Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka yiwa kanka adalci!"
Sarki Raja na jin wannan izgilanci ransa ya sake ɓaci ya sake kwarara uban ihu, sannan ya ɗaga wannan zabgegiar takobi dake hannunsa ya rugo kan su Aymanul Faris.
Jaruma Riya ta dubi Aymanul Faris tayi masa wata inkiya. Sai da suka bari saura kaɗan sarki Raja ya ƙaraso inda suke, ta sunkuya a gaban Aymanul Faris.
Shi kuma ya rugo da gudu ya taka tafukan jaruma Ria, ita kuma ta cilla shi sama. Aymanul Faris yayi wani wawan tsalle a sama, kafun sarki Raja ya ankara tuni ya doki ƙirjinsa.
Sarkin ya hantsila baya, kamar zai faɗi amma yayi taga-taga ya turje.
A fusace ya sake rugowa kansu, a wannan karon basu yi irin dabarar farko ba, saboda sun ga cewa sarkin ba zai faɗi ba saboda ƙarfin damtsensa.
Yana ƙarasowa inda suke tsaye, suka rabu, suka saka shi a tsakiya sannan suka ruguntsume da azababben yaƙi.
Aymanul Faris da jaruma Riya suka wanzu suna masu kaiwa sarki Raja muggan sara da suka ta ko'ina. Shi kuma saiya basu mamaki, domin kuwa duk sara da sukan da suke kai masa cikin zafin nama wanda yafi nasu yake karewa.
Wani lokacin ma baya kallon ta inda suke kai masa saran, amma a haka yake kare kansa.
Aymanul Faris da jaruma Riya sun cika da tsananin mamaki domin basu taɓa ganin mayaƙi kamar sarki Raja ba, ya iya yaƙi fiye da tunaninsu sannan ga ƙarfin damtse.
Tabbas in ba don sun haɗa ƙarfi da ƙarfe ba, da ba za su iya yaƙarsa ba. Saboda yafi ƙarfinsu nesa ba kusa ba.
Koda sarki Raja ya fuskanci cewa zasu ɓata masa lokaci, sai ya sake fusata. Ya daka tsalle a tsakiyar sannan yayi wani juyi da sawayensa. Dukkaninsu ya doke su a ƙirji.
Saboda ƙarfin wannan duka nasa sai da suka yi tsalle baya, sannan suka faɗo acan nesa bayansu ya bugu da ƙarfi.
Sarki Raja yayi wata mahaukaciyar dariya ya daka tsalle inda jaruma Riya take, ya kai mata wawan sara a kafaɗa. Cikin zafin nama ta mirgina amma dukda haka sai da ya samu nasarar saran damtsenta.
Wani irin zogi da raɗaɗi suka ratsata, jini yayi tsartuwa daga wajen.
Sarki Raja na shirin sake saranta kenan, yaji an doki gadon bayansa da ƙarfi daga baya. Duk tsananin ƙarfin damtsensa sai da yayi tsalle sannan ya faɗi a can gefe.
Ba wani ne ya aikata masa haka ba, face Aymanul Faris. Aymanul Faris ya fiddo wani farin ƙyalle daga cikin jakar guzurinsa ya ɗaure wannan rauni na damtsen jaruma Riya domin tsayar da jini.
Sarki Raja yayi wata irin tasowa sannan ya rugo kan Aymanul Faris suka soma ɗauki ba daɗi.
Tun da Aymanul Faris yake bai taɓa haɗuwa da namijin sadauki kamar Raja ba. Ga shi sadauki ga ya iya yaƙi.
Kafun a jima tuni ya fara galabaitar da Aymanul Faris. Jaruma Riya na ganin haka ta rugo ta bayan sarki Raja ta kawo masa wawan sara a wuya.
Bai ankara ba, sai da wannan sara yazo daf da wuyansa zai tsinke masa kai. Sannan yayi wani juyawa cikin zafin nama.
Dukda haka sai da wannan sara ya yanki wuyansa, amma yankan baiyi zurfi ba. Wannan abun wuya dake wuyansa ya tsinke.
Sarki Raja ya doki cikin jaruma Riya da ƙafarsa guda, lamarin da yasa ta durƙushe kan gwiwowinta kenan.
Yana shirin caka mata takobi, Aymanul Faris ya daka tsalle ya soka masa takobi a ƙirji. Takobin ta faso ta gaba ta fito.
Sarki Raja ya tofar da wani irin yawun jini, a lokacin da jikinsa ya soma kyarma. Idanunwansa suka soma gani dishi-dishi.
Ya durƙusa kan gwiwowinsa kamar wanda ya kusa mutuwa, Aymanul Faris ya zagayo inda jaruma Riya ke durƙushe yana duddubata.
Sarki Raja ya dafa ƙasa cikin shammace, ya daka tsalle ya doki ƙirjin Aymanul Faris. Saboda ƙarfin dukan saida Aymanul Faris yayi sama sannan ya faɗo acan nesa.
Sarki Raja ya tsaya a gaban jaruma Riya yana ta layi kamar wanda zai faɗi saboda jinin dake zuba daga ƙirjinsa, ya ɗauki wani ƙaton ƙarfe dake jikin gawar wani mayaƙi zai dokawa Riya a tsakiyar kanta.
Ba zato aka ga wata doguwar kibiya ta sauƙo daga sama ta cake shi a tsakiyar tumbinsa, sarki Raja ya sake kwarara uban ihu sannan ya durkushe kan gwiwowinsa yana aman jini daga bakinsa.
Jaruma Riya ta miƙe tsaye cikin tsananin juriya, ta ƙaraso gaban sarki Raja wanda ke kan gwiwowinsa ya kusa mutuwa.
Ta sa takubbanta guda biyu ta fille kansa.
Kan nasa yayi tsalle sama sannan ya faɗo baya.
Aymanul Faris da Oksu suka ƙaraso inda take, suna yi mata jinjina bisa nasarar samun kashe sarki Raja.
Jaruma Riya ta fiddo wannan makulli da ya tsinke daga wuyan sarkin ta gabatar musu. Cikin tsananin farin ciki Aymanul Faris ya rungumeta yana mai yaba jarumtakarta.
Wani gagarumin farin ciki ya lulluɓe jaruma Riya taji duniyarta gaba ɗaya tayi fari.
A daidai wannan lokaci ne Barban ya bayyana cikin haske, ya dubi Oksu ya ce, "Mun gode da gudunmawarka."
Oksu ya yi murmushi ya ce, "Fatan alheri!" Yayi girgiza ya juye izuwa mashi, mashin ya tashi sama cikin iska ya fara tsala azababben gudu.
Barban ya dubi su Aymanul Faris ya ce, "Jinjina a gareku. Mazan ƙwarai, jaruman da babu kamar su. Ku zo muje wajen tsoho Samazan domin sauraron hikayar babban sarki. Da fatan wannan makulli yana hannunku?"
Aymanul Faris ya nuna masa makulli wanda ya saka a cikin jakar guzurinsa.
Barban ya yi murmushin jinjina sannan ya dafa su gaba ɗaya suka ɓace ɓat daga wannan wuri. Suka bar gawar sarki Raja da dakarunsa gaba ɗaya.
****
Yau *06/02/2023*
Babi na gaba zaizo *09/02/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 82: *Hukunci*
*
ALLAH KA QARA KAWO MANA SAUƘI A ƘASARMU NIGERIA :'(
*
U*M*S
*
~Birnin Bahzam.
~Biyar ga watan Mayu.
*
A wannan rana, jama'ar wannan gari gaba ɗayansu sun taru a fadar ƙasar domin ganin an zartarwa da waɗansu mutane guda biyu hukunci.
Fada ce ƙasaitacciya mai girma na ƙwatance. Aƙalla za'a samu mutum dubu ɗari huɗu a wannan waje amma dukkansu wannan fada ta ɗauke su.
Wani hamshaƙin basarake ne zaune akan karagar mulkinsa, ya sha alkyabba wadda aka yiwa ado da alharini sai ɗaukar idanu take.
Fuskar a murtuƙe take tamkar bai taɓa dariya ba, sannan a duk lokacin da ya hango saman wani mumbari sai ya sake murtuƙe fuskar tasa.
Waɗansu mutane ne guda biyu, durƙushe akan wani mumbari sun sunkuyar da kawunan su ƙasa. Gaba ɗaya jikinsu daga wuyansu har ƙafafuwansu an saka sarƙoƙi an ƙulle babu yadda za'ayi suyi wani motsi na kirki.
Kasancewar fuskokinsu a rufe suke, babu wanda ya san ko su wane ne?
Wani narkeken ƙato na tsaye a gefensu bisa wannan mumbari, riƙe da zabgegiyar adda wadda ko shanu ya sara da ita sai ya rabe gida biyu saboda tsananin kaifinta.
Gaba ɗaya mutanen dake cikin wannan fada, sai ihu suke suna ta cewa, a kashe su! a kashe su!!
Ga dukkan alamu waɗannan mutane guda biyu dake durƙushe kan wannan mumbari, wani laifi suka yi wanda yasa gaba ɗaya jama'ar wannan gari gaba ɗaya suka tsane su.
***
A can cikin sararin samaniya kuwa, sarauniya Rauziyya ce tare da su sarki Kuffuru tafe a cikin gajimare. Boka Hubbazu yana duba madubin tsafinsa gami da gudanar da gajeruwar tsatsuba.
Cikin tsananin tashin hankali a firgici boka Hubbazu ya dubi sarki Kuffuru ya ce, "Ya shugabana! Mu gaggauta zuwa fadar birnin Bahzam yanzu-yanzu akwai wata gagarumar matsala?"
Cikin rashin fahimta sarki Kuffuru ya ce, "Matsalar me kenan? Wani abu ne yake shirin faruwa da Gidr?"
Maimakon boka Hubbazu ya bashi amsar wannan tambaya, kawai sai ya yanki babban ɗan yatsansa jini ya zubo.
Ya zuba wannan jini akan dardumar tsafi da suke zaune akanta.
Lamarin da yasa wannan darduma ta fara mahaukacin gudu kenan wanda yafi gaban tunanin mutum.
***
Wannan basarake dake zaune bisa karagar mulkinsa a birnin Bahzam ya miƙe tsaye, ya ɗaga hannunsa guda sama, dukkan jama'an dake wannan wuri suka yi tsit, suna jiran jawabansa.
Sarkin ya ce, "Waɗannan mutane guda biyu da ake gani durƙushe a gaban hauni, baƙi ne. Sun zo wucewa ta cikin wannan gari namu, sun tayar da tarzoma wadda ta janyo asarar rayuka da dukiya mai yawan gaske.
"A matsayina na shugaban wannan gari, na yanke musu hukuncin kisa - ta hanyar fille kai. Saboda su fanshi rayuka da dukiyar da suka jawo asararta..."
Wannan basarake na zuwa nan a zancensa ya dubi hauni ya gyaɗa masa kai.
Hauni ya matso da mutum na farko daga cikin waɗannan mutane biyu masu rufaffiyar fuska da aka yankewa hukuncin kisa, ya durƙusar da shi a gabansa yadda zai ji daɗin sare kansa.
Hauni ya ɗaga wannan zabgegiyar adda dake hannunsa, ya taƙarƙare yana shirin saran wuyan wannan mutum kenan.
Ba zato aka ji wata ƙara mai cike kunne ta sauƙa a tsakiyar wannan fada tamkar aradu.
Lamarin da yasa hauni dakatawa kenan, wannan basarake ya miƙe tsaye a fusace domin ganin abinda ya haddasa wannan gagarumar ƙara.
Bayan ƙura ta gama lafawa, waɗansu mutane guda uku suka bayyana a tsakiyar wannan fada. Mutum na farko boka ne, na biyu kuma sarki ne, ta ukun nasu kuma sarauniya ce.
Waɗannan mutane ba wasu bane illa sarki Kuffuru, sarauniya Rauziyya da boka Hubbazu.
Kwarjinin sarki Kuffuru kaɗai sai da yasa sarkin Bahzam yaja da baya a tsorace, saboda bai taɓa ganin sarki Kuffuru ba.
Ɗaya daga cikin waɗannan mutane da za'a sarewa kai, ya ɗago kansa ya kalli sarki Kuffuru.
Abin mamaki, idan mutum ya dubi cikin idanun, zai fuskanci cewa mace ce saboda tsananin kyawun idanun.
Waɗansu irin hawaye masu zafi suka soma zubowa daga cikin idanunta. Shi kuma wanda ke zaune a gefenta, wani irin firgice ne ya rufe shi.
Sarki Kuffuru ya dubi boka Hubbazu a hasale ya ce, "Ga mu mun zo fadar, mene?"
Boka Hubbazu ya nuna waɗannan mutane guda biyu da ake shirin sarewa kai ya ce, "Ga waɗanda muka zo ɗauka can!"
Sarki Kuffuru ya dube su ya murtuƙe fuska ya ce, "Hukunci aka yanke musu, meye ruwan mu a ciki?"
Boka Hubbazu ya nuna wadda take gefen dama ya ce, "Ka kalli wancar da kyau?"
Sarki Kuffuru ya sake haɗe fuska amma sai ya juya ya dubi wadda bokan ya nuna masa.
Idanuwansa na kaiwa cikin nata gabansa yayi wani wawan faɗuwa, jikinsa ya soma ƙyarmar fusata saboda ya gano cewa, ba wata bace illa ƴarsa Firziyya.
Cikin tsananin fusata sarki Kuffuru ya zaro takobinsa sannan ya dakawa sarkin Bahzam wani irin harara wanda yayi matuƙar girgiza shi.
"Domin rashin mutunci, ƴata kake yankewa hukunci?" inji sarki Kuffuru cikin tsananin fusata.
Sarkin Bahzam na jin haka ya haɗe fuskarsa ganin cewa anzo har cikin fadar birninsa za'a ci masa mutunci a gaban mutanensa.
Take shima ya zaro takobinsa, ya rugo da gudu kan sarki Kuffuru da nufin su yi mugun gamo.
Sarki Kuffuru na ganin haka yayi murmushi sannan ya jinjina kai, sai da ya bari saura taku bakwai sarkin Bahzam ya iso inda yake, ya daka wani wawan tsalle sama tamkar wanda aka harba daga cikin baka ya doki ƙirjin sarkin.
Sarkin Bahzam ya hantsila can baya, bayansa ya gwaru da garun wannan fada, ya faɗo ƙasa a galabaice. Sarki Kuffuru yayi masa kashedi da yatsa guda ya ce, "Kada ka kuskura ka sake tunkarata, idan ba haka ba, zan sare kanka!" inji sarki Kuffuru.,
A gaban idanun sarkin Bahzam ya ƙarasa inda Firziyya da Aydenlik ke ɗaure yasa takobinsa ya sassare sarƙoƙin da suka ɗaɗɗaure su, sannan ya tashe su tsaye. Boka Hubbazu da sarauniya Rauziyya suka ƙaraso wannan wuri.
Sarki Kuffuru ya kirawo hadimin aljaninsa ya bashi umarnin ɗaukar su gaba ɗaya. Aljanin ya ranƙwafa shi, Firziyya, Aydenlik, Hubbazu da Rauziyya suka haye bayansa.
Aljanin ya lulluƙa cikin gajimare, bai yi nisa ba, sarauniya Rauziyya ta dube su ta ce, "Bari naje na taho mana da Gidr, zan same ku a can!"
Sarki Kuffuru da boka Hubbazu suka gyaɗa mata kai alamun amincewa.
"Ƴata! Mene ne ya kawo ki wannan birni? Ba don mun zo da wuri ba, da tuni na rasa ki?" inji sarki Kuffuru.
Gimbiya Firziyya ta ɗago kai tayi masa wani irin kallo mai cike da tsantsar ƙiyayya sannan ta kawar da kai bata ce dashi komai ba.
Wannan abu yayi matuƙar baiwa sarki Kuffuru mamaki, sannan yayi matuƙar girgiza shi.
Tun da yake tare da gimbiya Firziyya bata taɓa yi masa irin wannan kallo ba, kullum tana tare da shi, ita ce abokiyar shawararsa a koda yaushe.
Ya ya za'a yi yanzu tayi masa irin wannan kallo wanda yake nuna tsantsar ƙiyayya. Shin wannan tafiya da yayi ne, yasa ta tsane shi ko kuma me?
Sarki Kuffuru ya ce, "Me ke faruwa ƴata, akwai abinda nayi miki ne?"
Har a wannan lokaci ba ta ce da shi uffan ba, kanta a sunkuye yake.
Sarki Kuffuru ya dubi boka Hubbazu kamar yana so yayi masa bayani, Hubbazu ya kawar da kai bai ce dashi komai ba.
Sarki Kuffuru yayi shuru ya faɗa kogin tunani, a wannan lokaci kansa ya gama kullewa. Ƴarsa wadda ya haifa ta fara nuna masa wani irin hali wanda bai santa da shi ba.
Idanuwan sarki Kuffuru suka kai kan Aydenlik, ya fara nazarin Aydenlik da siffofin jikinsa.
Aydenlik tsoho ne tukuf, amma ko kaɗan idanuwansa basa nuna alamun tsufa. Dukda cewa ya tsufa amma fatar jikinsa tana nan da kyawunta bata fara yamutsewa ba.
Sarki Kuffuru ya shafe kusan daƙiƙa ɗari biyu da tamanin yana kallon Aydenlik, kafun kansa ya fara sarawa.
Cikin tsananin fusata ya kamo Aydenlik da ƙarfi sannan ya cakomo kwalarsa ya shaƙe, ya ce, "Kayi min bayanin waye kai? Ko kuma wanda ke kwance a kabari yafi ka jin daɗi?"
Tunda tsoho Aydenlik yake rayuwa a duniya bai taɓa ganin fusataccen mutum kamar Kuffuru ba. A wannan lokaci idanuwan sarki Kuffuru tamkar garwashi suka koma saboda yadda suka kaɗa suka yi ja.
Tabbas ya fara fuskantar wani abu wanda zaiyi matuƙar ɓata masa rai.
Tsoho Aydenlik ya haɗe fuska ya ƙi yayi magana. Sarki Kuffuru yayi murmushin mugunta ya ce, "Za ka yi bayani!"
Yana fadin haka ya taƙarƙare ya gabzawa Aydenlik naushi a baki, wanda saboda ƙarfin naushin sai da haƙoran bakinsa guda biyu suka yi fitar burtu, jini yayi feshi daga bakinsa.
Waɗansu irin hawayen wahala suka zubo daga idanun Aydenlik. Sarki Kuffuru ya sake tambayarsa amma dukda haka bai yi magana ba.
Tsahon ɗan lokaci sarki Kuffuru yana ta dukansa domin dai yayi bayani amma ya ƙi. Lamarin da ya sake fusata sarki Kuffuru domin babu abinda ya tsana a rayuwarsa kamar taurin kai.
Suna cikin tafiya a sararin samaniya suka zo giftawa ta gefen wani ƙaton dutse, sarki Kuffuru na ganin haka yayi murmushin mugunta ya kamo kwalar Aydenlik yazo daf da wannan dutse ya tsaya.
Suna isowa daidai wannan dutse sarki Kuffuru ya ɗaga Aydenlik sama, sannan ya saita kansa da wannan dutse ya ce, "Kayi bayani yanzu, ko kuma kanka ya tarwatse?"
"BA ZAN YI BAYANIN KOMAI BA," inji Aydenlik muryarsa na fita da ƙyar.
Sarki Kuffuru ya fusata suna zuwa kan wannan dutse ya rotsa kan Aydenlik da shi, take kan Aydenlik ya tarwatse ƙwaƙwalwarsa tayi fata-fata.
Sarki Kuffuru ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan yayi jifa da gawar Aydenlik ƙasa.
Gimbiya Firziyya tana ganin wannan rashin imani na mahaifinta ta fashe da kuka, tana mai tsananin takaicin kasancewa yar sa.
Sarki Kuffuru ya taka yaje inda take durƙushe ya kamo gashin kanta da ƙarfi ya ce, "Ke yarinya! Waye ne wannan tsohon? Kiyi bayani ko kuma na gana miki azaba?"
Idan ka ji muryar sarki Kuffuru a wannan lokaci zaka rantse kace ba yarsa bace, saboda yadda ya riƙo gashin kanta.
Gimbiya Firziyya ma ta ƙi tayi magana a wannan lokaci, hawaye masu zafi suna zubowa daga idanunta.
Koda boka Hubbazu ya fuskanci cewa, idan bai faɗawa sarki Kuffuru gaskiyar al'amari ba, sarki Kuffuru zai iya hawa dokin zuciya ya hallaka yarsa sai ya ce.
"SU NE SUKA CECI MARGANU A BIRNIN SARAUNIYA RAUZIYYA."
Sarki Kuffuru na jin wannan batu yaji tamkar ruwa mai tsananin zafi aka watsa masa wanda zai ƙona jikinsa gaba ɗaya. Wani mugun jiri ya soma ɗibarsa.
Ƴarsa ta cikinsa ta haɗa kai da babban abokin gabarsa, suna ta shirye-shiryen kawo ƙarshensa.
Saboda tsananin takaici da ɓacin rai sarki Kuffuru waje ya nema ya zauna, domin hakan zai fiye masa sauƙi, idan ba haka kuwa jiri zai iya faɗar da shi ƙasa.
Idan ka dubi fuskar jaruma Firziyya zaka ga ko kaɗan babu tsoro ko kuma nadama a cikinta, kamar ma farin ciki take da sarki Kuffuru ya gano cewa da ita aka haɗa kai aka ceci Marganu.
Sarki Kuffuru ya ɗago fuskarsa wadda ta fara gatsinewa saboda tsananin fusata, ya dakawa gimbiya Firziyya wani irin harara.
Gimbiya Firziyya ta murtuƙe fuska ta kalle shi, fuskarta babu tsoro ko nadama.
A daidai wannan lokaci ne, wannan aljani dake ɗauke da su ya dira a cikin wannan daji wanda suka bar sarki Darwazu a cikinsa yana jiransu.
Sarki Kuffuru ya mangare gimbiya Firziyya da damtsen hannunsa, ta faɗo daga kan wannan aljani.
Boka Hubbazu da sarki Darwazu suka yi sauri suka taso suka riƙe sarki Kuffuru suna bashi haƙuri akan kada ya daki yar tasa.
Gimbiya Firziyya ta miƙe tsaye ta dubi sarki Kuffuru ta ce, "Na zaɓi nayi rayuwa da Marganua akan na zauna tare da kai, saboda tsananin zaluncin da kayi masa. Kayi sani cewa tun sa'adda nayi arba da Marganu a karon farko lokacin da yazo birninmu na kamu da ƙaunarsa. A yanzu ba zan iya rayuwa idan ba tare da Marganu ba."
Sarki Kuffuru na jin wannan batu na gimbiya Firziyya ya ƙwace daga hannun su sarki Darwazu sannan ya zabura cikin zafin nama ya sake mangare gimbiya Firziyya, ta sake faɗuwa ƙasa.
A fusace sarki Kuffuru ya hau kanta yayi ta gabza mata naushi tamkar ba yar da ya haifa ba.
Babu irin roƙon da su boka Hubbazu ba su yi masa akan ya rabu da ita ba, amma ya ƙi tamkar baya jin su.
Sai da ya gama yi mata jina-jina sannan ya miƙe daga kanta. Ya dube ta a hasale ya ce, "Duk wanda ya zaɓi soyayya, ya kama turba wadda ba zata fishe shi ba. Mun halaka mahaifin Marganu sannan mun halaka Marganun ma.
"Wannan abun kunya da kika yi, yasa na goge ki a matsayin yata, tabbas zan kashe ki da hannuna amma ba yanzu ba. Sai na kai ki kurkuku an gana miki baƙar azaba, sai na sa kinyi nadamar haɗa kai da Marganu sannan zan sare kanki."
Sarki Kuffuru na zuwa nan a zancensa, sarauniya Rauziyya ta sauƙo wannan fili daga sararin samaniya ɗauke da wani mutum a gadon bayanta.
Su sarki Kuffuru basa buƙatar ayi musu bayanin wannan mutumi wane ne domin kuwa sun gane shi.
Sarki Kuffuru ya dubi sarauniya Rauziyya ya ce, "Ku fara gina wannan kurkuku, bari naje wani waje na dawo!"
Yana faɗin haka ya doki gefen wuyan gimbiya Firziyya a take, ta sulale ƙasa sumammiya.
Sarki Kuffuru ya kirawo aljaninsa sannan ya bashi umarnin tashi da su, aljanin ya lulluƙa cikin gajimare sannan ya tambayi sarki Kuffuru ina suka nufa?
"KURKUKUN AZABA-UKU!" inji sarki Kuffuru.
Wannan aljani na jin haka ya ƙara ƙarfin gudunsa a cikin gajimare, kafun a jima tuni ya sauƙo a saman wannan dogon tsauni wanda aka gina wannan kurkuku a samanta.
Sarki Kuffuru ya ce wannan aljani ya jira shi a ƙofar shiga wannan kurkuku yana zuwa.
Ya saɓa gimbiya Firziyya akan kafaɗarsa sannan ya shige cikin wannan kurkuku.
Yana shigowa aljani Duksum ya taho da sauri ya faɗi a gabansa yayi gaisuwa.
Sarki Kuffuru ya cilla masa gimbiya Firziyya ya ce, "A kulle wannar a kurkuku sannan kullum a ɗinga gana mata azaba, sai ranar da nazo na karɓeta da kaina. Ina so a yi mata irin azabar da ba'a taɓa yiwa wani ba."
Sarki Kuffuru na gama faɗin haka ya juya ya fice daga cikin wannan kurkuku. Aljani Duksum yayi murmushi sannan ya ɗauki gimbiya Firziyya ya shige cikin irin waɗannan ɗakuna guda uku da ita.
Sarki Kuffuru na fitowa ya sake hayewa gadon bayan aljaninsa, aljanin ya tashi sama cikin gajimare sannan ya ɓace ɓat!
A cikin wannan daji sarki Kuffuru ya sauƙa inda ya iske magini Gidr na ta aiki.
Ginin nasa yana da ban al'ajabi, dukda cewa bai daɗe da fara ginin ba amma ginin ya soma yin nisa.
Babu wanda yake bashi umarni da yadda zai tsara ginin amma daga yanayin ginin mutum zai gane cewa gidan kurkuku yake ginawa.
Ɗaki guda tal ya gina a cikin ƙarƙashin ƙasa sannan yayi amfani da irin wannan tubali ya haɗa masa bangwaye.
Sarki Kuffuru yayi murmushi cikin jin daɗi sannan ya nemi waje ya zauna yana kallon wannan gini.
Tsahon wuni guda magini Gidr ya ɗauka yana gina wannan kurkuku sannan ya kammala.
Kurkuku ce ƙarama da aka gina da wannan tubali wanda idan mutum ya kalle shi zai ɗauka jar dalma ce aka dunƙula aka ginata da shi.
Daga ganin wannan tubali mutum zai gane cewa, wuta ko ruwa bai isa ya huda shi ba.
Ɗaki guda daya jal kawai aka gina a cikin wannan kurkuku sannan na ƙarƙashin ƙasa amma anyi masa tagogi biyu waɗanda zasu baiwa fursunan ciki damar shaƙar iska.
Anyi ginin ta waje tamkar doguwar husumiya, mutum idan yazo daga sama zai hango gini guda ɗaya a tsakiyar dokar daji.
Boka Hubbazu ya ce, "Barka da samun wannan kurkuku! Aiki guda ɗaya ya rage mana, shi ne kamo Barban amma kafun nan sai mun hallaka aljaninsa!"
Sarki Kuffuru ya ce, "A ina zamu samu wannan aljani?"
****
Yau *09/02/2023*
Babi na gaba zaizo *11/02/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 83: ISRABIL
*
YA ALLAH KA KAWO MANA SAUƘI A NIGERIA.
*
U*M*S
*
~Ɓangaren Yarima Marganu.
*
Tinjim! Marganu ya faɗo cikin wani ƙaramin tafki mai ruwa garai-garai. Gangar jikin Marganu tayi nutso sosai a cikin wannan tafki kafun daga bisani ya soma yin iyo yana tasowa sama, sai da ya ɗan ɗauki lokaci kafun ya taso saman wannan tafki ya shaƙi numfashi.
Marganu ya ƙarewa wannan waje da ya tsinci kansa a ciki kallo, kafun ya fito daga wannan tafki ya zauna a bakin gaɓa yana tunani.
Wajen gaba ɗaya a cike yake da bishiyoyin ƴaƴan marmari, sannan akwai dogwayen bishiyoyin masu tsaho da kauri da suka kewaye shi.
Marganu yayi shuru yana tunanin wannan gumurzu da ya fafata da wannan sadauki.
Mene ne dalilin da yasa sarki Kuffuru zai turo masa mutum-mutumi mai kama da shi?
Ina sarki Kuffuru yake a halin yanzu?
Wanne hali Aydenlik da gimbiya Firziyya suke a birnin Bahzam?
Kafun Marganu ya samu amsoshin waɗannan tambayoyi nasa, sai ya jiwo motsi daga bayansa alamar mutane ne tafe.
Cikin zafin nama Marganu ya miƙe tsaye sannan ya juya. Nan take ya hango waɗansu yan-mata guda uku kyawawan gaske sun ƙura masa idanu.
Tun da yake a duniya bai taɓa ganin mutane

Please Login or Register in order to submit comment