Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana kallon bakin ƙofa.
Wannan sadauki baya numfashi, baya ƙifta idanu, sannan baya motsi. Abinda kawai ya sani shi ne bin umarnin da aka bashi. Sarki Ayubu ya cika da mamaki matuƙa, bisa ganin yadda wannan sadauki yake matuƙar kama da sarki Kuffuru.
Tabbas in ba don aljani Jizid ya bashi labarin wannan tuggu ba, da ba zai yarda cewa wannan sadauki da yake hangowa ba sarki Kuffuru bane.
Wannan sadauki na cikin kallon ƙofar shiga kenan, idanuwansa suka kallo cikin wannan tsagu da sarki Ayubu yayi. Nan take idanuwansa suka kai cikin na sarki Ayubu.
Idanuwansu na haɗuwa sarki Ayubu yaji gaba ɗaya tsigar jikinsa ta mimmiƙe, wani irin kwarjini ya lulluɓe shi. Wannan shi ne kwarjinin da kowanne mutum yake ji, idan ya kalli cikin waɗannan idanu na ƴaƴan Infiro.
Sadaukin na ganin sarki Ayubu ya taso da sauri, sannan ya zaro wannan zabgegiyar takobi dake cake a cikin ƙasa wacce bata da bambanci da takobin Siwod-del-bulod dake hannun sarki Kuffuru ya tunkaro wannan ƙofa inda sarki Ayubu ke tsaye.
Sarki Ayubu na ganin haka ya ja da baya sannan ya sake riƙe takobinsa da kyau, wannan sadauki na fitowa suka yi kallo-kallo na ɗan ƙanƙanin lokaci. Babu cacar baki ko kuma wani kace-nace suka falfalo da gudu kan juna.
Wannan sadauki na wulwula takobinsa a cikin iska, shi kuma sarki Ayubu ya kafa takobinsa a ƙasa tana kartar ƙasa gami da haifar da ƙura.
A shirin sarki Ayubu yana so ya gama wannan fafatawa da wannan sadauki, ba tare da sanin su boka Biu Lin ba. In dai kamar yadda suka tsara wannan fafatawa haka abin ya kasance, su sarki Kim Sam zasu neme shi sama da ƙasa su rasa.
Suna haɗuwa a tsakiya sarki Ayubu ya kaiwa wannan sadauki wawan sara a wuya da nufin ya tsinke masa kai. Wannan sadauki baiyi wani yunƙuri na kaiwa sarki Ayubu hari ba, sunkuyawa yayi ƙasa wannan takobi ta sarki Ayubu ta sari iska.
Cikin zafin nama wanda yafi gaban tunanin mutum ya zagaya ta bayan Ayubu ya danƙara masa wawan sara a gadon baya. Sa'ar da sarki Ayubu ya ci ita ce, akwai sulken yaƙi a jikinsa wanda ya hana wannan takobi fasa shi.
Saboda ƙarfin saran sai da wannan sulke ya rabe gida biyu sannan ya zube ƙasa, sarki Ayubu ya bayyana babu riga a jikinsa. Haƙiƙa sarki Ayubu ma narkeken ƙato ne mai tsananin ƙira ta ƙarfi.
Shi kansa ya cika da tsananin mamakin zafin naman wannan mutum-mutumi, amma da ya tuna ba da mutum mai jini da tsoka yake yaƙi ba, sai hankalinsa ya ɗan kwanta.
Sarki Ayubu ya zaro wata ƙatuwar garkuwa daga cikin jakar tsafinsa, sannan ya sake dakewa ya fuskanci wannan mutum-mutumi.
Sadaukin yayi wani irin ihu mai kama da ihun matattu ya dako wawan tsalle ya kawowa sarki Ayubu sara, cikin zafin nama sarki Ayubu ya saka wannan garkuwa ya tare saran.
Saboda nauyin wannan sara sai da sarki Ayubu ya durƙushe bisa gwiwarsa guda. Wannan mutum-mutumi yayi amfani da wannan dama ya doki cikin sarki Ayubu da ƙafarsa guda.
Sarki Ayubu ya hantsila baya saboda ƙarfin wannan duka, wannan sadauki ya sake daka tsalle sama ya saita cikin sarki Ayubu da wannan zabgegiyar takobi dake hannunsa da nufin yana dirƙowa zai caka masa ita.
Saura ƙiris wannan takobi ta tsire cikin sarki Ayubu, amma ya mirgina gefe cikin tsananin zafin nama. Takobin ta nutse cikin ƙasa, tamkar rijiya aka tona haka wani ƙaton rami ya bayyana zururu.
Cikin zafin nama sarki Ayubu yasa ƙafarsa ya doki haɓar wannan sadauki, maimakon wannan sadauki ya hantsila baya, kawai sarki Ayubu aka ga ya riƙe ƙafar ya ƙwala ihu.
Don ji yayi tamkar kututturen bishiya ya nausa da wannan ƙasa tasa. Kafun sadaukin ya sake juyowa tuni sarki Ayubu ya daka tsalle gefe guda, ya tsaya yana haki gami da nazarin wannan sadauki.
Tabbas a yau yasan ya haɗu da gamonsa, wannan sadauki yafi shi zafin nama, ƙarfin damtse da iya yaƙi.
A fusace wannan sadauki ya juyo inda sarki Ayubu ke tsaye suka sake fuskantar juna. Sadaukin ya haɗe hannayensa a waje guda, bakinsa ya fara motsawa a hankali. Ga dukkan alamu ɗalasiman tsafi yake karantawa.
Nan take baƙaƙen kayan dake jikin wannan mutum-mutumi suka soma ƙara baƙi, wani irin baƙin hawaye ya soma zubowa daga cikin idanunsa, wannan zabgegiyar takobi dake hannunsa ta fara fitar da wani irin farin hayaƙi mai ɗaukar hankali.
Sarki Ayubu na ganin haka shima ya kirawo wani ɗalasimin tsafinsa, takubban dake hannunsa suka ƙara tsaho da tsini, wata ƙasaitacciyar iska mai bayar da ƙanshin sihiri irin na matsafan farko ta fara kewaya jikinsa.
Wannan sadauki ya falfalo da gudu kan sarki Ayubu yana kwarara wani irin uban ihu mai tsananin razanarwa da amsa kuwwa. Shima sarki Ayubun sai ya ruga da gudu ya tare shi.
Ai kuwa suna haɗuwa a tsakiya suka sake ruguntsumewa da azababben yaƙi wanda yafi na farko ban tsoro da kuma firgici.
Wannan sadauki ya wanzu yana mai kaiwa sarki Ayubu sara cikin baƙin zafin nama wanda ya ninka na farko sau uku, shi kuma sarki Ayubu sai ya wanzu yana kare hare-haren sadaukin iyakacin iyawarsa ba tare da ya samu nasarar mayar da martani koda sau ɗaya ba.
A duk lokacin da wannan sadauki ya kawowa sarki Ayubu sara sai kaga farin hayaƙi ya cika wajen, ba don sarki Ayubu tsohon mayaƙi bane da tuni wannan sadauki ya jima da yin kaca-kaca da namansa.
Idan mutum ya hango wajen da ake wannan gumurzu daga nesa zai ga baƙin mutum a cikin farin hayaƙi, wannan sadauki kenan.
Haka dai suka ci gaba da wannan gumurzu har tsahon rabin sa'a ba tare da ɗayansu ya sake samun wata nasara ta azo a gani ba, amma sai dai sarki Ayubu ya jikkata sosai. Im banda haki babu abinda yake.
Tun da yake fafata yaƙi da mazajen fama bai taɓa haɗuwa da mutum mai baƙin zafin nama kamar wannan sadauki da suke fafatawa yanzu ba.
Jan wannan yaƙi da yake, na daga cikin shirin sarki Ayubu domin a yadda suka tsara idan aka sami kamar sa'a guda ana wannan fafatawa wannan sadauki zai iya kiran ɗalasimin tsafi wanda zaiyi jifa dasu uwa-duniya.
Acan farkon wannan daji kuwa, sarki Kim Sam ne da boka Biu Lin da kuma Ruguzan suna tattaunawa akan ƙarar karafkiyar ƙarafan da suka jiwo daga inda suka yada zango a wannan wuri.
"Ya kamata mu kaiwa sarki Ayubu ɗauki," inji sarki Kim Sam. "Ga dukkan alamu a yayin da yaje leƙen asirin nan, sun gano shi, shiyasa yanzu suke fafatawa."
Boka Biu Lin ya ce, "Kwarai hakane,"
Suka ci gaba da sauri suka tasarwa inda suke jiwo ƙarar gumurzun. Ba su yi nisa ba suka soma hango wani irin farin hayaƙi ya cika wajen gaba ɗaya, babu abinda suke gani idan ba wannan farin hayaƙi ba.
Wannan ne yasa suka ɗan dakata basu afka cikin wajen da ake yaƙin kai tsaye ba.
Sarki Ayubu ya lura da zuwan su sarki Kim Sam kuma ransa ya sosu matuƙa don yana jin tsoron kada suna tsakiyar gumurzu da wannan sadauki wani daga cikin sarki Kim Sam ko boka Biu Lin ya soke shi da rantsatstsen makaminsa.
Sarki Ayubu ya murtuƙe ya juyo ya harare su, amma saboda akwai wannan farin hayaƙi basu gan shi ba.
Suka ci gaba da fafatawa da wannan sadauki har kusan wata rabin sa'ar wadda sa'a guda tana cika wannan sadauki zai kirawo ɗalasimin tsafinsa.
A lokacin ne wannan hayaƙi ya soma lafawa, siffar sarki Ayubu da ta wannan sadauki ta fara bayyana.
Wannan sadauki ya gama gajiyar da sarki Ayubu liƙis, har ta kai ta kawo cewa, da ƙyar sarki Ayubu ke iya kare hare-haren wannan sadauki.
Wannan hayaƙi na gama lafawa, wannan sadauki yayi wata alkafira sama ya doki haɓar sarki Ayubu da ƙafarsa guda. Sarki Ayubu ya hantsila baya ya faɗo ƙasa a galabaice.
Sadaukin ya tako a hankali yazo ya tsaya akan sarki Ayubu yana mai saita takobinsa ta tumbinsa, yana so ya tsire shi, yadda zai mutum lokaci guda.
Sarki Kim Sam, boka Biu Lin da boka Ruguzan suna ganin dukkanin abinda ke faruwa. Cikin tsananin ɗimauta sarki Kim Sam ya zaro wannan mashi nasa ya ruga da gudu ya nufi inda wannan sadauki yake da nufin ya hana shi cakawa sarki Ayubu wannan wuƙa.
Amma ina, kafun ya isa tuni wannan sadauki ya tattaro ƙarfinsa gaba ɗaya ya caka wannan takobi a cikin ƙasa, domin kuwa tuni sarki Ayubu yayi gaggawar mirginawa gefe guda.
Yana buɗe idanunsa da ƙyar ya kalli sarki Kim Sam a bayan wannan sadauki yana ƙoƙarin caka wannan mashin dake hannunsa, sadaukin bai san abinda ke faruwa ba saboda ƙoƙarin zaro takobinsa da ta nutse a cikin ƙasa yake.
Saura ƙiris mashin hannun sarki Kim Sam ya caki bayan wannan sadauki. Ba zato aka ga sarki Ayubu yayi wata irin tasowa daga kwancen da yake ya doki ƙirjin sarki Kim Sam da ƙafarsa guda.
Sarki Kim Sam yayi sama ya faɗo a can baya, Ayubu ya miƙe tsaye sannan ya ɗauki wani gungumen ice ya doki kan wannan sadauki da shi. Sadaukin ma yayi sama ya faɗo a can nesa.
Cikin tsananin mamaki sarki Kim Sam, boka Biu Lin da boka Ruguzan suka dubi sarki Ayubu suna son suyi masa tambaya akan abinda ya aikata. Ya za'ayi ya doki sarki Kim Sam wanda yazo domin ya ceci rayuwarsa daga halaka?
Ga dukkan alamu hankalin sarki Ayubu ba'a kansu yake ba, domin kuwa, ya tattara hankalinsa gaba ɗaya yana nazarin wannan mutum-mutumi dake tsaye a can nesa kaɗan.
Koda wannan mutum-mutumi yaga sarki Ayubu, sarki Kim Sam da bokayen nan biyu, sai hankalinsa ya tashi. Umarnin da aka bashi shi ne kashe sarki Ayubu amma ganin gawurtattun mutane a tare dashi ya saɓa da wannan umarni.
Babu abinda yafi ɗugunzuma hankalin wannan mutum-mutumi kamar makamin yaƙin dake hannun sarki Kim Sam.
Saboda wannan dalili yasa ya fara shirye-shiryen kiran ɗalasimin tsafi wanda zai cece shi daga tarkon da yake ciki, idan yaso daga baya sai ya tafi farautar sarki Ayubu.
Kamar an faɗawa sarki Ayubu abinda wannan mutum-mutumi yake shirin aikatawa, sai ya ruga da gudu ya tsaya kusa da shi.
Su sarki Kim Sam suka tsaya ƙyam, suna kallon abinda ke faruwa cikin tsananin mamaki.
Saura daƙiƙa biyar kawai wannan mutum-mutumi ya kammala kiran wannan ɗalasimi suka ga sarki Ayubu yayi tsalle ya rungume shi.
Wata irin baƙar guguwa mai tsananin ƙarfi ta taso wacce ta tashi hankalin dukkanin halittun dake rayuwa a cikin wannan daji. Guguwar ta kanannaɗe wannan sadauki da sarki Ayubu tayi jifa dasu cikin gajimare, tun su Kim Sam suna hango su har suka ƙule.
Saboda ƙarfin wannan ɗalasimi sai da wannan daji gaba ɗaya yayi girgiza, su sarki Kim Sam suka rikito ƙasa.
Bayan komai ya gama lafawa, sarki Kim Sam da boka Biu Lin da boka Ruguzan suka tashi zaune suka fuskanci juna cikin tsananin mamaki. Duk cikinsu babu wanda ya san dalilin da yasa sarki Ayubu yayi wannan abinda yayi.
Abinda ya tsaya musu a kai shi ne, mene ne dalilin da yasa sarki Kuffuru ya kira ɗalasimin tsafi wanda yayi jifa da su?
Ina sauran abokan tafiyar sarki Kuffurun? Meyasa sarki Ayubu ya rungume sarki Kuffuru suka ɓace a tare. Waɗannan tambayoyi su ne suka tsayawa su sarki Kim Sam a rai.
"Me ma'anar wannan abu da ya faru?" sarki Kim Sam ya tambaya. "Shin ina abokan tafiyar sarki Kuffuru? Wannan abu ya faru, ba kamar yadda muka tsara ba, meyasa?"
Boka Ruguzan da boka Biu Lin suka yi shuru suna tunani. Al'amarin akwai rikitarwa tun kafun su zo wannan wuri sun san cewa sarki Kuffuru ba shi ɗaya bane ya fito wannan tafiya.
Sannan basu san abinda ya faru da sarki Ayubu a yayin da yazo wannan leƙen asiri, shin gano shi aka yi ko kuma wani shiri aka yi masa ya faɗa? Babu wanda yasan amsar wannan tambaya.
"Ina ganin har yanzu bamu gama sanin waye ne sarki Kuffuru ba," inji Biu Lin. "Yana da kyau mu sake karantar sa domin ga dukkan alamu mutum ne shiryayye."
Sarki Kim Sam ya ce, "Hakane, amma ina sarki Ayubu yake a halin yanzu? Kun san cewa abokin tafiyarmu ne, yana da kyau mu san inda yake idan da hali ma, mu taimaka masa."
"Kwarai hakane," inji Ruguzan. "Ga dukkan alamu tarkon sarki Kuffuru ya faɗa. "
Boka Biu Lin ya sake samar da irin wannan madubin tsafi nasa mai fuska guda huɗu, ya saita ɓangaren da sarki Ayubu yayi sannan ya shafi madubin tsafin da hannun hagu domin ganin abinda ke faruwa.
Maimakon wannan madubin tsafi yayi haske ya nuna abinda suke buƙata, kawai sai gani suka yi yayi baƙi ƙirim sannan yayi bindiga ya tarwatse.
Cikin takaici boka Biu Lin ya dube su ya ce, "Sihirin tsafi ba zai nuna mana inda sarki Ayubu yake ba, a halin yanzu."
Boka Ruguzan ya ɗan haɗe fuska ya ce, "Yanzu mene ne abin yi?"
"Sarki Ayubu dai, shi ne wanda ya fafata da sarki Kuffuru," inji sarki Kim Sam. "Ya ƙwaci wannan taswira ko bai ƙwata ba, ba mu sani ba? Sannan babu mai bamu amsar wannan tambaya idan ba shi sarki Ayubun ba.
"Saboda haka mu bi bayansa kawai, wataƙila wannan taswira da za muyi farautar Hodon da ita, tana hannunsa. Ko ya kuka ce?" Kim Sam ya nemi shawararsu.
To, shi boka Biu Lin bawan sarki Kim Sam ne abinda sarki Kim Sam yace dole shi zaiyi. Shi kuma boka Ruguzan hadimin sarki Ayubu ne, don haka tafiya nemo sarki Ayubu ta zamo masa dole.
Saboda waɗannan dalilai babu buƙatar tambaya, waɗannan bokaye guda biyu zasu amince da wannan shawara ta sarki Kim Sam.
Nan take suka tsayar da magana akan cewa zasu tafi nemo sarki Ayubu a duk inda a faɗin duniya sannan wannan ɓangare da wannan guguwa tayi jifa dashi, nan za su bi.
Sarki Kim Sam ya kirawo wannan jibgegen shaho nasa ya haye kansa, shi kuma Biu Lin ya shimfiɗa dardumar tsafinsa, suka hau kanta shi da Ruguzan.
Nan take suka tashi sama cikin iska suka ɓangaren da sarki Ayubu yayi, suna masu tsala azababben gudu a cikin gajimare.
****
Yau *31/12/2022*
Babi na gaba zaizo *02/01/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 65-66: *Garuruwa Hudu*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A.
*
(The man with the sense of Adventure)
*
~Bangaren Yarima Marganu.
*
Nan take suka hango wadansu irin mutane a kofar shiga wannan gari. Mutanen gajeru ne sosai domin a cikinsu da wuya a samu wanda zai kai kugun gimbiya Firziyya a tsaho.
Ba sa dauke da makaman yaki amma sunyi shiga irinta mayaka, wani gajeren sadauki na tsaye a gabansu sanye da kayan sarauta masu ado da zubar daji.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su Marganu da wadannan mutane, tsahon dan lokaci babu wanda ya cewa dan uwansa uffan.
Wannan gajeren mutum dake sanye da kayan sarauta ya tako sawayensa ya nufo inda su Marganu ke tsaye shi daya jal, ba tare da wadannan mayaka sun biyo bayansa ba.
Yana isowa gaban su Marganu ya kare musu kallo, su ma suka kalle shi da kyau.
"Tun da nake mulkin wannan gari namu, ban taba ganin mutane irinku ba. Shin ku samudawa ne ko kuma adawa da muke karantawa a littatafan tarihi?" inji wannan gajeren basarake.
Idan mutum ya kwatanta tsahon wadannan mutane da na su Marganu mutum zai ga cewa, don wannan basarake yayi musu wannan tambaya ba abin mamaki bane.
Sai dai muryar basaraken bata iya magana sosai cikin wannan harshe da ya yiwa su Marganu magana da shi ba. Watakila bai kware a wannan yare bane, ko kuma ya dade baiyi zance da yaren ba.
"Duniya na da fadi," inji Marganu. "Mu ma mamakin ganin mutanen irin ku muke, saboda tunda muke yawo a duniya bamu taba ganin irin wannan gari naku ba."
Cikin tsananin mamaki wannan sarki ya gyada kai sannan ya dubi Marganu ya ce, "Shin zan san abinda ke tafe daku wanda yasa kuka ratsa ta cikin garuruwa guda uku masu mugun hadari?"
Kai tsaye Marganu ya ce masa, "Muna son zuwa garin Temisa ne domin dauko takobin sadauki Gayawa-jini wadda yake yiwa lakabi da tarwatsa-komai, wannan shi ne abinda ke tafe da mu."
"Hmm," wannan basarake yayi murmushi. "Garin fa Temisa fa ka ce?" Marganu ya gyada masa kai.
"Da garuruwa uku na farko da hudu na karshe duk bayin sadauki Gayawa-jini ne mu. Dukkanin mu da a cikin garin Temisa muke rayuwa amma sakamakon bayyanar wadannan halittu da suka fatattaka mu, sai muka shiga duniya kowa ya kama gabansa.
"Gaba daya mutanen kabilata gajeru ne, bayan dogon lokaci nayi tunani akan wannan gari namu sai naga ai kamata yayi ace mun dawo wannan gari muna shirye-shiryen sake kwato birnin mu daga hannun wadannan halittu.
"Daga baya, bayan mun gudanar da zurfin bincike a halwar tsafi muka gano cewa, ba mu isa mu sami nasara akan wadannan halittu ba, saboda akwai wani dalili wanda bamu san mene ne ba.
"Wannan abu yayi mugun bata min rai ba kadan ba, na tara dukkanin sauran kabilu na basu shawara akan 'me zai hana mu kafa garuruwan mu akan hanyar zuwa garin Temisa' watakila ko hakan zai sa wataran 'ya'yanmu su samo hanyar da zasu dauki fansa akan wadannan halittu.
"Mutane suka amince da wannan shawara tawa, daga wannan lokaci muka kafa garuruwanmu. Babu wanda tsautsayi ya taba dauko shi ya kawo shi yankin wannan garuruwa namu face ku din nan.
"Shin kun fafata da mutanen gari na farko, na biyu da na uku? A tsammanina ku ukun nan kunyi kadan ku ragargaza su?" inji wannan gajeren sarki.
Marganu ya yi murmushi ya ce, "Inda ace bamu ratsa ta cikin wadannan garuruwa ba, na tabbata da baza ka ganmu a wannan wuri ba. Tun da burinku shi ne karkashe wadannan halittu meye zai hana ka aikawa dukkanin wadannan sarakuna dake garuruwan gaba su bude mana mu wuce, na tabbata zamu ragargaji wadannan halittu harma mu kwato muku garinku."
Gajeren sarkin ya hade fuska ya ce, "A ce kun kwato wannan gari, abinda kuke son dauka yafi wannan gari da zaku kwato daraja. Saboda wannan zai sa baza mu barku ku wuce ba."
Marganu ya yi dariya ya ce, "Haba da gaske? Mu wuce wadancan garuruwa guda uku da bakaken dazuzzuka sannan ace an tsayar da mu anan, zai yiwu kuwa?"
"Ba sai ta kaimu ga zubar da jini ba, zan tura a kirawo wadannan sarakuna guda hudu. Kowanne daga cikinmu zai shirya muku gasa guda daya. Idan kuka yi nasara a wadannan gasanni guda hudu, zamu barku ku wuce cikin garin Temisa lafiya."
"Zancen banza kenan!" inji Marganu cikin tsawa. "Ku na tunanin zamu yarda ku bata mana lokaci ne?"
Wannan gajeren sarki yayi murmushi ya ce, "Na tabbata kafun ku wuce ta cikin wadannan garuruwa guda uku, kun sha bakar wahala. Idan har da farko kun sha wannan wahala, kuyi tunanin wahalar da zaku sha a cikin wadannan garuruwa guda hudu?
"Zan ba ku dama ta tsahon sa'a guda kuyi shawara akan abinda ya dace. Amma kafun nan, ku sani cewa, abinda sulhu bai samar ba, tashin hankali da bala'i ba zai samar ba. Sai mun sake hadewa a gaba."
Wannan gajeren sarki na gama fadin haka, ya juya ya nufi cikin mutanensa.
A fusace Marganu ya zare takobinsa zai bi bayan wannan sarki amma sai yaji hannun gimbiya Firziyya ta dafa kafadarsa daga baya ta jawo shi. A hasale ya juyo ya kalle ta.
"Kayi hakuri masoyina, tabbas wannan sarki yazo mana da tayi mai kyau. Meye amfanin fada da zubar da jini idan har akwai hanyar da za'a bi a sulhunta?" inji Firziyya.
Marganu ya girgiza kai ya ce, "Wannan ba zai yiwu ba. Aikin dake gaban mu ba wasa bane, wannan mataki da muke kai shi ne, mataki na farko. Idan muka tsaya bata lokaci za'a iya samun matsala. Ko ya kace tsoho?"
Aydenlik ya yi gajeren tunani ya ce, "Ya shugabana, a ganina shawarar da gimbiya tazo da ita, ita ce daidai. Tun kafun mu faro wannan tafiya ance mana babu wanda ya taba ratsowa a cikin wadannan garuruwa guda bakwai. Babu wanda yasan masifu da bala'in dake cikin su.
"Mun ratso ta cikin garuruwa uku na farko mun gwabza azababben yaki da arna, mun kashe na kashewa mun fatattaki wasu. Mun shigo cikin bakaken dazuzzuka mun gwabza mummunan yaki da dabbobin daji da kuma dodanni.
"A ganina idan ma wasa takobinka kake so kayi, a cikin wuraren da muka baro a baya ka wasa. Ba mu san bala'in da zamu tarar a gaba ba, idan kai zaka iya kare kanka daga kowanne bala'i, kayi tunanin mu.
"A ganina ya kamata ka duba wannan lamari kafun ka yanke hukunci?"
Marganu na jin batun Aydenlik jikinsa yayi sanyi, tabbas duk abinda dan tsohon ya fada haka ne.
Gimbiya Firziyya ta sake duban Marganu ta ce, "Sannan bamu san wacce irin gasa ce zasu zo mana da ita ba. Watakila gasar kwakwalwa ce bata zubar da jini ba."
"Hmm," Marganu yayi murmushi. "Bana jin haka. Tunda kun amince da abinda wannan sarki yazo da shi, ban isa nayi jayayya da ku, ku biyu ba. Nima amince za'a yi wannan gasa, amma ina da sharadi guda."
Marganu ya dan yi shuru ya tattaro hankalin Aydenlik da na Firziyya ya ce, "Kamar yadda ya ce, gasanni guda hudu za'a shirya. Ni a matsayina na shugaba a wannan tafiya tamu zan karbi gasanni guda biyu, sannan kuma dole ne kowanne daga cikinku ya karbi gasa guda-guda? Idan kun amince da wannan sharadi nawa yanzu zan kira wannan sarki na sanar dashi cewa, mun amince. Idan kuwa baku amince ba, yanzun takobina zata sha jini."
Marganu na gama fadin haka ya dora hannunsa kan takobinsa, yana jira su Aydenlik suyi jinkiri kadan ya zarota ya ruga kan wadannan arnan daji.
Aydenlik da Firziyya suka dubi juna cikin jimami. Komai shirinka da yarda da kanka idan baka san abinda zaka tunkara ba, sai ka razana. Zasu iya cewa sun amince zasu karbi gasa guda-guda da za'a shirya, to wadanne irin gasanni ne?
Rashin sanin amsoshin waɗannan tambayoyi shi ne zai yi matukar birkitawa su Aydenlik lissafi.
Har Marganu ya fara yin murmushi yana kokarin zaro takobinsa saboda jin shurun da suka yi. Caraf suka ce, mun amince cikin hadin baki.
Marganu ya yi gajeruwar dariya sannan ya daga hannunsa sama ya kirawo wannan sarki dake tsaye a can nesa tare da dakarunsa.
Dakaru guda hudu suka tako masa baya ya sake dawowa gaban su Marganu ya tsaya.
"Mun amince da sharaɗin shirya waɗannan gasanni kamar yadda kazo mana da shi ɗazu." inji Marganu.
Gajeren sarkin yayi murmushi ya ce, "Suna na sarki Wadu. Tabbas kunyi shawara mai kyau da baku yi tunanin afka mana da yaƙi ba. Ba wai don muna jin tsoronku bane, sai domin muna da wani babban kafi wanda sadauki Gayawa-jini ya bamu tun kafun yayi ƙaura. Idan muka saka wannan kafi a ƙofar shiga garin mu, babu uban da ya isa ya shigo mana gari, komai ƙarfin sa da shirinsa kuwa!"
Marganu ya yi murmushi kamar yana ƙwaƙwanton wannan magana ta sarki Wadu. Sarkin na fuskantar haka yayi murmushi sannan ya juya ya nufi cikin garinsa, ya cewa su Marganu su biyo bayansa.
Ba tare da shakku

Please Login or Register in order to submit comment