Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ƙara gigita Anbalu ya ƙara gudunsa ya tunkari inda yake jiwo ihun mazaje.
"Bai daɗe ba yana wannan gudu ya iso, wata unguwa a cikin birnin Ranayes wadda mafi yawa daga cikin gidajen da suke cikinta ƙango ne.
"A wannan unguwa ya iske mayaƙa masu yawan gaske sun haɗu a waje guda sai ragargazar juna suke. Anbalu na ganin haka gabansa ya sara, babu abinda ya fara faɗo masa a rai kamar sarauniya Rana.
"Anbalu bai kasance sadauki ko jarumi ba, balle ya ce zai ratsa ta cikin waɗannan dubbannin mayaƙa har ya isa tsakiyarsu yaga abinda ke faruwa. Amma saboda ziyarar da ya kai duniyar iska ya zamo gawurtaccen matsafin da ba zai yi shakkar shiga kowanne irin bala'i ba.
"Anbalu ya ƙaddamar da waɗannan korayen idanu nasa sannan ya nuna waɗannan mayaƙa da hannunsa guda na hagu, nan take wata iska mai tsananin ƙarfi ta ɗauke su gaba ɗaya tayi jifa dasu can nesa.
"Waɗansu mutane guda shida suka bayyana waɗanda suke fafatawa da wata jaruma guda ɗaya. Abin mamaki wannan jaruma ba wata bace illa sarauniya Rana, waɗannan mutane guda shida kuma yan majalisarta ne masu adawa da mulkinta.
"Sarauniya Rana tana riƙe da zabgegiyar takobi a tsakiyar waɗannan mutane suna ta kafsa yaƙi. Dukda cewa Rana ba ƙaramar jaruma ba ce, amma waɗannan dakaru sunyi mata raunika har guda uku a sassan jikinta. Biyu a gadon bayanta ɗaya kuma a damtsen hagu.
"Dukda cewa jini na zuba amma sarauniya Rana ta ƙi faɗuwa saboda tsananin jarumtaka, sai dai jiri ya soma ɗibarta a kowanne lokaci zata iya faɗuwa. Waɗannan jarumai na gab da ƙarasata kenan, Anbalu ya ƙwala mata kira da ƙarfi.
"Cikin tsananin farin ciki ta waiga, Anbalu ya jeho mata wannan allon tsafi. Rana tana ganin allon ta ɗaga hannunta sama, kamar mayen-ƙarfi haka hannunta ya zuƙo wannan allon tsafi.
"Ƴan majalisar suna ganin wannan allon tsafi ya shiga hannunta, cikinsu ya ɗuri ruwa. Ko ita kanta sarauniya Rana da ta kasance yar sarkin da ya samar da wannan allon tsafi bata kai waɗannan yan majalisa sanin ƙarfinsa ba. Saboda da yawa daga cikinsu manya ne waɗanda suka rayu tun a zamanin sarkin.
"A gigice dukkaninsu suka juya da baya da nufin su gudu, sarauniya Rana tayi murmushi ta rataya wannan allon tsafi a wuyanta sannan ta nuna su da hannu guda. Nan take sarƙoƙin baƙin ƙarfe suka fara bayyana suna kanannaɗe su tun daga sawayensu har zuwa wuyansu.
"Sauran dakarun da suka rage suna ganin haka, suka durƙusa bisa gwiwowinsu alamun miƙa wuya.
"Sarauniya Rana ta ruga da gudu ta rungume Anbalu tana tayi masa godiya bisa ceton rayuwarta da yayi.
"A gaban jama'a akan idanun kowa sarauniya Rana ta fille kan waɗannan maciya amana yan majalisarta, sannan aka ɗaura mata aure da Anbalu a wannan wuri.
"Anbalu da Rana suka ci gaba da rayuwa irinta ma'aurata cikin farin ciki har tsahon wata guda. Sa'adda Anbalu ya san Rana ya mace, sai wannan sirrin tsafi wanda ya samu a duniyar ya ninku wajen sau dubu.
"Lokacin da sarauniya Rana da Anbalu suka cika kwanaki arba'in da yin aure sai alamun ciki ya soma bayyana a wajen sarauniya Rana. Duk da cewa Anbalu yayi murna sosai amma sai ya nemi alfarma wajen matar tasa akan yana so ya koma gida ya ƙwato iyalansa da sarki Halad ya tsare a kurkuku.
"Saboda tsananin yadda Rana ta shaƙu dashi kuka ta fara yi, saboda ko kaɗan bata so yayi nisa da ita, sannan bata so ta hana shi komawa izuwa gida saboda ba ƙaramin halacci yayi mata ba da ya amince da wannan sharaɗi sannan yaje ya karɓo wannan allon tsafi, sannan ya amince ya aureta dukda cewa yana da mata da yawa a can wani wuri.
"Saboda haka ta amince masa akan yayi wannan tafiya, Anbalu ya shaida mata cewa, duk bayan mako biyu zai na zuwa wannan birni nata ya kwana biyu sannan koma.
"Anbalu ya koma yankin Barban lafiya, amma sai ya tarar da mutanensa a cikin wani mummunan hali domin kuwa sarki Halad yayi mugun ƙuntata musu har da yawa sun rasa rayukansu saboda muguwar azabar da suka sha.
"Kai tsaye Anbalu ya wuce wannan gidan kurkuku inda aka tsare matansa da 'ya'yansa. Yana zuwa gidan kurkukun ya nuna shi da hannunsa guda, nan take ginin ya soma tarwatsewa ɗakunan fursunoni suka soma bayyana.
"A taƙaice dai, wannan dawowa da Anbalu yayi ita ce ta kawo ƙarshen sarki Halad da zaluncinsa. Bisa dole aka ɗaura Anbalu akan karagar mulki.
"Wannan azababben yaƙi da aka gwabza tsakanin Meher da Deher shi ne ya kawo ƙarshen zaman mutane a wannan yanki na Barban. Saboda Anbalu yaga daular Shaha kanta ta karye, wannan yasa ya tattara sauran jama'arsa da iyalansa ya mayar da su birnin Ranayes suka ci gaba da rayuwa.
"Har yau, har gobe suna cikin wancan birni na Ranayes suna rayuwa cikin kwanciyar hankali.
"Anbalu shi ne kakana na uku. Koda yake ya kwashe mutanensa ya mayar dasu wancan birni, amma akwai ragowar yaƙi waɗanda ya manta dasu. Nima ina cikinsu, domin kuwa tun kafun a yi wannan yaƙi muka koma ƙauye da iyayena.
"Wannan shi ne yadda aka yi ƙabilata ta Aswad ta sami ɗaukaka a duniya. A halin yanzu don mutum ya ce babu wanda ya kaimu ƙarfin sihirin tsafi baiyi laifi ba.
"Tun daga wancan lokaci hadiman aljanu kala-kala dabam suke ta yi mana hidima.
"Meyasa na baku wannan hikaya? Saboda na bayyana muku ƙarfina a yanzu, ku tabbatar da cewa nafi ƙarfin a kama ni a duniya saboda na gawurta.
"Sannan saboda na sanar da ku matar da zan aura ta bayyana itama. A cikin zuri'ar sarki Anbalu da sarauniya Rana an samu wanda ya haifi wata gimbiya wai ita HELINA.
"Gimbiya Helina ita ce matar da zan aura na sake ƙarfafa sirrin tsafin dake jikina. A halin yanzu itama tana can cikin birnin Ranayes."
****
Yau *26/12/2022*
Babi na gaba zaizo ranar *29/12/2022* da izinin mai duka.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 63: *Shirin sarki Ayubu*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
UMAR SANGARU
*
Sarki Ayubu da su sarki Kim Sam suka ci gaba da tafiya a cikin sararin samaniya, suna durfafar inda su sarki Kuffuru suka nufa. Duk bayan rabin sa'a sai boka Biu Lin yayi bincike a madubin tsafinsa domin ganin inda su sarki Kuffuru suke.
Hakan ne ya bashi damar ganin inda su sarki Kuffuru suka yada zango a wannan daji. Biu Lin ya nunawa su sarki Ayubu wannan sansani na su Kuffuru da wuraren da suka kakkafa tantunan su.
Abin mamaki suna gama kallon wannan sansani wannan madubin tsafi ya ɗauke, ya daina nuna hotunan komai.
"A banza kenan," inji boka Biu Lin yana dariya. "Wai, sun ɓoye abinda ke faruwa a wannan sansani alhalin ba su san cewa mun ga komai ba."
Sarki Ayubu yayi dariya ya ce, "Daga wannan wuri da muke tafiyar kwana na nawa ce ta rage mu isa wancan sansani nasu?"
Boka Biu Lin ya ɗan yi murmushi ya ce, "Gobe i warhaka zamu isa inda su sarki Kuffuru suke harma mu gwabza da su."
"Idan haka ne ya kamata mu fara tsare-tsaren yadda zamu farmake su daga yanzu." inji sarki Kim Sam.
"Hmm," sarki Ayubu yayi murmushi. "Wanne tsare-tsare kuma? Ni ai tuni na gama shirye-shiryena tun kafun na fito wannan tafiya."
Boka Ruguzan ya dube shi ya ce, "Ya shugabana, ai cewa kayi kai. Tun da ka gama shirya musu sai ka bari muma muyi namu shirin."
Sarki Ayubu yayi murmushi ya gyaɗa kai alamun amincewa. Nan take wannan jibgegen shaho dake ɗauke da shi da sarki Kim Sam ya saki fuka-fukinsa ya dira a ƙasa. Yana sauƙowa wannan darduma dake ɗauke da su boka Ruguzan ta sauƙa a gefensa.
Boka Biu Lin ya samar da ƙaramin tanti a gabansu, shi, boka Ruguzan da sarki Kim Sam suka shige cikin tantin. Sarki Ayubu kuma, ya zagaya ta bayan wani dutse ga dukkan alamu wata buƙata zai kawar.
Suna shigowa cikin wannan tanti, sarki Kim Sam, boka Ruguzan da Biu Lin akan waɗansu kujeru guda uku da suka ƙaramin teburi guda ɗaya.
Boka Biu Lin ya sake samar da irin wannan madubin tsafi wanda ke ɗauke da sansanin su sarki Kuffuru a cikin sa.
Wannan sansani na ɗauke da tantuna guda biyar waɗanda aka yiwa siffar da'ira. Sannan akwai tarin itace masu ci da wuta a tsakiyar sansanin waɗanda suke baiwa sansanin ɗumi sakamakon sanyin da ake.
Boka Biu Lin ya nuna tantuna guda biyu na farko ya ce, "Duk yadda aka yi a cikin waɗannan tantuna guda biyu, sarki Darwazu ne da sarauniya Rauziyya." Ya sake nuna tantuna guda uku dake ƙarshe ya ce, "Waɗannan kuma duk aka yi na sarki Kuffuru ne da boka Hubbazu da kuma aljani Sheezuwa.
"Abinda yasa na ce haka shi ne, tun kafun sarki Kuffuru ya haɗu da su sarauniya Rauziyya kullum yana tare da su boka Hubbazu. Babu waɗanda suka san shirye-shiryensa kamar su Hubbazu saboda haka kullum zai kasance tare da su domin ganin sun taimaka masa wannan shiri nasa ya cika.
"Saboda haka mu ɗauka kawai sarki Kuffuru yana cikin waɗannan tantuna na ƙarshe, sannan wannan taswira tana hannun aljani Sheezuwa don yanzu shi ne abinda suka dogara da shi sosai.
"Wanne shirye-shirye da tsare-tsare zamu fito musu da shi? Kowa daga cikin mu ya faɗi shawararsa domin ganin mun samu nasara a wannan aiki."
Sarki Kim Sam da boka Ruguzan suka ɗan yi shuru suna ta tunanin shawarar da zasu kawo wacce zata dace da wannan aiki suke.
Kamar ba zasu ce komai ba, daga can sarki Kim Sam ya numfasa ya ce, "A gani na tunda mu huɗu ne, kamata yayi ace mun san ƙarfin kowanne daga cikin waɗannan abokan gaba namu. Misali kamar ace wanne irin aljani ko makamin yaƙi suke sarrafawa. Hakan zai bamu damar sanin abokin gabar da ya dace kowannen mu ya tunkara. Ko ya ya kuka gani?"
Boka Biu Lin ya gyaɗa kai cikin fahimta ya ce, "Wannan shawara ta ka tayi, amma abinda nake so ka fuskanta shi ne, bamu da tabbacin cewa kowa yana cikin wannan tantuna da muka nuna. Hasashe kawai muke, kada mu zo mu baiwa kowa abinda zai kaiwa hari azo a sami matsala. Da fatan ka fuskance ni?"
Sarki Kim Sam ya gyaɗa kai. Lallai ya fuskanci abinda wannan boka yake nufi. Yanzu misali a ce, boka Ruguzan ya zaɓi zai gwabza da sarki Darwazu sai yaje ya buɗe tantin, a samu matsala sarki Kuffuru ne a ciki. Kaga ƙarshen sa yazo kenan.
Boka Ruguzan ya numfasa ya ce, "Me ye zai hana mu kaiwa waɗannan tantuna gaba ɗaya hari a lokaci guda. Na tabbata idan muka haɗa ƙarfi da ƙarfe mu huɗun nan, muka farmake su alhalin basu sani ba, zamuyi cin galaba akansu ko kuma muyi musu mummunar illa.
Boka Biu Lin ya sake gyada kai. "Wannan shawara ta ka zan iya cewa, tafi ta sarki Kuffuru kyawu da kuma tsari. Kaima abinda nake so ka fuskanta shi ne, ƙarfin abokan gabar mu ya wuce muyi nasara akansu ta farat ɗaya. Kayi sani cewa a halin yanzu ma, ba abin mamaki bane idan aka ce sun san da cewa da muna biye da su!"
Koda sarki Kim Sam da boka Ruguzan suka ji wannan batu na boka Biu Lin sai suka sunkuyar da kawunan su ƙasa. Kansu ya gama ɗaukar zafi sun rasa wacce shawara zasu kawo wacce zata dace.
A daidai wannan lokaci da su sarki Kim Sam ke tattaunawa a cikin wannan tanti, acan bayan wani dutse kuwa, sarki Ayubu ne zaune a gaban wani ƙaramin aljani suna tattaunawa.
Idan mutum yasan Jizid zai ga shi ne a gaban sarki Ayubu ba wani ba. Ashe wannan rakuɓowa da sarki Ayubu yayi, dama yana so ya sami damar da zai gana da wannan aljani nasa ne.
"Meyasa sa'adda zaka fito wannan gagarumar tafiya baka tuntuɓeni ba? Shin ka san kuwa da ka so ka tafka babban kuskure da ka amince da mutanen birnin Sin farat ɗaya?" inji aljani Jizid.
Sarki Ayubu ya zaro idanu ya ce, "Me kake so ka ce? Shin sarki Kim Sam yana da wani shiri akan wannan aiki da muke yi tare?"
Aljani Jizid ya tuntsire da dariya irin tasa ya ce, "Bar wannan batu a gefe zan faɗa maka dukkanin abinda zaka yi a ƙarshen wannan tattaunawa ta mu..."
Kafun aljanin ya ƙarasa rufe bakinsa Ayubu ya haɗe fuska ya ce, "Idan ka faɗa min yanzun laifi ne?"
"Gaɓar wannan magana ne bamu zo ba," inji Jizid. "Kayi sani cewa sarki Kuffuru da mutanensa sun san da cewa kuna biye da su a baya, kuma tuni sun riga sun gama shirya muku."
Sarki Ayubu ya yi gajeriyar dariya ya ce, "Zan yi matuƙar mamaki idan aka ce sarki Kuffuru baisan da zuwanmu ba. Sannan nasan dole idan ya san da zuwan mu, nasan dole zaiyi mana kyakkyawan shiri. Abinda bai sani ba shi ne nima tuni na gama yin wani gagarumin shiri wanda yafi nasa."
Aljani Jizid ya yi ajiyar zuciyar zuciya ya ce, "Wannan shiri da kayi akan sarki Kuffurun da ka sani da ne zaiyi tasiri. Sarki Kuffuru na yanzu yafi ƙarfin dukkan shirinka, sai dai muyi masa dabara wacce idan muka yi sa'a zata iya kaimu wani keɓantaccen waje a duniya."
Cikin rashin fahimta sarki Ayubu ya ce, "Nifa ban gane abinda kake nufi ba? Wacce dabara ka shirya mana?"
Aljani Jizid ya bushe da dariya ya ce, "Bari nayi maka bayani dalla-dalla zaka fi ganewa." Sarki Ayubu ya gyara zama, shi kuma Jizid yayi gyaran murya.
"Kamar yadda ka jima kana ɓoye shirye-shiryen ka, haka shima sarki Kuffuru ya kasance. Sarki Kuffuru yana da wata rantsatstsiyar takobi guda ɗaya wacce ake kira Siwod-del-bulod.
"Wannan takobi gawurtacciya ce, tana iya samar da halittu guda talatin. Kowanne halittu daga cikin waɗannan halittu guda talatin yana da mugun haɗari wanda ya isa ya firgita mutum.
"To, a cikin waɗannan halittu guda talatin akwai waɗansu halittu guda goma da ake kira INFIROns. Waɗannan halittu da ake kira Infiro waɗansu sadaukai guda goma ne, da suka rayu a wani babban birni a kudancin duniya.
"Lokacin da za'a samar da wannan takobi aka hallaka su gaba ɗaya, sannan aka ɗauki jininsu aka haɗa sinadarin wannan takobi da shi.
"Waɗannan sadaukai guda goma gawurtattun sadaukai ne masu tsananin ƙarfin damtse da iya yaƙi har na Allah ya isa. Suna daga cikin dalilin da yasa Hasanul Jalwar bai samu nasara akan sarki Kuffuru a wancan zamani da suka gwabza yaƙi ba.
"A halin yanzu sarki Kuffuru yayi wani babban shiri da waɗannan sadaukai guda goma wanda zaiyi matuƙar girgiza dukkan wani abokin gabar sarki Kuffuru wanda ƙarfin sihirin tsafinsa bai kai yasan wannan sirri ba.
"A cikin wannan daji da suka yada zango, sarki Kuffuru da bokayensa sun kirawo waɗannan sadaukai guda goma, sun ƙaddamar da wani gagarumin shiri akan su.
"Wannan shiri nasu shi ne, kowanne ɗaya daga cikin waɗannan sadaukai an bashi fuska irinta sarki Kuffuru wadda idan mutum bai sani ba zai rantse ya ce sarki Kuffuru ne a wannan wuri.
"Duk duniya idan ban dani da aljanun da suka fi ƙarfin ifiritu babu wanda yasan da irin wannan shiri na sarki Kuffuru.
"Kayi sani cewa su sarki Kuffuru sun ƙyale muku sadauki guda ɗaya daga cikin waɗannan sadaukai guda goma, a matsayin sarki Kuffuru domin ya kawar da kai sannan ya kawar da duk waɗanda suke tare da kai.
"Tabbas koda zaku taru gaba ɗayanku ku ce za ku yaƙi wannan sadauki ba zaku iya kashe shi ba, saboda jikinsa babu tsoka da jini waɗanda zasu ya gaji a lokacin da yake fafatawa da ku.
"Sannan akwai babban sirrin tsafi a jikinsa wanda yafi ƙarfin naku gaba ɗaya. Idan muka ce wannan sadauki yafi ƙarfin sarki Kuffuru kansa bamuyi ƙarya ba.
"Tayaya kake zaton zamu ɓullowa wannan sadauki tunda mun riga mun san cewa ba sarki Kuffuru bane, sannan mun san cewa yafi ƙarfinmu?" Jizid ya ɗan yi shuru ya baiwa sarki Ayubu dama ya yi tunani.
Sarki Ayubu yayi shuru ya sunkuyar da kansa ƙasa yana tunani. A ce wanda suke tunkara yanzu ba sarki Kuffuru bane, sannan ace yafi ƙarfinsu. To tayaya zasu ɓullowa wannan al'amari?
Sarki Ayubu mutum ne mai tsananin hikima da hangen nesa, maimakon ya tsaya zurfafa tunani akan wannan tambaya da aljani Jizid yayi masa, kawai ɗago kai yayi ya kalli aljanin ya ce, "Kafun ka fara wannan bayani ka riga ka baiwa kanka amsa. Ka ce yafi ƙarfinmu amma akwai dabarar da zata iya ƙwatar mu?"
Aljani Jizid yayi murmushi ya ce, "Ina jin daɗin wannan hikima taka, shiyasa nake alfahari da kasancewa hadiminka. Kayi sani cewa yanzu su sarki Kim Sam suna can suna tattaunawa akan yadda ɓullowa su sarki Kuffuru, basu san cewa su sarki Kuffuru sun riga sun gama yi musu mugun shiri ba.
"Zan faɗa maka wannan dabara da na shirya wacce nake ganin zata ita kuɓutar da mu. A hasashena idan gumurzu yayi gumurzu wannan halitta (Infiro) zai iya amfani da wani babban ɗalasimi wanda su kaɗai (jinin Infiro) suke da shi.
"A duk lokacin da suka kira wannan ɗalasimi wata gagarumar guguwa ce take bayyana ta ɗauke su tayi jifa dasu uwa-duniya. Na tabbata idan wannan sadauki yaga babu ci a wannan yaƙi zai kira wannan ɗalasimi.
"A lokacin da kuke yaƙarsa ba'a so rantsatstsun makamai irinsu wannan mashi na sarki Kim Sam su sauƙa a jikinsa. In dai suka dira a jikinsa a take zai tarwatse ya bi iska. Saboda haka ta kowanne hali a yayin da kuke fafatawa kada ka kuskura ka bari sarki Kim Sam ya samu nasarar saran jikin wannan sadauki.
"Idan aka ɗauki kamar sa'a guda ana wannan fafatawa wannan sadauki zai iya kiran wannan ɗalasimi. Saboda haka duk yadda zaka yi, kayi wajen ganin wannan gumurzun ya ɗau lokaci.
"A hasashen da nayi idan wannan sadauki ya kira wannan ɗalasimi idan guguwa tayi jifa da shi, zai iya faɗowa a wajaje guda huɗu masu mugun haɗari.
"Waje na farko shi ne birnin Hereza dake yankin mutanen ƙabilar Nuyes.
"Waje na biyu shi ne tsaunin Rawas dake birnin Ersa.
"Waje na uku shi ne, dajin fatalwa. Wannan daji kuma babu wanda ma yasa a wace uwar duniyar yake.
"Waje na huɗu shi ne, tekun Kentauro da ake kira TAURON SI.
"Dukkanin waɗannan wajaje guda huɗu suna da mugun haɗari, musamman ma tekun TAURON SI domin kuwa waɗansu irin halittu ne a can masu gangar jiki guda biyu.
"Rabin jikinsu mutum, rabi kuma doki. Daga kunkuminsu yayi sama shi ne na mutum, daga kunkuminsu yayi ƙasa kuma shi ne na doki. Kentauron kenan."
Sarki Ayubu ya zaro idanu cikin tsananin mamaki ya ce, "Birnin Hereza! Tsaunin Rawas! Dajin fatalwa! Tekun Tauron Si! Ban taɓa jin sunan waɗannan wajaje ba amma ko a ina na faɗo a shirye nake."
Aljani Ayubu yayi murmushi ya dubi sarki Ayubu ya ce, "Idan muka yi sa'a wannan jifa da ɗalasimi zaiyi da kai ya cillaka tekun Tauron Si, ka yaƙi wani shirgegen jegari dake rayuwa a cikin tekun sannan ka sare kansa ka kawai mutanen wannan gari shi, indai kayi haka zaka bautar dasu. Bayan ka samu nasarar bautar da su zanyi maka bayanin motsinmu na gaba."
Sarki Ayubu na shirin buɗe baki ya yiwa Jizid tambaya, Jizid ya dakatar da shi da cewa, "Ka koma wajen abokan tafiyarka, don yanzu ma ka ɓata lokaci da yawa a nan."
Sarki Ayubu ya gyaɗa kai alamun ganewa, sannan ya miƙe zai koma wajen wannan tanti, amma sai ya jiwo muryar wannan aljani a kunnensa.
"Kada ka manta a yayin fafatawar ku da wannan sadauki, kada ka kuskura ka bari makami rantsatstse ya dira a jikinsa." aljanin na gama faɗin haka ya ɓace ɓat.
Sarki Ayubu yayi murmushi sannan ya nufi wannan tanti, yana zuwa ƙofar tantin yasa hannunsa ya yaye labulen da ya rufe ƙofar sannan ya kunna kai izuwa cikinta.
"A ganina mu tuntuɓi sarki Ayubu wataƙila ya kawo shawara mai kyau tunda ya kasance mutum mai tsananin hikima." sarki Ayubu ya jiwo muryar Ruguzan na bayar da shawara.
Suna ganin sarki Ayubu suka gyara zamansu sannan suka bashi waje shima ya zauna. Boka Biu Lin ya kwashe dukkan abinda suka tattauna ya zayyanewa sarki Ayubu sannan a ƙarshe ya nemi shawararsa bisa wannan al'amari.
Sarki Ayubu ya ce, "Ni dai bani da shawara sai dai ɗan gyara akan abinda boka Ruguzan ya ce. A ganin Ruguzan mu kai musu harin bazato a lokaci guda, wanda hakan zai bamu damar yi musu mummanar illa wanda zai sa muyi nasara akansu. Gyarana a nan shi ne, ba harin bazato ya kamata mu kai musu ba, kamata yayi mu fito gaba-da-gaba mu yaƙe su. Abinda nake nufi anan shi ne kamata yayi mu fara sanin a cikin wanne tanti suke kafun mu kai musu wannan hari.
"Zata iya kasancewa dukkanin su suna cikin tanti guda ɗaya sannan ace mun rarrabu mun kaiwa sauran tantunan hari, hakan zai sa su ankare da zuwanmu sannan su afka a yi gumurzu wanda a ƙarshe kowa ba zai ji daɗi ba.
"Saboda haka idan muka je wannan wuri, zan sayar da rayuwata na shiga cikin sansanin na yiwo mana leƙen asirin inda abokan gabar ta mu suke."
Koda su sarki Kim Sam suka ji wannan shawara ta sarki Ayubu sai suka amince nan take gaba ɗayansu.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, sarki Kim Sam ya sake samar da wannan jibgegen shaho nasa, ya haye kai, Ayubu ya zauna a gefensa.
Shima boka Biu Lin ya sake shimfiɗa wannan darduma tasa, da shi da boka Ruguzan suke zauna akanta ta tashi dasu sama, suka tunkari wannan hanya wacce su sarki Kuffuru suka yada zango a cikinta.
****
Yau *29/12/2022*
Babi na gaba zaizo *31/12/2022* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 64: *Azababben Yaƙi*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
UMAR SANGARU aka SARKIN SARKI
*
Tsahon kwana guda cir su sarki Ayubu suka ɗauka suna wannan tafiya sannan suka iso wannan sansani da su sarki Kuffuru suka yada zango a cikinsa. Tun daga nesa kaɗan suka sauƙa ƙasa domin kada su sarki Kuffuru su san da zuwansu.
Sarki Ayubu yayi sallama da su akan cewa zai je yayi leƙen asiri kamar yadda suka tattauna a wannan daji na baya. Sarki Kim Sam, boka Biu Lin da boka Ruguzan suka nemi gindin bishiya suka zauna suna jiran sarki Ayubu ya dawo da bayanan wannan leƙen asiri.
Babu shakku ko kuma tsoro haka sarki Ayubu ya kunna kai cikin wannan sansani, dama tun kafin su zo ya riga ya san cewa babu kowa a cikin wannan sansani face wannan mutum-mutumi na sarki Kuffuru wanda ke zaune a cikin wannan ɗaki yana jiran zuwansa.
Sarki Ayubu ya leƙa tanti na farko da na biyu bai ga komai a ciki ba, ya sake leƙa tanti na uku da na huɗu nan ma bai komai a ciki ba. Yana ganin haka, ya gyara riƙe takobinsa da kyau sannan ya tunkari ɗaki na biyar wanda yake da tabbaci ɗari bisa ɗari wannan mutum-mutumi na zaune a cikinsa.
Sarki Ayubu na ƙarasowa bakin tantin yasa takobinsa ya ɗan yage labulen da ya rufe tantin sannan ya leƙa a hankali ta cikin ɗan yagun da ya bayyana. Nan take ya hango wannan sadauki zaune a tsakiyar wannan tanti ya kafa takobinsa a ƙasa

Please Login or Register in order to submit comment