Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zana taswirar duniya akanta ya baiwa Samudul Ansari.
Boka Ƙaizadu ya nunawa Samudul Ansari wata doguwar hanya wadda ta ratsa ta cikin manyan biranai guda uku ya ce, "Idan kuka bi wannan hanya, zata kai har daular Gorgon.
"Kada ku yada zango a cikin kowanne birni dake kan wannan hanya taku, koda kuwa kun iso birnin ne da tsakar dare.
"Kuyi hankali da Gorgon saboda shaiɗancinsu yafi ƙarfin kan bil'adama."
Boka Ƙaizadu yana zuwa nan a zancensa ya dubi waɗannan dawakai da suke kai ya ce, "Waɗannan dawakai ba za su iya kai ku tsakiyar duniya ba, saboda tafiyar akwai nisa. Sannan ana so a wannan tafiya ku zage damtse banda yawan yada zango, ko kuma rashin sauri."
Yana zuwa nan a zancensa ya shuƙa waɗansu ƙananun takardu a cikin ƙasa.
Dai-dai inda ya shuka waɗannan takardu yayi haske, sannan waɗansu irin dawakai ingarmu suka bayyana.
Waɗannan dawakai, ba kamar sauran dawakai suke ba. Idanuwansu na haske ne, sannan kofatonsu ma na haske ne.
Boka Ƙaizadu ya fiddo wata zabgegiyar adda daga cikin jakar tsafinsa ya baiwa Samudul Ansari ya ce, "Wannan adda ita ce kawai zata iya nasara akan mutanen ƙabilar Gorgon a yanzu. Kada ka yaƙe su da kowanne irin makami idan ba wannan adda ba.
"Waɗannan su ne gudunmawata a yaƙi da ƙabilar Gorgon. Fatan nasara..."
Sarauniya Arya ta dafa kafaɗar boka Ƙaizadu ta ce, "Tabbas ka bayar da gagarumar gudunmawa, daular Shaha ba zata taɓa mantawa da kai ba..."
Boka Ƙaizadu yayi murmushi sannan ya koma cikin wannan kogon tsafi nasa.
Sarauniya Arya da Samudul Ansari suka hau kan waɗannan dawakai na sihiri da ya samar musu, suka kaɗa linzamin dawakan sannan suka hau hanya kamar yadda suke gani a jikin wannan taswira.
Waɗannan dawakai na da ban al'ajabi, suna da tsananin gudu domin zasu iya ninka asalin ƙarfin gudun doki sau goma, sannan duk wannan ƙarfin gudu nasu, iskar dake kan hanya bata damun wanda ke zaune akansu.
Samudul Ansari da sarauniya Arya suka ji wani aminci a ransu bisa ganin falalolin waɗannan dawakai. Tabbas boka Ƙaizadu ya bayar da gagarumar gudunmawa.
Saboda ƙarfin gudun waɗannan dawakai, yan-fashi ko muggan dabbobin daji basa samun yiwa su Samudul Ansari kyakkyawa kallo suke wucewa.
Sarauniya Arya tayi ta satar kallon Samudul Ansari tana so yayi mata magana, amma ga dukkan alamu hankalinsa baya kanta ma balle ya ce da ita wani abu.
Samudul Ansari irin mutanen nan ne, waɗanda indai ba kai ka fara yi musu magana ba, sai ku shekara ɗari basu ce da kai komai ba.
Jim kaɗan dai, haƙurin sarauniya Arya ya ƙare, ta dube shi ta ce, "Ji mana!"
Samudul Ansari ya waiwayo kaɗan ya dube ta.
Arya ta ce, "Wai kai baka magana ne? Tun safe muke ta tafiya yanzu har wajen Azahar amma baka ce dani komai ba..."
Samudul Ansari yayi guntun murmushi ya ce, "Ni haka nake. Tun ina yaro ƙarami ban kasance mai yawan magana ba.
"Ko ba komai kefa sarauniyata ce, kuma shugaba ta. Bai kamata na dame ki da yawan surutu ba..."
Sarauniya Arya tayi murmushin jin daɗi ta ce, "Ai a yanzu kaine shugabana saboda wannan tafiya a hannunka take. Idan babu kai, babu wannan tafiya. Duk duniya kaine kaɗai kake da ƙarfin zuciyar shiga daular Gorgon ba tare da tsoron komai ba.
"Ba ka lura da cewa boka Ƙaizadu kai yake yiwa bayanan wannan tafiya ba, saboda shi kansa ya cika da tsananin mamakin baiwarka."
Samudul Ansari yana jin wannan batu yayi murmushi baice komai ba.
Sarauniya Arya ta sake dubansa ta ce, "Yanzu bani labarin rayuwarka mana, yadda ka taso da irin wahalhalun da ka sha..."
Koda Samudul Ansari yaji abinda sarauniya Arya ta ce sai jikinsa yayi sanyi, idanuwansa suka sauya launi.
Kamar ta taɓo masa wani tsohon abu wanda ya daɗe yana damun zuciyarsa.
"Kayi haƙuri idan har wannan tambaya da nayi maka ta sosa maka rai," inji sarauniya Arya.
Samudul Ansari ya kaɗa kai ya ce, "Ko kaɗan wannan tambaya bata sosa min rai ba, amma ta tuno min da wani gagarumin abin baƙin ciki wanda ya taɓa faruwa a rayuwata."
Cikin tsananin mamaki sarauniya Arya ta ce, "Wanne abin baƙin ciki ne, ya taɓa faruwa a rayuwarka, bani labari mana..."
Samudul Ansari ya dubeta tsahon ɗan lokaci yana tunani. Wannan labari da take so ya bata, baya baiwa kowa shi face wanda ya yarda shi, saboda wani ɓangare ne na rayuwarsa.
Sarauniya Arya kyakkyawar gaske ce, saboda tsananin kyawunta da kuma kamalar dake kan fuskarta. Mutum yana ganinta zai san cewa mutumiyar kirki ce wadda bata yi kama da mugaye koda da ƙwayar zarra.
"Iyaye na talakawa ne, bamu da komai a duniya hatta abincin da muke ci kullum sai mun nema..." Samudul Ansari ya fara bata labarin rayuwarsa.
"Mahaifina yana da ƙani wanda suke uba ɗaya, mai kuɗi ne. Duk faɗin waɗannan ƙauyuka guda uku, babu wanda yayi rabinsa a kuɗi.
"Amma abin takaici shi ne, mu da ya kamata ace muna jin daɗin wannan dukiya tasa amma mu yafi muzgunawa da ita.
"Wannan ƙanin mahaifi nawa, yana da ɗa guda ɗaya wanda ake kira Gauhan.
"Gauhan saurayi ne kuma jarumi. Tsakani na da shi bama ga maciji.
"Babban abinda ya haddasa gaba tsakanina da shi, ita ce yarinya Zarifa.
"Zarifa yarinya ce budurwa mai kimanin shekaru goma sha-takwas. Ƴar wani mutumi ne a ƙauyen mu masunci (mai kamun kifi) da ake kira Sahes.
"Akwai gagarumar soyayya tsakani na da Zarifa tun tana shekaru goma na kamu da tsananin ƙaunarta, sa'adda ta girma ta cika budurwa sai na sanar da ita abinda ke raina.
"Tsahon shekaru uku kenan, muna ta gudanar da soyayya a tsakanin mu.
"Shekarar da ta wuce ne, Gauhan yayi arba da ita. Tun daga wannan lokaci shima ya haukace akan sai ya aureta.
"Gauhan da mahaifinsa gawurtattun attajirai ne, saboda haka suka fara amfani da kuɗi wajen saye zuciyar Zarifa ta guje ni sannan ta auri Gauhan.
"Tabbas na cika da tsananin mamaki bisa ganin cewa, abin duniya bai ruɗi Zarifa ba har kullum ni ne kaɗai a cikin ranta.
"Tabbas wannan abu yayi matuƙar burgeni sannan na tabbatar da cewa, Zarifa masoyiyata ce ta haƙiƙa kuɗi ko wani abin duniya ba zai sa ta guje ni ba.
"Koda Gauhan da mahaifinsa suka fuskanci cewa, ba zasu iya saye soyayyar Zarifa ba, sai suka fara ƙulla mana tuggu ni da mahaifina a wajen sarkin dake mulkin wadannan ƙauyuka guda uku.
"Yanzu muna zamani wanda babu mai gaskiya sai mai kuɗi. Sarkin waɗannan ƙauyuka namu muka ga ya fara muzguna mana, ba'a daɗe ba ya ƙara mana kuɗin haraji wanda yayi matuƙar wargaza mana lissafi.
"Shekarar da ta wuce Ubangiji ya albarkace mu da yin noma wanda ya bunƙasa sosai, muka sami amfani har wajen rumbu uku.
"Sati biyu kafun wannan lalura ta sami mahaifina, da tsakiyar dare aka cinnawa waɗannan rumbuna namu wuta, ana so a mayar damu wawaye mu ɗauka gobara ce ta ƙone su, alhali kuma mun san aikin Gauhan ne.
"Babban abin baƙin cikin da bana son tunowa shi ne, saura kwanaki uku wannan lalura ta sami mahaifina, Gauhan ya tare Zarifa da dare a hanyar da take tsakanin ƙauyen Salwaza da ƙauyen Zumur."
Samudul Ansari yana zuwa nan a zancensa muryarsa ta sauya izuwa mai kaushi wadda take cike da baƙin ciki da kuma alhini.
"Gauhan ya yiwa Zarifa fyaɗe wanda ya illata ta sosai. Yanzu haka mahaifinta ya ɗauketa ya tafi da ita wajen sarkin-ruwa na wannan daula gaba ɗaya domin yayi mata magani.
"Ban san cewa wannan lalura ta ritsa da su, ko bata ritsa da su ba. Tun da mahaifinta ya kasance mai yawan hulɗa da koguna."
Lokacin da Samudul Ansari yazo nan a zancensa sai tausayinsa ya kama sarauniya Arya sannan daga bisani wani irin azababben kishi ya turnuƙe ta wanda yayi matuƙar bata mamaki da kuma girgiza ta.
"Wannan shi ne taƙaitaccen labarina, bana faɗawa mutane face na yarda da su. Dan girman abin bautarki, ki bar wannan abu sirri a ranki, kada ki sanar da kowa..."
Sarauniya Arya ta ce, "Kada ka samu damuwa, akwai aminci a tsakanin mu wanda zai sa na ajiye duk wani sirri da ka sanar da ni.
"Tabbas bayan komai ya lafa, zan hukunta attajiri Daran da ɗansa Gauhan, sannan zan karrama ka na baka dukiya mai yawan gaske tare da babban matsayi a..." Sarauniya Arya ta gagara ƙarasa kalamanta saboda tuno cewa akwai wadda Samudul Ansari yake so.
Ko kaɗan wannan bai damu Samudul Ansari ba, kuma bai yi wani tunani akai ba, saboda shi a ganinsa magana da Arya ma, sai cikakken mutum a wannan daula.
Tuni sarauniya Arya ta kamu da tsananin son Samudul Ansari, tun sa'adda tayi arba da shi lokaci na farko.
Irin wannan siffa ta Samudul Ansari kallo ɗaya yake sace zuciyar mace, sai dai ta bar abin a ranta kawai.
"Ke kuma mene ne labarin ki?" inji Samudul Ansari cikin murya ƙasa-ƙasa kamar yana ganin matsayinsa bai kai ya yiwa sarauniya Arya wannan tambaya ba.
Waɗansu hawaye masu zafi suka zubo daga idanun sarauniya Arya amma kasancewar hankalin Samudul Ansari baya kanta, kwata-kwata bai lura ba.
"Tasowa nayi cikin gata da daula, ban san wahala ko kaɗan ba. Komai da komai yi min ake yi.
"Tun ina yarinya ƙarama na taso da baiwa ta kyawu, hakan yasa dubbannin sarakuna suka ɗinga zuwa birnin mu neman aurena.
"Tun ina shekaru goma sha-huɗu ake zuwa da ƴaƴan sarakuna, ƴaƴan attajirai da ƴaƴan manyan jarumai neman aure wajena.
"Amma ban taɓa ganin wanda ya kwanta min a rai ba.
"Har wannan shekara da ta wuce, akwai ɗan hamshaƙin sarkin da yazo neman aurena amma bai yi min ba.
"Ni kaina na rasa mene ne dalilin da yasa samari basa burge ni, har na fara tunanin anya bani da wata matsala kuwa?
"Wannan yasa na kaiwa boka Ƙaizadu ziyara a shekarun baya, yayi mini bincike inda ya tabbatar min da cewa, bana tare da wata matsala wanda zan aura ne kawai bai bayyana ba.
"Wannan batu nasa yayi matuƙar ɗugunzuma min hankali, domin ban gane abinda yake nufi ba.
"Tabbas a kwanakin nan, jikina yana bani cewa wanda boka Ƙaizadu yake magana a kai ya bayyana.
"Sai dai bayyanar nasa ta sake ɗugunzuma min hankali..."
Da sauri Samudul Ansari ya juyo ya dube ta ya ce, "Wane ne wannan wanda yafi kowa dacewa a duniya... Ga ki sarauniya ga ki kyakkyawa, ga dukiya ga ƙarfin mulki?"
"Hmm," sarauniya Arya tayi murmushi ta gagara baiwa Samudul Ansari amsa.
Koda ganin haka sai ya ayyana a ransa, wataƙila matsayinsa bai kai ya san wanda zai zamo mijin sarauniya na gobe ba.
Suka ci gaba da tafiya, ba tare da ɗayansu ya sake cewa uffan ba.
Har suka iso cikin babban birni na farko wanda yake kan hanyar zuwa daular Gorgon.
Birni ne ƙaton gaske wanda yake da ɗaukar hankali sosai.
Ba su yi nisa a cikin wannan birni ba, suka sami labarin bayyanar wata sabuwar cuta a bakin wani mayaƙi wai shi Nurbas.
Nurbas ya bayyana yanayin wannan cuta wanda yayi daidai da yadda suka baro gida.
Samudul Ansari ya bayyana masa cewa, daular Gorgon zasu je nemo maganin wannan cuta.
Mayaƙi Nurbas yaso ya bisu wannan tafiya amma mahaifinsa ya ƙi yarda. Dukda cewa yaji baƙin ciki sosai, amma a haka ya danne saboda bin umarnin iyayensa.
Wannan birni ana kiransa da suna Hawaruɗ.
Samudul Ansari da sarauniya Arya suka wuce birnin Hawaruɗ sannan suka sake kama hanya.
Suka ci gaba da tafiya tsahon kwanaki sannan suka ratsa ta cikin waɗannan garuruwa guda biyu dake gaba. Nan ma suka sake iske cewa duk wannan annoba ta shafe su.
Kwanci-tashi suka iso daular Gorgon wadda gari na farko wanda mutum zai fara riska a wannan daula shi ne, birnin Mesa.
Birnin ƙaton gaske ne wanda aka kewaye da ganuwa mai tsahon gaske.
A bakin ƙofar shiga wannan gari, akwai dakaru masu yawan gaske dake gadi.
A can saman ƙofar akwai wata toliya wadda aka kafa tuta mai ɗauke da hoton kan mutum da gashin macizai.
Tambarin ƙasashen Gorgons kenan. Duk inda mutum yaga irin wannan tuta tana nuni da cewa, birnin a ƙarƙashin ikon Gorgons yake.
Sarauniya Arya ta dubi Samudul Ansari ta ce, "A dai-dai ina tsaunin Hajarul Gorgon yake? Idan da nisa fa kasan zamu sha wahala sosai kafun mu riski wajen?"
Samudul Ansari ya fiddo wannan taswira wadda boka Ƙaizadu ya bashi ya dubata.
Daga bisani ya ɗago kai ya dubi Arya ya ce, "Wannan birni da muke gabansa sunansa Mesa, idan muka shiga cikin wannan birni akwai ɓarauniyar hanya wadda zata kaimu har tsakiyar wannan daula, inda Hajarul Gorgon yake."
Samudul Ansari yana zuwa nan a zancensa suka jiwo takun sawaye an tunkaro inda suke, cikin gaggawa suka ɗaga kansu sama.
Nan take suka hango gungun dakaru kimanin mutum ɗari, ɗauke da makaman yaƙi na tunkaro su.
Gaba ɗaya mayaƙan Gorgons ne masu gashin macizai.
****
Yau *20/02/2023*
Babi na gaba zaizo *23/02/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 88: *Hajarul Gorgon*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U*M*S
*
Samudul Ansari ya dubi sarauniya Arya ya ce, "Ki tsaya a inda kike, kada ki motsa, bari na fara kawar da waɗannan mayaƙan..."
Samudul Ansari yana gama faɗin haka ya zaro wannan zabgegiyar adda wadda boka Ƙaizadu ya bashi, sannan ya yiwa wannan doki nasa ƙaimi ya tunkari waɗannan mayaƙa da gudu.
Yana isowa inda suke suka ruguntsume da azababben yaƙi mai matuƙar ban tsoro da sanya firgici.
Samudul Ansari ya wanzu yana kaiwa waɗannan mayaƙa sara da suka da wannan zabgegiyar adda dake hannunsa, su kuma suna karewa da waɗansu irin garkuwowi dake hannunsu masu irin wannan tambari na wannan tuta.
Nan fa faɗan nasu ya soma daɗin kallo, domin waɗannan mayaƙa gaba ɗayansu sun ƴanƴame Samudul Ansari a tsakiya, shi kuma yana ta kai musu sara da wannan zabgegiyar adda.
Tsahon ɗan lokaci suna ta wannan gumurzu, ba tare ɗayansu ya sami nasara ta azo a gani ba.
Lamarin da yayi matuƙar fusata waɗannan mayaƙa kenan, saboda ɗaya daga cikinsu ma na iya hallakar da mutum ɗari a cikin rabin sa'a.
Ya ya za'a yi mutum ɗari su gagara hallaka mutum ɗaya?
Abinda basu sani ba fa shi ne, yau sun haɗu da gamonsu domin babban mayaƙi wanda aka daɗe ba'a gani ba ya shigo daular Gorgon.
Gashin kan waɗannan mayaƙa ya soma juyewa yana komawa macizai.
Samudul Ansari na ganin haka, ya gyaɗa kai, ya daka tsalle ya fice daga tsakiyar su ya tsirga acan gefe guda.
Duk wannan gumurzu da ake sarauniya Arya tana zaune akan dokinta acan gefe guda tana kallo, tuni jarumtakar Samudul Ansari tayi matuƙar burgeta.
Bayyanar waɗannan macizai akan waɗannan mayaƙa yasa zafin namansu da ƙarfin damtsen su ya ragu ainun.
Biyu daga cikinsu suka falfalo da gudu izuwa kan Samudul Ansari, suna ɗaga takubban dake hannunsu.
Samudul Ansari ya tsaya a inda yake bai motsa ba, har waɗannan mayaƙa suka ƙaraso.
Ɗaya daga cikinsu ya daka tsalle ya kawo masa sara a kafaɗa, ɗayan kuma ya kai masa sara ta ƙasa daidai tumbinsa.
Cikin zafin nama Samudul Ansari ya daka tsalle baya, waɗannan mayaƙa suka sari iska.
Samudul Ansari yayi amfani da wannan adda tasa, ya fille kan mayaƙi na farko wanda ke durƙushe a gabansa, sannan ya laftawa wanda ke tsaye a nesa sara a kafaɗa.
Kamar walƙiya haka wannan adda ta ratsa cikin sassan jikin waɗannan mayaƙa, sannan aiwatar da aikinta akansu.
Kan wannan sadauki dake durƙushe a ƙasa ya tashi sama, kafaɗar wannan wanda ke tsayen nan ta fashe hannunsa ya fara jalo-jalo kamar zai faɗi ƙasa.
Wannan sadauki bai san sa'adda ya kurma uban ihu ba, sannan ya zube ƙasa kan gwiwowinsa yana kukan azaba.
Gaba ɗaya waɗannan sauran mayaƙa dake tsaye a can baya, suka zaro idanu cikin tsananin mamaki.
Tun da wannan daula tasu ta kafu, mutum ɗaya kawai aka taɓa kashewa, ba wata bace illa wannan budurwa da ta fita yawon duniya a shekarun baya wadda manyan sarakuna suka haɗa kai suka kasheta.
A wancan lokaci ba wani damuwa aka yi da rayuwarta ba, amma dukda haka sai da daular Gorgon ta fusata.
Meye wannan saurayi yake taƙama dashi da har zai shigo cikin babbar daular Gorgon wanda kowa da kowa a duniya ke tsoro?
Me yake taƙama da shi da har zai kashe mutanen ƙabilar Gorgon waɗanda suke tsaron babban birnin Mesa?
Wacce irin takobi wannan saurayi yake amfani da ita, wadda take karkashe Gorgons ba tare da jinkirin komai ba?
Amsar waɗannan tambayoyi su ne abinda waɗannan mayaƙa suke jira, kuma shi ne dalilin da ya hana su afkawa Samudul Ansari.
Samudul Ansari ya juya ya dubi sarauniya Arya yayi mata murmushi, nan take ta mayar masa martanin murmushin mai nuna jinjina bisa wannan gagarumar jarumtaka da ya yi.
Waɗannan mayaƙa suka sake turo mutane hamsin daga cikinsu, suka rugo da gudu kan Samudul Ansari suna kwarara uban ihu mai razanarwa.
Idanuwan waɗannan mayaƙa suna ta haske da walwali mai matuƙar ɗaukar hankali da sanya razana a idanun mai kallon su.
Maimakon wannan ya razanar da Samudul Ansari, murmushi yayi kawai sannan ya daka tsalle ya bangaji mutane huɗu dake kan gaba ya faɗo a tsakiyar su.
Nan fa suka sake ruguntsumewa da azababben yaƙi mai matuƙar razanarwa.
A wannan lokaci Samudul Ansari wanzuwa yayi a tsakiyar waɗannan dakaru yana ta ragargazar su, jinin jikinsu da sassan jikinsu na ta shawaƙi a sama sannan suna zubowa ƙasa tamkar tsummokara.
Duk yawan waɗannan dakaru aka rasa mutum ɗaya wanda zai sami damar koda lakutar jikin Samudul Ansari saboda tsananin zafin namarsa.
Wani lokacin sai kaga yayi wani irin juyi a tsakiyar waɗannan mayaƙa, yayi amfani da wannan adda dake hannunsa ya tarwatsa da yawa daga cikinsu.
Wani lokacin kuma, sai kaga yayi amfani da ƙarfin damtsensa ya dafe su da hannunsa guda ya tura su baya, sannan ya yi amfani da addar nan ya fille kawunan da yawa daga cikinsu.
Tun da waɗannan mayaƙa suke basu taɓa bala'i irin na wannan rana ba, saboda Samudul Ansari cikakken jarumi ne wanda yake yaƙi domin nemawa kansa yanci.
Kafun a ɗau wani lokaci, tuni Samudul Ansari ya hallaka waɗannan sadaukai guda hamsin waɗanda aka turo masa.
Sauran na ganin haka suka ja da baya a tsorace.
Babbar cikinsu wadda ta kasance wata kyakkyawar budurwa ta falfalo da azababben gudu kan Samudul Ansari, tana ɗaga wata zabgegiyar takobi dake hannunta mai siffar maciji.
Macizan dake kan wannar budurwa sun fi na dukkan waɗannan mayaƙa girma da kwarjini.
Tana ƙarasowa inda Samudul Ansari yake, suka ruguntsume da azababben yaƙi.
Wannan budurwa ta wanzu tana kaiwa Samudul Ansari muggan sara da suka cikin baƙin zafin nama wanda yafi gaban tunanin mutum.
Cikin daƙiƙa ɗaya tana iya kai masa sara sau uku ko ma fiye.
Samudul Ansari gawurtaccen jarumi ne, wanda ya karɓi horon yaƙi mai wahalar gaske a wajen wani babban mayaƙi.
A wannan zamani komai iya yaƙin mutum indai mutum yana da irin wannan horon yaƙi na Samudul Ansari ba zai yi shakkar sa ba.
Wannan na daga cikin dalilan da suka sa Samudul Ansari ya sayar da rayuwarsa ya shigo wannan daula saboda ya yarda da kansa.
Bai taɓa tsammanin zai haɗu da gawurtaccen mayaƙi wanda zaizo da salon yaƙi na dabam tun a wannan gari na farko ba.
Wannan ya tabbatarwa Samudul Ansari cewa, lallai ya shigo daular mayaƙa, waɗanda suke da tsananin horo na yaƙi.
Idan ace wannan horon masu tsaron ƙofa ne? Ya ya horon manyan sarakuna da masu iko da wannan daula zai kasance?
Samudul Ansari ya ayyana a ransa, dole ne fa ya zage damtse idan ba haka kuwa, zasu yi zuwan banza sannan su fusata suje daular Shaha su kashe dukkan jama'ar cikinta su mamaye komai da komai.
Samudul Ansari yana cikin wannan tunani a ransa, wannan budurwa ta samu nasarar danƙara masa sara a kafaɗa.
Nan take wani azababben zogi ya shige shi, sannan wani irin dafi mai ƙarfin gaske ya soma yawo a cikin jikinsa.
Irin wannan takobi dake hannun wannan budurwa basu da bambanci da macizai.
In dai suka sari jikin mutum da irin wannan takobi, tamkar maciji ne ya sari mutum haka mugun dafi zai fara yawo a cikin jikin mutum.
Kai gwanda ma ace maciji ne ya sari mutum, domin yafi sauƙi.
Waɗannan takubba ana tsuma su da dafin macizai wajen kala dubu.
Duk wanda aka kalli kalar wannan takobi a hannunsa, to babban mayaƙi ne wanda ake ji dashi a wannan daula gaba ɗaya.
Ko daƙiƙu ɗari da tamanin basu shuɗe ba, wani irin mugun jiri ya soma ɗiban Samudul Ansari ya fara layi tamkar zai faɗi ƙasa.
Amma abinka da gawurtaccen jarumi wanda yake da tsananin ƙarfin damtse, sai ya turje ya tsaya a inda yake.
Wannan dafi yaci gaba da cin jikinsa har tsahon daƙiƙu ɗari uku da arba'in amma bai kai shi ƙasa ba.
Sarauniya Arya tana ganin haka, ta fara kuka tana zubar da hawaye, saboda bata so ko kaɗan wani abu ya samu Samudul Ansari.
Wannan budurwa ta ƙurawa Samudul Ansari ido cikin tsananin mamaki.
A tarihin irin wannan takobi dake hannunta indai suka sari jikin halitta mai jini da ita, iya daɗewar da zata yi a duniya, daƙiƙa sittin ne.
Ya ya aka yi Samudul Ansari bai mutu ba?
Shin wannan dafi baya aiki a jikinsa kenan?
Lallai idan masu iko da wannan daula suka sami labarin wanda ya kuɓuta daga sharrin irin wannan takobi, zasu ɗauki mataki na musamman.
Wannan budurwa ta kwarara uban ihu, ta dubi wannan takobi dake hannunta sannan ta dubi Samudul Ansari ta ce.
"KAINE KAƊAI WANDA WANNAN TAKOBI TA MU DA MUKE KIRA [BANKAI] BATA HALLAKA A CIKIN DAƘIƘA SITTIN BA.
"TABBAS KO MA DA ME KUKA ZO WANNAN DAULA, MUN FI ƘARFINKU.
"IDAN TAKOBIN BANKAI MAI MATAKI NA UKU BATAI NASARA AKAN KA BA, AI MAI MATAKI NA HUƊU ZATA HALLAKA KA..."
Wannan budurwa tana cin wannan alwashi, ta ɗaga wannan takobi dake hannunta, macizai guda huɗu

Please Login or Register in order to submit comment