suka yi kus-kus, kafun daga bisani su buɗe ƙofar shiga.
Mayaƙin ya juyo ya dubi Samudul Ansari da sarauniya Arya ya ce, "Ku zo ku shiga inda sarki yake, nima nan ne iyakata..."
Samudul Ansari ya kama hannun sarauniya Arya suka shige ta cikin wannan ƙofa, masu gadin suka mayar da ita suka rufe.
Suna shigowa suka tsinci kansu a tsakiyar wani wuri mai tsananin kyawu wanda aka ƙawatawa sosai da sosai.
A can ƙarshen wurin, suka hango wani mutum zaune akan wata ƙatuwar karaga ta mulki.
Mutumin dogo ne sosai, domin da wuya a samu mai tsahonsa a duk jama'ar dake cikin wannan jirgi.
Ƙahon dake kansa ba guda biyu bane kamar na kowa, ƙaho guda ɗaya ne wanda ke haske da sheƙi tamkar hular sarauta.
Ganinsa kaɗai yana sakawa mutane kwarjini, dukda cewa shiga yayi irinta sarauta mai nuna ado, ba shigar yaƙi ba.
Sarauniya Arya ta ɗan koma bayan Samudul Ansari ta tsaya saboda ba zata iya tsayawa a gaban kwarjinin wannan basarake ba.
Kai tsaye Samudul Ansari ya tunkari wannan karaga wadda sarkin ke zaune akanta, da nufin yana isowa gaban sarkin zai faɗi ya kwashi gaisuwa.
Basaraken na fuskantar haka, ya dakatar da Samudul Ansari da hannu sannan ya nuna masa wajen zama.
Shi da Arya suka ƙarasa kan wasu kujeru na alfarma suka zauna a gefen karagar wannan sarki.
"Shin zamu iya sanin wane ne kai? da kuma dalilin da yasa kasa aka kirawo mu?" inji Samudul Ansari cikin sanyin murya.
Wannan basarake yayi murmushi mai nuna ƙarfin ikonsa ya ce, "Ba za ku san wane ne ni ba! Sannan faɗa muku wane ne ni a yanzu baida wani amfani...
"Zan isar muku da saƙonnin da suka sa na shigo wannan duniya da kaina, sannan na baku maganin wannan cuta da ta addabe ku..."
Samudul Ansari da sarauniya Arya suna jin wannan batu na wannan basarake, suka sake gyara zama suna sauraronsa.
Dama daga ganin siffofinsa basu yi tsammanin a wannan duniya yake rayuwa ba, saboda babu mai irin wannan siffa tasa.
Sarkin ya ci gaba da bayani, "Ba zaku taɓa samun nasarar kawar da wannan cuta a wannan mataki na farko ba...
"Saboda ƙabilar Gorgon suna da ma'abota Bankai masu yawan gaske...
"Tabbas ba ƙaramin ƙoƙari kuka yi ba, da kuka iya kashe ma'abota Bankai har guda biyu dukda babu wani kyakkyawan shiri a jikinku.
"Kafun na sanar da ku waɗannan saƙonni, bari na nuna muku tattaunawar da ƙabilar Gorgon suke yi akan wannan hari da kuka kai musu..."
Sarkin na zuwa nan a zancensa ya samar da madubin tsafi bisa iska sannan ya nuna madubin tsafin da sandar tsafinsa.
Nan take madubin ya fara nuna hoton wani ƙaton ɗaki wanda kusan mutum ɗari suke zazzaune a cikinsa.
Gaba ɗaya mutanen guda ɗari zazzaune suke akan waɗansu ƙananun kujeru dake ƙasan wani tudu.
Dukkansu suna sanye da korayen tufafi masu ratsi-ratsin baƙi-baƙi.
Sun sunkuyar da kawunansu ƙasa cikin biyayya.
A saman wannan tudu akwai wata ƙatuwar karaga ta mulki, wadda take bayar da koren-haske da kuma sheƙi.
Wata tsaleliyar budurwa aka nuno zaune akan wannan karaga, tana sanye da koriyar alkyabba mai roɗi-roɗin baƙi.
Budurwar ba zata wuce shekaru ashirin zuwa ashirin da biyar ba a idanu, amma idan mutum ya matsa kusa da ita zai gane cewa, akwai ƙanshin tsufa dake tashi daga cikinta.
Idanuwan wannan budurwa suna da ban al'ajabi. Maimakon baƙin ido kamar na kowa, nata kore ne sharr.
Idanuwan a kafe suna bayar da buwaya, kwarjini, ƙarfin mulki da nuna isa. Kallon cikin waɗannan idanu kawai ya isa ya saka ƙaramin jarumi fitsari a tsaye.
Tana rataye da takubban Bankai guda biyu a gadon bayanta.
Ɗaya tana ɗauke da lamba casa'in da tara, ɗaya kuma tana ɗauke da lamba ɗari daidai.
Saran takobin Bankai mai mataki na hamsin na iya hallakar da alƙarya komai girmanta.
Amma ga mai mataki na casa'in da mai mataki na ɗari a hannun wannan budurwa. Hakan zai tabbatar da cewa wannan budurwa ita ce shugabar wannan daula gaba ɗaya.
Wani mutumi ya miƙe tsaye daga cikin waɗannan mutane guda ɗari dake zaune a ƙasan wannan budurwa ya kafa bakinsa a jikin wani bututun magana ya ce.
"Ziyazilu ta albarkaci mulkin ki, ta ƙara miki yarda. Tabbas waɗannan mutane guda biyu ta garina suka ɓullo, sun kashe masu gadin wannan gari nawa, sannan sun hallaka ma'abociya Bankai guda ɗaya..."
Wannan sarauniya tana jin abinda wannan basarake ya ce. Ta ɗago kanta tayi masa wani kallo da waɗannan idanuwa nata.
Nan take sarkin ya fara karkarwa, zufa ta fara ketowa daga jikinsa.
"SHIN KUN GANO WANE NE WANNAN JARUMI?" inji wannan budurwa.
Kalma na gugar kalma haka wannan maganganu suka fita daga bakinta. Bata buƙatar amfani da bututun magana, kowa dake cikin wannan ɗaki sai da ya jiwo abinda ta ce.
Wannan sarki wanda tuni ya gama jiƙewa da gumi ya dubi wani mayaƙi dake zaune a gefensa yayi masa inkiya.
Mayaƙin ya miƙe tsaye ya fara magana da irin wannan bututun magana ya ce, "Waɗannan jarumai suna amfani da waɗansu irin dawakai masu tsananin ƙarfin gudu, domin suna gamawa da dakarun birnin Mesa, kafun cikar rabin sa'a sun isa tsaunin albarka inda abar bauta Ziyazilu take.
"Sun gwabza yaƙi da masu tsaron ƙofar shiga gidan bauta; Khamsul-Bankai da Sittul-Bankai.
"A zahiri Khamsul-Bankai tafi ƙarfin wannan jarumi, domin kuwa kaɗan ya hana ta kashe shi, ya kirawo wani babban ɗalasimi wanda bamu taɓa gani ba.
"Ga hotunan yadda abubuwan suka faru;"
Wannan mayaƙi na zuwa nan a zancensa ya samar da baƙin ƙyalle a tsakiyar ɗakin wannan taro, baƙin ƙyallen ya soma nuna hotunan yadda wannan halitta ta sauƙa a cikin wannan baƙin hayaƙi ta hallaka Khamsul Bankai.
Wannan sarauniya tasu tana gama ganin yadda abubuwan suka kasance ta zare idanunta cikin tsananin mamaki.
"ABIN AL'AJABI!!!" inji wannan sarauniya.
Wannan mayaƙi ya risina sannan ya zauna.
Sarauniyar ta ɗago korayen idanunta dubi dukkan al'ummar dake zaune a cikin wannan ɗaki taro ta ce.
"Ya ku ahalin Gorgon! Umarni ya sauƙo daga abar bauta Ziyazilu...
"A NEMO WANNAN JARUMI DUK INDA YAKE A FAƊIN DUNIYA, A KAWOWA SHI ZIYAZILU DOMIN ƊAN-BAIWA NE.
"MAI GIRMA ZIYAZILU TA CE, WANNAN JARUMI BA KAMAR SAURAN MUTANE YAKE BA, KUMA SHI NE KAƊAI WANDA ZAI KAWO MANA MATSALA A YAYIN DA MUKA SHIGA SAURAN DAULOLIN DUNIYA.
"SABODA WANNAN DALILI, NA BAIWA JAMA'AR BIRNIN MESA DA JAMA'AR BIRNIN HAZRAM UMARNIN KAWO KAN WANNAN JARUMI.
"KAFUN CIKAR WATA GUDA... WANNAN UMARNINA NE!!!"
Wannan sarauniya tana zuwa wannan waje a zancenta, ta zaro takubbanta guda biyu ta ɗaga su sama, ta kwarara uban ihu.
Dukkan sauran waɗannan sarakuna guda ɗari suka yi koyi da ita...
Lokacin da madubin tsafin wannan sarki yazo wannan waje, sai yayi baƙin haske ya ɗauke.
Sarkin ya dubi Samudul Ansari da sarauniya Arya ya ce, "Wannan ita ce cikakkiyar tattaunawar da sarauniya YILAN GORGON da sarakunan dake ƙarƙashinta suka yi...
"Daga wannan lokaci sun ƙulla ɗamarar yaƙi da Samudul Ansari saboda sarauniya Yilan da abin bautarsu Ziyazilu sun gano wane ne Samudul Ansari.
"Bari na sanar da ku saƙonnin da na taho da su sannan na ba ku maganin wannan cuta..."
Wannan basarake na zuwa nan a zancensa ya fiddo wata takarda daga aljihunsa, yayi gyaran murya domin ya kama hankalin Samudul Ansari da sarauniya Arya saboda har a wannan lokaci tsananin mamakin suke bisa ganin sarakunan Gorgon da kuma sarauniya Yilan.
"Saƙo na farko: Dole ne ku bi mataki na biyu. Mataki na biyu ne kawai zai yi tasiri wajen yaƙi da ƙabilar Gorgon. Boka Ƙaizadu yafi kowa sanin wannan mataki don haka wajensa za ku koma yayi muku bayanin komai dalla-dalla.
"Saƙo na biyu: Samudul Ansari yana da kyau a wannan lokaci, ka san wane ne kai!
"Saƙo na uku: Dole ka cika sharuɗɗa guda uku, kafun yaƙar mutanen ƙabilar Gorgon...
"Zan yi muku kyakkyawan bayani akan saƙo na biyu, amma kyakkyawan bayani akan saƙo na farko da na uku... Dole ne kuje wajen boka Ƙaizadu saboda zaku fi fuskantar bayaninsa..."
Cikin kallon rashin fahimta Samudul Ansari da sarauniya Arya suka dubi wannan sarki.
Sarkin ya mayar da wannan takarda cikin aljihunsa ya sake yin gyaran murya ya ce, "Samudul Ansari kaine TAU'RIN!"
Samudul Ansari ya dubi sarkin ya ce, "Ban gane ni ne Tau'rin ba?"
"Hmm," sarkin ya yi murmushi ya ce, "Kalmar ma'ana guda biyu gare ta.
"Ma'ana na farko shi ne, 'MAGAJI' wanda yawancin mutanen duniya suke kiran magajin babban sarki da ita...
"Ma'ana na biyu wanda yake wajen mu, mu halittun sama da kuma mutanen ƙabilar Gorgon shi ne ƘARFIN RUHI; jarumtaka, baiwa, ƙarfin damtse, hikima da basira.
"Duk waɗannan abubuwa da na lissafo kalmar Tau'rin tana ɗaukar ma'anar su.
"Shin ka san wannan mutumi wanda kake kira yake bayyana a cikin baƙin hayaƙi ya ƙaddamar da duk aikin da ka saka shi?"
Cikin tsananin mamaki Samudul Ansari ya dubi wannan basarake ya gagara cewa komai.
Tun Samudul Ansari yana ɗan ƙaramin yaro, wannan mutumi yake bayyana masa amma bai taɓa cewa dashi komai ba.
Mafi yawancin lokuta sai Samudul Ansari ya keɓe a cikin daji sannan wannan mutumi yake bayyana, su yi kallo-kallo sannan ya ɓace.
Zaka iya cewa wannan mutumi shi ne ya cirewa Samudul Ansari tsoro, tun Samudul Ansari yana firgita sakamakon arba da wannan baƙin hayaƙi har ya daina.
Samudul Ansari bai taɓa bayyanawa wani labarin wannan baƙin mutumi ba, ba wai don baya so bane face yawancin lokuta zuciyarsa bata bin wannan umarni.
Samudul Ansari ya daɗe yana so ya yi tambaya akan wannan mutum mai baƙaƙen kaya amma ya gagara bayyanawa kowa labarin.
"Zan so na san wane ne wannan mutumi, wanda a duk sa'adda ya bayyana sai na rasa shekaru kaɗan daga cikin shekarun rayuwata..." inji Samudul Ansari.
Wannan basarake yayi murmushi ya samar da hoton wannan mutumi a cikin madubin tsafinsa ya nunawa su Samudul Ansari ya ce.
"Wannan abu da kuke gani ba mutum bane, domin baya numfashi...
"Ƙarfin sihirin tsafi baya tasiri a jikinsa, sannan shima baya amfani da sihiri ko kaɗan.
"Babban abinda wannan abu yayi imani da shi, shi ne JARUMTAKA.
"Kakana na arba'in da huɗu ya tabbatar da cewa, wannan halitta daga JARUMTAKA aka samar da ita.
"Ita ce JARUMTAKA, JARUMTAKA ita ce ita.
"Komai ƙarfin mutum da jarumtakarsa, bawa ne shi a gaban wannan ruhi.
"Duk wanda keda mallakin wannan ruhi, gagarabadau ne a duniya.
"Kakannina da kansu suna yawan kawo maganar wannan ruhi wanda aka halicci jikinsa da jarumtaka.
"Yilan Gorgon ta san cewa da wuya idan waɗannan garuruwa guda biyu da ta tura, su farauto Samudul Ansari zasu iya kamo shi, itama ta soma baiwa kanta horo tana wasa takobinta.
"Idan abin yafi ƙarfin yara sai ta shigo da kanta..."
Lokacin da wannan sarki yazo nan a labarinsa sai ya duba wani agogon sihiri dake hannunsa ya ce, "Mun kusa isowa inda zamu sauƙe ku...
"Shin ku na da wata tambaya ko kuma neman ƙarin bayani?"
Caraf Samudul Ansari ya ce, "Tayaya ni kaɗai zan iya yaƙar daula guda, alhalin ban kasance sarki ko wani mai iko ba?
"Idan ka san bayani akan wannan ruhi wanda yake bayyana a gare ni, mene ne dalilin da yasa idan na kira shi aiki kaɗan kawai yake min ya ɓace?
"Misali a ɗazu, kamata yayi ace ya hallaka waɗannan mayaƙa masu tsaron ƙofa dukkan biyu amma guda ɗaya hallaka kawai ya ɓace...
"Mene ne dalilin da yasa boka Ƙaizadu ne zaiyi mana bayanin wannan saƙo na farko da na uku, maimakon kai? Alhalin mun san cewa kafi boka Ƙaizadu ƙarfin sihiri da sanin sirruka nesa ba kusa ba?"
Wannan sarki ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "Amsar tambayarka ta farko boka Ƙaizadu ne zai amsata...
"Abinda yasa wannan ruhi baya daɗewa idan ka kira shi, shi ne akwai wani gagarumin jini wanda yake jira yaji yana yawo a cikin jikinka...
"Indai ka mallaki wannan jini, ruhin zai zauna a cikin jikinka din-din-din babu inda zai na zuwa... Zai zamo tamkar inuwarka a yayin da kake gwabza yaƙi.
"Ya ya kake ganin gumurzunka zai kasance, idan aka ce ga ƙarfinka ga ƙarfin wannan ruhi?
"Boka Ƙaizadu? Yaron mu ne, mu ne muka ɗaga darajarsa a duniya, a wannan zamani tsafi bai yi tasiri ba sosai a duniyarku.
"Mu ne muka kawo shi, domin ya tallata mana shi.
"Duk abinda boka Ƙaizadu ya sanar da ku, kafun ku taho da wanda zai sanar da ku yanzu idan kun koma, mu ne muka sanar da shi.
"Saboda haka idan kuna tare da boka Ƙaizadu tamkar ku na tare da mu ne..."
Wannan sarki na zuwa nan a zancensa, wannan ƙatoton jirgin da suke cikinsa ya tsaya cak!
Sarkin ya duba wannan agogon sihiri dake hannunsa ya ce, "Mun iso inda zaku sauƙa... Ku na fitowa daga cikin wannan jirgin ruwa nawa, za ku iske irin waɗannan dawakai da boka Ƙaizadu ya baku.
"Ku hau kan dawakan zasu kai ku inda boka Ƙaizadu yake domin ya sanar da ku; Mataki na biyu.
"Fatan alheri!" inji wannan sarki.
Wannan sarki na zuwa nan a zancensa ya ɗauko wata ƙatuwar kwalba dake gefensa ya baiwa Samudul Ansari ya ce, wannan shi ne maganin wannan cuta, ba zai taɓa ƙarewa ba, har zuwa nan da wata guda.
Samudul Ansari na shirin yin magana kenan, wannan badakare ya sake shigowa cikin wannan ɗaki sannan ya basu umarnin tashi su fita zai yi musu jagoranci izuwa waje.
Babu musu Samudul Ansari da sarauniya Arya suka fice daga wannan ɗaki, sannan suka fito daga wannan jirgi ta wannan ƙofa da suka shigo.
Bisa gaɓar wannan teku suka hango irin wannan dawakai suna harbin iska.
Samudul Ansari da sarauniya Arya suka ƙarasa bakin gaɓa suka tsaya.
Wannan mayaƙin ya mayar da ƙofa ya rufe, sannan wannan jirgi ya ci gaba da tafiya.
Tun Samudul Ansari da sarauniya Arya suna hango wannan jirgi har ya ƙule suka daina hango shi.
Sarauniya Arya ta dafa kafaɗar Samudul Ansari ta ce, "Ga dukkan alamu kaima kanka, baka san ainihin wane ne kai ba.
"Gwabza yaƙi da mayaƙan ƙabilar Gorgon!
"Kashe ma'abota Bankai har guda biyu!
"Sanya babbar sarauniya kamar Yilan mamaki!
"Karkato hankalin daular Gorgon gaba ɗaya izuwa kanka?
"Tabbas kai babban mutum ne mai babban matsayi..."
Samudul Ansari ya yi murmushi ya ce, "Zo muje wajen Ƙaizadu, lokaci yana ƙure mana."
Yana gama faɗin haka, ya haye kan wannan doki, sarauniya Arya ta hau kan na gefen suka ci gaba da tafiya.
Gudun waɗannan dawakai da suke kai, ya ma fi na waɗannan na farkon.
Kafun kace me wannan tuni sun iso waɗannan ƙauyuka guda uku.
Inda suka iske abin ya sake munana fiye da kowanne lokaci. Dukkan jama'ar waɗannan ƙauyuka suna kwance basu da lafiya.
Amma inda aka yi sa'a shi ne, wannan magani na likita Abu-Sharjas yana hana su mutuwa.
Kai tsaye Samudul Ansari yaje wajen

Please Login or Register in order to submit comment