Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayar da kariya.
Marganu ya zaro takobinsa ya kwarara uban ihu sannan ya ruga da gudu kansu, ya hau su da sara da suka babu ƙaƙƙautawa. Kafun a jima tuni ya gama da su gaba ɗaya.
Marganu ya sa takobinsa ya sare ƙofar shiga wannan gari sannan suka kunna kai izuwa cikin garin, nanma suka yi ta fafatawa da irin waɗannan halittu jefi-jefi.
Abinda suka fuskanta shi ne halittun dake cikin wannan gari, sun fi waɗanda ke wajen garin ƙarfi da iya yaƙi da kuma baƙar juriya.
Domin sai an ɗan kai ruwa rana, kafun a kashe su.
Su Marganu basu yi wata doguwar tafiya suka iso tsakiyar wannan gari, inda suka tarar da wani dogon gini wanda babu buƙatar a sanar da mutum 'gidan tarihi' ne.
A ƙofar babu ko badakare guda, hasalima ƙofar a buɗe take wanwar.
Ba tare da tsoro ko shakkun komai ba, Marganu, Firziyya da Aydenlik suka danna kai izuwa cikin gidan.
Gidan a cike yake da kayayyakin tarihi, kamar fatun dabbobin daji da suka yi zamani suka shuɗe da kuma makaman yaƙin mutanen zamanin da.
Komai dai na tarihi akwai shi a cikin wannan gida. A tsakiyar gidan suka kalli wani ɗaki guda ɗaya tal a kulle da garƙamemiyar ƙofa.
Cikin gaggawa su Marganu suka ƙarasa bakin ƙofar shiga wannan ɗaki suka tsaitsaya. A jikin ƙofar akwai zanen ƙwarangol ɗin bil'Adama da farin fenti.
Gimbiya Firziyya tasa hannunta guda ta tura wannan ƙofa da nufin ta buɗeta. Nan take wannan zane yayi farin haske, wata iska mai ƙarfin gaske ta fito daga cikin wannan ɗaki tayi jifa da ita.
Gimbiya Firziyya ta hantsila baya cikin iska, ta faɗo kan ƙasusuwar wata dabba. Bayanta ya bugu da ƙarfi, a gaggauce Marganu da Aydenlik suka ruga inda take suka tallafo ta.
Aydenlik ya bata ruwan magani mai kashe zogi ta sha. Marganu ya dubeta a hasale ya ce, "Daga yau idan ba umarni na baki ba, kada ki sake yin karambani, kin ji ko? A banza zan iya rasa ki!!!" Ya ƙarasa maganarsa ƙasa-ƙasa domin ya nuna mata fushinsa.
"Kayi haƙuri masoyina!" inji Firziyya a lokacin da take miƙewa tsaye.
Marganu ya wuce bakin wannan ƙofa ya dafa wannan hatimi dake kan damtsensa, take jikinsa ya juye izuwa haske sannan yasa hannunsa guda ya tura wannan ƙofa.
Wannan iska mai ƙarfi wadda tayi jifa da gimbiya Firziyya ta sake tahowa amma ta ɗinga wucewa ta cikin jikin Marganu tamkar haske take ratsawa, babu abinda ya same shi har ta gama wucewa.
A hankali wannan ƙofa ta fara buɗewa, har ta gama wangamewa gaba ɗaya.
Wani narkeken ƙaton mutum suka hango zaune a gaban wani tudu wanda aka caka takobin Tarwatsa-Komai akansa.
Kan mutumin na damisa ne sannan yana riƙe da zabga-zabgan takubba guda biyu a hannayensa. Yana ganin su Marganu sun buɗe wannan ƙofa ya ƙura musu idanu da jajayen idanunsa.
Ga dukkan alamu wannan mutumi shi ne shugaban waɗannan halittu.
Marganu ya dubi Aydenlik da Firziyya yayi musu inkiyar su koma da baya, kada su kuskura su shiga wannan gumurzu da zai yi.
Aydenlik da Firziyya suka ja da baya suka koma tsakiyar wannan gida suka tsaya.
Babu wata cacar baki Marganu ya zaro takobinsa ta haske ya ƙaddamar da baƙin haske a matsayin ƙarfen takobin, wannan halitta na ganin haka ya zaro zabga-zabgan takubbansa guda biyu ya tunkaro Marganu.
Yana isowa inda Marganu yake suka fara zabga azababben yaƙi mai tsananin razanarwa.
Wannan narkeken ƙato yayi ta kaiwa Marganu muggan sara da suka da waɗannan takubba nasa.
Ba don Marganu ya kasance mai tsananin zafin nama ba, da tuni ƙaton yayi daga-daga da namansa.
Nan fa wannan narkeken ƙato ya hana Marganu sakat, ta ko'ina muggan sara yake kai masa.
A duk lokacin da takubbansa suka haɗu da takobin haske ta Marganu sai an kwarara uban tsawa sannan wannan gidan tarihi gaba ɗayansa yayi jijjiga.
Kafun a jima tuni tukwanen dake ɗauke da abubuwan tarihi sun fara zubowa ƙasa, ƙura ta fara tashi.
Ana cikin haka wannan sadauki ya samu damar danƙarawa Marganu kyakkyawan sara a gadon baya, jini yayi feshi.
Marganu ya kwarara uban ihu. Wani irin takaici ya rufe shi. Shi da yake neman ganin bayan gogaggen mayaƙi kamar Kuffuru ace irin waɗannan halittu suna wahalar dashi?
Zuciyar Marganu ta fara tafarfasa, wannan sadauki na ƙarasowa inda yake, Marganu ya zille ta tsakankanin sawayensa sannan ya daka tsalle ya fizgo takobin Tarwatsa-Komai daga kan wannan tudu da take cake.
Hannunsa na taɓa takobin, aka sake kwararo wata tsawa tamkar aradu guda goma ne suka zubo a tare.
Wannan sadauki na ganin haka ya sake rugowa kan Marganu yana wani ihu, tamkar baƙar damisa wadda take jin ƴunwa.
Marganu ya riƙe wannan takobi da kyau, sannan ya cakata a ƙasa. Nan take ƙasar wannan wuri ta fara girgiza kamar zata rufta.
Wannan sadauki ya yanki jiki ya faɗi daga kanta. Kafun ya miƙe Marganu ya danƙara masa sara a kafaɗa.
Wata gagarumar ƙara ta bayyana, jikinsa yayi bindiga yayi filla-filla tamkar wanda aka daka a turmi.
Ƙarfin takobin Tarwatsa-Komai kenan, duk abinda aka sara da ita dagargajewa zai yi.
Marganu ya ɗaureta a kunkuminsa sannan ya fito daga cikin wannan ɗaki ya nufi inda su Firziyya ke tsaye.
Yana zuwa suka kalli wannan takobi a kunkuminsa sai farin ciki ya lulluɓe su, suka yi tayi masa barka.
Ba tare da ɓata lokacin komai ba, suka fice daga cikin wannan gari na Temisa suka tunkari inda ake gwabza yaƙi tsakanin su sarki Wadu da irin waɗannan halittu.
Suna isowa suka iske tuni an gama karkashe dukkanin dakarun sarki Wadu da waɗannan sarakuna guda uku, sarki Wadu ne kaɗai yayi saura.
Da ƙyar da siɗin goshi Firziyya ta shawo kan Marganu yayi amfani da wannan takobi ya hallaka sauran halittun nan wato ya ceci rayuwar sarki Wadu.
****
Yau *21/01/2023*
Babi na gaba zaizo *23/01/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 75: *Marganu vs Infiron*
*
DEDICATED TO AS USUAL ZAHRA.
*
NATURE LOVER
*
Sarki Wadu ya zaro takobinsa ya dubi Marganu ya ce, "Babu amfanin ceton rayuwata da kayi a yanzu, saboda an riga da an gama kashe dukkanin jama'ata da kuma iyalaina. Ba zan iya rayuwa a duniya ni kaɗai ba.
"Abokan gabata da na shafe tsahon lokaci, ina mummunan shiri akansu sun riga sun ƙare. Abin kunƴa ne a gareni, ace kun shigo har yankinmu kun ɗauke takobin shugabanmu kun tafi da ita akan idanuna, saboda haka ba zan ci gaba da rayuwa ba!"
Sarki Wadu na zuwa nan a zancensa ya cakawa kansa wannan takobi, take ya zube ƙasa yana ta shure-shure. Ko kallonsa Marganu bai sake yi ba, ya kama hannun Firziyya ya ja ta suka tafi. Aydenlik ya take musu baya.
Suka bar wannan fili cike maƙil da gawarwakin mutane, jini yana ta yawo a tsakaninsu tamkar kogi.
Aydenlik ya dubi Marganu ya ce, "Shi kenan. Har an shafe babin waɗancan mutane daga duniya fa?"
Marganu ya yi murmushi ya ce, "Ɓatan basira ce tasa suka dawo kusa da abokan gabarsu suka ci gaba da rayuwa..."
Kafun ya rufe bakinsa, wani irin haske mai kashe idanu ya bayyana a sararin samaniya a nesa kaɗan da su.
Aydenlik da Firziyya basu da ikon kallon cikin wannan haske, saboda baiyi musu kama da komai ba face hasken rana.
Shi kuwa Marganu babu abinda wannan haske yake yi masa, dukda cewa idanunsa na tsaye cak akan hasken.
Wannan haske ba wani bane a cikinsa face aljanin Marganu, aljani Isika. Aljanin Haske.
Isika ya sauƙo ƙasa a hankali, sannan ya rage hasken dake jikinsa wanda yake kashewa su Firziyya idanu, ya tsaya a gaban Marganu.
"Tsahon wannan lokaci da muka shafe muna wannan tafiya, ko sau ɗaya baka taɓa bayyana ba. Shin ka san irin wahalhalun da muka shiga kuwa?" inji Marganu.
Aljani Isika ya yi murmushi ya ce, "Idan ba haka nayi muku ba, tayaya zan gane cewa zaku iya kashe gawurtaccen sarkin da babu kamarsa a duniya?"
Marganu yayi murmushi ya gyaɗa kai ya ce, "To, naji. Yanzu ya aka yi?"
Aljani Isika ya ce, "Dama nazo ne domin na tayaka murnar mallakar wannan gawurtacciyar takobi wadda zata dagulawa sarki Kuffuru lissafi. Sannan na ɗaura ku akan hanyar zuwa inda kogon Rohishmu yake, inda zaka sha wannan tsumi wanda zai ƙara ɗaukaka kimarka a fannin tsafi."
Marganu ya ce, "To, muna jin ka wacce hanƴa zamu bi, mu je wannan wuri?"
Isika ya gyaɗa kai sannan ya ce, "Ba wannan ba ma tukunna, sarki Kuffuru da sarauniya Rauziyya sun san da cewa, baka mutu a garin arnan daji ba. Sannan kowanne daga cikinsu ya fara yi maka mummunan shiri, saboda sun san cewa barinka a raye ba zai haifar musu da ɗa mai ido ba."
Marganu na jin wannan batu maimakon ya girgiza ko kuma ya ɗaga hankali, murmushi kawai yayi ya ce, "Idan aka ce sarki Kuffuru da Rauziyya basu san cewa ina raye ba, ba zan yarda ba. Saboda gawurtattun matsafa ne.
"Wannan ba wani abun damuwa bane. Ka ɗaura mu akan hanya kawai. Tabbas tun da mun mallaki takobin Tarwatsa-Komai, idan muka sha wannan tsumi babu wanda zamuyi shakka a duniya."
Aljani Isika yayi murmushi cikin jin daɗin wannan ƙarfin zuciya na Marganu ya ce, "Ku na ficewa daga yankin baƙaƙen fata, hanƴar da tayi kudu wato wacce ta ratsa ta cikin birnin Bahzam kuyi ta tafiya, tsahon wata guda zaku iso wani ƙaton kogon dutse. To, nan ne inda tsumin boka Rohishmu yake.
"Lallai idan kuka isa wannan wuri, nima zan bayyana a gareku mu shiga cikin kogon tare." Aljani Isika yana zuwa nan a zancensa ya ɓace ɓat.
Marganu ya baiwa su Firziyya umarnin ci gaba da tafiya. Nan take suka ɗauki hanya.
Da yake akan sawayensu suke tafiya, suna isowa wani ƙauye. Marganu ya shiga kasuwa ya sayo musu dawakai guda uku ya kawo.
Suka hau dawakan sannan suka yanki daji. Tafiya babu dare ba rana, kullum a cikin tafiya suke har suka fice daga nahiyar baƙaƙen fata gaba ɗaya.
Kamar yadda Isika ya umarce su haka suka yi, wato suka kama hanyar kudu wacce zata kaisu wannan ƙaton kogo bayan sun ratsa ta cikin birnin Bahzam.
Tsahon wannan tafiya da suka yi, ko ƙatuwar dabbar daji guda ɗaya basu fafata gumurzu da ita ba. Tafiya suke cikin kwanciyar hankali har suka iso wannan birni na Bahzam.
Birnin Bahzam yanki daga cikin yankunan biranen ƙasar Hindu. Saboda haka mutanen garin irin shigar mutanen birnin Hindu ce da su.
Babu wanda su Marganu suka cewa wani abu har suka iso tsakiyar wannan gari, dukda cewa duk inda suka wuce sai jama'a sun bisu da kallo kuwa.
Suna isowa tsakiyar wannan gari ne, Marganu ya hango wani baƙin abu na tahowa daga can sararin samaniya. Amma saboda tsananin nisan dake tsakaninsu da abun, baya iya shaida ko mene ne.
Da farko Marganu bai ɗauki wannan abu komai ba, ya sauƙe kansa suka ci gaba da tafiya.
Bayan ƴan daƙiƙu ya sake ɗaga kansa sama, bisa mamaki ya sake ganin wannan abu na tunkaro su. A wannan lokaci wannan abu ya ƙara girma sosai, siffarsa tana kama da mutum-mutum aljani-aljani.
Saboda haka Marganu ya ƙaddamar da idanunsa na haske domin ganin mene ne.
A gaggauce Marganu yaja linzamin dokinsa ya tsayar da shi cak! Lamarin da yasa Firziyya da Aydenlik tsayar da nasu dawakan kenan, suka dubi Marganu cikin tsananin mamaki suna so su tambaye shi dalilin da yasa ya tsayar da dokinsa.
Kafun ɗayansu ya buɗi baki ya ce wani abu, tuni gagarumin baƙin hadari ya taso a wannan birni na Bahzam. Hadari ne irin wanda aka jima ba'a gani ba, domin ya tare hasken rana garin gaba ɗaya ya soma yin duhu.
Nan take aka soma kwararo tsawa da walƙiya tamkar tashin duniya za'a yi.
Mutanen wannan gari suka firgice suka soma guje-guje suna komawa cikin gidajensu, suna kulle ƙofofi.
Firziyya ta matso daf da Marganu ta ce, "Masoyina! Mene ne abinda ke faruwa muka ga ka tsayar da dokinka, sannan muka wannan sauyin yanayin?"
Marganu ya dube su ya ce, "Duk abinda zai faru a yanzu, kada ɗayanku ya kuskura ya ce zai kawo min ɗauki, domin duk wanda yayi gangancin hakan, zai rasa rayuwarsa. Ku koma gefe ku zuba mana idanu kawai! Lallai muna da baƙo a wannan birni."
Koda Aydenlik da Firziyya suka ji kalaman Marganu sai suka kaɗa dawakansu suka koma gefe guda suka tsaitsaya.
Jim kaɗan, wani abu daga sararin samaniya ya faɗo ya doki ƙasa da ƙarfi. Ƙasa ta rufta ciki, wannan abu ya faɗa cikinta.
Dawakan su Firziyya suka fara haniniya suna faman zubar da su ƙasa. Da ƙyar suka iya shawo kan dawakan.
Wani baƙin hayaƙi ya soma tasowa sama daga cikin wannan rami, kafun daga bisani ya soma juyewa izuwa siffar wani garjejen mutum mai sura ta sadaukai.
Tsahon daƙiƙu siffar mutumi tana ta haɗewa a waje guda, kafun ta gama haɗewa ta bayar da ainihin siffar sa.
Gimbiya Firziyya tana ganin mutumin tsikar jikinta ya fara tashi, kanta ya fara mummunan sarawa ta fara kallon duhu-duhu.
Hatta shi kansa Marganu sai da yayi mummunan girgiza bisa ganin wannan mutumi. Saboda bai taɓa kawowa a ransa, zasu haɗu cikin sauƙi haka ba.
Mutumin a sanye yake da baƙaƙen tufafi masu kama da likkafanin mutanen farko. Dukda cewa akansa akwai hular sanyi amma hakan bai hana su ƙarewa fuskarsa kallo ba.
Tabbas wanda ke tsaye a gabansu ba wani bane, illa sarki Kuffuru mahaifin Firziyya wanda ya kashe mahaifin Marganu da hannunsa.
Abinda yayi matuƙar basu mamaki kuma ya girgiza su shi ne, kwata-kwata hankalin sarki Kuffuru baya kan gimbiya Firziyya tamkar bata wajen.
A ganinsu idan har zai yi musu irin wannan zuwa ta bazata, to, babu wanda zai fara hukuntawa kamar Firziyya saboda yarsa ce ta cikinsa.
Idanunsa na tsaye cak! akan yarima Marganu koda sau ɗaya bai kalli inda Firziyya take ba.
Hakan ne ya fara sanyawa Firziyya kwakwanto a cikin ranta, akan cewa anya wannan asalin mahaifinta ne kuwa?
Marganu ya zaro takobin tarwatsa-komai daga kunkuminsa, rugugi da ƙara daga ɓangarori dabam-dabam na wannan birni suka soma tasowa.
Wannan sadauki na ganin haka ya zaro takobin Siwod-del-bulod daga gadon bayansa.
Gimbiya Firziyya ta gyara zama akan wannan doki nata, sannan ta ƙurawa wannan mutumi mai kama da mahaifinta idanu domin ta tantance shi.
Marganu ya dube shi ya ce, "Ina ganin kamar kayi gaggawa da ka kawo kanka inda muke, da jira kayi muka je muka sameka da kanmu. Amma ba wani abu hakan ma yayi."
Shuru wannan mutumi baice dashi uffan ba, kawai ƙura masa idanu.
Marganu na ganin haka shima ya fara kwakwanto amma dukda bai yarda da abinda zuciyarsa ke raya masa ba. Wataƙila sarki Kuffuru yana so yayi amfani da wannan dama ne, ya nuna kamar mutum-mutumi ne ya cutar da shi.
Marganu ya kwarara uban ihu, ya ruga da gudu kan wannan sadauki suka ruguntsume da azababben yaƙi.
Suka yi ta kaiwa junansu sara da suka cikin ƙwarewa ko alamun sassauta basa yi.
Wannan sadauki yana amfani da takobin Siwod-del-bulod, shi kuma Marganu yana amfani da takobin tarwatsa-komai.
Saboda wani dalili wanda babu wanda ya sani face shi kansa Marganu, baiyi amfani da takobin haske ba.
A duk lokacin da takobin Marganu ta haɗu da ta hannun wannan sadauki sai an kwararo uban tsawa, gidajen wannan gari da bishiyoyi suyi girgiza tamkar zasu zube ƙasa.
Dawakan su Aydenlik suka firgice suka yi ta haniniya suna tutsu tamkar zasu zubar da su ƙasa.
Gimbiya Firziyya ta sauƙa daga kan wannan doki ta zauna a ƙasa, sannan ta ci gaba da ƙurawa wannan gumurzu idanu.
Tsahon rabin sa'a suna ta fafatawa amma ko sau ɗaya wannan sadauki baiyi haki ba.
Sannan zafin namansa yafi gaban kwatancen mutum. A cikin daƙiƙa guda yana iya kaiwa Marganu sara sau uku ko ma fiye.
Tabbas Marganu ba ƙaramin namijin ƙoƙari yayi da ya ɗauki lokaci mai tsaho yana fafata wannan gumurzu da wannan sadauki ba.
Koda wannan sadauki ya fuskanci ba zai sami nasara akan Marganu ba, idan suka ci gaba da wannan gumurzu a haka saboda jarumtakar Marganu da juriyarsa.
Saiya daka tsalle baya, ya fara ƙarewa Marganu kallo daga sama har ƙasa.
Firziyya ta dubi Aydenlik ta ce, "Wancan mutumin ba mahaifina bane!!!"
Cikin tsananin mamaki Aydenlik ya dubeta ya ce, "Saboda wanne dalili kika ce haka, ga shi a fuska da komai yana kama da mahaifinki?"
Firziyya ta ce, "Saboda idan da ace mahaifina ne da tuni ya kai Marganu ƙasa yanzu!"
Aydenlik ya haɗe fuska ya ce, "Ban gane ba?"
Firziyya ta sake cewa, "Shin ka manta cewa mahaifina gawurtaccen jarumi ne?
"Shin ka manta abinda aljani Isika ya ce mana ne? Marganu ba zai taɓa samun nasara akan mahaifina ba, har sai ya hallaka aljani Djinn.
"Sannan matsayin da mahaifina yake a yanzu a harkar tsafi Marganu bai kai nan ba. Shi kansa Marganu ya fara fuskantar haka."
Aydenlik ya yi shuru yana tunani sannan yana kallon wannan mutumi kuma yana jinjina maganganun Firziyya.
Firziyya ta sake cewa, "Ka duba yadda kwata-kwata bai damu dani ba, tamkar ban kasance ƴar cikinsa ba.
"Anya akwai uban da zai yiwa yarsa abinda wannan yayi min kuwa?"
Aydenlik na jin haka ya sake tabbatar da abinda Firziyya ta ce masa.
A ɓangaren su Marganu kuwa, a tare suka rugo da gudu kan juna suna kwarara uban ihu. Koda ya rage saura bai wuce taku huɗu su haɗu ba, sai duk suka daka tsalle sama suka kawowa junansu muggan sara.
Marganu bai kaucewa wannan takobi ba, amma ya juyar da jikinsa izuwa haske. Shima wannan sadauki bai kaucewa takobin Marganu ba.
Takobin Siwod-del-bulod ta ratsa ta cikin jikin Marganu ta wuce. Takobin bata ji masa raunin komai ba, amma jini mai yawa yayi feshi daga bakinsa.
Haka shima wannan sadauki takobin tarwatsa-komai tana ratsawa ta cikin jikinsa, ya haɗe fuska alamar wannan takobi tayi masa mummunar illa ta ciki.
Dukkaninsu babu wanda baiji a jikinsa ba, sakamakon wannan mugun gamo da suka yi.
Marganu ya durƙushe kan gwiwowinsa ya caka wannan takobi tasa a cikin ƙasa domin ya tallafi kansa kada ya faɗi.
Wannan sadauki ya sake rugowa da gudu kan Marganu yana ɗaga wannan takobi tasa sama, da nufin yayi filla-filla da sassan jikin Marganu tunda Marganu na durƙushe a ƙasa.
Ya kawowa Marganu wawan sara a kafaɗa, saura ƙiris takobi ta dira a kafaɗar Marganu yayi wani irin juyi cikin zafin nama ya daka tsalle ya faɗo bayan wannan sadauki.
Marganu ya danƙara masa sara a gadon baya, sadaukin ya sake haɗe alamar wannan sara yayi masa illa ta ciki.
Wannan sadauki baya ƙwala ihu idan aka ji masa rauni, sai dai fuskarsa ta nuna alamun wahalar da ya sha.
Marganu tuni ya riga ya gano wannan sadauki ba sarki Kuffuru bane, kuma tuni ya riga ya gano hanyar da zai bi ya ɗinga cutar da sadaukin.
Nan take wannan faɗa nasu ya sake dawowa sabo, a duk lokacin da wannan sadsauki ya kaiwa Marganu sara, sai ya goce cikin zafin nama sannan ya danƙara masa a kafaɗa ko kuma a gadon baya.
Kafun a jima tuni Marganu ya gallabi wannan sadauki ya hana shi sakat.
Dukda cewa mutum-mutumi ne shi, amma wannan takobi dake hannun Marganu mai ƙarfin gaske ce. In dai ya sari jikinsa, sadaukin ji yake kamar zai tarwatse yayi daga-daga.
Saboda haka ko kaɗan baya so wannan takobi ta ɗinga taɓa jikinsa.
Suka ci gaba da gumurzu har tsahon wasu sa'a guda biyu. Marganu bai tarwatsa wannan sadauki ba, shi kuma sadaukin bai ji wa Marganu koda rauni guda ɗaya ba.
Sa'an biyun na shuɗewa Marganu ya yiwa wannan sadauki wani mahaukacin sara a gadon baya. Sadaukin ya daka tsalle baya, fuskar a murtuƙe ya ƙurawa Marganu idanu.
Bakinsa ya fara motsawa a hankali yana karanto ɗalasiman tsafi waɗanda babu wanda yasan abinda yake faɗa.
Marganu ya falfala da azababben gudu kansa, yana kwarara uban ihu. Aydenlik da Firziyya dake gefe guda, suka fara murmushin jin daɗi da samun nasara, don sun tabbatar da cewa lallai ƙarshen wannan taƙadarin sadauki yazo.
Sadaukin ko motsawa baiyi ba, balle ya fara wani shiri na kaucewa Marganu. Kawai ci gaba da karanto waɗannan ɗalasimai yayi.
Marganu na ƙarasowa gabansa ya kai masa wawan sara a kafaɗa, cikin kwanciyar sadaukin ya kauce, takobin Marganu ta sari iska.
Kafun Marganu ya juyo tuni wannan sadauki ya rungumo shi ta baya, a lokacin da ya gama karanta waɗannan ɗalasimai.
Wata irin baƙar guguwa mai tsananin ƙarfi ta taso wacce ta tashi hankalin dukkanin halittun dake rayuwa a cikin wannan birni. Guguwar ta kanannaɗe wannan sadauki da Marganu sannan tayi jifa dasu sama cikin iska.
Tun su Aydenlik suna hango Marganu har ya ɓace ɓat! a cikin gajimare.
Gimbiya Firziyya ta durƙushe kan gwiwowinta ta fashe da kuka, Aydenlik yazo yana lallashinta.
****
Yau *23/01/2023*
Babi na gaba zaizo *26/01/2023* da yaddar ALLAH
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 76: *Kyawun Sarauniya ARYA II*
*
SADAUKARWA GA MASOYA...
*
ALLAH KA KAWO MANA SAUƘI A ƘASARMU NIGERIA :'(
*
Copyright @umarsangaru
*
~Aymanul Faris
*
Su Aymanul Faris basu bayyana a ko'ina ba, sai a tsakiyar fadar aljani Ranganu. Aljanin na zaune akan karagar mulkinsa, yana ganin sun bayyana ya nuna musu waɗannan kujeru ya ce su zauna akai.
Babu musu suka zazzauna, Ranganu ya dubi waɗannan furannin dake hannun Aymanul Faris ya yi murmushi ya ce, "Ina tayaku farin ciki bisa samun nasarar tsinko waɗannan furanni, yanzu abinda ya rage shi ne gabatar da waɗannan furanni ga gimbiya ARYA.
"Amma kafun nan, ku fara zuwa birnin Darul Barban domin Aymanul Faris ya tattauna da mahaifiyarsa akan wannan sabon abu da ya ɓullo musu!
"Daga nan sai Aymanul Faris ya wuce birnin Damashkar wajen masoyiyarsa ya gabatar mata da waɗannan furanni. Idan kuka kammala waɗannan ayyuka sai ku dawo wannan fada tawa domin na sanar da ku aiki na shida, wanda shi ne na ƙarshe a jerin 'wajibabbu'."
Lokacin da Ranganu yazo nan a zancensa sai farin ciki ya lulluɓe su Aymanul Faris.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, suka yi sallama da Ranganu. Barban ya saka waɗannan aljanu nasa guda uku, suka ɗauke su suka ɓace dasu.
A tsakiyar birnin Darul Barban suka sauƙa, aljanun suka yi sallama da maigidansu suka ɓace ɓat.
Shima aljani Nara sai ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Zan koma gidana, idan ka gama tattaunawa da mahaifiyarka zanzo na ɗaukeka na kai ka birnin Damashkar wajen sarauniyar Arya!"
Aymanul Faris ya gyaɗa masa kai, aljanin ya ɓace ɓat.
Barban, Aymanul Faris da jaruma Riya suka yi ta kutsa kai, cikin birnin Darul Barban. Duk inda suka wuce sai ayi ta gaishe da su har suka iso wannan unguwa ta Barbanul Kuyur inda mutanen ƙauyen Gazwar gaba ɗaya suka tare.
Suka yi ta tafiya har suka iso wannan gida wanda aka sauƙar da mahaifiyar Aymanul Faris a cikinsa.
A cikin wannan ƙaton falo suka sameta tana zaune, bayan sun gama gaisawa Barban ya koma wani ɓangare daban na wannan gida ya basu dama domin su tattauna.
Aymanul Faris ya sunkuyar da kansa ya ce, "Kiyi haƙuri umma, ƙaddara tasa dole sai

Please Login or Register in order to submit comment