Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaske. Tabbas zaizo ya yi mana wannan aiki.
"Duk duniya babu wanda ya kai Gidr sanin yadda ake sarrafa tubali da kuma baiwar iya ɗaura gini.
"In dai ya gina mana wannan kurkuku kuma muka kulle Barban a cikinta, to, ya shiga kenan... Har duniya ta naɗe ba zai fito ba..."
Sarki Kuffuru yayi murmushi ya ce, "Wannan yafi komai sauƙi a duniya..."
Haka dai suka ci gaba da tattaunawa a wannan wuri akan yadda zasu samu nasarar zuwa birnin Bahzam wajen Gidr domin yi masa tayin wannan aiki.
Daga ƙarshe suka yanke shawarar zuwa wannan birni kai tsaye, ba tare da sun koma wajen Darwazu ba.
****
Yau *30/01/2023*
Babi na gaba zaizo *02/02/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 79: *Maharbi Oksu*
*
ALLAH KA KAWO MANA SAUƘI A ƘASAR MU NIGERIA!
*
SADAUKARWA GA MASOYAN MU...
*
U*M*S
*
Barban da Aymanul Faris basu bayyana a ko'ina ba, sai a tsakiyar unguwar Barbanul Kuyr dake cikin birnin Darul Barban. Bayan gama karɓan gaishe-gaishe daga jama'a suka wuce kai tsaye izuwa cikin gidan da Hajriya take.
Suna shigowa cikin wannan gida suka iske Hajriya da jaruma Riya suna zaune a falo suna tattaunawa. Jaruma Riya tana ganin Aymanul Faris ta ruga da gudu ta rungume shi tana mai tsananin jin daɗin sake kallonsa.
Da ƙyar Aymanul Faris ya samu ya janye jikinsa daga nata, ya je ya durƙusa a gaban mahaifiyarsa ya gaishe da ita kamar yadda ya saba.
Barban ya ja jaruma Riya gefe guda domin sanar da ita wannan tsare-tsare da suka ɓullo da shi na aikin ƙarshe.
Suka ƙyale Aymanul Faris da mahaifiyarsa kaɗai a wannan wuri domin su ma tattauna cikin sirri. Al'amarin ɗa da uwa dole akwai wani sirri wanda basa so kowa ya sani face su kaɗai.
Hajriya ta dubi ta ce, "Ɗana shin me kuka tattauna kai da Arya?"
Aymanul Faris yayi murmushi ya kwashe duk abinda suka tattauna da gimbiya Jaanu ya sanar da ita.
"Kun tattauna maganganu guda biyu masu muhimmanci: Tabbatar da ita ce Arya da kuma tambayarta akan cewa zata amince ta zamo matarka ta biyu?" inji Hajriya.
"Ta amince ita ce ARYA amma bata amince akan cewa zata zamo matarka ta biyu ba, har sai tayi tunani...?"
Aymanul Faris na jin haka zuciyarsa ta soma dukan uku-uku saboda yana tsoron kada mahaifiyarsa ta hana shi auren Jaanu.
Aymanul Faris ya gyaɗa kai a hankali alamun haka ne.
Hajriya ta gyaɗa kai tayi gajeren tunani ta ce, "Shin ka taɓa tambayarta matsayin yadda soyayyar ku zata kasance idan ka saro kan mahaifinta?"
Aymanul Faris ya gyaɗa kai ya ce, "Kwarai kuwa, ita da kanta ta bani umarnin sare kan mahaifin nata, saboda ta'addancin da yayi mana a shekarun baya." ya ƙarasa magarasa cikin sanyin murya tamkar wanda ke neman alfarma.
Hajriya ta sake yin gajeren tunani ta ce, "Ba don wannan yarinya ita ce ARYA ba, da babu yadda za'ayi na amince ka aureta saboda zuri'arta sun yi mana tabo wanda ba zai taɓa gogewa ba.
"Har yanzu wannan sharaɗi nawa yana nan; Riyalatu ita ce matar da na zaɓa ma, kuma dole ita zaka fara aura.
"Bayan tafiyar ku izuwa wannan birni, ni da Riyalatu mun tattauna akan aurenku, kuma tuni mun cimma matsaya. Kafun ka tafi nemo ruhin mai girma Samudul Ansari, zaka auri Riyalatu sannan tare da ita zaku tafi wannan kogo inda ruhin yake.
"Idan wannan yarinya ta amince zata zamo matarka ta biyu, zamu aura maka ita cikin ruwan sanyi. Kowa zai yi farin ciki. Amma idan ta ƙi amincewa, kayi sani cewa wannan lalura ta son haɗuwar jininku zata sa mu ajiye adalci a gefe, mu aura maka ita da ƙarfin tsiya."
Aymanul Faris na jin wannan batu na mahaifiyarsa zuciyarsa ta buga, gabansa yayi wani wawan faɗuwa.
Ba komai ne yasa Aymanul Faris ya ji waɗannan sauyin yanayi ba, face abubuwa guda biyu.
Abu na farko shi ne wannana aure da ake shirin ɗaura masa wanda yake daf da zuwa. Lokaci kaɗan ya rage masa ya tafi ɗauko wannan ruhi na Samudul Ansari. Tunda da zarar sun ƙwato makullin dake hannun sarki Raja sannan sun ziyarci tsoho Samazan ya sanar dasu hikayar Samudul Ansari zai tafi wannan aiki.
Idan kuwa haka ne, aurensa da jaruma Riya yan kwanaki ne kawai suka rage.
Abu na biyu shi ne ambaton cewa idan gimbiya Jaanu ta ƙi amincewa za'a yi mata dole. A halin yanzu yadda Aymanul Faris yake jin Jaanu a cikin ransa, ko Marganu bai kai shi ba. Idan aka taɓata zaiji tamkar shi aka taɓa.
Aymanul Faris bai da ikon cewa mahaifiyarsa a'a, saboda tsananin yadda yake yi mata biyayya da kuma yadda yake jin kunyarta.
Bisa dole ya amince da waɗannan sharuɗɗa nata, ba wai don yana so ba. A shirin Aymanul Faris yana so sai ya mallaki ruhin Samudul Ansari sannan yayi aure.
Abinda ya fara faɗowa a ransa shi ne, abinda babba ya hango fa, yaro bai isa ya hango ba.
Wannan yasa hankalin Aymanul Faris ya ɗan kwanta, ya san tabbas akwai abinda mahaifyarsa ta sani, wanda shi bai sani ba.
A daidai wannan lokaci ne, Barban da Riya suka sake dawowa cikin wannan ɗaki. Barban ya dubi Aymanul Faris ya yi masa inkiyar yayi sallama da mahaifiyarsa lokacin tafiyarsu yayi.
Jaruma Riya ta bi Aymanul Faris da wani irin kallo tana yi masa dariya. Tabbas ta san abinda mahaifiyarsa ta faɗa masa.
Aymanul Faris ya ɗan harareta, sannan yaje wajen mahaifiyarsa suka yi sallama. Barban ya dafa shi suka ɓace ɓat daga cikin wannan gida.
A tsakiyar fadar sarki Ranganu suka bayyana, inda suka iske shi yana zaune akan karagar mulkinsa kamar yadda suka tafi suka bar shi.
Kai tsaye suka zazzauna akan waɗannan kujeru masu fuskantar wannan karaga tasa.
Ranganu ya ce, "Sannunku da dawowa!"
Ba tare da ya tambaye su me da me suka tattauna ba, ya samar da wata taswira ta haske a jikin ƙaton bangon wannan fada tasa.
A jikin wannan taswira akwai ƙasashen duniya barkatai masu yawan gaske, wasu manya wasu ƙanana.
A jikin wannan taswira aka nuno yankin ƙasar Hindu da ƙasashen da suke ƙarƙashinta. Aka nuno wani yanki wanda ake kira Bahzam,
Ƙarƙashin wannan birni na Bahzam akwai garuruwa guda uku waɗanda suke a jere. Waɗannan garuruwa su ne: Lailuf, Maharja da Zerina.
Garin Zerina shi ne gari na uku a jerin garuruwan, dole sai mutum ya ratsa ta cikin garin Lailuf da Maharja kafun ya shiga cikin garin.
Ranganu ya nuna garin Zerina ya ce, "Wannan shi ne yankin da zakuje ku riski maharbi Oksu. Barban dole ne ka bashi kyautar taskokinka guda biyu, idan har ana so ya amince da wannan tayin aiki da kuka zo masa da shi.
"Barban da kai da Aymanul Faris zakuje wannan wuri, sannan a matsayin Barban zaka je, ba'a matsayin Hodon ba.
"Har ku je wannan wuri babu abinda zaku haɗu da shi na haɗari. Idan babu mai tambaya a cikin ku, zaku iya tafiya na sallame ku."
Caraf Barban ya ce, "Idan muka ɗauko wannan maharbi, kai tsaye zamu wuce birnina mu ɗauko Riya ko kuma zamu zo nan wajen ka?"
Aljani Ranganu yayi guntun murmushi ya ce, "Nan za ku zo mana. Ba zamu ɗauko Riya ba, har sai mun gama tsuma maharbi Oksu a cikin tsumin tsafinmu mai ƙarfin gaske." Ranganu ya amsawa Barban a taƙaice.
Barban ya gyaɗa kai cikin fahimta ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Shin kana da tambaya, ko kuma zamu tafi?"
"Ance wannan sarki da zamu kaiwa farmaki a birnin Hindu yake, sannan wannan gari ma (Zerina) da zamuje shima a yankin birnin Hindu yake, shin wannan sarki ba zai san da zuwan mu ba har ya ɗauki mataki?" Aymanul Faris ya tambayi Ranganu.
Ranganu ya yi murmushi ya ce, "Akwai abinda muka sani wanda ku baku sani ba, sannan babu buƙatar mu sanar da ku. Idan lokaci yayi ku da kanku zaku sani. Tambaya bata da wani amfani a yanzu."
Barban na jin haka ya risina a gaban Ranganu sannan ya dafa kafaɗar Aymanul Faris suka ɓace ɓat daga wannan waje.
A tsakiyar wani gabjejen ƙaton daji suka bayyana wanda yake cike da gabza-gabzan itace. Barban ya tafa hannayensa sau biyu, waɗansu ingarmun dawakai suka bayyana, ya hau guda ɗaya, ya baiwa Aymanul Faris guda ɗaya.
Suka yi ta kutsawa ta cikin wannan daji a hankali, ba tare da suna gudu ba.
Aymanul Faris ya dubi Barban ya ce, "Me aljani Ranganu yake nufi da kaje a matsayin Barban, ba Hodon ba? Shin ku biyu ne masu kama ɗaya, kodai juyewa kake izuwa siffa dabam-dabam."
"Wannan abu ne wanda bai shafe ka ba, gaba kaɗan zaka san komai..." Barban ya baiwa Aymanul Faris a taƙaice.
"Kayi wata tambayar amma ba wannar ba..." inji Barban.
Aymanul Faris yayi gajeren murmushi ya ce, "Wai shin ya ya batun wannan taswira da su sarki Kuffuru suka samar? Shin a halin yanzu suna wanne waje?"
Barban ya ce, "Wannan taswira tana nan amma baza su fara aiki da ita ba, face sun gina min wata gawurtacciyar kurkuku wadda zasu tsare ni a cikinta. Sun je ɗebo ƙasar wannan kurkuku ne shiyasa kaga sunyi shuru basa motsi amma yanzu suna daf da kammalawa, muma muna daf da kammala ayyuka shida 'wajibabbu'"
Cikin rashin fahimta Aymanul Faris ya ce, "Ban gane me kake nufi ba, shin ka san da cewa suna gina maka kurkuku sannan ba zaka ɗauki wani mataki akansu ba? Baka ji ance 'ɗan hakin da ka raina zai tsone maka ido ba?'"
Barban ya bushe da dariya ya ce, "Ɗaukar mataki? Ai inda ace ban shirya musu ba, da babu yadda za'a yi na gano wannan shiri nasu. Kada ka damu lokacin da zamu rabu ya kusa, kai da matarka za ku je ɗauko wannan ruhi."
A gigice Aymanul Faris ya dubi Barban ya ce, "Me kace? Kana nufin su sarki Kuffuru zasu kama ka kenan?"
Barban ya sake bushewa da dariya ya ce, "A kama ni? Duk duniya akwai wanda yake da izzar iya tsayawa a gaban jikan Anbalu da niyyar yaƙi? Ni Hodon nafi ƙarfinsu!!!"
Aymanul Faris yayi shuru saboda Barban ya gama saka shi cikin duhu. Wani lokaci ya ce sunansa Barban, wani lokaci ya ce Hodon, wai shin wanne ne na asali?
Gaba ɗaya maganganun da yake yi akwai rikitarwa, wani lokaci sai ya nuna kamar zasu iya kama shi, wani lokaci kuma sai ya nuna yafi ƙarfinsu.
Koda Aymanul Faris ya fuskanci cewa idan suka ci gaba da tattauna irin wadannan maganganu an dinga barinsa cikin duhu kenan sai ya kawar da maganar.
"Ya labarin sarki Ayubu? Shin ya samu abinda yaje nema a birnin Sin?" Aymanul Faris ya tambayi Barban.
Barban ya fara bayani, ba tare ya kalli Aymanul Faris ba. "Sarki Ayubu ɓatacce ne, yanzu yana wani waje a duniya mai mugun haɗari..."
"Kana nufin zai iya rasa rayuwarsa kenan?" inji Aymanul Faris kamar wanda baya so sarki Ayubu ya mutu a wani waje daban, ba tare ya sare kansa ba.
"Waye ya sani?" inji Barban a taƙaice.
Haka dai suka ci gaba da tafiya a cikin dazuzzuka Aymanul Faris yana ta yi masa tambayoyi, har suka kusan shafe sa'o'i biyu suna tafiya.
Abinda Aymanul Faris ya fuskanta shi ne wannan tafiya da suka yi mai tsahon gaske ce, dukda cewa dawakan nasu a hankali suke tafiya amma suna cin zango mai nisan gaske.
Sa'o'i biyu na shuɗewa suka shigo cikin wani yanki wanda Aymanul Faris bai taɓa zuwa ba, iya tsahon rayuwarsa.
Fasalin gidajen mutanen, yanayin kayan da suke sakawa, al'adunsu da komai Aymanul Faris bai taɓa gani ba.
"Mun shigo yankin ƙasar Bahzam" inji Barban.
Yana faɗin haka ya ja linzamin dokinsa ya tsaya cak! Aymanul Faris yayi koyi da shi. Barban ya baiwa Aymanul Faris sauƙa daga kan wannan doki, a lokacin da shima ya sauƙa.
Suna sauƙowa daga kan dawakan, Barban ya doki bayansu da tafukan hannayensa. A take suka zamo haske suka ɓace ɓat.
Barban ya dafa kafaɗar Aymanul Faris ya shafi suturar dake jikinsa, nan take wannan sutura ta juye izuwa irinta waɗannan mutane. Shima Barban tuni tasa ta riga ta juye.
Idan ka gansu a cikin waɗannan mutane ba zaka iya bambance su ba, saboda sun riga sun saje.
Barban ya wuce gaba Aymanul Faris ya biyo shi a baya, suka danna kai cikin wannan gari.
Ba su yi nisa suna tafiya ba, suka hango sojojin wannan gari sun kamo waɗansu mutane guda biyu. Budurwa da kuma tsoho tukuf.
Su Aymanul Faris ba su gane ko su wane ne aka kamo ba, saboda an saka musu baƙaƙen huluna an rufe fuskokinsu.
Barban da Aymanul Faris suka tsaya a gefe guda, waɗannan sojoji suka zo suka wuce, ko kallonsu ba su yi ba.
Barban yana kallon waɗannan mutane guda biyu, ya shaida su. Domin kuwa babu abinda yake ɓuya daga idanunsa.
Sojojin suna wucewa Barban da Aymanul Faris suka ci gaba da tafiya abinsu. Har suka fice daga cikin wannan gari na farko.
A cikin gari na biyu basu tsaya wani kalle-kalle ko dube-dube ba, suka fita daga cikinsa suka shigo cikin gari na uku wato garin Zerina inda maharbi Oksu yake.
Bayan tambaya da kwatance suka gano inda gidan wannan maharbi yake. Cikin gaggawa suka ƙarasa ƙofar gidan.
Gida ne ƙaton gaske wanda aka yiwa dogon gini, a saman katangar gidan akwai wani tulu wanda aka kafa kibiya tana yawo akansa alamar sarkin-baka.
Akwai masu gadi guda biyu tsaye a ƙofar wannan gida, suna riƙe da dogin kibiyoyi masu tsananin tsini sun tare bakin ƙofa.
Kai tsaye su Barban suka ƙarasa inda waɗannan masu gadi suke. Masu gadin suka yi gaggawa suka sha gabansu.
"Su wane ne ku?" inji ɗaya daga cikin masu gadin a cikin harshen Hindu.
Barban ya yi murmushi ya yiwa mai gadin kyakkyawan kallo ya ce, "Wajen mai gidanku muka zo, shin yana nan ne?"
Kalma na gugan kalma, haka wannan mai gadi yaji wannan magana ta Barban tamkar umarni aka bashi wanda dole ne ya bayar da amsa.
"Eh, yana nan!" inji mai gadin.
Barban ya dubi ɗayan ya ce, "Kaje ka ce ana masa sallama a waje!"
Sai dai kafun wannan mai gadi ya cika wannan umarni da Barban ya bashi suka jiwo gyaran murya daga zauren wannan gida, alamar mai gidan yana fitowa.
Waɗannan masu gadi suka yi sauri suka koma bakin wannan ƙofa suka tsaya kamar yadda suka saba.
Jim kaɗan Oksu ya fito daga cikin wannan gida suka kalle shi.
Mutumin dogo ne sannan siriri ne. Yana da zaratan hannaye da tsaho mai ban al'ajabi. Giran idanuwansa a haɗe suke da juna sannan baƙaƙe ne sidik tamkar idanuwansa.
Yana sanye da farar riga wanda aka yiwa babban tsagu daga kunkumi zuwa ƙasa.
A gadon bayansa kuma, yana rataye da wata zabgegiyar kwari da baka mai ɗaukar hankali.
Tun daga nesa ya ƙurawa Aymanul Faris idanu ko ƙiftawa baya yi, tamkar wanda yaga wani abin al'ajabi wanda tunda yake a rayuwarsa bai taɓa gani ba.
Barban da Aymanul Faris suka ƙame a waje guda, har ya iso inda suke idanuwansa na tsaye cak akan Aymanul Faris.
Yana zuwa ya rungumi Barban kamar wanda yaga wani ɗan uwansu na jini. Yana gama rungume Barban ya ɗan risina a gaban Aymanul Faris ya miƙa masa hannu suka yi musabaha.
Wannan abu yayi matuƙar baiwa Aymanul Faris amma saiya bar abin a cikin ransa baice komai ba.
Oksu ya shige gaba suka biyo shi a baya, suka shigo cikin wani ƙasaitaccen falo. Oksu ya nuna musu wasu kujeru suka zazzauna.
Ya kirawo matarsa ya bata umarnin haɗa musu abinci mai kyau. Tana fita shima ya nemi waje ya zauna, ya dubi su Barban ya ce, "Koma mene ne ke tafe da ku nasan babba ne, tun da naga kun taho tare da Tau'rin kansa?
"Ku sanar da ni mene ne abinda ke tafe da ku..." Yana magana yana kallon Barban, kamar matsayinsa bai kai yayi magana da Aymanul Faris ba.
Barban ya ce, "Da wani gagarumin aiki muka zo maka wanda ladansa zai kasance kyautar taskokin dukiyata guda biyu..."
Oksu ya zaro idanu cikin mamaki, iya daɗewarsa yana wannan aiki, bai taɓa samun mai tsadar wannan ba. Saboda haka yayi sauri ya ce, "Wanne irin aiki ne?"
Kai tsaye Barban ya ce, "Inuwowin sarki Raja muke so ka kashe mana su daga nesa..."
Bai ƙarasa rufe bakinsa ba, Oksu ya miƙe tsaye a fusace ya ce, "Wannan zancen banza ne! Kana tunanin zanyi wannan ganganci akan dukiyar da kazo min da ita?
"In dai aka harbe inuwowin sarki Raja yasan cewa ni ne kaɗai zan iya hakan, duk faɗin duniya. Saboda haka fansar da zai ɗauka nima zata shafe ni."
Barban ya yi murmushi ya ce, "Wannan ita ce damuwarka? Kwantar da hankalinka shima Raja ɗin ba zai tsira ba..."
Oksu ya girgiza kai ya ce, "Na yarda cewa zaku iya kashe Raja tunda ku na tare da Tau'rin... Ammafa ku sani cewa, Tau'rin ɗin ba zai iya kashe Raja ba, har sai ya gama cika asalin Tau'rin ɗinsa!!!"
A wannan lokaci ne Aymanul Faris ya saka baki a cikin wannan magana ta su. "Zan iya..." shi ne kawai abinda yace.
Oksu na jin haka ya ɗan lafa sannan ya nemi waje ya sake zama suka fuskanci juna.
"Tun da Tau'rin ya furta da bakinsa cewa zai iya, lallai zai iya ɗin. Saboda haka na amince... Ina ladar aikina, kunsan cewa bana fara aiki face an biya ni..." inji Oksu.
Barban yayi murmushi ya fiddo waɗansu kubobi guda biyu daga cikin jakarsa ya miƙawa Oksu, Oksu ya karɓe su ya saka a aljihu. Babu buƙatar a sanar da shi su ne ko ba su bane saboda sanin muhimmanci waɗanda suke gabansa.
Barban ya sanar da shi dukkan tsare-tsaren yadda wannan farmaki zai kasance.
Idan sarki Raja ya fito wannan rangadi izuwa garin Duhamul, wannan maharbi zai kwanta a waje mai nisan zango, sannan ya harbe wadannan inuwowi na sarki Raja.
Yana harbe waɗannan inuwowi Aymanul Faris da jaruma Riya zasu afkawa dakarun sarkin da yaƙi.
Suna gamawa da dakarun sarkin, zasu afka masa da yaƙi su sare kansa sannan su ɗauki wannan makulli.
Oksu yana jin wannan shiri nasu ya amince nan take, saboda ya gama gamsuwa da shirin yasan dole zasu yi nasara.
A daidai lokacin ne wannan mata tasa ta dawo ɗauke da farantin abinci, ta ajiye musu sannan ta fice.
Oksu yayi musu bismillah suka kimtsa cikinsu sosai. Oksu ya miƙe yaje ya sanar da matarsa wannan tafiya da zaiyi, sannan ya kammala dukkan kimtse-kimtsen da suka kamata.
Yana kammalawa ya dawo inda su Barban suke, ya shaida musu cewa ya shirya tafiya.
***
Yau *02/02/2023*
Babi na gaba zaizo *04/02/2023* da izinin ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 80: *Tsumin aljani Ranganu*
*
SADAUKARWA GA MASOYAN MU...
*
@umarsangaru
*
Oksu ya shige gaba Barban da Aymanul Faris suka take masa baya, suka fito daga cikin wannan gida nasa sannan suka nausa cikin gari. Oksu ya soma basu wani labari.
"Jiya aka fafata gumurzu a wannan birni namu tsakanin wani taƙadarin jarumi da wata halitta wadda muke tsammanin mutum-mutumi ce. Wannan gumurzu ya janyo asarar dukiya da rushe-rushen gidaje a wannan birni wanda har ta kai ga an rasa rayukan mutane huɗu."
Barban ya dubi Oksu ya ce, "Shin dama wannan jarumai a wannan gari naku suke ne, ko kuma zuwa suka yi?"
Oksu ya ce, "Wannan shi ne abinda kowannenmu yake so ya sani, amma dai akwai ragowar mutane guda biyu waɗanda basu gudu ba, kuma tuni sarki ya tura sojojinsa sun kamo su!"
"Ah! Jaruman guduwa suka yi kenan?" Barban ya tambayi Oksu.
Oksu ya ce, "Abinda mu ma kanmu bamu sani ba kenan. Muna daga can nesa saman bene muna hango wannan gumurzu nasu, daga bisani muka ga guguwa mai ƙarfi ta bayyana a wannan wuri wadda ta hana mu ganin komai.
"Guguwar tana ɓacewa muka neme su muka rasa, mutanensu guda biyu kawai muka tarar. Waɗanda tuni suna hannunmu domin a gudanar da bincike akansu daga bisani a yanke musu hukunci..."
A wannan lokaci Aymanul Faris ya saka baki cikin tattaunar tasu sannan ya sauya mata akala. "Mene sirrin wannan baiwa ta ka ta ƙwarewa a harbi?" ya tambayi Oksu.
Oksu ya yi murmushi ya ce, "Kakana sarkin-baka ne, babana sarkin-baka ne, nima sarkin-baka ne. Duk faɗin duniya babu wanda ya kai zuri'armu iya sarrafa kwari da baka..."
Yana zuwa nan a zancensa ya fiddo bakan dake ɗaure a gadon bayansa ya nunawa Aymanul Faris.
Baka ne ƙato wanda aka ƙera daga ƙarfen tagulla. Yana da igiyoyin harbi guda uku, waɗanda zasu baiwa mutum damar harba kibiyoyi uku a lokaci guda.
"Kaga wannan bakan?" inji Oksu. "Kakana ne ya samota a ƙarƙashin wani ƙaton teku a wajen sarkin-ruwa.
"Indai ɗan zuri'armu ya riƙeta zai iya harbo abinda yake nisan tafiyar zango goma sha biyar saboda tsananin saitinta da kuma ƙarfin gudun kibiyoyinta.
"Komai girman halitta walau dabba ko dodo indai muka harbeta da wannan kwari da baka ta ta ta ƙare."
Haka dai suka ci gaba da tafiya a cikin waɗannan garuruwa Oksu yana basu labarin magabatansa, lokaci-lokaci kuma yana wasa wannan kwari da baka nasa.
Har dai suka fice daga cikin waɗannan garuruwa guda uku, suka shiga cikin daji.
Barban ya tafa hannayensa sau uku, lamarin da yasa dawakai guda uku ingarmu suka bayyana.
Kowannensu ya hau guda-guda sannan suka ci gaba da tafiya a hankali.
Idan ka gansu zaka ga suna tafiya a hankali, a hankali ammafa suna cin zango.
Suna cikin tafiya suka iso gindin wani ƙaton tsauni mai tsahon gaske. Oksu ya ɗaga kansa sama ya hanga, sannan ya dubi su Barban yayi murmushi ya ja linzamin dokinsa ya tsaya.
Barban da Aymanul Faris suka tsayar da dawakansu suka dube shi, suka ce, "Lafiya?"
Oksu ya yi murmushi ya nuna saman wannan dogon tsauni ya ce, "Waɗancan dabbobin nake so, na harbo muku domin nuna muku wannan baiwa ta wa..."
Barban da Aymanul Faris suka ɗaga kansu sama inda suka hango waɗansu dabbobi yan mini-mini a can saman tsaunin, saboda tsananin nisan dake tsakanin saman tsaunin da ƙasansa basa iya shaida waɗanne irin dabbobi ne.
Barban ya ce, "Haba zo mu tafi kawai, dabbobin da ko shaida su bamayi, ta ya ya kake tunanin zaka iya harbo su?"
Oksu ya yi dariya ya ce, "Sa'an nan ban cika sarkin-baka ba kenan? Ku tsaya ku gani mana."
Yana gama faɗin haka ya zaro bakan dake rataye a gadon bayansa, sannan ya fiddo kibiyoyi guda biyu ya ɗana akan bakan.
Ya ɗagata sama ya saita saman wannan tsauni daidai inda dabbobin suke. Ya rufe idonsa guda ya kara bakan daidai ɗaya idon nasa buɗaɗɗe.
Tsahon daƙiƙu goma sha biyar kacal, kafun ya saki harbi.
Cikin wani irin gudu mai kama da na walƙiya waɗannan kibiyoyi guda biyu suka fice daga cikin wannan baka, suka yi saman tsaunin.
Tun su Aymanul Faris suna hango su, har suka ɓace ɓat!
Jim kaɗan kuma waɗansu manya-manyan damisoshi guda biyu suka faɗo ƙasa daga saman wannan tsauni. Ga kibiyoyin Oksu sossoke a jikinsu.
Oksu ya yi murmushi

Please Login or Register in order to submit comment