Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kama wadda ta taimaka mana muka kawo wannan matsayi wato masoyiyarka Firziyya ya kulleta a kurkuku ana ta gana mata azaba.
"A yanzu koda mun je inda yake, ba zamu iya hallaka shi ba, saboda haka tsarin yake, mutum ma'aboci aljani dole sai an fara kashe aljaninsa, kafun a kashe shi. Muddin aka ce bai sadaukar da aljanin ba."
Marganu ya haɗe fuska cikin ɓacin rai ya ce, "A ina zamu sami aljani Djinn domin mu ga bayansa?"
Isika ya yi murmushi ya ce, "Ayyuka guda biyu muke da a gabanmu - na farko kashe Djinn, na biyu kuɓutar da matarka ta gobe gimbiya Firziyya. Wanne zamu fara tunkara a yanzu?"
"Dukkan biyu," inji Marganu. "Mu je dajin Djinn mu hallaka aljani Buƙalshiyyu Djinn sannan mu wuce wannan gidan kurkuku mu ɗakko Firziyya."
Yana gama faɗin haka ya fice daga cikin wannan kogo, Isika ya take masa baya.
Suna fitowa daga cikin wannan kogo, Marganu ya dafa Isika, jikinsu ya rikiɗe ya juye izuwa haske sannan suka cilla sama cikin gajimare, suka tunkari dajin Djinn domin kawo ƙarshen Djinn.
***
Tun sa'adda Marganu ya ɗauki alwashin kashe aljani Djinn, daga wannan lokaci Djinn keta lura da duk wani motsinsa. Wannan na daga cikin dalilan da suka sa aljani Djinn ya daina bayyana wajen sarki Kuffuru domin a kullum idanuwansa na tsaye akan Marganu.
Zaka iya cewa tun sa'adda Marganu ya ƙaddamar da Isika a matsayin hadiminsa, idanuwan Djinn suke kansa.
Buƙalshiyyu bai taɓa tsammanin cewa Marganu zai iya mallakar takobin tarwatsa-komai ba, balle har ya sha tsumin boka Rohishmu dake cikin tukunyar Ilumni.
Djinn yayi tsammanin irin haka zata iya faruwa saboda haka tuni ya fara shiryawa. Yafi kowa sanin illar takobin tarwatsa-komai saboda musamman domin shi aka halicci wannan takobi.
A wannan rana da ya kalli Marganu na tunkaro wannan daji da yake, sai yayi murmushi ya shiga cikin kogon da yake barci ya ɗauko wani ƙullin magani.
Ya je ƙuryar gabas na wannan daji ya binne, sannan yaje yamma, kudu da arewa duk ya bibbinne.
Yana gama hakan ya koma cikin wannan kogo ya ɗauko wani ruwan tsumi ya kwankwaɗe, sannan ya koma tsakiyar wannan daji ya zauna yana jiran zuwan Marganu.
Tun da safe yake jiran zuwan Marganu, amma sai can da yamma Marganu da aljani Isika suka sauƙo cikin dajin.
Isika ya dubi Marganu ya ce, "Ni kam zan tafi, saboda bani da ƙarfin tsayawa a gaban wannan Ifritu dangin duwatsu."
Marganu ya yi murmushi ya ce, "A duk lokacin da nake son ganinka, zan kira ka..."
Isika ya risina sannan ya ɓace ɓat!
Marganu ya gyara ɗaura takubbansa, sannan ya fara kutsawa ta cikin wannan daji na Djinn.
Abin mamaki, tsahon daƙiƙa ɗari da tamanin yana yawo a cikin wannan daji amma baiga komai ba. Babu aljani Djinn babu alamunsa.
Mutum zai iya cewa mene ne dalilin da yasa Marganu bai ga aljani Djinn ba, dukda cewa yana tsaye a tsakiyar wannan daji?
Amsar wannan tambaya ita ce, wannan tsumi da Djinn yasha a cikin kogon da yake barci. Wannan tsumi nasa, hawainiya guda dubu ana narkar sannan aka juyar da jikinsu izuwa ruwa, aka ƙara da ɗalasiman tsafi masu girman gaske aka haɗa wannan tsumi da shi.
Saboda haka duk wanda yasha wannan tsumi jikinsa zai saje da kalar wurin da yake. Wannan shi ne dalilin da yasa Marganu bai kalli aljani Buƙalshiyyu Djinn ba.
Tun da Marganu ya shigo wannan daji, Djinn ya bishi da kallo kawai cikin nutsuwa.
Babban kuskuren da Marganu yayi shi ne, bai ƙaddamar da idanuwansa na haske waɗanda suke ganin komai ba.
Koda Buƙalshiyyu Djinn ya fuskanci cewa Marganu baya kallon shi, sai yayi murmushi sannan ya nufi ƙuryar gabas inda ya binne wannan magani.
Sautin murmushin nasa ya fita tamkar ƙarar ƙaramar aradu, Marganu na jin haka ya fara waige-waige yana ta dube-dube.
Djinn na ganin haka yayi sauri ya ƙarasa inda ya binne wannan magani, don kada yayi jinkiri Marganu ya ƙaddamar da idanuwansa na haske.
Djinn ya kunna wuta a daidai inda ya binne wannan magani, sannan ya ɓace ya bayyana a sauran waɗannan ƙuryoyi su ma duk ya kunna musu wannan wuta.
Wani irin jan hayaƙi ya soma tashi a cikin wannan daji, wanda ya gauraye ko'ina da ina na wannan daji.
Aka daina ganin komai idan ba wannan jan hayaƙi ba.
Wannan jan hayaƙi na lulluɓe Marganu, wani irin duhu mai kama da duhun ƙarƙashin ƙasa ya shiga kansa, ya daina ganin komai.
Kafun Marganu ya ankara tuni wani irin mugun jiri ya ɗebe shi, wanda tun da yake a rayuwarsa bai taɓa jin jiri irinsa ba.
Daga wannan lokaci bai kuma san abinda ke faruwa ba, domin wannan jan hayaƙi ya gama yi masa illa.
Lokacin da Marganu ya farfaɗo daga wannan suma da yayi, sai ya tsinci kansa ɗaɗɗaure a tsakiyar wani ƙaton kogon dutse. Wannan kogon dutse shi ne inda aljani Djinn yake kwanciya yayi barci.
Babu komai a cikin wannan kogon dutse face ƙaton gado guda ɗaya, da kuma manya-manyan tukwane waɗanda aka cika su fal da ruwan tsumi.
Marganu ya hango Djinn zaune akan wata ƙatuwar kujera yana kallonsa. Wannan siffa gaba ɗaya da sassan duwatsu akan halicceta.
Wannan halitta ita ce Buƙalshiyyu Djinn, aljanin dutse.
Djinn na ganin Marganu ya farfaɗo daga wannan suma da yayi, sai ya bushe da dariyar mugunta. Ya ɗauko wata ƙatuwar tukunya wadda ruwan cikinta yake ta zaɓalɓala saboda tsananin tafarfasa.
Djinn ya watsawa Marganu wannan ruwan tsumi. Ruwan na haɗewa da jikin Marganu, kayan jikin Marganu suka sake narkewa suka bi iska.
Marganu ya rage daga shi sai wannan gajeran wando wanda bai kai ko gwiwarsa ba.
Djinn ya cika da tsananin mamaki bisa ganin wannan ruwan tsumi nasa, bai ƙone Marganu ba. Wannan ruwan tsumi da waɗansu irin sinadarai aka haɗa shi wanda yake ƙone dukkan abinda ya taɓa.
Hatimin haske dake kan damtsen Marganu ya fara haske da walwali, yana ɗaukar idanu, tamkar madubi a tsakiyar hasken rana.
Djinn na ganin haka ya gyaɗa kai, ya ce, "Tabbas ba zan iya hallaka ka ba, face na kashe hadiminka (Isika)
"Hmm, ko da ba zaka mutu ba, ai zaka sha azaba..." Yana faɗin haka ya sake ɗauko wata tukunya ya kwararawa Marganu ruwanta.
Ruwan wannan tsumi ya mammanne a jikin Marganu, tsahon daƙiƙa ɗari da arba'in kacal, kafun ya soma juyewa izuwa ƙananun kunamai.
Kan kace me, kunamai sama da ɗari sun bayyana a jikin Marganu. Hannayensa a ɗaɗɗaure suke, balle ya juyar da jikinsa izuwa haske.
Waɗannan kunamai suka lulluɓe jikin Marganu sannan suka soma harbinsa.
Jikin Marganu ya soma ɗurar wani irin ruwa mai tsananin zogi wanda yasa dole Marganu ya fara kwarara uban ihu saboda azabar tayi yawa.
Djinn ya bushe da dariya, ya koma kan kujerarsa yana kallon yadda waɗannan kunamai suke ta azabtar da Marganu.
Kafun a jima tuni Marganu ya sake sumewa, sannan dukkan jikinsa ya ɗuri ruwa.
A daidai wannan lokaci ne wani irin jan haske ya dira akan waɗannan kunamai da suka yanyame Marganu.
Jan hasken ya narkar da su gaba ɗaya, kumburarren jikin Marganu ya bayyana.
A fusace aljani Djinn ya miƙe tsaye, ya waiga baya domin ganin wanda ya ceci Marganu.
Nan take yayi arba da aljani Isika tsaye a cikin asalin siffarsa ta haske.
Aljani Isika shi ne haske, haske shi ne Isika.
Jikin Isika yana ta haske da tartsatsi tamkar farar taururuwa a tsakiyar sararin samaniya.
Djinn yayi girgiza ya juye izuwa ainihin siffarsa ta duwatsu wadda muka fara kallonsa da ita farkon haɗuwarsu da sarki Kuffuru.
Isika ya ɗaga hannunsa sama, wani irin sunduƙin haske ya bayyana a hannunsa.
Djinn na ganin haka yayi murmushi ya cizgo waɗansu tsaunika guda biyu dake gabansa, take suka juye izuwa takubba.
Djinn ya ruga da gudu kan Isika, takun sawunsa guda na haifar da muguwar girgizar ƙasa wadda take saka wannan kogo gaba ɗaya yayi girgiza tamkar zai rikito ƙasa.
****
Yau *13/02/2023*
Babi na gaba zaizo *16/02/2023*
*
Akwai chapter 85-95 akan WhatsApp - 08136093283 duk mai so yayi min magana ta can, for N300 only.RUHIN JARUMTAKA
*
Babi na 85: *'Kuyurul Samudul Ansari'*
*
***HIKAYAR SAMUDUL ANSARI***
*
Dedicated to PRINCESS ZAHRA
*
U*M*S
*
Ƙaton ɗaki ne wanda haske ya gauraye shi gaba ɗaya, daga ganin yanayin wannan ɗaki, ka san babu tashin hankali ko firgici ga duk wanda ke rayuwa a cikin ɗakin.
Anyi waɗansu irin garu masu kauri kamar na mutanen birnin Misra. A tsakiyar wannan akwai ƙaton gado da kujera guda ɗaya a gefen gadon.
Anyi wani ƙaramin teburi a gaban wannan kujera, sannan daga gefe anyi kanta ƙarami inda aka saka littatafa.
Zaune akan wannan kujera wani dattijon mutum ne, mai yawan furfura. Ya ɗaura wani littafi akan wannan teburi gefen aci bal-bal yana nazari.
Da ganin wannan mutumi, zaka gane cewa tsohon manazarci ne wanda ya jima yana bincike akan littatafa.
Duk da cewa wannan ɗaki nasa a haskake yake, amma sai da ya saka ƙananun tabarau sannan yake ganin ƙananun rubutun dake jikin wannan littafi dake gabansa.
Jim kaɗan waɗansu mutane guda uku suka bayyana a cikin wwannan ɗaki amma gefen wannan mutumi.
Abin mamaki mutanen sun kasance maza guda biyu da kuma mace guda ɗaya.
Idan ka ƙura musu ido da kyau zaka gano cewa, ba wasu bane illa Barban, Aymanul Faris da Riya su ne suka bayyana a cikin ɗaki.
Wannan tsohon manazarci ko ɗago kansa bai yi ba, balle ya kalle su. Kai kamar ma, basa wannan wuri.
Barban ya kalli Aymanul Faris da jaruma Riya ya ce, "Wancan mutumin da kuke hangowa shi ne tsoho Samazan. Ance shi ne wanda yake da cikakkiyar hikayar sarki Samudul Ansari...
"Babu wani abu a duniya da ya faru wanda wannan tsohon malami baiyi bincike akansa ba."
Barban yana zuwa nan a zancensa ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, "Barka da wannan lokaci, babban malami. A yau ga Tau'rin yazo da buƙata wajenka..."
Wannan mutumi da aka kira tsoho Samazan ya ɗago kansa ya kalli su Barban tsahon lokaci, kamar yana nazari.
Daga bisani ya ce, "Jinin Anbalu, jinin Samudul Ansari da jinin Makau, barka da zuwa kogon bincike na duniya. A wannan wuri za ka samu dukkan bayanin abinda kake so a duniya, amma sai dai ana biya da kuɗi masu tsadar gaske."
Samazan ya yi shuru ya ƙurawa Aymanul Faris idanu, tsahon ɗan lokaci kafun ya risina a gaban Aymanul Faris ya ce, "Ya kuke daga tsaye, ku sami ku zauna mana. Tau'rin da kansa zaizo wajena, ban ba shi wajen zama ba?"
Yana faɗin haka ya nuna musu wata darduma mai laushin gaske ya ce su zauna a kai. Babu musu suka zazzauna akan ta.
"Bayani ko hikayar waye kuke so?" ya tambaye su.
Barban ya ce, "Hikayar babban sarki Samudul Ansari..."
"Hmm," Samazan ya yi murmushi sannan ya ƙare musu kallo sama da ƙasa.
"Kafun mutum ya sami hikayar Samudul Ansari sai ya cike sharuɗɗa guda uku..." Tsoho Samazan ya ci gaba da bayani.
Yana zuwa nan a zancensa ya binciko wata tsohuwar takarda a cikin wannan ƙaramin kanta dake gabansa ya miƙawa su Barban.
Barban ya karɓi wannan takarda ya warwareta, inda yaga anyi rubutu a cikin yaren Hindu.
Sharaɗi na farko: Samun Tau'rin a cikin waɗanda zasu saurari wannan hikaya.
Sharaɗi na biyu: Ƙin bayyanar da muhimman bayanan Samudul Ansari bayan an saurari hikayar.
Sharaɗi na uku: Biyan ladan wannan aiki, lu'u-lu'un kwarin Serish.
Waɗannan sharuɗɗa sune su ka sa, hikayar Samudul Ansari bata bayyana a duniya sosai ba, saboda waɗanda suka cika waɗannan sharuɗɗa basu da yawa.
Lu'u-lu'un Serish shi ne wanda Barban da Aymanul Faris suka ɗakko a birnin Askandariyya, cikin husumiyar sarki Darwazu.
Barban ya riga ya san waɗannan sharuɗɗa shiyasa aikinsu na farko ya kasance ɗauko wannan lu'u-lu'u.
"Idan kun cika waɗannan sharuɗɗa yanzu zan fara baku wannan ƙasaitacciyar hikaya mai cike da abubuwan ban al'ajabi, tausayi, gagarumar soyayya da tsantsar jarumtaka..." inji Samazan.
Barban ya matso gaban Samazan ya miƙa masa wannan takarda sannan ya ce, "Tau'rin yana daga cikin waɗanda zasu saurari wannan hikaya... Mun cika sharaɗi na farko.
"Tun kafun mu zo wannan wuri mun yi rantsuwa akan ba za mu bayyanar da muhimman bayanan Samudul Ansari ba..." Yana zuwa nan a zancensa ya saka hannu a cikin jakar tsafinsa ya fiddo wannar farar lu'u-lu'u wadda suka ɗakko a birnin Askandariyya.
"Ga cikon sharaɗi na uku... Ladan wannan aiki." Ya miƙawa Samazan wannan lu'u-lu'u.
Samazan ya yi murmushi ya karɓi wannan lu'u-lu'u ya saka a cikin wannan kanta dake gabansa sannan ya zaro wani tsohon littafi, ya saka a gabansa. Ya buɗe shafin farko ya nunawa su Aymanul Faris hoton wani sadaukin mutum dake tsaye riƙe da zabgegiyar takobi.
"Wannan sadaukin da kuke kallo, shi ne mai girma sarki Samudul Ansari..." inji Samazan.
Aymanul Faris, Barban da jaruma Riya suka ƙurawa siffar sarki Samudul Ansari idanu.
Samudul Ansari dogo ne amma baida ƙiba sosai. Jikinsa a mummurɗe yake, yana da farar fata da baƙin gashi kamar na sauran mutanen ƙabilar banu Kuyuru. Aymanul Faris yana ɗan kama da shi amma ba sosai ba.
Ganinsa a hoto kaɗai mutum zai tabbatar da cewa, yana da kwarjini da cika ido. Sadauki ne kuma kyakkyawa.
"Ku bani aron kunnenku..." inji Samazan, lokacin da yake rufe wannan littafi.
Aymanul Faris, Barban da jaruma Riya suka gyara zama sannan suka fuskanci Samazan da kyau domin sauraron wannan ƙayataccen labari.
Samazan ya fara bayar da labari kamar haka:
*TARIHIN SAMUDUL ANSARI*
Shekaru aru-aru da suka shuɗe anyi wata gawurtacciyar sarauniya a wata daula dake kudancin duniya. Wannan sarauniya tana mulkin wata babbar ƙasa da ake kira Ilam.
Ana kiran wannan sarauniya da suna ARYA.
Sarauniya Arya ta kasance kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance, mutanen birnin Ilam suna tsananin jin daɗin mulkinta, saboda tsananin adalcinta da kuma yawan kyautan ta.
Sarauniya Arya ta kasance mai yawan fita rangadi izuwa garuruwa da ƙauyukan dake yankin ƙasarta domin ganin yadda ake tafiyar da harkokin mulki.
Tun tana shekaru goma ta hau kan wannan karagar mulki, kuma tun daga wannan lokaci take wannan al'ada ta fita rangadi.
Wata rana sarauniya ta fita rangadi izuwa waɗansu ƙauyuka guda uku dake gefen wani kogi, tayi kiciɓis da wani mummunan abu.
Gawar wani mutumi suka gani kwance a gefen hanya a jefe, ya ɗebo ruwa daga kogi amma kafun ya isa ƙauye ya mutu.
Ba wai mutuwar mutumin bane ta basu mamaki, face yanayin mutuwar da yayi.
Sarauniya Arya ta bayar da umarnin a dakata, bayan an tsaitsaya ta baiwa waɗansu bayi guda biyu umarnin ɗauko wannan gawa.
Jikin waɗannan bayi na ƙyarma suka ruga inda gawar take suka ɗaukota suka kawo ta gaban sarauniya.
Gawar namiji ne. Jikinsa ya kumbura suntum sannan wani irin farin kumfa na zubowa daga bakinsa dukda cewa ya mutu.
Fatar jikinsa ta soma sauyawa izuwa kore-kore.
Sarauniya Arya ta sa aka saka wannan gawa cikin akwati sannan suka ƙarasa wannan ƙauye, wanda ake kira Huzula.
Sarkin dake mulkin wannan ƙauye ya kai sarauniya izuwa ƙaramar fadarsa suka zauna. Sarkin ya zauna a ƙasa, ita kuma ta zauna akan karagarsa.
Bayan ya gama ɗiban gaisuwa, sarauniya Arya tasa aka kawo masa gawar wannan mutumi wanda suka tsinta a gefen hanya.
Wannan sarki na ganin gawar ya ja da baya a tsorace, saboda bai taɓa ganin mummunar mutuwa irin wannan ba.
A duk bayan sa'a guda, wannan gawa ƙara kumbura take.
"Ina so a nemo masana na fannin lafiya da ƙwararrun likitoci, su gudanar da bincike akan abinda ya kashe wannan mutumin," inji sarauniya Arya.
A gigice wannan sarki ya fice daga cikin wannan fada, sannan ya shiga cikin wannan ƙauye da kansa ya kirawo likitoci guda biyu da kuma masanin lafiya guda ɗaya.
Suka dawo wannan fada sannan suka zube a gaban sarauniya Arya.
Sarauniya Arya tasa aka gabatar musu da wannan gawa, likitoci biyu da wannan masani suka zo kanta suka fara gabatar da gwaje-gwaje.
Bayan ɗan lokaci suka tabbatarwa da sarauniya Arya cewa, ba komai ne yayi ajalin wannan mutumi ba, face dafin maciji wanda su kansu basu san wanne irin maciji bane.
Sarauniya Arya ta dubi wannan sarki ta ce, "A tura mafarauta izuwa cikin dazuzzuka domin su yi farautar duk wani baƙon maciji da ya bayyana wanda babu irinsa a wannan yanki nasu."
Wannan sarki ya amsa da na'am sannan ya risina a gaban sarauniya Arya.
Da wannan sarauniya Arya ta kawo ƙarshen wannan rangadi na ta a wannan ƙauye sannan ta wuce ƙauyuka biyu dake gaba, su ma ta shaida bayyanar wannan maciji wanda ba'a san dafinsa ba, sannan ta bayar da umarnin farauto wannan maciji.
Washe gari bayan komawar sarauniya Arya izuwa ƙasarta, kimanin mutum ɗari suka yi irin wannan mutuwa.
Nan fa hankalin gaba ɗaya waɗannan ƙauyuka ya tashi saboda basu san babban abinda yake kashe musu mutane ba.
Mafi yawa daga cikin waɗanda suka mutu a gidajen su ne, kuma sun tabbatar da cewa babu wani maciji wanda ya sare su.
Al'umar waɗannan ƙauyuka suka naɗa wakilai guda goma suka tura su babban birnin Ilam inda sarauniya Arya ke mulki.
Manzanni suka je suka sanar da sarauniya Arya dukkan abinda ya faru, wannan abu yayi matuƙar ɗugunzuma hankalin sarauniya Arya domin ji take tamkar ita aka taɓa.
Sarauniya Arya ta keɓe kanta na tsahon sa'a uku a cikin wani lambu domin tayi tunani.
Mene ne abinda ke kashe waɗannan mutane, tun da ance da yawa daga cikinsu babu saran maciji a jikinsu?
Wannan tambaya ita ce ta tsayawa sarauniya Arya a rai, kuma ta ji tana buƙatar amsar tambayar dole.
Sarauniya Arya tayi hawa da kanta ta tafi ƙasar dake maƙwabtaka da nata, wajen wani babban likita wanda ake kira Abu-Sharjas.
Sarauniya Arya ta bashi kyautar dukiya mai yawan gaske, sannan ta gayyace shi zuwa waɗannan ƙauyuka guda uku domin ya gudanar da bincike akan abinda yake ajalin waɗannan mutane.
Likita Abu-Sharjas ya amince da wannan gayyata da sarauniya Arya tayi masa, shi da ita suka sake yin hawa suka dawo birninta.
Waɗannan manzanni guda goma suka yi musu jagoranci izuwa waɗannan ƙauyuka guda uku.
Suna isowa suka iske wannan abu ya sake munana, domin kuwa a wannan lokaci wajen mutum dubu ne suka mutu.
Duk cikin waɗannan ƙauyuka babu ƙauyen da ya kai ƙauyen SALWAZA jikkata saboda suna kusa da wannan kogi.
Sarauniya Arya da likita Abu-Sharjas suka wuce kai tsaye izuwa ƙauyen Salwaza, domin gudanar da kyakkyawan bincike.
Likita Abu-Sharjas yasa aka kawo gawar mutum ɗaya dsaga cikin waɗanda suka mutu, aka kwantar da gawar a gabansa.
Abu-Sharjas ya duba tafin hannun wannan gawa, sannan ya buɗe rufaffun idanunta ya duba, ya sake duba cikin bakinta.
Duk wata alama dake nuna saran maciji ne yayi ajalin wannan gawa, shi Abu-Sharjas ya gani.
Babu alama guda ɗaya dake nuna ba maciji ne yayi ajalin wannan gawa ba.
Wannan abu yayi matuƙar baiwa Abu-Sharjas mamaki domin kuwa ya bincika dukkan jikin wannan gawa, babu tabo ko inda maciji ya sari wannan gawa.
"Wannan abu akwai ban al'ajabi, domin kuwa a zahirin gaskiya yadda bincike ya tabbatar shi ne maciji ne yayi ajalin wannan mutumi amma kuma babu tabon maciji ko kuma saran maciji a jikinsa..." inji likita Abu-Sharjas.
Sarauniya Arya tana jin batun likita Abu-Sharjas jikinta yayi sanyi. A lokaci guda kuma hankalinta ya soma tashi.
Likita Abu-Sharjas shi ne babban likitan wannan daula gaba ɗaya, babu wanda ya kai shi ilimi a fannin likitanci.
A ce shi kansa ya gagara gane abinda ke sanadin mutuwar waɗannan mutane ai dole jikinta yayi sanyi, sannan dole hankalinta ya tashi saboda babban bala'i ne yake tunkaro ƙasarta.
"Gane abinda ke sanadin mutuwar waɗannan mutane sai cikakken ɗan-baiwa amma indai likitoci ne abin ya riga ya ƙure sanin mu..." inji Abu-Sharjas.
Sarauniya Arya ta ɗago kanta ta dube shi, idanuwanta cike da hawaye na alhini da baƙin ciki.
A wannan waje da suke zaune a ƙofar wani ƙaramin gida ne, wanda kana ganinsa ka san na talakawa ne.
Jim kaɗan ƙofar wannan gida ta buɗe, wani kyakkyawan saurayi ya fito daga gidan da gudu yana goye da wani mutum a gadon bayansa.
Sarauniya Arya tana yin arba da wannan saurayi, ƙirjinta ya buga da ƙarfi. Wani irin yanayi wanda bata taɓa tsintar kanta a ciki ba, ya shige ta.
Ta ƙurawa wannan saurayi idanu kawai ta gagara cewa komai, wani irin abu ya fara ratsawa ta cikin ruhinta.
Wannan saurayi ya ƙaraso inda suke ya zube a gaban likita Abu-Sharjas yana cewa, "Mahaifina ba zai mutu ba, shi kaɗai nake da a duniya... Ka ceci rayuwarsa daga wannan dafi wanda yake yawo a cikin jikinsa..."
Likita Abu-Sharjas ya karɓi mahaifin wannan saurayi sannan ya gudanar da bincike akansa kamar yadda ya yiwa sauran waɗanda aka kawo.
Sakamakon binciken nasa bai sauya ba, amma abu da ya tsaya masa a rai shi ne, ya ya aka yi wannan saurayi ya gano cewa akwai dafi wanda yake yawo a cikin jikin wannan mara lafiya wanda hatta shi kansa bai gano hakan ba?
"Ta ya ya ka gano cewa dafi na yawo a jikinsa, hatta ni kaina babban likita ban gano komai ba?" inji Abu-Sharjas.
Wannan saurayi ya ce, "Yanzu ba kwa ganin wani koren-dafi yana zarya a dukkan sassan jikinsa?"
Sarauniya Arya tayi shuru kawai tana ta kallon wannan saurayi ta gagara cewa komai.
Babban abinda ya bata mamaki shi ne, mene ne dalilin da yasa farkon kallonsa da shi ƙirjinta ya buga? Meyasa taji sauyin yanayi a jikinta sakamakon kallon wannan saurayi?
Abu-Sharjas ya ƙarewa wannan saurayi kallo sannan ya fara yi masa tambayoyi.
"Daga wanne lokaci wanne abu ya faru da mahaifinka?
"Shin ka ga maciji a cikin gidanku ko kuma wani alamu na maciji?"
Wannan saurayi ya ce, "Tun jiya da yamma muna tare da mahaifina, babu maciji ko kuma alamar maciji a cikin gidan mu.
"Daga lokacin da wannan abu ya faru da shi, shi ne lokacin da ya sha ruwan da bayin mu suka ɗebo, daga wannan lokaci na soma ganin wannan koren-dafi yana yawo a jikinsa."
Abu-Sharjas na jin haka ya ce, "Shin kai ka sha wannan ruwa da suka ɗebo ne?"
Wannan saurayi ya gyaɗa kai alamar a'a.
Abu-Sharjas ya ce, "Daga ina kuke ɗebo ruwa a wannan gari?"
Wannan saurayi ya ce, "A kogin dake bayan gari ne?"
"Mu je inda wannan kogi yake domin naga abinda ya haddasa wannan guba, wanda nake kyautata zaton daga cikin wannan kogi yake!" inji Abu-Sharjas.
Wannan saurayi ya miƙe tsaye ya juya da nufi hanyar wannan kogi, Abu-Sharjas ya take masa baya.
"Ji mana!" inji sarauniya Arya kafun su Abu-Sharjas su yi nisa. "Ina da magana da kai."
A wannan lokaci ne, hankalin wannan saurayi yaje wajen sarauniya Arya ya ƙare mata kallo, tun zuwansa wannan wuri a gigice yake.
A wannan lokaci ya gane wace ce, sannan ya gane matsayinta.
Cikin gaggawa ya ruga inda take ya zube a gabanta ya kwashi gaisuwa.
"Mene ne sunanka?" Arya ta tambaye shi.
"KUYURUL

Please Login or Register in order to submit comment